Karshe dai aka tantance Malaika ce ta hada rigima, amma dan a zauna lafiya aka karbi katinta tare da na sauran amma da sharadin ba za’a gansu ba sai bayan azahar. Su ka yi amanna suka koma gefe suka zauna, har yanzu bakin Malaika ya ki mutuwa.
Fadi take ita ba talaka ba ce, wata talaka bata isa ta taka ta, ta kyale ta ba. Mamaki ya kama jama’a suna ta kallon kodaddiyar atamfar da ke jikinta amma tana fadin ba su san ko ita wacece ba, ita da manyan likitoci ta ke kawance ba da Nurses ba.
Ma’aikaciyar jinya Nurse dai ta
fahimci Malaika ba sa’ar yinta bace, taga alama ta dame ta, ta shanye ta a fagen tsima da zakin murya, da alama ‘yar ta kife ce. Ta fara zargin ko tana shan benelyn don yanzu an ce har da matan aure ma sha suke, dan haka duk wanda ya kula ta ma zai zama mahaukaci. Ta kyale ta, tama daina kallon inda take, dan har yanzu Malaika harararta take tana nuna ta da hannu tana murguda baki.
Nasrin, masu kyamararta, Dr.Gumel da
Dr. Hala ne suka biyo kan barandar da su
Malaika ke zaune zasu wuce da alama dakin kwanciyar mararsa lafiya suka nufa. Da suka hango Malaika ta tunkaro su cike da fara’a, gaba dayansu babu wanda gabansa bai fadi ba, suka yi turus. Musamman Dr.Gumel yana tsoron kada ta tara masa jama’a.Lah kawata
Nastin Abdul Nasir.”
Malaika ta fada gami da rungume Nasrin.
Nasrin tayi murmushin karfin hali ta ce,
“sannunki. Kin sami ganin likita?”
Malaika ta ce, “Eh an shiga da katinmu, dan da har waccan ‘yar bakin cikin zata hana mu ganin likita wai mun makara.Ta nuna Ma’aikaciyar lafiya
Nurse yayin da Nasrin da Nurse suka hada ido, sai kunya ta sa Nasrin ta sunkuyar da kai kasa,kuma ta gaggauta barin wajen kamar yadda Dr. Gumel ya yi gaba da sauri bai tsaya ba.
Nasrin tana tafe tana magana ta ce, “zan dawo wajenki anjima”
Dadi ya kama Malaika ta koma wajen zamanta ta zauna tana mura tana korawa jama’ar wajen bayani, tana mai gabatar musu da su Nasrin har da
Karin karya wajen gabatarwar. Ta tabbatar musu da su kunna labaran tara yau zasu ga hirarta a talabijin din NTA.
Ma’aikaciyar jinya ‘Nurse’ ta juyo da sauri tana kallon Malaika kan ta ya daure.
Malaika aka harare ta,tamurguda baki ta ce “kalle ni da kyau ni ba karamar mace bace, kin dai gani da idanuwanki ko ni wacece.
Kuma idan karya nake ki kunna talabijin yau ko gobe idan baki gan ni a labarai ba ki kira ni makaryaciya. Ni talaka baya yi min raini, dan shi ba koman-komai ba ne.”Malaika dai bata Kara gamin Nasrin ba,sai bayan la’asar sannan likita ya ganta. Ta je har ofishin bata gansu ba, ofishin ma a datse.
Ta karade asibitin nan kakaf tana nemansu bata gansu ba. Ta je wajen da Dr.Hala ta ajiye motarta ta ga wayam babu mota, sannan ta tabbatar sun shanmace ta sun arce.
Shamaki ya kira wayarta fiye da sau ashirin bata dauka ba, ta ga kiran ta ki dauka dan bata san me zata ce masaba. Ta tari a-dai-dai-ta-sahu (Napep) ta tafi cikin fushi dan ba ta ji dadin rashin yin sallama da su Nasrin bad an tana saka ran samun kudi a wajensu. Unguwar Dorayi ta nufa anan take da zama, sai da suka yi fada da mai adaidaita sahun a hanya dan. yace ta koma tsakiya tayar gefe daya bata da iska. Ta fara fada wai ita bata son harkar talauci yana neman kudi amma ya kasa canja taya.
Mai a-dai-dai-ta-sahu (Napep) ya ji
lafazan Malaika suna yi masa shawagi a kwanya, sai ya saita mudubi ya Kara kallonta dan ya tantance mai kudi ya dauko wacce motarta ta sami matsala a hanya ta rufe ta hau babur dinsa, ko kuwa talaka ‘yar uwa ce take kasassabar magana?Ai kuwa daga dukkan alamu ‘yar uwa talaka ya hanga, kososuwa irinsa. Bai san amsar da zai bata ba, suka ci gaba da tafiya yana jira ya ga ta nuna katon get, sai gashi ta ce ya ajiye ta a kusa da bola, ya kaita har kofar gidanta ta shiga, nan ma ya sake gasgatawa ‘yar gidan malam shehu ce dai.
Ko ba komai ta barshi da zulumi da sunbatu.
Yana ta ambaton “Allah mai halitta!” Ta na isakofar gida tun daga kofar gida ta. fara jiyo ihun Karamin danta yayayyen
“Kasim’ ta shiga da sauri ta iske shi a zaure a zaune akan foh, yayin da babban danta’ Aliyu’ dan shekaru biyar yana dakan yaji a turmi a tsakar gida.Shamaki ya yi dagaje-dagaje da bakin gawayi yana dafa wake da shinkafa.
Malaika ta dora hannu aka tana shirin kur’ ma ihu, ta daure dai ta fasa, ta sauke hannun.Ta fada a bayyane “wallahi talauci bai yi ba.”
Shamaki ya fito daga kicin a sukwane yana nuna ta da hannu,ina kika tsaya kika qi dawowa gida?
Dan na san ba ganin likita ba ne ya tsayar da ke ba. Na kira wayarki kin ki ki dauka.
Malaika ta harare shi ta yi tsaki ta ci gaba da kutsawa cikin gida, yayin da take kokarin kwance goyo shima na goyen Ahmad kukan yake yi, ga gajiya ga ciwo.
Shamaki ya ci gaba da binta a baya yana balbalin fada, “kin bar yara a makwabta ba wanka, babu abinci, na zaci zaki riga ni dawowa har na yi lacca biyu na dawo ba ki
Hmmm