ABBAS
CHAPTER 1
‘Yan makaranta naga suke ta wucewa da alamar tashin su kenan daga makarantar,
daya ke yara qanana ne shiyasa mafi yawancinsu kafin ma su tashi ake zuwa zaman jiran daukan su,
wanda inka duba zaka ga motoci ne awurin suka fi yawa sai da tsirarun ‘yan adaidaita,
wasu kuwa daba nisa ne dasu ba sae suke qarasawa da qafafunsu da alamar sun riga sun gane hanyar gidan dakansu basai anmusu jagora ba,
kadan daga cikinsu kuwa musamman ake xuwa dan aqarasa dasu gida koda qafan ne
,hakan yana nuni dacewa ba’a so ne suka mo hanyar
gidan su kadai…..
Wata yarinya ce nagani atsaye bazata wuce shekara takwas ba,tsaye take da lunching box din ta kalar pink mai kyau ahannu…..
Atsayenta ta ke bata da alamar motsawa ko ina ga dukkan alamu itama jira take azo atafi da ita gida,
Har yara sun fara watsewa sae kuwa naga wani kyakykyawan yaro matashi ne wanda bazai haura 15 yrs ba yazo tabayanta ahankali ya lalla6o karab yarufe mata idanu,
Kokadan banga alamar razana atattare da ita ba sai ma dan dariya data yi irin nasu na yara.
sannan tadago hannun daman ta ta saita hannun daya rufe mata idon dashi ta sa ke mar mintsini mai shiga jiki
take ya bude mata idanun sannan yafara yarfe hannu
Kai ,
kai,
kai
“Haba ke kuwa dan Allah yafada kamar zaiyi kuka.
Dariya tafara yi masa tana qara kallonshi.
“Gaskiya yarinyar nan muguntarki ta shahara
Wama ya koya miki irin wannan abin ne dan Allah.”
Ya fada yana qara kallon cikin idanunta
Da alamar mintsinin yashige shi sosai
Kamo hannunta yayi daniyar su fara tafiya,zuwa gida don yasan daman bayaga dariyan toh ba magana zata sake yimar ba
Al’adarta kenan ita inde tamar mugunta toh sae de tayita dariya amma ko me zai fada bata ta6a bashi amsar maganrsa
Mu wuce gida toh”
yace da ita
Na kusan yin maganinki ae badae ni kike rainawa ba.
ah ah yayah
Bakai ne karufe min ido ba”
sai yanzun ta budi baki tayi magana tana me turo bakin gaba
Toh dan na rufe miki ido sae akace kuma ki gutsure min fatata?
Kalli fah yanda kika yimin!
fuskar tausayi tayi dan ganin gurin yayi jaa sosai
Sorry yayah
bazan sa ke ba!!
Kima sake kiga wanda zai ringa dawo da ke gida
Yitayi kamar zatayi kuka,ta tsaya da tafiyar
Miye kuma ya faru?
Bakai bane?
Toh yi haquri taho abinki daddy’s angel kinga yau akwai rana,muyi sauri muje gida kar rana ya dafa mu.
Tafiya tafara ahankali
ganin hakan yasa shi yah qara kamo hannunta tare da kar6ar lunchbox din dake hannunta
Nace kiyi sauri wannan ranar fah tafara damuna.
Wae ma ni kekam da ba ke kadai kike dawowa bane?
Wato dan nazo sau daya na rakaki gida kuma shikenan kema kika daena tahowa dakanki ko?
Zanyi maganinki ae yarinyah kwanan nan…….
Bata kula maganar daya ke yi mata ba.
Sai ji yayi tafara cewa yauwa yayah yau apple xaka siyamin tana fada tana tsalle irin na farin cikinnan tana kuma nuna mai teburin fruit din dayake junction din shiga unguwar tasu.
Ke nifah yau banfitoh da kudi ba…..
Take kuwa tafara kuka tana mar ihun ita kam dole sai ya siya mata bai kulata ba suka cigaba da tafiyah.
Aikuwa suna zuwa daidai gurin mai kayan fruits din ta kwace hannaunta daga cikin nasa ta qi wuce wa takafe awurin tana kwa6a fuska…..
Yasan ko mai zai ce da ita ba yadda zatayi ta bishi batare da ta ga abinda takeso din ahannunta ba.
“Maiyah”
yace qasa qasa sannan yawuce wurin mai fruits din ya kar6o mata aleda sunkai guda biyar akan anjima zai kawo masa kudin.
Dayake sun saba da mai fruits dinma sosai so bashida matsala da yaran yasan kudinsa zasu zo cas ba ragi shiyasa bai damu ba
daman kullum idan akazo daidai mai fruits din zakaga ta fara tsalle tana fadin abinda takeso asiya mata
Wataran tace pineapple,wataran watermelon,wataran kuma tace babana,ko kuma apple kamar yanda tayi nayau kenan.
Lemu ne kadae bata sha ita kwata kwata bata sonshi ma kokadan.
Kuma kullum Indai suka zo wucewa sai ya siya mata abinda yake ao din inkuwa bae siyaba toh kuwa zai sha rigima
sosai aranar
Sallama yayi apalourn kafin yatura qofar yashiga,ganin bakowa apalourn yasashi zama akan two seatern dake cikin palourn.
Ita kuwa ciki ta wuce dagudunta uniform kawai tacire ko kaya bata saka ba tasake fitowa da sauri ta nufi ledar da apple dinnata ke ciki.
Bai lura da ita ba harse data dau ledar tanufi kitchen kafin ya hango ta
“Teemah”
Yace da qarfi
Na’am ta amsa mai
Yayah wankewa zanyi neh a kitchen”
Ta tafada mar dan ita azatonta akai ne yake qiran nata.
Dawo nan
Yafada tare da miqewa xaune”
Dawowa tayi da ledar ahannunta tazo gabanshi ta tsaya
Hannu yasa ya kar6i ledar ya ajiyeh agefensa sannan yadaga hannu yakamo kunnanta daya
“Stubborn girl kike so ki zama ko”
Kuka zata fara
Ya daka mata tsawa
” oyah jeki sa kaya my friend”
yafada sannan ya sake mata kunnan nata.
Ban hanaki zama da pant ba ne acikin gida?
Wuche kije kisa kaya ni inbahaka ba zanga mai baki apple din ai.
Yarinya sai rashin jin tsiyah”
Dakuka tajuya dakin nata, taje tasako wata riga mara kauri iya gwiwanta tafito
Duk ta qagu taganta tanashan apple dinta .
Tana shigowa sae kuma ga fanni (house maid) dinsu ce itama tashigo.Kusan sa’ar sa ce itama amma zata dan girme masa kadan
“Fanni kunna min AC pls.”
Yafada da dan guntun tsuka da alama zafi Ya ishesa sosai.
Ha ‘ah kun iso kenan?
Matar dake shigowa ta wata qofah daban ta ke fadi
Ehh mundawo mummy tun dazu ma”
Matashin yaron ne yabata amsar maganar tata
Murmushi tayi
Sannan tace
ai kuwa najiyo hayaniyar ku dazu ina shirin tada sallah ne shiyasa ban fito ba
ehh nida wannan mara jin ne ai yafada yana kallonta.
ita kuwa ko ajikinta sai faman kokuwa ta ke yi da apple din dake gabanta.
Toh yau din kuma za aji kanku kenan”
ceawr mummyn nasu sannan taqara da cewa
“Yanaga hannunka kamar ciwo yayi ja.
Kallon Teemar yayi yaga ko ajikinta kamar bada ita ake maganar bama.
Bugewa nayi mummy
Ayyah sannu Abbas”
Shiga dakina akan mirror inaga akwai man zafi Kasamu kashafa awurin da wuri
Toh mummy.
Yace da ita….
Sannan yamiqe daniyar zuwa dauko maganin
Bayan fitarsa ne mummy tadawo da kallonta ga Teeman
tace da ita
“yau Teemah ko kulani ma bazakiyi bako kinsamu apple ya dauke miki hankali”
Dagudu ta taso tazo ga mummyn tana da dariya dan zuwa yanzu taci iya wanda zata iya ci daga ciki kuma ya isheta,daya da rabi ta cinye rabin kuwa sanda mummy ta mata magana ne ta ajiyeshi ta taho gareta
Qoqarin hawa jikin mummyn ta ke yi
mummyn ta dakatar da ita da fadin
“a’ a dakata daganan mamana bakiga hannunki bane”Maza jeki fanni ta watsa miki ruwa sae ki zo ina jiranki
kinji “
Da gudunta tafita ta nufi wurin fannin”
Dai dai nan shima ya dawo dakin yana me qarasa shafa maganin ahannunsa
Zama yayi a inda yatashi dazu
Yarinyan nan akwai rigima mummy……
Wani abin tamaka ko?
Mummyn tafada tana me tattaro hankalinta garesa
Nan yabata labarin
abinda Ya faru dazu awajen me kayan fruits
suka danyi dariya dukkansu.
Shiyasa ai naga ta nutsu ta bata hankalinta akai Ashe rigima tayi akai sosai.
Inka ci abinci sai ka zo ka miqa masa kudin nasa.
Uhmm barin ci abinci tukunna.
Abbas din yafda sannan ya miqe ya nufi daining side ya dibi abincin dai dai yanda xai iya ci,ko takanta bai bi
Dan yasan tunda tasha wannan abin toh ba qara waiwayan abinci zatayi ba.Mintina goma ya dauka agurin cin abincin,cak ya miqe tsaye
Dakinsa ya shiga ya watso ruwa yayi sallah Sannan yayi zaman shirya jikinsa da kyau. +
Abbas yaro ne shi amma sam bashi da wauta ko hayaniya irinta yarintan nan anatse yake komansa kamar wani babba.
Haka idan yayi gayu har mamaki zai baka don irin yadda ya iyah zama ya gyara jikinsa tsab kamar bashi ba.
Fitowa yayi da niyar zuwa gurin mummy,sai kuma yaganta a parlour tana kallon wani hausa movie.
Mummy dake zaune acikin parlourn
kallon inda taji motsin tafiya tayi,sarai tasan Abbas ne dan jiyo irin qanshin turaren dayake amfani dashi da tayi.
murmushi ne ya su6ce mata sanda ya bayyan aidanunta
Aranta ta ke jinjina irin tsabta da kula da kai da Abbas din
yake dashi
Qaraso wa yayicikin parlourn amma tunkafin yayi magana sai mummyn tariga shi dacewa
“harka shirya kenan”
Murmushi yayi mata batare dayayi magana ba.
‘Karaso wa yayi ya zauna agefenta
Sannan yace
“barka da hutawa mummy”
Amsa masa tayi da “yauwa dan albarka”
Sannan tajeho masa tambaya tana qara kallon inda yake zaunen daga gefenta.
“Yanzu zaka miqa kudin mai fruits dinne?”
Kai Abbas din yadaga mata alamar
“ehh”
cewa tayi
“Bari toh na dauko maka kudin “
tana fada ta miqe ta nufi bedroom dinta
2k takawo ta miqa masa.tare da zama a inda ta tashi dazu
Abbas. Bai kar6i kudin ba illah dariyah yayi kadan sannan yace
“Mummy inaga fah bazai wuce 1k ba kudin, dakyar ma inzai kai.
Cewa tayi kar6i de nikam Abbas ka kaimasa,idan kuma kaje da 1k din shikuma yace bai isa bafah, cewa yayi da ita “zai ma isa mummy “
Sa ke miqa masa kudin tayi tana fadin
“ungo kaje Abbas bana son musu”
Kar6a yayi sannan ya juya ya fita yana fadin
“sai na dawo mummy”
“Uhm”
kawai tace dashi sa nnan ta maida idonta taci gaba da kallon data keyi a television.
Teemah kuwa nacan bacci ne ma yadauke ta bayan fanni tamata wanka,kafin ta ahafa mata mai sai bacci ya dauke ta,ganin hakan fanni tasa ka mata pant kawai tabarta,adakin tafito taci gaba da ayyukanta.,3:00 dot tatashi abaccin, dayake ranar alhamis ce, ba islamiyah,
shiyasa babu wanda ya damu da baccin datayin.
Tana tashi kuwa dakin mummy ta fara zuwa da kwa6a66an fuskarta irin na yarinta da kuma yanayin bacci.
Tura qofar tayi tashiga,gani tayi bakowa adakin,amma jin motsin ruwa abayin yasata gane cewa mummyn nata bayi ta shiga,hakan yasa ta nufi bakin gadon mummyn ta dora kanta akai,amma ‘kafafunta suna a qasa.
Tsawon minti biyar mummyn ta qara sannan ta fito daga bayin,ganin Teemahr ahaka yasa ta taho gareta
Mummy
Zama tayi abakin gadon itama sannan ta ce
“ya akayi ne ‘yan mata”
Ta fadi tare da dago kan teemar ta tsayar da ita.
lumshashshun idanunta ta sau’ke akan na mummyn batare da tayi magana ba.
Ganin hakan yasa mummyn ta kama hannunta ta koma da ita bayin ta sake watsa mata ruwa dan ta warware daga baccin da tayin.
Tare suka fito da mummyn
Amma sai ita mummyn tawuce gaban madubi ta zauna akan dressing stool da niyyan yin shafa.
Gani tayi Teemar still tana tsaye,
“Ke baki da kunya ne kam da kika tsaya ahakan din”
mummyn tace da ita da dan tsawa kadan
“Maza jeki fanni tasa miki kayanki sai kidawo”mummyn tasake fada mata amma wannan karon idonta naga shafa man data keyi ne.
Pant din data cire shita dauka ta mayar jikinta sannan ta nufo inda mummyn ta ke ahankali,
Jikin mummy taje ta dora kanta a bayanta,
mummyn bata kulata ba itama ta ci gaba da abinda takeyi,sai bayan tagama ne zata miqe sannan ta sa hannu ta jawo ta gabanta
Kallon fuskar ta mummyn tayi da kyau sannan tace “wai ni yau me ke damunki mamana”?
Bude baki teeman ta yi tace
“Daddy! “
Mummyn kallonta tasakeyi tare da fadin
“me kuma daddyn yayi”?
Kwa6ah fuska Teema tayi tare da turo baki kamar anmata wani abin ne
Ganin hakan da mummyn tayi yasa ta fadin
“tsaya toh bari idan na shirya sai in qira miki shi.
Kai Teeman tadaga alamar toh
“Maza kema jeki wajen Fanni kice tasaka miki kayanki, Inyaso sai ki dawo inqira miki shidin kinji mamana”
mummy ne yi wannan maganar alokacin data duba kayan dazata dauko
Teema yi tayi kamar bataji abinda mummyn tace da ita ba.
Wata super exclusive atampa mummyn tadauko mai kalar ganye da zanen yellow yellow ajiki,baqaramar kar6arta kayan suka yi ba,tana gama shiri takamo hannun Teema tare daukan wayarta suka fito parlour, ahanyan zuwan ta ke cewa “bakijin magana ko Teemah?
So kike Abbas yayi fishi yadaina rakaki school ko?
sai yanzu Teemah ta 6udi baki tace
“a’a mummy zanfara jin magana”,
“Karki fada mishi kinji mummy”
Murmushi kawai mummyn tamata,
tunkan su qaraso mummy tafara kwalla qiran fanni,bakinta biyu ana ukun fanni ta amsa tare da nufowa parlourn da hanzarinta.
Atare suka iso cikin parlourn da fanni
“Gani hajiya”
Fannin ta fada tana mai risinar da kanta
Mummyn na shirin zama tace da fannin
“Don allah taimakeni da kayan yarinyar nan,yau rigima ta ke ji dashi”
“Toh hajiya”Fannin tace tare da juyawa dan dauko
abinda hajiyar ta umarce ta
Mummyn ne taqara fadin
“kinga fanni harda man shafar ta ki dauko min pls”
“Uhm”
fannin tace sannan taci gaba da tafiyah
Mummy wayarta tadago tayi dialling number din Daddy
Sallama tayi bayan yadauki qiran
Shima daddyn ya masa mata
“Yah akayi ne uwar gida?
Lpy lau”
Cewar mummyn sannan ta ciga ba dafadin
“Wannan qiran bana wa bane alhaji na angel dinka neh.”
Cewa daddyn yayi “ahh toh bata mana “
“Ina take “?
Yasake Fada !
Teemah da tun da taji muryar daddynta ta matso da sauri kamar ba wacce ta ke ta kwa6a fuska dazu ba.
Kallonta mummy tayi taga yanda ta warware daga sakalcin data ke yimata dazu.
“Ungo mummyn ta ce da ita”
Dawuri ta kar6a sannan taja gefe ta zauna akan wata kujerar daban dan nesa da mummyn,sannan ta dago wayar ta qara akunnenta.
“Daddy” tace da farin ciki afuskarta
cewa yayi “na’am mamana”!
” yah school?
“tace lafiya daddy “
“Yauwa mamana kina karatu ko?
Kai ta daga alamar ehh
Daddy yaushe zaka dawo ?
Cemata yayi “very soon angel zan dawo”
“kin ci abinci ko? Ya tambayeta
Cemasa tayi ” a’a daddy apple naci!
Yayah ne ya siyamin ahanyar school dinmu.
yace
“Gaskiya yayah ya kyauta
Abincin fah ?
“Shima zanci”
cewa yayi
“Toh je kici abincin sai muyi awayar ajima ko “
Toh “tace masa
Sannan ta tashi ta kawo wa mummy wayar
Akunne mummyn tasa ka
Anan daddyn yake tambayarta ina Abbas dinfah.
Dan dariyah tayi sannan ta bashi labarin abinda ya faru briefly,taqarashe da cewa Abbas yakai kudin mai
fruits dinne.
Cewa daddyn yayi idan “Abbas din yazo ta qirashi anjima.
Daga nan sukayi sallama kowa ya ajiye wayar.
Mummy kallon Teema tayi sannan tace iya fitinar dama kenan.?
Dariya kadan teemah tayi sannan tace
“mummy ina yayah yake “
“Ya kai kudin bashin da kika sa yaci….!
Amsar kenan da mummy ta bata.
Toh dayake bawani fahimta tayi ba hakan yasa tayi shiru bata qara magana ba.
mummy Kallon kayan dake ajiye agefenta tayi sannan ta ce
“Oyah zoki saka kayanki”
Tun dazu takawo lokacin kina waya”
Matsowa teema tayi kusa da mummyn.
Mai mummy tafara shafa mata sannan tasa mata kayanta pink din riga da wandon jeans mai kyaun gaske,sosai kayan ya kar6i jikinta.
Mummy tana gama shiryata ta miqe tace bari taje tayi sallar la’asar.
Tafiya tayi tabar Teemah tan game da wayarta awurin,koda mummyn ta idar ma bata sauqo dawuri ba can tayi zamanta adakinta.
Abbas ma sai da yayi sallah a masallaci kafin ya shigo gidan,aparlour ya taddata tana ta game abinta,koda yayi sallama ma batasan yayi saboda hankalinta yadauku a game din datakeyi din.
Zuwa yayi ta bayanta ahankali ya kwace wayar
Sai sannan tadaga kanta da sauri ta juya bayanta
Tana gani. Shi ne kuwa ta taso da gudu tazagayo inda yake,kafin ta iso shikuma yafara jada baya- baya ,itama sai ta biyo shi,guje guje suka farayi yanata mata dariya,ita kuma kamar zatayi kuka tanata binshi akan sai ya bata wayar wai,dayagaji da gudun sai ya zauna akan kujera yana dariyah,zuwa tayi itama inda yake din tana cewa
” yayah ni kabani “
ta ke masa qafa tayi
Dayaji zafi yace “wash”
Ke tsaya ni kin karyan yatsu”
Baya ta matsa kadan tana qare masa kallo
“Ungo “ya ce tare da miqa mata wayar “
Bata kar6a ba itama sai tsugunan datayi awurin qafar tasa inda hannunsa yake yana shafa qafar,nan itama takai hannunta ta daura akan hannun nasa,
“Sorry yayah”
Tafada kamar zatayi kuka,
shikenan ai yahuche ,ya daina zafin”
Haka yace da ita,
Don yadda yaga tayi yau din yabasa mamaki,bahaka tasaba yi masa ba musamman idan tasan ta mai mugunta,dariyah take qara binsa dashi,amma yau harda cewa “sorry”
datayi hakan sai yaji tabasa tausayi.Abbas akwai sa haquri sosai,bai fiya yin fushi ba akan abu.yakan bi komai ne da murmushi koda na 6acin rai ne,gashi akwai tausayi.
Ita kuwa Teema “sorry” data fada mar, tafada ne dan tsorotan datayi ganin yanayin fuskarsa,dukda wayo bai isheta ba amma tafahimci cewa yaji zafi sosai,kuma gashi bada niyyan mugunta ta takasanba…….arashin sani ne.shiyasa ta ce sorry.
Shikuma abbas ganin tayi hakan yasa shi daure wa yace mata yadaina jin zafinma,duk da azahiri bawai yadaina ji din bane.
Jin yace yadaina yasata danji dadi.
“Kinci abinci kuwa?
abbas ya tambayeta
Jijjiga kai tayi
Alamar a’a
“Oyah muje kici abinci”
Yana fada ya miqe tsaye
Teema kuwa niqe kai tayi gefe.
Ganin hakan datayi yasan bata da niyyan ci dinne.
Shiyasa yace
“Tashi kinji haba angel din daddy”
Still batah kula shiba.
“Tashi muje inbaki abaki”
Yafada tareda riqo hannunta,
Tashi tayi tabiyo shi suka nufi dinning din.
Haka yadinga bata abaki ita kuma tana bashi labarin cewa wai tayi waya da daddy dazu”
“Cewa yayi tayi shiru tukunna bakyau surutu in ana cin abinci, insun gama sai ta bashi labarin.
Shirun tayi kuwa ,shikuma yaci gaba da bata abaki
Suna zaune awurin mummy tasauqo itama,dayake dama tasan sun saba hakan shiyasa bata kulasu ba.illah tambayar teema datayi wayarta.Don mafi yawancin lokuta teemah bata yadda taci abinci dakanta,musamman in rigimarta ta tashi,sai dai abbas yabata abaki,inkuwa bahaka ba toh sai de tayi zamanta batare da taci abincin ba,randa taga dama kuma dakanta take cin abinta.
Abbas ne ya miqawa mummy wayar dayake ahannunsa ta ke.
Sannan yace “mummy kinga abinda nafada miki ko?
Yafada yana dan darawa,
“Meyafaru?
Tatambayesa.
#800 kawai yakar6a mai fruts din”
Yafada yana qoqarin ciro ragowar canjin daga aljihunsa,
Juywa tayi tafar tafiya.
Cewa yayi” mummy ga canjin”
Ka ajiye akwai gobe ai.mummyn tafada batare data juyoba.
Murmushi yayi sannan yakoma yazauna.daman yasan sarai mummy ba kar6ar kudin zatayi ba.
Ahankali yace “dauko hijab dinki muje mu sayo choculate.”
Ai tanajin haka ta miqe da gudu ta nufi dakinta.
Parlour ya koma dan ya jirata.
Bata da de ba tafito da half hijab dinta ahannu
Kar6a yayi sannan ya tsuguna dan yasamata.
Ahankli yace mata “mummy taganki?
Ah ah tace dashi hadi da jijjiga kai.
Toh muyi sauri muje mu dawo,kinsan tahan shan za’ki…..
fita suka yi daga ‘kofar palour cikin sauri don ma kar mummy tagansu,
cikin sa’a kuwa bata gansu dinba har suka je suka siyo choculate din suka dawo gida,
tarkace dayawa Abbas ya siya mata,sai dai bai hallaka kudin duka wajen siyan choculate din ba dan yana tunanin gobe idan Allah ya kaimu karta qara mar rigima irin na jiya a hanyar,shikuma be so ya sa ke dauko abu batare da kudi awurinsa ba
don gaskiya ya na kunyar sa ke tambayar mummy kudi,
Hakan yasa ya rago kusan #500 yabari a aljihunsa.
+
Duk kayan za’ki Abbas ya siya mata bai ma siyah wa kansa komai ba sai wani sweet guda biyu da basufi #50 ba.
Adakin Abbas din suka yada zango,anan yasata agaba tana ta cinye cinyen ta,daga ‘karshe suka fito suka dawo parlour,suka bar ragowan kayan adakin Abbas din.
lokacin ma daf maghrib ta yi,hakan yasa Abbas yace shi kam zai tafi masallaci.Yace itama ta je maza tayi sallah.
Toh”
tace tare da miqewa ta nufi dakin mummy.
Waya ta samu mummyn tanayi,sai kawai ta qaraso wurinta ta zagaya ta bayanta sannan ta kwantar da kanta a kafadun mummyn.
Mummyn bata kulata ba har sai da ta kammala da wayar kafin tace
“Angel din daddy daga ina haka?
Teemar cewa tayi
“Yawo mukaje da yayah”
“hmmm”
Mummyn tace sannan ta qara da fadin
“Lalle teemah,
wato kin samu Abbas kin mnta da ni ko?
Tafada da dan murmushi akan fuskarta
“har zaki je yawo ko ki fadamin?
Teeman
Cewa tayi
“sorry mummy munje siyan cho……..
Awwwn…….tace da wuri tare da kama bakinta ita adole kuskuren fa’da tayi.
Murmushi mummyn tayi sannan ta zagayo da ita ta gabanta
“in qarasa miki?
Tafa’di tana kallon idon teemah
Jijjiga kai Teemahr tayi alamun “a’a”
Meyasa ?
Mummyn ta tambaya.
“Yayah yace kar infada miki”
teema tafada da dan fuskar tsoro kadan.
kamo hannunta mummyn tayi ta matso da ita daf da ita,
sannan tace
Kun fi qarfi na ni kam Teemah ,keda Abbas bakwa jin maganata yanzu,shan za’kin nan ban sonshi kokadan amma keda Abbas baku ji ko.?
jijjiga mata kai tayi teemar tare dacewa
” mummy sorry baza mu sake ba”
Bata kula ta ba mummyn kawai ta miqe tsaye dan ji da tayi anfara qiraye qirayen sallah.
Bayan anyi sallahr isha suka hadu a dinning dan cin abinci.
Abbas yana bawa teemah abakinta tana ci,duk dama kafin ta kar6a sai yayi kusan spoon uku kafin ta kar6i daya.Mummy bata kulasu ba,har sai da suka ‘kare cin abincin kafin tafara wa Abbas fada akan shan za’kin nan dasu keyi.
+
mamaki Abbas yayi akan tayaya akayi mummy tasani.
kallon idon teemah yayi sai yaga ta sunkuyar da idonta ‘kasa hakan ya tabbatar masa da cewa ita ta fada wa mummyn.
Aransa yace “zanyi maganinki ai yarinya”
Afili kuwa ha’kuri yabawa mummyn tare da cewa insha Allahu bazasu sakeba.
Jinsa kawai mummy tayi don tasan abu mai wahalar kenan shi ne su daina din.
Musamman ma shi Abbas din.
matu’kar Teemah zata nuna masa tana son abu toh kuwa dole na fa sai yaga ya nema mata abun ko ma miye ne shi.
“Allah yasa” ta ce sannan ta miqe ta wuce parlour tazauna a akan cough.
Abbas kuwa mummy na tashi shima ya ajiye spoon din dake hannunsa kamar dama jiran tashin nata yakeyi,sannan ya kamo kunnen Teemah da ‘karfi.
Sosai taji zafin wajen
“Yayah”
Teemah tafada cikin azaba. Kamar zatayi
“Ganin dayayi tana shirin yi mai kuka ne yasashi tsare ta da idanu,tare dora dan yatsansa akan bakinsa yaqara da fadin.
“shiiiiii…….Don’t let that tears out”
‘Kasa ‘kasa yayi da muryarshi saitin kunnanta sannan yace
“Baki jin magana ko”?
Dawuri ta jijjiga kai alamar
“a’a
‘Kayi ha’kuri yayah bazan sake ba”
Ta fada tana mai kai wan hannu akan Hannunsa inda ya riqe mata
kunnan.
Tausayi ta bashi saiya sake ta da wuri.
Amma ahankali yace mata
“Wlh inbaki daina yawan gulman kinnan ba ko,zanga mai ‘kara rakaki makaranta ai.”
Turo baki tayi gaba don in akwai abinda ta tsana aduniya toh bai wuce Abbas ya ce bazai ‘kara rakata makaranta ba.
“Nifa yayah ban fada mata ba fah,dakanta ne tasani,”da kuka ta ‘karashe maganar.
Ganin haka yasa yace “toh naji ni,ya isah haka”.
“Abincin ya iSheki ne?
Ya tambayeta yana mai kallon fuskarta dayake ta sa hannunta akan fuskar so baya ganin idanunta,itama bata kulashi ba.
“Ina tambayar kiii?
Ya ‘kara fada cikin dan dagun murya kadan.
Tashi tayi da gudu tayi wajen mummyn tana kuka.
“Mummy kinga yayah ba”Tafada tana me dora kanta akan cinyar mummyn.
“Kun fi kusa ai mamana”
Mummyn tafada batare da damuwa da kukan da teeman keyi ba.
Don sarai tasan bai wuce akan case din shan choculate dinnan bane.
Shine har Sukayi fada akai.
‘Kara powern kuka teema tayi tare bubbuga ‘kafan ta akan tiles din dakin.
“Haba *TEEMAH* so kike kijiwa kanki ciwo ne ?
‘Dagowa teeman tayi sannan ta ce
” mummy bashi bane?
Me yayi ne wai ‘dan nawa.”
Mummyn ta tambayeta tana mai kallon fuskarta.
“Wai ma bazai rakani school gobe ba.
Cewa mummyn tayi
“Kiyi shiru wasa yake miki “
Daganan mummyn takamo ta ta kwantar da ita akan cinyarta sannan tacigaba da lalla6a ta,anan kuwa bacci ya dauke ta.
Abbas kuwa tun sanda ta gudo wajen mummy shima ya tashi ya wuce dakin sa.
Harya watsa ruwa yayi shirin bacci,sai kuma yaji dai inah, hankalinsa bai kwanta ba.
sai ya fito ya dawo parlourn da sallamarsa yashigo.anan ya samesu da mummyn teema harta yi bacci.Mummyn ne tace “yauwa abbas ‘kira min fanni man tazo takaita dakinta.
kaga hartamin bacci anan tana kan rigima.”
+
Cewa yayi “mummy bari kawai na kaita “
Owk .
“Matso wa yai ya dago ta amma sai da yayi nishi,don ba laifi teemah akwai nawi.
Da ‘kyar ya ‘karasa da ita dakin nata,ya kwantar da ita akan gadon yana haki.
Kafin ma ya fito sai ga fanni tashigo itama.
Cewa yayi “
yauwa saka ma ta kayan baccinta.
Sanan ya juya yatafi ko amsar fannin ma bai jira yaji ba.
Washe gari da zai kaita makarantar suna fita ya tare mai adai daita Ya ‘karasa dasu makarantar.
koda aka tashi ma haka ya sa ke tare musu wani adaidaitan suka sake hawa.
Teema bata ankara ba har se data gansu a ‘kofar gida kafin nan ta lura.
Aikuwa kuka tasaka tunkan ma sufito daga cikin adaidaitan.
‘Dan adidaitan ne ya juyo tare da fadin
“yadai ‘yan mata”
Abbas kuwa
Bai kulata ba illah ciro kudi da yayi ya miqawa ‘dan adidaitan,sannan ya fito,itama fitan tayi tana qara kwa6a fuska.
“Wuce muje”
Yafada a tsare.
Yarda abin da ke hannunta tayi ta wuce ciki
da gudu,da qarfi bu’de get ‘dinta ta shiga,don duk abinta tana tsoronsa wani lokacin,don inya tsare toh baya wasa .
Dagudunta tashiga gidan baba maigadi ma yana mata magana amma kota juyo.
Dayaga haka sai ya tashi ya leqa wajen shima don zatonshi ko wani abin ne yafaru.
Abbas ya hango yana tahowa hannunsa riqe da lunch box dinta data yar awajen.
“Aww ashe tare kuke ma”
Inji baba maigadi
Murmushi kawai abbas din yamasa
Sannan yawuce abinsa ciki.
Kodaya shigo bai ganta ba,sai yayi zaton ko tana wajen mummy neh.
Ai kuwa mummy tasha rigima aranar,
data gaji da rigimar ne sai ta aika aka ‘kira mata Abbas.
Koda yazo tambayarsa mummyn tayi
“wai meke faruwa ne?
“Cewa yayi mummy yau ba’a siyo fruits ba ! Ya ‘karashe da dariyah
Tambayarsa mummyn tasake yi
” akan me yasa toh be siya mata ba.”
Cigaba tayi da cewa
“mantawa nayi ne ma ,harfa naciro kudi akan zan baka lokacin dazaka tafi dauko tan saboda rigimarta
,amma ban tuna nabaka ba har sai da ka tafi nagani,
yanama ajiye akan mirror.
Dauko ka bawa habibu (drivern gidan)yaje ya siyo mata .
Dariya ya sakeyi kadan sannan cike da mugunta yace
“Rabu da ita mummy it’s her purnishment”.
Cewa mummyn tayi
“kamata toh kuje can ku
‘Karasa ni ta dameni da kuka.
Hannu yasa ya ‘dagota sama ya fice da ita,bai ajiyeta ko ina ba sai dakinsa.
Yana ajiyeta yana fadin yarinya ‘karama sai uban nawi.
Aikuwa ranar yasha rigima da ‘kyar yasamu yaje ya sallaci juma’ah,saboda hayaniyar kukan da ta keyi.
Ana sallamewa kuwa ya dawo gidan da sauri,don gaba daya hankalinsa na awajenta neh.
zuwa yanzu yafara regreting din ‘kin siya matan dayayi.
Yayi yayi taci abinci kuma ta’ki.
Har kusan la’asar ta ‘ki nutsuwa.
Daga ‘karshe tausayi tabashi sosai,haka yasa ya fita yaje gurin habibu ya bashi kudin sannan ya sanar dashi abinda zai siyo din kafin yadawo ciki.
Da ‘kyar ta yadda fanni ta mata wanka kafin habibun yadawo.
Daya ke ma wurin banisa ne dashiba a ‘karshen layinsu ne wajen mai fruits din,so habibun bai dade ba yadawo
lokacinma ko wankan ba’a gama mata ba.
Da fanni tagama shiryata saita kawota wurin Abbas din,Mummy kuwa duk wannan abin bata san anayi ba,alokacin mummy baccin ta ta ke yi.
Shima daya gata dawo din, tashi yayi yaje ya dauko mata ledar gaba daya ya dan’ka mata,kar6a tayi tare da fitowa parlour ta zauna akan kujera cikin sanyin jiki,kuma har alokacin bata daina ajiyan zuciyan kukan datasha ba.
Bata dade da zama agun ba bacci ya dauke ta rungume da ledar ahannunta,batare dataci komai daga ciki ba……..
Koda Abbas yafito zashi masallaci sallar la’asar ne yagan ta anan tana bacci.
Yaso yatashe ta saboda baccin la’asar babu kyau,amma ganin yanayin yanda take baccin sai yaji tabashi tausayi.
Hakan yasa ya’kyaleta kawai ya yi tafiyarsa masallacin.amma kafin yatafi sai da yadawo da ita ya kwantar da itaA tsakiyan ‘dakin.
Sannan yafice ya tafi.
Lokacin data tashi abaccin kuwa kamar ba ita ba,tsab ta warware,tamanta rigimar datayi.Washe gari Saturday wuni sukayi suna buga game a ‘yar ‘karamar laptop dinsa.anan ma zokuga drama awurinsu kamar TOM nd JERRY…….
+
Sai da lokacin islamiya yayi kafin suka tashi…..amma kafinma ace sun gama shiri,sUnyi sallah,sunci abinci har sun dan shiga lokaci.
Haka ahanzarce suka fito,dole yau sai habibu yah kaisu saboda kartayi latti,don inyace yauma da kafar zasu toh kuwa ba ‘karamin latti zatayi ba.
Koda suka sau’keta gida suka dawo abinsu shida habibun batare da ko sau’ka yayi a motar ba.bye bye kawai yamata tashiga ciki.
‘Karfe biyar daidai yakama hanya ya koma islamiyar don ya dawo da ita gida yanda suka saba abinsu.Dayake sai 5:30 ake tashinsu.
*****
Abbas ba’ko ne agidansu teemah watansa daya kenan da zuwa gidan yanzu.
Amma idan aka lissafa a duka duka wannan shine zuwansa gidan na uku kenan akaf din rayuwarsa.
kuma tunda yazo Habibu bai sa ke kaiwan Teema makaranta ba,haka ma dauko ta,dan acewar Abbas din ahakan ne zai ga gari da kyau,amma in amota ne wai bazai gani dakyau ba.
Teemah kuwa tun ranar farko dasuka zo daidai wajen mai kayan fruits daya siya mata babana,
shikenan tasamu abinka da yarinta wai kullum
Sai an siyah mata,kullum da kalan data ke za6a,in kuwa aka ‘kii siyah toh fah ranar antaro *match*…………
*****
The following day kuma takama ranar sunday ne,kuma aranar daddy yayi musu zuwan bazata.
Sosai sukayi farin ciki da zuwan nashi ,musamman ma daya cika su da tsarabobi ai sai suka sake rikicewa da farin ciki……haka suka yi ta murna da annashuwa…….
Awurin cin abinci ne bayan sun kammala da abincin Daddy yasake yimusu wata bazatar kuma…,,….
Don cewa yayi zuwa ranar laraba Abbas zai tafi makaranta.
Dama hutun J.S.C.E. yakeyi,so yanzu shima zai koma SS1,already ma daddy yace an kammala masa komai ,shi kawai yarage ya tafi………….
*Yah ne readers,* *kuma nasan daddy* *ya muku* *bazata ko?*