ZUMA CHAPTER 14 BY SHATUUU
Washegari, tunda mukai sallar asuba bamu koma ba Dan Abbah yace min da wuri zasu juya. Lubna tayi wanka bayan min idar da sallah ta shirya sannan ta zauna gefena tana cin noodles din da aka kawo Mata, ta dubeni tace+
” Yaya Nanah se yaushe Zaki dawo kuma”
Na danyi murmushi Ina shafa kanta nace
” Bazan Dade ba inshallah, I’m gonna miss you!”
Se ta goge hawayen da ya ciko idanunta tace
” I’m imagining yadda zamu rayu a gidannan bakya nan. It’s a hell”
Maganarta se ta karyar min da zuciya na kakaro murmushi nace
” Bazan Dade ba, Kinga Dole Zan dawo da wurwuri saboda shirye shirye, kuma lubna ba wannan ne Karo na farko Dana Yi tafiya ba”
Ta shagwabe fuska tace
” Naga wancan we’re just some miles away, Amma wannan wajen 500km fa”
Se na Mike na shiga bedroom din da muka kwana Ina murmushn lubna, Ummiey na zaune tana juye kayan da nazo dasu cikin space din data ware min a wardrobe, bamu samu munyi magana ba, I’m not sure idan tasan sunana ma, Ina murmushi na zauna nace
” Sannu da aiki”
Ta dago ta kalleni ta sakar min murmushin ta tace
” Call me Ummiey, kina son sunan?”
Na gyada Kai Ina Kara fadada faraata, ta aje abayar hannunta zatayi magana nace
” Ummiey, Wanda ya kawoni…”
Se nayi shiru Ina jin kunyar abinda Zan fada Mata, dawowa tayi gefena tareda bata Rai, kusan shi ne Karo na farko da naga Bata murmushi tace
” Kada dai yayi Miki aure Ina nan a zaune?”
Kaina na girgiza nace
” An kusa dai, saura six weeks ya rage, shi ne Wanda Zan aura”
Tayi salati tace
” Amma kin kyauta, yanzun tun jiya Kika ki fada mana.”
Se nayi dariya naga ta Mike ta dauki wayarta ta Kara a kunne, tayi magana da yaren da ba ganewa nake ba, se ta dubeni tace
” Wanne a ciki?”
Na sunkuyar da kaina Ina fidgeting da fingers dina na rasa me zance Mata, Se ta gyada kanta, bana son a Kara maganar na shiga wanka , ban Jima ba na fito na tarar ta dakko min Kaya hatta inners da man da Zan shafa. Cikin sauri tace na shirya na fito part din Nanne Dan lubna already na can, na gama shiryawa cikin skirt da riga na atamfa, na yafa veil sannan na fito bayan na Dan muurtsuka turare, a hankali nake takawa Ina tunanin ko Zan gane Dan buildings din duk kusan plan din wajen iri daya ne, ta bayana naji ance
” Beautiful Lady!”
Na Dan juya a hankali na kalleshi, yayi min murmushi tareda daga kafa har muka jera yace
” Daga ganin wannan fuskar lost but found daughter Ummiey ce.”
Na gyada kaina Ina gaishe shi, yace
” Ina Zaki?”
Nace
” Gurin Nanne”
Yace
“Kin bar hanyar ai, can I ?”
STORY CONTINUES BELOW
Na gyada Kai muka cigaba da tafiya yana min hirar irin jiran da Ummiey tayi min, Abu daya na fahimta yana da surutu. A parlon muka tadda uncles Dina dasu Nanne da kuma Ummiey se Abbah. Ina shigowa idanuna kanshi ya fara sauka, I was lost in those shiny brown orbs, Wanda ya rakoni nata min magana naji Amma na kasa bude baki na nayi magana, a hankali na daga kafafuna na shiga parlon Ina jin tamkar idon shi ne kawai me tasiri a kaina, har kasa na durkusa na gaishe su, Bah yace
” Ashe kina tareda abokina baki fada ba!”
Na danyi murmushi kawai tareda satar kallon shi,gaban shi an cika da breakfast,nayi dariya a hankali ganin yadda aka tarfa shi dan Bai fiya son breakfast ba. Daya daga cikin uncles dina yace
” Tun daga haka munsan ka dace ka aureta, tunda kayi kokarin hadata da mahaifiyar ta tun kafin ka aureta, muna muku fatan alkhairi”
Yayi godiya sannan ya Mike yace zasu tafi tunda they have a long way to go, Suka mishi adduar sauka lafiya hade da dimbin godiya, yaje ya tsugunna gaban Ummiey yace
” Ummi zamu tafi!”
Tana murmushi se naga kamar ni nake
” Nagode Allah ya saka maka da alkhairi, nagode”
Ya gyada kan shi yayi gaba su Bah Suka tafi raka shi, har lokacin Ina zaune, Nanne tace
” Fadimatu jeki Mana kiga tafiyar shi”
Dama haka nake jira, Sena Mike Ina jin tana cewa idan nayi Sanya zata kwace min shi, na rufe fuskata da veil na nufi gate, mukai Karo da su Bah sun dawo, daya daga cikin su yace
” Kiyi sauri kije, kuyi sallama kinji”
Na gyada Kai na nufi motar tasu,wannan Karan lubna da Yusuf na gaba se Abbah a baya, side din Yusuf naje nace
“Yaya Yusuf Allah ya kiyaye Hanya, nagode sosae. A gaida min Hanoon”
“Wallahi kunya nake ji idan Kika ce Yaya dinnan, Hanoon kuma Angama mamaaa”
Se na koma bangaren lubna na rike hannunta ganin kuka take nace
” I’m not staying long lubin, just take care of everything, the rest, yourself and Daddy”
Ta gyada kanta tana share hawayen, idanuna Suka ciko da kwalla na matsa zuwa inda Abbah ke zaune dukkan hankalin shi a kaina, nace
” Abbahna, I’m grateful, Allah ya tsare ka ya kiyaye Hanya, ya Kai min Kai lafiya!&”
Maimakon ya bani amsa se ya jefo min tambayar data bani mamaki
” Who’s that guy, da Kika shigo dashi dazun?”
Ina iya hango kishi a idanun shi, nayi murmushi tareda rausayar da Kai nace
” He’s just a cousin…”
” Not just Amour please!”
Da mamaki na kalleshi se naga kamar tsoro yakeji, yace a hankali Wanda daga ni se shi kawai muke jin conversation din mu
” Take care of yourself Dan Allah, know that Allah kadai yasan irin son da nake Miki”
Na danyi murmushi nace
” Know that Kai na zaba even if I’ll start over I’m gonna choose you again. Nothing will change my heart. Ina son ka tafi feeling relaxed, no anxiety I’m yours already and I’ll not change that inshallah Hombre❤️”
Na fada Ina sakar mashi cutest smile da nasan zai melting zuciyar shi, se naga ya fara murmushi yace
” Your words will keep me going, ki koma ciki se munyi waya”
Dan baya naja kadan Yusuf ya tada motar Ina kallo yana dariya kasakasa nasan kuma da uban shi yake, lubna na waving Dina Amma hankalina dukka wajen namiji daya dana zaba na rayu dashi!
STORY CONTINUES BELOW
🎼 Hello, hello can you hear me , as I scream your name
Hello! Hello, do you need me before I fade away!
Is this the place that I call home to find what I’ve become!
Walk alone the path unknown, we live , we love, we live!
Deep in the dark I don’t need the light, there’s a ghostinside me, it belongs to the other side. We live, we love, we
live!
A hankali na koma ciki Ina jin kamar an tafi da wani muhimmin Abu a rayuwata, Amma kuma Ina jin farin ciki madaukaki a zuciyata, kafin na karasa na Kira Daddy muka Jima muna magana, seda na updating din shi kan komai sannan mukai sallama. Ummiey na zaune ita da Nanne, da sallama na zauna nace
” Ummiey sun tafi”
Tace
” Allah ya kaisu lafiya!”
Irish ta zuba min da nama da kuma scrambled eggs, se tea me kauri, na zauna naci na koshi sannan nace
” Ina su Hasina?”
Nanne tace sunje makaranta, a parlon muka zauna Ummiey tace min
” Wanne suna ya saka Miki”
Na dago naji tausayin ta ya kamani, imagine giving birth to a child ko sunan shi baka sani ba, nace
” Nanah Fadima!”
Tayi murmushi tace
” I thought as much dama ya fada, Ina hauwa, sumayya, nasiba, Rahma da mariya?”
Nace
” Duk kin tuna sunan su, duk sunyi aure”
A sannu na fara Bata labarin gidan mu, amidst labarin tayi ta kuka tana fadin
” Na zata daga kaina Ibrahim ya gama saki, Ashe daurawa yayi, yanzun haka kuka rayu Babu mace”
Nayi murmushi kawai Ina jin tausayin ta, seda tayi shiru sannan na cigaba da Bata labarin karatu na da haduwata da Aliyu, matar shi, abinda ya faru har fara service dina
” Amma Mata na rashin hankali kuma ta rasu ta barshi, shi ne wannan kenan?”
Na girgiza Kai naga taji dadi tace
” Ai da zance da baki zabe shi ba, tunda seda matar shi ta mutu zai dawo. Some men shaa”
Nayi dariya na cigaba da fada Mata naga tayi farin cikin jin cewar na gama karatu har Ina daf da service, kuma ma a professional course like pharmacy! Nayi shiru na kasa Bata labarin Abbah se tace min da damuwa a fuskarta
” Ibrahim yayi forcing din ki ki aureshi”
Bana son abinda zai Kara jawa Daddy bakin jini gurin su dan dama shi me laifi ne babba, na fada Mata komai yadda muka hadu da latest development. Se tace min
” Are you ok marrying him? Kinsan auren irin su akwai challenges Wanda Nima I faced, his wife and his kids”.
Se ni kuma na Bata labarin yadda nake dasu Hanoon har Adnan ma yazo gurina a asibiti min gaisa bayan ya sakko daga fushin baban shi zai aure,sede Bai sake jiki kamar sauran ba. Bayan na gama tace min
” Bayan na haifeki Bah ya maida ke, Ibrahim ya dawo dake Bah ya Hana karbarki, nayi tunanin bazan tashi ba, nayi jinya hauka ne kawai banyi ba. Ganin halin da nake ciki yasa akai deciding nayi aure may be idan na haihu Zan Dan samu break, saboda ni tunanina kawai ba Zaki rayu ba, kawai gani nake without my warmth touch and you sucking you will die. Bah su hudu ne, Bah ne babba se Baba jafaru se ummaah, se Baba Ishaq. Gaba daya Banda ummaah dake aure a Niger dukka compound daya muke zaune kamar yadda Kika gani. Akwai Nanne ita ce kawai matar Bah, a gurin ta mu shida ta Haifa, Ya Hassan, Yaya hassana, Ya Ahmad, ya lamin, se ni se hajara. Aminu shi ne Wanda Bah ya hadani dashi, shi ne babban Dan Baba Jafaru. Ya Jima baiyi aure Dan ya girmi Yaya Ahmad ma, lokacin dana aureshi yana aiki a kaduna so kaduna na fara zama, bayan na shekara uku inata jinya har na Dan hakura sannan na haihu, na Haifa Muhammad, bayan wajen shekaru hudu na Kara haihuwar Sadiq. Duk lokacin inata rokon Bah ya barni naje gurin ki Amma se yace kada na damu Zaki zo da kanki, Abban Muhammad yaso kaini da kawai na samu peace of mind Amma gargadin bah yasa kowa yaki cika min burina. A hakan mukai wani get together da classmates Dina na secondary, wata Mansura friend Dita tace min ta ganki a dutse, anan naji hankalina ya kwanta ko Babu komai nasan kina raye kenan. Muka samu aiki a South Korea, muka tattara muka tafi anan ne bayan shekaru na Haifa Amna, anan Amira Yar hajara tace min ta ganki a Kano, nace taje cafe din ta karbo number din ki tace ya hanata, nayi kuka a lokacin Amma daga baya se naga Allah ke kwantar min da hankali Alan kina raye. Kullum ranar duniya expecting nake Zaki zo Amma shiru shiru har muka gama aikin muka dawo Abuja Babu Wanda ya Kara cewa ya ganki. Se jiya na gama hirar ki se gaki kinzo, you’re something I long to see darling”
Na goge hawayen idanuna nace
” Nima haka, Amma gashi Allah ya nufa. Ina su Amna din?”
Tace
” Basu kasar, sun bi baban su yaje wani assignment a Quwait, ni kuma inada case so shiyasa ban bisu ba, Allah yayi Zaki zo ki sameni”
Nayi murmushi nace
” To yaushe zasu dawo?”
Tace
” Munyi dasu se next week Amma nasan idan sun San kinzo baza su zauna ba”
Haka mukai ta hira har can bacci ya daukeni, se ta koma part dinta ta barni anan. Ban farka ba se ana Kiran sallar azahar, nayi sallah sannan na cewa Nanne zanje gurin Ummiey, na fita rike da wayata Ina Kiran Abbah Amma ban same shi ba haka lubna, nasan kilan Hanya ce. A kitchen na tadda Ummiey tana hada lunch, na zauna kan stool nace
” Ummiey Kika taho Kika barni”
Tace
” Ayya habibty na barki ki huta me, su Muhammad sun Kira zasu magana dake kina bacci, Amna tayi fushi wai ban fada musu ba tun jiya”
Cikeda dauki nace
” To ki kira su yanzun mana Nima I’m eager to hear from them”
Bata ma Kai ga Kiran ba Sega video call din su ya shigo. Suna zaune a parlon suite din da Suka sauka,
” Big sis!”
Daya daga cikin su ya fada, Ummiey dake murmushi a gefe tace he’s Muhammad, nace
” Mohammad!”
Yayi wani ihu yana fadin
” Yes! She knows my name! Big sis we waited for eternity for you”
Na hade hannuna nace
” I’m sorry I’m here! Yaushe zaku dawo? Ina su Amna”
Lokacin ta fito da mug, da sauri ta karaso ta karbe system din tana fadin
” Yaya welcome”
Har Dadda dinsu mukai hira, Sadiq yazo Shima mukai. Tamkar min Jima da sanin juna. Se yamma na samu mukai waya dasu Abbah sunje, na ta mishi godiya, Ummiey ta kaini duk gidajen dake cikin compound din tayi introducing dina, sannan tace washegari zamu fita. Da yamma dukka sisters dina suka kirani na hadasu da Ummiey sukai hira. I felt a complete being!Fitowata daga kitchen Ina goge hannuna da kitchen towel, wayata dake saman tv stand na hango tana ringing, karasawa nayi na dauka Ina murmushi kamar bakina zai yage+
” Abbah!”
” Amour howwa u?”
Nace lafiya Lau tareda tambayar shi kanshi yadda yake as always ya tabbatar min da lafiyar shi kalau, tareda fadin
” Kinje kinyi zaman ki, kin bar mutane da kewarki ko?”
Ni kaina Ina son Zama da Ummiey Amma believe me wallahi so nake na koma dutse, nayi kewar Daddy, siblings dina da uban gayyar!
” Zan dawo in two days time, yau su Amna zasu dawo”
Se yayi musu addaur Allah ya kawo su lafiya sannan yace
” Ko Zaki kunna data din ki? I’ve sent something to you”
Nace
” Definitely”
Ban ma jira me zaice ba na kashe wayar baki daya na kunna data tare da shiga Whatsapp, seda na jira dukka messages din Suka gama shigowa sannan nayi scrolling zuwa chat din mu na shiga, seda na zauna saboda uban pictures din daya turon, na fara downloading dinsu, atamfofi ne, laces da abayas . Kowanne daya turo looks fine, Kiran shi nayi nace
” Hombre ❤️ kayan menene?”
Yace
” Sunyi kyau?”
Nace
” Dukka sunyi kyau na menene?”
Yace
” It’s ok since you like them. Yawwa flight Zaki biyo Amma idan Zaki dawo ko?”
Nace
” Ehh, flight Zan bi zuwa Kano se na hau mota nazo dutse”
Yace
” Yafi Nima hankalina zaifi kwanciya. I don’t know your plan akan bikin? Zakiyi wani event ne?”
Na Dan yatsina fuska tareda girgiza Kai na kamar yana gefena nace
” No iya yini is ok”
” Saboda Zaki aura tsoho right…?”
Na katse shi da sauri nace
” Kai Hombre ❤️, ni ba haka bane ba fa…”
” To Yaya ne?”
Se nayi shiru kawai bance Masa komai ba Shima se yace min idan na Yi shawara I should alert him saboda satinnan yake son sallamar duk wannan abubuwan tunda bikin Kara matsowa yake. Aje wayar nayi Ina tunanin abinda yace and I was afraid ko yaji haushi ne. Ummiey da ta gama kwalliyar ta ta fito daga bedroom ta zauna tana kallon agogo tace
” Ba Zaki Kara ko da one week bane ba?”
Na danyi murmushi nace
” Ummiey Zan dawo fa, wannan ma excuse aka bani a gurin aiki shiyasa”
Se ta gyada kanta tace
” Shikenan ai tunda kinfi son baban ki a kaina”
Na danyi dariya Ina matsawa kusa da ita na kwantar da kaina jikin kafadar ta nace
” Ayya Ummiey why are you saying that. Zan dawo fa kuma Kinga yanzun I’ll be coming often tunda Abbah yaga Hanya”
Se ta Dan buga min baya na tace
” Kinga na manta ma fa, tashi kiga”
Na tashi na maida hankalina kan system din data jawo, kitchen utensils ne da equipment take nuna min, na maida hankalina sosae muna zaba, wani idan nace aa se ta fara fada min muhimmancin hakan, tace
STORY CONTINUES BELOW
” Batuul”
Kamar yadda take cemin, Bata taba cemin Nanah ko Fadima ba, da idan ta fada bana sanin da ni take, yanzun kuwan kowa a gidan Batul yake cemin, tace shi ne abinda tayi niyyar Kirana dashi tun bayan da Daddy yace Mata Fadima zai saka idan mace ta Haifa, she’s making up to
” So nake ki nutsu a gidan ki, kiyi ibada yadda ya kamata, ki faranta mishi Rai kamar yadda ya faranta Miki kema ki rama mishi, Allah ya sani banida wani da nake jin hankalina ya kwanta dashi kamar shi, yayi abinda uban ki dake Kiran yana son ki ya kasa for years…”
Na bata Rai nace
” Kai Ummiey Daddy ne fa?”
” Daddyn ni ai ba Daddy na bane.”
Na Kara hade Rai saboda bana son Bata face ta zageshi, kuma naga kamar har yanzun pain din abinda yayi Mata yana cikin ranta, se ta rungume ni ganin na Bata Rai da gaske ta bani peck a kumatu, nayi murmushi nace
” Ummiey ta”
Ta shafan fuskata,kafin tayi magana ihun Amna ya sata fadin
” Oh God! Your siblings are here!”
Na Mike da sauri na nufi kofar main parlon na bude, Yar budurwa Bata wuce Saar Aisha dita ba ta fado jikina tana fadin
” Yaya Batuul!”
Na rike hannunta ina murmushi sosae nace
” Welcome Amna”
Muka shigo tare, Sega Muhammad da Sadiq da Dadda dinsu, su seda suka je Suka gaida Nanne da maman shi itama a compound din take. Gaba daya part din ya kacame da murnar ganin Ummiey dani, har kasa na tsugunna na gaida Dadda sannan Ummiey tace kowa yayi wanka yazo yaci abinci. Haka kuwan sukai Nima kafin su dawo ni da Ummiey mun gama gyara parlon. Muka zauna cikin su munata hira and I felt I belong to them.
Kwanaki Suka tafi ranar Sunday tazo, tun Saturday da daddare Dana kwanta nake kuka Zan tafi na bar Ummiey, Ina son kuma komawa dutse wajen Daddy. Ana hakan Abbana ya kirani yaji muryata Ina kuka, kanshi ya dafa yace
” Amour what’s it, na zata mun gama kuka?”
Cikin kukan nace
” To Abbah ba gobe Zan dawo ba, kuma bana son barin Ummiey”
“Shhhhh….ya Isa haka. You know I love you right?”
Kaina na gyada Amma bance komai ba,yace
” Kinsan matata Zaki Zama, I can take you any where nake so, I promise you Zaki na ziyartar ta akai akai”
Da wannan ya lallashe ni nayi bacci, flight dina da safe ne, tun dare dama ta hada min Kaya da duk abinda ta siya min, se shirye shiryen biki take, a Dan zaman mu hatta kayan da Zan saka ta gama order dinsu kuma min riga min siya ma har na Kai dinki tunda dama haka muka Saba, Amma still ban Gaya Mata ba, ta kaini gun tailor ya gwada ni na zaba styles din da nake so.
Da naje yiwa Nanne sallama ta riko hannuna tareda min murmushi tace
” Se mun zo bikin, Allah ya bamu alkhairi ki gaida Yan uwanki”
Na gyada Kai Ina maida kwallar da take kokarin taruwa a idanuna. Mikewa nayi nai sallama dasu na shiga mota muka tafi, seda aka gama komai sannan Dadda ya dubeni yace
” Idan muka koma Abuja Zaki zo?”
Na gyada kaina dukda nasan ba haka bane amma to calm them yasa nayi karya, na rungume Ummiey na fara kuka bance komai ba, Ina jin yadda zuciyata ke bugawa da sauri, na saketa nace
” Ummiey se munyi waya”
” Allah yayi Miki albarka! Se nazo”
Daga haka na rungume Amna dake kukan Zan tafi, sadiq da Muhammed Suka dauka luggage din muka shiga sannan Suka koma daga inda se passengers kawai ke shiga. Tunda nayi boarding plane din nayi shiru, inata tunanin irin farin cikin da na samu a Yan kwanakinnan kuma duka Abbah Prof ne sanadi! A zuciyata yana da mukamin da bazan iya fada ba, Ina mishi son da Babu wani da namiji da Zan yiwa, Ina jin I can move the mountain for him, Ina jin Zan iya jure komai Dan na bashi farin ciki saboda Shima ya bani farin cikin da ban taba tunanin yana zuwa a rayuwa ba, kullum Rana burin shi kawai ya sani dariya, I remembered ya taba cemin only thing da yake buri a rayuwar shi shi ne ya sani farin ciki, kafin ya proposing seda yayi adduar idan dai shi ne zai bani farin ciki Allah ya dawammar damu tare, idan kuma bashi bane yana fata na samu Wanda zai sani hakan, Amma zuwan shi yasa komai nawa ya canja, na hadu da uwata through him!
Har bacci nayi kafin mu Kai, Ina sauka na kunna wayata na Kira Ummiey na sanar Mata mun sauka lafiya, tace
” To mu bamu koma gida ba ma, Dadda ya fita damu.yanzun ya zaayi kije dutsen?”
Nace
” Zan bi commercial drive ne”
Tayi min addua akan se munyi waya sannan na ja trolley na na fito daga departure hall. Wayata ce ta fara ringing na Ciro ta Ina murmushin ganin one and only Abbah Prof ke kira,
” Amour Kun karaso?”
Shi ne abinda ya fara tambaya bayan na dauka, nace
” Eh mun sauka yanzun nake Shirin barin airport din”
Se yace min ai yayi magana da Daddy Alan zai zo ya dakko ni, so yanzun gashi wajen da ake Taran mutane, naji dadi har Raina, Ina ta murmushi na karasa motar tashi, yana hango ni ya fito, yana sanye da brown trouser me haske se top da ya saka baka, he looks younger a cikin kananan kayan and as such you can mistaken him fa saurayi Dan talatin da wani Abu. Inata kallon shi har ya saka trolley cikin trunk din motar sannan ya zagayo gefena ya buden yace
“Kallon nan ya Isa haka, shiga mu tafi”
Naji kunya sosae na rufe fuskata da veil din jikina, Ina dariya kasakasa, muka fita a airport din ya daidaita akan titi sannan yace
” Har yanzun kunyar maganar tawa kike? Ki cire veil din daga fuskar Mana, na kwana biyu Banga murmushin ba”
Aikuwa na Kara sakin wani, se yayi Murmushin Shima ya cigaba da Jana da surutu har na ware, na fada Masa zai kaini gidan hibba Dan ta haihu kuma nasan idan ban je ba zaiyi wahala kafin biki na Kara dawowa. Ya jirani a mota bayan ya bani kudin barka dukda da farko naki karba Amma daya Bata Rai ban masan na karba din ba. Ta samu baby girl me suna Maryam haka muka Dan taba hira kadan sannan ta rakoni tana ta tsokanata Suka gaisa dashi
sannan muka dau Hanya. Ta ringim muka bi Dan se da na biya gidan Yaya mariya itama ta haihu, itama ta samu Mace sannan mukai dutse. Duk hirar tamu akan bikin ne, na fada Masa Ummiey tace zaayi kamu da nupe day a hade, Anty sumayya tace Zan hada ma friends dina get together a gida. Yace
” Tohm duk naji, ke wanne ne plan dinki? Kin ce na Ummiey Dana Anty sumayya wanne naki”
Nace
” Nifa Abbah…”
Ya katseni da fadin
” Wai meye Abbah ne? Ni fa bana son jin Abban nan a bakin ki.”
Ya fada yana hararata, nayi dariya nace
” To dadi yake min ni kuma, to Hombre ❤️?”
Yayi murmushi ya gyada Kai , hakan muka karasa gida bayan min gama tattauna wa, Ina son dinner a rayuwata Amma saboda na Kare martabar Abbah a wajen family dinsa shiyasa na kasa mentioning dinner din, na tabbatar duk yadda suke goya mishi baya akan aurennan bazasu so su ganshi yaje dinner ba, shiyasa na ce Masa instead of get together din se na gayyaci friends Dina da cousins Dina na hadejia Dana Bidda muyi dinner a gida, se mu dakko photographer, mu saka music da kanmu.