LIYAFA PALACE HOTEL KATSINA
dakin taron cike yake makil da jinsin mutane mata da maza ko wane tebur yana dauke da mutane biyu mace da namiji ko wanne namiji da yake a gurin kuma matarshi ce domin haka aka tsara masu aure ne kawai aka gayyata domin idanma ba matarka bace to kaika jiyo domin tsarin dai shiga gurin mace da namiji ne
An kayata gurin iya kayatuwa domin gurin ya samu halarta hadaddun yan boko da shahararrun masu kudi Dinner ce ta mussamman wanda aka shirya ma ALHAJ NURA SADA ISA MANI shida mai dakinsa HAJ NAJA’ATU HARUNA SALE wanda abokanshi irinsu bello ibrahim Senior suka shirya mishi saboda karin girma daya samu a gurin aikinshi
Wata sabuwar mota ce dalleliya ta sanyo kai a cikin farfajiyar Hotel din gurin da aka tanada don ajiye motoci direban Alhaj nura ya
faka motar da harizari direban ya fito daga cikin motar ya nufi dai-dai kofar da Ubangidan nasa yake kwance a cikin motar, ya bude masa.
Sai da ya dauki wasu ‘yan dakiku sannan ya zuro da kafarsa ta dama ya fito fuskarshi tana dauke da murmushi, dayan gefen direban
Direban ya nufa cikin yanayi na sauri ya bude haj naja’atu ta fito itama kamar yaddah
mijinta yake dauke da fara’a, haka nan ita ma fuskarta sai fitar da wani annuri take.
Hannunta ya riko suka nufi cikin hall din gaba daya duk mutanen da ke ciki suka mike domin girmamawa. Daga bisani suka zauna a guri na musamman da aka tanadar musu (higher table). Bayan sun zauna daya daga cikin abokan Alh. Nura mai suna Alh. Muhammad Ibrahim Na’iya ya tashi ya karbi lasifika ya gabatar da kanshi, sannan ya yiwa bakin da suka taru a gurin sannu da zuwa. Ya gabatar da dan takaitaccen tarihin Alh. Nura da irin gwagwarmayar rayuwar da ya sha kafin ya samu ya taka wannan matsayin da ya samu a yanzu. Daga nan kuma aka ci gaba da gabatar da kayan lashe-lashe da tande-tande. Sai kuma
wanda aka shirya liyafar domin shi ya fito shi ma ya gabatar da nashi jawabin gami da nuna godiyarsa ga Ubangiji da ya kai shi ga samun wannan matsayi.
‘Ya kuma gode wa abokanshi da suka shirya mishi wannan liyafa. Yana karashewa ya sauko kan step ya rinka bin abokan nashi suna gaisawa gami da yi musu godiya duk abin nan da ake Naja’atu tana biye da shi a bayanshi.
Daga karshe Sunusi Anu ya ci gaba da nishadantar da wurin da zakakan wakokinshi masu tausasa zuciyar masoya, daga can gefen Haj. Naja’atu take tsinkayo muryar wasu mata suna gulmarta. Daya daga cikinsu take cewa,
“Ai wallabi ina tausayin wadannan bayin Allah, saboda rashin haihuwar nan, dubi yadda suka ajiye dukiya sai dai babu magaji’
Dayar kuma ta ce, “Ai na ji ance, wai matsalar daga gurin matar take ba daga gare shi bane
Wata ta kusa da su ta yi tsagal ta sanya baki tace Ai ko idan da nice Alhaji Nura bazan yarda na zauna da macen dake juya ba,tunda har nasan ni din lafiyata Kalau, saboda
idan shi ne ke da matsalar ita ba zata iya yarda ta zauna da shi ba’
Naja’atu ta waiga ta kalle su, sai dai duk a cikinsu babu wacce ta lura da kallon da take yi musu, saboda dadin gulma.
Ranta a bace ta fito daga cikin hall din,
Alhaji Nura yana ganin haka ya yi saurin sallama da abokanshi ya fice daga cikin hall din shi ma. Cikin sassarfa yake tafiya tamkar zai kifa, ya karaso gurin da ta ke, yadda ya ga ta juya masa baya yasan lallai babu lafiya, don haka bai tsaya wani bata lokaci ba ya kira direba ya ja su zuwa gida.
Ko a cikin motar Naja ta bi ta yi kicin-kicin da fuskarta, don haka Nura ya kyale ta ya bari sai sun isa gida shi yasan hanyar da zai bi ya rarrashi ‘yan kayansa.
Direba yana yin fakin ba ta jira yazo ya bude mata ba ta bude kofar, ta yi sauri ta bar gurin. Nura ya fito daga cikin motar ya yi tsaye yana bin bayanta da kallo. Wani murmushi yayi, saboda yasan halin Najarsa, muddin ranta ya baci to sai ya sha rarrashi kafin ya samo kanta.Bin hayanta yayi zuwa cikin gidan, a falo ta yada zango, goggoron da ke sanye a kanta ta cire tayi wurgi da shi ta sanya hannaventa ta tallabi fuskarta yadda ya ganta ta zauna ta yi tagumi ya sanya ya shigo cikin falon. Kai tsaye gurin fridge ya nufa ya bude ya dauko robar ruwan Yankari ya zuba a cikin kofi ya kurbi kadan ya ajiye. Naja ko ga alama hawaye ne suke fita daga cikin gurbin idanunta.
Nur ya tsura mata idanuwa yasan yanzu yadda ranta ya baci ko da ya rarrasheta ba zata hakura ba, don haka ya nufi dakinshi.
Hakan data gani ya sake bata mata rai, wato bai ma damu da bacin ranta ba? Ta silalo daga kan kujerar da take zaune ta rinka kuka, ta daga hannunta cikin muryar kuka take rokon Ubangiji da ya ji kansu Ya basu ‘ya’ya masu albarka tare da Nur dinta,
Nur ya fito daga cikin dakinshi ya tarar har a lokacin Naja tana nan durkushe akan
Kafafunta tana sakin wani sautin kuka a hankali. Ya dan tako zuwa gurin da take, ya tsuguna ya kai hannunsa ya dafa kafadarta ya
Hmmm