ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
Suna cikin haka sai ga Haj Babba ta shigo
dakin, ta samu waje ta zauna. Nan Mama Bara ta
fada mata yadda suka yi, itama ta yi murna sOsai,
saboda ta fi kowa son ganin an hada auren don
wannan shi ne tsohon burinta. Nan suka shiga
shirya yadda za su bullowa da al’amarin idan sun
dawo.
Mama Bara’atu macece mai zafi da kuma
takama da kuma rashin son daukar raini. Kaf a
Cikinsu ita ce Babba babu wanda ya ke tsallake duk
abin da ta gindaya sai kaninta wanda ya ke binta
wato Alh Ja’afar. Gogaggiyar mace ce kuma
ma’ aikaciya ce babba a CBN na cikin garin Abuja,
ita da mijinta da kuma yaranta duk a can suke.
Fadilah ce auta cikin yaranta mata, Www.bankinhausanovels.com.ng
kannenta maza guda uku, ta na da yayye biyar,
maza biyu mata uku, duk kuma sun yi aure a can
Abuja din. Ta na da matukar burin ganin cikin
ya yanta an samu wanda ya auri wani daga cikin
ya yan dan uwanta, wannan ne ma ya sa ta tura
Fadilah karatu can gidansa da ya ke London tun
bayan hada karatun ta na Secondry.
Kwance ya ke kan gadonsa aka yi Knocking.
bai motsa daga inda ya ke ba ya bada damar cewa a
shigo, don yadda ya ke ji a zuciyarsa ba ya jin ko
dan yatsansa zai iya dagawa balle ya mike.
Abulrahem ne kaninsa ya shig0 tare da sallama.
nan ya amsa tare da CEWA.
Abul ya ya aka yi ne?. cewar Malam M.J.
kusa da shi ya karasa ya nemi gefen gadon ya
zauna.
Gani na yi tun safe ban ga motsinka ba, shi ya
sa na zO na dubaka Www.bankinhausanovels.com.ng
Ajiyar zuciyaya yi
Abdulrahem ina cikin damuwa da ta keSon
hanani duk wata walwala. ban fita daga cikin
wacce nake ciki ba Daddy ya zo ya sanya min
wata. Abdul wai yaushe ne Daddy zai daina jefa ni
Cikin damuwa, wai ko ni ba dansa ba ne?
A ah Yaya Muhammad, kada ka ce haka
mana, kai ne fa mai dora mu a hanyar gaskiya,
yanzu idan ka ki yiwa Daddy abin da ya ke so mu
ma muka zo muka yi masa, ka ga ba ka da bakin da
za ka yi mana fada. Wai ma me Daddyn ya yi
Sanna yaCe.
maka ne?
Matsaloli ne suka yi min yawa, ga matsalar
Baleriya ga kuma Rainatu. Duk ban gama su ba, sai
kuma ga shi jiya ya zo min da maganar wai ya na
SO ya hada ni da ‘yar gidan Abokinsa a can gida
Nijeriya, har fa da bani lambarta wai na kira ta
kafin na je, tunda yayi min maganar Wannan
satin ku za ku wuce, ni da Haaya ne za mu zauna
daga baya ma biyo ku tunda ta na da sauran
jarabawa ga kuma Graduation Award da za su yi.
Na fada mata ba zan taba auren Ahllil kitabi ba,
Raihanatu kuma matsalar ban fada mata cewa ina
sonta ba, sai dai kawai na fuskanci kamar yadda
nake sonta itama haka take sona, na ga alamu da
dama a tare da ita, na jima 1na neman wayarta
Amma ba na samu. Matsala daya nake gudu, kada
ta fada son Sameer kamar yadda mu ka yi magana
da shi kwanakin baya.
Abdul ba na son na batawa Daddy rai tunda
yanzu komai ya wuce na rashin jituwar mu da
sabani akan Mommy tun ina karami har zuwa
kwanaki, tunda yanzu ya canza tsarinsa da akidarsa
har ya nemi mu yafe masa, to nima ya kamata na
nuna masa cewa ya na da damar ba ni duk waccce
ya ke son na aUra Www.bankinhausanovels.com.ng
Yaya Muhammad ni shawarata a nan shi ne
ka fito kawai ka fadawa Daddy cewa kai Raihanatu
ka ke So, ina ganin komai Zai fi zuwar maka da
sauki, maimakon ya hadaka da ‘yar Abokin nasa
Ka na wannan maganar, idan ban da ni da kai
sai kuma Momi babu wanda ya san ni ne silar
gyara Zuri a dinmu, baisan zuwana Nijeriya ba da
kudirin tafiyata, bai kuma san na san Raihanatu ba
har na shiga cikin rayuwarta, bai kuma san cewa ni
ne na nemo Sameer na ba shi kwangılar hakan ba.
Ka fi kowa sanin halin Daddy 1dan ya kafe kan
Abin da ba ya so,
Idan na fito yanzu na fada masa abin da yake
faruwa, ba lallai ne ya yi farin ciki ba. Daddy shi
kadar yasan taurin kansa da na zuCiyar shi.
bayan wannan ma ka duba ka ga halin da Haaya ta
ke ciki, kaf cikin mu idan ka cire marigayi Yaya
Hameed, ba wanda yake so sama da Haaya, babban
burnsa ne da kudirinsa son komawa Nijeriya
kawai don ya yi kokari ya samawa Haaya farin ciki
ko Allah zai hadata da Mustaphan da ya janyo
mata matsalar CIWon da take ciki.
Ina tausayin Haaya, ina son na ganta Cikin farin
Ciki, ita kadai muke da ita mace a cikin mu, idan ba
mu ganta cikin farin cikı ba wa za mu gani
Haka ne maganarka, amma ni da1 abin da
nake gani a nan shi ne, ka ce masa to kawai. Kar ka
yi masa gardama ni na yi tunanin da Fadilah zai
hada ka ba wai ‘yar Abokinsa ba
Hmmm, Abdul ni dama bana ra’ayin Fadilah,
ita take sona, kuma ko za ta kashe kanta ba zan
aureta ba tunda har ta fito da bakinta ta ce na
aureta. Ni ta wani bangaren ina godewa Allah da
suka hana auren dole, don kada na auri Fadilah,
amma kuma ta wani bangaren na fi kowa shiga
fishi da damuwa idan na tuna cewa Raihanatu ma a
cikin Zuri ar mu ta ke
Murmushi Abdul ya yi ya ce. “To Yaya ba sai
ka hada biyu ba ka aura lokaci guda
“Abdul ba ka da hankali, ni na fada maka sam
Fadilah ba ta cikin tsarn matan da nake so ko
kadan, ka ma cire ta don bata cikin lissafina. Kawai
abin da zan yi idan mun koma shi ne, zan dage na
fadawa Daddy cewa Raihanatu nake so, idan na
fada a gaban ‘yan uwansa na tabbata za su goyi
bayana a fasa da yar Abokin nasa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan Abdul yace. “Kuma fa hakane maganarka,
gaskiya na goyi da bayan wannan tunanin naka.
Sun jima suna hira, daga nan suka fito wajen
Mommy. Ta na ganinsu tare ta saki fara a ta ce.
Tagwayen Mommy ya aka yi ne, da wane labari
aka zo min ne?
Tsakanin Muhammad da Abdulraheem akwai
tazara, shi ya ke biyewa Muhammad amma idan ka
gansu sai ka za Ce Hassan da Hussain ne shi kuma
Haaya ke bi masa, sai dai kawai shi Abdul kamar
Mommy ya daukO sak, shi kuwa Muhammad suna
kama da Hameed sosai don dai kawai shi bai da
farar fatar Hameed ne, amma duk wanda ya gansu zai
ga kama sosai. Allah sarki, Allah ya jikan Hameed
da Aziza.
Mommy don Allah zuwa na yi ki fadawa
Daddy ya janye maganar auren ‘yar Abokin nasa,
sam ni bana sonta akwa1 wacce na ke so
Muhammad wai ka manta cewa a Cikin
Zuri’arku babu auren Dangi?, shi ne za ka zo min
da wannan maganar. Mun yi burin haka, amma sun
ki yarda, ya ya ka ke ganin kuma za mu zo da
wannan maganar a karba
Mommy ku zuba idanu, Allah ya kaimu
Nijeriya, sai na yi duk yadda na yi na hada ‘yan
uwana Soyayya maza da mata, zan shiga jikin
kowa, lokaci daya kuma da ka
nsu za su wayi gari
su ga mun rikita su da soyayya ai kinga dole su
hakura ko da kuwa ba sa so. Amma a ce wai duk
yawan mu a haramta mana auren juna bayan kuma
su din shi aka yi mu su .
Wannan maganar ta ka ta y1 daida1, sai dai
kuma bana son ace kun kara samun matsala kai da
Mahaifinka ya zo ya na yi min gorin cewa ni nake
saka abin da ka ke yi
Girgiza kai ya yi sannan ya ce. Mommy
rayuwar da muka yi da ba na son tuna ta bare har
na bari wani ya J1, kinsha wuya da yawa a wajen
Daddy akan Zuri arsa. Kawai dai mu bar maganar
nan tunda ta wuce, mu kuma godewa Alah daya
sa Daddy ya gane har ya sanya muka manta komai.
Amma ni dai dole sai sun hakura sun dawo da
auren Zumunc1, wanda ba ya so kar a yi masa, mai
so kuma a barSu su auri yanunansu. Ko ba haka ba
Abdul?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Wannan haka ya ke Yaya Muhammad. Ko ni
kaina idan naje naga wacce ta yi min zan so abata
babu mai hanan1
Good Brother. Mommy tun yanzu a nan ma
har na fara yin nasara 1na kuma ga naje can, ai sai
abin da ya yi gaba. Gaba daya suka sanya dariya.
Mommy ce ta ce.
“To shikenan Allah ya cika muku birinku, ya
baiwa kowa abin da yake nema. Nan suka hada
baki wajen cewa “Ameen
Daidai lokacin da Haaya da Daddy suka shigo
falon. Yadda Alh Ja’afar ya ga Zuri’arsa cikin farin
ciki, sai shima ya tsinci kansa cikin farin ciki.
Haaya ce ta zo gaban Yaya Muhammad tace
Ya Muhammad guest what?
Ya murmusa ya ce. Na baki gari.
Am sorry to say, Daddy ya ce wannan tafiyar
da ni za’a tafi idan lokacin Graduation Award din
ya zo na dawo sai mu hadu ni da kai da shi mu
koma lokacin kai ka dauki hutu wajen aikin ka
Ya dan yatsina fuska ya ce. Am not happy,
gaskiya ban yarda, ai ba haka mu ka yi da ke ba,
Idan har ki ka yarda ku ka tafi, to ni kuma ranar da
Za ki dawo ranar zan taho. Don haka sai ki zaba
Langwabe kai ta yi ta ce.Please Yaya
Muhammad. mun gama komai fa har school sun
yarda zan karasa Exam dina kafin na tafi
Well, zan duba na gani. Ya fada ya na mai
juya 1danuwansa. Gaba daya suka sanya dariya.
Alh Aminu ne zaune a falo tare da mai
dakinsa Haj Zainab wacce yaranta suke kiranta da
Umma. Hira suke tare da kallon labarai a TV na
yadda yan tada kayar baya suke yi a kasahen
duniya.
Sameer ne ya shigo bayan ya yi sallama sun
amsa masa cikin jin dadi da kuma sakin fuska, nan
ya gaida su ya samu waje ya zauna a kasa kusa da
Mahaifinsa. Nan Allh Aminu ya dube shi cikin
salon wasa ya ce.
Malam Yellow, ya ake ciki ne?, don na
fuskanCi kamar da magana a bakin ka Sunan da
ya ke fada masa kenan duk lokacin da ya ke cikin
nishadi.
Eh Abba, ina so ne dama mu yI wata
muhimmiyar magana da kai ne Sameer ya fada.
Nan Haj Zainab ta ce. To bari na ba ku waje
kenan
Haba Umma, ina za ki je?, ki zauna kawai
Gaskiya ne, na meye kuma tafiyar kamar wata
bakuwa. Cewar Alh Aminu cikin zolaya. Sannan
ya numfasa ya ce. To ina jinka mai ke tafe da
ka1?, muna saurarenka.
Nan ya fara sosa kai tare da ‘yar rawar murya.
Abba da… dama ba wani abu bane, ni da
Raihanatu yar gidan kawu Mustapha muka
fahimci junan mu, shi ne na ce bari na zo na fada
maka
Gyara zama Alh Aminu ya yi sannan ya ce.
Sameer ban fuskance ka sosai ba, ka yI min
bayani yadda zan fuskanta Ya fada ya na mai
zaro idanuwa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yanayin da ya ga ya koma sai ya sanya ya dan
razana, nan ya dake ya kara da cewa. Abba dama
ba wani abu nake sOn cewa ba, mun yi maganar
aure da ita ne, shi ne ta ce na shaida mu ku”.
Cikin tsawa Alh Aminu ya ce. “Kai Sameer!
Nutsu sosai ka san irin maganar da ka ke fada min.
ba ka da hankali ne, ka na so ka janyo min magana
ne a ce an samu matsala daga gareni?. To bari na
fada maka, daga nan ba na son ka daga maganar
nan wani ma ya J1, saboda mu iyayenku mu muka
yi taro muka sanar da hana auren dangi gudun abin
da ya faru a baya ya zo ya sake faruwa.
Bana son daga yanzu ka kara zuwar min da
wannan maganar, matukar dai ba so ka ke raina ya
baci ba. Ka dai ji na fada maka
Ya na gama fadin hakan ya tashi ya bar masa
wajen shi da Mahaifiyarsa. Wani irin bakin ciki ne
da tashin hankali suka taru suka rike masa wuya.
Ya dubi Mahaifiyarsa cikin damuwa ya ce.
Ummaa wai wannan wace irin rayuwa su Abba
suka tsara mana a cikin wannan Zuri ar ne, shin su
basa
mantawa da abin da ya faru a baya su
fuskanci kuma abin da ya ke zuwa gaba. Amma
ace saboda wani abu da ya faru tun muna yara
kuma yanzu sai a haramta mana abin da ba addini
ne ya zO mana da shi ba.
Gaskiya 1dan har zuwa yanzu suna nan akan
wannan bakin tsarin na su, to kuwa za mu Cigaba
da rayuwa cikin kunci da damuwa gaba daya mu
da su. don idan sun hana mu abin da muke so, Wasu
Cikin mu idan sun yarda, wasu fa ba za su yarda ba.dole ransu ya baci mu ma kuma na mu ran ya baci.Kinga kenan dai kowa sai ya shiga damuwaa
Sameer ba na son gardama. Kai kadai ne cikin
Zuri ar da za ka zo mana da wannan maganar.
Tunda
mahaifinka ya hanaka daga wannan
maganar, to daga yau nima ban goyi bayan ka zo
min da ita ba, tunda su suka zartar da hukuncin, bai
kamata kuma shi ya zo da wannan maganar ba.
Ka je ko ina ne ka nemo matar aure. idan kuma
ba ka so ne sai na yiwa Haj Amina maganar ‘yar
wajenta Nana, kwarai na yaba da halinta
Umma na rokeki kada ki yi mata magana ta,
Da yarsu Raihanatu din ce kawai ta fi
kwanta min a raina
To ai kuwa dole ka cire ta, tunda ka ji abin da
mahaifinka ya ce. 1dan kana gudun bacin ransa,
idan kuma ba haka ba, sal ka yi abin da ranka yake
so. Ta na gama fadin haka ita ma ta tashi ta bar
shi a wajen. Www.bankinhausanovels.com.ng
Damuwa ce ta Cika masa zuciyarsa fal. Tabbas
ya na Cikin tsaka mai wuya, ta ya zai iya janye
wannan al amarin, ya ma zal 1ya cire Haana daga
ransa, ga tausayin Rauda ma da yake kwana ya
Tashi da shi. Dama ya zo ne ya fadawa iyayensa
cewa duk su biyun zai hada ya aura. Ya fara kawo
maganar Haana ne don ya ji yadda za su karbi abin,
sai kuma ga shi natan ma ba su karba ba, balle
kuma a je ga batun na Rauda.
Ya ma rasa yadda zai yi da damuwarsa. Sai
kawai ya dauki wayarsa ya kira Rauda, Wajen sau
uku ya na kiran wayar amma ba’a daga ba, sai a na
hudun daf da za ta tsinke ta daga.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG