ABBAS CHAPTER 3

ABBAS 

CHAPTER 3

Tana fita daga d’akin nasa waje tayi tana haki,taje tasamu k’ark’ashin wata bishiyar mango da ke acan bayan d’akunan gidan tayi zamanta dayake akwai abin zama agurin,aranta take ta tunani wai daman wannan neh yah Abbas d’in,?

Wannan ai babba ne,wata zuciyarta tace ta ce mata amma fah yah had’u,mtssew taja tsaki afili ,toh sai a gidanmu zai zauna neh,ni bana sonshi wlh, nafi son yah Abbas d’ina na dah,don mummy tace har makaranta yake rakani da islamiyah harda yawo muke zuwa,amma wannan dagani mugunta zai yi.

Haka ta zauna ita d’aya agurin tana ta tunani batare da ta je tafad’awa mummy sakamakon aiken ba.

Daddy da mummy neh kad’ai suke zaune a cikin parlourn sanda ya shigo,cikin hikima yad’anyi yawo da idanuwansa acikin ilahirin d’akin ta yanda babu wanda zai lura da abinda ya akaita ko kuma manufar yin hakan,amma bai ganta ba,ya k’araso inda yakamata ya zauna,harya samu wuri ya zauna mummy bata ga Teemah ba, da farko ta zaci abayansa zata shigo tunda basu shigo tare ba,amma sai taga wayam,hakan yasa ta dube shi sannan tace “ina kuma ‘yar aiken ta tsaya?”

“Tun d’azu fah ta taho mummy”

Abbas d’in ya bawa mummyn amsar tambayanta,fuskar sa cike da murmushi.

wayar dataje dashi d’in ya miqawa mummyn

“Harta manta wannan ma”

“Hmm” mummyn tace tare da miqk’a hannu ta kar6i wayar,sannan ta k’ara da fad’in kaga kuwa bata biyo tanan d’in ba,ta fad’a tana me daidaita zamanta, “kode yasar min wayar tayi garin haukarta ko? Mummyn ta tambaya tana kallonsa

Jijjiga kansa yayi alamar a’a.

Daddy kam bai kulasu a maganar tasu ba,don gaba d’aya ya tattara hankalinsa ne akan kallon labarai.

“Yah gajiyar hanya toh?

mummyn tasake tambayar Abbas d’in tana kallon labaran itama.

Da Alhamdulillah ya amsa mata.

Daganan mummyn tamiqe ta isa ga dinning,Bismillah ta musu tana me k’ara shishshirya wajen da kyau.

Abbas ne ya fara mik’ewa tsaye,kallon Daddy yayi sai yaga kamar ma bai san dasu awajen ba gaba d’aya,dan bashi da alamar miqewa,gaba d’aya labarun ne suka d’auke masa hankali,murmushi ya saki sannan ya isa gaban TV d’in ya tsaya k’ik’am ya tare komai,Daddy bazata kawai ya gansa tsaye agabansa,waiwaya wa yayi ya kalli gefensa tukunna kafin ya sawo da kallonsa ga Abbas d’in,dan bai san ma sanda ya bar gefensa ba.

Hannu ya ware ya dan k’wali 🖐🏻Abbas d’in dashi,tare da fad’in “kaci gidanku”

Dariyah Abbas ya k’yalk’yale dashi,yana kallo, daddyn.

“Abinci zaiyi sanyi kuma naga alamar baka da niyyan tashi”Abbas d’in ya fad’I bayan ya tsagaita dariyar tasa

Mik’ewa daddy yayi ya isa ga Abbas d’in,hannu yasa ya kamo kunnan Abbas d’in d’aya yana murmushin shima,fara jan sa yayi ahakan ya nufi gurin cin abincin dashi.

Yana kama kunnan

Abbas d’in take yayi k’asa ya rage tsayi kad’an, dan ba bak’aramin zafi yajiba.Daddy da k’arfi ya kama kunnan nasa.Awchhh daddy zafi”Abbas d’in yafad’I tare da dafe kan hannun daddyn da duka hannayansa biyu. +

Ahaka har suka isa gurin dinning d’in bakin Abbas baiyi shiru ba sai cewa yake “afuwan,afuwan daddy wlh bazan k’ara ba”.

Daddyn sakinsa yayi har se da suka isa daf da wajen cin abincin.

Dariyah suka ji an k’yalk’yale dashi daga bayansu.

Daddy dayasan wace mai dariyar ko juyawa baiyi ba yasake kunnan Abbas d’in,dan yasan wannan aikin sai Teemah,dama yamasa hakan nema dan ganin bata nan,datanan da ko farawa bazaiyiamba dan sanin halinta dayayi.

Waigawa Abbas yayi inda yaji sautin dariyar,four eyes sukayi da ita,take ta zaro ido waje tare da d’ago hannunta ta rufe bakinta dashi,da gudu tajuya tayi hanyar d’akinta,daman shigowarta kenan,sai taga daddy yana jan kunnansa shine ta tsaya dariyar mugunta.

Mummy da tunda taji dariyar itama ta waiga tana kallonta da mamaki.”Allah ya shirya”mummyn tace bayan Teemahn ta wuce ciki.

Cigaba tayi da zuzzuba musu abincin,tana aikin zubawan ne tace wannan yarinyar akwai shakiyanci wallahi,Zo ka zauna Abbas manta da ita zanyi maganinta ai…….

Tahowa yayi yaja kujera ya zauna d’in kamar yadda mummyn tafad’a,

yana zama mummy ta tura masa nasa abincin danshi daddy kam ma har ya fara aikawa da su.

Bismillah yayi shima yafar ci,kamar yanda kowa dake gurin yayi,amma ga mamakinsa har suka kusan gamawa babu Teemah babu alamarta kuma babu wanda ya damu da rashinta awurin.

Baisan cewa su sun riga da sun saba da rashin cin abincinsu batare da ita ba.

Gyaran murya yayi kad’an sai yaga duk sun kallo sa.

Ganin hakan sai ya d’aga hannunsa ya nuna inda tabi d’azun tare da fad’in wancen yarinyar bata cin abincin ne ita?
yayi maganar ne batare da kallon kowa ba daga cikinsu.kuma hakan kenan yana alamta cewa daga bakin kowa ma amsa kawai yake da bukata inda hali.

Daddy ne ya d’an murmusa sannan yace “kamanta kaika koya mata?,

“Wannan yarinyar ai rainonka ce Abbas”sai da yad’an bud’o idansa kadan sannan yasake fad’in “ta kware yanzu kuwa a wannan tafiyar”

Abbas kallon daddy yayi da fuskar mamaki.

“Ehh”

Daddyn yasake tabbatar masa da abinda ya fad’i.

“Tun barinka gidannan Teemah bata bar al’adarta ba na k’in cin abinci da rana ba sai ranar data ga dama take ci.

K’asa yayi da kansa yaci gaba da cin abicinsa batare da yayi magana ba.

Mummy ce taci gaba da fad’in

“Aini bakina har kusan tsayi yayi akan cin abincin nan,sai da naga da gaske takeyi sannan na kyaleta nima na hutawa raina.”

Murmushi kad’an Abbas yayi acikin ransa yace “zakuwa musa k’afar wando d’aya da ita”.

Babu wanda yasakeyin magana acikinsu har suka k’are cin abincin.

Daddy ne yafar tashi awurin ,yabar mummy da Abbas wanda shima tun d’azu ya ajiye spoon d’insa dan already yaji shi full,amma bai bar kan dinning di’nba illah baya da yayi ya jingina da jikin kujeran dayake zaune akai

Har sai da yaga tashin Daddy tukunna kafin ya dawo da jikinsa kan kujerar da kyau,sannan ya fusaknci mummy.

K’asa yayi da muryarsa yanda ba kowa zaiji sa ba.

“Mummy “

Ya ambata ahankali
Kallonsa tayi batare da ta amsa ba,ko dan ganin suna kusa ne oho, +

“Kardai waccan Teemah ceh”yafad’a tare da nuna hanyar databi d’azun kamar yanda yayi da farko da zai tambaye su ita.

‘Daga masa kai mummy tayi alamar “ehh”tana d’an murmushi,daganan tacigaba da duban cikin wayarta data keyi tun da farko.

Abbas kuwa baya yayi yakoma ya jinginu tare da lumshe idansa yakuma bud’esu atake.

Arannasa yake jinjina al’amari irinna ubangiji da ba’a ta6a yimasa gyara.

Tsinkayo muryar mummy yayi tana cigaba da bashi labarin irin rigimar da suka sha bayan wancen tafiyar tasa.

Mamaki yaringa ji aransa danshi bai ta6a zaton ma zata jima batare data manta dashi ba,saboda bawani jimawa yayi tare da ita ba alokacin, its just 3month l,bud’an baki yayi yace “lallai mummy kinsah rigima.

Murmushi mummyn tayi sannan taci gaba da fad’in aikasan halin yaro sai ahankali, yaro yana da saurin saboda kamar yadda yake da saurin mantuwa,dan idan yaro ya riqe abu akansa zaka samu ba fiya mantawa ba,sai dai idan akayi rashin sa’a ya manta d’in toh kuwa da wuyah yasake tunawa.

Jinjina kansa yayi alamar gamsauwa da maganar mummyn,dan kuwa shima yasan da hakan dan baya raba d’ayan biyu yanzu Teemah tamanta da ko shi d’in waye ne agurinta.

Koda ya koma d’akinsa ma kwanciyah yayi bayan ya cire rigar da ke sanye ajikinsa,rigingine ya kwanta yana tina yarintar Teemahn,

Murmushi yasaki daya tino inda mummy tace wai Teemah tace mummy tak’irashi da yah Abbas ba Abbas ba,So ths stubborn girl bata manta dani da wuri ba kenan,take yaji yana ma son yaganta dakyau, dan duk haduwar da suka yi ba haduwar arzik’i bace tunda yazo gidan.so yake ya ganta da kyau yanzu.

Juyi yayi zuwa d’ayan b’angaren hannunsa,ya cigaba da tuno rayuwar da suka yi abaya,muguntar yarinyan nan har yanzu bai barta ba.

“Hmm” yace afili sanda ya tuno irin dariyar data k’yalk’yale dashi dan kawai taga daddy yana jamasa kunne.

Tashi yayi ya zauna ya d’au wayarsa yak’ira wani abokinsa.sukayita surutusu.Daganan ya tashi ya canza kaya sannan yabi jikinsa ya feshe da turarukansa masu dad’in k’anshi,wayoyinsan yasa hannu ya d’auka,ya fice daga cikin d’akin cikin tafiyarsa mai k’ayatarwa.

Gurin habibu ya nufah yaje ya anshi key d’in mota,da kansa yayi driving ya fice daga gidan zuwa inda zashi.

Teemah kuwa tun fitar ta d’azun bat k’ara fitowa ba,bacci ne yad’auketa bayan tagama dariyar muguntar ta,ita adole in anbarta wai taga babba yanan kuka,”kai daddy ya iyah purnishment tafad’a cikin dariyar,nima fah haka mummy take min inna yi mata laifi,gashi nima yau daddy yarama min,Horhh daddy kabiya ni wallahi” +

Haka tayi ta sumbatu ita kadai,har tafara jin bacci,takuwa kwanta tayi baccinta bayan tacire doguwar rigar dake jikinta.

Ba ita ta tashi ba sai kusan la’asar,tashi ta yi ta watsa ruwa tare da d’auro alwala.

Sai da tayi sallar kafin tashirya cikin uniform tafito taahiga kitchen neman abinda zata ci,duk ba wani abin kirki taciba,amma ita tana ganin hakan yafi mata akan ta zauna taci abincin.

Koda tagama kale kalen nata a kitchen d’in d’akin mummy taje,bata samera a parlourn ta ba,hakan yasa ta wuce bedroom d’in mummyn,sallah tasame ta ta nayi,amma azaman tahiya take,ganin haka yasa tawice gaban mirror tana k’ara gyara fuskarta da kyau.

Tacikin mirrorn ta hanago mummy ta yi sallama,ganin hakan sai ta baro wajen datake tsayen ta taho ga mummyn

“Mummy natafi islamiyah”

Kallonta mummyn tayi batare data yi magana ba dan bat so ta yanke azkar d’in datakeyi,sai d’an yatsanta data d’aga ta nuno Teemahn dashi tana d’an juya shi kad’an.

“Mummy bacci ne fah ya d’auke ni shiyasa na makara’?” Tafad’a da d’an ta6e baki alamr shagwa6a dan tasan ma’anar hakan da mummyn tamata.

Jijjiga kai mummyn tayi kawai tare da d’auke idanta daga kan Teemar.

Ganin hakan yasa Teema ficewa daga d’akin,dan mummy ta gama sallamarta.

Waje tayi tanufi cikin gidan,tana fita kuwa tafara kwalla wa Habibu k’ira,shima yanaji ya taso da d’an saurinsa ya iso inda taken dan wajen da ake parking motocin gidan ta nufah ita.

“Y’ar gidan daddy ganinan ya akayi”

Cewa tayi

“yauwa malam habibu ka kaini makaranta mana, yau na makara wallahi”

baki yakama sannan yace “ta6,

“kinga kuwa babu key awurina,shiga ki kar6o key saiki zo mutafi dawuri”

Kallonsa tayi sannan tace “toh ina na wurin naka”?

“Wannan bak’on ne yafita dashi.”Ya bata amsa.

“Wai yah Abbas kake nufi?”Tasake tambayarsa.

“Oho ai bansan sunansa ba.”Zaro ido yayi kamar wanda yaga wani abin tsoro 

“Kar dai wannan shine Abbas d’in gidan nan”ya yi tambayar yana kallonta.

“Ehh wai shine inji mummy”itama ta bashi amsa.

“Baki habibu ya sake kamawa cikin tsananin mamakin gani wannan murd’ad’d’en ne wai Abbas,ta6d’i”

Habibun ne yasake cigaba da fad’in “Abbas ne yayi irin wannan girman h………….

Kafin yajai ayar magabar tasa sukaji adanno horn daga wajen gidan,da gudu mai gadi yaje ya lek’a sannan yadawo da kansa ciki ya wangale get d’in

Ahankali motar ta shigo tazo tayi parking gefe dasu kad’an,

Habibu ne yace “yauwa gashinan ma yadawo”

Teemah kam batayi magana ba illah ido data tsurawa motar.

Tsawon mintina biyu da tsayuwar motar sannan taga anbud’e marfin motar,ta 6angaren da suke tsaye,ita da habibun.

“Wow”

Tace azuciyarta tareda kwalalo ido waje tana kallonsa.
Gani tayi yayi kyau da sky blue d’in shaddar dake jikinsa tare da farin glass a idonsa,iyah abinda ta lura dashi kenan ajikinsa amma ba k’aramin kyau yayi mata ba.
Abbas kuwa tun tsayu warsa agurin yake kallon su hannunsa nakan stairy,kallonsu yake musamman ma ita, tare da mamakin tsayuwar uwar me take yi awurin,gashi jikinta sanye da uniform. +

Dayake tinted glass ne da motar shiyasa babu wanda ya hangosa,motar daddy ce dayafi amfani da ita,duhun glass d’inne yahana su ganshi ,duk da lura da yayi duk hankalinsu naga motar dayake d’inne da alama duk ak’age suke suka fitowar tasa.

Hakan ne yasa shi fitowa.

Yana fitowa bayan ya maida k’ofar ya rufe, gurinsu yanufah direct,hannu yad’aga sama, tana ganin haka ta rintse iso da k’arfi,dan atunaninta sauk’ar mari zataji,murshi yayi dayaga yanda ta tsorata d’in,sai ji tayi yakam kunnanta irin yanda daddy yamasa,harya fara tafiya sai kuma yajuyo,yah wullo wa Habibu key d’in motar,sannan yacigaba da tafiyah.

Cafe key d’in Habibu yayi sannan yacigaba da kallon bayansu

tunani yake aransa taya akayi wannan yazama Abbas?
Abbas ai bay kyashin yiwa mutane magana,amma wannan sai zafin kai,d’azu da kar6ar abu zaiyi awurina ai yamin sallama,amma ganshi yanzu ko kallon arzik’i ma bansamu ba,ballantana sallama.
acewarsa fah😏

Teemah kuwa

Zafi taji kamar tayi tsallen wahala,harda guntun kwallarta,shikuwa k’in sakinta yayi har se da ya isa d’akinsa yatura k’ofar bayan sun shigo,sake kunnan nata yayi,sannan ya tsaya agabanta yana k’are mata kallo.

K’asa tayi da idanunta tare da turo baki gaba,hannunya d’aya kuma na sama kan kunnan tana shafawa ahankali,

“Mugu” tace acikin ranta

Uniform d’in jikinta yasakr kallo,dayake yamma ne,yasan sai dai na islamiya,.

Gyara tsayuwa yayi yan kallon nata sannan yace

“Anan ake islamiyar ko?

Kanta ta jijjiga batare data d’ago ta kalleshi ba,dan muryarsa har cikin kanta take jinsa,lion voice ne da shi mai ratsa jiki,musamman yanzu da yake maganar da ita ,sosai yanayin muryar tasa ta ratsa ko ina ajikinta.take tsoronsa ya shigeta.

“Toh tsayuwar me kike yi agun kuma?

Yasake jeho mata wata tambayar.

Kasa magana tayi dan wannan tambayar bayyanan niyar amsa take da buk’ata.ita kuma sam bazata iya furta komai ba.

Yawan hawayenta taji yaqaru akan d’an guntun dayake mak’ale tun d’azun,ta ke suka fara sintiri akan fuskarta.

Kallonta yayi da mamaki aransa yace “lallai yarinyar na bazata canja ba”

Juyawa yayi yafara tafiyah sannan yace “jeki”

Tanajin haka ta juya da sauri ta fice daga d’ajin.

Gurin mummy taje ta sameta a babban parlour, fad’awa jikin mummyn tayi tana kuka mai sauti,hankalin mummyn ba k’ara min tashi yayi ba da jin kukan da Teemahn keyi ba.
Dan a zatonta ma tuni Teemahn ta tafi islamiyar.

Dakyar ta samu tayi shiru sannan ta tambaye ta dalilin kukan,

bud’e baki teemah tayi sannan tace

‘”bawan nan yayan bane yakama yayita jan kunnena ba,kuma ni babu abinda namasa”.

Tsaki mummyn taja kad’an sannan ta kauda kanta daga kallon temmahn

“Yah kyauta ai,bake rashin ji ba”

Shine harda zuwa kisani agaba da irin wannan kukan Teemah”?
Ke kinmanta d’azu ba dariyarsa kika yi tayi ba dan iskanci”?

Baki teemah ta turo gaba jin mummy bata goyi bayan ta ba.

“Toh islamiyar fah? Mummyn tsake tambayarta. +

Teema ta bud’e baki zatayi magana kenan sai idonta ya hango mata mutum atsaye daga bakin k’ofar shigowa parlourn.

Suna had’a idanun da ita sai ya ce

“Assalamu alaikum”

Mummy ce kawai ta amsa masa sallamar tasa.Teemah kam kyautar harara ta bashi,amma sai yayi kamar bai gani ba,hakan yabata damar cigaba ta hararsa har ya iso gefensu ya zauna.

Gaida mummy uayi bayan ya zauna,daganan suka cigaba da hirarsu da mummy babu wanda yasake bi takanta.

Haushi kamar ta sa hannu ta buge sa,abinda ya zaunar da ita ma jin da tayi suna hirar su Hannah ne lil sister d’inshi,da badan hakan bama da tuni tabar inda suke d’in,

Ji tayi hirar tafar dawowa kanta,abin sai yafara bata haushi,wai ita ai ta tsaya canje canjen makaranta ne shiyasa har yanzu bata yi nisa ba ga Hannah nan tana SS2 yanzu,mummy ne tafad’i hakan jin datayi cewa wai Hannah na SS2 daga bakin bakin Abbas.
sannan tak’ara da fad’in ai Daddyn naku ne ma dayake biye ta wlh duk laifinsa nake gani”

Ga dukkan alamu dai wannan abin ya sosa ran mummy,

dayake daman tun sanda sukeyin abin tana tsananin jin haushi,ganin cewa duk makarantar da aka kaita sai tace wai bai mata ba,ba taso,daddy kuwa yabiye mata ya canja mata wani da kyar akasamu ta zauna awannan d’in da ke yanzun,kusan makarantu hud’u tacanja.

Teemah najin haka ta mike ta fice daga d’akin afusace.

Dan tasan anta6o mummy kenan indai akan makarantar tace.

Binta suka yi da kallo dukkansu kowa da abinda ke ransa har ta 6acewa ganinsu.sannan suka ci gaba hirarsu.

Ita kuwa tana shiga d’akin ta fincike hijab d’in da ke kanta tare da rigar sanna ta cire wandon ma duk ta watsar dasu,sai kace sune sukayi mata laifin.Zama tayi abakin gadonta daga ita sai pant da bra ranta amatuk’ar 6ace,asama take jin ran nata,”wai wannan shine yah Abbas d’ina kuwa anyah? +

“Ayanda mummy take fad’a min ai yah Abbas baya min mugunta,amma shi wannan daga zuwansa gidanmu har ya iyah bayyana nashi salon muguntar,kamar fah yasan abinda nafi tsana kenan arayuwa ta wannan jan kunnan,don ko mummy duk ranar da ta min ma wuni nake bana kulata,shiyasa ma ban fiyah yin abinda nasan zai sa ta min irin hakan ba,sosai nake kiyayewa,Ai kuwa da daddy zan had’a shi ya ramamin abuna.

Murmushi ne ya kwace mata dalilin tunowa datayi da sanda daddy ke jan kunnansa,

“Allah shi kara”

Tace afili.harda cije bakinta irin na muguntan nan.

Daga nan ta ta shi ta nemi kaya tasaka sannan ta fito tasamu Mummy da Baabah Lami a kitchen ko kulasu ba tayi ba,ita adole fishi take yi an mata ba daidai ba,mummy ma ko inda take bata kallah ba,Sai Baabah Lami ce ma tayi mata magana,ita ma maganar tata k’ara 6ata ran Teemahn yayi, dan cemata tayi

“Fatun daddy ya akayi ne naga kinata shan k’anshi haka?

Bata kulata ba sai baki data k’ara turowa,dan ta tsani wannan sunan wai

“Fatu,”

Fuuu……ta juya tafice daga kitchen d’in aikin da batayi ba kenan,daman mummy ce tace matuk’ar tana gida lokacin yin girki yayi toh dole ne tashiga kitchen d’in ayi da itah,shiyasa yanzun ma ta zo,toh amma tun kan ma takama aikin Baabah Lami ta kunnata dayake daman a 90 take,kuma dama tun asali ta tsani “fatun” nan, abakin Baabah Lami kad’ai tafara jinsa

kuma suna yawan shan rigima da baabah Lami d’in akan sunan,kwanaki harta da’n daina fad’ar sunan sai gashi kuma shi yau kuma ta tuno dashi,kawai sai ta fake da hakan k’ara gaba abinta,dama ba son yin girkin takeyi ba tsoron mummy yasa tafito.

Murmushi mummyn tayiwa Baabah Lami tana kallon fuskar ta tace “kin k’ara rura mana wutar kuma ai inaga”

“Aikuwa dai,naga alama”cewar Baabah Lami d’in tana d’an dariyah.

Mummyn ce ta k’ara da cewa “fushi takeyi wai yanzun da yayanta,amma inaga abin kowa ma bai tsirah ba.”

Murmushi sukayi dukkan su,daga nan suka ci gaba da sabgoginsu akitchen d’in suna yi suna d’an ta6a hira jifa-jifa.

Basu k’ara had’uwa ba sai bayan isha’i,dasuka zo cin abincin dare,Nan ma mummy tace taje maza tak’ira shi.

Tana jin abinda mummy tafa’da ta fara bubbuga k’afafu ak’asa,tana fad’in “haba mummy shi wai bazai zo da kansa ba sai ank’irasa”?

Tsawa mummy ta daka mata “bana son rashin kunyah Teemah,aiken nawa ne bazaki ba ko kuwa shid’inne kika fi k’arfin ki k’irashi”

Tana jin haka ta juya ta fara tafiyah zuwa d’akin nasa,

“mthww” mummy taja tsaki biyan tajuya d’in, ita kuwa haushi kamar ya kasheta sai mita takeyi k’asa-k’asa ahankali “wlh mummy duk so take yi ta zubar min da ajina agun wannan mutumin😅,so take ya raina ni gaba d’aya.(kujimin yarinya fah🤔😏)

Bakinta kuwa kamar na 6era tsabar yanda ta turo shi gaba.

Duk da ran mummy a6ace yake,amma bata kasa fahimtar yanayin Teemahn ba,kuma duk tasan bazai wuce akan abinda yafaru d’azun bane,take wannan abun.Haka taje k’ofar d’akin ta tsaya daga waje tana knock in d’in k’ofar,jitayi babu wanda yace mata ko cikanki ne,sake bugawa tayi da ‘dan k’arfi,amma still shiru taji, babu alamun ma anjita.

Hakan yasa ta tura k’ofar azuciye,tashiga cika batare ma da sallama ba.

Gani tayi yanzun d’akin da haske ba kamar d’azu da ta zo ba.

Ta6e baki tayi tare da rarraba idanu ad’akin dan bata ga alamar mutun ba aciki.Komai nakin tsaf dashi tagani,babu gurin data isa ta kushe ad’akin,sai uban k’anshin turarensa mai dad’in shak’a.

Ita kuwa dan iskanci sai ta d’aga hannunta ta toshe hancinta da su,harda ta6a fuska,adole wai turaren bai mata ba ita.

Dai dai shima yabud’e k’ofar d’akin ya shigo,ga mamkinsa sai yaga tana toshe hanci,k’arasa shigowa yayi a mamakance idonsa na kanta,so yake yaji menene dalilinta na toshe hanci a muhallinsa,tunda yasan bai bar komai ad’akin da zai sa har aji wani abu makamancin wari ba,dan ko bayin dake cikin d’akin ma atsaftace yake,ko abinci inta kama sai ka iyah ci aciki,balle ma shi bayaga wanka babu abinda ya had’a sa da bayin tunda yazo gidan sai ko alwala.

Bin d’akin ya sakeyi da kallo akaro na biyu sannan ya kalleta, wuri-wuri tana rarraba idanu,taku yad’anyi kad’an zuwa inda take,tana ganin haka tayi baya itama da sauri,ganin haka sai ya tsaya a inda yake d’in.

“Wani isakanci ne yasaki toshemin hanci ad’aki?”

Dan sosai abin yaba shi haushi,ba k’aramin cin fuska bane yin hakan ga wani,babu wanda zai so ace anji wani abu da ya danganci hakan a inda yake rayuwa,balle mutun irin Abbas da tun tashinsa da tsafta aka sanshi,tun yana yaro ya tsani k’azanta…………………

“Ba tambayarki nakeyi bane”

Ya fad’a atsawace dan jin bata amsa masa tambayar farkon ba.

Muryarsa na razana ta amma,dan jikinta har rawa ya fara,amma haka ta dake ta bashi amsa da

“d’akin yana wari ne”

Ranshi a6ace yake amma baisan sanda ya zaro idanu waje ba tsabar mamaki,

“Wari kuma…….?

“Warin me toh?
Ya tambayeta.

” *Turare* “

Ta bashi amsa kanta tsaye.

Tsabar takaici kasa yin magana yayi,illah kallon daya bita dashi,amma dai yad’an ji nutsuwa datce warin turare ne,abin takaici kuma har yanzu bata bar toshe hancin ba.

Gani da yayi still tana rufe da hancin ta ai sai ya yunkura zai kamota,tana ganin ya nufota kuwa ta juya baya,dagudu tabar d’akin,cikin sa’a ma abud’e tasamu k’ofar,dan mamakinta ne yasa daya shigo ko k’ofar bai mayar ya rufeta ba,shiyasa tasamu sauk’in gudu,fit ta fice abinta batare da ta tsaya jan k’ofar ba.

Sai da ta tsaya wani lungu ta daidaita numfashinta kafin ta isa wurin mummyn,

“Mummy wai yana zuwa”

“Uhm” mummyn tace sannan ta k’ara. Da fad’in yakin da’de,

“Bansame shi ad’akin bane mummy” tafad’a kamar wata mumina, dan ji take ranta wasai yanzu dalilin wannan abin data yimasan.

Shikuwa bayan fitar ta ad’akin sai yaje ya tura k’ofar tare da fad’in “useless kawai” sanin da yayi wa kansa, k’anshi ko wari ko yaya suke kuwa sai ya jiyosu indai wad’annan abubuwan ne,bata isa ta nuna masa jinsu ba.

Dawo wa yayi cikin d’akin yatsaya ya sake k’arewa ilahirin d’akin kallo,sai kuma yayi murmushi,

“zan had’u da ke ne yarinya”
afili ya fad’i hakan sannan ya ka’rasa bakin gado ya ajiye wayarsa.

Shima ya zauna ya fara 6alle botiran rigarsa,
har ya kusan 6allewa sai kuma ya tuna k’ila aikota akayi,
tunda yanzu lokacin cin abincine agidan kamar yadda yasani tun ada,
take sai ya mik’e ya fice daga da’kin.
Ya nufi main parlour……………..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *