MISBAH CHAPTER 19 BOOK 1 END BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH CHAPTER 19 BOOK 1 END BY SA’ADATU WAZIRI

         WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 


Mun tsaya 

Doctor ,kaga nima doctor ne ,likita ne cikakke,sai dai ban kware ba,ni ba professional bane,hala ilminka ya kai inda za’a iya yiwa mutum wankin kwakwalwa?ka  bude mun kwakwalwata da zuciyata ka wanke mun su tas ,ina son manta dukkan mutanen nan a rayuwata,bana son tuna su balle in tuna abinda ya faru. Kaga wannan painful memories din abinda ya faru dani ,ina so ka bude ka wanke mun su duka saboda ba zan iya rayuwa da su ba,suna min ciwo sosai ,baza su barni in rayu ba ,ni kuma inaso in rayu. Please Doctor ka taimake ni..””

   Tun yanayi a hankali har ya fara da tsawa,lokaci guda ya haukace musu,da kyar aka samu aka masa allurar bacci ya kwashe shi.

     Ba mama ba har baba ya shiga cikin mummunan tashin hankali da Abba ,har suka yi nadamar abinda suka aikata masa.

   Mama tana kuka tana tofa masa addu’a haka daga farida har shamsu kuka suke bamai lallashin wani

Wasa gaske al’amarin Deeni ya tsananta,wani lokaci ka ganshi lafiya wani lokaci ya haukace musu,gana daya baya hayyacinsa,bai san me yake yi ba,hankalin iyayensa da masoyansa ya kai kololuwar tashi. Daga karshe Alh ya fita dashi kasar india ,anan aka ci gaba da duba lafiyar kwakwalwar sa,saboda abin yamatukar taba masa kwakwalwa,kwakwalwarsa ta kasa dauka da jurewa wannan damuwar.

    Ana duba lafiarsa a asibiti kuma ana masa rokon Allah,tare da sauke masa Alkur’ani ,da haka da taimakon ubangiji Deeni ya soma dawowa hayyacin sa. Sai ya zamana ya daina surutu tunda suka dawo gida,ba ya kula kowa ,baya cewa kowa komai. Kullum yana zaune a dakinsa,baya fita sai dai wani ya tafi masallaci ya dawo. In an kai masa abinci wani lokaci zai ci ,wani lokaci kuma haka abincin zai kwana wani ya tarar da wani

      Lokaci guda rayuwar Deeni ta canja ,ya yi baki,ya rame ,kuma baya aikin komai sai kwanciya da zaman gida. Ya dawo rayuwar sa sam bata da wani manufa. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

    A duk lokacin da Deeni zai kwanta bacci,to yakan rufo ido ya hango shi da farida,lokacin da hoton farida da shamsu zai bayyana a fuskar sa yakan yi saurin bude ido wanda a nan za su rine suyi ja,yaji kansa ya fara sarawa ,ya kama kai da kirji . Wani lokaci sai dai a shigo a same shi a sume. 

    Halin da Deeni ya shiga ya daga hankalin kowa a zuri’ar su,musamman iyayensa da kuma shamsu da farida. Wani lokacin mahaifin sa sai ya zubar da hawaye saboda bakin cikin halin da dansa ya shiga. Rayuwarsa ta dawo useless bata sa wani amfani ,ya yi da na sani tare da jin bakin cikin abinda ya yi.

     Kulum yana binciken asibiti ko masu maganin gida da za su dawo da shi dai dai,sai dai abu guda yake ji kullum,shi ne abin ya mugun taba masa kwakwalwa da zuciya,wanda fitar sa a wannan hali sai a hankali . Sai dai dayawa masu magani ko likitoci na bashi shawarar cewa ya canja masu wuri,wato ko dai ba ya bar garin ko kasar ,ko dai wani wurin da zai nesanta deeni da rayuwar da yayi ta baya.

   Wannan yasa Alh Umar ya tattara nasa ya nasa da kasuwancinsa ya raba su biyu ya koma lagos ,ya yin da ya barwa Shamsu sauran kasuwancin sa a kaduna .WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Alh Umar ya tattara iyalinsa,wato hajia A’i da Deeni da lukman suka koma garin lagos ,ya bar Arewa gaba daya. Saboda ya san Deeni yana da sha’awar zama a garin ,sannan yana ga zai ji dadin tafiyar da kasuwancin sa. Haka Deeni zai samu kyakkyawan canjin yanayi ,yayin da ya bar Shamsu da Farida a kaduna. 

     

    Tabbas Alh.Ahmad ya yi bakin cikin rabuwa da abokinsa,makwabcinsa,wanda yake kamar dan uwansa Alh. Umar . Ya daukar masa amanar dansa da kuma hakkin kula da shi da kasuwancin da ya bar masa,da ya dinga kokarin sa ido inda yaga ya karkace ya yi masa gyara.

     Farida da mama sun rabu cikin kuka tare da bakin cikin rabuwa da juna.

***      ***     ***    ****      **

    “”ALHAJI ! ALHAJI   !!

Haj. A’i ta shigo falonsa tana kwada masa kira .

    Ya kalleta a firgice ,” lafiya cikin daren nan ?

Ta mika masa wani farin takarda ,ya kalleta cike da mamaki.

   “Menene wannan ?

   Tace ,Address ne na samu,inda zamu kai Deeni,yanzu na kasa bacci na kunna tv kenan naga suna tallen wurin nan. Na lura masu matsala irinta Deeni sun samu waraka..””

  Ya kalleta ransa bace ,ya ce,”Dana ba mahauci bane ,kuma ba dan shaye shaye bane da za a kaishi REHABILITATION CENTER 

   Cikin nuna damuwa Haji. A’i tace. Alhaji ka duba ka bincika ,wannan wurin ba mahaukata ko ‘yan shaye-shaye bane,kafin in baka sai da nayi bincike naji komai akan su. Abinda yafi jan hankalina gare su ahi ne,sun hada da Addini da kuma magungunan musulunci . Deeni yana bukatar taimako na Addini da na asibiti duka,wanda duk sun hada.

       Dakyar ta samu ta shawo kansa ya yarda zai binciko,in ya masa yadda hankalin sa zai dauka to zai yi tunanin tura Deeni wurin…..

Ruwan sama ake tsugawa sosai ruwa irin na lagos,wanda idan ya fara sai anga tsayawarsa. Iska ce me hade da feshin ruwa ya shigo ta windo ya wanke mata fuska,hakan yasa tayi saurin bude ido hade da addu’a. 
    Ta mike ta nufi jikin window din ta lumshe ido tana shakar daddadar iskar da ke dukan fuskarta tana jin yana ratsa ta ,yanayin da tafi so fiye da kowanne yanayi kenan.tuni taji zuciyarta tayi mata fari,ta tsinci kanta cikin wani nishadi.
    Karar door bell ne da aka danna ya ja hankalinta zuwa kofa,Doctor Bahijja kenan tayi saurin zarar hijabinta ta nufi kofar falon , a nan mai gadi ke fada mata suna da baki da ke son ganinsu,sunje cikin asibiti aka ce basu iso ba ,shi ne suka biyo su gida,sun ce wai yana da matukar muhimmanci suga likita. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 
   Tayi murmushin da tasaba wanda kullm yana makale a fuskarta ,ta ce
 ” Kaisu falon baki,kace su jira ko ?
     To madam
Ya amsa tare da juyawa ,duka cikin harshen turanci suke maganar..
    Nan ta juya ta nufi dakin barcinsu,kai tsaye ta same shi har yanzu bacci yake duk da iska mai sanyi da ke ratsa dakin ,yana ratsa fuskar shi bai sa shi farkawa ba .
      A hankali ta sa hannu tana jan bargon da yake lullube tana murmushi ,amma sai ta ga ya dunkule guri guda ya ci gaba da baccin sa tamkar wani baby.
    Ta kalli kyaykkyawar fuskar sa me kunshe da annuri da lafiya ,tare da kwanciyar hankali . Soyayyar sa taji ya kara tasiri a zuciyarta ,cikin muryar shagwaba tace.
   “”Please my dear” ka tashi mana,kana da baki “
   Bai saurareta ba sai kokarin jawota jikinsa da yayi yana narke mata a jiki,ya cigaba da kwanciyarsa a jikin ta,yana jin sonta na karawa baccin nasa dadi.

    Girgiza kai tayi tana murmushita kwace jikinta tare da sa hannu tana jan hancinsa,tana wasa da shi .
     My dear please ka tashi ka duba time fa karfe sha daya na safe ,baccin ya isa haka. Ba don ruwan sama ba da fa ka fita tun karfe takwas.”
   Cikin muryar bacci ya ce,”shiyasa nake son damuna ,yana bani hutu ,ina samun nutsuwa da Bahijja na,amma ina!! Wannan likitar ba zata bar wannan likitan ya huta ba.
    In barka ka huta daga baya kace me yasa ban tashe ka ba ? Ka fa tuna me kace mun “
  ,” Komai bacci me dadi da nake ki tashe ni ko da kamshin jikinki” 
 Rungumota ya sake yi ya cigaba da kwanciyar shi”
 Bata kulashi ba ta mike ta nufi gadon Muhammad da taji alamar ya tashi yana ta ciccilla kafa yana wasa tare da surutai irin na yara. Yana ganinta kuwa ya wangale baki yana mata daria,yana sanye da body suit dinsa masu kyan gaske da ban sha’awa .(hmm, kaga dan likitoci ,😀)kaunar dan nata taji ya kara shiga zuciyarta ,dariyar da yake mata ya sa taji kaunar danta har cikin zuciyarta tare da godewa Allah da ya azurta ta da kyakkyawa kuma lafiyayyen da son kowa.( dama ahalin likita na cuta ne 😜😜ciwon ma tsoran gidan likita yake)
   Tasa hannu ta daga shi,yaro ne da bai wuce wata shida ba ,ta rungumo shi a jikin ta ,ta ce. 
    Ni dai na kasa tashin Abbanka ,amma ni da kai zamu tashe shi tare.
   Nan taje ta ajiye shi a kansa,nan da nan ya wangale baki har da tsalle saboda ya ga abokin wasansa. Nan ya hau sukuwa a kansa yana jansa tare da masa yaren su na yara ,dolensa ya bude ido yace. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 
   ” Ta nan mommyn ka ta bullo ko ? Ta hada ni dambe da kai,to bari in mike muyi.
  Nana ya tashi ya biyeshi suna wasa yana cilla shi sama ,shi kuwa yana ta dariya,itama ta taya su. Sannan ta barsu ta nufi toilet don shirya masa bayi ,ya yi wanka . Tazo ta karki Muhammad ta kai shi gurin baba Andi,dattijuwa me kula da shi in bata nan. Sannan ta dawo ta taimaka masa ya yi wanka,ya shirya kusan komai ita ta masa,hatta turare ita ta fesa masa ,gyaran fuska da komai ,sannan ta kalleshi ta ce . 
    Perfect!!! Mijina is d best” Ya jawota jikinsa yace,”A’a mama ta is d best ,,ina sonki Bahijja na,ina son ki sosan gaske ,musamman in kina sakaltani ,ina jina kamar dab baby. Zan iya yin tiyata inyi allura in bada magani in duba mara lafia,amma ba zan iya kula da kaina ba,ko daurawa kaina tied bazan ita ba balle shafar mai ko sa kaya. Ko siyen sutura nawa ban iyawa saboda Bahijja na ta bata ni,ban iya komai nawa.
   Allah ya bar mun ke Bahijja na,Allah ya miki albakrka ,Allah ya hadani da ke har a gidan aljannah”
     ” Ameen my dear””
 Ta fada a lokacin da take kokari. Kwanciya a jikinshi,idon ta a lumshe ,ta ce.
   Wa zan sakalta in bata in ba mijina ba ? Kai ne first baby na,babyna na farko kafin Muhammad,kaine zuciyata, kaine rayuwata,kaine mutumin da bazan taba gajiya da masa hidima ba har iya karshen rayuwata. You are my world nd my happiness duk wani abu a duniya bayan Addini na to komai ya biyo bayan kai da Muhammad ,bani da kamar ku.
   Aure na da rayuwarsa gaba daya na daukeshi ibada ne,sai nayi dace da samun soyayya da kwanciyar hankali da duk wani abu da mace zata bukata a rayuwa . Na gode Mislihu ,Allah ya saka ma da gidan Aljanna. Duk wani abu da nake maka ban yi rabin wanda kake min ba .”
     Yayi murmushi ,A duk lokacin da na kalle ki da Muhammad da kuma asibitina,yadda kike taimako na ,kika fahimce ni,yadda kika yi spporting dina sai naji tamkar Allah ya biya mun dukkan wani bukata ta na rayuwa,sai fatan Allah ya hadani da ke har a Aljannah. Ina alfahari da ke Bahijja.”
   Tayi murmushi ,Nima ina alfahari da kai Mislihu..”
   Nan ta ja shi zuwa dining area kamar kullum kamar yadda suka saba,ta tabbatar ya ci ya sha abinda ya kamata ,sannan ta raka shi har kofar ya fita wurin bakin sa. Sun rabu cikin soyayya da kaunar juna kamar yadda suka saba.
       Dr Mislihu ya samu bakinsa a falo Alh. Umar ne da amininsa Alh. Tahir suka zo da maganr Deeni . Nan ya nemi jin abinda ke damun sa ? Me ya faru dashi ? Dan yana son ganin medical report dinsa wanda ya tabbatar musu da sai in yaji case din irin wanda suke maganin matsalar sa ne ,to zai karbe shi. 
Alh. Tahir ya masa bayanin komai sannan suka yi alkawarin kawo mishi medical report dinsa washegari. Da wannan suka rabu akan za su hadu washe gari a cikin asibiti……… . 
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 
MU HADU A BOOK 2 WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *