Wata Zankadediyar mata ce ta gifta a wata mota, akan titin Nasarawa G.R.A, Kano. Hakika matar nan ta hadu, ga kudi, ilimi, ga kyawu duk daga Rabbil samawati. Malaika a zaune take da nono a bayan
Babur ana ta zuga gudu da ita, amma bata cikin hayyacinta, bata Kara sanin inda hankalinta yake ba tun sanda ta yi arangama da wannan Zankadediyar matar da ta gifta ta gabansu a cikin tsaleliyar mota.
Ta zama tamkar mutum-mutumi, ta daskare kamar kankara, ji take tamkar ba’a cikin wannan duniyar take ba. Tunani ya wurga ta wata sabuwar duniya, dan haka bata sake fahimtar abubuwan da suke faruwa a gabanta.Jirgin tunani ya lula da ita duniyar gajimare, ta hango ta har ta zama waccan matar itama ta shige cikin tsaleliyar mota tana juya sitiyari.
Malaika bata farfado daga duniyar tunani ba sai da ta ji muryar mijinta yana kwada kiran sunanta. Ta yi firgigit ta dawo duniyar da take sai a lokacin ta ga ashe har sun shigo cikin asibitin Nassarawa. Da ta ganta a bisa Babur sai ta ja dogon tsaki, ranta ya baci dan ita tunaninta ya kai inda tayi male-male a cikin jirgin sama ma ba a mota ba.
Kallo dауа Shamaki ya yi mata ya
tabbatar ciwonta na tunanin’ kanzon kurege’ ya tashi.
Ya harare ta ya girgiza kai, yace “amma kina tare da wahala in dai yanzu ma tunanin nan kike mai kama da mafarki. Na yi miki nasiha, na yi miki fada, na yi gargadi amma duk a banza. Allah Shike azurtawa, Shine mai talautawa, ki gode maSa da Ya baki lafiya Ya rufa miki asiri, Ya baki miji mai zuciyar nema dan ban taba barinki da yunwa ba. Ya baki yara uku biyu masu lafiya daya ne mai sikila, amma sai Ya bamu hali da damar jigilar kawo shi asibiti, Ya bamu kudin siyan magani. Ba ma bara, ba ma rokon wani ya taimaka mana.”
Malaika ta ji nasihar mijinta tamkar zaginta yake, ranta ya baci, ta turo baki gaba ta kawar da kai gefe, sai kuwa idanuwanta suka dira akan tsaleliyar motar Zankadediyar matar nan data hango a kan hanya ashe itama asibitin zata je. Sai Malaika ta shiga murmushi tana yi mata kallo tamkar ta hadiye ta. Tuni ta manta akwai wani bawa a kusa da ita yana yi mata magana.
“Tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya halicci wannan mata mai kyau da kudi.
Wannan idan ba minista bace to matar minista ce. Zankadi! Ga kyan fuska, ga dirin jiki, ga ilimi. DA MA NICE . . . ” Malaika ta fada a bayyane ba tare da tasan zancen zuci ya fito sarari ba. Yayin da take kallon matar tana murmushin kauna.
Sanda matar ta fito daga mota ta zo ta gifta ta gefen Malaika, sai Malaika ta lumshe ido ta shaki daddadan kamshin turaren jikinta.
“Hakika wannan mata ko a cikin masu kudin ma ita ‘yar gayu ce. *Dama in zama kamarki.
(” Malaika ta fada cikin rada amma karab a kunnen
Shamaki.
Sai ya ji takar ya dora hannu a kai ya rusa ihu amma ya daure, ya girgiza kai ya saka hannu a aljihu ya dauko kudi Naira dubu daya ya mika mata, shima bata san yana mika mataba har sai da ya nanika mata a hannu, tana can tana kallon Matar nan.
Ya fada a fusace “ki je ki bi layi da sauri, da na yi niyyar jiranki har ku gama in mayar da ke gida, amma naga alamar kin shiga layin da zaki ci gaba da bata min rai gara in kin gama ki hawo adaidaita sahu ki dawo gida.”
Ta kalli kudin ta jujjuya ta yamuise fuska ta ce «a dubu zan yi kudin adaidaita, in sayi magani in yi cefane? Cafdijam.” Yace “kada ki sayi magani ki kawo min katin da daddare zan saya a kemis din unguwarmu, muna saka ran karbar albashi yau.”
Malaika ta wuce a fusace tana zunkuda goyo tana gunguni, ta ce “Allah Ka raba ni da auren talaka, komai babusai kullum an jira albashi.” Shamaki ya dade a tsaye yana kallonta cike da takaici. Ji yake tamkar ya dauko hankali da tunani ya cusa a cikin kwakwalwar matarsa. Yana kallonta bata nufi layin mararsa lafiya ba, ta nufi ofishhin da wannan matar ta nufa. Ya san magana zata je ta yi mata idan taga fuska sai ta tambayi lambar waya da adireshi. Ya san ko ya bi ta, ba zai iya hana ta abinda ta yi niyya ba, dan bata ganin girmansa saboda shi talaka ne. Ya ji kwalla ta cika masa ido ya hau kan babur dinsa a sanyaye ya burga ya yi gaba.
Gudu yake ta shararawa a hanya dan tafiyar ta sa da yawa daga nan zuwa. Jami’a (B.U.K) ba karamar tafiya ba ce, ga go slow a hanya kasancewar yau litinin ma’aikata da ‘yan makaranta sun firfito. Tabbas ya san ya rasa laccar karfe takwas zuwa tara sai dai ya sami ta karfe tara zuwa goma shima sai ya yi da gaske sannan zai samu.
MALAIKA SHAMAKI
Zuciyar Malaika cike da fargaba ta nufi ofishin da hadaddiyar matar nan ta shiga amma sai ta tsaya a bakin kofar ta kasa shiga don ta na jiyo muryarta ta na magana da maza likitoci cikin harshen nasara, nan ma suka tafi da imaninta dan tana so ta ji ana ragargazar yaren Nasara abin yana bata sha’awa.
Kwatsam! sai ga wata burdurwar yarinya mai dankaren kyau, ilimi da gayu, ta ci ado da dankareren leshi ko gale bata yafa ba tana tafe, tana rangwada tamkar ba zata taka kasa ba. Da alama a cikin hutu ta taso, dan babu alamar wuya a tare da ita. Ta na rataye da jakar
“lap-top’ a kafadarta, tafiya take ta na amsa waya, wayar ma abar kallo ce, ta zamani.
Da ta zo daf da Malaika zata wuce sai
Malaika ta zabura ta dafa kafadarta, ta ce
“sannu kawata. Dan Allah ina da tambaya.”
Kyakykyawar budurwa ta yi mamaki bata san sanda ta katse wayar da take yi ba, ba tare da tayi sallama da shi ba.Ta zubawa Malaika ido tana jiran ta ji tambayar.
Hmmm