JARIRI CHAPTER 2 BY AMEERA ADAM

JARIRI CHAPTER 2 BY AMEERA ADAM

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Goggo waigawa tayi jin babu wanda ya tako hanyar ɗakin domin kawo mata a gaji ta buɗe baki ta kuma magana da ƙarfi ta ce. “Jama’a ku dubeni ku dubi tsufa ku taimaka mun zai hallakani da raina, ku zo ku fitarmun da shi yau na shigesu nikam ina ganin salawaitun rayuwa” Wani uban tsalle Jaririn ya buga har sai da zanin Goggo ya ɗaga sama sannan ya fito ya cigaba da dafe ƙeya yana wani irin rangaji sannan yayi tsalle ya faɗa cikin robar wankan, ga mamakin Goggo sai ji tayi ya fara magana cikin wata iri gwarjejiyar murya kamar ta ƙaton gardi yace. “Ko da wasa naji kin buɗi baki da niyyar magana sai shaƙe  miki wuya kin mutu har lahira” Goggo buɗe baki tayi tana zaro idanu ana cikin haka su Inno suka shigo ɗakin da sauri Nusaiba ta ce. “Goggo lafiya naji kina ta kurma ihu” Inno ta hau tattaɓa kafaɗar Goggo ta ce. “Oh ni

jikar mutum huɗu Hansai ince dai wannan ɗan ƙundalon Jaririn ba wani rashin ɗa’ar yayi miki ba, dan wannan ihun ɗiban albarkar ba banza ba” Goggo ido ta zurawa Inno tana jin bayaninta sai kuma ta tuno da kashedin da Jariri ya yi mata, nuna hannu ta fara yi irin na kurame tana gunguni da baki kamar yadda kurame suke yi idan zasuyi magana.+

    Goggo nuna Jariri tayi da hannu sannan ta ɗan bankaɗa zaninta tana nuna mata, Nusaiba ta ce. “Goggo kiyi magana mana  kya dinga bankaɗa zani me zamuyi a ciki” Goggo ta kuma kallan Jaririn ta bankaɗa zani sannan ta nuna gado, sai kuma ta nuna dai-dai maƙogaronta. Inno ta rafka salati ta ce. “Yau naga abinda ya tsone idon Kakata Laure mun shigesu Hansai Kurumcewa kikayi?” Goggo kasa magana tayi ta kuma nuna Jaririn ta bankaɗa zaninta ta ce. “Ummmm ummmmm” Inno ta riƙe baki ta ce. “Hansai ban fahimci ɗiban albarka da kike nuna mun ba ta bankaɗa zani, wai ko haihuwa kike sha’awar yi” Goggo da sauri ta gyaɗa kai sai kuma ta nuna Jaririn ta ce. “Ummmm ummmmm” Inno ta ce. “Yoooooo Hansai ko sharafa kike yi ke da haihuwa ai har abada banƙi ba ko a lahira idan anayi, amma wallahi ina jiye miki tsoron ɗiban albarkar da yaron nan yayi mun yayi miki shi a cikin zanin nan da kike ta bankaɗawa.” Goggo na jin haka ta fara gyaɗa kai tana cewa. “Ummmmm Ummmm”Inno ta rafka salati tana tafa hannuwa haɗe da karkata kai ta ce. “Wannan bankaɗar ɗiban albarkar da kike mana na meye haka Hansai?” Nusaiba da takaici ya rufeta ta ajiye kayan Jaririn a kan gado ta fice daga ɗakin dan yin wanka, Inno sunkuyowa tayi ta ce. “Hansai ki dubi Allah kimun magana karfa daga wasa abu ya zama gaske dan wannan ɗiban albarkar ya fara bani tsoro” Goggo ta sauke wata ajiyar zuciya murya na rawa ta ce. “Rakiya babu komai lokaci ɗaya ne kawai naji salawaitun bakina ya ɗauke” Inno ta taɓe baki ta ce. “Wallahi keda Allah ƙarya kuma haramun ce amma duk wanda ya ƙare miki kallo yasan kina cikin halin rashin ɗa’a, wallahi badan ina duba zumuncin Allah ba da tuni na kwashe miki albarka yadda kika faɗar mun da gaba, haka kawai ki ɗora mun ciwo ki cuci ƴaƴana ki barsu da jinya suna kashe kuɗaɗe banda ma Allah ya rufa musu asiri, Kai duniya ni jikar huɗu Hamsai ina zaki bar mugun hali? Kiyi ki wanke musu ɗa kin tsaya bankaɗe-bankaɗen ɗiban albarka.” Inno ta ƙarasa faɗa tana wucewa cikin ɗakin, kamar wacce ta ga mugun abu da sauri Inno ta dafe ƙirjina tana zaro ido ta ce. “Hansai waya yiwa jika ta wannan rashin ɗa’ar da labulaye, Oh nikam yau naga abinda ya tsone idon kakata Laure anya wannan ɗanƙundalon yaron aljannu basu mulmuleshi ba” Goggo cikin suɓutar baki ta yarfe hannu gefe ta ce. “Yoo Allah na tuba ba dole kiga sabon salawaitun abubuwa ba, muna tare da Ƙunduss…”+

  (ME SAN JIN YADDA NA SAMO SUNAN ƘUNDUSS YA NEMI LITTAFINA NA ƊAN BA ƘARA🤣 WOLLAH DARIYA SAI TA KUSA SAKU FITSARI A ZAUNE)

     Da sauri Goggo tasa hannu ta rufe bakinta tana zare idanu kamar wacce tayi saɓo sabida tuno kashedin da jariri yayi mata, Inno ta dafe ƙirji ta ce. “Allahu Akabar kabiran Alhamdulillahi kema ya nuna miki ɗiban albarkar ko” Goggo da tayi fiƙi-fiƙi da idanu ta ce. “Waye kuma?” Inna ta keɓe baki ta ce. “Ina ce da wannan ɗan ƙundalon kike?” Goggo da sauri ta ce. “Nina gaya miki wallahi karki zabga mun sabuwar salawaitin ƙarya ido biyu, abinda baki sani ba wannan Jaririn ya fi mun ke sau dubu” Inno ta zaro ido ta ce. “Jaririn da kika sani jiya-jiya shine ya fini a gurki saboda ɗiban albarka” Inno ta fara matsar ƙwallanta ce. “Yanzu saboda uban yaron nan na da abun duniya ko Hansai?” kafin Goggo tayi magana Halifa ya shigo cikin ƙananan kaya ba ƙaramin kyau yayi ba, Inno washe baki tayi tace. “Halifun har an fito” Halifa yace. “Goggo wai har yanzu ba’ayi masa wankan ba? So nake fa na kaisu asibitin nan da wuri inasan na shiga office da wuri”

   Goggo ta ce. “Au dan ƙaddara yanzu Halifa sai munje asibitin nan bazaka haƙura ba?” Inno ta kalleshi a watse ta ce. “Yoooo ina zai haƙura yana fama da idanun rashin ɗa’a a tsaye-tsaye bishiyar kuka, Ni bansan sanda yahudu ya lalata mutane ba ace wai Jariri ma sai anyi masa BBC wannan ɗiban albarka har ina? da ruwan zafi zaiji ko da allurai sai kace sanda na haifi ubansa allurar akayi masa, kuma uban me ya same shi Allah ba tuba kowane kibibabbe ya yi ɗiban albarkarsa ya gama.” Nusaiba ce ta shigo ɗakin da tawul a jikinta ta fito daga wanka ta tsaya jin abinda su Inno suke faɗa.

    Inno kallan Nusaiba tayi tana jan dogon salati tana tafa hannu ta ce. “Nusaiba yau sabon ɗiban albarkar da zaki mana kenan wai ke me miji kin fito gandandan kinyi tsaye kina rangaji a gefensa cikin kissa, bakisan kin haramta agaresa ba, anya Nusaiba zamu iya zaman kwana arba’in a gidan nan kuwa, ummm Allah na tuba nima banda abu na me zan zauna yi a gidan yara tsofai-tsofai da ni, bari ma nayi wanka na kira Salisu yazo ya ɗauke ni ya maidani gida bakina alaikum.”

    Halifa ya tsuke fuska yace. “Inno wai ya kuke neman haramta mun mata ta ne ina ji ina gani, gaskiya nifa sa idon ku yayi yawa wallahi kawai dan ta fito daga wanka ta tsaya kusa dani shikenan ba matata bace?” Halifa ya ƙarasa Faɗa yana rungumo Nusaiba har tawul ɗin jikinta na niyyar faɗuwa, da sauri Inno da Goggo suka saki wani uvan salato lokaci ɗaya Inno har tana runtse ido Goggo ta ce.

     “Oh yau naga abinda zai ƙonemun idani ni  Hafshe yau na shiga uku Allah na tuba Alla ka yafe mun” Inna daɓar ta zauna kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki tana zubda hawaye ta ce. “Allah mun tuba nida ƴar uwata kana ganin bamu da laifi a ciki,  kai jama’a Allah ka yafemu ni ƴasu yau naga takaina Halifa ashe ɗiban albarkar taka takai haka, wallahi nan dai ba gidan zama bane na rantse da Allah kuyi gaggawar tuba kar fushin Ubangiji ya tabbata akanku sakarkaru marasa ɗa’a” Inno na gama faɗa ta bankaɗa zaninta cikin kajarta ta zura hannu ta ɗauko waya ta miƙawa Halifa ta ce.

   “Maza maza kiramun Ubanka tun fushin Allah bai sauka a kanmu ba” Halifa ya tsuke fuska yace. “Bazan kira ba ke ki kirashi mana, ke Nusaiba idan bazasu yi masa wankan ba ki karɓa ki masa ki shiryashi mu tafi asibiti, na lura waɗannan tsofaffun nan gaba kafurtamu zasu fara yi” yana gama faɗa y
a fice.

   Inno ta rushe da matsanancin kuka ta ce. “Wallahi duk waɗannan maganganun rashin ɗa’ar ka gayawa ubanka Salisu Hansai ki wanke musu ɗa mu wuce dan baza’a dinga aikin kafurci a gabana ba”

    Goggo taba ɗau lokaci ba ta wanke Jaririn ta tsane shi a towel ta kwantar da shi akan gado Inno sai aukin danna wayya take, ita dai taga lamba amma batasan ko ta wa ta kira tana ji an ɗaga ta ce. “Salisu duniya da lahira waya halicce mu?” daga cen ɓangaren akace “Allah” Inno tace “To wallahi Idan baka maza kazo ka ɗauke mu daga gidan nan ba sai na ɗebe maka albarka, saboda gidan Halifa sam ba gidan zaman musulmi na gari bane, nikam wallahi har azumi sai nayi na tuba ga Ubangiji wannan saɓon Allah har ina, ace dan jaraba yarinya tana cikin biƙi jage-jage amma yaro na naniƙe da ita to Allah ya yafe musu wannan kam ya riga da faru amma tun kafin fushin Ubangiji ya sauka kazo ka ɗaukeni atoh, yoo Allah na tuba dama fa Jikoki ne banda ma ƙaddara me zai kawo ni gidansu” daga cen ɓangare taji an kashe wayar batare da an amsa mata ba. Inno rushewa tayi da kuka tace. “Amma wallahi Salisu ya iya ɗiban albarka ki duba kiga Hansai wai ni Salisu zai wulaƙanta.” tana kuka ta miƙe ta nufi hanyar banɗaki dake cikin dakin ta ce. “Wallahi nan ko gidan Ubana me salati ne na barshi kenan bari nayi wanka na fito” Inno ta faɗa banɗaki tana kici-kicin cire kaya taga Hansai tsaye a gabanta. Zaro ido waje Inno tayi tana dafe ƙirji ta ce. “Yau wata sabuwar ɗibar albarkar kike ji da kika biyo ni har banɗaki ki ga tsiraicina?”Goggo shiru tayi tana raba idanu sai kuma ta juya ta kallo ɗan Jarirn dake kwance saboda tsoro take a barsu su biyu daga ita sai shi a ɗaki, Inno haushi taji ganin irin diriricewar da Goggo takeyi cikin ƙufula ta ce. “Hansai magana nake kina ta wani waige-waige saboda rashin ɗa’a yanzu inba ɗiban albarka ba me zaki mun a banɗaki tsofai- tsofai da rai, Allah na tuba me zaki gani sabo da baki sani ba? Anya hanyar da kika ɗauko me ɓillewa ce Hansai haka kawai ki kai kanki ga halaka yoo halaka mana duk wanda zai ga tsiraicin wani ai hau ta hau shi” Inno ta ƙara tamke fuska ba alamar wasa ta ce. “Hansai tun ban kai kukuna gurin Ubangiji ba ki fice ki bani guri, wallahi banda ma ina duba zumuncin Allah mu biyu muka rage da tuni na kwashe miki albarka kowa ma ya huta” Goggo gabaɗaya ta tsure ƙasa tayi da murya ta ce. “Wallahi Inno tsoro nake ji ina gudun salawaitun da zai ƙara samuna ni kaɗai a ɗaki” Inno ta keɓe baki ta ce. “Hansai me ye gamunmu dake? Uban me zan miki da kika biyo ni ke tsohuwa ni tsohuwa me zan iya yi miki? Yoo Allah na tuba duk ɗiban Albarkar da za’ayi mana me zan iya? Ki fice mun ki bani guri kar fushin Allah ya sauka a kanki ki jaza mini salalan tsiya” Goggo tayi ƙasa da murya saitin kunnen Inno ta ce. “Wallahi Rakiya Jaririn cen nake ji” Inno wata shewa tayi harda tafa hannu ta ce. “Allah na dawo inji kishiyar me yaji. Wallahi Hansai idan baki fitar mini daga bayi ba sai na kwashe miki albarka kowa ya huta, ke da kika ce Jaririn ya fini sau dubu a gurinki to ahir ɗinki karki kara kusantoni, yoo to Allah na tuba ma wacece ke wacce alaƙa garemu Hansai? Allah ya jiƙan me salati dai nasan Mahaifinmu ne sai Mahaifiyarmu Kande banda wannan ki gaya mini dangantakarmu? Wallahi tun muna mu biyu ki fice mini tun kafih nayo yekuwar neman agaji” Goggo tuni idanunta suka ciko da ƙwallah a hankali ta fara takawa ta fice daga banɗakin tana leƙe-leƙe.+

    Inno ta ci gaba da mita tana cewa. “Ke kiji mace haka kawai kina gidan jikana ki butulcemun saboda yana da abun duniya, sai da kika kwasowa kanki ɗiban albarka zaki tuno da ni, Astagafirullah ina zaman zamana zata jamin masifa da fushin Ubangiji ta sani magana a banɗaki ban shirya ba, banda ma Allah yana kareni da kariyarsa da tuni Sheɗanu basu nuna mini rashin ɗa’a da ɗiban albarka ba, cen kije ki ƙara ta keda ɗan ƙundalon ya yi duk abinda zaiyi kiki ma, Allah na tuba ka yafe mun wannan zunubin da na ɗauka” Inno ta gyara tsayu ta ci gaba da cewa. “Allahumma inni’azubika minal kubisi walkaba’isi, yoo wayasani ma ko dama cen Hansai ta saba ɗiban albarkan a banɗakin Allah na tuba ko ta iya addu’ar shiga banɗakinma oho” Inno ta ci gaba ƴan ƙananan maganganun sannan ta fara wanka.

   Goggo kamar wacce ta haɗa gurmin gulma haka ta dinga sunne kai ƙasa tana juye-juye har ta nemi guri ta zauna, a hankali ta fara satar kallon Jariri da ƙyar tayi ta maza ta ɗauko shi ta fara shafa masa mai, tana cikin saka masa kaya Inno ta fito daga wanka tana watsawa Goggo wani kallo. Wayar Inno ce ta fara ringing da sauri ta ɗaga tana faɗin. “Salisu me kakeyi har yanzu baka ƙaraso ba?” Daga cen ɓangaren aka ce. “Wai ke babu me kiranki a waya sai Salisu ne, ɗazu kin kirani ina hanya kike ta kawo ƙorafi gani na shigo gidan Halifan.” Inno ta taɓe baki ta ce. “Wai Ado ne?” aka ce. “Idan kin fito kya gani da idonki” Inno ta katse wayar ta ce. “Yara sai tatalar ɗiban albarka saboda bani na haife su ba sun baidani kamar yawun bakinsu sai abinda suka ga dama zasu gaya mini, kai Allah wadaran naka ya lalace bantaɓa sanin zan samu marasa ɗa’a a zuri’a ta ba. Hansai kiyi ki kintsa mu tafi asibitin nan naji ance ba’a san yiwa yara bbc ɗin nan idan rana tayi” Goggo dai bata kula Inno ba ta gama shirya Jariri ta wuce banɗaki a fakaice take watsawa Inno harara, babu jimawa Goggo ta fito lokacin tuni Inno ta gama shiryawa cikin fallelliyar atamfarta, mayafinta ta ɗauko ta fito falo tana zuwa ta sameshi a zaune shi da Halifa suna hira. Riƙe baki Inno tayi ta ce.”Ado ashe da gaske kaine wallahi na ɗauka waya ce ta mun ƙarya da naji kamar muryarka ce” Ado yace. “Inno sauri nake fa na biyo dan nasan idan ban zo ba zaki ɗagawa su Daddy hankali ne ana zaune ƙalau” Inno kan kujera ta hau tana watsawa Ado harara ta ce. “Wannan dai ba halin Muntarina ka ɗauko ba wallahi dama nasan sai iyayenku sunyi muku huɗubar tsiya akaina, Allah ya mun tsari da mugun halinka wato iyaka zaka yi mini da ƴaƴana ko? Tashi ka fice Ado ka ɓalɓace bazan kuma magana da kai ba bansan da wane mugun abun kazo ba” Ado ya miƙe tsaye yace. “Brother gaskiya kana cikin hazo waɗannan kayan ciwon kan haka kake fama dasu” Halifa ta gyaɗa kai fuska ɗauke da damuwa yace. “Bro Adam ya na iya? Haka zanyi haƙuri har lokacin tafiyarsu yayi” Inno baƙin ciki ya cikata jin maganganun dasu Halifa suke yi  ta fara matsar ƙwalla ta ce.

    “Wallahi yadda kuka kwashe mun albarka tass sai a kunnen iyayenku, tun da uwa ta haifeni ba’a taɓa cin zarafina irin wannan ba, kuma tunda tsiyar da kake mun kenan Halifa zamana a gidan nan daram zanga uban da zai fitar dani kuma zan Kira Salisu ya kawo mun sauran kayana, yooo dama waye gatanka  Halifa idan bani ba Allah gatanka nice gatanka tunda ko ubanka da uwarka Salmai basa ƙaunarka kamar yadda nake sanka…” bata ƙarasa magana ba Goggo ta fito fuska a ɗaure ta ƙaraso cikin falon kamar a jefota ta ce. “Zauna zauna Ado babu inda zaka je a gidan nan sai ka mun iyaka da Rakiya maza-maza ka mun iyaka da ita kuma tsakanina da ita babu sulhu, ba dai zumunci bane take taƙama da shi daga yau na datse shi ta yi rayuwarta nayi tawa bazan iya da wannan sabon salon salawaitin rashin mutumcin da take mini ba” Halifa ya kallesu ya dafe kai bai tanka musu ba, Ado ne yace. “Goggo wa zai shiga tsakaninku cen ku ƙarata kunfi kusa mutum yayi magana ku kwashe masa albarka haka kawai” Goggo ta saki baki ta rafka wani uban salati tana tafa hannu ta ce. “Rakiya kin jimun salawaitun da Ado yake gaya mun, yanzu tunda muke mun taɓa kwashe musu albarka yaron nan zai sako salawaitun ƙarya ido biyu” Inno ta kalli Ado sheƙeƙe ta ce. “Hansai kece baki da zuciya tun da kika fito bakiga ɗiban albarkar da suke yi mun ba, kina gani fa da kika yi magana Halifa shiru yayi miki, ki barsu wallahi tarasu nake yadda suka kwashemun albarka sai na tara iyayensu sannan zan kwashe musu albarka da hujja.” Ana cikin haka Nusaiba ta fito shirye cikin doguwar rigar atamfa tayi kyau sosai gaisawa sukayi da Adam ta wuce ɗaki ta ɗauko Jaririnta t
a fito, Inno na haɗa ido da Jariri ya zaro mata ido yana juya idanunsa sama har wani zaro harshe yake, Halifa miƙewa yayi ya ce. “Inno zamu je kai yaro allura ba daɗewa zamuyi ba zamu dawo.” Inno ta saki kabara ta miƙe tsaye ta ce. “Wallahi ko ubanka Salisu bai isa ya hana inbiku asibitin nan ba, Saboda Allah Hansai uban yarinyar nan ba amanarta ya damƙa manan ba? yanzu idan aka kwana biyu aka ga rashin ɗa’a ya bayyana a jikinta wa za’ a zaga kina ganin uwarta da ubanta zasu yafe mana? A’a ni bangaji cin amana ba idan ka ga nayi nesa da Nusaiba tayi arba’in, amma baza’ayi haka dani ba ƙafarku ƙafata” Halifa zaiyi magana Adam yace.

    “Brother samun kwanciyar hankalinka ku wuce kawai dan waɗannan tsofaffun kasan babu tuggun da bazasu iya haɗa maka ba” Halifa ya juya ya watsawa su Inno harara, Goggo ta ƙarasa tana dungurewa Ado kai ta ce, “Aniyarka ta bika bazamuga tuggu a rayuwarmu ba Batulu ce zata ga tuggu ganin idonta, sakarai mu zaka nunawa salawaitun iskanci da tijara” daga Halifa har Adam babu wanda ya kula su Goggo Adam ne ya fara wucewa Halifa da Nusaiba suka rufa masa baya, Inno da Goggo suka fito kowacce da hijabinta a hannu.

    Adam yana fita ya ɗauki mashin ɗinsa ya fice, Goggo da Inno bayan mota suka shiga Nusaiba ta shiga gaba sannan Halifa ya tayar da mota suka nufi asibitin AMINU KANO TEACHINIG HOSPITAL.

    Akan titin su na zuwa asibiti a dai-dai wani junction ɗan karota da yake bada hannu ya tsayar da mota su Halifa da ke ƙoƙarin tsallakawa ya bawa ɗaya ɓangaren hannu, Inno ce ta ja dogon tsaki ta ce. “Halifa wane irin ɗiban albarka ne wannan zaka tsaida mota a tsakiyar titi bayan ga sauran motoci cen suna wuce wucewa.” Nusaiba ta ce. “Inno baki ga ɗan Karotan cen ne ya tsayar da mu ba?” A hassale Inno ta ce. “Ɗan Karotar banza da wofi da zai tsaida jikana yana tsaka da tuƙi aikuwa me hanani ɗebe masa albarka a duniyar nan sai ya shirya” Inno na gama magana ta buɗe murfin mota ta fice Halifa yana ƙwala mata kira ko waigensa batayi ba, tana fita kai tsaye ta wuce gaban Ɗan Karota ta warce katakon da ke hannunsa ta buga masa a baya cikin masifa ta ce. “Kaci ƙwal ubanka yau ba sai gobe ba sai na kwashe maka albarka a gurin nan”

_INA FATAN ZAKU SAMBAƊO RUWAN COMMENTS KU DUBI ALLAH KARKU NUNA MUN HALIN RASHIN ƊA’A SABODA KU ƊIN ƳAN  AMANATA NE BAZAN IYA ƊEBE MUKU ALBARKA🤣🤣🤣😂😂

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *