Nan gefan abdallah ya kwanta yana ci gaba da kuka tamkar wani qaramin yaro,jin zuciyarsa yake kamar zata fashe,janyo abdallah yayi cikin jikinsa yana magana qasa qasa mai cike da kalmomin nadama yana ci gaba da kuka.
Sai da rana ta soma bugun naman jikinta sannan ta iya miqewa a daddafe ta yafa mayafinta,takalmi kuwa basu sakuwa a hannu ta riqesu hadi da jakarta,da qyar da jan qafa ta kai kanta titi ta tari adaidata sahu ta hau duk da cewa bata da qwadalar da zata bashi,qofar gidansu ya sauketa tace ya jira ta miqo masa kudin,tana sallama ta zube a tsakar gidansu tana maida numfashi,mamarta dake wanki bakin fanfo ta dago tana dubanta,mamaki ya cikata saidai bata da ikon tambayar ta abinda ya sameta,murya can qasa da qyar ta qwalawa qanwarta kira
“Idan akwai naira dari jakarki fita waje ki bawa mai adaidaita sahu,mama dora min ruwan zafi” kowannansu da to ya amsa mata,maman ta saki wankin ta shiga kitchen.
Gashi tayiwa kanta sosai tamkar kai jego,tanayi tana runtse ido zuciyarta na zafi da quna,tana tuna yadda mukhtar ya dinga jibgarta kamar wanda ya sayi jaki mai taurin kai,dakinta ta koma ta shafe jikinta da man zafi ta samu ta kwanta sannan ta janyo wayarta tayi kiran abokiyar shawara da shaidancinta zinatu,tana dagawa ta buqaci ganinta,cikin sa’a kuwa tana kusa.
Cikin mintuna qalilan zinatun ta iso,suka gaisa da maman wanda ke zaune tsajar gida tana shirin dora abincin rana,da kallo tabi zinatun har ta shige dakin,
“Lafiya?,na zaci zaki cemin gaki gidan mukhtar anyi kome sai nazo na sameki kina tashi da qyar haka?”baqinciki ya sake tokare zainab,cikin bacin rai ta soma fadin
” ni malam zai ciwa kudi zinatu,ni zai ha’inta?,kalli jikina ki ga abinda mukhtar ya yimin duba zinatu”
“La la lal” shine kawai abinda zinatu ke fada tana gyada kai
“Garin yaya haka zainab” tas ta kwashe yadda komai ya faru ranta na quna ta qunduma ashar sannan ta dora
“Ba sai na warke ba gobe gobe zamu koma wajen malam,wallahi sai na nuna masa ni ‘yar tasha ce,duk abinda ya buqata nayi masa,kwana nayi yana sasukata duk warin dake tashi a jikinsa amma ban damu,shine ni kuma zai rainamin wayo an gaya masa ni gara ce,to wallahi Allah ya nuna mana gobe shege ka fasa” haka ta dinga bambami zinatu na tausarta da haka sukayi sallama da niyyar gobe da sassafe zasu dirarwa malam
Tana zaune bakin gadonta tana ninke kayan sawarta a hanakali,tunanin abdallah na kai komo cikin ranta tun safe,tunda ta haifeashi basu taba rabuwa daidai da kwana guda ba banda sanda ta yayeshi sai wannan lokacin,yanzu haka watanni kusan shida kenan bata sanyashi a idanunta ba,gidan nasu yau shiru yake tun safe har yammaci,hajiya na bangarenta yau bata jin dadi,tunda ta kammala mata girki sai ta barta ta dan kwanta ta huta,karima ta hada kan yaran sun tafi sunan qanwarta data haihu,bata kuma bar nuwaira ba haka ta kada ta suka tafi tare,yaran baki daya sunci ado banda ita,a haka da sauqi tunda sumayya ta tattara dukkan yagaggun kayanta ta boye ta hanata sakasu tafiddo mata da wasu,haka karima ta haqura bayan sa’insar da suka sha da sumayyan,a yanzu bata da goyon bayan hajiya lukman kuma bai gari yayi tafiya bare ta hadata da shi.
Hudu da rabi na yammacin taji sallamarsa bakin qofar dakinta,a hankali ta daga kanta tana dubansa,ta mance yaushe rabon data sanyashi a idanuwanta tun kafin yayi tafiyar nan wadda ita kanta satinsa biyu kenan baya nan,sanye yake da shadda dinkin tazarce da hula saman kansa sai takalmi sau ciki,kafadarsa rataye da jaka ta matafiya,kallonta yake yana mata murmushi
“Sannu da zuwa” ta fada tana gyara daurin dan kwalinta
“Yauwa sumayya,ya gidan?” Ya fada yana zama gefanta yana mai ci gaba da kallonta
“Lafiya qalau” ta fada tana hada kayanta waje guda tare da miqewa ta zura hijabinta tana shirin ficewa
“A’ah,ya haka kuma,ya zaki fita ki barni”
“Au da dawa nake barinka” ta fada tana gyara zaman hijabinta gami da kallonsa
“Amma dai ai yau gidan babu kowa ko?,wa zai kula da ni?”
Qugu ta riqe tana duban idanuwansa
“Sai babu kowa cikin gidan sannan nake da amfani a gunka?,to gun hajiya zani na dubata na barota bata jin dadin”damuwa qarara ta gani ta bayyana kan fuskarsa karo na farko kan maganar da ta shafi mahaifiyarsa
” subhaballahi tun yaushe?,muje na ganta”ya ajjiye jakarsa ya miqe yabi bayanta.
Ganin yadda ya damu qwarai ya sanyata cewa
“Ba wani ciwo me mai zafi ba,qafarta ce kawai ta motsa”tayi furucin tana kallon gabanta,ajiyar zuciya yayi bai sake cewa komai ba har suka qarasa dakin hajiyar.
Tana kwance a falo da alama sallah ta idar,sosai tayi mamakin ganin lukman din wai tazo dubata,saidai bata nuna masa ba,suka gaisa fuskarta a sake,shi da itan duka wani dadi suke ji,sai gashi suna hira kadan kadan,hatta da sumayya sai data dinga jin dadi,ta dade da sanin dadin da iyaye ke da shi a gun d’a,hakanan zuwa yanzu tasan yadda uwa ke jin dadi a duk sanda ta daga ido ta kalli danta ko diyarta cikin kyakkyawan yanayi.
” kaje ka huta lukman ka dawo daga baya idan hirarce”hajiyan ta fada qasan zuciyarta a karye,don tasan ita kanta fada kawai tayi,saboda babu lallai ya sake zama da ita irin haka matuqar karima baqar daga ta dawi cikin gidan,ta fada ne don kawai kada ta shiga haqqinsa shi da iyalinsa,saboda zuwa yanzu ta yarda kura kuran da ta tafka a baya zunubinsu ke bibiyarta,amsawa yayi da to don shi kansa yanason kasancewa da matarsa,miqewa yayi yayi gaba wanda tilas sumayyan tabi bayansa don tana kunyar hajiya da ganin girmanta,bata son ta fuskanci komai daga gareta.
Gaba ya sanyata har zuwa dakinsa,karo na farko data fara taka dakin tun zuwanta gidan,kan gado ya zube yana dubanta
“Hadamin ruwan wanka na gaji sumayya,sai ki yo alwala idan na fito zamuyi sallah”
“To” kawai tace masa tana tunanin lokacin sallar magaribar ai baiyi ba aqalla akwai kusan awa guda nan gaba,sai daya shiga wankan sannan tayi alwalar kamar yadda ya buqaceta,a nan gabanta ya shirya duk da dauke kai da tayi sannan ya umarceta da tatashi suyi sallah,bata fuskanci abinda yake nufi ba sai suka idar da sallar taji yafara addu’a,take jikinta yayi sanyi,tsoro kuma ya cikata,tana jin ta yaya zata sake wata sabuwar rayuwar da wani sabon mutumin na daban ba wanda ta saba da shi ba?,saidai babu yadda ta iya din saboda tana da cikakkiyar masaniyar cewa da mijinta take tare wanda ya biya sadakinta shaidu kuma suka shaida,to shi kansa kamar baqo haka ya bijiro mata,sai daga bisani ya fara warewa a hankali,hawaye ne suka dinga gangaro mata,ambaton Allah ta dinga yi cikin zuciyarta.
Tana gaban madubi tana gyara gashin kanta bayan ta gogeshi tare da maida masa ribbom dinsa,shi kuma na zaune bakin gado yana kallonta,tabbas babu shakka kyauta Allah ya masa,a cikin mata hudu da ya aura har da karima cikon ta biyar din bai taba cin karo da mace kwatankwacin sumayya ba cikin duniyar ma’aurata,babu abinda ke kai kawo cikin qwaqwalwarsa sai yadda ya samu sumayyan cikin sahun mata na musamman wadanda suke ‘yan kadan ne cikin daruruwan mata,amma sai ya fuskanci babu wata fara’a ko walwala sam a fuskarta,wanda hakan sai yaji sam bai masa dadi ba,a hankali ya kira sunanta ta amsa gami da waiwayowa tana daura dankwalinta ba tare da ta dubi qwayar idonsa ba
“Sumayya,naga kamar bakya farinciki da ni ko?,nasan fushi kike da ni haushina kike ji,nasan dole kiji haushi bake bama koma wacece,don Allah don annabi kiyi haquri sumayya,wallahi ba laifina bane,bansan dalilin da ya sanya idan karima ta bani umarni ba nake kasa bijire mata,bansan me ya sanya ba nake tsananin tsoronta,duk da cewa a yanzu cikin kashi dari inajin babu kashi hamsin yana raguwa sosai,kiyimin haquri sumayya ina saka ran in sha Allahu komai ya kusa dai daita,ina miki godiya kan namijin qoqarin da kike kan gyaruwar gida na,ina sane kuma ina lura da komai,wasu kuma karima ta sanarmin sa niyyar na na taka miki birki,wallahi sumayya ban taba ganin mutumin dake taka karima itama kuma take shakka shakkarsa ba saike,kiyi haquri kici gaba da yin haquei komai mai wucewa ne in sha Allah” yanayin yadda yake maganar kawai ya isa ya sanar mata bilhaqqi da gaske yake,sai taji tausayinsa ya kamata,mutum cikakke kamar lukman amma sharrin mace ya maidashi wani iri
“Babu komai,kowanne bawa da irin tasa QADDARAR a rayuwa,Allah ya mana magani ya shige mana gaba,ka riqe addu’a kaima insha Allahu HASKE na nan zuwa….”.
Bai kai ga bata amsa ba suka soma jin bugun qofa mai tsananin qarfi
“ka bude lukman bude,ina fatan ba abinda nake zargi bane,wallahi idan har shine ka kuka da kanka”idanuwansa ya runtse gabansa na faduwa,sumayya dake zaune a nutse abinta ta soma nazartarsa da nazartar yadda ya tsorace,babu laifi da sauqi,tunda idan da dane da tuni ya arta da gudu yaje ya bude din
” ka ambaci Allah cikin ranka hakan shi zai cire maka tsoron dake cikin ranka”
“Allahumkhfinihim bima shi’ita”ya fara ambata daya daga cikin addu’ar da yaji hajiyansa na ambata tun bayan zuwan sumayya gidan aduk lokacin da taga karima.
Sumayya ce ta tashi ta isa bakin qofar dakin ta murza key din ta bude,karima ce tsaye bakin qofar rataye da jaka,shigowarta gidan kenan ta hangi motar lukman fake,ta tambayi mai gadi ya sanar mata kusan awanshi biyu da kenan da dawowa,dama tun tana gidan sunan taji hankalinta yayi gida,abun mamakin shine dukka yaranta na tsaye bayanta harta da qaramarsu,abinda ya sake daurewa sumayya kai kenan,nufinta a gabansu zata tijara babansu?,da yanayin da tazo mata taso itama ta tarbeta,amma ganin yaran ya sanya sumayyan murmushi
“A’ah,maman nuratu,kece kuma da yaran baki daya haka?”harara ta balla mata sannan tace
” munafukar Allah bake nake nema ba,babban magulmacin nake nema,matsamana mu shige”murmushi ta kuma yi tana gyada kai
“Mai zai hana na barki ki shiga,ke da dakin mijinki,amma bai kamata ku dunguma baki daya ba,saboda bakisan a yanayin da zaku ruskeshi ba” ta fadi maganar tata ta qarshe qasa qasa yadda kariman ce kawai zata iya ji
“Bismillah” sumayyan tace sa ita bayan ta janye mata jiki,sai data ja tsaki sannan ta wuce kamar zata bangajeta,yaran suka yunquro zasu shiga ta sha gabansu,ta dubi nuwaira wadda ta tabbatar itace mai hankalin cikinsu
“Nuwaira,maza ku tafi dakinku ku sauya kaya,mamanku na fitowa,kama hannun basma ku wuce ko?”
“To anty” ta fada tana kama amma da nuratu sukayi gaba,tsare sauran tayi da idanuwa tilas duk rashin kunyarsu suka bi bayan nuwaira daidai sanda maganganun karima cikin ihu suka soma tashi
“Na shiga uku na lalace,yanzu lukman sai da ka kwanta da matarnan,lallau namiji d’an kunama ne,wayyo Allah yau naga ta kaina” ta fada tana dora hannu a ka tare da qarewa gadon nasa kallo,tsaye sumayya tayi harde da hannayenta tana kallonta,wato badon ta kora yaran ba nufinta gabansu zatayi wannan tambelan?,gaskiya ne dole wasu matan su janyo a dinga kiran mata masu naqasun hankali,takawa tayi ta dafa kafadarta wanda ya sanya karima waiwayowa tana dubanta
“Meye na tashi hankali haka?,tun ranar farko kenan?,bakisan somin tabi bane yanzu aka soma?,ki godewa Allah ma da bakizo kin samu ana third round ba” ta fada tana kewayeta tare da komawa bangaran gadon ta soma gyara bedsheet din tana murmushi.
Ashar ta lailayo ta danqarawa sumayyan irin wadda bata taba jin irinta ba
“Wallahi kinyi qarya kin kwana da yunwa duk malantar ubanki baki isa ba,duk wanda yaci tuwo da ni miya ya sha,wallahi sai kin gane kurenki,saikin gane shayi ba komai bane face ruwa,sai na cusa miki baqinciki fiye da wanda kika cusa min” sai ta waiwaya inda lukman ke zaune,tayi tsammanin ganin tashin hankalinsa qarara yadda aka saba sai ta ganshi zaune ko gezau
“Kai kuma tashi mu wuce dakina” ta fada a tsawace
“Ba inda zanje” ya fada yana jin shakka shakka na tasowa can qasan ransa yana qoqarin danneta,idanuwa ta zaro,jikinta ya soma bari,ba shakka alqadarinta gab yake da karyewa,kasa magana ma tayi sai kallonsa da takeyi
“A’ah,ki wuce mana kije tunda dai shi din yace bashi zuwa” a fusace ta waiwayo ta tunkuda sumayyan wadda bata zata ba,hakan yayi sanadin da tayi taga taga zata fadi lukman din ya tareta,sai ta miqe daga jikinsa tana murmushi kamar ba ita aka yiwa ba
“Babu komai,duk cikin haushi ne” qwallar baqinciki ce ta fara qoqarin zubo mata,da hanzari ta juya ta fice a dakim saboda batason sumayya ta gani har ta gane ta soma samun rauni,qofar sumayyan tabi ta kulle sannan ta dawi ga lukman wanda ta lura hankalinsa ya soma tashi,sosai ta zauna gabansa tana karanta masa abubuwan da suka dace har ya soma daidaita,sannan suka tashi suka sake komawa duba jikin hajiya wadda mamaki ya sake kamata ganin sun sake dawowar duk da taji shigowar karima gidan.
Qarfe goma da rabi suna dawowa daga wajen hajiya suka ratso ta falon,islam suka gani na matse hawaye ta tari gaban uban tana cewa
“Abba kaga kasa mamanmu ta hada kayanta ko ta tafi,kuma tace ba zata dawo ba” wani matsanancin faduwar gaba ya ziyarce ya zaro ido yana dubanta
“Tun yaushe?”
“Dazu,naje dakinka baka nan” duk sai sumayya taji babu dadi,kada dai abinda ya faru dazun ya sata bar musu gidan,sai ya kama hannun yarinyar yana fadin
“Ya isa,kada ki damu mamanku gobe zata dawo kinji,sumayya jeki da su suna dakinsu ina zato” amsa masa tayi,saidai qememe yarinyar taqi yarda ta kama hannuwanta haka suka tafi,koda ta shiga dakin suna zaune baki dayansu tsuru tsuru,duk sai taji tausayinsu ta dinga jin babu dadi,da fari duka qin sakin jikinsu sukayi da ita sai nuwaira kawai,amma ganin nuwairan ta saki jiki sai basma qaramar cikinsu itama ta ware,daga baya nuratu ta sake itama,sai islam kawai da tayi kicin kicin taqi shiga sabgarsu,ba ita ta barsu ba sai da taga sunyi bacci sannan ta musu addu’a ta bar dakin.
Sumayya na wucewa wayarsa ta dauki ruri,lambar karima ce hakan ya sanyashi dagawa cikin hanzari yana cewa
“Haba karima,haba karima,meye haka din da zaki bar yaranki ki kwashi kaya,yaji da girmanki da komai”
“Saurara ba wannan na kiraka ka gaya min ba,kiranka nayi na gaya ma ka sanar da wannan matar taka diyar malamai masu kwanan buzu cewa,ta bar murna karanta ya kama kura,babu inda zani ina nan dawowa,kuma dawowata ba zata yi mata dadi ba wallahi wallahi sai ta gwammace kida da karatu,don babu wata ‘ya da zan bari ta shigarmin rayuwa ba tare da na nuna mata kuskurenta ba,kuma kada ka soma wahal da kanka kace zaka nemeni don ba samuna zaka yi ba,har sai randa na dawo da karan kaina,ina fata ka gane”qit ta datse kiran sai yabi wayar da kallo yana kada kai aljihu ya maidata yana amsa sallamar da sumayya tayi masa.