DEEMAH CHAPTER 2 BY ZAHRATEEY
Tun daga ranar da _Baba k_ ya auri _Mama Qudi_ abubuwa da yawa suka fara chanjawa, yan uwan nasa sun juya mishi baya, matansa da yake d’an bribing suma sun karo wayo sun dai na ba shi ko kobo, _Inna Abu_ kuma komai da komai yan uwansa suna saya mata amma na wata wata suke bata saboda sanin halinta dana yayan nasu, tsaf zai kwashe ko kuma ita zata ba shi ba tare da wani tunani ba. Ganin ba sarki sai Allah yasa ya fara aikin tuka wani attajiri a layinmu.
+
Abubuwa basu kara 6aci ba sai da aka haifeni a ranar aka koreshi daga aikin daya fara a gidan attajirin wai da sunan an kamashi yana zance da d’iyar gidan. Sosai yan gidanmu sukayi bakin cikin haihuwata bama kaman _Inna Abu_ da _Baba K_ kamar su fige naman jikina ko kuma su yasar dani a rijiya ko bola. A lokacin da mutane suka fara tozali dani, nan fa kananun magana ya fara tashi, wai ni ba mutum bace saboda kalar idanuna da duhun fatana duk da kasancewata jaririya, wasu ma sukace mayya ce ni shiyasa abubuwa suka fara lalacewa a rayuwar _Baba K_, ai ko _Inna Abu_ kamar jira takeyi ta fara zagi da habaici kala kala ba kara ba kunya.
Kannen _Baba K_ da yan uwan _Mama Qudi_ ne suka fitar da _Baba K_ kunya a lokacin sunana domin sun mishi kokari sosai gurin hidimar suna, duk da haka bai gode ba dan ko sannu bai yi musu ba, hakan yasa yan uwan mahaifiyarmu suka cire hannu a cikin lamarin mu. Bayan suna da wasu yan watanni ana cikin wannan ha’ula’in _Baba K_ ya had’u da wasu yan safaran yara, ba tare da 6ata lokaci ba ya fara musu aikin tuki, inda zai kwaso musu yara daga gari daban daban ya kai musu ba tare daya san abin da ya d’auko ba, sai rana d’aya jami’an tsaron kwarai suka rafkeshi, ya dinga zare ido kamar yayi sata, duk da bai san me yake d’aukowa ba amma ya tsorata sosai da suka tsaidashi.
Kasancewar motan bus ne wanda gilashi ya raba tsakanin dreba da kayan da aka d’auko yasa bai ta6a sanin cewa yara yake kwasowa ba, ana searching mota sai ga yara kananu duk an rufe musu baki sai barci wahala sukeyi. Sosai _Baba K_ ya tsorata da lamarin, dak’er aka iya tracing inda mutanen suke aka kamasu baki d’aya. Watannin _Baba K_ biyar sannan aka fito da shi daga gidan yari, sosai _Inna Abu_ ta sake daura mana karan tsana nida mahaifiyata, shima _Baba K_ ya fara yarda da zancen _Inna Abu_ na cewa nice silar rushewar farincikinsa da arzikinsa.
Tunda aka haifeni sau d’aya _Baba K_ ya d’aukeni, _Inna Abu_ kuwa ko kallona bata son tayi balle a kai ga d’auka. A haka harna fara wayo ina gane masoyana da makiya, tun a lokacin nima na fara zama da kowa yanda yake zama dani, dan kiri kiri idan ka nuna baka sona nima zan fad’a maka na tsaneka, tun abin na damun _Mama Qudi_ har ta daina damuwa ta rinka bina da addua.
A hankali idan akayi abu mutum yayi karya zan tona mishi asiri, idan aka bibiya kuma sai aga ina da gaskiya, tun ana ganin cewa dama ina sane har aka fara gane cewa haka nake ba wai anyi a gabana bane kawai baiwa ce ko wani abin na daban. sai ya zamana idan abu ya faru haka za’a sani a gaba ina bada gaskiyar lamari, karshe dai na koma jari wa _Baba K_ harda notice a kofar gidan mu ga masu neman shari’a a saukake, cikin mintina kalilan ba tare da lauya ko alkali ba, ba tare da sun 6ata kudi mai yawa ba su tuntu6i lambarsa idan sunzo.
STORY CONTINUES BELOW
Cikin lokaci kad’an aka fara gane gidanmu, duk wani me mako ko rashin son batar da kudi a gidan mu suke yada zango da sunan sunzo in duba musu, k’aramin sharia mara wahala shine dari biyar, manyan shari’a kuma dubu dubu ake bayarwa, a rana _Baba k_ yana iya had’a dubu uku dubu biyar, daganan fa ya dai na kokarin sake neman aiki, na koma jarinsa k’arfi da yaji, kuma ya sayo kayan buk’atun gida na yau da kullum ya jibge a store tare da saka kwad’o me girma ya 6oye key d’in. Abin ba wani wahala idan zakiyi girki zai baki dai dai yanda zai isa, idan kin gama zaki zuba a kula a kai k’ofar d’akinsa, kowa zai zo yabi layi dan kar6a amma iya kud’inka iya shagalinka. Idan ma kana son d’anye ne zaka saya ka dafa abin ka, sai ka bada kudi ya auno maka ko da rabin taliya zaka saya akwai farashi, saukinta dai bai kai kudin da zaka saya a waje ba kila ragin goma ko ishirin, shiyasa yake ciniki sosai wani lokaci harda makota ke aikowa sayan kayan abinci a gidan mu gurin _Baba K_.
Tun daga lokacin abincin gidan mu ya koma na sayarwa, a lokacin kanne na uku, shekara uku ne tsakanina da _Kabira_ masu bi mata kuma duk shekara daya daya ne a tsakanin su, wato _Kule_ da _Khadija_ har sauran da aka haifa daga baya, kuma duk wacce ta haihu da kud’inta take suna take fita kunyar jama’a hatta ragon suna kuma duk _Baba K_ yana kiwonsu, iya kaci ki sayi a farashi mai sauki. Nice dai ba sai an sayamin ba yana bani daga cikin cinikin da mukayi, kullun abinci na a wadace yake har bana iya cinyewa sai dai in bawa _Kabira_ da _Kulle_ saboda _Khadija_ jaririya ce a lokacin.
Duk cikin kannena _Mamita_ wato _Khadija_ itace mafi soyuwa a raina, tunda aka haifeta ina mak’ale da ita ko gurin duban da muka fara da _Baba K_ tare da ita nake zuwa, barci ne kawai ke raba mu, ko kuma idan taji yunwa in kaita gurin _Mama Qudi_ in ta k’oshi in d’auketa mu fita ko muyi wasa, lokacin inada shekaru shida, idan ba kanne na ba, ba nida abokanan wasa ko huld’a kowa gudu na yakeyi saboda lak’abin aljana da mayya da akayi min acikin unguwar mu. Wani lokacin na kanyi kuka a 6oye amma ban ta6a bari wani yaga weekness dina ba, inada dakakkiyar zuciya ga taurin kai da zafin zuciya, idan nace zanyi fad’a da mutum shine a ruwa domin duk wani asirinsa tsaf zan tono ko kuma inyi mishi mugun illa, shiyasa da yawa suke shakka ta ko da kuwa zan nemi fitinar su, sun gwammace su kyaleni musanman idan basu da gaskiya ko suna da wani abin assha a tare dasu.
Shekaruna goma sha uku na daina yiwa _Baba K_ aikin da yake kawo masa kud’i, sosai ransa ya 6aci har da dukana, ni kuwa hakan bai wani d’ad’ani da kasa ba. Sosai rigima ya 6arke a tsakaninmu nace ba zanyi ba na daina, idan kuma har zanyi sai dai mu rinka raba kud’in daya samu in ya yarda shikenan idan bai yarda ba ni ba zanyi ba, sosai hankalinsa ya tashi gashi yanata samun customers kala kala harda masu kud’i sosai wanda gidansu ke cike da makirci da sarkakiya, ga kud’i masu soka da zai samu amma fir naki, har sai da ya yarda da abin da nace kafin muka cigaba da gashi.
Ko wace mace a gidan mu ita take kula da kanta da yaranta amma banda _Mama Qudi_ dan duk na d’auke maka nauyi, idan na samu kud’i kullun ita nake bawa dan tayi mana hidima dashi, duk da cewa a dole take kar6a ba’a son ranta ba saboda bata son wannan abin da mukeyi nida _Baba K_ amma ya ta iya shine dai rufin asirin nata dan bata da jari balle tayi sana’a, yan uwanta kuma suna nasu kokarin, ba zata iya d’aura musu nauyi ko yaushe ba, suyi mata na suna idan ta haihu kuma suyi mata sauran abubuwan rayuwa ai da gajiya, shiyasa take hakuri take kar6an nawa. _Ya Kolo_ kuwa bata da wani matsala kafin rasuwan mahaifinta tana samun sako a kai a kai kona kaya ko kud’i ko kayan abinci, dadina da ita bata da rowa idan ta samu tana dibawa mutanen gidanmu, wani l
okaci kud’i har dubu bibbiyu take basu idan an aiko mata, sauran matan gidan mu suma suna kokarin sana’a amma irin wanda _Baba K_ baya sayarwa, dan idan ya ganki kina gasar sayarda abin da yake saidawa zaku saka kafar wando d’aya karshe ya kwace kud’in sai kiyi zaman kashe zani a bakin murhu, saukin su d’aya a sati ya fara basu dari biyar ladan aikin gida shine suke d’an adanawa suke had’awa da wanda suke samu a gurin _Ya Kolo_ duk dama a gurinshi kud’in ke karewa wajen sayan abinci.
A haka har manyan yayyin mu maza yaran _Inna Suwaiba_ suka girma suka fara aikin karfi, duk kuma kafinta suka tafi inda Allah yasa wa sana’ar tasu albarka, har suka sanyamu a boko duk da girman mu, suma suka shiga adult education, kuma ta hakan sukayi aure harma suka taimaka gurin yiwa kannen su aure, duk wanda aka yiwa aure a gidan mu, kud’in yayyin mu dana kawunan mu ne sukayi ciwon kai sai na iyayen mu mata wanda suke d’an adanawa. Ko kwandalar _Baba K_ babu a cikin kayan auren yayyinmu, shi dai nashi yayi ta wage hakora kamar me tallan makilin yanajin dadi ya kawar da ‘ya’ya mata daga gabansa, ko kuma ya aurar da yara ya raje aukin mutanen gidansa duk da cewa baya ciyar da kowa a kyauta amma har Allah Allah yake ace za’ayi auren yaransa ko kunya ma bayaji.
Inada shekaru sha shida na bar aiki tare da _Baba K_ sosai mukayi fad’a dan nace na daina, kuma duk yanda yayi iya kokari gurin ganin mun shirya sam naki amincewa nace na daina ya kyaleni, abin kunya _Baba K_ harda kuka da majina wai na k’ara kassarashi na lalata rayuwarsa da kaddaransa, to wani irin kaddara ne wannan mara tushe, rayuwar tawa ake 6atawa abanza na zama kamar malamar tsubbu, banbanci shine ni bana aiki da aljanu kuma ba komai ne idan zai faru da kai nake iya sani ba sai wanda Allah ya bani ikon gani, fata-fata mukayi da _Baba K_ har magana muka daina yiwa juna kowa yana wa d’an uwansa gani gani, idan ya ganni yayita harare harare kamar idon zasu fad’o ni kuma cewa nake aikin banza harara a dubu.
A lokacin kannena takwas wanda muke uwa da uba daya, yan uba kuma kannena uku, a d’akin _Goggo Fulera_ dan duk sauran yaran d’akin _Inna Suwaiba_ da _Ya kolo_ sune manya sai yaran _Goggo Fulera_ su biyu sannan sa’ata d’aya _Kaltume_ ita ma a d’akin _Goggo Fulera_ take kuma tayi aure sauran duk kanne nane.
Cikin Hukuncin ubangiji yayyin mu suka gama karatunsu harma suka samu gurbi a jami’a, mu kuma muka kammala makarantar secondary, a yanzu _Kisma_ ce kawai bata gama karatu ba, tana aji hudu a secondary. Kawunan mu sunce ba zamuyi karatun jami’a ba, sai dai a gidan mazajen mu, idan suna so sai su saka mu, dan haka kaf ahalin mu, maza ne kawai sukeyin karatun jami’a.
Abubuwa da yawa sun faru a cikin rayuwar mu, ciki harda talaucin daya sake kama _Baba K_ sai jarin cikin gida kawai da yake d’an maneji. Abu na biyu shine engagement din su _Faruk, Fahad, Kabiru, Kursum, Kursiyya da Khalimah_ wanda akayi watanni biyar da suka wuce har ma an saka rana, nan da wata biyu masu zuwa idan da rai da lafiya.
Abu na karshe kuma wani bala’in da _Baba K_ ya sake janyo mana wanda yayi sanadin rasa rayuka hudu _Kabira, Kule, Kubra_ da _Khadija_. _Baba K_ ya dad’e yana taro match sai dai wannan match din yafi karfin mutane, mutuwa shine sakamakon da muka samu ko ince muke kan samu.
Garin shegen son kud’i irin na _Baba K_ yaje ya had’e da yan shan jini, a irin zaman kashe wandon da yakeyi a chan majalisar su ya had’u da wani mutum, ganin cewa mutumin bai yi kalarsu ba yasa _Baba K_ ya damu ya san sana’ar da yakeyi, abin da kawai yace mishi shine “kud’i kam zai samu har ya fita ta kanshi amma fa idan zai iya aikata koma meye aka saka shi” ba tare da damuwa ba _Baba K_ ya amince saboda kudin shine kawai a ransa, mutumin ya bashi address dinsa yace ya zo ya same shi washe gari a gidansa, zai kaishi gurin da zai zama mai kud’i. Sosai _Baba K_ yayi murna kuma yayi alkawarin zuwa.
Washe gari da safe _Baba K_ ya shirya cikin jamfa farare tas, ya d’ora hula baki, sannan yasa takalmi baki ya daura agogo shima baki, duk wanda ya gashi a ranar ya san yana cikin farin ciki, kafin ya fita yasa aka bud’e store ya kwashi kayan abincin duka ya rabawa yan unguwa da kuma yan uwan matansa, sannan ya aikawa kannensa suma, haka garken dobbobinsa duk yasa aka fito da komai yayi rabiya, in takaice muku, babu abin da _Baba K_ ya bari a gidan duk sai da ya kyautar, wasu a yan uwansa wasu yan uwan iyayen mu wasu kuma a mak’ota, mutane da yawa ranar sunyi tunanin mutuwa _Baba K_ zai yi. Haka a cikin gida aka yanda raguna uku wai a soye naman, sai kayan abinci daya bamu a wadace ko wacce aka zuba mata a store din 6angarenta. Sannan ya musu sallama ya fita zuwa samun sabbin kud’ad’e da sai ya gaji da gani inji sabon abokinsa.
A lokacin ina shagon _Iya Loja_ ban dad’e da fara aiki a gurinta ba, ta dalilin d’an ta da mukayi karatu a makaranta d’aya kuma muna mutunci sosai da shi, shine nake mishi magana akan ina son in samu aiki komai wuyarsa dan in taimakawa _Mama Qudi_ shine ya had’ani da _Iya Loja_ mahaifiyarsa. Ina cikin hutawa bayan mun gama abincin safe sai ga Kursiyya ta kirani tana fesamin labari da dumi-duminsa, sosai nayi dariya harda yar kwallata domin nasan tabbas _Baba K_ sai yayi jinya akan abin da ya aikata duk da bansan me ke tafiya ba amma naga rashin wayo a lamarin, koma menene ai sai ya bari sai ya ji dumus.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan _Baba K_ ya isa gidan mutumin, suka gaisa cikin mutunci, har da cin abinci, bayan sun gama suka d’auki hanyar _Abuja_ kasancewar shi _Baba K_ samun kud’in shine muradinsa yasa kwata-kwata bai damu da inda zasuje ba, awa biyar sukayi a hanya shima wai saboda go slow, dan sosai dreban yake gudu dasu.
Suna isa suka sauka a wani hotel, abinci suka ci sukayi wanka, sannan mutumin ya fita, shi kuma _Baba K_ yayi salla, bayan ya idar yayi zaman jiran mutumin, sai bayan magriba mutumin ya dawo daganan suka fita tare da _Baba K_. Wani gida suka nufa a bayan zuma rock acikin _Suleja_ bayan sunyi parking direban ya tsaya jiransu, su kuma suka nausa cikin dajin, tafiya sukayi mai tsawo kafin suka isa madaidaicin gida a cikin tsakiyar dajin, suna zuwa aka bud’e musu gate din gidan, bayan sun shiga suka nufi wani d’aki inda mutumin ya shiga ta ciki ya chanja kaya zuwa ja da bak’i sannan ya fito ya bawa _Baba K_ irin kayan shima ya shiga ya sako, duk da cewa a yanzu ya fara tsorata da lamarin saboda ganin irin kayan da suka saka, sai dai a haka yayi ta dauriya har suka fito suka zagaye ta wani kofa, kafin kiftawar ido harsun 6ace, sai ga shi sun bayyana a wani guri mai cike da taron mutane masu irin kayan jikinsu _Baba K_ ga kuma yara da manya kananu a daure a jikin wani bunki babu alamun rai a tare dasu, sosai jikin _Baba K_ ya fara rawa saboda tashin hankali, ko ba’a fad’a ba ya fahimci inda ya kawo kansa, kafin ace kobo harya fara tsiyaya fitsari a jikinsa, gurin yayi shuru, bayan an gama kai gaisuwa ga shugaban kowa ya kar6i kofi cike da jini ya kwankwada sannan kowa ya fad’i abin da ya bawo wannan bunkin, _Baba K_ bai gama shiga tashin hankali ba sai da yaga mutane na bada iyayensu da yaransu da yan uwansu da matayensu, wasu ma yaran suna cikin ciki ko haihuwarsu ba’ayi ba.
Ana gama wannan hidimar aka gabatar da sabbin members kowa yana gabatar da kansa tare da bada wani nasa, sannan sai a bashi kofin jini ya kwankwad’a, _Baba K_ shine mutum na karshe a gurin kuma shine wanda aka hango tarin alkairi a tare dashi idan har ya kasance cikin kungiyar, ana zuwa kansa ya fara adduo’i harda na shiga ban d’aki kai wasuma bai son ko addu’ar meye ba, kawai dai yi yakeyi ba tsayawa, ganin haka yasa akayi saurin fita dashi domin karya 6ata musu aiki ya kuma 6atawa sarauniya rai tare da bunkinsu, ba’a ajiye shi a ko ina ba sai a bakin kofar gidansa a garin _Bauchi_.
Kamar a mafarki naji ana buga k’ofar gida, yanayin bugun k’ofar akwai alamun ba lafiya ba, da sauri na duro daga kan gado na sanya takalmi na fito falo, kicibus mukayi da _Mama Qudi_ da toci a ha
nnunta, cire takalmin nayi a bakin falo sannan na saka wanda muke amfani dashi a tsakar gida, tare muka fita, a tsakar gida muka had’u da _Ya Kolo_ itama da toci a hannu sai sauran samarin gidan da suka fara fitowa, k’ofar gidan muka nufa, kafin mu tambayi ko waye muka farajin shessheken kukan _Baba K_ da sauri _Khalil_ ya bud’e, ai kuwa shine a raku6e a jikin gini jikinsa sai rawa yakeyi kamar wanda aka watsa mishi ruwan kankara, a hankali samarin suka cincin6osa zuwa cikin gida sannan aka rufe k’ofa. Zuwa lokacin duk mutanen gidan sun fito suna tsaye cirko cirko, a tsakiyan falonsa suka ajiyeshi, sai da yayi kuka mai isarsa sannan ya fara bada labarin abin da ya faru dashi daga fitansa zuwa yanzu daya ganshi a k’ofar gida.
Dayawan yan gidan mu suka hau kuka yayin da wasu sukayi jugum jugum ba bakin magana balle na kuka, a ranar dai kwanan zaune mukayi a falon _Baba K_ barcin ma bai yiyu ba saboda yawan firgitan da yakeyi, kuma tsaf na karanci cewa sune suke tsorata shi, sosai hankalin mu ya tashi domin bamu san abin da zai iya faruwa ba, muna zaune na tashi a firgice bayan na kalli duka yan d’akin amma banga _Kubra_ ba, ban tsaya tambaya ba na wuce part din _Goggo Fulera_ wani irin faduwar gaba ya riskeni jin nayi tuntu6e da mutum, da sauri na kunna switch din wutan falon, Kubra ce kwance a k’asa idanunta sun kakkafe, wani irin ihu na saka wanda ya janyo hankalin saurin mutanen da basu fito ba, wanda suka biyo bayana kuma suka hau kuka, tabbas _Baba K_ ya janyo mana bala’i akan wannan son kud’in daya saka a gaba.
Kaaancewar asuba ne yasa masu salla a cikin mu suka tashi dan yin salla, bayan mun idar muka dawo 6angaren _Baba K_ inda aka ajiye gawon _Kubra_ bayan anyi mata wanka, kuka muka taras yan cikin falon sunayi musanman wanda suke uwa d’aya da _Kubra_ gefenta na zauna na bud’e likafanin, har yanzu idonta a rufe yake, idona na saka a cikin nata “tunda har ya kawo kansa kuma ya take doka na farko dole ne mu nuna masa kuskurensa har sai ya dawo da k’afafunsa, aje a datse rayuwar wanda yafi so a cikin ‘ya’yansa” suna zuwa suka taras da _Kubra_ tana kokarin fitowa daga 6angaren su, kasancewar tana kewaye sanda kowa ya fito, sai bayan data gama uzurinta sannan tayi niyyar biyo sahunmu, tana fitowa suka mayar da ita, harshenta suka yanke, sannan suka sanya wani abu kamar allura mai girma da tsawo, cikin kankanin lokaci suka zuke jininta tas, sannan suka wurgar da ita a tsakiyan falon suka 6ace”.
Ina gama gaya musu abin da ya faru na mata addua sannan na bar gurin, 6angaren mu na koma saboda bana son k’ara ganin fuskar _Baba K_ a lokacin domin a yanda nakejin zuciyata tabbas zan iya mishi illa kila shima in kasheshi yabi bayan yar uwata.
Bayan rasuwan Kubra da shekara daya suka kashe _Kule_ kanina, shima guba suka saka mishi a lemo yasha ya margaya, sannan suka kwakule mishi idanu duka biyu, bayan shekara d’aya _Kabira_ tabi bayansu, ita kuma yankan rago suka mata tare da zuqe jininta, sai lastly _Mamita wato _Khadija_ duk dai kisan walakanci sukeyi tare da shanye jininsu, kuma har zuwa yanzu _Baba K_ yaki amincewa da zuwa garesu, acewarsa dama lokacinsu yayi shiyasa suke mutuwa, duk da fargaban da muke ciki a kullun hakan bai sa wani abin ya ragu a 6angaren _Baba K_ ba yananan da shegen son kud’i, bayan rasuwan _Kubra_ yan uwansa suka tausaya mishi tare sa bashi jari shine ya sayo kayan abinci ya cigaba da sayar mana a gida haka zalika garken dabbobi ya sake zuba wasu a gurin kiwon nasa.
_Wannan shine takaicecen labarin gidan mu_
________________________Ina zaune a kan gado ina shafa muhallabiyya a jikin lallen dana kunsa jiya da dare, bayan na wanke da safe sai nake shafa muhallabiyya dan ya k’ara yin ja. _Kisma_ ce ta fad’o d’akin da gudu tana cewa ” _Baba K_ ya mutu Anty Dee, kiyi sauri ki zo kigani gasu _Mama Qudi_ chan suna ta kuka”.
Sosai maganar ya girgiza zuciyata, _Baba K_ ya mutu, to ya mutu yaje ina da zunubin da yake ta kwasa babu alamun tuba a tare dashi, hakkin yara da manya da matansa duk bai sauke ba, idan ma ya mutu ai direct wuta zai je, cikin sauri na tashi tare da cire banzan tunanin dana fara daga cikin raina.
Matan gidan mu na tsaye cirko cirko sunsha hijaba bak’i kamar masu shirin takaba, sauran yan mata da samarin kuma sai girgiza kai sukeyi suna sharar kwalla kamar kadangaru. _Baba K_ na gani kwance nashe nashe a kasa, babu takalmi sai katon binjima da hula kamar na aro dan yafi karfin kansa. Kallo na kare mishi sosai naga alamar akwai abin da ya same shi, tsugunawa nayi na d’aga hannunsa tare da duba jijiyar gurin, ajiyar zuciya nayi ganin cewa yana raye domin jijiyar na harbawa a hankali ” _Khalil_ ku taro taxi mu kai shi asibiti bai mutu ba tukunna da sauran aiki a gabansa” ajiyar zuciya duk sukayi tare da hamdala.
Muna isa asibitin aka kar6eshi tare da sanya shi a gadon majinyata sannan aka wuce dashi emergency unit, duka yan gidan mu na tsaye cirko cirko a waje suna jiran sakamako, mun dad’e a tsaye a k’asan wani bishiya kafin _Faruk_ ya na cewa “mungode Allah ya farfad’o, amma wai mu jira nan da awa d’aya kafin mu samu ganinshi”.
Zama mukayi duka a kan tabarman da _Faruk_ ya d’auko daga masallacin cikin asibin, bayan awa gudu muka d’unguma zuwa private d’akin da aka kaishi, a zaune muka same shi yana shan ruwa kanshi yasha bandeji sai ajiyar zuciya yakeyi minti minti, kowa a d’akin ya gaisheshi amma banda ni, hakan yasa ya d’ago kansa muka had’a ido, nasan ni yake nema kuma inason sanin abin da ya faru shiyasa naki inyi magana dan nasan ba zai ta6a kallona ba, cikin idonshi na kalla na yan mintina sannan na d’auke kai tare da kwashewa da dariya.
Kallo ne ya dawo kaina ganin yanda nake dariya babu alamun dakatawa, sake kallon _Baba K_ nayi na sake kwashewa da dariya “me ya kai ka shiga abin da babu ruwanka, gashi ai ka d’ebo wa kanka jinya, mu dai bansan ranar da zaka barmu mu hutu ba a cikin rayuwarmu, kai bada bamu ba, bada nema dan mu ba, muda nema kuma da karas da kud’in gurin jinyar fitintinun da kake jawo mana, a gaskiya ka chanja hali inba haka ba ni kam ba zan sake 6ata kud’ina gurin taimakon ka ba tunda nima baka taimakeni ba”.
“Asibiti ya shiga gurin wani abokinsa daya bashi dubu uku da sunan zai mishi aikin shi na ranar saboda shi ba zai samu zama ba akwai inda za shi, ko da _Baba K_ ya gama aikin nasa ya fito sai ya had’u da wasu mutane ana hayaniya, d’ayan na kwance rai a hannun Allah ana kokarin shigar dashi cikin asibitin, shi kuma d’ayan yana kokarin son kashe shi ga kuma folisawa a gurin sun zo tafiya dashi amma bai daddara ba, wai gwara ya k’arasa kashe abokin nasa sai aji dadin tafiya dashi kurkuku, kuma duk fadan akan waya ne, shi me laifin ya kasance me dauke dauke shine majinyacin ya rasa wayarsa bayan zuwansa gurin shi, daya tambaye shi, sai yace ai ya mishi sharrin sata sai ya yanke hukuncin kashe shi, bayan ya 6urma mishi wuka aka kawo shi asibiti shine ya biyoshi dan ya k’arasa kashe shi (ya faru a gaske a yobe state, kuma duk yaran masu kud’i ne & family friends ne) kafin ya k’arasa abin da yayi niyar har majinyacin ya cika, bayan folisawa sun bar gurin shine _Baba K_ yaje dan son samun rahoto, karshe bai samu rahoto ba ya samu duka a gurin yayan mamacin wanda ke cikin 6acin rai da kunan zuciya, daker aka kwace shi, maimakon ya tsaya ayi mishi dressing sai ya fito ya kamo hanyar gida, anan ne kuma ya had’u da 6arayi suka kwace kud’in aikin sannan suka mishi dukan tsiya na taurin kai da zagin su da ya rinka yi, daker ya samu wani mai Napep ya kawo shi cikin anguwarmu, karewarta dai awaje ya kwana da zazzabi sai zuwa safiya ya samu tattaro jiki ya k’arasa gida daga rumfar me shayin daya zauna, yana zuwa ya fad’i saboda jiri daya kwashe shi, doguwar suma yayi wanda akayi tunanin ya mutu” ina gama fad’a musu na kakka6e riga na nayi gaba, nikam banga gurin zama ba anan, gida na nufa direct cike da takaicin halin _Baba K_ duk ya tayar musu da hankali bayin Allah iyayen mu ko yaushe ba dai yasan wahalar su ba sai dai su suyi wahala da damuwarsa.
STORY C
ONTINUES BELOW
Ina zuwa gida na shirya na wuce gurin aikina, ko da na dawo na samu an sallamo shi, yana kwance a bakin kofar 6angarensa kansa dai yasha bandeji kamar goggoro, ga fuskar nan ya kumbura kamar wainar da aka cikawa yeast, ko sannu banyi mishi ba nayi wucewa ta, ina kallon yanda yaran gidan mu suke kus-kus amma ban tanka musu ba, ina shiga na gamu da hararan _Mama Qudi_ gaisheta nayi ta amsa chan ciki, bai dameni ba saboda nasan dan mijinta take hakan.
Sallamar mutumiyar me ya fito dani daga d’aki, dan neman magana na fita tsakar gida inda kowa ya fito dan kwasan gaisuwa, nesa dasu na zauna a saman kujera ina kallonsu d’aya bayan d’aya, na lura sam _Inna Abu_ ba’a son ranta ta shigo gidan namu ba, dan neman magana sai gani ina gaisheta, a darare ta amsa tana ankare da rashin mutuncin da zan iya gabza mata, ko minti goma cikekke ta kasa yi, haka tayi wa yan gidan sallama ta kama hanyar gidanta, sosai na kwashi dariya bayan tafiyarta, dama nasan za’a rina gwara dana fito mata a mutum ko ba komai uwata zata huta da zagi da cin mutunci.
Cikin kwanaki biyu _Baba K_ ya warke harya cigaba da sabgarsa kamar babu wani abin da ya sameshi, kasancewar yau munada aikin biki a shagon _Iya Loja_ yasa na tashi da wuri nayi wanka na hada shayi da bredi nasha, a lokacin da zan fita kowa na barci amma banda me girkin ranan, dan karfe takwas ake fara rabiyan abincin sayarwa, _Kisma_ kuma suna hutu shiyasa bata tashi dan tafiya makaranta ba.
Ina zuwa shagon na samu _Iya Loja_ batanan ta d’an fita, masu hankali a gurin nayi wa sannu sauran na bawa iska ajiyarsu, kitchen na wuce inda na samu _Ruky, Ola, Mama Bulus, Inna Hansi, Blessing, Joy,_ da _Hajara_ suna ta ayyukansu, d’akin dake kitchen d’in na shiga na chanjo kaya zuwa na aiki sannan na dawo tare da yi musu sannu. _Fried rice, Jollof rice, Moimoi, Semosa, Spring roll, Doughnut_ da _Pepper chicken_ shine abin da zamuyi a yau, kasancewar muna da yawa kuma karfe bakwai ake buk’ata yasa muka bada himma komai yake tafiya dai-dai.
Karfe biyar dai-dai muka gama girke-girken, d’an hutawan minti talatin mukayi kafin muka fara packaging, ko wani take away _Friedrice/Jollof rice_ aka zuba sai, foil paper da mukasa snacks din a ciki sai alalen ganye da muka saka a foil daban, sannan muka zuba ko wani package din abin da mukayi a cikin babban ledar da suka bamu daga gidan bikin me d’auke da tambarin company din _A&S limited_, sai kuma sunan couple’s d’in a rubuce a jikin ledar gwanin ban sha’awa.
Bakwai saura kwata muka kammala, alokacin _Iya Loja_ ta dawo, sosai taji dadin aikin da mukayi kuma komai yayi dai-dai da tayi tasting, ni, _Joy_ da _Hajara_ zamu kai a motar da _Iya Loja_ take haya, _Sani_ dreban tane ya kaimu inda za’ayi bikin achan _A&S garden_.
_A&S garden_ wani babban garden ne dake cikin garin bauchi, akwai gurin shakatawa, gurin shirya shagulgula da kuma gurin wasan yara wanda ya k’awatu da kayan zamani masu kyau da tsada. Duk da haka kuma komai a sauk’ak’e yake ba kamar sauran gurin wasan yara da ake cikawa kud’i ba, shiyasa gurin baya rabo da mutane 24/7. Muna isa _Joy_ ta kira numbern madam din da _Iya Loja_ ta bamu, mun d’an dad’e a tsaye kafin matar tazo tare da wasu samari uku cikin uniform din masu aiki, gaisheta su _Joy_ sukayi ni kuwa sannu kawai nayi mata, godiya tayi mana bayan ta duba komai, sannan ta bamu ledan abincin kowa park d’aya duk da cewa dama akwai wanda akace mu d’auke daga chan muda mukayi aikin amma sai da ta k’ara mana tare da bamu dubu bibbiyu ladan kawowa, godiya mukayi mata sannan muka wuce. A bakin hanya muka sauka ko wacce ta tare abin hawa zuwa gida bayan mun kwashe kayan mu na cikin motan, shi kuma _Sani_ ya wuce shagon _Iya Loja_ dan mayar da motan.
Na isa gida a gajiye, na samu _Mama Qudi_ tana salla, d’akina na wuce nayi salla sannan nayi wanka da ruwan dumi saboda gajiya, bayan na gama na fito na cewa su _Kisma_ su kira su _Khalil_ muci abinci yau ba sai mun saya a gurin _Baba K_ ba, kasancewar abincin bashi da yawa sosai yasa muka k’ara da bredi da shayi, bayan mun gama mazan suka wuce 6angarensu, mu kuma mukayi zaman mu bamu fita ba, anan ne nakejin wai yau anyi dambe a gida tsakanin _Baba K_ da _Inna Suwaiba_ sosai abin ya bani mamaki, matan gidan mu dai nasan basu da irin wannan halin, ko me yayi zafi haka a cikin yara dambe tsakanin iyaye, to Allah ya kyauta.
Da safe muka tashi da muguwar labari wai yayarmu _Safiyya_ ta rasu, sakamakon jininta daya kare, babu wani jininta daya kare a harsashena mutanen _Baba K_ ne kawai suka cika aiki, duk da cewa shekaru guda suke badawa kafin suyi abin da sukayi niyya amma tabbas wannan ma sharrinsu ne, _Safiyyan_ da take bada jininta ma a asibiti wani lokaci dan ceton ran wasu, kasancewar bata ta6a haihuwa ba tunda tayi aure yasa take wannan jihadin injita da fad’a, domin jininta me wuyar samu ne, shiyasa take yawan badawa, shine za’a ce wai jininta ya kare bayan babu ya da za’ayi a cigaba da kar6an jininta matukar babu me yawa a tare da ita, tabbas akwai matsala dole ne muyi tunani da sauri mu san abin yi tun ba’a gama da zuri’ar mu baki d’aya ba. Sai a lokacin na gano dalilin damben _Baba K_ da _Inna Suwaiba_ ashe _Safiyyan_ tana asibiti ne a lokacin kuma an tabbatar da cewa jininta ne yake ta tsotsewa ba tare da an gano dalili ba.