CIKAKKEN TARIHIN KABIRU JAMMAJE
Suna: Kabiru Musa Jammaje
Inkiya: Jammaje
Kwarewa: Mai shirya fim, marubucin, mamallakin Jammaje Academy
Gari: Jammaje
Jaha: Kano
Kasa: Nigeria

WANENE KABIRU JAMMAJE
Cikakken sunansa Kabiru Musa Jammaje yakasance Fitaccen marubuci, Mai wallafa littattafai, Gawurtaccen mai shirya fim, Kuma malamin koyarda harshen turanci Kuma mamallakin makarantar Jammaje Academy.
HAIHUWARSA
Anhaifi Kabiru musa jammaje a garin Jammaje, dage Karamar hukumar tudun wada a jahar Kano.
karanta: Tarihin Kannywood (masana’antar film na Hausa)
KARATUNSA
Kabiru musa jammaje yayi Karatunsa na matakin primary a makarantar Jammaje primary school bayan kammalawane yashiga makaranatar government teacher’s college Tudun-Wada inda yayi Karatun Junior secondary School na tsawon shekaru Uku (3).
Kabiru musa jammaje yayi Karatunsa na senior secondary School a makarantar Army day secondary School dake a Kano.
Bayan kammalawane yasamu damar shiga college of art science and remidial studies domin Karatun diploma a harshen turanci.
Daukakarsa
Jammaje Yafarane da bude makaranatarsa nakansa Mai suna jammaje academy wacce takasance itace makarantar farko a arewacin Nigeria da aka fara budewa musammman domin koyarda harshen Turanci.
Daga bisani yafara Aiki a gidan rediyon freedom wajen gabatarda shirye shiryen koyarda harshen Turanci.
Shigowarsa masana’antar Kannywood
Kabiru jammaje yashigo masana’antar Kannywood ne a matsayin Mai shirya Fina finai dakuma bada Umarni.
Jammaje yashigo masana’antar da sauyin yanayi domin yazone da sabon salo Wadda ba’a Saba ganin irinta ba domin mafiya yawancin Fina finansa ana shiryasu ne a harshen Turanci.
Duk dacewa a baya akwai wasu shirye shiryen masana’antar Wadda anyisu da Turanci Amma jammaje ya Kara ingantawa sannan yakara ma Shirin armashi.
Karanta: CIKAKKEN TARIHIN HAFSAT IDRISS
Acewarsa yashigo masana’antar ne da kudiri guda you (3)
Na farko itace tinkarar kalubalen fasara da ake samu a masana’antar wato (English Subtitle) domin mafiya yawancin Fina finan Hausa inkaga subtitle nasu ba dadai akeyiba Kuma hakan Yana taba mutuncin masana’antar.
Wadda Acewarsa tabbas yafara yaki da hakan Kuma ana samun nasara.
Kudirinsa na-biyu itace domin samarda fina finan na Hausa Wadda zasu tafi kan turbar ilimi
Sannan Na-uku itace yasamar da fim a harshen Turanci Wadda yayisu dadama.
Jerin Fina Finanda Yashirya A masana’antar Kannywood
There is a way
This is a way
In search of a king
Bakar walkiya.
JERIN JARUMAN DA JAMMAJE YAYIWA FIM
Nuhu Abdullahi
Hauwa maina
Umma Shehu
Rabi’u Rikadawa
Ibrahim mandawari
Umar malamfashi ( A bankaura)
Sani mu’azu
Saratu Gidado
Tijjani faraga
Hajara isah jalingo
Zainab booth
Dasauransu