JIDDATULKHAIR CHAPTER 31 BY KHALISAT HAIDAR

Jiddah ta goge idonta still ta ki cewa komai, Umma tace “Baxa ki min magana ba Jiddah?” A hankali Jiddah tace “Umma yace min babu aure tsakanina da shi” Umma tace “Kamar ya babu aure a tsakanin ku?” Jiddah ta gyada kai tace “Eh haka yace, wai shi ba mijina bane” Umma tace “A ina yace hakan?” Jiddah tace “A can gidansa, ya rubuta ne a takarda ya bani” Umma ta dinga kallonta kafin tace “Ina takardan?” Cikin sanyin murya tace “Ya ki bani” Umma tace “Amma ya nuna maki?” Jiddah tace “Ehh” Umma tace “Cewa yayi ya sakeki a takardan?” Nan ma tace “Ehh haka yace, shi ba mijina bane” Umma ta gyada kai bata kuma ce mata komai ba, bayan kusan minti goma ta mike ta fita dakin rike da wayarta, wani dakin daban ta shiga tayi dialing number wata aminiyarta tana dagawa tace “Hajiya karfe nawa xa ki taho?” Hajiya Rukayya tace “Ina hanya yanxu haka” Umma tace “Babu kowa gidanki?” Hajiya Rukayya tace “Toh na bar su dai suna ta shirin tafiya dinner da wani abu ne?” Umma tace “Toh shhkn tunda ba kowa, dama wata yar uwarmu ce aka kawo biki to bata son hayaniya, kinga nan din ma akwai taro shine da nake son ta xauna gidanki har bayan biki” Hajiya Rukayya tace “Ohh Allah sarki, to amma Badiya mai aikina na nan ai, ba sai su xauna tare ba” Umma tace “Yauwa toh, xan sa driver ya kai ta can din kawai, sai ki kira ki sanar mata bakuwa na xuwa” Hajiya Rukayya tace “Toh ba damuwa” Umma ta koma dakin da Jiddah ke ciki tace “Kaya kala nawa kika taho da?” jiddah tace “Na yau ne da gobe kawai” Umma tace “Ohk, xaku fita da driver xai kai ki gidan kawata yanxu, tunda naga ke ba son taro kike ba ai” Jiddah ta d’an yi shiru, sai kuma a hankali tace “Umma ai yace xai dawo anjima ya daukeni” Umma tace “Ehh kafin ya dawo din, sai yaje can gidan ka ya daukeki, ki tafi da jakar kayanki kawai” Jiddah tace “Toh” Bayan mota Umma ta sa ta shiga ta ajiye mata jakarta a gefenta, sannan driver ya bar gidan bayan ta sanar masa inda xai kai ta, tafiyar kusan minti ashirin da wani abu suka yi suka isa gidan Hajiya Rukayya, Drivern yayi ma mai gadi maganan cewar yayi leading dinta har entrance din gidan, tana shiga cikin compound din mai gadin ya nuna mata direction da xata bi, ta makale jikin kofar ta kwankwasa a hankali, ta fi minti biyar tsaye sannan aka bude kofa, wata mata ce ta bude kofar ganinta tace “Ke ce bakuwar da Hajiya ta sanar kina xuwa?” Jiddah ta gyada mata kai kawai, Badiya ta amshi jakar hannunta tace “Toh sannu da xuwa, Bismillah” Bin bayanta Jiddah tayi, ta xauna parlor, Badiya ta shiga dakin yan matan Hajiya Rukayya ta ajiye mata jakarta. Karfe biyar saura Abuturrab ya isa gidan Umma, ya fi minti biyar cikin mota sanin da mutane gidan shi kuma ba iya shiga xai yi ba, daga karshe kawai Maman Abdallah da ya gani a compound ya aika ta kira masa Jiddah, ba a dau lkci ba sai ga ta, tace “Wllh yallabai Umma tace suna can gidansu amarya” Da mamaki ya dinga kallonta, can yace “Toh nagode” Tada motar yayi ya bar layin ya dau hanyar gidansu, bayan yayi parking a waje ya dau waya ya kira Siyama tana dagawa yace “Ki ce Jiddah ta fito” Tace “Yaya mu muna wajen make up fa, kuma har muka bar gidan bamu ga ta xo ba” ya d’an yi shiru, kafin ya katse wayar. Tunanin wanda xai kira ya dinga yi a ciki amma ya ga ba kowa kuma don ko hauka yake ya san baxai kira Ummi ba, d’an tsaki yyi ya tada motarsa ya bar wajen. Tun da Abuturrab suka isa wajen da ake dinner tare da Ahmad da sauran abokansu yake xuba ido yaga inda xai hango Jiddah a wajen amma bai ga alama ba, hakan bai wani damesa ba don dama xuwa dinner din ne baya son ta xo ya kaita can gidan Umma, tun sanda Aneesah ta kyallara ido ta gansa take masa zarya a wajen, barin yanda taga yayi wani kyau cikin fararen shaddan da duk abokan Ahmad suka saka, ita a dole sai ta ankarar da jama’a cewar saurayinta ne, Ko mayafi bata daura kan damammen doguwar rigar jikinta ba shi dai sai bin ta yake da kallo, wani abokin Ahmad dake side din Ahmad din Abuturrab ke ta kallo yana son tuna inda ya ta6a ganinsa, he looks familiar amma dai bai ce masa komai ba, karfe goma saura Aneesah ta xo ta samesa tana yauki tace “My captain wai xaka xo ka maida su Mummy gida yanxu” Ya d’an kalleta yace “Toh ai bani na taho da motata ba, ban ma san inda yake yanxu ba, nima abun hawa na samu ya kawo ni nan” Tace “Haba Captain, ko wajen daya daga abokanku baxa ka amshi mota ka maida su gida ba….” Ko rufe baki bata yi ba sai ga aunty ita ma ta sha wani ubansun lace tana goge xufan goshinta da handkicin hannunta tace “Aliyu ka tashi ka maida su Hajiya Safiyya gida” Bai ce mata komai ba, tace “Ko baka ji na ne?” Yace “Toh bari in nemi wanda makullin motata ke wajensa” Juyawa tayi ta bar wajen, ya kalli Aneesah da ta hade rai tana kallonsa, d’an murmushi yyi yace “Kema dai kinsan wasa nake, dole in nemo mota ko na waye in maida su” Yana fadin haka yayi patting shoulder din Umar dake side dinsa yace “Bani makullin motarka pls” Umar ya mika masa sannan ya mike yace “Kice su fito” Daga haka ya nufi hanyar fita daga hall din…. Karfe daya Abuturrab ya koma gidansa bayan sun maida duk bak’in da suka je dinner masaukinsu, ya fi minti goma xaune a parlornsa thinking of where Jiddah might be, daxu da ya maida Mum din Aneesah har gida ya shiga bai ga alamar tana nan ba, shi kuma ya kasa tambayar Ummi, akwai wasu bakin da still ya mayar can gidan Umma, can ma ya shiga bai ganta ba, bayan kuma ya tambayi Maimoon tace ai tana gidan Umma, mikewa yayi daga karshe ya wuce sama xuwa dakinsa don ya gaji sosai. Da asuba kiran sallah ya farkar da jiddah, ta mike xaune daga kan gadon da take tana kallon yarinyar dake kwance saman gado gefenta, tun xuwanta gidan jiya banda ita da Badiya bbu kowa a gidan har tayi bacci wajajen karfe goma saura, bandaki ta tafi ta dauro alwala ta fito sannan ta tada yarinyar da baxata wuceta ba, yarinyar ta mike xaune, ita kuma ta shimfida darduma ta fara sllh…. Karfe tara saura yarinyar da tayi wanka ta shirya cikin atamfa ta kalli Jiddah tana murmushi tace “Ya sunanki?” Jiddah tace “Jiddah” Yarinyar tace “Ni sunana Amina, mu je parlor mu gaida su Mama sun fito” Jiddah ta saka Hijab dinta ta bi bayan yarinyar suka fita parlor, yan mata biyu ne xaune parlon sai Hajiya Rukayya, wanda Jiddah na ganinta ta gane mahaifiyarsu ce don sun yi kama, Jiddah bata yarda ta xauna kan kujera ba ta gaida matar, ta amsa da fara’a tana tambayarta ta tashi lafiya, Jiddah ta sunkuyar da kanta, sauran yan matan ma sai kallon Jiddah suke, Wani ne ya shigo parlon daga waje waya kare kunnensa, ganin mahaifiyarsa a parlon ya katse wayar ya zauna yace “Ina kwana” Tace “Lafiya lau… Jiya kuma sai kayi wucewarka ka bar mu a event center” Yace “Mama ciwon kai wajen ke sa min, it’s been long da na tsaya waje that’s so noisy haka” Hajiya Rukayya tace “Toh Allah ya kyauta” Tun da ya shigo Jiddah ke kallonsa kamar taga wani mugun abu, Ganin xai kalli direction din da take ta dauke kanta da sauri gabanta na faduwa, Yace “Mama bakuwa ku ka yi?” Hajiya Rukayya tace “Ehh, ga breakfast dinka can a dining” Yace “Ohk” sannan ya mike ya tafi dining din, Mikewa Amina tayi ta tafi dauko ma ita da Jiddah breakfast don taga alamar yayyinta duk sun yi, kuma da ba don Jiddar ba tare xata je ta xauna su yi breakfast din da yayanta, gaba daya Jiddah ta kasa sakin jiki a parlon, lkci lkci take satan kallon hanyar dinning din, daga karshe dai ta mike xata wuce daki, Hajiya Rukayya tace “A daki xaki yi kumallon?” Ta d’an yi murmushi ta gyada kai ta wuce daki da sauri, dole dakin Amina ta kai masu Breakfast din. A ranan bayan an sauko juma’ah aka daura auren Ramlah da Ahmad… Abuturrab na tsaye daga bakin kofa a bedroom din Umma bayan sun gaisa yace “Tana gidan nan ne Umma?” Umma ta kallesa tace “Wa?” Jin bai ce komai ba tace “Wai Jiddah?” Yace “Eh” Tace “Ba a jima ba suka tafi can gidanku da Maman Abdallah” Bai kuma cewa komai ba, tace “Hajja kuka tace tun da ta xo baka je ka gaisheta ba” Yace “Ai ban je can gidan ba Umma, anjima da daddare xan shiga in gaisheta” Tace “Yauwa gwara kaje din da daddare dama ya fi, an kai maku abincin kuwa?” Yace “Ehh an kai” daga haka ya juya ya fita. Da yamma su Amina duk suka tafi gidan yinin Biki, Hajiya Rukayya kuma tun karfe goma dama ta bar gidan, gidan ya rage daga Jiddah sai Badiya, tana kitchen tare da Badiya tana tayata girkin dinner, wayar Badiya dake parlor ya fara ring, Badiya tace “Dauko min wayar Jiddah…” juyawa tayi ta fita xuwa parlor, dai dai nan kuma aka bude kofar parlon suka hada ido, sanye yake da farar shadda idonsa sanye da glasses, sosai gabanta ya fadi, ta sunkuyar da kanta tana kalle kallen inda xata ga wayar Badiya, kasa karasowa cikin parlon yyi, sbda rudewa ta ma rasa inda wayar yake ta juya xata koma kitchen din taji yace “Jiddah” juyowa tayi suka sake hada ido, tayi murmushin karfin hali tace “Ina yini?” Ya karaso cikin parlon yana ci gaba da kallonta da mamaki, bata jira me xai ce ba ta juya da sauri ta koma kitchen din. Har Hajiya Rukayya ta dawo wajajen magrib Jiddah bata sake yarda sun hadu da Yousuf ba, can daki ta shige taki fitowa through out, Hajiya Rukayya na shigowa gidan ta kira Yousuf a waya don baya nan, yana shigowa tace “Don Allah bakuwar nan xaka ajiye min gidansu Ahmad yanxu, Hajiya Ramlah tace ka kaita” Yousuf yace “Ohkk” Har mota su Amina suka raka Jiddah, shi da Yousuf na xaune cikin motar tasa, Jikin Jiddah yyi sanyi ganin shi xai maidata, hannu kawai ta daga ma kanninsa har suka fita compound, sai da suka d’an yi nisa taji yace “Dama ke yar uwar Ahmad ce?” Kai ta gyada masa kawai, ya d’an kalleta yyi murmushi yace “Har yanxu sai kice min baki da waya ko?” Ta gyada masa kai, yace “What if na baki tawa wayar?” Ta xaro ido tace “Sai in ce wa ya bani?” Yace “Ni” ta girgixa kai tace “Aa bana so” yace “Jiddahh” ta d’an kallesa suka hada ido, yace “Kin san wani abu?” Ta girgixa masa kai, yace “Tun da muka hadu dake a jirgi kullum nake addu’an Allah ya sa in sake arba da ke, sae gashi kin xo har cikin gidanmu, kinsan me yasa hakan ya faru?” Nan ma ta girgixa masa kai, yace “It is because i have good intention toward u…” Jiddah dai tayi shiru kamar ta gane me yace. And the rest of the ride was silent, yayi parking dai dai kofar gidansu Ahmad ya juya yana kallonta, yace “Tunda baxa ki amshi wayata ba, xan kiraki ta wayar Maimoon” Ita dai bata ce komai ba, ta bude motar ta sauka, ta bude baya ta dau jakan kayanta, Yousuf na kallonta yace “Sai na kira” Tace “Toh” sannan ta nufi gate, shi kuma yayi reverse…. Dama Umma Jiddah kawai take jira don har ta saka Hijab dinta tana parlor a xaune, Jiddah na shigowa kuwa ta saka driver ya kai su can gidansu Abuturrab, har sannan da akwai sauran yan biki a gidan duk da tun wajen shidda saura aka kai amarya, direct parlon Abban Abuturrab Umma ta nufa tare da Jiddah suka shiga da sallama, Abban Abuturrab da brothers dinsa ne a parlon sai Hajja dake xaune kan carpet, bayan ta xauna suka gaggaisa, ta gaida Hajja ma, Hajja tace “Ni dai tun jiya nake ta kallon ki Ramlah, ya aka yi kika amince kika narka uban kiba haka, to ai ba kyau, mu a masar da tuni an kai ki asibiti duk hankali a tashe, mu ba ma haka a can” Umma dai bata ce mata komai ba, Can ta kalli Jiddah da ta sunkuyar da kanta tun bayan gaida su Abba tace “Ita kuma wannan sadaka yallar fa?” Nan ma babu wanda ya ce mata komai, Abba ya dau waya ya kira Ummi ya sanar mata Umma ta iso, su xo tare da Aunty, Hajja tace “Ai masar tayi wallahi, ba ruwanmu da abinda bai shafemu ba, kowa ta kansa yake, shi yasa xuwa jibi nake son idan Allah ya kai mu in koma, nafi wayo a can…” Ummi ce ta shigo parlon tare da Aunty, tunda Jiddah taga Aunty gabanta ke faduwa, Brother din Abba dake gefensa yace “Ka kira Aliyun ne?” Abba yace “Ehh na kirasa” Abba bai rufe baki ba Abuturrab ya shigo parlon da sallama, sosai gabansa ya fadi ganin Jiddah da Umma a parlon, ya dai dake ya xauna, sannan ya gaida kowa na parlon…. Brothers din Abbansa ne kadai suka amsa gaisuwarsa, Abba na kallonsa a takaice yace “Ina takardan da ka rubuta ma yarinyar nan?” Abuturrab ya buda ido sosai ya kalli Jiddah, da farko kasa cewa komai yayi, can kuma yace “Takarda kuma Abba?” Lkci daya hawaye ya kawo idon Jiddah ta kalli Umma da ta hade rai, Abba yace “Ina tambayarka kana tambayata? Are u stupid?” Yyi kasa da murya kamar wani mara lfya yace “Abba ai ban san wani takarda ba” Umma ta kalli Jiddah tace “Ya rubuta takarda ya baki ko bai rubuta ba?” Hawayen idonta na xuba ta kalli Umma ganin yanda ta daure fuska cikin rawan murya tace “Ya rubuta” Kallonta kawai Abuturrab yake ko kiftawa babu, Umma tace “Yace maki me a jikin takardan?” Da kyar tace “Wai ba aure a tsakanin mu, shi ba mijina bane” Aunty dake ta gyara xama taji kamar ta saki shewa a parlon murmushinta ya kasa boyuwa, on a serious note Abba na kallon Abuturrab yace “Mu ka mayar kananun mutane Aliyu? Ashe baka dau addininka bakin komai ba bamu sani ba, for all this while kana xaune da yarinya babu aure Aliyu??” Da kyar Abuturrab yace “Abba wllh wllh ba saki na rubuta a takardan ba…” Hajja dai ta hangame baki tana bin kowa da kallo a parlon, Caraf Aunty ta amshe tace “Toh ai aikin banxa kenan, tunda duk ka bi ka sanar ka saketa aure kuma ai ya lalace, ko ka mance addininka ne? Ni kaina kace min ka saketa ya fi sau talatin, ga Aneesah ga Ahmad da abokanka, ka ga kuwa ta saku” Abuturrab ya kalleta xuciyarsa na tafarfasa yace “Toh ai ita bance mata na saketa ba, na dai ce mata ni ba mijinta bane, ban ta6a bude baki nace mata na saketa ba….” Mikewa Abba yayi ya tafi daki sai gashi ya fito…. Abuturrab ya dinga kallonsa xuciyarsa na bugawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *