ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 5 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Cikin damuwa ta ce. “Zahra ba na son na yaudari kaina, ai kin ji abin da ya ce?. Allah ya kawo min wani cikin rayuwata da zai taimaka min”, Www.bankinhausanovels.com.ng
Dariya Zahra ta yi ta ce “Ai taimako ya ce zai yi, ba wai zai so ki ba ya ke nufi. Addu’a kadai za mu yi, don ba mu san abin da Allah ya shirya nan gaba ba”.
Rauda ta ce “Haka ne Zahra. duk na fada mata wannan. Shi ma wata Kila ya na can ya ma fi ta shiga damuwa, amma ga ta ita za ta janyowa kanta damuwa. Idan da bakya cikin ransa da ba abin da zai sa ya tuno ki har ya turo miki da saKo ya nuna miki cewa kina ransa”. Haka suka dage sai da suka kwantar mata da hankali kan abin da ya faru da ita. Dole ta saki ranta ba don ta so ba.

Kusan duk kwanan duniya sai Haana ta kira wayar Malam M.J, amma a kashe. Haka za taci kukanta ta share hawaye. Ta na cikin wannan halin kuma Sameer ya takura mata da yawan shisshigi, sai dai kuma bai fito ya fada mata abin da ya ke ransa ba, amma da ka ga yadda ya ke mata za ka fahimci neman cusa kansa ya ke a wajenta.
Kwanaki biyar da faruwar hakan. Ta na kwance a daki ta na tunani, sai kawai zuciyarta ta ke tuno mata da cewa, ba dai addu’ar Malam M.J ta ci ta ba, na cewar Allah ya kawo mata wani cikin rayuwarta da zai taimaka mata wajen gyara matsalar Zuri’arsu. . Www.bankinhausanovels.com.ng
To yau kuma ga shi Allah ya kawo Mr.Sameer, kuma ga shi ya na KoKarin duk abin da Malam M.J din ya ke yi a lokacin da suke tare
A yadda suka tsara a gobe ne zai shirya kai su Kaduna don ganin: Zuri’arsu, ita da Granny da Rauda ne za su yi tafiyar cikin sirri ba tare da kowa ya sani ba. Haka kawai ta dinga juya maganar da suka yi da Sameer da yamma.


“Raihana kina hanani lokaci da damar da nake so mu yi magana da ke mai muhimmanci. Na rasa wace irin damuwa ki ka ajiye cikin ranki. Abu biyu kawai na roKa ki bani dama, amma har yanzu kin
’ hanani, to sai yaushe ne za ki bani damar da zan san matsalarki bare kuma ni ma na fada miki tawa”.
“No Mr.Sameer, kada ka yi min mummunar fahimta ba haka nake ba. Damuwata da matsalata
ina da wanda muke tattaunawa da shi, ba kuma na so na baiwa kowa wannan damar. A kuma ganina shi kadai ya ke da wannan matsayin a zuciyata.
Kuma shi kansa bai san ina cikin wannan halin ba don ban fada masa ba saboda ya na daf da dawowa. Kuma na fi so ya dawo na fada masa. Ba kuma kowa ba ne sai Yaya Abba.
Mr.Sameer ka yi hakuri, Yaya Abba shi ne solution na dukkan rayuwata, ba na wani abu sai da yardarsa, kuma idan har na yi bai sani ba dole zan fada masa, idan ya hanani kuma dole na hanu”’.
Mikewa kawai ya yi daga inda ya ke zaune ya ce. “Shikenan tunda ni ba ni da wani matsayi Sai Ya Abbanki shi kadai. To ki je abinki insha Allah ba zan Kara yin wata magana ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya na gama fadin hakan kuwa ya sa kai ya yi wucewarsa. Mamakin wannan zafin da ta ga ya dauka, shi ne har yanzu ta ke mamakinsa. Shin ya kuwa san irin yadda suka shaKu da har ya ke kawo kansa haka?. To ya je abinsa shi ya ga zai iya.
Washe gari kuwa tun Karfe goma suka gama shirinsu, lokacin Haana ta manta ma da abin da ya shiga tsakaninsu saboda ta na doki da zumudin zuwa gaanin Zuri’arsu,
Lokacin da suka hadu da Mr.Sameer ya na dakin Granny ya.na KoKarin fito mata da kayanta. Ya na kallonta ya wani bata rai sannan ya dauke idonsa daga wajen da ta ke. nan kuwa dariya ta kama ta, sai ta kalle shi ta ce ,
“What is wrong with you Mr.Sameer, ba dai fishi ka ke yi da ni ba?. Ni na manta ma da abin da ya faru. sai da na ganka sannan ma na tuna”.
Har ya yi kamar ma ba zai tanka mata ba, sai dai ya daure ya ce
“Me zai sa ka yi fishi da mutumin da bai damu da kai ba, har zai iya cewa ba ka da muhimmanci a cikin rayuwarsa?”’Zaro idanuwa ta yi waje ta ce
“Au haka ka fassara maganar kenan?, ko kadan
ba haka nake nufi ba Mr.Sameer. ka na da matuKar muhimmanci a cikin rayuwata da kuma wani matsayai ma su tarin yawa wanda ba wanda na baiwa su face Mr Sameer. ‘ Ka ga na farko kai dan uwana ne, Abokina wanda ya ke Kokarin hadani da burina na shekara da shekaru da na rasa mai taimaka min sai kai din da ka zo. idan kana ganin ba ka da matsayi a wajena yanzu ga shi ka ji, saboda kai kadai ne wanda ya yi Kokarin sada ni da Zuri’ata a yanzu haka ma kai ni wajensu za ka yi.
Mr.Sameer akwai wanda zan baiwa wannan. matsayin da ya wuce kai da ka bani farin ciki irin wannan a rayuwata?. Ka saki ranka, na yi maka alkawarin baka ko wacce irin dama da ka ke so a wajena, sannan zan nuna maka kai din mai matsayi ne a rayuwata da zaraar na je na ga Zuri’ata a matsayin tukuicinka”.
Wani irin Kasaitacccn murumshi ya sakar mata ya ce. “Da gaske ki ke Raihanatu?”,
“Eh mana, ai ni bana magana biyu”’. Ta fada itama ta na murmushi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daidai wanann lokacin ne Rauda ta Karaso. Ganin irin nishadin da suke ciki a take ta ji zuciyarta ta yi mata nauyi, ta ke ta ji ba za ta iya jure ganinsu a irin wannan yanayin ba. Da yake babu wanda ya ganta a cikinsu sai kawai ta juya da baya.
Tunda suka shigo garin Kaduna Haana ta dinga jin wan irin nishadi ya na ratsa zuciyarta ga kuma -wani doki na son ganin sun Karasa ta ga Zuri’arsu.
Kai tsaye Unguwar Rimi suka nufa. Tunda suka shigo ta dinga jin yanayin unguwar ya na mutukar birgeta. Su na shan wata kwana daga ita har Rauda sai da suka juya suka kalli junansu tsabar tsananin mamaki. Banda da su aka yi tafiyar da sai su ce rufe musu ido kawai aka yi aka dawo da su gida.
Ba don komai ba sai don ganin gidan da suka zo ba shi da bambanci da na su Estate din, komai iri daya idan ka cire gidan da suke makwaftaka da su, hakan kawaii shi zai tabbatar musu da cewa ba nasu Estate din bane. Cikin murmushi Sameer ya juyo ya dube su, don dama su a bayan motar suke, Granny kuma a gaba, sannan yace Na ji bakin ku ya mutu, kun shiga duniyar mamaki ko?. To wannan kadan kenan daga cikin aikin Marigayi Alh Nasir Dan fillo. Ku duba sunan
Estate din da za mu shiga ku gani, duk sunan sane kamar yadda na can Kano yake
Ku bari mu shiga za ku ga tarin bambancin da ya ke da wancan, don da kanku za ku kira wanccman kango. Don haka sai ku yi Kokarin mu fara duk  abin da muka shirya daga yau’’
ShessheKar kukan Granny suka fara ji fa na cewa. “Sameer maigidana Allah ya yi maka Albarka ya kuma baka dukkan abin da ka ke nema a rayuwarka. Na godewa Allah da ya nuna min wannan rana mai dauke da farin ciki. Yau burina ya cika na tsawon shekaru masu tarin yawa”’.
Gaba daya hankalinsu ya gama tashi. Dole ta sa Sameer ya kashe motar ya koma rarrashin Granny. Nan da nan kuma Rauda da Haana suka shiga taya ta. Shi kadai ne bai yi kukan ba.
Amma ganin yadda suke kukan sai ya rasa ma wa zai baiwa baki, dole shima sai hankalinsa ya tashi. Bai sa
n lokacin da ya fara yiwa Haana da Rauda tsawa ba ya na cewa
*‘Haba don Allah, ku kuma mene ne naku na kukan?, maimakon ku tayani ba ta hakuri, sai kuma ku biye mata, kamar wadanda aka aikowa da  mutuwa”’.
Cikin alhini Granny ta ce ““Maigidana ka barsu su yi ta kukan, da na zuci nake yi, amma yau ga shi ina yin na fili tunda Allah yau ya nuna min wannan rana. Maza ka kaini wajen ‘yan uwana mu ga juna”’,
“Shikenan Granny na ji, amma don Allah ku daina wannan kukan, duk kun saka jikina ya gama yin sanyi. Abin farin ciki ne fa, ba wai wani abu ne da zai sa ku kuka ba. A haka dai ya yi nasara suka dan yi shiru.
Da ma Haana tasan irin yadda tsarin Estate din ya ke a labarin da Granny ta bata a Boye, duk sai ta ke ganin kamar a na su Estate din ta ke.
Cikin lokaci kadan labari naa zuwan Granny da jikokinta. Nan da nan kuwa gida ya cika da jama’a, iyaye maza da mata tare da yara. Da ya ke ranar asabar ce kowa ya na gida. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsananin mamaki ne da murna ya kama Haana, yadda ta ga tarin jama’a ake kuma sanar da ita cewa duk danginta ne, haka itama Rauda.
Duk mutanen da suka ga Haana sai da gaban su ya fadi, ba don a gabansu aka wanke marigayiya Aziza ba, da sai su ce ita ce don tsananin kamar ta yi yawa. Da dama daga ciki sai da suka zubar da hawaye don tuna baya da suka yi na rashin yarinya mai karsashi da shiga rai a cikin Zuri’arsu, don har yanzu ba su samu wanda aka yiwa wannan so da Kauna ba kamar su Aziza da Hameed.
Bayan komai ya dan nutsa an gama koke-koke. na tuna baya da kuma neman yafiyar juna. Daga baya kuma da iyaye maza suka zo suna gaida Granny cikin nauyi da jin kunyar abin da suka yi baya.
Haka Alh Aminu da Lukman da kuma sauran ‘yan uwansu guda biyar suka zube a gabanta cikin
kuka suna neman ta yafe musu abin da suka yi a baya a matsayinta na uwa da ta ci tudu biyu ma.
Ita ma kukan ta cigaba da yi tare da fadin ita kanta ta yi laifi da ba ta waiwaye su ba. Abokan zamanta Haj Aisha mahaifiyar Alh Ja’afar da Haj Rukayya mahaifiyar Alh Aminu, su ma ban hakuri suka shiga yi hade da nasu kukan. Duk dai ana ta neman gafara da neman a yafi juna.
Alh Aminu ya sa aka kira masa Haana da Rauda ya gafatar musu da kowa, shi kansa saida ya ji Kwalla ta cika masa ido lokacin da ya ga Haana, tabbas kamar ta da Aziza ta baci. Ya cikin bayaninsa sai kawai hawaye suka fara zubar masa. A take ya Kara yiwa Aziza da Hameed addu’ar Allah ya sanya rahama a Kabarinsu.
Ganin yadda shima ya ke kuka, sai duk su Haana da Rauda suma suka shiga nasu tare da cewa. “Abba ka daina kuka haka, Allah ne ya shirya cewa duk hakan za ta faru. Babu kuma wanda zai ja da Kaddar”.
Alh Lukman ne ya ce “Ku tashi kuje abinku Mamana, Allah ya yi muku albarka. dan anjima za mu nemeku”
– Har cikin ran Haana ta ji farin ciki yadda taga tarin nadamar da iyayensu suka yi, ai take ta ji wata Kaunarsu na shigarta tare da yi musu_fatan alkahiari. Bayan fitarsu Alh Lukman ya Kara kallon Granny ya ce.
“Umma don Allah mun yi muku laifi, kuma mun cutar da ku, don Allah a yafe mana da ni da
sauran wadanda muka yi muku laifi duk muna neman afuwarku.Grannny ta daga masa hannu ita ma cikin
hawaye ta ce, Mu komai ya wucce, tunda dai muka zo nan ai mun kori shaidan, komai ya riga ya wuce fatan Allah ya yafe mana gaba daya”,
Kowa sai da ya sake zuwa gabanta ya nemi gafara har sai da kowa ya kasance cikin farin ciki. Sannan Granny ta dora da magana.
“Ina son ku sanyawa maigidana Sameer albarka, saboda namijin KoKarin da ya yi da kuma fatan Allah ya sa wannan zuwa da muka yi ya zamo sandiyyar daidaituwar komai da kuma manta duk abin da ya faru”’Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan suka amsa gaba daya da cewar, “Insha Allah za mu yi masa. Ubangiji ya yi masa albarka tare da sauran ‘yan uwansa: Insha Allahu kuma komai ya daidaita”’.
Nan kuma Haj Aisha ta ce “Aminu kira min dan uwanka a waya ka hadani da shi’. Bugu daya a
‘ na biyun aka daga. Bayan sun gaisa ne ya ce
“Hajiya Babba ce ke son magana da kai”. Sai ya mika mata wayar. Suna gaisawa ya tambayeta ya ya jikin. Ta amsa masa da “Sai dai godiyar Allah kawai. Sannan ta dora da cewa, ina son ganinka cikin wannan satin, idan ma da hali zuwa gobe ko jibi nake so, kuma bana son musu”.
Cikin ladabi shima daga can ya amsa da “Allah ya nuna mana Haj, insha Allah za ki ganni’. Suka
yi sallama ya kashe waya. A nan kuma suka cigaba da tattauna maganganunsu ma su muhimmanci. A ranar dai kowa ya samu kansa cikin farin cikin da aka jima ba’a samu irinsa a Zuri’ar ba.
Granny da jikokinta biyu aka kuwa aka shiga karrama su, kowa so ya ke ya faranta mu su.
Cikin kwana uku da faruwar hakan sai ga Alh Ja°’afar nan shi kadai kamar yadda ya saba zuwa. Tsananin kunya ce ta kama shi da ya zo_ya ga Granny tare da mahaifiyarsa suna zaune. A nan ya ji duk batun da aka yi.
Duk da tarin girmansa da ya gama saurare Sai da shima ya zubar da hawaye tare da dumbin nadamar abin da ya faru a baya. Haka ya shiga baiwa Granny hakuri tare da dumbin nadamar abin da ya yi musu a baya ya na mai cewa “Sharrin shaidan ne da kuma zuciya”
Ganin Haana da ya yi, ya Kara sanyawa zuciyarsa rauni hade da faduwar gaba, don ganin fuskar Aziza da ya gani a tare da ita. Da sauri ya mike tare da rungumeta, suka hadu suna kuka.
Duk wanda ya ga Alh Ja’afar a wannan lokacin, Sai ya ga tsananin nadama da danasania tare dashi. — Ta ke ya dinga jin so da Kaunar dan uwansa Mustapha ya Kara shigarsa. Sai ya Kara cira kai ya dubi Granny ya ce.
“Umma ku yafe min, a yau bana jin zan iya kwana ba tare da na ga dan uwana ba ,mun hadu mun nemi yafiyar juna. Matukar ban ganshi ba, ba
zan daina jin damuwar nan da nake ji ba. A bani lambarsa na kira shi yanzu”’Www.bankinhausanovels.com.ng
Kowa da ya ke wajen sai da ya samu kansa cikin farin ciki tare da zubar da hawayen murna hadi da godiyar Allah da ya kawo Karshen wannan gaba cikin sauki, don kuwa dama shi din ake ji, tunda kuwa ya bada kai bori ya hau shikenan.
Ko da yake da dama cikinsu suna da burin hakan, amma rashin tsayar da zuciyarsu waje daya da kuma tsananin rashin kyautatawar da suka yi musu ya sanya suna jin kunyar tunkarar su.
Granny ta fi kowa jin dadin haka. Sai ta fara magana. “Alhamdulillahi. A yanzu dai ba ya Kasar nan, muna dai sa ran dawowarsa a kowane lokaci cikin satin nan, don mun dan kwana biyu ba mu yi waya ba tun da na zo nan”.
“Babu komai Hajiya, ni ma ba zan tafi ba har sai ya dawo. Ni da kaina zanje har gida na ba su hakuri shi da Mukhtar da Maryam har da Alh . Aliyu ma” Www.bankinhausanovels.com.ng
Haana da Rauda sun zama abin tararaiya a‘cikin Zuri’arsu, kowa da irin so da Kaunar da yake ba su. Haka sukejin farin ciki na Kara kamasu, sam ba ma za ka gansu tare ba saboda daga wannan ya ja wancan, sai wannan ya janye wancan sai kuwa suka dinga jin dadi.
Abin da idanun Haana ya ke mata shi ne gizo, duk wani da namiji da yake cikin zuri’arsu sai ta ga ya na yi mata kama da Malam M.J, musamman Alh

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *