gabansa kawai aikin da yake gabansa ya fi komai muhimmarci a tare da ita.
Zai gwada ya gani ko zai iya danne son da yake mata wanda a duk lokaci da suka hadu sai ya ji shi cikin wani irin mayen so da kaunarta tabbas
Bahijja ba irin macen da za’ a iya kalla a hakura da itaba ce tana da wani irin karisma da wani irin charming da ba lallai ka yi mata kallon haka kawai ba da wanna tunanin ya juya ya koma sama zuciyarsa na masa zafin ganin hawayen da ya zuba a tare da ita haka ya dinga jin kamar ya je ya hada ta da jikinsa ya rarrashe ta sai dai kash bashi da wannan damar dole ya hakura ya koma dakinsa don samun saukin zuciyarsa.
Ta saman dakinsa ya hange ta zata tafi har yanzu cikin yanayin fuskarta akwai damuwa haka ya dinga ji a ransa kamar Hajiya bata kyauta mata ba ganin damuwa a fuskarta ya nemi farin cikinsa ya rasa. bata jima da fitaba shima ya dauki
• Muhammad suka fice yawo don ya samu abinda zai dawo masa da farin cikinsa.
Washe gari Hajiya ta sha mamakin ganin yadda
Bahija ta sake da ita kamar wace babu wata magana ta taba mata rai kamar basu yi komai ba wanda da ita a tunaninta ko ta zo zata ga sauyi amma sai ta ga akasin hakan wannan yasa ta kara jin kaunar Bahijjan cikin ranta.Kamar yadda ta saba haka ta cigaba da gudanar da aikinta duk abida take nata burge Hajiya yake nan taji kaunar ta na kara karuwa a ranta. haka shi kuma Farouk kullum addu’arsa Allah ya kawo masa hanyar da zai samu abinda da zai haska masa wani abu akan rayuwar Bahijja kullum sai yayi wannan addu’ar a dukka sallolin da zai yi.
A hankali cikin Bahijja ya shiga watan haihuwarta tayi nauyi sosai haihuwa yau ko gobe. cikin shirinta tsaf ta gama ta dauki Jakarta tace
“Baba Audi ni na gama zan wuce sai na dawo.”
Baba Audi ta kalli Bahijja tace “Bahijja wai ni wannan aikin naki ba a samun hutu ne kullum kina kan hanya ya kamata dai kidan samu hutu duba da nauyin da kika yi ko so kike ki haihu a hanya ne.”
Murmushi tayi tace “Baba Audi kar ki damu wannan fitar da nake yi tana saka ni samun garfin jiki na motsa jikin da nake da tattakin da nake yi duk kara samun lafiyata ne da abinda ke ciki na, kuma karki manta alkawari muka yina zan ke zuwa duba yaron nan kullum, ina son naga dukkan alkawarin dana dauka na cika, wannan dalili yasa bazan nemi hutu ba saboda da wanda muka yi alkawarin akansa shima yana bin dukkan alkawarin da muka yi dashi don haka nima zan cigaba da cika nawa alkawarin da na dauka.”
“To babu komai Allah ya taimaka sai kin dawo a kai da min da mara lafiyar idan kin je.”
Cikin jin dadi tace “To Baba Audi zai ji”nan ta fice murmushi dauke a fuskarta. ta samu driver din suka ja suka tafi.
Zaune suke a falon duk su ukun kasancewar yau
Farouk bai je aiki ba haka ya ji yau sam baya son fita ko ina. Muhammad ne ya shigo falon ya ringa jan hannun Bahija a kan lallai sai ta taso sun yi wasan guje guje a falo kamar yadda suka saba, nan kuma ta mike ya fara gudu daga nan bayan kujera zuwa waccan haka ita dinga biye masa.
Hajiya ce ta dakatar da Bahijia akan tana bari tana hutawa duba da yanayin jikinta. nan ta ce
“Hajiya ina jin dadin hakan da muke yi ni da shi nima excersice nake yi.”
Farouk yace “Docter yana da kyau fa kina hutawa ki duba fa yadda kika ke ina ganin ki dauki hutu ki je gida ki huta nake kawo Muhammad can inda kike kina duba shi.”
Nan take Hajiya tace “A’ah ba haka za’a yi ba ina ganin gwara kawai ta dawo nan har zuwa lokacin da Allah zai sauketa lafiya idan yaso sai ta koma.”
Murmushi tayi tace “Nagode sosai da kulawar ku gare ni amma maganar daukar hutu ko dawo nan duk babu mai yuwa cikinsa zan iya komai, duk gajiyar da nake yi a nan idan na koma gida ina samun kulawa sosai a gurin mahaifiyata tare nake da ita take min komai tana bani kulawar da nake bukata Hajiya ba raina abin da kika ce min nayi ba nayi ina ganin tunda ina iya yin abinda zan yi ku barni kawai.
Ko a yau na samu na haihu babu abinda zai hanani zuwa na duba Muhammad mutukar ina da lafiya a tare da ni.” “Babu laifi Allah ya budi ido lafiya ya kuma nuna mana lokacin lafiya.” Hajiya ta fada.
Cikin sauri Farouk yace “Ameen Hajiya.” nan
Bahijja ta cira kai suka kalli juna murmushi yayi mata ita kuma tayi saurin kawar da kanta kamar bata ji mai ya fada ba.
Nan ya mike ya bar falon zuciyarsa cike da farin cikin wani haske da ya samu cikin furucinta na hirar da suka yi ya gode Allah da yau bai fita ba gashi ya samu abinda ya kenema ashe Bahijja tare take da mahaifiayar ta bai taba sani ba tabbas yau
Allah ya amsa masa addu’arsa ya samu hanyar da zaibi уа samu labarin
Bahijja meye rayuwata?meye dangatakar da
wannan kauyen?daga ina suka zo tana da aure ko bata da shi duk yana son amso shin wadannan tambayo yin babu kuma wanda zai bashi wadannan amsar sai mahaifiyarta na tabbata ita zata fada min komai cikin yardar Allah.
Nan ya shiga nishadi cikin ransa Allah Allah yake gobe tayi ya je kauyen ya nemi mahaifiyarta cikin sirri suyi Magana da ita domin ya samu nutsuwa a ransa domin idan yaje yanzu tana daf da tafiya gida idan ta zo ta same shi da mahaifiyarta komai na iya faruwa don haka ya bar komai cikin ransa ya bari sai gobe idan ta zo sai ya saci jiki ya je su had da wannan tunanin ya wanzu cikin farin ciki.
Washe gari hakan a kayi kuwa sai da ya tabbatar driver din da ya tura a dakko ta ya zo sannan ya dauki motar ya nufi kauyen don zuwa ya binciko labarinta. har ya isa kauyen ya rasa wacce hanya zai bi nan take wata dabara ta fado masa bayan ya shigo cikin kauyen ya zo kafar gidan mai gari yace don Allah yana son gain Mahaifiyar Dr. Bahija ta aiko shi ya karbi sako a gurinta.
A rude Baba Audi ta fito cikin tashin hankali ta zo ta samu Farouk tsaye jikin motarsa tana ganinshi tace Dana lafiya dai ince ko dai wani abu ya faru da Bahijja ne.” Cikin ladabi ya dubeta yace “Baba kada ki daga hankalinki babu abinda ya faru da ita, dama gurinki na zo ina son ganinki zamu yi Magana da ke nine Alh. Umar wanda take zuwa duba yaron na kan lalurarsa.”
Sai yanzu ta samu nutsuwa ta tattara hankalinta tana saurarensa tace “To dana wacce Magana zamu yi da kai ne dana.”
Nan ya rusuna yace “Baba ina son zuwa na nan ya zama sirri wanda nasan idan Bahijja taji zata iya nuna rashin jin dadi, ina son sanin Bahijja matar aure ne ko bazawara domin ina son na aureta ne ina kuma son jin meye ke damunta a takaice dai ina son jin labarinku daga ina kuka zo domin ta fada min cewa ke mahaifiyarta ce shine na janyo jiki na zo cikin sirri.”
Abu daya zuwa biyu zan iya fada maka game da
Bahijja bayan haka kuwa babu wani abu da zan fada maka domin Bahijia mai sirri ce tana son sirri tsakanina da ita akwai amana da yana da kyau kayi
Hmmm