biyunsa Kaduna, a yanzu mun kirkiri kamfani guda uku Bauchi Sokoto sai Abuja duk da cewar reshin mu na Abuja hadin gwiwa ne to amma hakan ma nasara ce, kamar yadda na za6o ku na kiraye dukkanin ku, ku ne zababbu kuma wadanda zasu tafi domin kulawa da wadannan kamfanoni, na so abin ya gudana tun a wancan watan to an samu akasi saboda samuwar hadari dayan mu wato Umar Abubakar.
. Gaba ki dayan ku, ga takaddun ku na wuraren da za
ku tafi. Fatan nasara a gare ku, ba ma fatan mu sake bukatar ku, a nan sai dai fatan mu bukace ku yayin da aka Kara samun bunkasa zuwa Ghana Nijar da sauran kasashen da suke kewaye da mu.
Kowannen daga cikinsu aka kira shi aka ba shi
envilop wacce take da takaddar apointment na in da zai nufa.
Bayan sun amsa sannan ya Kara tabbatar musu cewar
akwai sakonnin da suke tafe insha Allahu zuwa safiya kowa zai ga na shi,
Umar zaune yake yana juya envilop din dake
hannunsa domin kwata-kwata bayanan basa yi masa dadi don bai yi zato ko tsammani ba, yana jin cewar zai iya mayar da bukatar mai gidansa domin baya jin zai iya barin kano ya tafi wani gari saboda jin dadin zaman da yake a garin. Amma a lokacin da Alhaji Nasir yasallami kowa sai ya yi umar ni da Umar da ya jira tare da Zilahat, Bayan kowa ya ta fi Umar da Zalihat na zaune. Alhaji Nasir ya dube su ya ce “Na ce ku jira ne saboda ina son muhimmiyar magana da ku, amma kafin nan ina so ku bude.
‘enbelop din ku”
Umar da Zalihat suka warware a nutse suna duban
sakon dake ciki. Gaban Umar ya fadi lokacin da ya ga an rubuta Abuja.
«Amma Alhail ya a ka yi haka, bana bukatar zuwa
Abuja?”
Alhaji Nasir ya dube shi “Me yasa?”
Umar ya yi shiru saboda bai da amsar da zai ba shi.
Alhaji Nasir ya ci gaba da cewa “Umar kai ne kadai ake bukata a cikin ma’aikatar Abuja, dalilinka mu kasamu hadin gwuiwa da WOLD DECORATED AND AND BUILDING yarjejeniya a tsakanin kamfanonin biyu nasara ce ba karama. Umar duba, ka fahimce ni,
na riga da na fuskanci irin damuwar ka, saboda tun a lokacin da
ka zo jahar kano baka bukatar wani abu ya hada ka da Abuja, ban
san dalili ba, sai dai a kodayaushe ina tuna maka cewar nan ne
mahaifarka nan ne cibiyar family na ku, babu wani abu da yafi
dangi, kome ne ne ya rabo ka dagarin ku, to komai kuma naka
yana can, ina da kyakkyawar zuciya a kan ka, ina so ka rayu a
Abuja duk da jin dadin kasancewarka da ni a nan. Ka taimakawa
kasuwanci na ka taimakawa zumüncinka domin samun albarka
rayuwa ka da wani abu ya shige maka duhu, ga Zulihat na san
cewar za ta taimaka maka fiye da kima, amana ce ita a gare ka,
wannan tamkar shi ne matakin daukakar ka, ina fatan ba za ka zuba min kasa a ido ba
“Amma.”
“Ba sai ka ce komai ba, shi ke nan?”
Alhaji Nasir ya katse shi. Umar ya ji abin da ya yi bai
kyauta ba don haka yasanyaya?”
“Me yasa ba ka tambaye ni dalilin da yasa bana son
zuwa Abuja ba?”
“Saboda na san tun fil’ azal baka bukatar a tambaye
ka, tun da baka taba sanarwa da kowa ba”
** Na amince, na kuma gode bisa Kokarinka na nuna
mana hanyar ci gaban mu”
Ba tare da ya ce komai ba ya mike “Na barku lafiya
ku yi shirye shiryen ku a nutse sati mai zuwa ya ishe ku shiri.
Ke kuma Zulihat, dalilin ina da magana dake ba wacce ta shafi kamfani ba ce magana ce da ta shafi family kafin
ku tafi ki tabbatar da cewar kin same ni available”.
Insha Allahu kawu”
Suka mike suka fita a tare “Umar in ba za ka damu ba
ina da tambaya?”
Ya dube ta “In dai dangane da Abuja ne ka da ki
tambaye ni Zulaihat, ba yau kadai ba ma har abada”
Ransa ya sosu sosai don haka ta dakata maimakon ta
Kara cewa wani abu ta ce “Shi ke nan Allah ya tashe mu lafiya?”
Bai bata amsa ba ya shiga mota ita ma ta shiga tata
motar suka bar wajen
BIRNIN TARAYYA
Umar Abubakar da Zulaihat Rashid sun shiga Abuja
cikin karramawa da aka shirya a babban hall na cikin kamfanin
WAB saboda tarbar su, saboda Karancin lokaci da ake da shi yasa suna sakkowa daga jirgi kamfanin suke nufo. An shirya taro ne na dan mintuna talatin za a ci asha a kuma gabatar musu da office dinsu.
Kamar yadda aka tsara haka ne ya tabbatar. Jawabin
da Umar ya yi a wajen taron ya tabbatarwa da ALhaji Hashim cewar lallai labarin da yakeji na yaron sumun tabidi ne
Lokaci shi ne rayuwarka, ka yi amfani da shi kafin
kurewarsa, ba da muhimmanci a kan lokacinka sharewar zunubanka ce, in har ka na da Kokarin wajen ba wa komai muhimmanci to lallai za ka nemi lokacin shiririta ka rasa a rayuwarka. Ina so na gaya muku a takaici ba wa komai muhimmanci shine jagoran ci gabana na dan kankani lokaci.
Daga karshe ina yi muku fatan nasara ina rokon
Allah ya ba mu ikon yi wa kamfanin ku dai-dai, kuma ku yi mana dai-dai.
Bayan gama jawabinsa aka tafa masa. Haka ita ma
•Zulait Rashin ta yi nata jawabin. Duk abin dake faruwa Abas na zaune a kusa da mahaifinsa shi da Alhaji Sunusi sun saka kujerar Alhaji Hashim a tsakiya.
Alhaji Hashim mutum ne mai kwazo mai bayar da
himma ga mai himma, babban abin da yake masa dadi a rayuwa ganin mutum mai mayar da hankali akan nema, wadda baya wasa ko kadan wajen neman na kai. Sannan Kwararre a fännin aiki, wannan dalilin ne yasa ya farauci Umar ta amincewa da su saka hannun jarinsu a kamfaninsu.
An ci an sha an yi hotona, sannan an gabatar musu da
office dinsu. Sannan ne Umar ya nufi gidan su. A shekaru uku da suka gabata bai ko ta ko in da suke ba, saboda yi musu ba zata bai sanar da su komai dangane da zuwan na shi ba abin da bai sa ni tuni alhaji Nasir yasanar da su komai dangane da shirin sa na dawo da shi gida.
Rantsattsiyar mota ta yi parking da shi a köfar gidan direban ya fito ya bude masa, sannan suka yi sallama ya zubawa gidan idanu, gyare gyaren da yasa a yi a gidan na su ya gudana abin ban sha’awa ya bi gidan da kallo abu daya yake ta kokarin dawowa masa cikin zuciyarsa amma yana ta kokarin ganin ya hana shi zuwa gare shi amma sai da ya tuna. A kofar gidan a tsaye shi da Yasmin “Ina son na zauna a gidan nan abin so na dan Allah”
“Mu da muke da rayuwa mai fadi dan meye zamu
rayu a cikin gidan manya, ni a ganina ki sauya tunani ina so na rayu dake a in da ko kuda ba zai takura mana ba, ki ajiye wannan don ba zan iya ba’
Ta shagwade kamar za ta yi kuka “Ka san me yasa
nake son na rayu da Mama?”
Ya shiru yana dubanta “Ina son na samu na koyi irin
dabi’ unka, kullum kwaikwayon kana ke na kasa dan Allah ka rabu da ni na zauna tare da ku, ina son kowa a gidan nan kowa na. birge ni”.
Ya yi murmushi “Yasmin Ke ma rayuwar ki abar so
ce, abar yabawa ce kowa a cikin gidan nan sha’ awar rayurki yake kowa son ki yake Yasmin”
Ta yi murmushi ta na kallonsa “Dagaske”.
*. Murmushi shi ma ya yi ta ce “Ina son Mama dan
Allah Umar?””
“Mene ne?”
“Anan gidan zamu zauna”
Kiran da Mama ta yi masa a lokacin da ta fito daga
cikin gida yasa ya dawo daga duniyar tunani. Yana murmushi ya karasa. Ta fahimci damuwa karara a tattare da shi don haka take ta nan nan da shi don ta mantar da shi akan damuwarsa.
Bai yi tsammani ba ashe duk yan gidan na nan suna
jiran Karasowarsa. Ya yi ya yi su gaya masa wane ne yasanar da su zai zo amma ba wanda ya gaya masa.
Shagali da abinci mai rai da lafiya a ka zuba masa
yasha santi abincin Mama kuwa.
**
A lokacin in abincin dare Yasmin na zaune a daki
Siyama daya daga cikin ma’ aikatan gidan Alhaji Hashim ta shigo cikin dakinta, “Hajiya Yallabai ya ce a sanar dake lokacin dinner ya yi”.
Wani irin takaici ne ya kamata ta dube ta “Ga ni nan”.
Siyama ta fice daga cikin dakin Yasmin ta gyara
kwanciya sai dai wani abu da yasa tayi saurin ta shi ta san in ma ba ta fita ba sai ya shigo mata cikin daki ya takura akan ta je su ci abinci, dalili ke nan yasa ta daka tsaki ta fita falon.
Wato na fuskance ka Abas ba ka yi farin ciki da zuwan Umar ba.
“Me yasa ka ce haka Daddy”.
“Saboda na ga kwata-kwata ba ka farin ciki a yau, ina
fuskantar abin da ya faranta maka da wadda ya bakanta maka a kan füskar ka. Ka sa ni cewar ni mutum ne wadda a yanzu busness ne rayuwata, duk abin da zai habbaka rayuwata da ta ka to zan yi Kokari na mayar da hankali a kai, yaron nan yana da matukar amfani a gare mu, ina son mutum mai amana jajurcewa da kuma sadaukarwa. Umar ya hada komai don haka ka da ka nuna masa halayen kana zahiri domin ina son kusamu shiri sosai ta hakane zamu cimma gaci akan al’amaruran mu.”
- Abas ya yi murmushi “Daddy ba wani abu ba ne
- kawai yana ji da kansa ne, ni kuma ban ga wadda zai ji da kansa ba bayan ina nan, saboda haka dole a taka masa birki”.
“Ji da kai dabi’ace ka yi iyanaka shi ma zai yi iyana
shi, abin da na sani bai isa ya kai yakai ba”
Abas ya kwashe da dariya, mahaifiyarsa ta saka musu
baki tana dariya “Ka ji shawarar mahaifinka Abas duk wadda ya zo domin samun arzikin mahaifinka ya zone domin ya taimake ku, saboda haka bawanka ne shi, sai dai ka yi Kokari ka sarrafa shi ta siga mai sauki”.
Abas yasaki jikinsa musamman ganin Yasmin ta Kara
so, ta zauna a mazauninta kusa da shi,
“Sannun ku da yamma?”
Ta fada duk suka amsa “Yasmin me ke damun ki ne,.
na ga alamun kadaicin nan ya fara yi miki yawa kina da basira kina da amfani da gudunmawa da zaki ba mu ya dace ka samar mata office a kamfani mana Abas”
Abas ya yi dariya “Daddy ka ga ga ta nan ka yi mata
wannan kokarin ni ma haka nake fata”
Hmmm