AaLIMAH COMPLETE BY SUMAYYAH ABDULKADIR

 AaLIMAH COMPLETE BY SUMAYYAH ABDULKADIR 

Jirgin ‘American Airways’ ya sauke AALIMAH MANSOUR a birnin Massachusetts na kasar Amurka a ranar ashirin da biyar ga watan Mayu, na shekara ta dubu biyu da goma sha shidda(2016). A sannu ta bi jerin gwanon masu saukowa daga jirgin rataye da matsakaiciyar jakar hannu ta mata.  Sanye ta ke da doguwar riga da veil dinta kirarTahran (maroon colour) ta zagaye fuskarta da veil din rigar. Takalmin kafarta baki ne mahadin jakar hannunta marar tsayin dunduniya. Taku ta ke cikin nutsuwa har ta taka kwaltar filin jirgin

(Boston Logan International Airport) ta shiga van din da sauran fasinjoji ke shigawadda za ta karasa da su zuwa ainahin ginin cikin filin jirgin, inda aka yi mata duk wasu immigration checks, daga karshe ta dauko jakar kayanta ta fito.                       Hasken sassanyar ranar da ya soma ketowa ya dallare mata ido, ta sanya tafin hannunta ta kare saman idanunta daidai lokacin da masu taxi suka soma isowa gare ta.                    Tambayarta suke inda za a kai ta. Ta diregajiyayyun dara-daran idanunta a kansu kamar mai kiyasi, kamar kuma mai tantance wanda ya kamata ta zaba,da ganinta ka ga bakoa kasar da bai taba zuwa ba, kafin ta tsaida idonta a kan wani dan tsamurmurin bature ta nuna mishi adireshin inda zai kai ta, wanda ke rubuce cikin jotter dinta, wadda ta fiddo daga jakar hannunta. Daukar jakar tata ya yi ya sanya a bayan motarsa ya bude mata kofar baya, ta shiga ta zauna. Ya zagaya ya shiga mazauninsa, ya tada motar. Tafiya suke sannu kan hankali a kan kwaltar manyan titunan birnin Massachusetts tana karewa kyawawan titunan kallo. Birnin Massachusetts na daya daga cikin manyan biranen da kasar Amurka ke tinkaho da su. Ya kuma kunshi al’ummatai daban-daban, daga yarekala-kala na duniya. An kiyasta population din birnin Massachusetts a shekarar (2017) da adadin (685, 094 population). Yana kusa da Cambridge daga gabas, tana iyaka da Hampshire da Vermot daga Arewa, daga yamma zagaye yake da babban birniNew York, daga Kudu da birnin Connecticut da Rhode Island. Daga gabas kuma zagaye ta ke da Atlantic Ocean. Birni ne daga Arewa maso gabashin USA. 

DOWNLOAD HERE👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *