ABDUL-MALEEK (BOBO) COMPLETE
💖 ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce3
page 1⃣&2⃣
………..Kowa ka kalla yana harkokinsa acikin makarantar, wasu karatu sukeyi wasu kuwa hira da samarinsu ko k’awaye.
Shigowar wata bak’ar mota wulik cikin makarantar shine yaja hankalin mafi yawan d’aliban.
Safna tasaki Baki da hanci da ido itama tana kalo.
Motar tatsaya daidai wata bishiyar dalbejiya, ayanzu kallo yakomane akan Wanda zai fito daga cikin wannan mota mai k’yau da d’aukar hankali.+
K’afarsa yafara zirowa k’asa maisanye da sauciki na farin takalmi, yakuma zuro d’ayar itama, saikuma yafito gaba d’ayansa.
Ajiyar zuciya safna ta sauke tareda fad’in ya salam!.
Zeenat tad’ago tana kallonta Dan ita kokad’an batasan bikin da akeyiba, tasaka iyafis akunne tana wayane.
Safna wai lfy mikike kallone haka kamar wata sakara?.
Safna da bakinta yaymata nauyi takasa cewa uffan, tad’aga hannu dak’yar tanuna mata matashin saurayin dake tsaye, Wanda ak’alla zaikai shekara 33 aduniya.
Masha ALLAHU zeenat tafad’a itama tana mik’ewa tsaye.
Farine sosai dogo kuma dankuwa yanada tsayi sosai, kallo d’aya zaka masa kagane k’ak’k’arfane saidai bashida k’iba, masha ALLAHU akwai k’yawun fuska, gashi kuma ya k’awata fuskar tasa da saje bak’i sid’ik, yakwanta sai wlk’iya yakeyi, sanyake da farar shadda wando da Riga d’inkin zamani, kayan sun masa k’yau….
Tunaninsu yatsaya lokacin dasukaga ya sunkuya yafiddo wata yarinya mai tsananin kama dashi, “bazata wuce shekara 6 ba aduniya.
Sanye take da doguwar riga ja iya kwaurinta Dan batakai k’asaba, ank’awata adon rigar da fararen filawoyi, kanta kam kalbace irin mai nannad’ewarnan kamar igiya (twisting), yasha ribom ja da fari, sai lilo sukeyi.
Ta rik’e d’an k’ugunta da hannu biyu tana kallon saurayin, baby inanenan mukazo?, tafad’a tana bin ko ina da kallo.
Murmushi yay mata Wanda yazauta dayawan ‘yammatan gurin, musammamma safna, shima yarik’e k’ugunsa baby nan makarantace, munzo wajen uncle Hamza ne.
Lah baby dama uncle Hamza baigama makarantaba har yanzu?, yafayi babba sosai?.
🤦🏻♂kansa yadafe ya ce, “o,o me baby, kefa magana bata k’are miki, kinga muje ciki saiki tambayesa.
‘Yar dariya tayi tareda kama hannunsa suka nufi office d’in uncle Hamza, Wanda yakasance lecturer a makarantar.
Cikin farinciki uncle Hamza yamik’e cike da murmushi yana fad’i oyoyo Nawal d’ina.
Itama sakin hannunsa tayi taje da gudu tashige jikin uncle Hamza, yarungumeta yana juyi da ita suna dariya.
Shikam yajingina da k’ofa yana musu murmushi, uncle Hamza ya ajiye Nawal suna sauke numfashi da dariya.
Sai sannan ya kalli saurayin, cikin zolaya ya ce, “oyoyo my Bobo!.
Shima hararsa yayi cikin wasa, kace hakafa yanzu, bayan baka kulaniba tun d’azu sai baby.
Hhhhhh afuwa kasan nida Nawal ba’a shiga tsakani, daga ina haka?.
Bobo yayi murmushi yana sauke numfashi, wlhy daga gidansu Ni’ima muke kasan mama babu lfy shine nace bari mubiyo mugaisheka.
Kai amma naji dad’i wlhy sosai, amma yajikin mama?, da sauk’ika gsky.
To ALLAH yak’ara sauk’i, nima anjima nashiga nak’ara dubata.
Okey ALLAH yakaimu.
Surutu Nawal takema uncle Hamza babu ko k’ak’k’autawa, shikam sai dariya yakeyi.
Bobo kam yamaida hankalinsa akan latsa wayarsa.
Aka kwankwasa k’ofar.
Uncle hamza ya ce, ” ashigo.”
Safna ce da zeenat k’awarta, risinawa sukai suna gaishesu, idon safna nakan bobo.
Uncle Hamzane kawai ya amsa, amma Bobo ko d’agowa baiyibama.
Safna incedai lfy?, uncle Hamza yatambaya yana kallonsu.
Zeenat ta zunguri safna dake kallon Bobo babuko k’yafta ido.
Uncle Hamza yana kallonsu, Dan haka ya girgiza kai.
Ina saurarenku yak’ara fad’a idonsa akansu.
Um….um sir dama….. Saikuma tayi shiru tana satar kallon bobo.
Bobo yad’ago yad’an kallesu fisha saikuma yamik’e, Ya Hamza bari muwuce mubarka da d’alibanka.
Baby oya tashi muje.
“Kai bobo da wuri haka?, cewar uncle Hamza yana kallonsa.
Karka damu gobe idan ALLAH yakaimu zanshigo na gaida aunty Ruky, baby taso mana.
Nawal ta mak’ale kafad’a zatayi kuka, a’a nidai zan zauna wajen uncle Hamza.
Harararta yayi baby banason rigimar banza fa kinsani, idan nabarki da aikinsa zaiji kokuwa da shegen surutunki magananniya.
Dariya uncle Hamza yayi, yashafa kumatun Nawal, kinga my durling kibisa kuje, idan natashi aiki, zanzo gidan Ammi na d’aukeki nakaiki wajen ya Ahmad ko?.
Da sauri ta d’aga kai tana ‘Yar dariya, by by uncle.
By my Nawal.
Hannu bobo yabashi sukayi musabaha yafita rik’e da hannun Nawal.
Duk abinnan yana faruwane agaban su Safna.
Safna tabisu da kallo kamar ta had’iyeshi.
Murmushi uncle Hamza yayi, Dan yasan K’anin nasa yayi sata batareda yasaniba.
Ina jinku yafad’a yana maids hankalinsa kansu………..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 3
……..cikin in ina safna ta ce, “sir dama akan test d’in dakayi jiyane, wlhy banida lfy shiyyasa banshigo school ba.
d’an murmushi yayi kawai, yasan bayau yafara lecture safna bata nanba, amma bata ta6a neman afuwaba sai yau.
Ita kullum kanta Asama yake, tana gani tafi kowa, yasan yauma akwai abinda yakawota, bai wuce ganin bobo ba datayiba, Dan kallon datake masa kawai ya fallasa asirin zuciyarta.
Ajiyar zuciya yasauke tareda fad’in babu damuwa safna zan duba.
Godiya suka masa suka fice.
Binsu yayi da kallo yana girgiza kai, afili ya ce, ” lallai safna kinada aiki, bakisan waye Abdulmalik bobo ba.+
*_Wacece safna?._*
Alh Bilal mai Gold, shine sunan mahaifinta, cikakken bakano d’an asali, d’an kasuwane babba Wanda yake juya Gold yazama Naira.
Matarsa d’aya Haj Sa’adatu, suna kiranta (Ummi).
Yaransu hud’u mata biyu maza biyu.
Shaheed shine babba, yayi aure harda yara biyu, sai Muneer shima yayi aure, matarsa tanada tsohon ciki yanzu, sai Safna tana karatu yanzu, saikuma auta Rahma, bana ta kammala Secondary.
Yaran ‘yan gatane sosai, saidai wannan baihanasu samun tarbiyyaba, iyayensu suna kula dasu sosai.
Saidai Safna batajin magana ko kad’an.
Wannan kenan.
++++++++++++
Suna fitowa daga office d’in zeenat taja tsaki, kai Safna ALLAH yau kinbani haushi, wai ina ajin nakine?, haba Dan ALLAH, jibafa kigani sabida wulak’anci kod’agowa yakallemu baiyiba yanata latsa waya, daga k’arshema saiyayi tafiyarsa…….
Kinga zeenat ya isheni haka, idanfa bazaki taimakamin nakai ga nasaraba tofa sauraramin, ninagani na ce, “inaso, angaya miki shi sakaran namijine da 1 time zai dubemu, ashema babu aji taredashi.
Mtsooow zeenat taja tsaki, aii idanshi ya iya rik’e NASA ajin, kekam naki yana hanyar zubewa.
Tana gama fad’a tayi gaba abinta.
Itama Safna abin yabata haushi, danhaka tashige motarta tayi gida
+++++++++
Bobo kam gida yanufa abinsa, yana tsaida motar Nawal tafita da gudu zuwa cikin gida, kansa yagirgiza yana fad’in ALLAH ya shiryeki baby.
(nace amin).
Bayan yakashe motar yakwashi wayoyinsa shima yay ciki.
Ammi dake zaune Nawal nakusada ita ta kwa6e fuska zatayi kuka, ta amsama bobo sallamarsa.
Yak’araso cikin falon yana kallon Nawal, kekuma lfy daga dawowarmu?.
Ammi tasauke ajiyar zuciya ta ce, ” maganar kullumce dai takawo rigimar.
Shiru yayi baice komaiba.
Ammi takalli Nawal dahar tafara hawaye ta ce, “haba tagidan Appa kiyi hak’uri insha ALLAHU kinkusa ganin momynki kinji.
Da sauri bobo yad’ago yana kallon ammi, k’irjinsa sai harbawa yake da k’arfi, yakasa cewa komai.
Ammi takauda kai, ranta a6ace ta ce, ” nagaji da ganin kukan yarinyarnan wlhy, amma babu komai bari Appanku yadawo, zand’auki mataki.
Hannun Nawal takama suka haura sama.
Bobo tamkar zai fasa ihu haka yakeji, yarintse idanu zuciyarsa na zafi, afili ya ce, “baby miyasa kikeson sakani a matsalane?.
Ganin babu maibashi amsa yamik’e yanufi d’akinsa.
*_Wanene Bobo_*
Abdulmalik d’ane ga Alh Aliyu Abdulmalik Hamshak’i.
d’an siyasa sananne wad’anda suke gwagwar Maya da ilimi dakuma nemawa talakawa ‘yancinsu, matarsa d’aya Haj. Zahura (Ammi).
Yaransu shidda maza hud’u mata biyu.
Is’haq shine babba, yanada mata d’aya da yara hud’u, sai Sulaiman, shima yaransa uku da mata d’aya, sai Hamza matarsa d’aya shima da yara biyu, sai Abdulmalik (matarsa ta rasu) yarinyarsa d’aya, sai ‘yan biyu duk mata basuyi aureba.
ALLAH ya azurta Alh Aliyu Hamshak’i da yara maza masu kwazo da himma, yaa is’haq ma’aikacine na banki, yaa Sulaiman kuwa likitane, sai yaa hamza lecture, sai Abdulmalik (bobo) cikakken lauya mai zaman kansa.
Kansu ahad’e yake, idan kagansu saika d’auka abokaine musamman ma yaa hamza da Abdulmalik, komai zasuyi saida shawarar junansu.
*_Abdulmalik_*
Mutumne mai zafi da sauk’i, gaba d’aya ‘yan uwansa yafisu fad’a, saidai zasuzo daidai da ya is’haq (Dan shima mafad’acine).
Abdulmalik mutumne dabayason raini ko kad’an, baya wasa da mutane, baizama dolema kuzauna har kurabu kaga dariyarsaba, kullum cikin d’aurewa yake, amma yanada son jama’a sosai.
Abdulmalik bobo, yasamo sunan bobone tun yana k’arami, kasancewarsa mayen shan Bobo sai ‘yan uwansa suke kiransa da bobo, ahankali sunan yay tasiri kowa Yakoma cemasa bobo, bayan ya girma saiya zama bobo na gsky saboda gayunsa ga k’yau ga kud’i ga ilimi, komaidai zam zam.
Bayan ya kammala karatunsa yafara aiki iyayesu sukace saura aure.
Yay tsalle yadire bashida budurwa, wannan yasa Appa yanema masa auren d’iyar k’anwar Ammi mai suna Ni’ima.
Da farko baya sonta ko kad’an, amma k’yawawan hali irin na Ni’ima yajanye hankalinsa harya tsunduma a k’aunarta.
Shekararsu biyu da aure ta haihu mace, wadda taci sunan Ammi, suna kiranta Nawal, shekarar Nawal d’aya Ni’ima takuma samun ciki, amma wajen haihuwa ALLAH yay mata rasuwa itada abinda ke cikinta.
Bobo yashiga rud’ani Dan saida aka had’a da addu’a sannan yadawo daidai.
Tundaga nan baisake kallon wata mace da sunan so ba, damashi matan bawani damunsa sukaiba.
Bobo yanada k’yau daidai gwargwado, gashi d’an gayu, akwai tsafta da iya d’aukar wanka, dolene mace mai lfy taga bobo ta k’yasa, kullum cikin k’amshi yake.
Shiyyasa Madeena ta k’yasa.
(To aunty bily dai ta ce, “ki kama kanki Dan bama kulaki zaiyiba, danshi aharkar mata ba gwani bane😜).
Shekarar Ni’ima 5 kenan da rasuwa amma bobo yak’i k’ara aure, iyayen sunata fama dashi amma yak’i sunata fama saidai yace zaiyi amma yak’iyi.
Kullum zancen Nawal akaita gurin momynta, haka take damunsu Ammi da Appa hardashi dadyn Nata, itadai tanaso taga momynta, kullum zancen kenan.
Abin yana damun yayyensa da iyayensa, shikam ko’a kwalar rigarsa, harkar gabansa kawai yakeyi.
Wannan kenan.
Mundawo labari💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 4
…….Safna tadanna hon afusace, da sauri maigadinsu yazo yabud’e mata get, ta danna hancin motarta cikin gidan, tana kashe motar tasuri jakarta da wayoyinta zuwa cikin gida.
Wani wawan tsaki tasaki Dan ganin Rahma k’anwarsu kwance akan cinyar ummi.
Daga Ummi har Rahma baki suka saki suna kallonta.
Ummi ta ce, “kekuma lfy daga shigiwa zakiyi mana tsaki?, wai Safna ban hanaki halinnanba ne?.
Baki ta turo gaba tana Harar Rahma, haba Ummi ALLAH wannan abun kunyane, wannan k’atuwar yarinyar shrkara 17 haryanzu bataida halin yaraba, aiiko jafar d’in ya Shaheed baya wannan ta6arar.
Rahma ta girgiza kai danjin akanta yayar tata take tada jijiyar wuya, tarasa miyasa basa shan inuwa d’aya da ‘Yar uwarta, (ita aganinta abin yafara wuce fad’an sako da sako), afili kuma sai ta ce, ” aunty Safna miyayi zafi shiba wutaba, zauna ki huta Dan ALLAH…….
Duka takaima Rahma ummi ta kare, Safna kishiga hankalinki danifa, uwarmi tamiki daga shigowa?.
Cikin huci ta ce, “ummi kinajinfa maganar datake fad’amin, ALLAH yarinyarnan ta rainani, zan koya miki hankali kwanannan wlhy.
Ummi ta tamke fuska tana nunama safna hanya, kinga tashimin anan.
Ran safna a6ace tabar wajen tanufi d’akinsu tana mita.
Rahma kam ta sauke ajiyar zuciya tana k’ara gyara kwanciyarta.
Ummi ma kai ta girgiza ALLAH ya shiryaki Safna tafad’a tana shafa kan Rahma.+
Safna tacire kayanta tanata masifa harta shiga wanka, (nikam mamaki take bani, Dan banga abin fad’aba anan).
Rahma tanason shiga d’akinsu tayi wanka tana tsoron masifar Safna, Dan tasan wlhy bata bartaba, k’ilama yau kwana zatayi bala inta da mitar tsiyarta.
d’akin umminsu tanufa dantayi wankanta kawai, yafi sauk’i.
+++++++++++++++
Bobo yana kwance ad’akinsa sai juye2 yakeyi, barci yakesonyi amma yak’i d’aukarsa, maganar Ammi ce kemasa yawo akwakwalwa.
Yasan Ammi sairai babu sauk’ice, indai Abu ya6ata mata rai saita d’auki mataki, shikam yana tsoron zancennan yaje kunnen Appansu, yad’an cije le6e yana sauke numfashi, tund’azu soyake yafita amma yana shakkar had’uwa da Appa.
Yasan fita tazame masa tilas Dan dole zasu had’u wajen cin abinci…….
Bai rufe bakiba aka buga k’ofar, batarda ya d’agoba ya ce, “ashigo.
Khairiyyace k’anwarsa, cikeda da tsoro ta ce, ” yaya kazo wai aci abinci.
Hannu yad’aga mata kawai, bata gane nufinsaba Dan haka ta ce, “ka k’oshi kuma yaa Bobo!?.
Harara ya watso mata sannan yamik’e, da sauri tayi waje, shikuma yad’auki doguwar riga fara yazura yafito.
Kowa ya hallara shikad’ai ake jira, rissinawa yayi yagaida Appa da Ammi sannan yazauna.
Khursiyya ta ce, ” yaya ina yini, harara ya watsa mata, ya ce, “k d’azu dasafe miya hanaki wankemin bayi?.
Kanta ak’asa ta ce, ” wlhy yaya ina uzirin makarantane, dakuma nadawo na manta.
Tsaki yaja kawai baisake cewa komaiva.
Ammi tazubama Appa abinci, tasakama kanta, kairiyya kuma tasakama bobo shima, suma suka zuba.
Nawal tana kusada Appa.
Suna cikin cin abinci kamar antsikari Nawal ta ce, “aunty khursiyya.
Na’am Nawal miya faru?, khursiyya ta fad’a.
Cike da murna ta ce, ” Ammi tace nima ankusa kawomin momyna.
Ayya my dear natayaki murna.
Ran bobo yak’ara 6aci, fuska ad’aure ya gallama Nawal harara, Appa da Ammi suna kallonsa, amma basuce komaiba.
Itama Nawal saitayi shiru kafin ya bibbigeta, Dan dukda yana wasa da ita hakan bai hana yaci k’aniyartaba idan ta k’uleshi.
Harsuka kammala cin abinci babu Wanda yakuma cewa komai, bayan sun kammala kowa yakama gabansa.
Bobo yaji dad’i Affa baimasa maganaba har dare.
Da daddare yana zaune a babban falo daga can gefe, wasu buks yake dubawa, khairiyya da khursiyya da Nawal suna zaune suma kallo sukeyi, Ammi tasakko daga d’akin Appa, takkali Bobo da hankalinsa kekan bincike ta ce, “Mukarram kaje Appanku na kiranka.
Wani irin fad’uwar gaba da tsinkewar zuciya suka sameshi a lokaci d’aya, bakinsa yana rawa yace Ammi lfy kuwa?.
Babu komai mikake tunani?.
” kai ya girgiza mata yana sauke ajiyar zuciya.”
Asanyaye ya haura saman Appa, Appa nazaune yana kallon labarai Bobo yashiga da sallama.
Fuska asake Appa ya amsa, bayan yazauna ya ce, “Appa gani.
Appa dattijo mai hikima da iya kama mutum, saiyayi murmushi, dama bawani Abu bane, inasonjin ya shari’arku da B.. Sadiq?.
Ajiyar zuciya bobo yasauke wadda hartaso bama Appa dariya amma saiya dake.
Komai yayi Normal Appa, Dan insha ALLAHU zuwa Monday komai zai k’are, alk’ali zai yanke hukunci.
A to Alhmdllh haka nakesonji, daga nan Appa yacigaba dajansa da hira harya saki jikinsa.
Cikin hikima Appa ya ce, “Mukarram waini yamaganar aurene?, kodai haryanzu?.
Bobo yad’an Sosa gefen wuyansa Appa Dan ALLAH kudaina yawan damuwa akan aurena insha ALLAH zanyi amma ba yanzuba.
Tofa, bayanzuba sai yaushe Mukarram?, koso kake saika tsufa agidane?, ai ko bakayi aure Dan kankaba kayi Dan Zuhra, kullum maganar yarinyar nan momy momy to yakamata asamo mata momyn nan.
Inkuma bazaka iyaba ba awannan karonma zan samo maka matar aure, Dan naga kai tsoron matan kakeji.
Appa kayi hak’uri, ak’aramin lokaci, insha ALLAHU nanda k’arshen shekara zanyi.
Appa yad’an zaro ido, Mukarram karshen shekarafa kace?, kai kana ganin zamu iya barinka harnan da watanni Tara babu aure, nifa nagaji da ganinka hakanan gsky.
Ammi tashigo hannunta d’auke da tire, yaa is’haq yana biye da ita.
Appa ya ce, “yauwa aii gara dakukazo.
To miya faru Alhaji?.
A’a wai Murarram nakeyima zancen sure, shine yake rik’ona abarsa sai k’arshen shekara.
K’arshen shekara kuma ya ishaq yafad’a yana kallon Bobo dayake wani 6ata rai. Kai idan anbarka zuwa k’arshen shekarar saika yarda?.
” emana yaya aii nake ganin zaifi ko?.
shin wai Abdulmalik kodai bakada lfy ne?.
Yaya banida lfy kuma kamar ya?.
Harararsa ya ishaq yayi ya ce, ” bansaniba.
Appa ya k’atsemusu zancen dafad’in Ishaq babu wani abinda ke damunsa iya shegene kawai irin nasa. Amma nima abin yana bani mamaki wlhy, hakamafa lokacin aurensa na farko mukaita fama, kokuwa maganar ishaq gsky ce?.
Ran Bobo yakuma 6aci, aii dama yasan tunda wannan masifaffen yazo saidai ALLAH, gashinan yak’arama wutar fetir…….
Appa yakatsema Bobo tunani da fad’in Mukarram baka jinane?.
Kansa ya girgiza, murya a sark’e ya ce, “wlhy Appa lfy ta k’alau.
Appa ya kalli ammi, kai ammi ta girgizama Appa kawai.
Appa yayi murmushi, ya ce, ” shikenan Mukarram tashi kaje, ALLAH yakaimu k’arshen shekarar.
Yakwa mik’e yana washe baki yafice, azuciyarsa ya ce, “su yaa Ishaq ansamu game over.
(Nikam dariya yabani, Dan k’ila shine mai game over d’in).
Ammi ta ce, ” Alhaji nifa ban fahimcekaba?.
Appa yay murmushi, yanzu zan fahimtar daku, shekaran jiya naje mun gaisa da abokina Alh bilal, anan nakemasa maganar ranshin auren Mukarram abin yana damuna.
To yanzudai azancen nan danake muku munyanke hukuncin had’a auren mukarram da ‘Yar wajensa.
Ammi tayi murmushi tana fad’in Alhmdllh, kai nayi farinciki wlhy, ALLAH ya tabbatar da alkairi.
Amin ya ishaq yafad’a shima fuskarsa cike da annuri.
Ya gaida Appa Dan ko gaisawa basuyiba ma, daganan suka tattauna akan bikin, ya Ishaq yatafi………..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 5
washe gari_
Da wuri Bobo yatashi yay shirin zuwa wani bincike akan shira dazaiyi.
Fes yakejinsa akan maganar dasukayi jiya da su Appa.
Yafito sanye cikin shadda ruwan k’asa d’inkin boda, kayan sunmasa k’yau sosai, sai tashin k’amshi yakeyi, wayoyinsa yad’iba da jakar aikinsa.
Babu kowa afalon ya kalli bak’in agogon fata dake d’aure a tsintsiyar hannunsa 7:23am, yasan yanzu babu Wanda yatashi, Dan al’adar gidance indai sukayi sallar asuba sukoma barci, ficewarsa yayi saboda yanada uzuri.
Yabude d’ayan gefen motarsa yazuba kayan hannunsa sanan yazagaya yashiga ya zauna.
Saida yatsaya suka gaisa da maigadi sannan yafice, anguwar shiru babu hayaniya saidai iskar Safiya dake kad’awa, gakuma rana tad’an hasko maibada d’umi mai dad’i, cikin nutsuwa yake juya sitiyarin tamkar bayaso, yafito daga layin gidansu yahau babban titi, tafiya kad’an yayi saiya hangi taron jama’a a tsaitsaye agefen titi, wasuma daka gansu suna cikin rud’ani, harya wuce saiya dawo baya yanemi guri yay fakin.
Fitowa yayi daga motar yanufi wajen taron jama’a.
Malam lfy kuwa?, yatambayi wani matashin saurayi daketa zage2.
Saurayin ya balla masa harara, kacemin lfy kuwa, aii dama duk irinkune, kud’i sunsaku bakwa tsoron ALLAH, gani kuke komai kukayi kunada kud’i zasu kareku…….. Hannu Bobo yad’aga masa, kaga bawannan nake tambayarkaba nikam, mike faruwa anan?.
Saurayin ya share hawayensa sannan ya ce, “wani mara imanine yayma yarinya fad’e yazo nan ya yardata.
Fad’e!!, Bobo yafad’a arazane, da sauri yafara kutsa kai cikin taron jama’ar batareda ya saurari maganar da saurayin yake masaba.
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’u yafad’a yayinda yay tozali da k’aramar yarinya kwace tamkar gawa.
Da sauri ya rarumi yarinyar batareda yakula da jinin dake zuba ajikintaba, wasu daga cikin mutanen suka fara tambayarsa koya Santa?.
Bai sauraresuba yabud’e mota yasakata abaya, harya shiga mota yakira saurayin d’azu ya ce, ” shiga muje.
Babu musu saurayin yashiga, Bobo yaja motar a 360 suka nufi asibiti.
Azuciyarsa yana Addu’a ALLAH yasa ya Sulaiman yana asibitin.
Suna Isa aka amshesu cikin gaggawa Dan ansanshi k’anine gamai asibitin.
Ma’aikatan masu gaisheshi ya tambaya ya sulaiman yazo?.
A’a baikai ga k’arasowaba wata matashiyar budurwa tafad’a cikeda sanabe.
Baibi takantaba yafara kiran ya sulaiman.
Bugu d’aya ya d’auka.
Cikin zolaya ya ce, “Bobon Ammi ya akayi?..
Muryar bobo na rawa ya ce, Yaya kana ina?.
Ina hanyar zuwa asibiti miya faru?.
Alhmddlh Bobo yafad’a, saika k’araso kawai, nima ina asibitin, baijira amsar ya sulaimanba ya yanke wayar.
Gudu ya sulaiman yak’ara danjin Bobo ya ce, ” yana asibiti.
Cikin k’an k’anin lokaci ya iso, atsorace yake kallon jikin bobo da jini ya 6ata.
Bobo daketa safa da marwa ak’ofar d’akin da aka shigar da yarinyar ya hango yaa sulaiman yashigo cikin asibitin arazane.
Cikin hanzari yatareshi, yayana Dan ALLAH ka taimaki yarinyar nan karta mutu plzzz…….
Cikin rashin fahimta ya sulaiman ya ce, “nutsu Abdulmalik miya samu Nawal d’in?.
Yaya ba Nawal bace wata yarinyace, kaje wajenta zanmaka bayani daga baya plzzz.
Ya sulaiman yasan halin bobo da rikici Dan haka da Sauri ya afka d’akin Dan ganema idonsa.
Kansa yadafe cikin tashin hankali yafara yima Nos masifa akan sunzubama yarinyar ido babu abinda sukai mata.
Kayi hak’uri sir aikin banamu bane dole saikazo, inazaton Fad’e akamata.
Ajiyar zuciya ya sauke, taimakon gaggawa yafara bama yarinyar.+
A waje kam Bobo yakasa zaune yakasa tsaye, sai kaida kawo yakeyi, hankalinsa atashe, yanzunan haka al’umma suka lalace akan zalinci?, insha ALLAHU saiya k’ar6oma yarinyar nan ‘yancinta, zaiyi bincike kod’an gidan ubanwaye saiya gurfanar dashi a gaban shari’a.
Wayarsa dake wringing ya Ciro a aljihu, Br….. Kamal yagani, yarintse idonsa Dan yamanta abinda ya fiddoshi daga gida, bai d’agaba har wayar ta yanke aka k’ara kira.
Daurewa yayi ya d’auka suka gaisa, AA Hamshak’i wai ya akayine?, kacemin kafito gida amma najika shiru.
Sorry Kamal ina nan zuwa, wlhy wani abune ya rik’rni ahanya, amma plz kabani minti talatin zuwa arba’in zan iso.
Okey saina ganka.
A can kuwa bobo nabarin wajen police suka zo, mutane suka sanar dasu wani ya d’auki yarinyar zuwa asibiti.
Wane asibin ne?, wani d’ansanda ya tambaya fuska atamke.
Muma bamu saniba wlhy, amma antafi damai shagonnan, suka nuna shagon dake kusadasu.
d’ansandan baice komaiba yashiga mota suka juya.
Gulma mutanen gurin suka fara da zagin ‘yan sandan, wai sai yanzu suka gadamar zuwa, bayan tun d’azu aka kirasu.
Wani ya ce, “bar munafukai malam aii k’asarnan munga takanmu, buharine kawai ke k’aunar talaka, (ALLAH dai ya k’ara masa lfy).
Amin ya rabbi Garzali.2
+++++++++++++
Safna tafito sanye cikin atamfa Riga da siket, sunmata d’am kamar zata fashe.
Rahma ta kalleta ta girgiza kai, wannan lamari na 6ata mata rai, ita bataga wayewaba ga mace mai saka suturar dake fidda jiki, shiyyasa fad’e yaketa k’ara yawa aduniya, to matan basusan darajar jikinsuba, (suyita fiddo jiki tamkar akuyoyi da sunan wayewa)………
Me wait lfy kike kallona?, karfa ki cinyeni wlhy.
Rahma takauda kai saga kallonta, ta ce, ” aikinsan Nina mayya bace.
Da sauri safna takai mata duka, to ubanwaye mayen?.
Rahma ta kauce tana dariya, maida wuk’ar ta hannun damar Abba, Dan ALLAH zanbiki makarantar wlhy zaman gidannan ya isheni.
Safna ta harareta tozoki hau kaina uwata.
A’a ALLAH yabaki hak’uri, yi tafiyarki zanje gidan yaa Munir nama taya aunty Naja’atu aiki.
Yafimiki sauk’i, dama da ‘yan aiki kike kama aii, safna tafad’a tana ficewa.
Baki Rahma ta ta6e tareda Jan tsaki.
Ummi tafito tana fad’in kekuma lfy?.
Lfy lay ummi nida aunty Safna ne.
Ina Safna d’in?.
Tafita makaranta.
Shine yau ko sallama babu?, dariya Rahma tayi ta ce, “haryanzu aljanun masifar nasu saukaba.
Ummi batace komaiba tashige kicin.
+++++++++++++
Asibiti kam lamura saidai addu’a bak’aramar mugunta akaima yarinyarba, amma cikin ikon ALLAH yaa sulaiman yayi nasarar ceto ranta.
Bak’aramin lokaci ya6ataba kafin yafito, zuwa yanzu bobo na tsaye jingine da bango ya hard’e hannuwansa biyu ak’irji, k’afarsa d’aya dogare a bango fuskarnan d’aure tamau.
Ya sulaima yafito yana shere zufa, da sauri Bobo ya taresa, Yaya ya jikin nata??.
Alhmdllh. ya sulaiman yafad’a, yaja hannun Bobo suka shiga office d’insa.
Koda ya zaunar dashi saiya bude firij yad’akko fresh milk ya tsiyaya a kofi yamik’ama Bobo.
Bobo ya ce, “ya…. Hannu ya d’aga masa, kaga k’ar6a kasha kasamu nutsuwa, nasan ko karyawa bakayiba kafito.
Ajiyar zuciya Bobo yayi, yakar6i kofin yasa abaki, ahankali yakesha harya shanye tas.
Cikin zolaya ya sulaiman ya ce, ” Bobon Ammi damadai yunwa kakeji, ko a k’ara?.
Murmushi yayi batareda yace komaiba, ya girgiza kai.
Ya Sulaiman ya zauna yana dariya, saida yayi rubuce2 sannan yad’ago ya kalli k’aninnasa, Abdulmalik ina kasamo yarinyarnan?.
Ajiyar zuciya Bobo ya sauke shima yayan nasa yake kallo, ya ce, ”Yaya wlhy abakin titi….. Nandai yakwashe komai yasanar dashi.
Girgiza kai ya sulaiman yayi, ya ce, ”ALLAH ya saka mata, amma yanzu yakamata musan iyayenta kafin ad’au mataki, sannan ina yaron dakace kunzo tare?.
Yana nan awaje.
Wani Abu ya sulaiman ya danna, saiga Nos tazo, ya ce, “akwai wani saurayi anan waje shigomin dashi.
OK sir………….💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 6
Assalamu alaikum.
Wa’alaikassalam yaa sulaima da bobo suka amsama saurayin.
Gurin zama yaa sulaiman ya nuna masa, bayan ya zauna yabasa hannu sukayi musabaha.
Ya sulaiman ya ce, “d’an uwa ance awajenku aka samu yarinyarnan ko?..
Eh anan akazo aka yardata wajen misalin k’arfe 6:44am, fitowa ta kenan zan bud’e shagona naga wata jar mota ta tsaya agurin, nasan su basu ganniba nida abokina Nura, Dan saida suka wawwaiga sukaga babu mai kallonsu sannan aka turota waje.
Bobo ya cije le6ensa zuciyarsa na k’ara zafi.
Ya sulaiman ya jinjina kai, Yakuma fad’in to kunsanar da police?.
Eh suna barin wajen muka kira ‘yan sanda, amma har bawan ALLAH nan yazo ya d’auketa basu zoba.
Ya sulaiman ya sauke numfashi, babu damuwa ayanzu nasanar da wani d’an sanda dan kes d’in dolene police sushiga, namata abinda duk yadace, kuma narubuta bayanai akan komai…….
Kwankwasa k’ofarne yahana yaa sulaiman cigaba da magana, wata nos tashigo tana sanar dashi wani police nason ganinsa.
Shigo dashi mana ya sulaiman yafad’a.
Bayan d’an sandan yashigo shida wani suka gaisa dasu bobo sannan sukayi musu bayani akan komai.
Har d’akin da yarinyar take aka kaisu, bobo tamkar yay kuka danganin yarinyar, shidama haka yake da tausayi dukda kasancewarsa masifaffe.
Bayan sun kammala komai ‘yan sandan suka tafi, shima saurayinnan yatafi akan zasu sake nemansa.
Ya ce, “insha ALLAHU duk sanda sukazo zai basu had’in kai.
Godiya sukai masa yatafi, bobo yay masa alkairi.+
Ya sulaiman ya kalli bobo, Abdulmalik kaima yakamata katafi gida ka canja kayannan duk sun 6aci da jini.
Sai asannan yakula, yad’anyi tsaki wlhy yaya bamma kulaba, bari naje wajen Br kamal Dan yana jirana, idan muka gama saina koma gidan.
Dadai kafara zuwa ka canja kayan tukunna.
To yaya bari naje, saina dawo.
Okey saika dawo.
Saida sukad’an rungume juna sannan sukai musabaha yatafi.
+++++++++++++++++
Rahma tafito sanye cikin dogon hijjab har k’asa yake ja, hijjabin mai hannune Dan haka hannunta rik’e da fos, sallama tayima ummi sannan tafito.
Ta wawwaiga bataga idiris diraiba ba, d’an tsaki taja ta k’arasa wajen mai gadinsu, rissinawa tayi ta gaisheahi.
Ya amsa cike da fara’a, yana k’aunar yarinyarnan saboda hankalinta da girmama nagaba da ita, halinta ya banbanta da yayarta sosai…..
Rahma tak’atse masa tunani da fad’in baba ina Idris!.
aiko d’iyata Idris yaje gida yanzu babu dad’ewa, kinsan suna cikin tashin hankalin 6atan k’anwarsu tun jiya da yamma.
K’anwarsu kuma?, 6ata tayi?.
Wlhy kuwa haka yake gayamin d’azu, wai tunjiya bata dawoba daga aikenta.
Tofa ALLAH yabayyanata, Toni bari naje na hau adaidaita.
diyata dakanki?, toki tuk’a kanki mana.
Murmushi tayi ta ce, “A’a baba, Abba ya hanani tuk’i.”
ALLAH sarki ‘Yar albarka, aii haka akeson mutum yaringa bin maganar iyayensa, ALLAH yay miki albarka, yabaki miji nagari.
Murmushi Rahma tayi, ahankali tace ngd baba saina dawo.
To adawo lfy.
Rahma tafito daga gida, tad’an wawwaiga anguwar babu mutane sosai, sai jefi jefi, dakuma motoci dake fitowa daga gidaje inaga masu Fita aikine da kasuwa.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tafara tafiya da addu’ar ALLAH yasa tasamu adaidaita da wuri, Dan tsakaninsu da titi da nisa.
Tad’anyi tafiya kanta ak’asa, jitai ance a’a Rahma sai Ina?.
Ad’an tsorace tad’ago takalli inda aka ambaci sunan nata, tayi murmushi lah ya kamal kaine.?.
Nine Rahma ykk?.
Lfy lau yaya, lfy naganka anan?.
Wlhy lfy k’alau wani abokina nake jira, amma shiru bai zoba shine naked’an shan hantsi anan.
Ayya, yasu momy da aunty Ameera.
Lfy lay suke, bazaki Shigabane?.
A’a yaya gidan ya Muneer zanje wlhy ka gaidaminsu.
Zasuji, to amma ina direbanku kika fito ak’afa.
Hummm wlhy wani d’an uzuri yarik’eshi.
Okey, to amma ba girmanki bane.
Dariya tayi kai yaa kamal to miye girmana?.
Kafin yabata amsa wata mota ta tsaya adaidai saitinsu.
Kamal ya ce, “ga abokina nan ya iso.
Waigawa tayi takalli motar, saikuma tadawo da kallonta kan kamal, tom nikam nawuce.
Bazaki tsaya Ku gaisaba.
A’a yaya aii bai sanniba.
Bobo yafito daga motar fuskarsa babu yabo babu fallasa, yad’an kalli Rahma datazo zata gitta ta gefensa, kanta ak’asa ta gaisheshi.
Ya amsa da lfy, yana kauda Kansa daga kallonta.
Gaba tayi tana Jan tsaki, dukda bata kalleshiba abin yabata haushi, tana bak’in cikin ta gaida mutum ya ce, ” mata lfy.”
Bobo yak’arasa wajen kamal suka gaisa, sannan suka Shiga cikin gidan.
Rahma kam tana k’ara ‘Yar tafiya tasamu adaidaita tashiga.
.+.+.+.+.+.+.+.+.+.
Safna Ana makaranta, yau itace harda zuwa office d’in yaa Hamza amma ta tarar baizoba.
Basira ta kalli safna daketa jan tsaki tana kallon agogon hannunta, wai safna lfy kuwa?, naga kinsamu zuwa office d’in malam Hamza miye dalili?.
Zeenat dake zaune gefensu ta ta6e baki, kazar wahala ALLAH ya yanka mata shiyyasa tafara figa.
Kazar wahala kuma kamar ya?.
Zeenat tabama Baseera labarin abinda yafaru jiya, Dan ita batazo school ba.
Wata dariyar mugunta Baseera tasaki, o, ni Baseera wai yau Safna kece saurayi ya sacema zuciya?, lallai zanso ganin wannan guy mai suna Bobo, nasan tabbas ya amsa sunansa bobo.
Hummm kibari kawai Baseera wlhy jiya banyi barciba, mafarkinsa nayitayi, harda mafarkin munyi aure harda yara.
Dariya zeenat da Baseera suka saka harda cafkewa.
Safna ta 6ata rai tana hararsu, kuga nifa banason ciki da iskanci kunsani, zeenat damafa haushinki nakeji, Dan maganar jiya ta 6atamin rai wlhy.
Cikin dariya zeenat ta ce, “afwan Tawan, ALLAH yabaki bobo.
Amin, namasan yabani tunda har yasamun sansa azuciyata.
Zeenat tad’an ta6e baki tana fad’in garadai adogara ga ALLAH.
Baseera tai saurin kar6ewa toda dake tace ta dogara?, Safna karki damu ina bayanki d’ari bisa d’ari, kota halin k’ak’a saikin mallaki Bobo.
Safna tayi murmushi shiyyasa nakesonki k’awata ALLAH yabarmu tare ngd.
Zeenat tana jinsu bata kuma tankawaba.
+.+.+.+.+.+.+
_3:30pm_ Bobo yashiga cikin asibitin, kai tsaye office d’in ya sulaiman yanufa, suka gaisa ya tambayi yamai jiki?.
Da sauk’i Bobo, aiina zata bazaka dawoba?.
Tab yaya wlhy hankalina yana asibitin nan, yanzu haka bamu gama aikinba nabarma Br kamal nataho, yaya ta farka kuwa?.
A’a har yanzu tana barci, ana buk’atar tahuta sosai yanda zata tashi k’wak’wal warta Normal, ta wannan hanyarne kawai zamuyi saurin samun bayanai daga gareta.
Okey tom ALLAH yabata lfy.
Amin Mukarram d’in Appa, mai suna kalakala.
Dariya Bobo yayi ya ce, ”yaya aii duk kune kuka mak’ala mini.
Sukayi dariya harda tafawa kamar wasu abokai.
Sai k’arfe 5:00pm dai dai sukabar asibitin, kuma har sannan yarinyar bata farkaba, kai tsaye gida suka nufa har ya sulaiman shima zai gaidasu Ammi.
Kowaya yafito cikin motarsa suka nufi cikin gidan suna ‘yar hira.
Gaba d’aya mutanen gidan suna falon sama, Dan haka suma can suka nufa…………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 7
Da gudu Nawal ta taso ta rungume ya Sulaiman, yad’agata sama yana dariya, Nawal kin k’ara nauyifa yafad’a yana lakatar hancinta.
Ta kalli daddynta ta ce, “baby waikaji uncle yace nak’ara nauyi.
d’an hararta yayi cikin wasa, ya ce, “sai yanzu kika ganni baby.
A’a baby naganka tun d’azufa, nafara gaida uncle ne ko uncle?.
Ya Sulaiman yad’aga mata kai yana dariya, cikin falon suka k’arasa.
Bobo ya ce, “o kace yau family ya had’u?.
Ya Is’haq da ya Hamza, sukayi dariya suna mik’a musu hannu.
Khairiyya da Khursiyya ma dariyar sukeyi.
Guri suka samu suka zauna, ya Hamza ya ce, ” ashe kuna tare?.
Eh wlhy muna tare, naje Asibitinne.
Tofa miya sameka?, cewar ya Is’haq.
No bani bane wata yarinyace……
Fitowar Ammi ta k’atse masa zance, tazauna cike da farin cikin ganin manyan ‘yayan nasu.
Gaidata ya Sulaiman da bobo sukayi, fuskarta cike da fara’a ta take amsawa, tareda tambayar aikinsu dakuma iyalin ya Sulaiman.
Suna lfy wlhy Ammi.
Ammi ta kalli bobo, Mukarram yadai naganka wani iri?.
Fuska ya shagwa6e yana kallon Ammi, ALLAH Ammi nagaji over yau, kaina hard’an ciwo yakeyi.
Yanda yay maganar a shagwa6e saiya basu dariya.
Ya Is’haq ya ce, “Bobo shagwa6ar dakayi ko Nawal bata yinta.
Murmushi yayi kawai baice komaiba.
Ammi ta ce, ” kubarmin Mukarram d’ina yayi shagwa6arsa lokacinsane ko bobon Ammi?.
Nanma dariya sukayi gaba d’aya, ya harari su khairiyya dake tuntsura dariya harda rik’e ciki.
Ku yarannan nakulafa kun fara rainani?.
Ya Hamza ya ce, “to aii abin dariya kayi, saika hanasu su dara?, kawai kayi maganin abun.
Bobo ya ce, ” ta yaya kenan?.”
Kayi aure kabar musu gidan cewar ya Sulaiman.
Mik’ewa Bobo yayi danjin and’akko maganar dabayaso, kunga bari nad’an watsa ruwa nadawo.
Baridai kagudu idan angama maganar kadawo, ya Is’haq yafad’a yana dariya.
Nanma dariya kowa yasaka harda Ammi.
Shikam yay shigewarsa d’aki yana fad’in kwa gaji kubarni.
Ammi ta ce, “nidai inaga Mukarram tare yake da aljana shiyyasa baya son maganar aure.+
Ya Sulaiman ya ce, “Lah Ammi wane irin aljana kuma?, wlhy ras yake, shidai haka ALLAH yayosa bashida matsala da mace.
Hakadai kuke gani, nifa abinda na lura dashi ga Abdulmalik kawai bazai iya tunkarar mace ya ce, yana sonata bane, gani yake ajinsa zai zube kawai.
Hhhhhh wlhy hakane Hamza, Bobo dakake ji dagani akwai d’aukar kai agaban mata kai harma mazan, kamar wani jinin sarauta.
Dariya aka kumayi, Ammi ta ce, ” aii yashafi sarautar, kunfa takurama yarona gsky.
Ya Is’haq ya ce, “ALLAH ammi yaron nan yawuce yanda kike zato, amma kwanannan zamuyi maganinsa, aure zamu MASA kawai.
Dakun k’yautamin wlhy, nidai nagaji da ganin Mukarram babu mata, nasan har yanzu rashin Ni’ima na damunsa, amma idan yayi auren ALLAH yasa aka dace da matar k’warai komai zai zama tarihi.
Insha ALLAHU ammi komai yazo k’arshe karki damu…
Daga nan suka cigaba da tattaunawa, annan ma ya Sulaiman take basu labarin yarinyar da bobo yakai asibiti da safe.
Zancen ya girgizasu daganan suka Shiga tattauna matsalolin fad’e da yara k’anan suke fuskanta ak’asar nan.
+
Bobo kam yana Shiga d’aki yacire kayansa, wanka yashiga yayo, yashafa mai yazura doguwar Riga blue da dogon wando bak’i.
Falo yadawo Inda ‘yan uwansa suke akacigaba da hira da tattauna al’amuran rayuwa, ahaka har Appa yadawo.
Gaba d’aya suka mik’e cikin girmamawa sukayi MASA sannu.
Fuskar Appa cike da annuri yabi matasan samarin ‘ya’yan NASA da kallo, masha ALLAHU yaukuma gidan cike yake da basawa.
Dariya sukayi danjin furicin mahaifin nasu.
Ya ce, ” bari naje nawatsa ruwa sainazo ayi hirar dani ko?.
To Appa asakko lfy sukafad’a atare.
d’akinsa yanufa rik’e da hannun Nawal data k’ar6ar MASA jakka, dama kullum itace mai kar6a inhar tadawo school.
Hirarsu suka cigaba dayi, kiran sallah yasa suka mik’e sukayi alwala, Appa yafito ya samesu suka tafi masallaci abin gwanin sha’awa, shima Appa sai dad’i yakeji ganinsa cikin samarin ‘yayansa ababen alfaharinsa.
Ko’a masallaci sun burge mutane, Dan a sahu d’aya suka jera reras.
Agidama khairiyya da khursiyya da Nawal sallar sukayi, ammi ma haka.
Bayan an idar ammi tasakasu suka shirya abinci a tsakkiyar falon Dan yau duk su ya Is’haq anan zasuci abinci, suka gama shirya komai da taimakon ‘yan aiiki sannan suka koma d’aki domin gabatar da sallar isha’i da aka kira.
Basu dawoba saida akayi sallar isha’i, suka rankayo zuwa gida suna ‘Yar hirarsu da tsokanar juna.
Afalon suka zube Appa ya ce, ”aini zuwannan naku yamin daidai, kamar kunsan dama ina nemanku.
Ya Hamza ya ce, “to Appanmu ALLAH yajishemu alkairi.
Amin suka fad’a gaba d’aya.
Ammi dasu khairiyya suka fito suma, rissinawa sukayi suka gaida Appa da yayyensu, Nawal taje jikin Appa tazauna.
Yashafa kanta yana fad’in amaryata kinyi sallah?.
Kai ta jinjina tana dariya.
Tomi kika rok’amana?.
Hannunta tasa abaki idonta na kallon p,o,p d’in falon alamar tunani, can takalli Appa tana washe wawulinta da hak’ori biyu yafad’i, ta ce, ” Appa kasan mina rok’a?.
Saikin fad’amin amaryata.
Narok’i ALLAH ya kaimu Aljanna nida kai, da Ammi, da baby, da uncle Sulaiman, da uncle Hamza, da Uncle Is’haq, da aunty khursiyya da aunty khairiyya, da mom din gida uncle Is’haq, da momyn ya Ahmad da aunty Sameera, kuma nace ALLAH yasa muje makakka muduka sau dubu dubu babu iyaka muga kabarin Manzon ALLAH a madina.
Tafi sukai mata gaba d’aya suna fad’in ameen mai sunan manya.
Ya Is’haq dake kusada ita har sumbatar hannunta yayi.
Appa ya ce, ”lallai na more da amarya Ashe.
Ta ce, “Appa kasan mikuma na rok’a daga k’arshe?, ya girgiza kai yana murmushi, canayi ALLAH yasa nima naga momyna.
Gaba d’ayansu kallonta sukayi, tabasu tausayi sosai, Appa ya rungumeta cikeda tausayi, Bobo kam k’asa yayi da kansa zuciyarsa tayi rauni sosai, jiyake tamkar yafasa kuka saboda tausayin ‘yarsa, tausayinta yana d’aya daga cikin abinda yasa yak’i k’ara aure, bayason ya auro wadda zata takurama d’iyarsa sanyin idaniyarsa.
Ya Hamza ya ta6ashi d’agowa yayi yana kallonsa, ya Hamza ya jinjina masa kai fuskarsa d’auke da tausayi.
Murmushi bobo yayi.
Saikuma ya kalli sauran ‘yan uwannasa da iyayensa yaga dukshi suke kallo.
Kansa yamaida k’asa yana cigaba da murmushi mai ciwo.
Ganin haka Ammi ta katsesu da fad’in bismillah kusauka ga abinci.
Kowa ya sakko tskkiyar falon in da abincin yake.
Bayan Ammi tasakama Appa kowa yafa k’ok’arin zubama Kansa abinda yakeso.
Falon yayi tsit bakajin motsin komai sai k’arar filat da cokali, saikam surutun Nawal lokaci2.
Bayan sun kammala cin abincin ‘yan aiki suka gyara wajen tsaf, Appa yakalli khairiyya ya ce, “auta zoki kaita d’aki ta kwanta.
To Appa khairiyya tafad’a tana mik’ewa, d’aukar Nawal tayi daga jikin Appa tanufi d’aki.
Falon yay tsit kowa ya maida habkalinsa kan Appa.
Appa yamusu sallama suka amsa.
Ya gyara zama cikin hikimar zance yafara musu nasiha da k’ara jaddada musu muhimmancin zuminci da hak’uri da juna, ahankali ya gangaro kan auren Bobo, Wanda tunda Appa ya ambaci sunansa gabansa yafad’i.
Appa yabasu labari kamar yanda yagayama su Ammi da ya Is’haq jiya.
Ya d’ora da fad’in yanzu dai mun yanke hukunci ranar juma’a idan ALLAH ya kaimu za’a tura dakomai har sadaki Dan badogon lokaci za’a d’aukaba, k’arshen watannan za’ayi bikin kowa ya huta.
Zuface tafara fita addukan sassan jikin Bobo, yakasa koda motsi dukda tsokanarsa da ‘yan uwansa sukeyi suna fad’in ango kasha k’amshi.
Ammi ma sai dariya takeyi danjin dad’i, sai Alhmdllh take dad’i, su khursiyya kam harda ‘yar bud’a.
Bobo ya galla masu harara.
Gaba d’aya akayi dariya harda Appa.
Daganan suka cigaba da tattauna yanda biki zai gudana da shagalin daza’ayi.
Appa ya ce, ” suyi duk abinda sukeso bazai hanasuba, Dan Andad’e ba ayi wani shagaliba agidan.
Har k’arfe tara suna gidan, saida Appa yace yakamata sutafi gida hakanan wajen iyalinsu sanan suka mik’e kowa yanufi gidansa.
Bobo bayan yarakasu harabar gidan yanufi d’akinsa jikin a sanyaye, yama rasa wane irin tunani zaiyi shikam………….💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 8
_Gidansu Safna_*
Safna na kwance akan gado tana chart, sai faman murmushi takeyi, da alama tana jin dad’in charting d’in.
Rahma dake zaune akan sallaya tana karatun alkur’ani ta waigo ta kalli safna dataketa 6a66aga dariya harda rik’e ciki, kai Rahma ta girgiza tareda fad’in ALLAH ya shirya azuciyarta.
Kanta tamaida tacigaba da karatunta.
Safna kam bamatasan tanayiba, dariyarta taketayi cikin farinciki, hira takeyi da Baseera akan nemomata Bobo, Baseera tana gayamata akwai wani guy a unguwarsu sunansa *boy shiyakama subama aikin, Dan tasan cikin sauk’i zai samomusu bobo da labarinsa.
Tak’ara wani d’an ihun farinciki, tareda fad’in saini mata agidan Bobo.
Rahma takuma kallonta cike da mamaki, ganin bazata barta tayi karatunta cikin Nutsuwaba yasa tarufe alkur’anin tayi addu’oin ta tamik’e ta ajiye alkur’ani ama’ajiyarsa.
Hijjabinta tacire tana fad’in aunty Safna kofa sallar magriba bakiyiba har anyi isha’i amma kina kwance kina charting akan abinda k’ilama bazai amfaneki da komaiba.
ALLAHU Akbar maikaratu nagaba, Safna tafa idonta akan waya, tacigaba da fad’in malama Rahma jawo wata ayar na haddace wannan.
Ajiyar zuciya Rahma ta sauke, ta ce, “Niba malamarki bace, kuma ba wa’azi nake mikiba, ina tunatar dakene dannaga kin shagala.
Wani wawan dundu safna tasaukema Rahma abaya, Dan ubanki idan aljanna takice ki hanani, shegiya ‘Yar iska uwar tsari, kenikam daba agabana ummi ta haifekiba wlhy danace anmata canji a asibiti, anya kuwa acikin ‘yan barka wata bata sace ainahin d’iyar da ummi ta haifaba ta ajiye mata ke?.
Rahma tashare hawayenta ta ce, ” kije kitanbayeta k’iladai kece aka canja mata, Dan halinki daban dana mutanen gidanna.
Afusace Safna taduro daga gado tana d’urama Rahma zagi.
Tuni Rahma tafice tabar mata d’akin.
Afalo taci karo da abbansu yadawo masallaci, sannu da dawowa Abba. Yauwa d’iyar albarka ina zuwa haka?.
Ba inda zani Abba, nadai fito falone nasha iska.
Masha ALLAHU, ina ‘Yar uwar taki to?.
Tana d’aki Abba.
Yauwa jeki kiramin ita zamuyi magana, ina umminku?.
Ganinan Abba Shaheed ummi dake fitowa daga d’aki tafad’a.
Tamai sannu dazuwa sannan tafara shirya musu abinci.+
Rahma tatsaya abakin k’ofa ta ce, “aunty Safna kizo Abba yana kiranki.
Shegiya munafuka gulmata kina kaimasane?.
Niba munafuka bace, yace dai kizo…, tana gama fad’a tafice.
Safna tasakko daga gadon tana mita, zan koya miki hankaline ‘Yar banza maikan dankali.
(Araina nace kekuma maikan doya ko?.)
Kusada Abba taje tazauna, Abba gani.
Kanta yashafa yana murmushi haba safnan Abba miya faru kika k’unshe kanki a d’aki?.
Zamanta ta gyara tana ballama Rahma harara, babu komai Abba nayi sallane INA zaune ina Azkar.
Da k’yau ‘Yar albarka.
Rahma kam ido tazaro waje danjin k’aryar da safna ta gilla, saikuma ta k’unshe baki tana dariya.
Safna na kallonta, Dan haka haushi yak’ara kamata.
_(Hattara iyaye kuringa kula da addinin ‘ya’yanku, akwai yara dayawa masu wasa da salla irinsu Safna, wata zakiga tana zaune tana chart za’a kira salla, amma ko’a kwalar rigarta, har Matan aurema akwai masu halinnan, musamman yanzu da karatun Novels sukayi tasiri arayuwarmu, yakamata duk lokacin da aka Shiga sallah kiringa lek’a d’akin yaranki kitabbatar suma suyi, ALLAH yasa Mugane)._
Ummi ta ce, “kutaso ga abinci, atare suka tashi har zuwa dani, anacin abinci Safna na chart saida ummi Tamata magana sannan ta ajiyewayar tana zum6ura baki.
Bayan sun kammala Rahma takwashe kayan, takaima masu aiki su wanke.
Falon tadawo Inda iyayenta suke zaune harda safna.
K’asa ta zauna kusada Abbansu.
Zamansu babu dad’ewa ya Shaheed da ya Muneer sukayi sallam.
Cikin girmamawa suka gaida iyayensu, suma suka tambayesu ya iyalinsu?.
Kowa ya amsa da lfy k’alau.
Suma su Safna suka gaishesu.
Bayan gama gaishe2 Abba ya ce, “dama bawani abune yasa na tarakuba zancen auren safna ne yatashi.
Wata irin d’agowa Safna tayi arazane, aurena kuma Abba tafad’a da k’arfi!!!.
Suduka kallonta sukeyi, Abba ya ce, ” eh aurenki safna ta, kiyi hak’uri abin yazo miki wani iri kuma 1time, wlhy nima haka lamarin yazomin babu shiri.
Kuka safna tafasa tana fad’in itafa wlhy akwai Wanda takeso Dan haka bazata yardaba.
Ya Shaheed ya daka mata tsawa, wlhy idan bakimana shiruba jikinki zaiyi tsami, iskancim banza kawai, Abban kike fad’ama haka?.
Toni Dan ALLAH baza’a bari aji uzurinaba haka kawai amin auren dole, narantse bana sonsa karma afara wlhy.
Idan bahakaba kuma wlhy zanbar gidannan.
Duka ya Muneer yakai mata tatashi dagudu tashige d’aku tana kuka da fad’in wlhy itafa bata sonshi.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce, “akwai matsala kenan?……
Babu wata matsala Abba Shaheed ashema ita ta haifemu bamu muka haifetaba, wlhy acigaba da hidima kawai, idan ankaita ta mutu aranar, ni wlhy dama halin Safna ya isheni agidannan.
Shikenan ummin Muneer yanzu dai munyi dasu ranar juma’a zasu kawo komai, nasanar da Alhaji Rabi’u, (yayan ummi), sannan kuma suma su yaya na sanar dasu shida Abubakar.
Tom ubangiji ALLAH ya tabbatar da alkairi yasa ayi damu.
Amin Abba yafad’a, ya kalli su Muneer ya ce, ” to manyan yayye yakukace?.
Dariya sukayi, yayi daidai Abba ALLAH ya Sanya alkairi, insha ALLAHU zamu fara shirya biki.
Tattauna maganar bikin suka cigaba dayi har zuwa wani lokaci, daganan su ya Shaheed suka tafi gidajensu.
+.+.+.+.+.+.+.+.+.+.+.
A 6angaren bobo kam abubuwa biyune suka cinkushe masa tunani, ga tunanin yarinyar da akaima fad’e, gakuma tunanin zancen Appa na yau, yasan appa sarai mutumne mai sauk’i da sanyi, komai zaiyi zaiyishine cikin hikima da lallashi, to amma mutumne kaifi d’aya idan ya ve e babu maisakashi fad’in A’a, Dan duk abinda zaiyi baya yinsa da ka saiyayi bincike.
Yasan ko giyar wake yasha bai isa ya gujema Auren nan ba, to amma shikam harga ALLAH baiji zaiso wata mace bayan Ni’ima ba, duk macen datayi kuskuren shigowa rayuwarsa bazata samu wani farincikin saba, ya rintse idonsa, ahankali yak’asa gaban wani k’aton hotonsa shida Ni’ima, sunyi k’yau sosai ahoto, suna tsayene gaban wasu filawoyi sun fukanci juna, yad’an rissina yadafa cikinta sannan tanada cikin Nawal, itakuma tana kallonsa shida cikin tana murmushi.
Hoton sunyi bala’in k’yau, wasu hawaye suka zuraro akumatunsa, baidamu daya gogeba sai shafa hoton daya cigaba dayi, yad’au tsawon lokaci yana kallon hoton daga baya yafad’a kan gado yana hawaye kamar wani mace.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Babu 6ata lokaci aka su Appa suka kai k’ud’i da komai ranar juma’a, antarbesu tarba ta mutunci da girmamawa, cikin girmama juna komai ya gudana aka tsaida biki sati uku kacal, saidai daga amarya har ango suna cikin tashin hankali, garama angon yadaure sosai yamaida komai ba komaiba, harma yanad’an saka baki idan ‘yan uwansa suna maganar shagalin bikin.
Haka yasa ammi taji dad’i sosai itada Appa, sai albarka suke saka masa.
Nawal ma sai murana take ankusa kawo mata momynta.
Shirye shiryen biki ya kankama sosai Dan hidima akeyi babu kama hannun yaro, abubuwa sosai su ya Hamza suke shiryawa.
+.+
Yarinyar da akaima fad’e tana samum sauk’i saidai har yanzu bata iya magana, kullum sai Bobo yaje asibitin safe da yamma, har yanzudai ba’a samu iyayentaba ana kan nema, gashi bata magana bare asamu wasu bayanai daga gareta.
‘Yan sandama suna aikinsu na binciko Wanda ya aikata laifin ta hanyar Number motarsa da matashin nan ya d’auka.
To ALLAH yasa adace amin.
A6angaren Safna kam abubuwa sun cakud’e danta tsaya kaida fata batason auren, anbuga anbuga tak’i, anyi lallashin abanza, hardai takai yau ya Shaheed ya zaneta amma abanza, Dan tace wlhy aka matsa mata zatabar gidan.
Hankalin Abba yatashi sosai, yarasa mafita, gashi har anfara shirye shiryen biki, Dan gobe za’a kawo lefe…………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 9
Tana kwance agadonsu tana sharar kuka Rahma tashigo, da sauri tak’arasa gaban gadon tana fad’in haba aunty Safna yakamata kibar kukannan haka, ko sokike kizo kanki yana ciwone?.
Safna ta tashi zaune dolene nayi kuka Rahma kinajindai yanda ya Shaheed yace aure babu fashi, wlhy nikuma bana sonsa….
Rahma ta katsemata zancen da fad’in toni aunty Safna ganinake tunda bawani kike soyayya dashiba kawai kiyima su Abba biyayya mana. Tunda kinsan bazasu cutar dakeba.
Safna takamo hannun Rahma tarik’e gam kamar tana gudun kar’a kwace mata ita, ta ce, “Rahma bazan 6oye mikiba, zan gaya miki dalilin bijirema su Abba.
Wlhy sati hud’u dasuka wuce zuciyata tayi tuntu6en kamuwa dason wani bawan ALLAH, a makarantarmu muka had’u kuma wlhy ina bala’in sonsa, kullum sainayi mafarkinsa.
Lokaci k’an k’ani guy d’in ya sace zuciyata, nikam nad’auki aniyar nemoshi duk inda yake, inaji ajikina shine uban ‘ya’yana, yanzu haka nabada kwangilar nemosa, shiyyasa duk abindasu Abba zasuyi saidai suyi bazan yarda amin Auren doleba.
To amma aunty kina ganin kinyi dai dai kenan?.
Da Sauri tad’aga mata hannu kinga baneman shawara nakeba, nabaki labarin sirrin zuciyatane kawai, Dan haka sauraramin, ragamar rayuwata ahannuna take Dan haka bazan yarda azalunceniba inaji INA gani.
Ainaga kema kin isa auren, miyasa Abba bazai aura masa keba saini?, idan kinajin banyi daidaiba toke kice su aura masa ke, nikuma abarni da Wanda nakeso, danhaka tashimin anan banason shishshigi da k’wala kai afaranti.
Haka Rahma ta hak’ura dukda k’ok’arin datakeyi na fahimtar da yayar tata muhimmancin biyayya ga iyaye, da illar bijire musu, amma firr Safana taki’i saurarenta, daga k’arshema abin fad’a yaso yazamar musu.
Rahma tabata hak’uri ta tashi tafita.+
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Bikifa ya kankama, bak’i harsun fara sauka, ayau kuma za’a kai lefe Dan haka matansu ya Is’haq duk suna gidan.
Akwatuna har goma sha biyu nagani baje afalo, dangi anata d’agawa ana jinjina kai dayaba k’yan kayana, Appa da babban yayane sukayi lefe, ya sulaiman yad’auki nauyin duk wani abincin daza’aci, ya Hamza kam suna 6angaren cashiya, shine yahad’a faty za’ayi dina da daddare bayan an d’aura aure ankawo amarya.
Ammi ta had’a mother night ana gobe d’aurin aure.
Suma su khairiyya da matan su ya hamza ba’a barsu abayaba sun had’a Sisters day washe garin d’aurin aure da safe kafin ayi walima.
(Nace hummm kaga bikin d’an gata).
Ango kam babu abinda zaiyi saidai gyaran gidansa, Dan za’a canja MASA fenti da abundan ba’a rasaba tunda andad’e babu kowa agidan, “tun bayan rasuwar Ni’ima daya Shiga rud’ani kamar yayai hauka yasa Appa ya tattaroshi yamaido gida kusadasu.
Kayan lefe kam sunyi masha ALLAHU saidai mak’iyi aunty Rashida matar ya is’haq tafad’a tana fesama kanta turare.
Dariya suka shek’e da ita suduka, aunty Sameera matar ya Hamza ta ce, “k’yaface haka aunty Rasheeda tunda kina ragema amarya turare…….
To aii gara kafesa, k’ila idan amaryar tazo wannan mijin nata maikama da soja ya hanaka fesawa.
Dariya suka kuma shek’ewa da ita harda tafawa kamar wasu k’awaye.
Adai dai wannan lokacin kuma Bobo yashigo falon shida ya Hamza.
Ahankali suka fara tsagaita dariyar tasu, ya Hamza ya ce, ” kukuma lfy?, miya sakaku dariya haka?.
Aunty Sameera ta maimaita musu abinda yafaru, dariya ya hamza yayi, bobo kam saiyayi murmushi yana kallon aunty rasheda dake dariya, ta ce, “ka kafeni da ido konayi k’aryane?.
Kauda Kansa yayi yana murmushi, ya ce, ” aunty Rasheeda kenan, kisanifa saikin biyama matana turarenta babu d’aga k’afa.
Nanmadai dariya akayi, Aunty ummy ta ce, “lah bobo dama kanason auren nan amma idan anyi magana kaita wani basarwa?.
Okey da kin d’auka banasone aunty ummy?, tsaya kiga ikon ALLAH bayan d’aurin aure zakisha mamaki Romeo zan zama.
Dariya sosai sukeyi harda ya hamza da Ammi dake sakkowa daga saman Appa.
Shikam bobo d’akinsa yashige yana murmushi.
Bayan sunyi dariya mai isarsu suka koma tsokanar bobo ya Hamza yana kare masa, danshi tunda yashige d’aki yak’i fitowa.
STORY CONTINUES BELOW

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Alhmdllh yau lefe ya iso gidansu Safna, anyima ‘yan kawo lefe tarba ta girmamawa, kowa ya kalli lefen saiya jinjina kai, Dan kayane masu k’yau da birgewa.
Sund’an dad’e agidan sannan suka tafi cikeda tukuyci na girma.
Cikeda zumud’i Rahma tashiga d’akinsu, Safna tana zaune tana chart da baseera daketa k’ara zugata wai karta yarda da wannan auren, *boy ya ce, ” yana gab da samo mata bobonta.
Murmushin jin dad’i taketa zabgawa, k’arar rufe k’ofa da Rahma tayi yasa Safna d’agowa, Rahma tak’araso gurinta tana washe baki, aunty Safna kinga kayan lefenki kuwa jar ubancan kai, wlhy kamar basusan ciwon kud’iba.
Baki safna ta ta6e sannan tagallama Rahma harara yarinyarnan na kula kemafa kanki da motsi, banace kidaina jingina aurennan danibane Dan uwarki, kakin yakamata kitaya farinciki Dan lefennan nakine baniba kam, saikuma tayi wata ‘Yar dariya Rahma lefena yana nan zuwa daga Bobona, k’ilama sannan kinada ciki hhhhhjhhhh ta shek’e da dariya harda rik’e ciki.
“Na ce, ” hummmmm”.
Rahma kam girgiza kai kawai tayi, tana mamakin halin kafiya da dagiya irinna Safna, tanayin Abu kamar batada ilimin addini, ALLAH ya k’yauta tafad’a afili tana ficewa ad’akin.
Amin safna tafad’a ita tana Raka Rahma da harara.
Ran Abba a 6ace yake, sai safa da marwa yake afalonsa, gobe d’aurin aure amma Safna ta tsaya kaida fata bata son aurennan, yau Uncle Abubakar sau biyu yana dukanta shida ya Shaheed amma tace Sam batasan zancenba, daga k’arshema kayanta tahad’a waizata bar musu gidan.
Ya Shaheed ne yashigo falon Abba da sallamasa, Abba ya amsa yana mai tsurama Shaheed d’in ido kamar yau yafara ganinsa, ya Shaheed ya rissina ya gaida Abba sannan ya zauna ak’asa kan kafet.
Shima Abba saiya nemi waje ya zauna.
Ya Shaheed ya sauke numfashi Kansa ak’asa ya ce, “Abba dama wata shawarace nazo da ita.
Ina jinka Shaheed Abba yafad’a da hanzari.
” Hummm Abba inaga tunda Safna tak’i har yanzu, dataje tamana abin kunya inaganin kawai mubarta, inhar zasu yarda kawai abashi Rahma.
Abba yazaro ido waje, Shaheed baka ganin Rahma batayi k’ank’antaba!?.
Abba batayi k’ank’antaba, tafa gama secondary, kuma yanda nasan Rahma da hakuri da biyayya bazata bijirema umarninkaba kamar yanda safna tayi, nasan zata yarda ta auri Abdulmalik indai Rahma ce……
Dai dainan Rahma tashigo falon, tiren dake hannunta ya su6ce, abinda ke ciki yazube jikinta sai rawa yake saboda jin furucin ya Shaheed na k’arshe.
Ya Shaheed ne yamik’e da sauri yakamota ya zaunar, cikin taushin murya ya ce, kiyi hak’uri Rahma kibi umarnin Abba kifiddashi daga kunyar mutanen daya tara, kikalli gidannan cike yake da danginmu, wasuma daga wani gari suka taso, kituna d’unbin mutanene da Abba ya gayyata wad’anda zasu halarci taron d’aurin aure gobe idan ALLAH ya kaimu.
Rahma kema kinason Abbanmu yaji kunya?, kamar yanda Safna tayi, jibi kiga yanda hankalin Abba yake atashe akan abinda baifi k’arfiba daga garemu.
Rahma tad’ago kai takalli mahaifinsu dashima su yake kallo, gabad’aya fuskarsa ta canja, Abbansu muntum mai sauk’in kai da hak’uri amma yau 6acin rai ya maidashi wani iri, ita saitagama kamar yarame…..
Ya Shaheed yad’an ta6ata, da sauri takalleshi, ya ce, “baki aminceba kema ko?.
Yanda ya Shaheed yay maganar saiya bata tausayi shima, ahankali ta jinjina kai, cikin kuka ta ce, ” nayarda yaya wlhy na amince zan fidda Abba kunya… Shashshekar kuka tahanata k’arasawa.”
Cikin farin cikin ya Shaheed ya rungumeta, Abba kuma yarungumesu gaba d’aya.
Sai albarka suke saka mata da addu’ar fatan alkairi, itakam tana kuka tana sharar hawaye.
Abba yakira Appa ya sanar masa komai bai 6oye masaba.
Appa ya ce, “babu wani damuwa da Safna da Rahma duk d’ayane tunda daga tsatso d’aya suka fito, shima yayta sakama Rahma albarka.
Abba yaji dad’i sosai, sukayi sallama.
Ummi ma Abba yakirata tazo d’akin, jin abinda yafaru yasa ta rungume ‘yartata cikeda farinciki dakuma saka mata albarka, saidai gefen zuciyarta tana tausayin Rahma, aganinta nawa Rahmar take, amma babu yanda zasuyi, sun tara d’unbin mutane wannan ne kawai mafita agaresu Baki d’aya.
Fatanta ALLAH yasa mijin nata yakasance mai kula da tausaya mata, Dan Rahma tanada rauni sosai, dukcikin ‘yayansu babu Wanda yakai Rahma hak’uri, daga ita sai ya Muneer, sune suka d’ebo halin mahaifinsu Sak, na Rahma ma yafi nasa, Dan Rahma akwai hak’uri, kuma yaran gidan duk sunfita k’yau sosai.
Rahma ba fara bace amma tanada d’an haskenta daidai gwargwado, zamu iya kiran rahma tsaka tsaki batada tsawo bakuma gajera bace, tanada d’an jiki Dan ‘Yar lukutar ummi ma da akece mata, idan akafad’a tayita kuka bataso, tanada k’yanta daidai gwargwado (saidai Safna tafita k’yau nesa ba kusaba), Abu mafi d’aukar hankali ajikin Rahma shine idanunta, wasu irin idanu Rahma take dasu masu hasken tsiya da girma kamar suffar kwai, duk yanda ran Rahma ya6aci basa canja kala saidai su k’ank’ance.
ALLAH yabama Rahma baiwar juya idanu, gasu masha ALLAHU da girma, sau dayawa idanun Rahma kan fisgi hankalin mutane kanta Dan danan tashiga ransu Dan ita mutumce mai saurin Shiga rai, indai zaka zauna da ita saita shiga ranka.
Wannan kenan.🤸🏻♀👌🏼
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Labaridai ya isa kunnene Bobo “wai Amarya bata sonsa”, amma abin bai bashi haushiba sosai, tunda dama shima ba auren yakesoba, Dan haka da yarinyar tasoshi da karta soshi duk uwar ubansu d’aya ko akwalar rigarsa, shi dama wadda za’a bashi yanzu d’in ta ce, ” itama bataso, da wlhy har k’yauta zai mata.
Na ce, “hummmm………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 10
Kafin la’asar zazza6i yarufe Rahma, tana d’akin Abba kwance ak’udundune, ya Muneer yashogo da Dr kaleed har cikin falon Abba.
Abba da kansa yashiga d’akinsa yatasoda Rahma daketa rawar sanyi, saman kujera ya zaunar da’ita Doctor yashiga aikinsa, babu wata matsala Alhaji ‘Yar damuwace kawai Dr Kaleed yafad’a.
Abba ya ce, “to Dr babu wani taimako da za’ad’an bata kenan?.
A’a zan mata allura da magani tad’an samu barci, insha ALLAHU daga nan zuwa yamma zata koma Normal, yanzudai idan namata allurar tad’an samu koda tee ne tasha saitasha magani tayi wanka da ruwa maid’an sanyi ta kwanta, insha ALLAHU normal zata tashi nanda anjima.
To madallah Dr mungode sosai.
Babu damuwa Alhaji aii aikinane.
Babu 6ata lokaci Dr yayma Rahma duk abinda yadace, ummi tabata shayi tad’ansha kad’an tabata magani Wanda tashashi da k’yar Dan Rahma akwai tsoron allura da magani, bataso ko kad’an allurarma saida lallashi akayi.
Bayan tasha maganin ummi ta taimaka mata tayi wanna a bayin Abba, kaya aka d’akko mata tasaka takuma kwanciyarta a gadon Abba sai barci.+
Hummmm wai ina Safna?.
Tana nan acikingidan kuma labari yakai mata, ancanjeta da Rahma, Dan haka tadage tarink’a tsallen murna ita taci nasara, shikenan zata mallaki bobonta nanda lokaci kad’an, har ruwa tazuba k’asa tasha Dan dad’i.
Cikeda farinciki takira Baseera ta guntsa mata, murna sosai ta tayata harda jinjina da yaba k’ok’arinta na dagiya.
Bayan sungama da baseera takira zeenat itama, zeenat ta ce, ” wlhy Safana kin tafka babban kuskure a rayuwarki, na tabata nangaba saikinyi Dana sani Mara iyaka, son zuciya yasa kin bijirema iyayenki akan Wanda baima San da zamankiba, ke kanki bakisan Inda yakeba yanzu, bakida tabbacin zai kar6eki kobazai kar6i soyayyarkiba, wlhy kidaina biyema hud’ubar baseera zatayita kaiki tana baroki a tashar wahala ne……
Safna ta k’atseta atsawace, kee!!! Dallah malama yimin shiru, nakiraki nafad’a mikine danki tayani murna ba surutun banzaba, aiikin banza kawai mtsowww taja tsaki tana yanke wayar.
“Daga can Zeenat ta girgiza kai tana fad’in ALLAH ya shiryeki Safna, amma zakiyi nadama wlhy na tabbatar.”
Babu Wanda yakumabi takan Safna shagalin biki akacigaba da gudanarwa, itama tafita harkar kowa agidan lamuran gabanta kawai takeyi harda yima Rahma dariyar mugunta.
Na ce, “hummmm.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*
Bobo ya lalubo wayarsa dake wringing daga aljihun jins d’insa, ido yad’an zaro tareda kallon Ya Sulaiman dake duba yarinyar da akaima fad’e.
Lfy kuwa bobo?.
Tab ya Is’haq ne kasanfa sunacan suna jiranmu….. K’ara kiran da akayine yasa Yakuma kallon wayar, ya is’haq d’innedai, d’agawa yayi tareda yin sallama.
Abdulmalik wai kuna inane kaida sulaiman?, ya Is’haq yafad’a daga can.
Wlhy muna asibiti wajen yarinyarnan amma gamunan zuwa Ku k’ara hak’uri.
Tom yakamatafa kuyi sauri Dan akwai abubuwa agabanmu masu yawa.
Gamunan yanzunan insha ALLAHU.
yanke wayar yayi tareda dawo da kallonsa kan ya sulaiman, ya Sulaiman yakamatafa muje kasandai masifar babban yaya, muk’arasa kafin ya k’ulu.
Gsky ne muje kawai aii nagama harma takoma bacci.
Bobo yad’an lek’a fuskarta, ya ce, ” baiwar ALLAH, wlhy rashin maganar yarinyarnan yana damuna, yakamatafa ace iyayenta sunsan halin datake ciki.
Hakane gsky to amma yazamuyi? tunda bamusan idan takeba, saidai mucigaba da addu’a. Idan kuma tak’ara samun lfy mubi shawarar Ammi mumaidata wajenta kawai.
To shikenan bobo yafad’a yana fitowa.
Waje yanufa shikuma ya sulaiman yashiga office Dan ajiye kayan hannunsa.
Babu dad’ewa yafito, mota yashiga Inda bobo ke zaune a mazaunin direba, bobo yatada motar suka fice daga asibitin.
.+.
Gidansu Safna kuwa anyi shirin kamu Wanda aka had’a a babban harabar gidan nasu, saidai matsalar amarya babu lfya tana d’akin Abba kwance tana barci.
Hafsat matar ya Shaheed ta kalli ummi, ummi to yanzu yaza’ayine harfa dangin angon sun iso ga babu amarya, dama Safna zata mana alfarmar yanzu kawai saita zauna amadadin Rahma d’in.
A’a barta kawai hafsat, nibanamaso muna saka Safna acinkin sha’anin bikinnan, takalli agogon dake hannunta, hafsat inaga bari kawai atada Rahma d’in dukda dai bata dad’e da kwanciyaba.
A’a ummi abarta kawai likitafa ya ce, tana buk’atar Hutu, gashi dangin ango since k’arfe tara akwai mother Night, yakamata tasamu ishashshen barci kafin sannan, yanzu bari nayima Basman aunty Yahanasu magana saita shirya tazauna amadadin amarya tunda kusan kansu d’aya.
Yauwa hakama yafi, dama gasu suna kama ba laifi.
Haka suka saka Basma aunty yahanasu k’anwar ummi tashirya tsaf tamkar amaryar, idanma baka saniba saika d’auka Rahma d’ince Dan suna matuk’ar kama, idanuwa kawai Rahma zatafi Basma.
Dahaka aka gudanar da kamu Wanda yak’ayatar da dangin ango, su khairiyya da khursiyya dasu aunty Rasheeda sai zuba lik’i suke wa amarya, Dan basusan ba amaryarsu bace.
Dahakadai taro yatashi gab da magriba Alhmdllh.
Duk shagalinnan da akeyi Safna tana d’aki kwance abinta, da barcima takeyi kid’an da’aka sakane yasa tatashi tana mita da tsaki anhanata barci wai, wayarta ta d’auka takira *boy danneman k’arin bayani akan aikin data bashi.
Ya ce, “mata yana nan yana k’ok’ari.
Tana yanke wayar takira Baseera sukaita labarinsu Rabi duk akan bobone.
Na CE hummmm.
STORY CONTINUES BELOW

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Su bobo suna isa gidan suka Tatar da ya Is’haq da ya Hamza zaune aharabar gidan, harda wasu samari wajensu bakwai, cikin samarin danginsune, ya Hamza yana cikinsu sunashan shafta.
Ya Is’haq kam yana gefe zaune saman mota Dan bakomai yake Shiga cikinsuba kasancewarsa babba.
Bayan bobo yayi fakin suka fito, wajensu ya Hamza suka k’arasa, hannu sukaita bama matasan samarin ana musabaha🤝.
Bayan sun gama gaisawa Bobo yanufi Inda Ya Is’haq yake.
Hannu yabashi shima suka gaisa.
Ya ce, “kunje kun wani mak’ale a asibiti tamkar kun manta da abinda me gabanku.
Sorry babban yaya, bobo yafad’a yana had’e hannayensa waje d’aya alamar tuba🙏🏻.
Dirowa ya Is’haq yayi, to yazanyi idan ban hak’uraba ma.
Motocine suka fara shigowa gidan, bobo yabisu da kallon yana fad’in wannan gayarfa daga ina?….
Daidainan ya Hamza da ya sulaiman suka k’araso garesu.
Ya Hamza ya ce, ” daga gidan amaryarka suke, sun halarci kamune.
Baki bobo yad’an ta6e ya Hamza miye kuma kamu?.
Kafin ya Hamza yabashi amsa aunty Rasheeda da aunty ummy suka k’araso, aunty sameera dasu khursiyya suna biye dasu.
Bud’a aunty Sameera tarangad’a akunnen bobo, yay saurin toshe kunnansa, saida tagama sannan ya kalleta fuska a shagwa6e, kai aunty Sameera dodon kunne zaki kashemin?.
Dariya suka shek’e dashi suduka, yayinda aunty Rasheeda tafara fesama bobo turare mai shegen k’amshi, kaima ankamaka kamar yanda mukaje kama amaryarka.
Dariya su ya Sulaiman suka saka danganin yanda bobo ya kwa6e fuska tamkar zaiyi kuka, ALLAH matannan nakula kun rainani yafad’a yana hararsu.
Dariya sukayi gaba d’aya harda wasu daga cikin dangi dasuka zagaye wajen.
Aunty ummy ta ce, “tab wlhy Bobo matarka ta had’u jar ubancan kai, kaiga wasu idanu masha ALLAHU, (” nace hum danma bakiga na asalin amaryarba kenan), tacigaba da fad’in aifa inaga aka kawo amaryarnan bazaka ringa fitaba, aikinma hak’ura zakayi dashi.
Dariya sosai ake shek’awa, dukda haushi da yacikama bobo ciki wannan bai hanashi murmusawaba, ya ce, ”yan sa ido, kunje kunata k’arema yarinya kallo, halan har muninta kun gano?.
Wata Zainab acikin danginsu ta ce, “wlhy ya Abdulmalik babu mai iya gano munin Rahma amarya, masha ALLAHU kam komai yaji zam zam….. Tak’are maganar da rufe baki.
Nanma dariya akayi, shikam ya ce, kwadaiji dashi sa’idinniya kawai masu barci da ido d’aya, yana gama fad’a yafito daga wajen.
Wasu daga cikin ‘yammatan jisuke inama sune da wannan guy d’in, lallai yaci sunansa Bobo.
Wasukam kishine yacika zuciyarsu, Dan sundad’e suna nuna masa so yana basarwa saboda jin kai, wasukam har iyayensu saida sukai masa talla amma ya ce, “kai kasuwa.
Cikin gidan yashiga Dan soyake ya d’auro alwala, babban falon k’asa cike yake dam da mutane, yanashiga suka hau tsokanarsa wai angon k’amshi angon k’amshi.”
” aransa ya ce, “za’a gogudai”.
Haka yagaida wad’anda zasu iya jinsa ya haye sama d’akinsa bayi yashiga yad’auro alwala yafito, su aunty Sameera ma duk sunshigo ciki.
Yazo zai fita Ammi ta ce, ” mukarram!.
“na’am Ammi ya amasa yana juyowa, k’arasowa tayi Inda yake takama hannunsa suka fito.
Wani d’an lungu tajashi ya ce, ” Ammi lfy dai ko?.
Lfy lau mukarram dama tambayarka zanyi d’azu kuwa kaje gidansu amaryar taka?.
Gefen wuyansa ya sosa, afuwa ammi, wlhy abubuwane sun mana yawa.
Kanta ta girgiza haba mukarram ya inamaka kallon mai hankali amma kanason 6ata wayonka?, babu dad’ifa, iyayen yarinyarnan bazasuji dad’iba ace bakaje gidanba tunda aka fara maganar aurennan, shin kai zakaso ayima su khursiyya hakane?.
A’a wlhy ammi bana fata, amma Dan ALLAH kiyi hak’uri nayi kuskure, insha ALLAHU zan bata hak’uri anjima idan munje mother night.
To shikenan ammadai Baka k’yautaminba, Bahaka nasoba.
Tom kiyi hak’uri Dan ALLAH.
“Ya wuce.”
Yauwa ammi an kar6o d’inkin Nawal kuwa?, wlhy namanta shaf, kuma harda wanda zata saka anjima.
Eh khairiyya ta amso d’azu kafin sutafi wajen kamu.
Yauwa harnaji dad’i, bari naje sallah ammi har an tayar inagama su yaya sun wuce.
To saikun dawo.
Masallaci yanufa ammi kuma takoma ciki.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Anayin Sallar magriba Safna ta sid’ad’e tabar gidan, sai gidansu kamal, acewarta bazataje wajen wani mother Night ba, saikuma tana zuwa gidan ta tarar dasu Ameera suna shirin zuwa harda momynsu.
Dayake momynsu kamal tasan komai Dan baba abubakar yasanar da ita, (k’anin Abba ne, kuma mahaifi gasu Br kamal abokin aikin bobo) batace mata komaiba itama, safna tashige d’akin Ameera tayi kwanciyarta, sukuma suka nufo gidansu Safna d’in, akabarta itakad’ai agidan sai ‘yan aiki.
Rahma ta farka bayan sallar magriba, kasancewar tana fashin Sallah saikawai aunty Madeena matar ya muneer tasata tayi wanka.
Mai kwalliya tafara aikinta na fente fuskar Rahma.
Itadai Rahma bin kowa kawai takeyi da ido, kad’an kad’an saita share hawaye, saida mai kwalliya tamata magana sannan ta tsagaita da kukan aka tsantsara mata kwalliya ta d’aukar hankali.
Wani doguwar riga bubu aka bata tasaka, tawani material Orange da d’igo d’igon lemon green ajiki, aka nad’a mata lemon green d’in d’ankwali, sai fashion na ‘yankunne da sark’a maid’an tsawo, tasaka bak’ar coka wadda ta manne awuyanta.
Yasalam nafad’a yayinda naga amaryar k’amshi tafito ras kamar ba Rahman ummiba, tayi k’yau masha ALLAHU.
Fos aunty hafsat tabata, wadda itama takasance lemon green, sannan tasaka takalmi lemon green shima mara tudu.
Hummm komaifa yaji ajikin amarya.
Ihsan k’anwar Br kamal tamatso kusada ita, kai Rahmana kinyi k’yau wlhy, na tabbata angonnan yaganki saiyace gwamma da akayi, wlhy saikin susutashi.
Basma ta ce, “ni tsorima nake karya rikice yace daganan sai gidansa.
Duka Rahma takai musu, cikin dasashshiyar muryarta datasha kuka ta ce, ” yan iska kawai, aii dama halinku d’aya.
Dariya suka shek’e da ita harda tafawa.💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 11
A 6angaren bobo kam bayan sun dawo daga masallaci aharabar gidan suka sake zama, hira aketayi da barkwanci, saida aka k’ara kiran sallar isha’i sannan suka mik’e, masu sake alwala suka sake, wadda tasu bata karyeba sukayi gaba.
Ana idar da sallah suka shigo gidan, shiri suka fara, kowa yana k’ok’ari kada time ya k’ure.
Bobo kam wanka shima yashiga, yafito d’aure da tawul fari a k’ugunsa, k’arami kuma yana goge kansa zuwa fuska da wuya har k’irjinsa zuwa k’asa.
Wurga tawul d’in yayi saman kujera, yaja kujerar madubi ya zauna, mai yafara shafawa, hardasu farar fauda afuska, yashafe kansa da mai mai k’amshi har zuwa sajensa dad’an gemunsa na gayu, yasa kum yak’ara taje kansa da gemunsa, sannan yay amfani da burosh wajen kwantar da sajensa, yako kwanta luf sai walk’iya yake da tashin k’amshi.
Turarurruka yad’auka kala kala yafeshe jikinsa, sannan yanemi guri abikin gado ya zauna batareda niyyar saka kayaba.+
Atsakar gida kam mutane harsun fara fita, Dan kowa bayaso atafi abarsa, dandanan motoci suka fara d’aukar mutane, kowa ya cakire da kalar kayan dayakeso, manyan iyayene kawai suka saka wani Dan datsetsen less fari tas, suka nad’a Orange d’in gwagwgwaro, masha ALLAHU abin sai Wanda yagani.
Su khairiyyama ba’a barsu abayaba, sunci ado da dogayen riguna na lemon green d’in material sunyi k’yau masha ALLAHU, suda matansu ya sulaiman duk iri d’aya suka saka.
Nawal ma anshiryata cikin farin less irinnasu Ammi, doguwar riga aka mata, aka nad’amata Orange d’an kwali, yarinyar tafito d’as kamanninta da bobo ya k’ara fitowa.
Tare suka shiga Mota da Ammi.
Ya Hamza yafara waige waige, cikin Jan tsaki ya ce, “wai mi Bobo yakeyine tun d’azu yafasan saiyaje sun taho da amarya, gasu ammi harsun wuce.
Ya is’haq shima yay tsaki ALLAH yaron nan d’an wulak’ancine, Hamza kaje d’akinsa kaga miyakeyi?.
Ya Hamza yanufi d’akin Bobo, ya Sulaiman dai baice k’alaba.
La’ilah Abdulmalik minene haka?.
Bobo dake zaune yana latsa waya yad’ago yana kallon ya Hamza daya had’e cikin Farin Suit sai k’amshi yake.
Minayine yaya?.
Bansaniba, dallah malam kana 6atamana lokaci katashi kasaka kaya, su Ammi harsun wuce.
Baki yaturo kamar wani k’aramin yaro, nikam wlhy ya Hamza barcima nakeji.
A’a kakan barci kakeji ya Hamza yafad’a ahasale, wlhy zankira ya Is’haq.
Da Sauri bobo yamik’e, yafara saka gajeren wando da bes, ya warware had’ad’d’un Suit lemon green sai d’aukar ido sukeyi.
Wandon yafara sakawa da Orange d’in Riga mai dogon hannu, ya tsuke k’ugunsa da belt, ya Hamza yad’auki nektayit d’in green yafara saka masa, shi abumma dariya yabasa, amma baiyi dariyarba gudun kar ya Hamza yasake k’uluwa.
Da taimakon ya Hamza yasaka rigar Suit d’in, yafara saka botiran ya hamza na gyara ma kwala d’in. Takalmima saida ya taimaka MASA yasaka, sannan yak’ara feshe jikinsa da turare, yad’auki wayarsa d’aya yazura a aljihun Suit d’in, suna tafiya yana d’aura agogo.
Na ce o’o me bobon Ammi sai a slowly.
Saida ya Hamza yaga yashiga mota a baya, sannan shima yashiga mazaunin direba Nasiba d’iyar k’anwar Ammi na gefensa.
Suma su ya is’haq suka tada mota, suna gaba su bobo na bayansu har anguwar su Rahma.
Ak’ofar gida suka faka, ya Hamza yafita shida Nasiba har cikin gidan suka Shiga sukace afito da amrya ango yazo.
Gaban Rahmane yafad’i Ra’s, jitake tamkar tafasa ihu, kowacce irin tarba angon zai mata ta tanbayi zuciyarta?.
Batada mai bata amsa, tana cikin zancem zuci aunty Ruk’ayya ta ce, taso Rahma angonki yazo.
Jitake tamkar ta ce, bazataba amma yazatayi.
Haka aunty Rukayya takamo hannunta sukayo waje, dama dayawan mutanen sun tafi sai k’alilan suka rage.
Kowa yashiga mota amarya kawai akejira.
Ya Hamza yabud’e d’ayan gefen da Bobo yake zaune Dan ganin amarya tafito. Azuciyarsa ya ce, ”masha ALLAHU, gsky amaryar auta ta had’u…….
Isowarsu ta k’atse masa tunani, yayinda gaban Rahma keta fad’uwa azatonta Ya Hamzane angon, kanta na k’asa aunty Ruk’ayya tasakata amotar.
Wani k’amshine da sanyi suka bigi hancinta, tashak’a talumshe ido azuciyarta ta ce, ”oh ALLAH, wannan wane irin k’amshine?.
K’ok’arin gyara zama tayi saitaji ta dunguri mutum, dasauri tajuyo ta kallesa, yana zaune ak’ame kamar wani jinin sarauta, saidaifa k’amshin amaryar tasa ta narkar da zuciyarsa, saiwani lumshe idanu yakeyi, ahankali yajingina bayansa da kujerar ya lumshe ido.
K’irjin Rahma sai dukan uku uku yake, jitayi wani sabon zazza6i yana neman rufeta, dukda kallon fisha tayima angon nata ta tabatar ya had’u masha ALLAHU.
YA Hamza dake tada mota ya ce, amaryarmu ykk?.
Muryar Rahma na rawa ta ce, “ina yini.
” lfy lau, ya fara hidima?.”
Alhmdllh tayi maganar ahankali.
Tad’an kalli gefen Bobo ta ce, ina yini.
Dukda yagane dashi take amma yay shiru.
Takuma cewa ina yini, sai asannan ya amsa da lfy, ykk?.
Kasa amsashi tayi, sai kawai tayi k’asa da kanta tana wasa da zoben hannunta.
Sunkusa isa wajen faty d’in Bobo yatashi zaune sosai, wata leda yad’akko agefensa yazaro rafar ‘yan 200 guda hud’u yad’ora saman cinyarsa.
Rahma data k’urama zonen hannunta ido saikawai taga mutum ya d’oro hannunsa saman cinyarta, gabanta ya ce, “wani Rasss!, fos d’inta yazare data d’ora saman cinyarta ta d’ora hannunta akai.
Tabud’e idonta ahankali daga rintsewar datayi, Fos d’in yabud’e yaga ‘yan 50 rafa biyu sai wayarta, wayar yaciro yasaka kud’in daya ciro aleda yasa a fos d’in maida wayar yayi zai rufe fos d’in amma tak’i shiga dan tacika dayawa.
Ciro wayar yakumayi yarufe fos d’in yad’ora mata saman cinyarta, wayarta kuma yasaka cikin aljihun suit nasa, nufinsa idan sunje angama taron talik’a kud’in saiya bata.
Itadai Rahma batace masa k’alaba Dan batasan miyayi da fos d’inba.
Har gaf da d’akin taron ya Hamza ya faka, yafito yabud’e musu k’ofa, asanyaye Rahma tafito, duk kunya ta isheta tasaba duk inda zataje saida k’aton hijjab, amma yau gata kod’an gyale babu, sauk’intama Rigar bubuce kuma tabud’e bata matsetaba.
Su yaya Ishaq suma fitowa sukayi daga motarsu, suma kayansu iri d’aya dana ya Hamza.
Suma sun yaba da amaryar k’anin Nasu sai masha ALLAHU suke jerowa.
Ya Hamza yashiga d’akin taron yasanar da MC amarya da ango sun iso.
Aiko nanfa yafara kayayato, falon taron yay tsit anzuba ido aga amaryar Bobo d’an gayunnan maiji da kansa.
Ahankali Bobo yatako har zuwa gaban Rahma data duk’ar dakai k’asa kamar ace ar ta gudu.
Ahankali ya ce, “bismillah muje.
Jerawa sukai suna tafiya ahankali har cikin wajen, bayansu kuma su ya Sulaiman ne suka take musu baya.
Tunda suka shiga wajen taron jikin Rahma yay sanyi, Dan ita irin mutanan ne masu tsoron shiga mutane, dandanan tafiyarta ta sauya, sai wani sassarfa takeyi.
Raf raf raf raf!! d’akin taron yad’auki tafi lokacinda Rahma ta hard’e taigaba kamar zata fad’i, da sauri Bobo yaruk’o hannunta yana fad’in ezeee madam.
Ajiyar zuciya tasauke danjin bata fad’iba, a u okey?, yafad’a yana kallonta. Kai tad’aga da sauri.
Tom kiyi ahankali plzz karki ji ciwo.
Ngd tafad’a tana kallon k’asa, to muk’arasa ya nuna mata hanya.
Ahankali suka taka zuwa inda aka tanar musu, sunbirge mutane gsky saidai mak’iyi, kowa fad’i yake sun dace da juna, Ammi saijin dad’i takeyi Dan harga ALLAH Rahma tashiga ranta.
Suna zama DJ yasaki wak’ar because, i luv u. Wannan wak’ar Bobo ce dayake bala’in so sosai, ya Hamza yabada wak’ar asaka Dan Bobo.
Aikuwa sai sakin lallausan murmushi yakeyi danjin dad’in wak’ar.
Masu hotuna kam sai aikinsu suke, itadai Rahma kanta yana k’asa tana shak’ar daddad’an k’amshin turaren Bobo.
Bayan wak’ar tak’are aka fara gudanar da abinda ya tara mutane.
Ammi tayi bayani da godiya ga d’unbin mutane dasuka halarci mother’s Night d’in, sannan taima amarya da ango fatan alkairi.
Rahma taji dad’in bayanin ammi itada danginta, wannan kad’ai ya isa yanuna mata dangin mijin nata suna sonta.
Ankira amarya da ango filin rawa, shuru sukayi kamar bazasu tashiba, kowa da abinda yake kitsawa a zuciyarsa, saida mc yasakeyin magana sannan suka mik’e ahankali.
Afilin rawar suka tsaya k’ik’am babu mai motsi balle rawa, itakam Rahma dama bata rawa da dadai safan ce kam wannan gwanace.
Bobo yafiddo rafar kud’i yafara lik’ama Rahma idonsa k’yam akanta, itakam kanta na k’asa, Dan danan guri yad’au ihu da tafi, jiki a sanyaye Rahma itama tabud’e fos d’inta danufin d’akko ‘yan wazo d’inta saitaga kud’i dayawa.
d’agowa tayi ta kalli bobo, shikuma yad’aga mata gira kuwa, da sauri tamaida kanta k’asa, yamatso da bakinsa wajen kunnenta cikin muryarsa mai taushi da laushinnan ya ce, “ko bakisone?.
Ajiyar zuciya ta sauke itama ahankali ta ce, ” ngd sosai”.
Hak’k’ine akaina aii yafad’a idomsa agefe kamar bashi yayi maganarba.
Batace komaiba itama tazaro kud’in tafara lik’a masa gashi yamata tsawo, amma ahaka taringa masa lik’i ihun mutane da tafi yak’aru, masu hotuna da video sai haskasu sukeyi.
Ammi ta taso itama ta rungume Rahma tana saka mata albarka, tafara lik’ama Rahma ‘yan dubu dubu, (abin na manyane masu karatu), Bobo ma yakoma lik’ama Ammi sai murmushi yake saki itama Ammi haka, Rahma kam kanta ak’asa itama tana lik’ama ammi.
Su yaya sulaiman ma suka taso, dandanan gurin ya kaure da lik’i kamar ba’asan ciwon kud’iba, k’awayen ammi da danginta duk suntaka rawar gani, hakama dangin Rahma ba’a barsu abayaba, kai wannan taro ya k’yatar masha ALLAHU.
*_(can na hango Aunty bilyn Abdul tana lik’a ‘yan naira 5🤣😜🤐, ba ruwana kartajini)._*
_karfa kuce nina fad’a🤸🏻♀_
Sai k’arfe 11:30pm taro yatashi lfy, kowa yafara k’ok’arin tafiya, Rahma duk barci yacika mata ido, cikin mota take zaune tana jiransu bobo sugama sallamar bak’i shida yayunsa, saida kuwa suka gama sannan suka shigo, yanzu kam wani d’an uwansu bobone zai maidasu ba ya Hamza ba, su ya Hamza matansu suka d’auka da yaransu sukayi gida.
Rahma ta kifa kanta kan cinya harta fara barci, kallonta kawai yayi baice komaiba, shifa koma sunanta bai saniba, bai tada itaba har sukaje gidan.
Yay shiru yana tunanin yanda zai tasheta.
Lukman ya kallesa Bobo kona baku gurine?, a’a malam wane kabamu guri gida zata shiga, ita barcima takeyi.
To ka tada ita dare na k’arayi shabiyu saura fa.
Daurewa yayi yad’an ta6a bayanta, ko motsi batayiba, yakuma d’an bubbugawa, firgigit ta tashi da addu’a abakinta, tad’an kallesa, shima idonsa na kanta, munzo yafad’a akasalane.
d’auke kanta tayi tabud’e motar, saida safe tafad’a cikin muryar barci, harta rufe motar Lukman ya ce, “haba malam aii ka rakatadai kasani kotanada magagin barci.
d’an tsaki bobo yayi shima yafito, harta fara tafiya yad’an hanzarta ya cimmata, dama ita kad’ai mai gadi yake jira Dan haka k’ofar abud’e take.
Dariya Lukman yashek’e da ita, sai Bobon Ammi yafad’a harda dukan sitiyari.
Har k’ofar falonsu yarakata, saida takama k’ofar zata bud’e sannan ta ce, ” saida safe.
ALLAH yakaimu yafad’a yana juyawa.
Amota yasamu Lukman yashiga gaba suka wuce gida suma……….💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 12
Jiki a sanyaye Rahma tak’arasa cikin falon, tamaida k’ofar ahankali tarufe.
Ajiyar zuciya ummi dake zaune a fallo tana jiran dawowar Rahma ta sauke.
Dama ita take jira dantaga kowa yashigo amma banda Rahma.
“Lah ummi bakiyi barciba?, Rahma tafad’a a sanyaye. Mik’ewa ummi tayi tana murmushi, inani ina barci auta bata dawoba.
Murmushi Rahma tayi kanta ak’asa.
Ummi ta taso takama hannunta suka nufi d’aki, mutane duk sunyi barci, wasukuma suna gidansu ya Kamal.+
Rahma tarage kayan jikinta sannan tazauna bakin gadon inda ummi take zaune itama da wasu tarkacen robobi agabanta.
Ummi miye wad’annan?, Rahma tafad’a tana d’aukar wata robar Zuma tana kallo.
Maganin basirne, kinga k’ar6i wannan takardar kiduba, d’azu malam saddiqu na islamiyyarku yakawo bayan fitarku.
Cikin mamaki Rahma takar6a tana bud’ewa, murmushi tayi tareda d’agowa tana kallon ummi da itama kallonta takeyi, ummi wai kinsan miye?.
A’a saikin fad’a.
Sak’one daga islamiyyarmu, wai gobe idan ALLAH yakaimu sun shiryamin walima k’arfe 9:00am to 12:00pm, dukda abin yazo babu shiri.
ALLAH sarki bayin ALLAH, ummi tafad’a cikeda jin dad’i, aiko mun gode musu da wannan karramawa.
Aiko dai, Rahma tafad’a.
Abubuwa ummi ta rink’a dannama Rahma a darennan, harsaida Rahma ta ce, ” ALLAH ummi nak’oshi cikina zai fashe.
Dariya ummi tayi ta ce, “to barshi haka saida safe.
Daga nan wasu kayan gyaran jiki ummi ta murjema Rahma jiki dasu sannan suka kwanta.
*_BOBO._*
suna Isa gida yanufi d’akinsa, kayan jikinsa yafara ragewa, yana k’ok’arin zaro wayarsa a aljihu saiyaga ta Rahma, Kansa ya dafe O ALLAH, namanta ban bata wayartaba, zubesu yayi a durowar gefen gadon harda tasa, daganan yacire kayan jikinsa, bayi yashiga, bayan wasu ‘yan mintuna yafito, badai wanka yayiba.
Shirin barci yayi ya kwanta, saidai barcin yak’i d’aukarsa, fuskar Rahmace take MASA gizo, k’yawawan idanunnan NATA yake hangowa, yasaki wani lallausan murmushi Wanda bansan na miyeba, saikuma yaja siririn tsaki yana gyara kwanciya.
Nima waje nayo nabarsa.
*_Washe gari_*
Tunda sassafe Rahma ta tashi tai wanka kasancewar tana fashin sallah, Basama tafara yarfa mata k’unshi, masha ALLAHU nafad’a Dan k’unshin yana bada ma’ana.
Jikin Rahma duk yayi sanyi, ta tabbata yau babu fashi saita bar gidansu, cikin dabara take share hawayenta dankar Basma tagani dansukad’aine a d’akin.
Zuwa 8:00am angama k’unshin, yayi k’yau sosai, 8:30am akasa Rahma yayi wanka agurguje dantafiya walimar makarantarsu.
Shiri tayi cikin zani da riga na atanfa pink, ta d’ora bak’ar alk’yabba mai shara shara wadda amaren zamani ke yayi, tayi k’yau sosai dukda yau babu kwalliya afuskarta, dak’yarma tayarda Basma tasaka mata pink d’in janbaki Wanda shiga da kwalliyar alk’yabbar.
Wajen walimar yayi k’yau sosai, acikin harabar islamiyyar za’ayi, malaman sunyi k’ok’ari gsky dukda abin yazo babu shiri.
Wajen da’aka tanada na musamman dan d’alibai su Rahma suka zauna, iyayen yara dayawa sun halarci wajen, su Abba ma duk sunje, su ya kamal ya muneer ya shaheed, da sauran matasan anguwar da iyayensu, dan Rahma mutuniyar kirkice, tsakaninta da kowa a anguwar sai girmamawa, batada hayaniya wannan yasa takasance mai jama’a kowa yana sonta.
Gurin yayi tsit ana addu’a, shigowar wasu motoci hud’u yaja hankalin mutane kowa soyake yaga suwaye?.
Appa yafara fitowa shida wasu dattijai uku, da alama abokansane, mota ta biyu kuwa matasan family nasune, ta ukuma haka harda ya ishaq da wasu zasukai sa’anninsa, motar k’arshe kuwa, ya Hamza da sulaiman, Lukman da tauheed ne, sai Bobo Wanda yakashe kala cikin manyan kaya, purple d’in shaddace mai haske ajikinsa, rigar iya guywa d’inkin zamani, yayi k’yau sosai harda d’ora bak’ar hula.
Wow! Wasu ‘yammata dake gefen Rahma suka fad’a, d’aya tace kai Ruma guy d’incan ya had’u wlhy, dama ya ce, “yana sona?.
Rahma tad’ago dantaga wanene wai suketa kurantawa haka?, gabantane ya fad’i tayi saurin kauda kanta.
Abbane yataso shida abokansa da shuwagabannin makarantar suka tarbi su Appa.
Masauki maik’yau aka basu kamar ansan da zuwansu.
Bayan gaishe2 akaima bak’i barka da zuwa.
Itadai Rahma tunda tamusu kallo d’aya bata sakeba.
STORY CONTINUES BELOW

Dukda da daddare yaganta hakan bai hanashi ganetaba, babu laifi yarinyar tanada k’yau da nutsuwa, bobo yafad’a azuciyarsa.
Mayun idanunsa yadasa mata batareda ya saniba.
Rahma datakejinta atakure, jikinta yana bata kallonta akeyi, tana d’agowa sukaima juna kallon ido cikin ido, Dan suna fuskantar junane.
Da sauri ta janye nata gabanta na fad’uwa, hular alk’yabbar taja takuma rufe fuskarta.
Samun kansa yayi da sakin lallausan murmushi, ya sauke ajiyar zuciya yana kauda kai daga kallonta.
Addu’a aka fara gabatarwa sannan aka buk’aci Rahma tafito tayi karatu.
Gabantane yafad’i, tatuna d’unbin mutanen dake wajen amma acikinsu akeso tafito tayi karatu?….muryar malaminsu taji yana k’ara nanata sunanta.
Ihsan ta ta6ata Rahma kitashi mana.
Ihsan inajin kunya wlhy.
Kinga saka wannan gilas👓 zaki rage jin kunyar.
Siririn farin gilas d’in takar6a tasaka, o ALLAH nafad’a danganin k’yawun da gilas d’in ya k’ara mata.
Ahankali tamik’e tak’araso har inda ake buk’atar ganinta, malam jamilu yabata abin magana.
Tunda tatsaya gaban tebir d’in da aka ajiye alkur’ani mutane ke kallonta, wasukam halittar ALLAH suke yabawa da nutsuwa Rahma.
Appa sai dad’i yakeji Dan yarinyar tashiga ransa.
Gurin yayi tsit danjin zazzAk’ar muryar Rahma tafara fidda sautin karatun alkur’ani mai girma cikin suratul Maryam.
Bobo yalumshe idanunsa danjin muryar Rahma na ratsa ko ina na sassan jikinsa, ALLAH ya albarkaci rayuwarki yafad’a azuciyarsa, ahankali yabud’e idonsa yasauke akan Rahma dake karatu tana hawaye Wanda gilas d’in bai hana agansuba.
Masu hotuna sai k’allata suke, wasu kuma da waya suke mata, harda masu vedio d’inta.
Saida takai har k’arshen surarar sannan taje ta zauna tana cigaba da share hawayenta Wanda narasa namiye?.
Angabatar da nasiha ga amarya da Ango mai ratsa jiki da 6argo, har malam yana tsokanar Rahma da ALLAH yasa wata shekarar su taru haka a sunan baby, dayawan mutanen wajen sunyi dariya dafad’in ameen, (bobo kam murmusawa yayi kawai).
Angabatar da k’yaututtuka ga amarya Rahma, Wanda makaranta suka karramata da yaba k’ok’arinta na hazik’ar d’aliba mai ilimi da girmama manya da rashin karya dokar makaranta.
Abba sai dad’i yakeji.
Cikin abokan Appa dasukazo tare yamik’e shima ya ce, “yayma Rahma k’yautar mota sabuwa dal saboda namijin k’ok’arinta.
(Kabbara akayi da tafi).
Rahma tamik’e tayi godiya, takuma godema iyayenta da malamanta dasuka taka rawar gani arayuwarta, ta ce, ”iyayena sune gatana dasuka tsaya tsayin saka Dan ganin ingantuwar ilimin mu na addini dana zamani, tana kuka tana godiya ga iyayenta abbanta da umminta da yayyaensu da malamanta,……. Kuka mai k’arfi yaci k’arfinta takasa magana sai shashsheka.”
Ahankali bobo yamik’e yataka har Inda take, hanky yamik’a mata fari tas daketa tashin kamshin daddad’an turarensa.
Jiki a sanyaye takar6a idonta ak’asa ta ce, ” ngd tafad’a cikin shashshekar kuka.
Abin maganar yakar6a daga hannunta, yafara mik’a godiya ga iyayensu da kuma malamai da ‘yan uwa da abokan arzik’i dake wajen taron, yahad’a da sakama Rahma albarka da yaba mata.
Kabbara akayi da tafa MASA, abin ya burge mutane gsky, Rahma taji dad’i sosai, dukda tasan ba Sonta yakeba tunda had’asu akayi, amma yay mata wannan karamcin.
Abba da yayuntama sunji dad’i abinda bobo yayi.
Hakama su Ya Hamza bobo yaburgesu, fatansu ALLAH yasa yad’ore haka har gidan aurensu.
‘Yammata kam dayawa sun k’yasa saidai sun 6oye kodan Rahma.
Bayan jawabin manyan bak’i da nasihohi taro yatashi lfy, daga nan akayi hotuna kowa yakama gabansa.
Kowa yana zuwa gida yafara shiri a gaggauce Dan ana sakkowa daga masallaci za’a d’aura auren.
Kowa yafito anata shiga mota Dan tafiya sallar juma’a da d’aurin aure.
Masha ALLAH nafad’a yayinda na hango muku ango Bobo yaci kwalliya cikin Sky blue d’in shadda harda babbar riga, wayyo masu karatu bayyana muku k’yan dayayi 6ata lokacine, ammafa ya had’u.
Masallaci suka nufa.
Bayan sakkowa suka wuce anguwar su Rahma.
_Alhmdllh anguwar tacika mak’il da jama’a, wasuma akan mota suke zaune, gurin yacika har babu gurin faking, dukda nisan da su Rahma suke dashi da titi, wasu sai abakin titi sukayi faking motarsu._
K’arfe 3:30pm d’umbin al’ummar Annabi suka shaida d’aurin auren *_”Abdulmalik Aliyu Abdulmalik hamshak’i, da amaryarsa Rahma Bilal Basheer mai Gold. “_*
(To ango da amarya saimuce ALLAH yabada zaman lfy da fahimtar juna ameen).
Dak’ar na iya samo muku Rahma amarya ad’akinsu itada gayyar k’awayenta Wanda yawanci duk yaran family nasune, wasu kuma ‘yan islamiyyarsu da boko.
Tahad’u cikin less ja mai adon farin siton masha ALLAHU, amarya tafito ras saidai mak’iyi.
anacewa and’aura auren tafara kuka, su Ihsan suna lallashinta.
(To Rahma sai hak’uri aii).
*_Safna_*
Safna ana gidan su ya kamal, ita adole tayi gudun hijira, ko wanka batayiba bare kwalliya, tana kwance ad’akin Ameera tana chart abinta hankali kwance, fira suke da k’awayenta a group suna tsokanarta wai tamusu bak’inciki, dayanzu sunata shan shagalin biki.
Dariya tayi ta ce, ” karku damu aii kwanannan zakusha bikin nida bobona.
Toma ALLAH ya kaimu…
Kafin tabada amsa Zainab autarsu Ameera tashigo tana fad’in an d’aura aunren.
Wata gagarumar fad’uwar gaba tariski safna dake kwance, tadafe k’irji tana fad’in ya salam, saikuma ta sauke ajiyar zuciya takoma takwanta, haka kawai taji jikinta yayi sanyi, zuciyarta tayi k’unci.
Zuwa wani lokaci kuma saitaja tsaki, tomima zai dameni tunda ALLAH ya tsallakar dani daga wannan auren k’addarar.
Rahma ALLAH ya yanka miki kazar wala sai aje aita figa.
Sainazo gayyatarki aurena da Bobo na…..
Na ce, “hummmmm.💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 13
Biki yacigaba da gudana cikin farin ciki da Annashuwa, gidajen biyu anata hada hada.
Bayan kammala d’aurin aure anguna suka shigo cikin gida akayi gaishe gaishe da hotuna, itadai Rahma koda wasa bata yarda sun had’a ido da Bobo ba har aka gama hotuna suka tafi.
Shikam jinsa yake wani iri kuma cikin nishad’i, komai na Rahma yana burgeshi, musamman yanda take komanta cikin sanyi.
Haka suka k’arasa gidasu, nanma cike yake da mata, tunda suka shigo akai caa kan bobo, sai tsokanarsa su aunty Rasheeda sukeyi, baya cewa komai saidai murmushi.+
+.+.+.+.+.+.+.+.+.+.+
*_5:30mp_* aka gama shirya amarya domin mik’ata gidan angonta, tana falon Abba inda dangi suka zagayeta anata nasiha gareta, sai rabzar kuka take tamkar zata shid’e, ummi ma kuka takeyi Dan takasa cewa komai yayinda aka kaimata Rahma gabanta dan taimata nasiha, babu abinda take fad’i sai ALLAH yay miki albarka Rahma, yanda kikai mana biyayya kema ALLAH yabaki ‘ya’ya masu yimiki, kuka yaci karfin ummi takasa cigaba.
Haka aka hak’ura aka fito da Rahma, Abba dakansa yasakata mota tanata kuka, ya Hamza dazai tuk’a amarya jiyayi tabashi tausayi, shima kamar yay kuka yakeji.
Kuka sosai Rahma takeyi abin tausayi, momyn su Ihsan da Maman Basma suka shiga motar suma, tsakkiya suka saka Rahma daketa kuka har numfashinta na d’aukewa.
Yayinda Abba yaga motocin amarya sun Lula, yatabbatar da gsk yau Rahma ta barsu, sai kawai yaji hawaye sun cika masa ido, yasa gefen rigarsa ya share tareda juyawa gida.
Canma tararwa yayi ummi NATA kuka, yashiga lallashinta damata nasiha.
Gayyar amarya ta isa gidansu Bobo, Dan nan za’a ajiye amarya sai gobe idan ALLAH yakaimu amaida ita gidanta.
Har cikin harabar gidan aka shiga da motar amarya.
Suna fitowa saiga Ammi da gayyar k’awayenta, wasu sosuke kawai suga mace mai sa’a data samu bobo amatsayin miji, Dan sunsha bashi ‘yayansu amma ya ce, a’a, (basu San itama had’asu akayiba ba soyayya bace).
Sanye Rahma take cikin shadda ruwan madara zani da Riga, ta lullu6a da k’aton mayafi ruwan k’asa mai turuwa, hakama takalmin k’afarta, kanta arufe yake shiyyasa masu tsogumi basu ganiba, Ammi tarungume Rahma tana lallashi, kama hannunta tayi takai har cikin d’akinta na sama, lallashinta tad’anyi na minti biyu saida taga tad’an tsagaita da kukan sannan tafito aka tura k’awayenta.
Gida ya harmutse Dan cike yake dank’am da jama’a, gashi yau Ammi takeyin yinin biki dama.
Sai bayan magriba dangin amarya suka juya domin zuwa suyi shirin tafiya wajen dinner daza ayi k’arfe 8:30pm to 12:00.
Gidan yad’an rage hayaniya kad’an tunda mutanen sund’an ragu babu laifi.
Duk wannan hidimar da akeyi bobo yana can cikin lambun gidansu da aka k’awata da haske, shikad’aine zaune akan kujera mai lilo idonsa alumshe yana duniyar tunanin rayuwarsa shida marigayiyya Ni’ima.
Yatuna itama haka akaiyi aurensu baya sonta, Dan ko taro d’aya bai halartaba alokacin na shagalin bikinsu, shiyyasa yake mamakin wannan karon komai Appa yace yayi baya musu saiyaje yayi.
(Wata zuciyarsa ta CE sannan ai kana kan hayak’in samartaka ne).
Hakane kuma yafad’a afili.
Bud’ar data cika gidance da k’aruwar hayaniya ta tabbatar MASA da amaryarsa ta iso, yamatse idonsa dake arufe tareda fad’in ALLAH yajik’anki Ni’ima ta, kifahimceni ba laifina baneba, nima sakani akayi dole badan inason aurenba.”
Jiyay tamkar maganar Ni’ima acikin kunnanensa tana fad’i masa, _”karka damu mijina Nima zanyi farincikin kasancewar Rahma amatsayin matarka, kodan tarin alkairai dake tartare da ita, na tabbata Nawal tasamu uwa tagari wadda kullum take maka nacin samu, INA tayaku farincikin mallakar Rahma kaida Nawal, ka kwantar da hankalinka kakuma rik’eta amana”._
Shirun dayajine yasakashi mik’ewa zumbur yafara dube dube da mutsike idanu, Kodai mafarki yakeyi?, da gsk fa muryar Ni’ima yaji wlhy.
Jikinsane yafara Rawa, cikin Sauri yabar cikin lambun Dan aganinsa wata aljanace takeson bud’e MASA ido.
Cikin hanzari ya iso harabar gidan inda su ya ishaq suke, Dan bandasu wajen maida ‘yan kawo amarya.
Najeeb abokin ya Ishaq ya ce, “ango lfy kuwa naganka a hargitse?, ko duk murnar zuwan amaryarne?.
Saurin saisaita nutsuwarsa yayi ya sauke ajiyar zuciya yanajan farar kukera d’aya ya zauna, babu komai ya Najeeb yafad’a ad’an d’arare.
Wai tun d’azu kana ina?, ya Ishaq ya tambayeshi.
Ina lambu.” Yabada amsa atak’aice.
Hira su ya Ishaq sukeyi amma bobo kokad’an baya sakamusu baki, addu’oi kawai yake zabgawa azuciyarsa, fatansa ALLAH yasa abinda yaji ya tsaya iya haka.
Suna nan zaune har aka kira sallar isha’i suka tafi sukayi.
STORY CONTINUES BELOW

Amarya tanacan ana zabga mata kwalliya, da k’yar aunty Sameera da aunty ummy suka lallasheta tayi shiru aka fara kwalliyar.
Hummm amaryafa tagama had’ewa abin kamar babu gobe.
Shiryata akayi cikin farar doguwar riga ta aure, amma mai dogon hannu, aka nad’a mata d’aurin d’ankwali da bak’in d’an kwali, tasha sark’ar gold wadda k’yautace daga Abba, kai jama’a yaufa take sallah, amma awajen amarya da ango, amaryakam tayi d’am kamar kasaceta ka gudu, na tabbata ko bobo yagani yau saiya narke.
Shimadai ba’a barsa abayaba wajen d’aukar wanka cikin farar shadda harda babbar riga, ya murza bak’ar hula sai kyalli takeyi, sajensa da sumarsa sun kwanta luf luf sai tashin k’amshi yakeyi, cikin hanzari yake d’aura agogon azurfa ahannunsa saboda masifar da ya sulaiman yake masa.
Haba Abdulmalik kai kullum sai anjiraka?, aurenka nefa, kai yakamata ace komai kana gaba amma kaine abaya haba Dan ALLAH.”
yi hak’uri nidai ya sulaiman muje nagama aii.
Haka suka fito sai zabga k’amshi yakeyi, yaukam amarya tarigasa, Dan tuni tana mota, bud’e masa Ridwan yayi yashiga inda Rahma take.
K’amshinsu yahad’e Dana mortar ga sanyin AC saiya bada wani yanayi mai dad’in gsk.
Rahma kam lumshe idanunta tayi dataji shigowar Bobo motar, kanta na k’asa Dan bataso su had’a ido ko kad’an.
Shikam saida ya zauna sosai harma sun fita daga gidan sannan yakai kallonsa kan Rahma da k’amshin turarenta ya addabesa.
Tsigar jikinsace ta tashi yarrrrrrr O ALLAH, yafad’a ahankali wandda har Rahma taji furicinsa, wani Abu yaji yana mintsinin zuciyarsa, da k’yar yay control d’in kansa, murya k’asa2 ya ce, yauma aramin fos d’inki.
Bata kalleshiba tamik’a masa bak’ar fos d’in wadda tasha adon fararen duwatsu sai kyalli suke.
Jiki a sanyaye yak’ar6a, yauma kud’i yazuba mata, rafar ‘yan d’ari biyar Biyar, sababbi k’al.
Bai bata fos d’inba har suka isa wajen taron, itakuma bata tambayeshiba.
Bayan tsayawarsu Ridwan yabud’e musu suka fito, Rahma tana tsaye har bobo yak’arso wajen, hasken wutar lantarkin daya yalwatu awajen yabashi damar k’are mata kallo sama da k’asa, itadai kanta na k’asa Dan dukta Raina kanta kallon dayake mata.
Murmusawa yayi Dan ganin yanda take sinne kai k’asa, fos d’inta yamik’a mata, tasaka hannu biyu takar6a tareda fad’in ngd.
Baice komaiba yagyara tsayuwarsa suka jera.
A Bokansa da ‘yan uwa samari da ‘yammata duk suna bayamsu kowanne shida budurwa d’aya, gabansu kuma Nawal ce da Kaleel d’in ya Ishaq, suma anmusu kwalliya cikin kaya kamar su Rahma doguwar Riga Nawal, Kaleel ma kwalliyarsa kamar ta bobo harda malum malum.
Abin ya k’ayatar da jama’a masha ALLHU.
Ahankali taji Bobo yasak’a hannunsa mai azabar laushi da sanyi cikin nata, da sairi ta kalleshi, shima kallonta yayi da sauri danji wani laushi na musamman da hannun nata yakeyi, k’asa ta maida kanta danjin wani yarrrrr ajikinta saboda lallausan murmushi da Bobo yasakar mata.
Tafiya sukeyi ahankali Rahma tana zancen zuci, tunda aka fara bikinnan koda wasa bobo bai ta6a jikintaba sai yau, saikuma jiya data kusa fad’uwa awajen mothars night, wannan kuma takalleshine amatsayin taimako daya bata dankarta fad’i. Dan haka k’irjinta ya hau luguden daka, (zuciyarta ta ce, “yanzu kinzama matarsa sa6aninda daba halalinsa bace ke.)
Kobabu komai ya burgeta, tunda yakasance mumum mai sanin muhimmancim addininsa da bin dokokin ALLAH.
Har suka k’arasa inda aka tanadi kujeru biyu ajere dansu, saida tafara zama haryanzu hannunta na cikin nasa, sakin hannunta yayi ya tattare babbar rigarsa ya zauna shima fuskarsa ad’an sake babu laifi.
Nawal dasuka rakosu tazo kusada shi tatsaya, baby tafad’a ahankali.
Kallonta yayi yamata murmushi tareda kamo hannunta, babyna kinyi k’yau yau, miya faru?, tayi ‘Yar dariya bakomai baby amma wacece wannan?.
Juyawa yayi yakalli Rahma da kanta ke ak’asa tana wasa da duwatsun jikin fos d’in ta, yay murmushi.
Zan fad’a miki amma ba yanzuba, kije ga ya Kaleel can yana kiranki Ku zauna wajensu momy.
To baby bye, tafad’a tana sauka daga wajen.
Shima hannu yad’aga mata yana murmushi.
Taro aka cigaba da gudanarwa yanda yakamata, yauma amarya da ango basuyi rawaba, saidai lik’i dasukaita zubama juna, yayinda dangima suka rufesu suna lik’a musu suma, mai wak’a yaga ruwan kud’i yakuma haukacewa yana wak’e ango da amarya.
Bayan sun koma mazauninsu akace su yanka cake.
Mik’ewa sukayi suka k’arasa inda aka ajiye cake d’in mai hawa uku, Wanda tasha ado mai k’yau, Rahma aka umarta tafara d’ora hannunta akan wuk’ar, sannan Bobo yad’ora nasa hannun akan na Rahma, bayan k’irga uku suka yanka, tafi akayi Raf raf raf.
Akace Rahma taciyar da Bobo, kunya dukta isheta amma yazatayine, haka taciro daidai bakinsa ta rissina tasaka masa abaki idonta ak’asa, aka kuma sakin tafi, tasaka masa kofin lemo abaki, kur6a biyu yayi tajanye tasaka hanky tagoge masa bakin, ihu aka saka ana bata tafi.
Itadai kanta nak’asa tayi d’an murmushi, bobo madai murmushi yakeyi.
Shima akace yabata.
K’aramin shima yaciro, yamatsa daf da ita sosai tamkar zai shige jikinta, batayi auneba taji yasak’alo hannunsa ak’ugunta, ajiyar zuciya ta sauke ahankali.
Cake d’in yasaka mata abaki, tafi mai k’arfi aka bashi, fuskarsa d’auke da murmushi yasaka mata cup d’in lemo, ku6arta d’aya ta kauda kai, yasaka hanky shima yad’an goge mata baki kad’an saboda janbakinta, sai kawai taji yabata Sumba akumatu (kiss) wani ihu aka saki gaba d’aya wajen ana tafi.
Rahma jitake kamar zata nitse awajen Dan kunya, gashi yak’i sakinta.
Dahakadai taro yatashi lfy, bayan hotuna da aka yi.
Amarya da ango suka shiga mota aka maidasu gida.💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 14
Kowa yagaji, ana shiga gidan gurin kwanciya kawai mutane suke nema.
Rahma kam harma tafara barci a mota, saida bobo yatada ita, aiko ko kallonsa batayiba tafice saboda kunya.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Wanka yafarayi sanan yay shirin barci, kad’an kad’an saiyayi tsak’i dad’an cije le6e, candai yakasa jurewa yakira khursiyya.
Duk suna d’akin Ammi inda Rahma take harda matamsu ya Sulaiman Dan suma yau anan zasu kwana.
Sunata shirin Barci aunty Rasheeda na tsokanar Rahma tanata murmushi da 6oye fuska.
Aunty ummy tamik’oma Khursiyya wayarta.
Kai aunty waye Dan ALLAH a darennan?, ke Bobo nefa.
Ya bobo kuma?, lfy bayanzu muka rabuba?.
Cikin tsokana aunty Sameera ta ce, “kika sani ko muryar matarsa yakesonji…….. Dariya sukayi yayinda Khursiyya tad’aga wayar tasaka akunne hello yaya.
Muryarsa can k’asa ya ce, ” kidafamin Lipton kimatsa lemon tsami biyu manya aciki, baijira amsartaba ya yanke wayar.
6ata rai Khursiyya tayi tamkar zatayi kuka ta ce, ”kai wlhy nidai nabani, daga dawo ga barci inaji amma zaiwani sakani aiki, ALLAH yasa abaka matarka gobe kuwuce muhuta da saka aikin tsiyarka…….
Lafiya kekuma aunty Rasheeda ta tambayi Khursiyya?.
ALLAH ya Abdulmalik d’innan ne, wai atsohon darennan zaisha Lipton Dan iyayi harda lemon tsami, nibansan tsiyar dayakeji ashan Lipton da lemon tsamiba.
Dariya su aunty Rasheeda suka kwashe da ita harda tafawa, aunty Sameera ta ce, “aii dolene yay control kansa da lemon tsamin irin wannan Sumba d’azu dayabama amarya awajen Dinner, o ni Abdulmalik anaso ana kaiwa kasuwa, suka k’ara shek’ewa da dariya.
Itadai Khursiyya fita tayi tana k’unk’uni da kumbura Baki, Dan batasan Inda zancen matan yayen Nasu yadoba.
Itama Rahma ba fahimtarsu tayiba, Dan haka ta tashi tashige bayi dan k’imtsa jikinta.
Akicin ta iske Ammi tana d’ibar abinci.
Ke kuma lfy baki kwantaba?, wakikema k’unk’uni ma haka?.
ALLAH Ammi ya Abdulmalik d’innan ne mana, wai adarennan zaisha Lipton hardasu lemon tsami, kawai salon saka aiki.
To idan kinyi hak’urima aii yaune kawai, gobe iyanzu yana gidansa.
Hakane ammi, ammafa kullum kamar ibadar ALLAH saiyasha shayinnan. Azuciyar Ammi saitake mamakin halin Abdulmalik, yana cikin damuwa amma bazaiyi aureba sai ammasa ta k’arfin tsiya, shidai halinsa daban acikin ‘yayanta, ALLAH ma kad’ai yasan tun yaushe yake acikin wannan halin.
Afili kuma saita girgiza kai tana fad’in kidafa masa to dare nak’arayi.
Bayan fitar Ammi Khursiyya tadafa Lipton tanata mita, ta matsa masa lemon tsamin sanan tasaka a k’aramin tire tafice zuwa d’akinsa.
Akwance tasameshi rufda ciki, sanye yake cikin kayan barci.
Yaya gashi tafad’a tana ajiyewo.
Baice mata k’alaba bare ya d’ago.
tajiye tafito cike da haushi, babu yanda za’ayi yasaka ka aiki kaimasa yaymaka godiya bayan kagama, duk cikin yayinyunsu shine halinsa da ban, duk masifar ya ishaq yafi yaya bobo sauk’i.+
Shikam kobayan fitarta yakai Monti Biyar sanan yatashi zaune yana matse fuska.
Dukda turirin da shayin yakeyi saboda zafi, haka yayta shansa yana cije le6e, yana gamawa wata zufa tafara karyo MASA adukkan sassan jikinsa.
Kwanciya yayi ahankali yana sauke numfashi, bayan wani lokaci yasamu nutsuwar sarayar ciwon nasa.
Kwanciyarsa yagyara barci yay a won gaba dashi.
*_washe gari_*.
K’arfe 10:30am aka fara gudanar da sisters day aharabar gidan, masha ALLAH komai tayi k’yau, yaudai basuga idon bobo ba, yana d’aki kwance barcinsa yaketa kwasa na gajiya.
Sisters day kam yabada ma’ana, amaryama yau tasha k’yau, su khairiyya sun raba k’yaututtuka taro yatashi lfy.
2:00pm aka gabatar da walima, mutane suka fara kama gabansu, wasuma bak’in sun wuce tun safe, wassu kuma sai gobe idan ALLAH yakaimu.
Rahma dum jikinta yayi sanyi tunda aunty ummy tashigo tace ta shiraya da angama sallar isha’i za’a mik’ata gidanta.
Kallo ihsan dake zaune Kusada ita tayi, ihasan wai ina wayatane?, kwana biyu wlhy bangantaba nazata tana wajenki.
A’a wlhy wayarki bata a wajena, amma bari akira muji.
Kiran wayar suka farayi….
Bobo nazaune ad’akinsa yana danna laptop yaji wayar Rahma dake caji tana wringing, kamar bazai dubaba saikuma yamik’e yad’auka.
Ana d’agawa ihsan tamik’ama Rahma wayar tana fad’in and’aga.
Cikin sanyinta ta ce, “Assalamu alaikum.
Lumshe idanunsa yayi danjin sassanyar muryarta.
Wa’alaikissalam ya amsa cikin nutsuwa.
Gabantane yafad’i danjin murayarsa, taganeshi sarai amma saita dake ta ce, ” Dan ALLAH wanene?.
Jin haka shima saiya basar ya ce, “kema wacece?.
Mai wayarce, Dan ALLAH ya akayi tazo hannunka?.
Murmushi yayi tareda shafa gemunsa na gayu, ya ce, ” mijinkine, nasamu wayar ahanunkine kuma.
Ajiyar zuciya ta sauke, muryarta nad’an rawa ta ce, “to shikenan.
Yanke wayar yayi kawai yana murmushi shima.
Ihsan dataji komai bata Neman k’arin bayani dantaji komai.
Screen d’in wayar yadasama ido, photon Rahma ne ajiki da Safna, sunyi masifar k’yau ahoton.
Tunda wayar tazo hannunsa baita6a tunanin dubataba, Dan tunda ya ajiye baibi takantaba, yau yaji tanata kukan k’arewar caji shine yasaka mata cajin.
Yad’an lumshe idon yabud’e akan wayar, kowacece wannan kuma?, yafad’a aransa.
K’ila yayartace, (wadda tace bata sona kenan?) Afili yay maganar, bakinsa yata6e yana k’arema safna kallo, tabbas tafi rahma k’yau, amma Rahma tafita kwarjini da fuskar kamala.
Bakinsa yak’ara ta6ewa yamaida wayar a caji.
Hawowa gadon yayi yacigaba da aikinsa.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Bayan Sallar isha’i Rahma tagama shiri cikin kyakykyawar Shiga ta material siket dariya, tayi k’yau sosai kuwa, sai tashin k’amshi turare takeyi.
Haka wasu k’alilan daga cikin danginsu, dakuma su aunty Rasheeda sukai mata rakkiya had’ad’d’en gidan Bobo dayasha gyara tamkar sabo.
Idonta na rufe tanata sharar kuka, da tunanin gamonta da ango yau, koyaya zai k’ar6eta kuma?, dukda yanuna mata kulawa awajen taron bikin hakan baya tabbatar mata dazata samu kulawarsa ayayin zamansu.
Dan zai iya yuwuwa yayima iyayensa biyayyane kamar yanda itama tayima nata biyya……
Da wannan tunani su aunty Rasheeda sukaimata sallama harda su ihsan suka tafi.
Kuka sosai tashiga rabzawa harda shashsheka, tana tausayama kanta da rayuwarta. Amma tana rok’on ALLAH tazama mai hak’uri da juriyar biyayya ga ALLAH da MANZONSA, dakuma iyayenta.
Zamewa tayi ta kwanta tana cigaba da kuka maiban tausayi da tsuma zuciya.
.*……*…….*……..*…..*.
A6angaren Bobo kam yana d’akinsa harya kwanta hankalinsa kwance.
Ammi takalli agogon falon karfe 9:53pm amma har yanzu Bobo bai fito yatafi gidansaba.
Mik’ewatayi ta haura saman Dan gidan mutane sun ragu sosai.
Kallon mamaki tabisa dashi.
Shima yad’ago yana kallonta, Ammi na lfy kuwa?.
Lfy lau, mikakeyi har yanzu baka tafiba?.
Cikin mamaki ya ce, “Ammi ina kuma zani?.
Gidanka mana.
Gidana kuma?, Ammi canakefa sai gobe?.
Harararsa tayi, cikin d’an fad’a ta ce, ” tunda d’azu su Rasheeda suka dawo daga rakkiyar matarka, amma kananan zaune, katashi katafi gidanka anbarta ita kad’ai, nasan tanacan atsorace.
Bata jira amsarsaba tafice afisace.
Ajiyar zuciya yasauke yana turo baki gaba kamar wani k’aramin yaro.
Haka yatashi ya canja kaya kamar zaiyi kuka Dan haushi.
Farar shadda yasaka sai maik’o takeyi, yad’ora jar hula da silifas ja mai k’yau, turare yafeshe jikinsa dashi, sannan yajawo jakar lop-top d’insa yasaka duk abinda zai iya buk’ata na 6angaren aikinsa, yakashe kayan wutar d’akin yafito sai zabga k’amshi yakeyi.
Ammi yatarar afalonsa tana jiransa, ganin ranta ad’an 6ace yasa yasaki fuska, cikin murmushi da zolaya ya ce, “Ammi na nayi k’yau.
Itama fuska tasaki tana kallonsa, ta ce, ” masha ALLAHU Mukarram d’ina kayi k’yau sosai, ALLAH yaymaka albarka kaji, yabada zuri’a tagari, ya albarkaci wannan aure.
Biyayyar dakake mana ALLAH yasa kaima ‘ya’yanka suyi maka.
Ammin Ammi na ngd sosai da addu’arki gareni, bari naje wajen appa namasa sallama ina baby mutafi?.
A’a ita ba yauba, sai bayan sati d’aya tukkuna.
Ammi saboda mi?, cikin shagwa6a yay maganar.
Dariya ammi tayi ta ce, “shagwa6a66ena sai angama amarci tukkuna, idan d’iyata tagama hutawa da gajiyar biki saikazo kad’auki Nawal d’in.
Shike nan ammi, amma…….
Katsesa tayi da fad’in kaga jekayima Appanku sallama dare nak’ayi.
Haka yahak’ura yanufi d’akin Appa, bayan sun gaisa yaymasa nasiha sosai da saka masa albarka sannan yafito yatafi.
Mota yashiga yabar gidan cike dakewar iyayen NASA.
Awajen wani gasa naman kaza ya tsaya, yasayi guda biyar sai k’amshi sukeyi, yasayi kayan fruit dayawa yanufi gidansa zuciya acinkushe da tunani kala kala………..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 15
Hon yayi mai gadi yabud’e masa gate, saida yatsaya suka gaisa sannan yay cikin gidan, guri yasamu yay fakin zuciyarsa cike da tunani kala2.
Yafito tareda kwasan kayansa yanufi ciki, tafiya yake tamkar bayaso, zuciyarsa cike da waswasi, yaushe rabonsa da gidan nan a rin wannan lokacin?…… K’ofar falon yabud’e yashiga, wani k’amshin dad’i yadaki hancinsa, yashak’a ya lumshe idannunsa sannan yabud’e, bin ko INA na falon yakeyi da kallo, komai masha ALLAH, Iyayen amaryar tasa sunyi k’ok’ari gsky, komai na falon farine da ratsin golden.
Hasken fitilun yak’ara yalwata k’yawun falon sosai, ajiye ledojin yayi yad’au jakar lap-top d’insa kawai yanufi d’akinsa.
Yazube kayan tareda fad’awa saman gado yana fad’in wash ALLAH na.
Yay lamo yana tunani Wanda bansan namiyeba, yakai minti goma ahaka sannan yatashi, harya fara cire ma6allin wuyan rigarsa saikuma yatsaya yana tunani, koba komai yakamata ya lek’a d’iyar mutane, k’ilama bataci komaiba, mik’ewa yayi yafito falon, kicin yafara shiga yad’auki filet da Kofi yadawo falo yasaka kaza d’aya afilet d’in, hakama kayan fruits d’in yazuba awani filet d’in daban, yad’orasu saman babban tire harda ruwa da fresh milk sannan yanufi d’akin.
Tiren ya ajiye ak’asa saman kafet d’in dake gefen lafiyayyayen gadon nata, yabita da kallo tana kwance ta takure waje d’aya kamar tanajin sanyi, yad’anyi tsaki yana kauda kansa daga kallonta, “k! Yafad’a ad’an kausashe.
Komotsi batayiba Dan bama tasan yanayiba, fuska yak’ara had’ewa yana kuma fad’in ” k!! Wai bak’ya jinane?, ganin bata motsaba har yanzu yasashi matsawa Kusada ita daf, ashema barci takeyi yak’arshe maganar da tsak’i. Hannunsa yasa ya bubbuga filon data saka kanta, firgigit ta tashi tana kad’a manyan danunnan NATA masu suffar kwai.
Kauda idonsa yay daga kallonta Dan idanunta suna masifar tafiya dashi babu k’arya, ga abincinan kitsashi kici yay maganar yana k’ok’arin ficewa daga d’akin.
Ngd, amma nak’oshi, nitsatstsiyar muryarta ta daki kunnuwansa, bai juyoba amma yatsaya, hannayensa cikin aljihu wandonsa ya ce, “wannan yarage kuma naki, yay waje abinsa.
(Ni bilyn Abdul nace sabon salo, bobo Yakuma zaka canja mana?, bamuyi zaton hakabafa☹).+
Itakam Rahma hawaye tamatso takuma komawa takwanta, saida tayi kuka mai isarta sannan ta tashi zaune, afili ta ce, ” dama nasan bazan samu farincikiba, duk wata kulawa Daka nunamin awajen taron bikin naganin idon danginane danaka, ya ALLAH ka kawoma rayuwata d’auki, kodan darajar biyayya danaima iyayena, nashare musu hawayensu alokacin dasuke zuba, Nima ALLAH kaji k’aina ka daidaita zamana da mijina yafuskanceni tamkar kowacce mace, takuma rushewa da kuka.
(Ayya Rahma tabani tausayi gsky).
Sauka tayi daga gadon tad’auki tiren tafito, kicin tanufa Dan saida su aunty Sameera suka Nuna mata ko INA na gidan kafin su tafi, firij tabud’e ta saka komai Inda taga yasaka sauran, tad’auki fresh milk d’in da kofin tafito.
ko tsayawa kallon falon batayiba takoma d’aki, saida ta kulle k’ofarta sannan tacire kaya tayi canji Dana barci.
Zama tayi bakin gadon tasha fresh milk d’in sosai sannan tashiga bayi tai burosh tadawo tai kwanciyarta bakinta d’auke da addu’ar barci.
Shima yana komawa d’aki kayan jikinsa yarage yasaka na barci yahau gadon yazauna, jakar dayazo da ita yabud’e ya fiddo lap-top d’insa yafara aiki.
Ganin ba kwanciya zaiba nayo waje nikam Dan barci nakeji sosai.
_washe gari._
Da asuba kafin yawuce madallaci saida ya kwankwasa mata k’ofa, saida yaji alamar ta tashi sannan yafice.
Jin yafita takoma tayi kwanciyarta Dan har yanzu tana Hutu.
Saida gari yay haske sannan bobo yadawo gida, barci Yakoma abinsa Dan yana buk’atar Hutu sosai.
*_7:48am_*
Rahma ta tashi, wanka tafarayi sannan tagyara gidan tsaf dukda ko ina fes yake amma tak’ak’k’ara gyarawa, tabud’e ko ina da k’amshi, tana k’ok’arin komawa d’aki taji ana kwankwasa k’ofa, saida tad’anyi shiru nawani lokaci sannan. Tanufi k’ofar tabud’e, ganin khairiyya da khursiyya yasata sakin murmushi, hanya tabasu suka shigo sannan tamaida k’ofar tarufe.
Itama zama tayi suka gaisa (Dan zasu iya zama sa’anni itada tagwayen Ammin), ta ce, “yasu Ammi?.
Lfy lau tanama gaisheki, ga break fast tace akawo muku.
ALLAH sarki Ammi mungo sosai.
Khursiyya ta ce, ” Yaya fa?.
Saida tayi k’asa da kai sannan ta ce, “yana barci bai tashiba.
Khairiyya da khursiyya suka kalli juna suna dariya, saikuma suka mik’e tomu bari muwuce sai anjima.
Kai haba dawuri haka?, ALLAH nazata anan zaku wuni.
Rufana asiri wannan mijin naki bayason warigi, khairiyya tafad’a ahankali.
Saida tarakasu har bakin k’ofar sannan tajuyo ciki, kwandon abincin ta d’auka takai dinning, ta ajiye komai inda yadace, taje kicin tad’akko duk abinda za’a buk’ata ta ajiye, abincinta tad’iba takoma bedroom taci.
Bobo kam ana gado ana kwasar barci, sai 10+ yatashi yay wanka yashirya cikin k’ananun kaya yayi k’yau sosai masha ALLAH, yaci sunan nasa Bobo.
Yaji dad’in ganin falon fes dagani kasan yak’ara shan gyara, baibi takan Rahma ba yanufi firij d’in dani danufi d’aukar fresh milk yasha saiyaga abinci, ganin kamar kulolin gidan Ammi yasa yazauna yaci abincinsa yay nak sannan yafice.
(Araina nace yadace ace yalek’a yaga yata kwana aii).
Rahma tanajin fitarsa, danhaka tarabga tagumi tana tunanin sabuwar rayuwarta ta yanzu.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Asibiti yanufa Dan duba yarinyarnan da akaima fad’e, jikinta yayi kyau sosai Alhmdllh, saidai har yanzu bata magana, tsakaninta da Bobo saidai kallo, tana bashi tausayi sosai Dan yanajinta tamkar Nawal, yasan idan Nawal ce ko cikin ‘yayan yayensa ko k’annensa mata biyu wata tashiga irin wannan halin yasan zasushiga cikin tashin hankali fiyema da haka, ALLAH kad’ai yasan itama halin da iyayenta suke aciki yanzu………jiyowa yayi dasauri danjin an ta6asa, ya Sulaiman ne.
Kaikuwa miya fiddoka da sassafennan?.
Haba Yaya yanzune safiyar?.
Harararsa ya sulaiman yayi, ya ce, “amatsayinka na sabon ango wanda aka kaimar sabuwar amarya jiya baikamatama duk yau aganka awajeba, kai daganan harma sati d’aya.
Hummm Yaya kenan, amma yanada k’yau nazo naga jikin yarinyarnan, kagafa tunda aka fara bikinnan bana samun damar zuwa.
To aii yanzu kaganta saika koma.
Yay…… Hannu ya sulaiman yad’aga masa alamar baya buk’atar jin komai.
Bayanda zaiyi haka yaymasa sallama yatafi.
Indai tak’aicemuku bayani yau tsawon kwanan amarya takwas bata saka angonta a idoba, sadai taji motsin shigowarsa da fitarsa, ko motsin cin abinci, kulum tana d’aki, inkaga tafito wani Abu zata d’auaka shima saita daidaici baya falon.
Aganinta shine yakamata yajata ajiki ya sake mata, tunda shine mai gidan, ita yanzu tamkar bak’uwa take agidan.
Shikam yana ganin ita yakamata taringa masa abinda zai sake mata d’in Dan da wannan halin Ni’ima tai saurin cafe zuciyarsa har yake ganin tafi sauran mata…………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 16
Kwance take akan had’ad’d’en gadonta Wanda yaji shimfid’u na alfarma, tajuya kwanciyarta zuwa rigingine, idanunta suka sauna kan agogon dake manne a bangon d’akin 3:42am.
Ta waro manyan idanunta Dan mamakin yanda lokaci yatafi, afili tafurta kai kenen na kwana banyi barciba?.
Taja dogon tsaki da k’arfi, dama da gsk ne idan mutum ya ce, “yakwana baiyi barciba?, gsky itakam tana k’aunar iyayenta, tanaso kuma tayimusu biyayya, saidai tunkan ayi nisa tafara hangen tarin matsaloli a rayuwar auren nata. Domin kuwa alissafinta yau kwana takwas da kawota gidannan, saidai tundaga randa aka kawota gidan bata sake saka angon nataba a idonta, saidai taji motsin shigiwarsa dakuma fitarsa, kocin abincinsa, idan tatuna kulawar dayayta bata awajen taron bikin saitaita mamaki wlhy, mutum tamkar mai aljanu, kodayake saitaga kamar itama akwai laifinta, tunda ad’aki take wuni, saidai idan taji yunwa tadameta tafita tad’ebo abincin da Ammi ta aiko musu, gidan kansa takasa nutsuwa taimasa kallon tsaf……..
Kwala kiran sallar asubane yadawo da ita hayyacinta, tamik’e domin gabatar da sallar, jitayi jikinta duk yayi nauyi saida tayi wanka sannan ta d’auro alwala.
Tana idar da sallah taji wani irin barci na d’ibarta, tashitai ta haye gado ta kwanta, cikin ‘yan mintuna barci yay gaba da ita.+
A6angaren bobo kam yamaida dukkan hankalinsa wajen binciko Wanda yayma yarinyarnan fad’e, sukansu ‘yansandan dukya addabesu da masifar basusan aikinsuba, sanin shi d’an babban mutumne yasasu dagewa sosai kuma ana hangen nasara zuwa yanzu.
Rahma kam yana buk’atar ganinta amma aganinsa ita yakamata tafara nemansa tunda shine babban, ganin kamar tana shamasa k’amshi shiyyasa yafita harkarta ya maida hankalinsa akan aiki.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Sai k’arfe d’aya Rahma ta tashi, takai dubanta kan agogo, kai harnakai haka ina barci?, lallai nasha barci sosai.
Wanka tashiga, bayan tafito tashirya cikin Riga da siket na atanfa kayan sun bala’in mata k’yau, tayi sallar azhur sannan tanufo kicin Dan cikinta yafara kiran ciroma, gashi jiya tacema Ammi adaina kawo musu abinci zata cigaba da girkawa, Dan aganinta yakamata tamik’e wajen juya akalar mijinta zuwa gareta.
Alokacin Bobo yana gidansu, Nawal tamak’ale masa saita biyoshi yakawota wajen momynta.
Ammi ta ce, “Mukarram inaga katafi da ita kawai nasan insha ALLAHU Rahma zata rik’eta da Amana, kasan yarinyarnan kullum burinta ta kasance da mamanta akullum.
Bobo yahad’iye yawu Ammi ba tafiya da Nawal bane matsalar ina ganin kamar idan nad’auketa ban k’yauta mukuba.
Ammi tayi murmushi Wlhy ko d’aya mukarram aii munsan ba k’waceta kayiba, dama tunjiya Appanku yay maganar yau idan kazo kawuce da ita.
To shikenan Ammi ngd, ahad’a mata kayanta to muwuce.
Ammi tahad’o mata kayanta, wasu kam sai ahankali aringa kaimata.
Nawal kam sai murna take yau zata wajen momynta.
Ammi bari mutafi naga Appa haryau bai dawoba, gobe idan ALLAH yakaimu ma had’u, Dan zan koma aiki.
Ammi ta ce, tom ALLAH yatsare, yakaimu lfy, tazo gefen Nawal tana d’aga mata hannu.
Bobo yatada mota, yauwa Ammi idansu khairy sun dawo suhad’amin kayana duka Nima.
To zan Sanar musu agaidamin da d’iyar tawa.
” zataji.”
Haka suka fice ammi da Nawal suna d’agama juna hannu.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Rahma na zaune a falo tazurama filet d’in indome idanu, dukda ‘Yar Karen yunwar datakeji amma abincin yagagara ciyuwa agurinta.
Tabi falon da kallo, caraf idanunta suka sauka akan wani hoton Bobo yana zaune akan wata kujera, fuskarsa d’auke da tsadadden murmushi mai kashe zuciya, saina kusadashi shida Nawal, wanikuma a can gefe shida yayyensa maza dasu Ammi da khursiyya da khairiyya, sunyi k’yau sosai, daka gansu Kasan ciki d’aya suka fito masha ALLAH….
DA gudu Nawal tashigo tana kiran Momy! momy!!, da Sauri Rahma tamik’e Nawal tafad’a jikinta, itama saita rungumeta.
Ahankali Nawal ta ce, momy I miss u.
Miss u too my baby Rahma tafad’a tana mamakin ‘Yar waye kuma wannan?.
Nawal takatse mata tunani da fad’in , momy inakikaje kika barni?, kullum saina tambayi baby da Ammi sai sucemin kina zuwa amma baki zoba.
Cikin mamaki Rahma tad’agota daga jikinta tana kallonta, gata ‘Yar mitsila sai zance irin na manya.
Bobo na a tsaye yana kallonsu, Wanda azahiri kallonsa akan Rahmane, Ashe k’yan dayake kallonta dashi awajen taron biki tafi k’yau a Natural batareda kwalliyaba….. Maganar Rahmace takatse masa tunani, ta kuma rungume Nawal tana fad’in tom gani nadawo babyna kiyi hak’uri kinji.
Ita sai yanzu tatuna ance mata Bobo yanada d’iyama, jitayi tausayin yarinyar ya mamayeta, ALLAH sarki Rayuwa, ALLAH baya Barin wani Dan wani yaji dad’i, tafad’a acikin ranta.
Nawal tazare jikinta tanufi Inda Bobo yake, hannunsa takamo cike da murna tana fad’in baby naga momyna yau.
d’an murmushi yayi ya ce, “natayaki murna babyna, karasowa cikin falon sukai yazauna.
Rahma ta daure ta ce, ina yini?.
Lfy ya amsa batareda ya kalletaba.
Rahma ta ta6e baki aranta ta CE, ” dama baka amsaba aii, dama na gaidakaine saboda kana gaba dani.
Maganar Nawal ce tasakata dawo da hankalinta Kansu, Nawal ce takai bakinta Kusada kunnen Bobo wai zata masa Rad’a, amma kuma kanajin maganar tata.
“Baby mikayima momy tak’icin abinci?, koka duketane?.
Da sauri Bobo ya kalli Nawal a’a baby ban daketaba, k’ila batada lfyane.
Tamaido dubanta kan Rahma, momy waibakida lfy inji baby.
Rahma tayi d’an murmushi A’a lfy ta k’alau, to momy idan lafiyarki k’alau miyasa bakici abinciba?, ko kinaso baby yabaki dakansane?……
Kafin Rahma tayi magana Nawal tamaida dubanta ga Bobo, baby kabama momyna abinci abaki kamar yanda kake bani idan nak’ici.
Bobo ya ce, “to baby idan banda abinki……. Da Sauri ta ce, “baby indai baka bama momyna abinci abakiba mun 6ata daga yau, ta tashi daga kusadashi takoma kan cinyar Rahma data daskare azaune danjin furicin Nawal.
Rahma tadaure ta ce, ”kinga babyna zanci dakaina, Dan lfy ta k’alau, kibar Dady yahuta kinga ya gaji ko, tashima muci tare.
Nawal ta tashi zaune, Rahma taringa bata abincin itama tana dannawa badan yaymata dad’iba, saboda damuwar dataima zuciyarta yawa.
Bobo yanad’an satar kallonsu, tabbas yaji dad’in yanda Rahma takar6i d’iyar tasa wadda akullum yake zullumin sama mata madadin mamanta data rasa……
Yanata tunaninsa harsuka mammala, Nawal ma tafara barci, mik’ewa Rahma tayi da ita zuwa d’aki, dama zaman dukya gundireta.
Yabita da kallo k’asa k’asa babu laifi tanada k’yau daga na fuska harna jiki, saidai bazai sotaba Dan Ni’imarsace kawai keda gurbin zama azuciyarsa.
“na ce, “hummmm ALLAH yasa.”
Itakam Rahma koda takwantar da Nawal saitayi zamanta bata sake fitiwaba, sai bayan sallar la’asar.
Sannan baya falon, tanufi kicin tana fad’in baridai yau nayi girki kodan Nawal, had’ad’d’en abinci na gargajiya tahad’a mairai da lfy, tagyara kicind’in tsaf kamar ba’ayi komaiba, hakama falon takuma bad’e ko ina da nau’in turarurrukan wuta.
Saida tayi Sallar magriba sannan tayi wanka tayima Nawal, shiri tayi cikin wando dariga na Pakistan sky blue, rigan iya cinya sai wandon yakamata sosai, amma tayi k’yau kamar kasaceta kagudu, itama Nawal tasaka mata ‘Yar Riga Mara nauyi.
Harzasu fito Nawal ta ce, “saita goyata, Rahma taduk’a Nawal tad’ane.
Falon suka fito inda ta tarar da Bobo zaune akan kujera mai d’aya ya d’ora k’afafunsa saman k’aramin tebir na gilas yana karanta jarida, gefensa lemo na kwali da Kofi anzuba rabi, yana sanye da wando 3/½ fari da riga ja Mara hannu.
Masha ALLAHU Rahma tafad’a azuciyarta.
Baby kalleni Nawal tafad’a tana d’agama Bobo hannu.
d’an d’agowa yayi ya ce, ” naganki baby yamaida Kansa.
Rahma tasauketa tana fad’in tonima gobe saikimin goyon.
Nawal tawaro idanu waje kamar wata babba, lah momy bazan iyaba saidai baby yay miki, taje tadafa bobo, baby.
Ya ce, “na’am.
Zaka ramama momy goyon data minko?, kagani ban girmaba, bazan iyaba..
Bobo yakalli Rahma dake zaune tana mamakin wayau da surutu irinna Nawal, Dan yau d’aya tafahimci Nawal d’in tanada shegen wayau irinna sai antona d’innan ake samun irinsu.
Ahankali ya janye idonsa yamaida kan Nawal eh zan rama miki.
Tanufo Rahma tana murna, momy taso baby yagoyaki kinji.
Rahma tayi murmushi k’arfin hali a’a babyna nayafe basai yagoyaniba, kinga muje kici abinci, tafad’i hakane Dan mantar da Nawal wancen zancen.
Ta kalli Bobo daya maida hankalinsa kan karatun jarida ta ce, “ga abinci dady.
d’agowa yay yana kallonta danjin takirasa da daddy, itakam tai k’asa da kanta, takirasa da dadyne Dan batasan yazatace masaba, kuma baikamata takira sunansa kai tsayeba.
d’an lumshe idanunsa yayi yana wani guntun murmushi, tabashi dariya wlhy, amma saiya dake, wai dady yakuma maimaita sunan azuciyarsa.
Haka yamik’e yanufi dinning d’in.
Tuwon shinkafane miyar Agusi wadda yaji busashshen Kofi da nama sai tashin k’amshi takeyi, saikuma lemon ayaba Wanda yaji had’i na musamman.
Aransa ya ce, ” ya akai tasan abincin danafi so ko Ammice tasanar da ita?.
Itadai Rahma tazuba masa komai tatura gabansa.
Tayi mamakin yanda yaci abincin sosai, Dan ita tayi tunanin zaice bayacin tuwo, tunda taga d’an hutune.
Bobokam abincinnan yaymasa dad’i jiyayi Rahma tak’ara girmaba a idonsa, taburgeshi sosai gata yarinya k’arama amma ta iya girki mai dad’i.
Bayan sun kammala suka dawo falo……….💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 17
*_SAFNA_*
Tun bayan biki ‘yan gidan suka fita harkarta gabad’aya, gaisuwarta kawai suke amsawa, itama aciki cikin.
Itako hakan bai dametaba Dan ta ce, “sagaji su sakkone tunda itaidai ALLAH ya tsallakar da ita daga auren dolen da akayi nufin k’ak’aba mata, to duk abinda zasu suyi tayi daga baya kenan.
Yau tana school, zaune suke itada k’awayenta zeenat da Baseera, hirarsu suke hankali kwance sunata shek’a dariyar shak’iyanci ga wani d’alibi bai suna Rabi’u, yayi wani dressing ne waishi adole babban yaro, yazo gurunsu yana fafa sukuma sai famfashi suke suna masa dariyar shak’iyanci.
*boy ne yak’araso wajen, tunda Safna ta hangoshi tafara washe Baki, ta ce, R.. Boy kaga k’ara gaba sai anjima mun had’u.
Sanin halin rashin mutuncin safna yasa Rabi’u barin wajen.
A’a *boy yayane?, incedai akwai labari mai dad’i?.
Aiko akwai labari mai dad’i saidai……..
Saidai me?, kai dad’ina dakai komai dad’in zance saika nemo abinda zai 6atashi, baseera tafad’a tana hura hanci, Dan halinsu d’aya da Safna, shiyyasa sukafi shiri.
Muzauna kabamu misha zeenat tafad’a cikeda shak’iyanci.
*boy yakalli zeenat, zee baby yanajiki tsit ne.
Zeenat tayamutse fuska, babu Marsala kawai ina mamakin k’awatane yanda tarud’e akan wanj, saikace wata sakarai.
Harara safna ta watsa mata, indai bazaki dad’i alkairiba to kiyi shiru, Dan indai bansamu guy d’innanba to bak’in bakinkine yajamin.
Ido zeenat tazaro to ALLAH ya k’yauta yasa kisamu guy d’inki k’awata.
Baseera ta ce, “yanzu kikayi magana *boy jamuje.+
*boy yagyara zama ya ce, ” guy d’inki sunansa Abdulmalik Aliyu Abdulmalik, amma ana kiransa da (BOBO), lauyane maizaman kansa, mai tausayin talaka da kwatar musu ‘yancinsu, danshi kud’i ba matsalarsa bace.
*boy yafara bama su Safna cikakken tarihin bobo daga farko har k’arshe, har aurensa nafarko da mutuwar matarsa, da kuma d’iyarsa Nawal.
Safna tazaro ido waje, *boy yanada d’iyafa kace?.
*boy ya ce, “shiyyasa nace, ” miki akwai Abu Mara dad’i alabarin, ayanzu danake gaya miki kwana goma kacal da aurensa……
Aure kuma!!!?. suka fad’a suduka arazane.
Jikin safna Yakama rawa, tamik’e arazane batareda sha’awar jin k’arshen labarinba.
Zeenat tarik’eta da sauri, safna ina kuma zaki?, hannunta tafusge cikin rawar murya ta ce, “gidan zanje.
Gida kuma?, munfa kusa shiga lecture.
Tsaki taja batareda tabata amsaba tayi gaba.
Zeenat ta ta6e Baki tana fad’in ‘Yar wahala.
Cikin masifa Baseera ta ce, “dammi zakice mata ‘Yar wahala?, soyayyafa ba k’arya baceba.
Nima aii bance k’arya bace, amma ta safna batada tsari, kuma kad’anmma tagani indai tak’amarta bijirema iyaye, ta tashi fuuuu tabar wajen.
*boy ya ce, “nifa kuji dani Basee, cikon kud’inafa”.
kaga dan ALLAH kaje idan mun had’u agida zanbaka, itama ta tashi tabar wajen.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Rahma tare sukai kwanciyarsu itada Nawal, koba komai tasamu ‘Yar tayon kwana da hira, barema harga ALLAH tanason Nawal, jiya kad’ai dasuka rayu tare taji son yarinyar sosai a zuciyarta, dawuri ta tashi ta had’a musu break, kasancewar su Nawal suna Hutu yanzu bata tada ita daga barciba saidai tagama komai na gyaran gidan.
Tana d’aki zatayi wanka Bobo yafito cikin shigar suit bak’ak’e hannunsa d’aukeda k’atuwar rigar lauyiyi, d’ayan hannun yarik’e da jakar aikinsa da hular lauyoyi, yau yanada shari’a k’arfe 9:30am.
Ganin babu kowa Afalon saidai yasha gyara sosai sai k’amshi ke tashi, yad’an lek’a d’akin Rahma batanan sai Nawal kad’ai kwance tana barci akan gado, ahankali yak’araso yaymata kiss akumatu sannan yafito, dinning yanufa Dan yanajin kwad’ayin k’aracin abinci Rahma ayauma.
Itakam tana bathroom tana shirin yin wanka taji k’amshinsa, takafar mukulli tad’an lek’o ta hangesa yanama Nawal kiss akumatu, a ranta ta ce ,”yau albarkacin d’iyarsa anshigo d’akina kenan?, dukda dai bai nemi inda nakeba tad’an ta6e baki.
Shikam yana gama lodama cikinsa abinnan mai dad’i dasaka kunnen maici mik’ewa yatashi tareda yin hamdala dasakama Rahma albarka, agurguje yafice Dan time yawuce sosai.
STORY CONTINUES BELOW

.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Ikon ALLAH ne kawai yakai Safna gida, tana shiga d’akinta tanufa Dan falo babu kowa tasan ummi tana barci k’ila.
Tafad’a kan gado jagwaf kamar wadda akacema Abba yamutu haka tashiga kuka rurus, saidai tayi mai isarta sannan tayi shiru danba mai lallashi, yauce rana tafarko dataji kewar Rahma, Dan dukda tsangwamarta datakeyi indai yarinyar taganta cikin damuwa ita take lallashinta da kwantar mata da hankali, amma yau tamata nisa.
Tacije le6enta tana k’ara zubda kwalla masu zafi, ta ce, ”nad’au alk’awarin kota halin k’ak’a saina auri guy d’inanan, kuma saina rabashi da matar tasa Dan bazanyi shearing d’insa dakowacce maceba, banta6a Neman Abu narasaba a duniyar nan, nasan kaima bazan rasakaba bobona.
Ban ta6a bin malamaiba ko bokaye, bammasan inda sukeba, amma awannan karon duk inda suke saina nemosu, kuma zan kashe konawane Dan in mallakeka mijina, wasu zafafan hawaye suka zubo mata, kuka takeyi sosai da zuba sambatu harma da sa6o.
( Na ce, “hummmmm safna kenan, duk d’an daya hana uwarsa barci tofa shima bazai yiba).
————————:::::::::::
Agidan Bobo kam Rahma da Nawal ne suke wasan ‘Yar 6oye, Rahma tarufe ido da k’yalle Nawal kuma ta6uya Rahma na nemanta, Nawal ta ta6ata tana fad’in momy kin ganni, da Sauri Rahma tajuyo inda taji maganar Nawal.
Bobo yashigo da sallama wadda babu Wanda yajita, tsayawa yayi yana kallonsu cike da burgewa, Rahma dake laluben Nawal tak’aro inda yake tana laluben Nema, jitayi ta damk’i wani hannu mai laushi da santsi.
Da sauri tacire k’yallen data rufe fuska danjin Nawal tana tafa hannu tana dariya dafad’in shikenan baby zai goya momy.
Kallon ido cikin ido sukaima juna shida ita saikuma suka dawo da kallonsu kan Nawal.
Baby ka ajiye jaka ka goya momy kawai.
Da sauri Rahma ta ce, ” nikam Nawal na yafe.
Nawal ta k’ya6e fuska tana fad’in um um nidai sai yayi miki goyon, saikitacewa kin yafe kullum kullum.
Kan Rahma ak’asa ta ce, “toki bari yahuta kinga yazu yadawo daga aiki, tajawota jikinta tana lallashi.
Bobo yawuce d’akinsa yana murmushin darun Nawal.
Bayan yayi wanka yafito sanye da wando iya guywa da Riga k’arama, Rahma tamik’e kanta ak’asa ta ce, ” ga abincifa.
Baice mata komaiba yanufi dinning, itama baya ta take masa, bayan ya zauna tafara had’a masa komai, sai satar kallonta yake k’asa k’asa, tagama takoma falo taja Nawal suka koma tsakar gidan dansu sha iska.
Bayan kamar minti 30 suka dawo, sannan bobo ya kammala yanazaune da jaridar tasa ta fama.
Nawal ta ce, “yauwa baby tashi kagoya momyn to.
Da sauri Rahma tanufi d’aki dantaga rigimar Nawal bazata k’areba.
Bobo yajawo Nawal yad’ora kan cinyarsa, kinga babyna kibari zan goya momynki amma ba yauba, kinga yau nagaji, yak’are maganar da sumbatar kumatunta.
Nawal ta k’ya6e fuska ita adole bata yardaba.
Ganin zata takura masa, shikuma soyake yahuta saboda yagaji sosai, ya ce, “to tashi muje na goyata, tamik’e yarik’e mata hannu suka nufi d’akin Rahma.
Tana zaune bakin gado tana wasa da wani d’an babyn Nawal, suka shigo, ta d’ago kai tana kallonsu, suna had’a ido da bobo ta kauda idonta.
Nawal ta ce, ” momy tashi baby yamiki goyonki.
Rahma tabud’e baki zatayi magana Bobo yad’aga mata hannu, karki damu yarinyar nan taki ba k’yalemu zatayiba inhar ba’ayi goyonnanba, Dan haka taso kawai nayi muhuta.
Da sauri Rahma takallesa danjin furicin bakinsa, yama za’ayi harta iya yarda ya goyata saikace wata yarinya.
Bata ankaraba taga ya tsugunna yana jiran tahau kenan.
Cikin sanyin murya ta ce, “Dan ALLAH kayi hak’uri bazan iyaba.
Juyowa yay yana kallonta fuska a d’aure, ya ce, “amma dai kinsan Nawal dashegen naci, indai ba goyonnan nayiba ba barina zatayi na hutaba, nikam natsani adameni da hayaniya.
Ganin yanda yake magana cikin fad’a amma hakan baihana muryarsa fita cikin nutsuwa da taushiba yasa dole tasakko daga gadon, amma tayi tsaye takasa hawa saboda tana matuk’ar jin kunyaarsa.
Momy kihau baby yana jiranki Nawal tafad’a tana kallonta.
Hararar da Bobo ya watso matace tasata saurin d’anewa bayansa.
Shikuma yamik’e yanufi falo da ita, Nawal nabiye dasu tana dariya.
Yajuyo yana kallon Nawal to nagama ko baby?.
Lah baby saikaje d’aki da’ita sau uku kana dawowa, haka yayta zarya daga falo zuwa d’aki harsau uku, ana ukunne yadireta saman doguwar kujera yana fad’in wash bayana, wlhy momyn Nawal kincika nauyi.
Rahma tayi k’asa dakai cike da kunya, yabata dariya wlhy, sai wani yatsine fuska yake da rik’e k’ugu tamkar zaiyi kuka, amma saita gimtse, wai yau itace namiji yagoya, da gudu tabar wajen tanufi bedroom.
Shikam dariyama tabashi Dan haka yad’an murmusa tareda zama saman kujerar, wani nishad’i na musamman yatsinci kansa aciki, yajingina kansa da kujera tareda lumshe fararen idanunsa yana cigaba dasakin lallausan murmushi.
Har aka kira sallar magriba yafita Rahma bata sake fitowaba, gani take bazatama iya had’a ido dashiba aii.
Saida akayi isha’i yashigo gidan dakayan kwalam da mak’ulashe, Rahma najin motsin dawowarsa ta tura Nawal itakam tayi kwanciyarta tak’i fita.
Nawal taje tafad’a jikinsa tana masa oyoyo, shima rungumeta yayi yana fad’in babyna kinyi sallah?.
Eh nayi nida momy, harta koyamin karatu.
Ya ce, “iye kaga ‘Yar gatam momynta, ina momyn taki to?.
Tana d’aki wai zatayi barci, nikuma nazo wajenka nayi fira.
Murmushi yayi Dan yagano tanajin kunyane dankarsu had’u, ya ce, ” jeki kiramin ita.
Da gudu tanufi d’akin, tafad’a saman Rahma dake kwance kan gado, momy kizo baby na kiranki.
Rahma tadafe kai banace kice masa ina barciba?, kuma daga yau kiringa cemasa dady ba beby ba kinji babyna.
To momy zandinga fad’a tashi muje to.
Badan Rahma tasoba tasakko suka nufi falo itada Nawal.
Yana zaune idonsa akan Tv yana kallon labarai ta ce, “sannu da dawowa.
Yauwa yafad’a batareda ya kalletaba, ya ce, “ga wannan yamik’a mata ledan kayan motsa bakin.
ALLAH yasaka da alkairi tafad’a tana kar6a, kicin tanufa itada Nawal suka juyo afilat, wad’anda bazasu ciyuba tasaka afirij.
Takawo masa nasa itakuma tad’auki nasu danufi sutafi d’akinta suci, ya ce, ” ina zakuje kuma?.
Kanta ak’asa ta ce, “d’aki.
sabodani zakuje d’aki cin abinci?.
Dawowa tayi tazauna batareda tabashi amsaba, saidai akunyace takeci, shikuma yana satar kallonta har suka gama tashige d’aki tabarsu shida ‘yarshi.
Shirin barci tayi tai kwanciyarta, dama kayan barcine ajikin Nawal.
Yana gama kallon labarai shima yamik’e da Nawal ajikinsa datai barci, yakashe komai sannan yanufu d’akin Rahma.
Ahankali yasauke Nawal akusada ita, yay musu addu’a sannan yaja bargo yarufesu idonsa akan Rahma, yanda take barci hankali kwance sai fuskarta tayi wani wasai.
Jiki asanyaye yanufi d’akinsa yay shirin barci shima yakwanta……………
[14:23, 10💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 18
Hankali tashe Alh sunusi ya iso gidansa, ko fakin bai bari direbansa yagamaba yafice.
Matarsa na zaune afalo itada k’annen Haneef d’in yafad’o ko sallama babu.
Arazane suka mik’e suna binsa da kallon mamaki, dukda ba yaune rana tafarko daya fara shigowa gida ahakaba.
Ina my son?, yafad’a aburkice.
Cikin mamaki haj Falmata ta ce, “Haneef?.
“Eh,” ya bata amasa afusace.
Yanzu babu dad’ewa yafita aii, wani abune yafaru?.
Wata uwar harara yasakar mata, waike wace irin shashashar uwace?, wai kina nufin bakisan ‘yan sanda sunzo har gidannan sun kamamin yaroba?.
Afirgice ta ce, “naga takaina ni Falmi, yaushe hakan tafaru?, yanzufa Haneef d’in yashigo gidannan ya sauya kaya yafita.
Bai sauraresuba yafice yabarsu cike da tashin hankali.
Abin kamar wasa Alh sunusi har dare yana Neman Station d’in da akakai Haneef amma babu ko Alamarsa, ransa yak’ara 6aci da harzuk’a, aiiko wlhy saiya d’auki mataki akan ‘yan iskan police d’in dasukai k’arfin halin shigar masa gida harda kama masa tilon d’ansa namiji.
Gida Yakoma danufin zaije ga Qumissioner of police gobe idan ALLAH ya kaimu, saidai zuciyarsa namasa rad’ad’i idan yatuna Haneef zai kwana a Station yau.+
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
*_9:30pm_* ya isa gidansa duk agajiye, jinsa yake yau fes tunda ankama masa d’an iskan nan, bayan sun gaisa da mai gadi yashige cikin gidan.
Babu kowa afalon, har TV akashe yake ga gidan tsit kamar babu kowa, da alama masu gidan har sunyi barci.
K’ofar yamaida yarufe sannan yanufi d’akinsa, yazube kayan hannunsa cike da gajiya, babu 6ata lokaci yacire kayansa ya fad’a bayi domin yin wanka.
Bayan yafito yagabatar da shafa’i da wutiri, ‘yan dube dube yafayi da alama akwai abinda yakeson gani, amma babu, d’an k’aramin tsaki yayi tareda mik’ewa yafice.
Cikin barci Rahma taji ana bubbugata, afirgice ta tashi, Dan dama tsorace takwanta, saboda rashin dawowar mai gidan.
Ganin shine atsaye yasa ta sauke ajiyar zuciya, ahankali ta ce, “sannu da zuwa.
Bai amsaba ya ce, ” ina shayina?.
Tad’an dafe kanta, wlhy na manta ne.
Aii yanzu na tuna miki, yafad’a yana ficewa.
Asanyaye Rahma tasakko daga gadon, Dan barcin data fara yasa jikinta yin lakwas, haka ta k’arasa kicin tana jan k’aramin tsaki, idonta cike da barci tadafa masa shayin, tajuye akofi tareda yanka lemon tsami ta matsa aciki, tad’ora akan k’aramin tire tafice.
Ganin baya falo gabanta yafad’i, kenanfa d’akinsa zata kai masa?, tai shiru kamar mai nazari, zuciyarta ta ce, “kije kikai karya huce Rahma ki k’ara jama kanji wani laifin”, tunda tazo gidan yauce rana tafarko dazata Shiga d’akinsa, Dan haka k’irjinta keta dukan uku uku, haka tadaure ta kwankwasa, saida tayi kusan Monti biyu sannan ya ce, ” tashigo.
Ahankali ta tura k’ofar tashiga, wani k’amshi yadaki hancinta tashak’a talumshe idanunta, saikuma ta bud’e ta sauke akan Bobo dake zaune abakin gado yana latsa laptop, k’afarsa d’aya ak’asa d’ayar kuma ya tank’washeta a gadon, sanye yake da kayan barci ruwan ganye mai turuwa, tana mamakin yanda yakeson latsa laptop da karatun jarida.
Jin shiru bata ajiyeba, bakuma tayi maganaba yasashi d’agowa ya kalleta, shima baiyi maganaba saidai tura mata k’aramin tebir na gilas dayayi.
Ganin haka yasa itama tad’ora batareda ta ce, “k’alaba.
Bayan ta ajiye saikuma tayi tsaye takasa tafiya.
Yana danna laptop d’insa yana shan shayi, tsawon minti 7 ita batayi maganaba shikuma ya shareta yanata aikinsa, yakula bazatace komaiba, kuma akwai magana abakinta, Dan haka shi ya daure ya ajiye NASA shan k’amshin ya ce, ” kinada matsalane?.
Kad’an ta kalleshi taga har yanzu idonsa nakan laptop d’in.
gyara tsayuwarta tayi, muryartan nan mai kasheshi ta daki kunnensa, dama sonake naji yau ko lfy Baka dawo da wuriba?.
Cak ya tsaya da abinda yakeyi, yad’ago fararen idanunsa ya sauke akanta, sanye take cikin dogon hijjabinta har k’asa, sa6anin d’azu daya Tatar da ita da kayan barci.
Ahankali yasauke ajiyar zuciya, koba komai yaji dad’in kulawarta agareshi, cikin miryarnan tasa ya ce, “babu wata Marsala aikine yamin yawa a office.
” okey saida safe.”
Harta kai k’ofa yana binta da kallo, yadaure ya ce, “incedai babu wata damuwa daga babyn taki?.
Bata juyoba amma ta tsaya, Dan furucinsa na k’arshe yaymata dad’i, muryarta araunane ta ce, ” a’a babu Marsala, saidai tata jiran dawowarka, harta gaji tayi barci….. Bata jira amsarsaba tafice.
STORY CONTINUES BELOW

Ajiyar zuciya ya sauke tareda lumshe idanunsa, zuwa wani lokaci ya bud’e idon, d’an murmushi naga yayi Wanda bansan da liliba, saikuma yacigaba da aikinsa yana shan shayi.
Itakam Rahma tana komawa d’aki tahaye gado ta kwanta abinta sai barci.
::::::::::••••••••••••:::::::::
Washe gari Rahma ta tashi kamar yanda tasaba ta had’a break fast da gyaran gida, taima Nawal wanka itama tayi, kwalliya sosai taima yarinyar tai tsaf da ita, Dama ga ruwan k’yau d’an Asali, kan baby Nawal yasha gyara Dan jiya da yamma Rahma tayi mata kalba, kasancewar yau juma’a.
Tana cikin saka mata janbaki yaturo k’ofar yashigo da sallama ciki ciki kamar Wanda akaima dole
Da sauri Nawal ta hantsilo daga kujerar madubi danta hango daddynta ta madubi, oyoyo papa na tafad’a cike da farinciki tana rungumesa, shima d’aukarta yayi yad’aga sama yana dad’in “I luv u my child,” yasumbaci kumatunta.
Ta shagwa6e fuska, papa shine jiya kak’i ka dawo ko?, lah nadawo mana, saidai kinyi barci sannan kitanbayi momy kiji?.
Nawal takalli Rahma dake kallonsu cike da sha’awa, wai haka momy papa yadawo jiya?, kai Rahma tad’aga mata tana murmushin daya kusan narkar da Bobo atsaye, hakane babyna yadawo kina barci.
Nawal tasunbaci kumatun babanta da k’asunba ta kwanta luf tanata shek’in gara.
Shikam hankalinsa nakan Rahma yana mata wannan munafikin kallon NASA k’asa k’asa.
Talura dashi tsaf dan haka tatsargu, rissinawa tayi ta ce, “INA kwana?.”
Lfy, yafad’a cike da basarwa shi adole ba ita yake kalloba.
Rahma ta d’an ta 6e baki, dukda ta fahimci salon amsa gaisuwarsa kenan…… Muryarsa ta katse mata tunani, kushirya idan mungama break gida zamu wuce, Dan duk juma’a a can kowa yake yini.
Ahankali ta jinjina kai kamar wata k’adan garuwa.
Shikam yajuya yafice da Nawal ahannu.
Itama fitowa tayi tahad’ama kowa abinci agabansa, hankalinsa kwance yakecin abinci shida d’iyarsa, amma Rahma duk atakure take, haka kullum take cin abin ci atakure, bakuma danwai bata saba da ahakan bane, saidai kawai nauyinsa datakeji, tunda agidansu gaba d’aya suke had’uwa suci abinci tuntana yarinya.
Tananan tana juya cokali haryagama shida Nawal, yad’auketa suka koma falo suna jiranta.
Ganin yatashi yasata sakin jiki taci abincinta sannan takwashe kayan taje ta d’auraye.
d’aki takoma tacanja shigarta cikin wani had’ad’d’en doguwar rigar shadda pink colour, kayan sunmata k’yau sosai, tasaka k’aton farin hijjabinta sannan tafito, babu kowa afalon, danhaka takashe komai na kayan wuta, gamawata keda wahala yafito shida Nawal daga d’akinsa, hannunsa rik’eda jakar aikinsa.
Kallo d’aya yaymata yad’aukekai, saidai har azuciyarsa yaji dad’in hijjabin data saka, yanason kamilar mace arayuwarsa, gaba yay suka bishi abaya.
Tashaya kulle k’ofar falon shikuma sukai gaba cikin mota shida Nawal.
Ganin Nawal abaya itama tabud’e bayan zata shiga, ahankali yay maganar tamkar mai ciwon baki.
“Halan ni direban kine?.”
Cak tatsaya tafasa bud’ewa, kuma tak’i dawowa gaban.
Yakuma cewa kina 6atamin lokacifa, kuma wajen aiki zanje, jiki a sanyaye tabud’e gaban tashiga, shima baisake cewa komaiba yatada motar suka fice bayan sun gaisa da baba mai gadi.
Karatun Alkur’ani yasaka musu, cikin k’ira’ar shiek Abdurraham sudes, ahankali Rahma kebin karatun, yana kallonta ta gefen idonsa, jiyay tak’ara girma a idonsa.
Har sukaje gidan Appa babu Wanda yay magana, garama Nawal takanyi jefi2.
Saida yatsaya suka gaisa da baba mai gadi, yaymasa alkairi kamar yanda ya saba sannan yashige ciki.
Yana faka motar Nawal tafice da gudu zuwa cikin gidan, sukuma suka fito cikin nutsuwa, da gudu khairiyya da khursiyya suka fito, rungume Rahma sukayi suna farin cikin ganinta.
Ta ce, “aini nayi fushi, daga zuwa d’aya baku sakeba.
Kiyi hak’uri auntyn mu, Ammi ce ta ce, ” mubari sai nan gaba.
Bobo yak’araso yana harararsu to maganannu ai kwabari kushiga gida dai ko?, yay gaba abinsa.
Khursiyya ta ta6e Baki, aifa yau munga banu jarabatu yazo, ALLAH yasa aiki zai wuce cewar Khairiyya.
Rahma najinsu dai tayi murmushi kawai.
Cikin gidan suka shiga, hakan tayi daidai da sakkowar Ammi daga saman Appa, Dan Nawal nazuwa canta haura.
Ta rungume Rahma tanamai jin dad’in ganinta, cike da kunya Rahma ta rissina ta gaida Ammi, ta amsa cikeda fara’a, da tambayarta ya zaman babudai wata Marsala ko?.
Kan Rahma ak’asa ta ce, “Ammi babu matsalar komai, to Alhmdllh d’iyata haka nakeson ji.
A’a mukarram d’ina lfy dai ko?, Ammi tafad’a tana kallon bobo dayay tsaye yana kallonsu tun d’azun.
yaturo baki gaba kamar wani yaro, yo Ammi sai yanzu kika san dani?.
Ammi taje takama hannunsa, o ni na isa namanta da babana, kawai ina murnar ganin d’iyatane.
Yakuma turo Baki, Toni bari nakoma tunda bak’ya murnar ganina, yanda yay maganar ashagwa6e yasa su khairiyya kwashewa da dariya.
Harara ya watsa musu suka bar wajen, itadai Rahma murmushi takeyi da mamakin Bobo, irin wannan shagwa6a haka kamar wani d’an shekara 5, anace mata tanada shagwa6a toga Wanda yatakata iyawa.
Ammi ta lallashesa suka haye sama domin gaida Appa.
Appa yaji dad’in ganinsu sosai, Dan haka yaymusu nasiha sosai sannan bobo yamik’e yaymusu sallama Dan wucewa aiki, saikuma antaso.
Yakalli Rahma k’asa k’asa ya ce, “saina dawo.
Kanta ak’asa ta ce, ” ALLAH yatsare yabada sa’a.
Yaji dad’in addu’arta Dan dama ita yake son ji.
Ammi taji dad’in addu’ar da Rahma taima bobo, hakama Appa, suma sukai masa yatafi.
Zuwa 10:30 gidan yagama cika, aunty Rasheeda da ‘yayanta, aunty Sameera ma da NATA, aunty ummy ma haka, mazan kuma suna ajiyesu suka wuce wajen aikinsu.
Dan danan gidan ya haukace da hayaniya, yaran duk suna falon sama wajen Appa, sukuma iyayen suna falon k’asa sunashan hira kamar wasu k’awaye, babu wannan shegiyar ak’idar ta kishin Sauri, hirarsu suke sosai, Dan danan Rahma tasaki jikinta dansu, su aunty Rasheeda akwai saurin shiga rai, gasu khursiyya iyayen shafta………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 19
“K!, ina zakije da sassafennan?.
Safna ta kwa6e fuska, ummi munafa da Lectures k’arfe 7:30am kuma malamin baida kirki wlhy, gashi ya CE, ” test zai mana, tak’are maganar da turo baki gaba.
Ummi ta ta6e Baki, ta ce, ” shikenan jeki, amma idan kin dawo inason magana dake nida mahaifinku.
Gaban safna yafad’i ta ce, “ummi magana kuma?, tami to?.
” idan kindawo k’yaji, Dan inama son aikenki gidan Rahma.
Kai ummi gidan Rahma fa kikace?, saikace wata k’anwarta.
To tunda tarigaki aure aikin zama k’anwar tata aii, ko kina nufin dankince bak’yason mijinta bazakije gidantaba?.
Nifa Bahaka nake nufiba ummi, kawai INA dai ganin da kunya.
Harara ummi tasakar mata, o sai yanzu kika San kunyar?, alokacin dakikai shirin wulak’antamu kin manta da kunyar.
Nidai ummi ALLAH yabaki hak’u, ALLAH fa yariga yarubuta itace matarsa kawai, amma ni ban wulak’antakuba, kawai ina gudun kar asakamin kaina atunkunya ne, saina dawo, tayi saurin ficewa, Dan batason jin amsar ummi, tasan halinta sarai, yanzu saita hau sama ta 6ata mata shirinta, itako awannan lokacin bata fatan abinda zai hanata fita.
Ran ummi yak’ara 6aci, duk cikin ‘yayanta babu Mara kunyar irin Safna, ita bata iya tauna magana ga mahaifaba, ta maidasu tamkar wasu k’awayenta, kodan gatan dasuka nuna matane abaya?.+
Tana fita taci karo da Baseera ak’ofar gida.
A’a kice kina nan?, dafa shirin shiga gidanku nakeyi, to waima inbanda iskanci miye natsayawa anan?, gidan bak’onkine?.
Baseera tarufe murfin motar tana fad’in Bahaka baneba, banason nashiga mu 6ata lokacine kawai.
Dariya safna tayi, haba k’awata aganinki zan 6ata lokacine?, kenifa k’agara nayi gari ya waye, yanzun haka jinake tamkar nayi tsuntsuwa na ganni agaban malaminnan.
Baseera ta tuntsure da dariya kai k’awata kemafa bakida dama akan abinda kikeso, lallai guy d’innan yayi babbar sata.
Safna tak’ara dafe sitiyarin motar, ai wlhy Basee guy d’innan ba k’aramar sata yayiminba, wlhy gaba d’aya ya haukatani, saidai idan natuno kafinni harya zauna da mata biyu nakanji raina ya 6aci, badan ina sonsaba sosai da watsar dashi zanyi.
Shiyyasa Nima na d’auki alk’awarin saina mallakesa amatsayin miji kota halin k’ak’a, ke namiki mai kankat wlhy har yarinyarsa saina rabashi da ita, Dan dagani sai ‘ya’yana nakeso mu zauna dashi.
Hummm ‘yammata ace insha ALLAHU dai.
Safna ta gallama baseera harara, to aii dama komai insha ALLAHU ne, koko insha Baseera ne?.
A’a Dan ALLAH karki mana sa6o mudai kisa akifar damu, kefa wani lokacin kamar bakiyi islamiyyaba haka kike.
Banza Safna tai mata, Dan idan tabiye mata fad’a zasuyi, itakam lalla6ata takeyi tasamu arakata gun malami.
Sun isa gidan malam amma da mutane, Dan haka suka jira a mota.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*
Bobo a police tetion yasaka ‘yan sanda gaba sai masifa yake musu, wai basu san aikinsuba.
Haba Dan ALLAH wai mikuka maida kankune?, yau sati nawa ace angagara nemo mai laifi, hanyafa mai sauk’ine gano koma wane d’an iskane, saboda anbaku no. d’in motarsa, wlhy nabaku nanda gobe idan ALLAH yakaimu inhar baku zomin da mai lafinnanba zan d’au mataki, Dan saina saka anta6a aikinku, tunda bakusan abinda kukeyiba…
Sudai ‘yan sanda cikinsu ya d’uri ruwa Dan sunsan kowaye Abdulmaleek, tunda bayau yafara d’ora su akan aikiba.
Tsaki yaja yafice, afusace yashiga mota yafigeta.
Yayi nisa atafiyarsa sai masifa yakeyi shikad’ai amota, tamkar zai ari baki.
Wani haushine yak’ara turnik’eshi Dan ganin wani banzan Go slow mara dalili, kamar ance ya waiga idonsa yasauka akan number motar guy d’in dasuke nema.
Jikinsa har rawa yake yad’auki waya yakira ‘yansanda, saidai yana yanke wayar ana sakin Go slow d’in, da hanzari yatakema motar baya, binsa yake cikin dabara har zuwa wani kantamemen gida, ya sauke numfashi afili ya ce, “gidan Alh Sunusi Dala kuma?, kenan wannan motar tanada alak’a da gidan?.
Wayarsa ya d’auka dake wringing ‘yan sandane suke tambayarsa yana ina?.
Kusameni gidan Alh Sunusi dala.
Kansa ya kwantar jikin kujera, saiyanzu yagane abinda yasa ‘yansandan suka kasa kama mai laifin, tabbas sunsan yanada alak’a da wannan gidan…….
Tunaninsane yatsaya alokacin da motar ‘yan sandar ta iso, bai fitoba amma yabud’e murfin motar.
‘Yan sanda biyu suka k’araso inda yake, fuska ad’aure yakallesu, nan gidan motar nan tashiga, Dan haka saikuyi aikinku.
Cikin d’an sanda d’aya yabada wani k’ululu, baki narawa sukace nan gidan kuma?.
Cikin daka tsawa ya ce, “e nan gidan, dama nasan kunsan Wanda ya aikata, amma kwad’ayi irin naku yasa kuka kasa d’aukar mataki, to yanzu saiku za6a, kamashi kokuma asarar aikinku……
Kafin yarufe baki sunnufi k’ofar gate d’in gidan, dak’yar maigadi yabarsu suka shiga.
Daidai nan Haneef yafito cikin sabuwar shiga danufin sake fita, harya fara k’ok’arin bud’e mota yadakata Dan ganin ‘yan sanda.
K’arasowa sukayi har inda yake tsaye, sallama sukai masa, ko amsasu baiyiba, saima kallon banza dayake bisu dashi.
d’an sanda ya had’iyi wani yawu sannan ya ce, ” yalla6ai u onder arrest.
Me!, Haneeff yafad’a cikeda rainin hankali, yacigaba da fad’in Ku harkunkai matsayin dazaku shigo cikin gidanmu kuce kunzo kamani?, toma awane dalili?.
Kayi hak’uri yalla6ai zamu maka bayani idan munje can, Dan duk abinda kafad’a anan zai iya zama hujja agareka a kotu.
Kan uba…… Saikuma yay shiru yakasa k’arasawa, yaja numfashi kumuje zan biku abaya, yayi hakane danya kafa musu tarko.
A’a kamuje kawai aiiba dad’ewa zakayiba…. Maganar Bobo tadaki kunnuwansu.
Kai kuma awa?, haneef yafad’a yana kallon Bobo.
Karka damu da matsayina, kaidai kadamu da kanka kawai my friend.
Cikin 6acin rai Haneef ya ce, “kadai iya bakinka k’aramin k’waro.
Wata banzar dariyar rainin hankali Bobo yasaki, wadda zan iya cemuku yauce rana tafarko danaga dariyarsa, ya kalli ‘yan sandan ya ce, mikuke jira?, yana gama fad’a yafice daga gidan.
Cikin 6acin rai haneef ya ce, “kumuje to, ammafa yak’udiri aniyar wulak’anta d’an saurayinnan da ‘yan barandarsa.
Haneef yashiga motar ‘yan sanda, bobo kuma yashiga motarsa.
‘Yan unguwar sai dad’i sukeji da ganin Haneef amotar ‘yan sanda, yayinda agefe kuma tuni magulmata sunkira Alh Sunusi sunkai masa rahoton kama Haneef da ‘yan sanda sukayi yanzu.
Hankalinsa atashe yabaro office yanufo gida.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Suna nan zaune har layi yazo kansu, sannan suka shiga.
Bayan sun gaisa da malam da’u safna ta ce, “malam……
Da sauri yad’aga mata hannu karkice komai, tunkafin kizo sud’an tsito sun sanar dani komai.
Kin kamu da son wani saurayi, kinkumasa ayimiki bincike akansa, yanada mata ba’a dad’e dayin aurenba, kuma yata6a aure matar tamutu harda ‘ya atsakaninsu, koba hakaba?.
Cikin mamaki da rawar jiki Safna ta ce, ” to amma ALLAH ya gafarta malam ta INA kasan wannan?.
Malam da’u yatuntsure da dariya, kai yaro yarone dai, kedai fad’i buk’atarki kawai ‘yammata kiga aiki da cikawa.
Cikin tsoro Safna ta ce, “malam dama inaso shi wannan saurayin yazo dakansa gidanmu ya ce, ” yana sona, kuma yasaki matarsa Dan wlhy inada kishi sosai malam, kuma inason sa sosai har inaji idan ban sameshiba zan iya mutuwa wlhy, Dan ALLAH malam ataimaka mini.
Malam da’u ya ce, “babbam taimako aljihunki ‘yammata.
Baseera da dama tasaba indai bin malamine, hankalinta kwance ta ce, ” malam kaima Kasan kud’i ba matsalarmu bace aii, inhar buk’ata zata biya to kad’auka kasamu kud’i konawane.
Malam da’u ya wangale bakinsa dake cike da damzar goro, wasu hak’oranma sun fita, ya ce, “baseera indai kece aii saidai nafad’ama wani, Dan haka kisanar da k’awarki tagama samun abin sonta.
Wani faranti yajawo dake cike da k’asa, yafara Zane Zane yana motsa baki, bayan yagama yamaida kallonsa Kansu, kince ya sunansa?.
Safna ta CE, ” nidai bobo nasani, amma Wanda nasaka yamin bincike akansa ya ce, “Abdulmaleek.
Malam da’u yakuma maida kansa k’asa, shiru yayi Dan shikad’ai yasan miya gani, to ammafa yana fad’a mata gsky bazata sakar masa nairoriba, gata kallon d’aya zaka mata kagane kud’i sun jik’ata, Dan haka ya canja shawara, ya ce, ” zaki gansa anan kusa kam, saidai bazan fad’a miki ranarba, sannan kuma saikun had’u zan fara aiki akansa, ga wannan yazama kwallinki, wannan kuma hoda.
Kar6a Safna tayi tai godiya.
50k suka ajiye masa suka tafi suna godiya.
Na ce, “hummmm.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Bobo har police tetion yaraka ‘yan sanda, saida aka gark’ame Haneef Wanda tuntini hankalinsa yafara tashi, yaza’ai kamarshi d’an gata ace anakawoshi nan gurin?, gashi sun kar6e masa waya bare yakira dad nasa yasanar MASA halin dayake ciki.
Yad’au alk’awarin Indai yafita agurinnan saiya wulak’anta yan sandar nan da saurayin nan.
Saida yayama police d’in nanan gargad’i sosai akan wlhy kowaye yazo karsu bada belin Haneef, sannan yawuce yanufi office d’insa, yanason fara shirya yanda zasu shiga kotu.
+
Yaduk’ufa sosai wajen latsa lap-top, gaba d’aya hankalinsa yana wajen binciken family d’in Alh Sunusi Dala, da sauri yad’ago danjin an ta6ashi, jar uban nanan kai yafad’a cikin ihun farin ciki, rungume juna sukayi shida bak’on nasa.
Ammar yaushe a k’asar?.
Ammar yay dariya wlhy mutumin jiya da daddare, shiyyasa yau naimaka sakko amma natarar kafita.
Kabari kawai wlhy naje wajen yaranka ne sukamamin wani d’an iskan mutum.
Kai Bobo kana nandai baka canjaba?, yanzu kuma wa’aka kafama tarko ne?.
Wani murmushi bobo yasaki, kamar mai rad’a ya ce, d’a gurin Alh Sunusi Dala!.
Ammar yad’an zaro ido, Bobo Kasan kuwa sunanwa ka fad’amin?.
Kwarai kuwa nasani, ni kam ainafi kowa farincikin dawo warka wlhy, inason kaima yaranka magana su k’ara gark’ameminshi sosai, Dan ranar litinin nakeson mufara sharia.
Baka da damuwa da hakan abokina.
Yes sir!, Bobo yafad’a yana sarama Ammar.
Dariya ammar yayi yace d’an iska, ALLAH dai ya shiryaka, duk kabi katakurama ‘ya’yan manyar garinnan, ina baby Nawal da amarya?.
Saida ya sauke numfashi sannan ya ce, “suna lfy.
Masha ALLAH, kasanar da amarya zanshigo weekend cin abincin amarci, daganan naga amaryar tamu, tunda ALLAH baisa ansha biki daniba.
ALLAH ya kawoka Bobo yafad’a.
Daga nana hirarsu suka cigaba dayi, dagani kasan sunyi bala’in shak’uwa da juna.
*Waye Ammar?.*
Ammar Khaleed Adam, d’ane ga Alh Khaleed Adam, abokin Appa na k’ut da k’ut wanda yayma Rahma k’yautar mota ranar walimar makaran tarsu, su 7 mahaifansu suka haifa, shine na biyar agidansu, yanada yayye maza da mata su hud’u, sai k’anne biyu mata, Ummy matar ya Hamza dakuma autarsu Lubna ita sa’ar su khairiyyace.
Tare sukayi karatu da Bobo tundaga primary har secondary, daganan kowa Yakama inda yafi wayau, Bobo yatafi karatun lauya, shikuma yafad’a aikin ‘yan sanda, ayanzu haka shine Qumissioner of police na jihar kano, sun shak’u sosai da Bobo, bashida wani aboki sai Ammar da yayyensa.
Duk wani aiki da Bobo yarikito Wanda yake buk’atar tsaro to Ammar ne ke taimaka masa, yanzuma yayi wata ‘Yar tafiyane ta wata biyu, shiyyasa baisamu damar halartar bikin Bobo ba.
Shima matarsa d’aya da yara biyu duk maza.
Wannan kenan………….1..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 20
washe gari
Rahma tatashi tayi duk abinda tasabayi dukda tasan yau weekend Bobo bazai fitaba, tana cikin saka turare a falo bobo yafito sanye da jallabiya ruwan toka mai gajeren hannu, rissinawa tayi ta gaidashi, kamar yanda yasaba ya amsa da lfy.
Amsa gaisuwar nan nabama Rahma haushi, amma babu yanda zatayi.
Yad’anbi falon da kallo komai tsaf, gawani k’amshi na musamman, yana jin dad’in kasancewarta mace mai tsafta.
Itadai cigaba tayi da abundan takeyi. Ya ce, “bari nad’anje wani waje nadawo.
Aranta tace kofa wanka bakayiba, amma afili ta ce, ” to ga Break.
No barinaje nadawo, aiba dad’ewa zanyiba, yafad’a yana ficewa.
Itama ta ce, “ALLAH ya tsare.
Dukda yafita amma yajiyo addu’arta.+
Bayan takammala saka turaren zuciyarta tabata shawara dataje ta gyara masa d’akinsa, kamar bazatajeba saikuma tatuna nasihar mahaifiyarta da ummansu Basma.
d’akin tanufa da tunanin ALLAH yasa bai rufeba, tana tura k’ofar tabud’e, k’amshinnan yana nan kamar kullum, yau tanutsu takalli ko ina na d’akin, komai farine tas, aranta tace farin Abu name tsaftane.
Sai manya manyan hotunanan Ni’ima Maman Nawal, bani gurin ita kad’a, wani gurin kuma shida ita.
Ko kad’an bataji haushiba bare kishinta, Bata 6ata lokaciba tafara gyara ko ina, Dan danan tagama d’akin yak’ara d’aukar haske komai yana d’aukar ido.
Bathroom tashiga zata wanke saitaga kaya ajik’e abokiti.
Shiru tayi tana tunanin ta wanke kota barmasa abinsa, wata zuciya ta ce, ” ki wanke, kobabu komai zaki samu lada aii.
Haka tazauna tahau wankin gajerun wandunansa da vest, akunyace take wankin tamkar tana gabansa, gudu gudu sauri sauri tagama bataso yazo yataddata tanayi.
Dandanan tagama tawanke bayin, tad’auki kayan tafito waje, acan baya taje tashanyasu sannan tadawo d’akinta tashiga wanka, Dan Nawal bata tashiba.
Shigarta wanka babu dad’ewa yashigo gidan, d’akinsa yanufa kai tsaye, baki da hanci da ido yasaki yana kallon d’akin NASA, yalek’a bayi nanma fes, bokitin daya jik’a kaya wayam, wani lallausan murmushi yasaki, labulen window d’insa yad’aga, can yahango kayan ashanye.
Jiyay wani Abu nata6a zuciyarsa, afili ya ce, ”ALLAH yaymiki albarka.
Fitowa yayi yanufi d’akin Rahma, hakan yayi daidai da fitowarta daga wanka, daga ita sai guntun tawul iya cinya.
Wata tsayuwar sojan badakkare bobo yayi, sai Raba idanu yake akan Rahma, da wannan munafikin kallon nasa k’asa k’asa.
Itakam dukta rikice, waige waigen abinda zata rufe jikinta kawai takeyi, can ta hango hijjabin sallarta, amma dole saitabi tagabansa zata d’auka, ganin haka saikawai takoma cikin bayin da sauri.
Murmushi yayi tareda sauke ajiyar zuciya, yak’arasa inda hijjabin sallarta yake yad’auka, ahankali yak’arasa har k’ofar bayin ya kwankwasa, Rahma dake jingine da k’ofa tagwalo ido waje, k’irjinta sai dukan Tara Tara yakeyi.
Yak’ara kwankwasawa.
Muryarta narawa tamkar zatayi kuka tace yes, yanda tayi maganar tabashi dariya amma saiya gimtse ya ce, “bud’emin k’ofar.
Innnalillahi tace azuciyarta, wai mi mutumin nan yake nufi………maganarsa ta katse mata tunani, ” wai kobaki jinane?.
Bayan k’ofar takoma tala6e sannan tabud’e, gaba yay tamkar zai Shiga, saikuma yamik’a mata hijjabin, dasauri takar6a tamaida k’ofar burum tadatse.
Girgiza kai yayi yanad’an ta6e bakinsa, yazauna bakin gadon yana shafa kan Nawal daketa barcinta hankali kwance, shi mamakin kansama yakeyi, wai miyake jirane?, zuciyarsa ta ce, “kanason sake kallon Rahma ne.
d’an tsaki yaja yamik’e yafice, shi adole zuciyarsa tayi k’arya.
Saida taga yafita sannan tafito, taje tasakama k’ofar key, sannan tazauna tagyara jikinta, tasaka Riga da wando na Pakistan, nakula tana son irin kayannan sosai.
Nawal ta tashi itama tayimata wanka tashiryata cikin wandon Jin’s da pink d’in T shert mai k’yau.
Falo suka fito, fitowarsu babu dad’ewa shima ogan yafito, haryayi wanka yashirya cikin jins blue da farar Riga sai zabga k’amshi yakeyi.
dinning suka nufa, Rahma sai sinne kai takeyi Dan kunya, shikam ko’a kwalar rigarsa, yanacin abinci Nawal namasa surutu, iyakarsa Yamata murmushi koya d’aga kai.
Rahma ta ce, ” azuciyarta, muskili kafi mahaukaci ban haushi.
Suna kammalawa Nawal taja hannun Rahma wai suje tamata lilo, fitowa sukai sukabarsa kwance saman doguwar kujera yana kallon film.
STORY CONTINUES BELOW

Sunacan a lambu Rahma NATA biyema Nawal suna lilo, jiyay falon babu dad’i Dan haka yafito, jiyo dariyarsu alambu yasashi nufarcan, Rahma na zaune akan lilo, Nawal na shillata suna dariya, k’arasowarsa yasa Nawal cewa lah papa kaima zona lilaku.
Kai ya girgiza mata alamar A’a.
Takwa6e fuska zatayi kuka, cikin takun k’asaitarsa yak’arasa wajen lilo d’in, Rahma tayi yunk’urin sauka Nawal ta ce, “momy kubiyufa zanyimawa, sandarewa Rahma tayi azaune, kafin ta farga Bobo ya haye lilo d’in amma d’an nesa da ita.
Da k’arfi Nawal ta hankad’a lilo d’in, aiko sukayi gaba kamar zasu fad’i, da Sauri Rahma ta ruk’unk’ume Bobo, shima yarik’eta.
Nawal Yar kwal uba tacigaba da lila lilo da k’arfi, basuda za6i bayan rik’e junansu dak’yau, Nawal dai sai dariya takema iyayen nata, saida tagaji Dan kanta sannan tadaina lilasu.
Bobo yabud’e idanunsa ahankali danjin lilo ya tsaya, ga Rahma na mutsu2n kwace kanta, yana sakinta tasauka, da Sauri tabar wajen, binta da kallo yayi yana murmushi, Nawal takatse masa tunani, baby d’orani muyi tare tunda momy tagudu.
daukarta yayi yad’ora sukacigaba da lilonsu zuciyarsa cikeda tunani kala kala.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Safna zaune gaban Abba da ummi da alama fad’a ake mata, Dan fukarnan adagule take.
Abba ya ce, ” wlhy nabakinan da wata uku zuwa hud’u kifito da miji a had’a aurenku keda amira, inbandama auren ameerar da sati biyu zan baki, amma Abubakarne yaceceki ya ce, “abari ahad’a bikin dan a samu sauk’i.”
To saikiyi gaggawar sanar da Wanda kikace kinason harkikaso wulak’antamu akansa.
Insha ALLAHU Abba zan kawoshi, nidai kuyi hak’uri kubar ganin laifina, ALLAH yariga yarubuta Dama shid’in Mijin k’anwatane baniba…
Dallah yimana shiru!!, ummi takatseta atsawace, Mara mutunci kawai, Indai duniyace aigaki gata nan, kuma koyaya Wanda kikace kinason yake wlhy haka ZAMU aura miki shi, kijecan kiji da bak’in halinki, tashi kibamu waje mu.
Mik’ewa Safna tayi tabar falon tana k’unk’uni.
Na ce, ” ALLAH ya shirya to.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Ad’an hanzarce takeyin aikin gidan, Sauri take tagama dawuri taje tayi girki Dan maigidan ya ce, “mata yau abokinsa zaizo da iyalinsa, tagama komai tsaf har girkin ta kammala d’akin bobone kawai yarage mata shima Dan yana kwance ad’akinne.
Saiwajen 12 yafito daga d’akin yafita danufin siyo ruwa datace masa babu.
Yana fita tashiga d’akin Dan gyarawa, tagama aikinta lfy lau, tsautsayi yasa takai hannunta kan wani hoton Ni’ima datayi bala’in k’yau, Ashe bai zauna da k’yauba aiko yafad’o jikake taratsatsa!!! ya tarwatse ak’asa abinka da gilas.
Hakan yayi daidai dashigowar Bobo falon, da hanzari yanufi cikin d’akinsa, aiko abinda yake zarginne yagani, dandanan fuskarsa ta canja kama idonnan sukayi ja danshi aganinsa da gangan Rahma tayi saboda batason ganin hotunnan tunda dai yasan mata da kishi.
Tunda yashigo jikinta ke rawa, tabud’e baki arazane zatayi masa magana yadaka mata tsawa.
Dallah yimin shiru, dama kina shigowa gyaramin d’akine danki kashemin hotuna?, to wlhy idanma kishi kikeyi da ita kidaina Dan babu yanda kika iya da ita, wannan dakike gani itakad’aice nabawa zuciyata, daga itakuwa babu wata mace dazata samu haka daga gareni, wlhy akan wad’an nan hotunan sainayi mugun sa6a miki, banason cikin da iskanci.
Rahma tamatso danufin tsugunnawa tabashi hak’uri amma abisa tsautsayi ta taka gilas ak’afa, runtse idonta tayi saboda azaba, dama ga hawaye tuni sun wanke mata fuska.
Tsawa yasake dama mata, dallah malama fitarmin ad’aki, kuma karna sake ganin k’afarki ad’akina.
Ran Rahma ya6aci sosai ganin yanda yake cimata mutunci akan hoto, Wanda inyanzu yaso zaikai amaida gilas d’in daya fashe, haka tataka k’afa tabar d’akin tana kuka, tanazuwa tazube akan gado, ga azabar da k’afarta take mata amma bata kulaba, sai kuka maicin rai data saki.
Duk abinnan yake faruwa Nawal tana can baya tana wasa, Rahma taturata wajene dantabarta tayi aiki, batason surutu.
Bobo kam tana fita yadurkushe agaban hoton, d’agosa yayi yana gogewa tamkar zai fasa kuka, muryarsa na Rawa ya ce, “kiyi hak’uri Ni’imana bada sanina tayiba, ALLAH ya gafarta miki ya yafe miki kinji.
Nawal tashiga d’akin Rahma tana kwala mata kira momy! Momy!!, tak’arasa cikin d’akin da murnarta, amma ganin jini ahanyar sai jikinta kuma yay sanyi, tak’arasa har bakin gadon tana kallon k’afar Rahma da gilas ke jiki ga jini yanata zuba ak’asan wajen.
Fitowa tayi da gudu tanufi d’akin Papan ta, har yanzu yana gaban Hoton adurk’ushe, papa papa zokaga k’afar momy jini yanata zuba dayawan tsiya.
d’agowa yayi yana kallonta, yanda tabirkice shima sai jikinsa yay sanyi, mik’ewa yayi suka nufi d’akin Rahma d’in, gsky shima abin yabashi tsoro ganin jinin dad’an yawa, ga gilas babba kafe ak’afarta, tana kwance rubda ciki tana darzar kuka.
Tsugunnawa yayi Kusada k’afar yakama gilas d’in zai cire tasaki wata k’ara wadda tasaka Nawal fashewa da kuka itama, ga gilas d’in yakafe dayawa, ganin karya k’ara jimata ciwo yasa yamik’e dasauri yaje d’akinsa yad’akko key d’in mota.
Dawowa yayi ya ce, ” tashi muje asibiti acire miki wannan kwalban.
Banza tayi masa tacigaba da kukanta, wani haushi yak’ara turnik’eshi, baisan lokacin daya sungumetaba yay waje da itaba, Nawal nabinsa abaya, Nawal tabud’e masa k’ofar motar yasakata aciki, suma suka shiga sai asibiti………
luv u oll my fans
(((C)))……….💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 21
Asibitin ya sulaiman sukaje, ALLAH yasosu sun tarar dashi.
Aiko ansha fama wajen cire gilas d’in nanan, Rahma tasha kuka dukta fita hayyacinta, ga k’afar harta d’an kunbura.
Shikansa Bobo ya tausaya mata, saiyanzu yake ganin abinda yay mata bai k’yautaba, to amma idan yatuna miyakai hannunta wajen hoton saiyaji ransa ya 6aci.
Da hakadai aka kammala, ya Sulaiman yamata allurai tad’an samu nutsuwa.
Bayan an kammala bobo ya ce, “ya yarinyar nan kuwa?.
Jikinta kam saidai muce alhmdllh, ammafa yakamata asan iyayen yarinyar nan Abdulmaleek, gashi kace zaku fara shiri’a ranar talata, kasanfa Alh sunusi dala mutumne mai had’arin gsk, sarai zai iya bincike akan yarinyar, kuma zai iya aikata kimai Dan ganin d’ansa ya ku6ta.
Hakane Yaya, amma inata iya k’ok’arina wajen Neman iyayenta, saidai kutayamu da addu’a kawai.
To ALLAH ya taimaka.
Amin dai, bari mubiya muganta saimu wuce gida.
Okey, kardai kamanta kusiyi maganin.
Babu damuwa, k’arasawa yay inda Rahma take fuskarsa babu walwa, yakama hannunta ta sakko.
Ya Sulaiman dake kallonsu ya ce, ” saidaifa kad’auketa kamar d’azu, Dan babu yanda za’ayi ta iya taka wannan k’afar.
K’ara 6ata rai yayi, kamar bazaiyi maganaba, saikuma ya ce, “Yaya ba ancire ba?, eh ancire, amma karfa manta yanda gurin yake a yanzu, idanmma kunje gida ad’an gasa k’afar da ruwan zafi.
Baice komaiba ya d’auketa, saiwani kauda kai yake daga saitin fuskarta, itama saita runtse ido Dan bata son ganinsa.
d’akin da yarinyar nan take yakaita, yadireta saman kujerar gaban gadon, lahh Muheebat! kece?, Rahma tafad’a tana kallon yarinyar.
Itama tashi tayi zaune tana dariya Dan ganin Rahma.
Bobo ya ce, ” kinsanta ne?.
Eh nasanta, K’anwar direban muce idris, dama sunata nemanta tun tuni wlhy.
Ajiyar zuciya bobo ya sauke ya ce, “Alhmdllh, yaciro wayarsa yakira Ya Sulaiman, babu dad’ewa kuwa ya iso, shima yaji dad’i sosai dajin labarin.
Sun ajiye magana akan anjima zasuje gidansu Muheebat, dukda bata iya magana to tanajin abinda suke fad’a, Dan haka taita murmushi.
Bobo Yakuma d’aukar Rahma zuwa Mota, daganan sukayi gida, motar tsit babu mai magana kamar wasu kurame, Bobo sai shan k’amshi yakeyi, itama ganin haka saita d’auke kanta, dama can suka baro Nawal zatabi ya Sulaiman gidansa.
Koda suka shiga harabar gidan saiya bud’e motar yay tafiyarsa ciki yabarta.
Rahma tayi wata dariya azuciyarta ta ce, ” kama dawo wlhy, dan babu inda zan motsa.
Aiko tayi zamanta amotar, shikam haryaje k’ofar falon saiyaji babu motsinta abayansa Dan haka ya waiga, can ya hangota cikin mota ko motsawa batayiba, afili ya ce, “wai mi waccan abar take nufi da nine?, koni bawantane dazanta d’aukarta ina ajiyewa mtsooow, yak’arashr maganar dajan tsaki.
Komawa yayi wajenta sai wani d’aurewa yakeyi, Rahma ta hangoshi yana tahowa, tayi murmushin mugunta tana fad’in kadaiji dashi.
Bemata maganaba yabud’e motar ya d’auketa, itako ta lumshe idonta kamar mai barci, haushine yak’ara turnuk’e zuciyar bobo, gani yake tana k’ara langya6ewa ne kawai.
Koda yadireta a gadon bai kalletaba yajuya ya fita.
Ita kuma taimasa gwalo��, wai dole dai ad’auketa. lol.+
Tana nan zaune har kusan minti talatin, harta fara tunanin yanda zata fita taci abinci Dan yunwa takeji sosai, tayunk’ura zata tashi taji wani azababben zafi, danhaka takoma ta zauna, wai miyasama tabar Nawal tabi ya Sulaiman ne?, yanzu da tananan ai data rage mata wani abun………bata rufe bakiba taji anturo k’ofar.
Kamshinsane ya tababbatar mata dashine, Dan haka tak’i d’agowa danko sallama bataji yayiba.
Tire yadire ak’asa na kayan break, Rahma tayi kamar bata ganshiba, shima ko kallo bata isheshiba yad’akko kofin tee ya mik’a mata.
Kamar bazata amsaba saikuma ta amsa Dan ganin yayi tamau da fuska kamar bai ta6a dariyaba, yamik’o mata filet d’in soyayyar doya.
Saman kujerar dake d’akin Yakoma ya zauna yana danna waya, ganin haka yasa tadake taci abincinta Dan yunwa takeji sosai.
k’asa² yake kallonta, aransa ya ce, “k’aryar ciwo kikeyi yarinya, tumda har kika iya share filet guda na doya, Rahma ta kalleshi ta ce, ” nagama.
Banza yay mata yacigaba da danna wayar, saida ya mula Dan Kansa sannan yataso yazauna saman durowar gefen gadon, maganin yacira yabata.
Tofa anan akeyinta, Rahma tayi kwalkwal da ido zatayi kuka, tsak’i yayi yana harararta, idan bazaki amsaba kibarsa kece zakisha wahalarki ke kad’ai wlhy, danni yanzuma zanbar miki gidan.
Yanda yake zabga ruwan masifa yasa ta k’ar6a, saidai tana hawaye tana sha, idan tasha d’aya saitayi kamar zatayi amai saikuma ta daure, shidai yana kallonta ta gefen idonsa Dan yacigaba da latsa waya, hakadai tadaure tasha maganin.
Tashi yayi ya d’auki kwanukan yafita dashi, babu dad’ewa yadawo da k’aramar roba da ruwan zafi aciki, sai k’aramin tawul.
Baiyimata maganaba yajawo d’ank’armin tebir na gilas dake kusada kujera ya zauna, Rahma ta ce, “kasada aranta.
K’afarta yad’auka yad’ora saman stool na madubi, itadai ikon ALLAH take kallo kawai.
Dukda yaga kallon datake masa bai kulaba yafara aikinsa batareda yabi takantaba, yasaka tawul d’in aruwan zafin yad’an yamatse, daganin yanda yake matsar tawul d’in kasan ruwan da zafi, amma Dan bak’ar mugunta ahaka ya nanama Rahma akan k’afar, wani wahalallen ihu tasaki, yay saurin rik’e k’afar yana harararta, kawai saitaji hawaye nabin kumatunta.
Raguwar banza yafad’a afili.
Itama ta ce, ” ruwanfa da zafi wlhy, yanda tayi maganar ashagwa6e saiya tsaya yana kallon bakinta, ta kauda fuskarta tana tura Baki gaba.
Shima bakin yata6e yacigaba da aikinsa.
Da zame zame da mazurai aka gama wannan gashin k’afar, yad’auki maganin shafawar ya shafa mata sannan yakwashe kayan yafice itakuma ta kwanta tana sauke numfashi.
STORY CONTINUES BELOW

Bai sake shigowa d’akinba harsu Ammar suka iso shida matarsa da yaransu biyu duk maza.
Cikin farinciki yataresu, yanda yaketa murmushi saika d’auka bashibane yagamawa Rahma mazuraiba yanzu.
Cikin falon suka k’araso, Sumayya matar Ammar ta ce, “nibanga amaryarba ko ka sakata ta 6uyane?.
Murmushi yayi ya ce, ” 6uyan lfy, tana d’aki kwance batada lfy.
Ammar yashek’e da dariya mutumina komun samu k’annen Nawal ne?.
Harararsa yayi kaifa bakada kirki wlhy, to Abu ta taka ak’afarta d’azu da safe.
Ammar ya ce, “ayya ALLAH yakiyaye gaba, amma yanda na sanka d’innan ai yanzu munsami baby duk wani zame ²n ka.
Kadaiji dashi d’an iska, bobo yafad’a yana nufar d’akin Rahma.
A zaune ya Tatar da ita tagama saka kaya, Dan k’afar tad’an saki shine taje tayi wanka.
Ki taso su Ammar sunzo.
To. tafad’a atak’aice, haryaje k’ofa takatseshi dafad’in bafa zan iya fitaba.
Cak yatsaya kuma bai juyoba, yakai minti uku ahaka saikuma ya waigo, yawani saki murmushin mugunta danyasan maganar dazaiyi, okey kinaso nad’aukeki Dan kinji Ammar ya ce, ” namiki ciki ko?, kinaso su tabbar kenan?.
Ido Rahma ta gwalalo waje ta ce, “nid’in?.
Baki ya ta6e tareda takowa har inda take, taho na d’aukeki nikuma namiki alk’awarin tabbatar musu da hakan.
Matsawa tayi gefe, ta ce, ” kabarsa kawai zan iya.
Dariya yayi ya ce, “Yar rainin hankali, yana gama fad’a yafice yana cigaba da dariyarsa.
Rahma tarike baki o ni Rahma dama haka mutumin nan ya ke?, barikiga natashi kafin yaje ya nafkamin wani sharrin.
Haka ta d’ingisa har zuwa falon, ta zauna suka gaisa sunata tsokanarta, itadai bata iya cewa komai sai murmushi, mik’ewa tayi danufi basu ruwa da abin motsa baki, ya ce, ” ina zaki?.
Ruwa zan basu tafad’a tana tafiya da d’ingishi.
Sumayya ta ce, “kinga dawo kizauna amarya, bari na d’akko mana aimu ba bak’i bane, Rahma ta ce, ” haba daga zuwanku sai asaka ki aiki?.
Karki damu kinji, idanma kika kusa haihuwa nan gidan zan dawo, hannu tasa tarufe fuskarta Dan kunya, Ammar Kuma yayi dariya, Bobo ya ce, “Ashe na huta nikam?.
“Aiko ka huta.”
Sumayya ce tamusu komai daya dace Rahma tayi, abincima atsakar falon sukaci, mutuminku sai wani kaffa² yakeyi da Rahma, ita abunma kunya da dariya yaringa bata, idan kukaga kulawar dayake bata saika d’auka haka suke kullum.
Har dare su Ammar suna gida, sai bayan isha’i suka tafi, bobo kuma yatafi d’akko Nawal Dan gobe zasu koma makaranta.
Rahma tad’an daddogara kamar gurguwa tad’an gyara abinda yadace sannan tayi wanka, shirin barci tayi tazauna jiransu.
Bayan wasu ‘yan mintuna da zamanta saigashi ya iso da Nawal akafad’a tayi barci.
Saman gadon ya kwantar da ita, Rahma ta ce, ” sannu.
Yauwa, tafad’a atak’aice.
Batabi ta kansaba harya sauyama Nawal kayan barci, shima baice mata komaiba yafita, babu dad’ewa saigashi da ruwa da Kofi, abakin gadon ya zauna yaciri magungunanta ya mik’a mata, tuni ta 6ata rai amma babu yanda zatayi haka ta amsa tana matse ido ta shanye, hawaye harsun cika mata ido.
Baki yata6e yayi kamar baiga hawayenba, yad’auki maganin shafawar yad’ago k’afarta yad’ora saman cinyarsa, maganin yashafa mata, ta lumshe idanu danji take kamar yana mata tafiyar tsutsa.
Shikanshi cikin nishad’i yake shafa k’afar, Dan yakai minti 7 yana shafa maganin, saida tad’an janye k’afarta sannan yadakata.
Mik’ewa yayi yamusu sallama yafita.
Rahma ta sauke ajiyar zuciya aranta ta ce, *_”Zaki na Ammi da Appa kafi karfin wargi”._*
_(Nikam Bilyn Abdul kirarin nata yabani dariya, nima zan kiya naringa yima my Abdul d’ina lol.)_
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Yau bobo dakansa yayma Nawal wanka, yaymata shirin makaranta, Rahma kuma tadaure tahad’a musu break da abincin Nawal na makaranta.
Sauri² sukayi break d’in suka fita.
Har harabar gidan Rahma tarakasu, tana musu addu’a, bobo daya tada motar yalek’o kansa yana kallon Rahma, ‘Yar gurguwar gidanmu akuladai karkuma akarya d’ayar.
Yana gama fad’a yafigi motar suka fice.
Ita maganar tasama dariya tabata wlhy, afili ta ce, “dama yanama mutane wasa?.
Tayi murmushi tareda shigewa ciki.
—————————+
Yana ajiye Nawal a school yanufi office, amma duk saurin dayakeyi saida yatadda mutane na jiransa, ciki harda Alh Sunusi Dala.
Kasancewar kowa yasan waye Alh sunusi dala suka barsa yafara shiga domin ganin Bobo.
Hannu yabashi suka gaisa, sannan ya ce, ” Alhaji mike tafe dakai?.
Alh sunusi yasauke ajiyar zuciya, Brr… abunda ke tafe dani babbane kuwa, d’ana ‘yan sanda suka kama tun ranar juma’a, kuma sunk’i bamu belinsa wai saisun kaimu kotu, gashi lauyana baya k’asarnan naturashi wajen wasu kayana a k’asar Chaina.
Alh to yanzu ni mikakeso namaka?, bobo yayi tambayar kamar baisan komaiba.
Saboda sunce munemi lauya, nasa abincikamin kwararren lauya shine aka kawoni wajenka, kuma nima idona ya tabbatar mini da hakan.
Shiru Bobo yayi yana karantar Alhaji sunusi, saida yaja minti biyu sannan ya ce, “Alhaji kozan iya ganin takardar sammacin da aka baku?.
A wannan mai sauk’ine aii Brr, Alh sunusi tafad’a yana mik’ama bobo takardar.
Saida yagama karantawa sannan ya ce, ” Alhaji gsky akwai Matsala?.
Matsalarmi kuma Brr……?.
Wato wad’anda suke k’arar d’anka sunzo sun sameni tun ranar juma’a, kuma nine lauyansu.
Wani huci Alhaji yasauke, saikuma yay k’ok’arin 6oye 6acin ransa, ya ce, “Brr kataimakeni kamaida musu, ni namaka alk’awarin zan biyaka nikin baninkin d’in abinda suka baka wlhy.
Murmushi bobo yayi, sorry Alhaji hakan bazai yuwuba, duk Wanda yad’aukeni aiki a farko shinake yimawa gsky, inabaka hak’uri akan hakan, saidai nace maka mutari gaba kuma……..
Kai k’aramin shashasha!!!! Alhaji sunusi yakatse Bobo a tsawace.
Shima Bobo ya katseshi ta hanyar d’aga masa hannu, Alhaji sauraramin nan office d’inane ba gidan kallon boll ba, ra’ayinane kuma nayi duk abinda nakeso alokacin danakeso gakuma Wanda nakeso, Dan zaman kaina nakeyi bana waniba…..
Kwafa Alhaji sunusi yayi tareda mik’ewa, yanuna Bobo dad’an yatsa yaro yarone, nakula bakasan koni wayeba, amma ina gab da sanar dakai, ni nafika zafin kai Brr…… Dan haka muzuba nidakai.
Mtsowwww muzuba mana Alhaji, nidakai za’a tantance damisar takarda.
Fuuuuuuu alhaji Sunusi yafice, masu tsaronsa suka take masa bayan.
Bobo kuma yaja wani wawan tsaki tareda zama saman kujerarsa.💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 22
waye Alh Sunusi dala?._
Alh sunusi dala rik’ak’k’en d’an siyasane, kuma d’an kasuwa Wanda yay zarra akan canjin Dala, matarsa d’aya haj Falmata da yaransu hud’u, Surayya itace babba yanzun haka tayi aure yaranta biyu, sai Haneef shikam babuma auren a tsarinsa, sai Hafeeza da Shareefa suduk ‘yammatane.
Alh Sunusi bashida kirki ko kad’an, mutumne mai matuk’ar had’ari, idan yanason Abu zaibi takowace hanya ya sameshi, yana matuk’ar Son Haneef kasancewarsa shikaid’aine d’ansa namiji, sosai Haneef yad’akko halayen mahaifinsa harma yaso zartashi, Dan Haneef tamkar d’an bunsuru yake wajen Neman mata, idan yakwafama mace tota shiga uku, kasancewarsa k’yak’yk’yawa gakuma kud’i saiya zama ‘yammatan dakansu suke kawo Kansu gareshi, Ak’alla Haneef yakai shekara 36 amma yak’iyin aure sai iskanci da ta6ara.
Kwata kwata haj Falmata bata k’aunar halin d’an nata, kullum cikin yimasa nasiha take da nuna masa kuskurensa, amma yayi burus da zancen nata acewarsa har yanzu bata wayeba.
Halin Haneef da haj Falmata take k’yamata shine yasa Alh Sunusi yake ganin bata son Haneef d’in kwata², aganinsa tafison yaranta matane.
Itadai kullum cikin nuna fasa ba haka bane take, amma baya ta6a saurarenta, Dan haka tazuba musu ido shida Haneef d’in.
Yaranta mata duk halinta suka biyo, suma basa k’aunar halin babansu da d’an uwan Nasu, amma babu yanda zasuyi saidai addu’a kawai.+
Toyanzu mugun halin Haneef yaja masa Shiga tarkon bobo, shikam bobo karanbani yaja masa shiga tarkon mahaifin haneef, Alh Sunusi dala, toko waye keda nasara?.
Saimun cigaba dabin labarin zamu tabbatar.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
K’afar Rahma ta warke, amma tasha bak’i ‘yan dubiya, ammi kanta saida tazo dubata, Matansu ya Ishaq ma haka duk sunzo, harsu ya ishaq d’in kansu.
Itakam daga Rahama saitace gara dataji ciwon, Dan kobabu komai acinkin kwana ukun kullum gidan yana cike da dangi asha hira, su khursiyya kuwa kullum suna gidan.
Kwata² tadaina gyarama Bobo d’akinsa, tun ranarma bata sake kallon ko hanyar d’akinba, su khairiyyane suke gyara masa idan sunzo.
Dama bawani shiga harkarsa takeba, to akwana ukunnan ma talura yana matuk’ar busy, Dan kullum yana danna laptop, wani sa’inma saiyakai 10 baidawo gidanba.
Dukda abin na damunta tanason kuma tambayarsa abinda ke faruwa?, amma tana tsoron wulak’ancinsa, Dan haka ta shareshi itama, tanadai tayasa da addu’a samun nasara akan abinda ya burkitashi haka.
+++
A6angaren bobo kam ya ajiye komai gefe, gaba d’ayan hankalinsa yabada akan shari’arsu da Haneef, bak’aramin shiri yayma shari’arba, Dan yayi bincike na musamman akan halayyar haneef, wannan yasa yakeson ceto sauran yara daga gudun fad’awa tarkon Haneef d’in na gaba, Dan ance mai halin bata barin halinsa.
Tun washe garin daya kai Rahma asibiti taga muheebat kuma yaji tasanta, da safe yakar6i address d’in gidansu Idris, tare sukaje shida ya Hamza da ya sulaiman har gidan suka maida muheebat.
Dangin hebba sunyi murna da dawowarta garesu, sunkuma sakama su bobo albarka gameda taimakon dasuka bama yarinyar, saidai sunyi kuka sosai akanjin k’addarar data afka mata.
Nansu ya Hamza sukaita lallashinsu, sukace sukwantar da hankalinsu zasu kwatoma Hibba hak’inta dukda dai budurcinta yatafi bazai dawoba.
Sunji dad’i sosai tareda yimusu k’yak’yk’yawar addu’a.
Bobo ya ce, ” zamu tafi, amma ga no. d’ina Indai dawata Matsala sai’a kirani, sannan akan rashin maganar heeba d’in kodama tanada wannan matsalar?.
Eh damacan bata iya magana tun bayan ciwon k’yanda datayi lalurar ta sameta, amma tanajin abinda ake fad’a cewar baba Hamisu mahaifinsu hibba da idris.
ALLAH sarki, amma baba kunta6a d’aukar mataki akan hakan?. Dr sulaiman ya tambaya?.
A’a yaro, gsky bamuta6a yiba kasancewarsa kada muyima ALLAH shishshigi.
Hakane baba amma yana da k’yau anema mata magani, Dan naga zata iya samun lfy, ban yimata aikin bane dama saboda inaso saida izininku, amma insha ALLAH zamu yimata wani aiki komai zai dawo daidai, Dan matsalarta bata cika tsananiba.
To shikenan mungode ALLAH yasaka muku da alkairi, yayma Rayuwarku albarka, ALLAH yajik’an mahaifa.
Ameen suka fad’a suna mik’ewa, sukai musu sallama suka tafi akan sai suhad’u a kotu ranar talata.
STORY CONTINUES BELOW

*…………………..*
Washe gari talata su bobo suka shiga shari’a.
Tun azaman farko hankalin lauyan Haneef yatashi, dan tabbas yasan Bobo kwarone tunda bayau suka fara karawaba, yasan kuma bobo baya tsayama Mara gsky koyaya suke kuwa, komin k’arfin alak’arsu.
Zaman nan nafarko kawai bobo yakawo hujjoji da dama wad’anda suka saka mutane dayawa yadda Haneef ya aikata abinda ake zarginsa dashi, amma dayake alk’ali yaci kud’i saiya d’aga shari’ar sai nan da sati biyu masu zuwa.
Anan lauyan Haneef yanemi Belin haneef amma bobo yace Sam bai yardaba, Alk’ali yasan halin bobo dabin kwakwaf dama kuma bawani shiri sukeba, Dan haka yace k’orafi bai kar6uba, zasucigaba da rik’e Haneef.
Ran Alh Sunusi ya6aci, sai kallon miye haka?, yakema Alk’ali.
Alk’ali kuma yanamasa magana da ido akan subi ahankali.
Duk abinda ke faruwa bobo yana kallonsu, Dan haka yasaki murmushin sa na mugunta, Wanda Ammar kankira da yafi saukar Boom ban tsoro, amma ga Wanda yasan ma’anar murmushin ga bobo kenan.
Suna fitowa daga shari’ar gida bobo yay shirin tafiya, daka gansa Kasan yana cikin farinciki, bud’e motarsa yayi zai shiga Alh Sunusi da masu tsaronsa suka k’araso wajen, bobo yaja sirin farin gilas d’insa k’asan ido Wanda yadawo k’arshen hancinsa ya tsaya.
_( na ce, “anyi shirin rashin arzik’i kenan��)?._
Alh Sunusi ya watsama bobo harara, yaro har yanzu kanka yana rawa ko?.
Murmushi bobo yayi, tareda bud’e motar yawatsa kayan hannunsa a sit d’in baya, yarufe murfin sannan yajingina da motar yana kallon Alh Sunusi cikeda basarwa.
Alh wai minayi maka hakane dazafi? kasaka rayuwata agaba.
Yakamata ka lura dawani Abu, ni lauyane mai zaman kansa, banida banbanci dad’an kasuwa, so saina gadamar saida maka hajata, idan banida ra’ayi saikaje gaba kasiya, Alhaji karik’e girmanka, banaso mufara game tare dakai, Dan akwai matsala.
da d’anka nake shari’a bada kaiba, so ka kalli gabanka kada katsaya kallon ruwa kwad’o yayi maka k’afa wlhy.
Yana gama fad’a yashige mota, Alh Sunusi kuma yana zabga ruwan masifa da bala’i, jiyake yak’ara tsanar yaronnan.
Fuuuuu bobo yaja mota tareda bud’ama Alh Sunusi k’ura, by Alhaji sai zama na biyu, bobo yafad’a yana figar motar yabar harabar get d’in.
Kwafa Alhaji Sunusi yayi, tareda fad’in zakasan koni waye yaro.
.×.×.×.×.×.×.×.×.×.×.
Da sallamarsa yashigo falon, saidai shiru babu kowa, yakalli agogon hannunsa 12:15pm Nawal bata dawo school ba, aransa yace to ina momynta?.
K’arar Rahma yajiyo daga d’akinta, da sauri yanufi d’akin, hakan yayi daidai dafitowar Rahma dagudu daga bayi, daga ita sai tawul, jikin bobo tafad’a tana rawar jiki, bashida za6i saina rungumeta, yanda jikinta kerawa kawai ya isa kasan wani abune yabata tsoro.
“K!, miya farune?.”
Dadyn Nawal Dan ALLAH kataimaka ka kashemin shi wlhy inajin tsoronsa, kataimakeni plzzz, tafad’a tana kuma ruk’unk’umesa, tamkar zata fasa jikinsa tashige.
Bobo ya girgizata “k kinutsu kifad’amin minene mana?.
d’agowa tayi tana d’an hakki, tuni idanun nan NATA masu kasheshi sun wani sake fitowa, yakula duk yanda yarinyar tashiga rud’ani ko tsoro idonta baya canja kala….. Tunani takatse masa da nuna hanyar bayi.
Hannunta yakama suka nufi bathroom d’in, kinga Nutsu ki nunamin banason shirme, abayansa ta mak’ale, tashiga waige² Neman abinda yatsotata saidai wayam yabar wajen.
Yaja tsaki yarinyarnan ALLAH kinyi mugun rainani, yanzu inbanda raini minene a Bathroom d’innan?.
Wlhy naganshi da idona, saidai idan ya 6oyene, harara ya watsa mata yayo baya zai fita yad’an matseta da bango.
Sukur² taji abayanta, Dan haka tayi saurin turashi takalli bango, wani k’ara takuma fasawa tatafi luuuu zata fad’i.
Da sauri yatareta tafad’o jikinsa, Tawul d’in jikinta ya kwance, yakai dubansa ga abinda tagani, wata ‘Yar k’aramar k’adan garuwace, (Tsaka), da alama ta’inda zata fita ma take nema, yamaido kallonsa kan Rahma wadda yakeda tabbacin ta suma, runtse idonsa yayi Yakuma bud’ewa a kan k’irjin Rahma, shima jikin nasa rawa yafarayi, da sauri yakauda kansa yaja tawul d’in ya rufe mata jikinta, d’aukarta yayai cak, jikinsa dukya mutu yafito da ita zuwa kan gado.
Zama yayi yadafe kansa Dan yau surar Rahma ta tsokalishi, babu abinda yake ambata sai _”Hasbinallahu wani’imal wakil”_, tuni idonsa yakad’a yay jajur, zumbur yamik’e yafita kafin yayi aika², kichin yashiga yabud’e firij yakwaso lemon tsami har biyar, jikinsa har rawa yake wajen yankawa, dandanan yamatse ruwan lemon akofi yashanye, ko azababben tsamin baijiba.
Yadire kofin saman tebird’in tsakkiyar kicind’in, yadafe hannayensa biyu tareda runtse idanu, yakai minti10 ahaka sannan yabud’e ido yaja d’aya daga kujerun kicind’in yazauna yana sauke ajiyar zuciya, tamkar jinjirin daya kwana ya wuni baisha nonon mamansaba.
Nanma kwantar da kansa yayi atebir d’in, yad’an jima ahaka sannan yatashi jikin a sanyaye yad’auki ruwa mai sanyi ya kwankwad’a, yakusa shanye gora d’aya kafin yacire yana sauke numfashi, goran ruwan yad’ago ya kalla sannan yafice daga kicin d’in.
d’akin Rahma Yakoma, har yanzu tana nan inda yabarta, yak’arasa gaban gadon ya zauna, yayyafa mata sauran ruwan hannunsa yayi, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, saikuma tamik’e zumbur ta kwakumeshi tana fad’in dadyn Nawal plzzzz kaje kafiddata wlhy banason ganinshi wayyo ALLAH ummi kizo ki ceceni na bani………
Ganin yanda take gogamasa jikinta gashi tabi ta k’adandaneshi, idan suka k’ara d’aukar lokaci ahaka bazai iya jurewaba, sai kawai yadaka mata tsawa.
k!!!!!!!, dallah ki nutsu banason shashanci, miye abin tsoro a tsaka?, duk kinbi kin wani rud’a kanki har kina k’ok’arin illatamin lafiyata Mtsooooow, yaja tsaki.
Tuni Rahma tashiga hankalinta, amma har yanzu jikinta rawa yakeyi, harma batasan Tawul d’inta ya k’ara zamewaba.
Gaba d’aya hankalin bobo yakuma tashi, yatsurama k’irjin Rahma ido tamakar zai cinyeta d’anya.
Ganin kallon k’urillar dayake mata yasa itama ta kalli jikinta dantaga miyake kallone haka….. Idanu tawaro tareda jan bedsheet d’in ta k’udun dune jikinta.
Mik’ewa Bobo yayi yayo kanta…………….💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 23
Safna ga sir Hamza canfa yazo, baseera tafad’a tana kallon Safna data rafga tagumi kamar wadda akace ummi zata mutu yau.
Zumbur tamik’e tana fad’in habadai?.
ALLAH kuwa yanzu yashiga office d’insa.
Kinga tashi muje kirakani.
Mubari Zeenat ta iso mana tunda ta ce, “tana hanya.
Mtsooow dallah shareta tashi muje, kinsanfa bakomaine take Goya mana bayaba.
Mik’ewa Baseera tayi tana kakka6e doguwar rigarta, hakane kuma wlhy, kinsan zeenat ya ustaz CE.
Aii saitaji da ustazancin ta ita kad’ai.
Saida suka kwankwasa yabasu izinin shigowa, sannan suka shiga, bayan sun gaidashi baseera ta ce, ” Sir mun biyo sawune.
Kallonsu yake cike da mamaki, amma baice komaiba yarubuta musu number Bobo, ya d’ago yana kallonsu, ban tanbayesaba Dan ina mantawane, amma baridai yau nabaku Dan kun fara bani tausayi, dukda bansan mizakuyi da no. d’in *Abdulmaleek!* ba.
Wlhy bawani mugun Abu zamuyi da itaba, kawai zamu sada zumincine.
Girgiza kai kawai ya Hamza yayi, yamik’a musu number, gashi to, nadai baku number sa gama gari tunda bannemi izinin saba bare nabaku number sa mai muhimmanci, amma insha ALLAHU zaku samesa da wannanma.
Mungode sir, ALLAH yak’ara girma.
Amin yafad’a yana binsu da kallo atak’aice, shifa mamaki suke bashi wlhy, koda yake basuda laifi k’anin nasa ya had’u, ga k’yau ga iya wanka, uwa uba kamun kai.
Cigaba yayi da aikin gabansa kawai.+
A can kuwa suna fita Safna ta daka tsallen murna tareda rungume Baseera, wayyo k’awata yau na mallaki number Bobona.
Dariya baseera tayi, kinga Laila karki karyani nikam.
Miye kuma laila?, safna tafad’a tana yatsine fuska.
Dariya baseera tayi, laila majnun mana, aigara mufara kiranki Laila kafin bobo yazama majnun.
Dariya Safna tayi tareda Jan hannun Baseera suka nufi class.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Baya Rahma tashiga matsawa tana fad’in inna’lillahi wa’inna ilaihirraji’un.
Ina Bobo baisan tanayibama, kanta kawai yayo tamkar wani zaki maijin yunwa.
Gadon ya hawo yafincikota jikinsa, jikinta sai Rawa yake, ga kukanta ya k’aru, bakinsa da nata ya had’e yashiga wasa da harshenta tamkar yasamu alawar lollipop, agefe kuma hannunsane ke murza ko ina najikinta, Rahma dai sai dukansa da tsungune takeyi, amma baimasan tanayiba, shidai sak’o kawai yake burin isarwa.
Yakai tsawon minti 13 yana Abu d’aya, tuni Rahma tabar kukan tsoro saidai na ceton kai.
Shikam Bobo idonsa yarufe baimasan mi yake aikatawaba, shidai kawai burinsa yake son cikawa, jin hannunsa a k….. Yasata k’ara rikicewa.
Shima da sauri yasaketa danjin pad alamar tana period kenan.
Zubewa yayi agefe sai wani wahalallen numfashi yake saukewa, Rahma tayi saurin sauka daga gadon takoma jikin bango ta mak’ale tana kuka, sai kallon yanda Bobo yake fidda numfashi tamkar zai mutu takeyi, nan take kuma tausayinsa yakamata, jitai hawayenta sun k’aru.
Tanaso taje ta taimakeshi amma tana gudun karya k’ara damk’arta.
Sunkai minti15 ahaka, shi yana cikin wahalar ciwon mara ko magana yakasa mata, itakuma tana cikin tsoro da abinda yamata gakuma halin dayake ciki abin tsoro.
Bobo ya daure dak’ar ya ce, “ki matsemin lemon tsami please zan mut u……….yak’arasa maganar da k’yar danji mararsa da kansa tamkar zasu fashe.”
Da gudu tafita zuwa kichin, cikin sauri tamatse lemon tsami wajen takwas, dama tasaka ruwan zafi kad’an awuta, tajefa lifton uku dantaga wani sa’in haka yakecewa ta dafa masa, juyewa tayi akan ruwan lemon tsamin tad’auka tanufi d’akinta yanata turiri.
Da k’ar ya iya tashi yakar6a, dukda zafin da shayin yake dashi bai sauraraba yakafa kai ya shanye kamar yasamu ruwan sanyi.
Mik’amata kofin yayi yakoma yakwanta, jikinsa har Rawa yake, ya ce, ” lullu6eni sanyi nakeji, kuma ki kashemin AC.
Duk abinda yace tayi masa da saurinta, sannan takoma gefe tazuba masa ido.
Lumshe idonsa yayi, danda nan zazza6i ya rufeshi, jikinsa yad’auki azababben zafi kuwa.
Rahma sai kallon sa takeyi tana hawaye, yanzu ba kukan abinda yaymata takeyiba, kukan halin dayake cikin takeyi, tarasa yanda zata fassara al’amarin nasa.
Idonsa alumshe yake amma yana kallonta ta k’asan idonsa, saiyaji tama k’ara bashi haushi.
Tunda yake baita6ajin abinda yaji yau ga mace ba sai akan Rahma, shekararsa wajen 5 babu mace, dukda yasan yana cikin buk’atar macen, amma hankalinsa bai ta6a tashiba irin yau, yarasa wace irin mace ce Rahma da jikinta yazame masa tamkar wani magana d’isu, jiyake tamkar zai mutu Dan azaba, amma lemon tsamin data kawo masa yad’an rage masa azabar dayakeji, yamanta tsawon lokacin daya d’auka rabonsa da zazza6i mai zafi kamar haka, yarintse idonsa yana ambatar sunayen ALLAH.
Zuwa wani lokaci kuma sai barci ya saceshi.
Rahma ta sauke ajiyar zuciya, yanzu kuma matsalarta d’aya shine a ina zatayi wanka?, Dan bazata sake shiga bayin taba sai an kashe tsakar can.
Zuciyarta ta ce, “kije d’akin mijinki tunda barci yakeyi.
Aiko tayi na’am da wanga batu, d’akinsa tanufa ta shiga bayinsa tayi wankanta sannan tafito.
Harta shirya yana barci, kichin taje tafara girki, zuwa 2:00pm tagama takuma gyara ko ina, tana falo zaune tana kallon Hausa film Nawal tadawo, direbanta ya d’akkota.
Dagudu tashigo gidan tana kiran momyna! Momyna!!, Rahma tamik’e da sauri Nawal tafad’a jikinta, d’agata tayi tana juyi da ita afalon suna dariya.
Hayaniyarsu ce ta tada Bobo, yamik’e dak’yar Dan Marar tasaki saidai zazza6in shima kad’an, falon yafito, sukam bama su gansaba sunata murnar ganin juna itada Nawal d’inta.
d’an murmushi yayi yashige d’akinsa, ko babu komai yanajin dad’in yanda Rahma take kula masa da yarinyarsa, idan ba fad’a maka akayiba bazaka ta6a cewa ba ita ta haifetaba, saidai kawai idan ka kalli Rahma d’in zakaga yarinyace batakai ta haifi kamar Nawal ba, ammafa duk wata kulawa irin ta uwa akan d’anta Rahma tana k’ok’arin bama Nawal, kuma har zuciyarta takeson yarinyar.
Kama hannunta tayi suka shiga d’akin, tabi gadon da kallon mamaki to ina yaje?, tafad’a azuciyarta, tad’an lek’a bayi daga nesa taga wayam, inaga to yana d’akinsa.
Da wannan tunanin tacirema Nawal kayan makarantar.
‘Nawal!.’
Na’am momy.
Kije d’akin papa kigani barci yakeyi, idan barci yakeyi muje can namiki wanka.
Lah momy bayinmu fa?.
Akwai ojuju aciki ina tsoron shigane.
Kai, momy kema kinajin tsoron Ojuju.
Dariya Rahma tayi ta ce, “kinga kedai jeki duba kidawo.
Tamata hakane Dan tambayar ta tsaya haka.
Da gudu Nawal tafita sai d’akin Papanta.
Fitowarsa kenan daga wanka, yana zaune abakin gado yana shafa mai, Nawal ta shigo aguje tafad’a jikinsa.
Uccch yafad’a yana rungume Nawal d’in, saboda yaji zafi data fad’a jikinsa.
baby bana hanaki guje²n nan bane?.
Sorry papa nadaina.
Yalumshe idanunsa yana kad’a kai, toya School?, harkun dawo?.
Eh papa, tad’ago tana kallonsa, papa kaima bakada lfy kamar momy?.
Kallonta kawai yakeyi yakasa magana, ta girgizashi kaji papa, ajiyar zuciya ya sauke, a’a baby lafiya ta k’alau, itama momy aita warke ko?.
Eh mana ta warke, yanzuma catayi Nazo naduba idan kana barci saitazo tamin wanka a bayinka, wai bayinmu akwai ojuju tanajin tsoronsa.
Papa dama idan mutum yay babba yanajin tsoron ojuju?.
Bobo dake shafa mai yanajin zancen Nawal yayi murmushi, baby Momynki tacika tsaorene, amma zan koya mata yanda zata daina, jekice mata tazo tamiki.
Papa nima zaka koyamin Dan nadaina tsoron ojuju d’in?.
Eh zan koya miki, jeki kirata.
Fita Nawal tayi kiran Rahma.
Momy tahoto kimin.
To Babyna, amma papa fa?, yananan ad’akin.
Atunanin Rahma yana barci Nawal take nufi Dan haka takama hannunta suka fito zuwa d’akin bobo.
Kanta tsaye tashiga d’akin, saikuma tatsaya cak Dan ganin bobo tsaye yana saka ma6alin rigarsa, baya tayi zata koma, batareda ya kalletaba ya ce, ” kizo kimata wankan mana.
Rahma tayi k’asa da kai kamar wata munafuka tanufi bayin rik’eda hannun Nawal.
Shikam baki yata6e yad’auki brush yana k’ara kwantar da sajensa bak’i sid’ik, yak’ara fesa turare sannan yafice daga d’akin.
Masallaci yanufa, saida yayo sallah yadawo sannan ya d’auki Jakar aikinsa daga fallo, yamanta a can yabarta, yacire laptop d’insa da wayoyi ya ajiye a tebird’in tsakkiyar falon sannan yakawo jakkar d’aki Yakuma fita.
d’akin Rahma yashiga, yanufi bayimta danya kashe matsa tsakar, dube² yahauyi, can yahangota kwance a bango, tsintsiya yasa yabugota tafad’o, Yakuma bugunta ta mutu, yawanke hannunsa yafito.
Daidai nan Rahma tashigo d’akin itada Nasal.
Batareda ya kalletaba ya ce, “gatacan na kashe saiki fidda.
Tuni hawaye sun cika idon Rahma, kanta ak’asa tace, ” Dan ALLAH ka fidda wlhy bazan iyaba.
Eh tunda nazama yaronki ko?.
A’a Dan ALLAH ka taimakeni nidai.
Tausayi tabashi, yalura harga ALLAH tsoron tsaka takeyi, komawa yayi yasharota a faka, yay nufin tsokanar Rahma, danhaka gadan gadan ita yanufa.
Ganin tsaka afaka kuma wajenta yayo tadaka tsalle tareda kwallah k’ara.
Tabashi dariya amma saiya gimtse saida yafita sannan ya shek’e da dariya harda rik’e ciki, mai gadi yana hangensa abin yabashi mamaki Dan yadad’e baiga Bobo yana dariya hakaba, dama dariya mai yawa ba sabon bobo bace, sai Abu yakai matuk’ar tik’ewa yake bashi dariya, murmushinma saiya gadama yakeyi balle dariya.
Komawa yayi ya k’ara wanke hannunsa, sannan Rahma tana shirya Nawal.
Fallo yadawo ya kwanta saman doguwar kujera.
Ya d’auki remote ya canja tasha, babu dad’ewa suka fito suma, Nawal taje ta zauna kusadashi tana fad’in baby kamomin MBC 3 naga cartoon.
Rahma ta ce, “Nawal mikikace?.
Baki tarik’e kamar wata babba, momy yi hak’uri bazan sakeba, Dan ALLAH karkice kin fasa zuwa danifa.
Zanje dake ammafa idan kin daina.
To na daina, papa aidai yanzu bana cemaka baby ko?.
Bobo yakalli Nawal yana kad’a kai, yamaida kallonsa kan Rahma data nufi dinning, murmushi yad’anyi.
Baby ina momy ta ce, ” bazataje dakeba indai kina cemin baby.
Nawal takawo bakinta saitin kunnen Bobo ta ce, “catayi bazataje dani makkah da madina ba muga kabarin Manzon ALLAH.
(S,A,W) BOBO yak’arasa mata, to baby yanzu kindaina cemin baby kenan?.
Eh bazan sake fad’aba, momyna ta ce, ” nace maka papa.
Jawota yayi jikinsa ya rungume, yabata kiss akumatu, I luv u my baby.
Itama ta ce, “luv u too my papa.
Rahma tak’araso da kuloli ta ajiye a tsakkiyar falon bayan ta janye tebir d’in, saida tagama kawo komai sannan ta ce, “ga abinci.’
Mik’ewa yayi zaune yana satar kallon Rahma, itakam sai duk’ar dakai takeyi, yakula batason had’a ido dashi tun d’azu, ko kallan ma inda yake batayi.
Haka suka zauna cin abincin Wanda Bobo kejin dad’insa.
Yasani lokaci d’aya Rahma taja zuciyarsa rusuna akan burin daya d’auka nayi mata rashin mutunci agidansa harsai tagudu da k’afarta, yafara gudanar da shirinsa ta hanyar fita harkarta, hartayi tsawon kwana 8 a gidan bata ganshiba, amma daga randa yakawo Nawal gidan yaci girkinta sai zuciyarsa tayi sanyi da d’ora alamar ? Akanta.
Abi na biyu shine son datake nunama gudan jininsa Zuh’ra (Nawal), wad’an nan abubuwan suntaka rawar gani wajen ganinta da mutumci da daraja, dukda har yanzu bazaice yana sontaba, ‘Dan Ni’ima ce kawai macen dazaiso aganinsa‚’’ to amma yabama Rahma wani 6angare azuciyarsa kad’an kodan k’aunar Nawal datakeyi………….wringing d’in wayarsane yadawo dashi hayyacinsa, yakalli Screen d’in wayar batareda ya d’aukaba, bak’uwar number yagani.
Sharewa yayi yacigaba da cin abincinsa, aka k’ara kira akaro na biyu, nanma yay burus.
Rahma ce tad’ago ta kallesa danjin ank’ara kiran wayar, cikin sa’a kuwa suka had’a ido, tai saurin janye nata, shikuma yad’an lumshe idanunsa.
Ba’a sake kiran wayarba harsuka kammala cin abincin Rahma tagyara wajen.
Saman kujera yakoma ya zauna, yad’ora kafafunsa saman tebir, yad’auki laptop ya d’ora saman cinyarsa yana Dane dannensa na fama.
Rahma kam homework take koyama Nawal.
Falon yayi shiru kowa yana harkar gabansa sai k’arar TV kawai Dana AC, Wayar d’azuce dai aka k’ara kira.
Wani wawan tsaki Bobo yasaki, afusace yad’auki wayar yana mita, wai miyasa mutane suke San takuramin ne?, ina gidan nawama baza’a barni nahuta da iyalina ba mtsooooow.
Rahma dai tana jinsa bata d’agoba, aranta tace su iyali manya.
Wayar yad’auka yasaka akunnensa batareda yayi maganaba………….💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 24
Safna ta mik’e zumbir danjin and’aga wayar, saisaita kanta tayi ta ce, “Assalamu alaika.
Saida yaja aji sannan ya ce, ” wa’alaikissalam.
Safana ta ce, “ina yini?.
Lfy, ya amsa atak’aice.
Rasa mizata kuma cewa tayi, Dan duk muryarsa ta rikitata, gashi yana amsa mata magana ad’age.
Abinne yafara bashi haushi, amma kasancewar yasan number data kira ta harkar aikinsace saiya dake, yayi tunanin akan aikine.
Yakatse shirun dafad’in mikike buk’atane?.
Uhm….u…u Dan ALLAH kozan iya samunka office gobe idan ALLAH ya kaimu?.
Lumshe idanunsa yayi yabud’e, ya ce, ” akanmi kikeson ganina?.+
Gabad’aya ta daburce, tarasa mizata fad’amasa, jin takasa magana sai kawai ya yake wayar yay tsaki, gaba d’aya kashe wayar yayi ya wurgata gefensa yana mita.
Duk abinda ke faruwa Rahma tanajinsa, saidai batasan mi ake fad’a ad’ayan 6angarenba.
Aikinsa yacigaba dayi, itama yacigaba da koyama Nawal aikinta na homework.
Acan kuwa safna kaita dafe, takira Baseera danta bata shawara
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*
Safna wai mikikeyine har yanzun baki fitoba?, wannan wane irin yinine har k’arfe 2 ba’a tafiba?.
Ganina fitowa ummi, safna tafad’a tana figar handbag d’inta.
Afalo ta Tatar da ummi tsaye da bak’ar leda ahannu.
Ummi tamik’a mata ledar ga wannan ki kaimata, Safna Dan ALLAH ki kama kanki, kingadai gidan mijin k’anwarkine.
Karki damu ummi, insha ALLAHU babu abinda zai faru wlhy, ainamiki alk’awari zan canja nakoma yanda kikeso.
To ngd ALLAH yayi miki albarka.
Amin ummi na safna tafad’a tana fita.
Hartakai k’ofa saikuma ta waigo, ummi wai miye wannan d’in?, tafad’a tana kallon ledar da ummin tabata.
Karki damu zankirata namata bayani.
Ummi ni baza’a fad’aminba.
A’a lokacinki bai zoba, ai yanzu autana takwace girman, tazama Yaya kinzama k’anwa.
Baki safna tatura tafice, aranta ta ce, “ummi nasan kayan matane aii.”
Tana Shiga motarta ta kalli wayarta, hankalinta dukya tashi ganin bai bata amsaba, tunranda takirashi yakashe wayar saita k’yaleshi bata sake kiraba.
Yaudai abin ya dameta shine tatura masa message akan yabata address d’in office d’insa tazo, amma shine har yanzu babu kira babu sak’o.
Ranta duk adagule yake, takirashi sau wajen uku yak’i ya d’aga, hak’ura tayi tatada motar tanufi gidan Rahma.
Dama Dan tanason zuwa wajen bobone ta ce, “ma ummi tanaso yau taje wajen Rahma.
Ummi tayi murna, azatonta Safna tafara hankaline.
“Araina na ce, “koya zata kaya?.”
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Yana zaune a office yaduk’ufa da duba wasu takardu, kallo d’aya zaka masa kagane yana matuk’ar busy, takardun dayake dubawa kuma sunada muhimmanci.
Yana kallon wayarsa tana wringing yay burus da ita, Dan baya k’aunar abinda zai dakatar dashi daga aikin gabansa.
Kwankwasa k’ofar office d’in akayi, sanin sakatariyarsa ce kawai keda wannan damar yasa ya amsa da yes.
Turo k’ofar tayi tashigo, haryanzu bai d’agoba ta had’iye wani yawu tareda tsura masa ido tamkar zata lashesa, sir kayi bak’o.
Waye?, bobo yatanbaya kansa har yanzu yana k’asa.
Cikeda salo ta ce, ” bak’on jiyane Alh Sunusi Dala.
Sai yanzu yad’ago, aransa ya ce, “mi mutumin nan yakeso danine, afili kuma ya ce, ” kigaya masa bana buk’atar ganinsa, kuma……..saikuma yayi shiru ya ce, ”jeki wannan ba aikinki bane.
fita tayi cike da salo.
Batamasan shi tuni yamaida Kansa ga aikinsaba.
Zuwa tayi ta Isar da sak’on oganta ga Alh sunusi, maganar tak’ara Sosa masa rai, amma tunda bobo yak’i bashi had’inkai to lokaci yayi dazai d’auki matakin k’arshe akansa.
Fuuuu yabar wajen, masu gadinsa suka take masa baya.
STORY CONTINUES BELOW

“na ce, “humm kowane mataki kuma Alh sunusi ke shirin d’auka akan bobo?.��”
+++
Da sauri yad’ago danjin anta6ashi, danufin yin bala’i yad’ago azatonsa Alh sunusi ne yanunama sakatariyarsa fin k’arfi yashigo, ganin Ammar ne saiya sauke ajiyar zuciya tareda yin murmushi.
Ammar ya ce, ” mutumina irin wannan fusata haka?, tamkar zaka bigeni.
Ajiyar zuciya Bobo ya sauke kayi hak’uri wlhy nazata wannan shashashanne Alh Sunusi.
Murmushi Ammar yayi ya ce, “munzo shigowa naga fitarsa Ashe na shaida motocin nasa kuwa.
Baki bobo yata6e batareda yayi maganaba.
Saican yace halan yauma kazo kacikamin bakin office da yaranka?.
Hhhhhhh kaima Kasan dolene Dan babu yanda za’ayi subarni nafito ni kad’ai.
Bobo Yakuma ta6e baki, Sakai awahala kenan, haka kawai ace duk Inda mutum zayi ana binsa tamkar wata jela?.
Girman kenan my guy Ammar yafad’a yana dariya.
Ammar ya ce, “mutumina kafa rame wlhy mike damunka?.
Bobo yafitar da huci mai zafi, babu komai Ammar.
To shikenan tunda babu komai yafad’a yana mik’ewa.
Da sauri Bobo yaruk’oshi Dan yasan haushi yaji, yi hak’uri abokina zauna muyi magana.
Ammar yadawo yazauna, wlhy Abdulmaleek kana bani mamaki yanda kake iya 6oyrmin wasu al’amura naka awasu lokutan.
Bobo ya ce, ” kayi hak’uri Ammar bawai ina 6oye maka wani Abu baneba, saidai ina ganin wannan sirrin gidanane, dukda nasan babu abunda zan iya 6oye maka arayuwata, kai kad’aine abokina Dana yarda dashi, nasan kaima hakane.
Hakane Bobo amma Dan ALLAH miyasa kake 6oyemin abinda ke damunka?, ina kula dakai tunda nadawo kana cikin damuwar datafi tada akan Rasuwar marigayiya Ni’ima.
Sabodafa damuwar dakake ciki su Appa suka yanke shawarar yimaka Aure, to amma maimakon asamu sauk’i sai kuma damuwarka ta k’aru.
Minene damuwarka Abdulmaleek?, kasanar dani mu nemo mafita.
Bobo yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, yadafe tebir d’in gabansa da hannu bibbiyu.
Wato Ammar da ina cikin kewar matatane Dana rasa, dakuma tausayin Nawal na rashin uwa, wannan yasa nak’iyin aure dukda dama Kasan matan bawai suna agabana bane, su Appa sun takura nayi aure harda kai aciki, amma na ce, “muku har yanzu ban shiryaba, an auramin Rahmane saboda bijirewar yayarta akan aurena.
Tundaga randa aka kawo yarinyar gidana ban k’ara yarda ta ganniba saida na d’akko Nawal..
” amma kasan wani abin mamaki?.”
Ammar ya girgiza kai.
Koda muka shigo gidan saitamana tarba ta mutunci, ko kad’an bata nuna fushinta akan rashin zuwana garetaba.
Wannan itace jarabawa ta farko data cinye, saikuma yanda take kula da Nawal, wlhy idan baka saniba bazakace ba ita ta haifetaba, abu na uku tsafta, iya girki, saidai akwai shegen muskilanci atareda yarinyar wlhy.
Ammar ya tuntsure da dariya, to aii indai miskilancine babu matsala tunda kaima halinkane.
Harara Bobo ya galla masa malam aii wannan ta fini.
Bobo acigaba da bandamuba kafin ayi auren, amma yanzu ganinta agidan saina shiga wani hali, Dan gsky ina buk’atar mace.
Ammar yagyara zama, to aii ni banga abin damuwa ananba, ba matarka bace?, kawai kanemeta mana.
Ammar baka fahimceni bane, haryanzufa yarinyar k’aramar yarinyace, bata wuce 17 ba, banafa ta kammala secondary, kosu khursiyya sun girmeta da shekara d’aya.
Murmushi Ammar yayi, karka damu abokina aii yaranma sunfi bada Nutsuwa ka gwada kagani kuma.
Amma Dan ALLAH karagema kanka damuwa.
To aiini bakasan wani abuba, tayayama zan tunkareta na nuna mata ga abinda nakeso?, kasanfa banason raini wlhy.
Dariya Ammar yayi ya ce, “Abdulmaleek Aliyu Abdulmaleek hamshak’i, wlhy AAA kana bani dariya, lokuta da dama nakan rasa kai wane irin mutumne?, wlhy da aikin Soja ka dace ba lauyaba, kaifa wani irin murd’ad’d’en mutumne, towai sanda kake gwadama Margayiya Ni’ima soyayaya kirana kayi na koya makane?.
Ajiyar zuciya Bobo ya sauke, bazaka ganebane kawai kadai.
To ganar dani cewar Ammar yana kallon Bobo.
Komawa yayi yalafe jikin kujerar yanad’a lilata ahankali, Ammar ya ce, ” my guy kafito kawai anamijinka kaji, kakula da matarka na tabbata Rahma Alherice arayuwarka, kaga kuwa yanda ka canja kak’ara fari, so ka kwantar da hankalinka kayi k’ibama, Rahma k’yak’yk’yawar yarinyace nitsatstsiya ga ilimin addini, wlhy randa na kalli vedio d’in bikinku jinayi inama ina wajen, bak’aramin birgeni tayiba awajen walimarnan.
d’an iska awajen biki kanata tattalin yarinya amma yanzu kazo kana mata muzurai.
Murmushi bobo yayi ya ce, ”kankadai akeji.
Kaima za’aji nakane, amma saikaje hanun Rahma, mik’ewa yayi yana dariya kaga bara nawuce sumayya nacan na jirana harkaja na wuce lokaci.
Bobo daketa murmushi tun d’azun ya harareshi iskanci zakamin kenan?..
A’a babu wani iskanci gsky dai.
Bobo ma ya mik’ewa yayi, nima tafiyar zanyi zanje na d’auki Nawal a school, yau direbanta babu lafiya.
Ayya ALLAH yabashi lfy.
Amin.
Tare suka fito, kowa yashiga motarsa, Ammar da tawagan ‘yan sandansa suka tafi, shima Bobo yanufi school d’in su Nawal ya d’auketa sai gida.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Sun shigo gidan falo babu kowa, sai k’amshi da k’arar AC ke tashi, saikuma TV dake kunne amma babu k’ara sosai.
Nawal ta ce, “papa momy na d’aki zomuje, tarik’e masa hannu.
Rahma tana tsaye jikin wardrobe tana d’aukar kaya suka shigo, batayi zaton taredashi sukeba, Cikin farin ciki tad’auki Nawal tana juyi da ita suna dariya, babyn papa da momy ya School.
Momyn lfy.
Masha ALLAH my lovely daughter, muje namiki wanka to kiji dad’i.
“K indai kina tareda Nawal baki ganin kowa sai ita?.
Da sauri ta kalli gurin da maganar take fita, Dan batayi tunanin suna tareba.
Kayi hak’uri basan tare kukeba aii sannu dazuwa, sai matse jikinta takeyi Dan daga ita sai tawul.
Baice komaiba yajuya yafita, amma ya rikice daganin surar Rahma, dukda k’aramar yarinyace amma tanada sura mai k’yawun gani, yanaso yak’ara ganin ainahin Rahma d’in.
Da wannan tunanin yak’arasa d’akinsa, kaya yacire yashiga wanka.
★★★
Bayan wasu ‘yan lokuta kowa ya kammala abinda yakeyi, suka had’u afalo sukaci abinci, itadai Rahma kanta ak’asa.
Yakula tunranda yay mata abinnan bata sakewa dashi, kuma bataso su had’a ido, tak’ara birgeshi da samun matsayi a zuciyarsa Dan yana k’aunar mace mai kunya
_(kunya tana d’aya daga cikin tarbiyya ga mace, amma ‘yammatanmu na yanzu sun 6arar, aganinsu rashin kunya itace wayewa, gsky anama wayewa bahaguwar fahimta, yakamata mugyara, kunya tana d’aya daga cikin alamomin imanima wlhy, ALLAH yasa mugane.)_
Duk suna falo zaune, Rahma da Nawal suna game da aka had’a da TV, shikam boss yana karanta jarida.
Safna tayi hon maigadi yalek’a danyaga wanene, ganin bak’uwar motace yasa yaytsaye batarda ya bud’eba, cikin haushi Safna talek’o tana masa magana cikeda masifa, aii babu shiri yabud’e mata gate d’in tashiga, guri tasamu tai farking sannan tafito, sai harar mai gadin takeyi, sanye take cikin jan less Riga da siiket sun kamata sosai amma sunyi mata k’yau, ta d’ora siririn farin gyalenta a kafad’a, takalmi da handbag d’inta duk farare, tad’auki sak’on Rahma tanufi k’ofar datake zaton itace zata sadaka da gidan.
Sallama tayi tareda kwankwasa kofar.
Rahma tamik’e da sauri lah kamar muryar aunty Safna nakeji.
Da sauri Bobo yad’ago kai yana kallonta danjin ta ambaci Safna.
K’ofa Rahma tanufa, shikuma ya ta6e baki yaudai zaiga yarinyar datace bata sonsa..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 25
Safna ta mik’e zumbir danjin and’aga wayar, saisaita kanta tayi ta ce, “Assalamu alaika.
Saida yaja aji sannan ya ce, ” wa’alaikissalam.
Safana ta ce, “ina yini?.
Lfy, ya amsa atak’aice.
Rasa mizata kuma cewa tayi, Dan duk muryarsa ta rikitata, gashi yana amsa mata magana ad’age.
Abinne yafara bashi haushi, amma kasancewar yasan number data kira ta harkar aikinsace saiya dake, yayi tunanin akan aikine.
Yakatse shirun dafad’in mikike buk’atane?.
Uhm….u…u Dan ALLAH kozan iya samunka office gobe idan ALLAH ya kaimu?.
Lumshe idanunsa yayi yabud’e, ya ce, ” akanmi kikeson ganina?.
Gabad’aya ta daburce, tarasa mizata fad’amasa, jin takasa magana sai kawai ya yake wayar yay tsaki, gaba d’aya kashe wayar yayi ya wurgata gefensa yana mita.
Duk abinda ke faruwa Rahma tanajinsa, saidai batasan mi ake fad’a ad’ayan 6angarenba.
Aikinsa yacigaba dayi, itama yacigaba da koyama Nawal aikinta na homework.
Acan kuwa safna kaita dafe, takira Baseera danta bata shawara
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*
Safna wai mikikeyine har yanzun baki fitoba?, wannan wane irin yinine har k’arfe 2 ba’a tafiba?.
Ganina fitowa ummi, safna tafad’a tana figar handbag d’inta.
Afalo ta Tatar da ummi tsaye da bak’ar leda ahannu.
Ummi tamik’a mata ledar ga wannan ki kaimata, Safna Dan ALLAH ki kama kanki, kingadai gidan mijin k’anwarkine.
Karki damu ummi, insha ALLAHU babu abinda zai faru wlhy, ainamiki alk’awari zan canja nakoma yanda kikeso.
To ngd ALLAH yayi miki albarka.
Amin ummi na safna tafad’a tana fita.
Hartakai k’ofa saikuma ta waigo, ummi wai miye wannan d’in?, tafad’a tana kallon ledar da ummin tabata.
Karki damu zankirata namata bayani.
Ummi ni baza’a fad’aminba.
A’a lokacinki bai zoba, ai yanzu autana takwace girman, tazama Yaya kinzama k’anwa.
Baki safna tatura tafice, aranta ta ce, “ummi nasan kayan matane aii.”
Tana Shiga motarta ta kalli wayarta, hankalinta dukya tashi ganin bai bata amsaba, tunranda takirashi yakashe wayar saita k’yaleshi bata sake kiraba.
Yaudai abin ya dameta shine tatura masa message akan yabata address d’in office d’insa tazo, amma shine har yanzu babu kira babu sak’o.
Ranta duk adagule yake, takirashi sau wajen uku yak’i ya d’aga, hak’ura tayi tatada motar tanufi gidan Rahma.
Dama Dan tanason zuwa wajen bobone ta ce, “ma ummi tanaso yau taje wajen Rahma.
Ummi tayi murna, azatonta Safna tafara hankaline.
“Araina na ce, “koya zata kaya?.”
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Yana zaune a office yaduk’ufa da duba wasu takardu, kallo d’aya zaka masa kagane yana matuk’ar busy, takardun dayake dubawa kuma sunada muhimmanci.
Yana kallon wayarsa tana wringing yay burus da ita, Dan baya k’aunar abinda zai dakatar dashi daga aikin gabansa.
Kwankwasa k’ofar office d’in akayi, sanin sakatariyarsa ce kawai keda wannan damar yasa ya amsa da yes.
Turo k’ofar tayi tashigo, haryanzu bai d’agoba ta had’iye wani yawu tareda tsura masa ido tamkar zata lashesa, sir kayi bak’o.
Waye?, bobo yatanbaya kansa har yanzu yana k’asa.
Cikeda salo ta ce, ” bak’on jiyane Alh Sunusi Dala.
Sai yanzu yad’ago, aransa ya ce, “mi mutumin nan yakeso danine, afili kuma ya ce, ” kigaya masa bana buk’atar ganinsa, kuma……..saikuma yayi shiru ya ce, ”jeki wannan ba aikinki bane.
fita tayi cike da salo.
Batamasan shi tuni yamaida Kansa ga aikinsaba.
Zuwa tayi ta Isar da sak’on oganta ga Alh sunusi, maganar tak’ara Sosa masa rai, amma tunda bobo yak’i bashi had’inkai to lokaci yayi dazai d’auki matakin k’arshe akansa.
Fuuuu yabar wajen, masu gadinsa suka take masa baya.
STORY CONTINUES BELOW

“na ce, “humm kowane mataki kuma Alh sunusi ke shirin d’auka akan bobo?.��”
+++
Da sauri yad’ago danjin anta6ashi, danufin yin bala’i yad’ago azatonsa Alh sunusi ne yanunama sakatariyarsa fin k’arfi yashigo, ganin Ammar ne saiya sauke ajiyar zuciya tareda yin murmushi.
Ammar ya ce, ” mutumina irin wannan fusata haka?, tamkar zaka bigeni.
Ajiyar zuciya Bobo ya sauke kayi hak’uri wlhy nazata wannan shashashanne Alh Sunusi.
Murmushi Ammar yayi ya ce, “munzo shigowa naga fitarsa Ashe na shaida motocin nasa kuwa.
Baki bobo yata6e batareda yayi maganaba.
Saican yace halan yauma kazo kacikamin bakin office da yaranka?.
Hhhhhhh kaima Kasan dolene Dan babu yanda za’ayi subarni nafito ni kad’ai.
Bobo Yakuma ta6e baki, Sakai awahala kenan, haka kawai ace duk Inda mutum zayi ana binsa tamkar wata jela?.
Girman kenan my guy Ammar yafad’a yana dariya.
Ammar ya ce, “mutumina kafa rame wlhy mike damunka?.
Bobo yafitar da huci mai zafi, babu komai Ammar.
To shikenan tunda babu komai yafad’a yana mik’ewa.
Da sauri Bobo yaruk’oshi Dan yasan haushi yaji, yi hak’uri abokina zauna muyi magana.
Ammar yadawo yazauna, wlhy Abdulmaleek kana bani mamaki yanda kake iya 6oyrmin wasu al’amura naka awasu lokutan.
Bobo ya ce, ” kayi hak’uri Ammar bawai ina 6oye maka wani Abu baneba, saidai ina ganin wannan sirrin gidanane, dukda nasan babu abunda zan iya 6oye maka arayuwata, kai kad’aine abokina Dana yarda dashi, nasan kaima hakane.
Hakane Bobo amma Dan ALLAH miyasa kake 6oyemin abinda ke damunka?, ina kula dakai tunda nadawo kana cikin damuwar datafi tada akan Rasuwar marigayiya Ni’ima.
Sabodafa damuwar dakake ciki su Appa suka yanke shawarar yimaka Aure, to amma maimakon asamu sauk’i sai kuma damuwarka ta k’aru.
Minene damuwarka Abdulmaleek?, kasanar dani mu nemo mafita.
Bobo yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, yadafe tebir d’in gabansa da hannu bibbiyu.
Wato Ammar da ina cikin kewar matatane Dana rasa, dakuma tausayin Nawal na rashin uwa, wannan yasa nak’iyin aure dukda dama Kasan matan bawai suna agabana bane, su Appa sun takura nayi aure harda kai aciki, amma na ce, “muku har yanzu ban shiryaba, an auramin Rahmane saboda bijirewar yayarta akan aurena.
Tundaga randa aka kawo yarinyar gidana ban k’ara yarda ta ganniba saida na d’akko Nawal..
” amma kasan wani abin mamaki?.”
Ammar ya girgiza kai.
Koda muka shigo gidan saitamana tarba ta mutunci, ko kad’an bata nuna fushinta akan rashin zuwana garetaba.
Wannan itace jarabawa ta farko data cinye, saikuma yanda take kula da Nawal, wlhy idan baka saniba bazakace ba ita ta haifetaba, abu na uku tsafta, iya girki, saidai akwai shegen muskilanci atareda yarinyar wlhy.
Ammar ya tuntsure da dariya, to aii indai miskilancine babu matsala tunda kaima halinkane.
Harara Bobo ya galla masa malam aii wannan ta fini.
Bobo acigaba da bandamuba kafin ayi auren, amma yanzu ganinta agidan saina shiga wani hali, Dan gsky ina buk’atar mace.
Ammar yagyara zama, to aii ni banga abin damuwa ananba, ba matarka bace?, kawai kanemeta mana.
Ammar baka fahimceni bane, haryanzufa yarinyar k’aramar yarinyace, bata wuce 17 ba, banafa ta kammala secondary, kosu khursiyya sun girmeta da shekara d’aya.
Murmushi Ammar yayi, karka damu abokina aii yaranma sunfi bada Nutsuwa ka gwada kagani kuma.
Amma Dan ALLAH karagema kanka damuwa.
To aiini bakasan wani abuba, tayayama zan tunkareta na nuna mata ga abinda nakeso?, kasanfa banason raini wlhy.
Dariya Ammar yayi ya ce, “Abdulmaleek Aliyu Abdulmaleek hamshak’i, wlhy AAA kana bani dariya, lokuta da dama nakan rasa kai wane irin mutumne?, wlhy da aikin Soja ka dace ba lauyaba, kaifa wani irin murd’ad’d’en mutumne, towai sanda kake gwadama Margayiya Ni’ima soyayaya kirana kayi na koya makane?.
Ajiyar zuciya Bobo ya sauke, bazaka ganebane kawai kadai.
To ganar dani cewar Ammar yana kallon Bobo.
Komawa yayi yalafe jikin kujerar yanad’a lilata ahankali, Ammar ya ce, ” my guy kafito kawai anamijinka kaji, kakula da matarka na tabbata Rahma Alherice arayuwarka, kaga kuwa yanda ka canja kak’ara fari, so ka kwantar da hankalinka kayi k’ibama, Rahma k’yak’yk’yawar yarinyace nitsatstsiya ga ilimin addini, wlhy randa na kalli vedio d’in bikinku jinayi inama ina wajen, bak’aramin birgeni tayiba awajen walimarnan.
d’an iska awajen biki kanata tattalin yarinya amma yanzu kazo kana mata muzurai.
Murmushi bobo yayi ya ce, ”kankadai akeji.
Kaima za’aji nakane, amma saikaje hanun Rahma, mik’ewa yayi yana dariya kaga bara nawuce sumayya nacan na jirana harkaja na wuce lokaci.
Bobo daketa murmushi tun d’azun ya harareshi iskanci zakamin kenan?..
A’a babu wani iskanci gsky dai.
Bobo ma ya mik’ewa yayi, nima tafiyar zanyi zanje na d’auki Nawal a school, yau direbanta babu lafiya.
Ayya ALLAH yabashi lfy.
Amin.
Tare suka fito, kowa yashiga motarsa, Ammar da tawagan ‘yan sandansa suka tafi, shima Bobo yanufi school d’in su Nawal ya d’auketa sai gida.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Sun shigo gidan falo babu kowa, sai k’amshi da k’arar AC ke tashi, saikuma TV dake kunne amma babu k’ara sosai.
Nawal ta ce, “papa momy na d’aki zomuje, tarik’e masa hannu.
Rahma tana tsaye jikin wardrobe tana d’aukar kaya suka shigo, batayi zaton taredashi sukeba, Cikin farin ciki tad’auki Nawal tana juyi da ita suna dariya, babyn papa da momy ya School.
Momyn lfy.
Masha ALLAH my lovely daughter, muje namiki wanka to kiji dad’i.
“K indai kina tareda Nawal baki ganin kowa sai ita?.
Da sauri ta kalli gurin da maganar take fita, Dan batayi tunanin suna tareba.
Kayi hak’uri basan tare kukeba aii sannu dazuwa, sai matse jikinta takeyi Dan daga ita sai tawul.
Baice komaiba yajuya yafita, amma ya rikice daganin surar Rahma, dukda k’aramar yarinyace amma tanada sura mai k’yawun gani, yanaso yak’ara ganin ainahin Rahma d’in.
Da wannan tunanin yak’arasa d’akinsa, kaya yacire yashiga wanka.
★★★
Bayan wasu ‘yan lokuta kowa ya kammala abinda yakeyi, suka had’u afalo sukaci abinci, itadai Rahma kanta ak’asa.
Yakula tunranda yay mata abinnan bata sakewa dashi, kuma bataso su had’a ido, tak’ara birgeshi da samun matsayi a zuciyarsa Dan yana k’aunar mace mai kunya
_(kunya tana d’aya daga cikin tarbiyya ga mace, amma ‘yammatanmu na yanzu sun 6arar, aganinsu rashin kunya itace wayewa, gsky anama wayewa bahaguwar fahimta, yakamata mugyara, kunya tana d’aya daga cikin alamomin imanima wlhy, ALLAH yasa mugane.)_
Duk suna falo zaune, Rahma da Nawal suna game da aka had’a da TV, shikam boss yana karanta jarida.
Safna tayi hon maigadi yalek’a danyaga wanene, ganin bak’uwar motace yasa yaytsaye batarda ya bud’eba, cikin haushi Safna talek’o tana masa magana cikeda masifa, aii babu shiri yabud’e mata gate d’in tashiga, guri tasamu tai farking sannan tafito, sai harar mai gadin takeyi, sanye take cikin jan less Riga da siiket sun kamata sosai amma sunyi mata k’yau, ta d’ora siririn farin gyalenta a kafad’a, takalmi da handbag d’inta duk farare, tad’auki sak’on Rahma tanufi k’ofar datake zaton itace zata sadaka da gidan.
Sallama tayi tareda kwankwasa kofar.
Rahma tamik’e da sauri lah kamar muryar aunty Safna nakeji.
Da sauri Bobo yad’ago kai yana kallonta danjin ta ambaci Safna.
K’ofa Rahma tanufa, shikuma ya ta6e baki yaudai zaiga yarinyar datace bata sonsa……💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 26
Rahma tarungume Safna cikeda farinciki, itama rungumeta tayi Dan tayi kewar ‘Yar k’anwarta abokiyar fad’anta, I miss you my lovely aunty.
Miss u too my lili na.
Safna tad’agota daga jikinta tana fad’in ‘Yar lukutar ummi kinfa k’ara lukucewa, mi angon naki yake baki haka?.
Rahma tarufe fuskarta saboda jin kunya, kai aunty Dan ALLAH ki bari.
To na bari Safna tafad’a tana kama hannunta sukai cikin falon.
Rahma ta kalli mazaunin Bobo wayam, Nawal ta kalla data maida hankalin akan game, baby ina papa?.
Nawal tad’ago tana dariya, yashiga d’akinsa momy….. Tsayawa tayi tana kallon Safna, saikuma ta kalli Rahma, momy wacece wannan?.
Aunty ce babyna.
Nawal ta taso ta rungume Safna, oyoyo aunty na.
Itama safna rungumeta tayi tana fad’in oyoyo babyn mom.
Bayan sun zauna Safna sai bin Nawal da kallo takeyi, gani take kamar tasan yarinyar.
Rahma tadire tiren kayan motsa baki agaban safna, tana fad’in wlhy aunty banyi zaton ganinkibafa.
‘Yar dariya safna tayi ta ce, ”saikuma gani kin ganni.
Zama tayi sukafara hira, kamar basu bane sukeshan fad’a ada.
Sun shagala sosai akan firar idon Safna ya sauka akan hoton Bobo, wani k’ululu cikinta yabada, batagama dawowa daidaiba Bobo yafito daga d’akinsa.
Ah bak’uwa mukayi agidan??.
Afirgice safna tad’ago tana kallonsa, fad’uwar gaba, bugun zuciya, murd’awar ciki, duk suka k’ara samunta alokaci guda, yanda take raba ido akan Bobo sai kawai ya d’aure fuska.
Itama Rahma kallonta takeyi ita atunaninta Safna taji kunyane akan abinda ta aikata abaya.
Safna taduk’e k’anta bisa cinyarta danjin falon yana juya mata, jikinta sai rawa yakeyi, lallai ta tabbata kuka rahamane tunda gashi ita yau takasayinsa.
Bobo yana zaune saman kujera yad’ora k’afa d’aya kan d’aya, dagashi har Rahma idanunsu nakan Safna, Nawal ma tana mak’ale abayan Rahma tana lek’en Safna, bobo yakalli Rahma, dama tanada wani ciwone?.
Kai Rahma ta girgiza masa ta CE, ”amma dai ban saniba ko bayan nabar gidan.
Lumshe idanunsa yayi ya ce, “bata ruwa tasha, Rahma ta tsiyayama Safna ruwa a Kofi tabata, jikin Safna na Rawa takar6a ta shanye duka tamik’ama Rahma kofin, k’ara mata bobo yasake fad’a.
K’ara mata takumayi, aii ko ta shanyeshi tas.
Rahma takalli Safna kamar zatayi kuka, aunty ki kwanta kihuta, kiringa fad’in _innalillahi wa’inna ilaihirraji’un_ zaki samu nutsuwa insha ALLAHU.
BABU musu Safna tabi shawarar Rahma ta kwanta, dukda ayanzu jitake babu Wanda tatsana aduniya sama da Rahma d’in, jitake tamkar tatashi ta shak’eta ta mutu, talumshe idanu tana ambatar innalillahi….. Danjin zuciyarta tana shirin fashewa.+
Bobo dai tuni yad’auke kai daga kallon Safna, ya maida hankalinsa ga TV.
Bayan kamar minti15 Safna tad’anji Nutsuwa tazo mata, tabud’e ido tareda tashi.
Rahma tai saurin fad’in aunty Yaya jikin?.
Murmushi Safna tayi Wanda yafi kuka ciwo, da sauk’i kuyi hak’uri na rud’aku, juwace nakeji dama tun ina hanya.
Sannu Rahma tashiga jero mata, Dan ita tayarda da zancen na Safna 100%.
Bobo kam azuciyarsa ya ce, ” juwar kuma bata tashiba saida kika ganni?, shifa Sam bai yarda da maganartaba, Dan haka yacigaba da kallonsa batareda yak’ara kallon ko inda sukeba.
Safna kam tafad’i hakane saboda tunowa da maganar malaminta, dayace kota had’uda bobo karta nuna masa komai harsaitaje wajensa yabata wani sirri, da wannan tunanin tad’anji sanyi aranta, shiyyasa ta tashi ta zabga wannan k’aryar.
Takai kallonta ga bobo daya maida hankali kan latsa wayarsa, muryarta na rawa ta ce, “ina yini.
Lfy, kawai ya ce, ” yamaida Kansa ga waya.
Falon yay shiru nawasu ‘yan mintuna, safna dai satar kallon Bobo takeyi, sai yanzu yak’ara tabbatarwa da k’yak’yk’yawane ajin farko, Ashe ranar kallon tsoro sukayi masa, lallai ALLAH yayi halitta awajennan masha ALLAH, sai sambatun k’yawun bobo takeyi ita kad’ai zuciyarta.
Rahma kam tayi shiru tana tunanin halin da safna tashiga yanzun nan, kome ke damun ‘Yar uwar tata?.
Bobo yamik’e Dan ganin kallon k’urillar da safna take masa, yakalli Rahma bara nad’an kwanta kafin sallar la’asar, kitadani idan lokaci yayi.
To. Rahman tafad’a kanta ak’asa.
Shikuma yanufi d’akinsa, harya shige safna tanabinsa da kallo.
STORY CONTINUES BELOW

Nawal ma tamik’e momy zanje wajen papa.
A’a Nawal kibar papa ya huta kinga ya ce, “barci zaiyi, Nawal ta kwa6e fuska tana shirin yin kuka, momy nimafa barcin zanyi.
Tokije d’akinmu ki kwanta, kamar gsk tanufi d’akin Rahma, dataga basa kallonta saita gudu d’akira, papan ta.
Safna ta ce, ” wannan yarinyarfa ina kuma samota?.
d’an murmushi Rahma tayi, aunty yarinyarsa ce wadda matarsa tarasu tabari.
Baki safna ta ta6e shine kekuma aka jajibo aka kawomiki?, kedai sakaraice wlhy, kina ‘Yar yarinyarki har anfara kiranki da suna momy mtsoooow, nibansan randa kanji zai wayeba wlhy, danice agidannan wlhy saidai yasan Inda zaikai ‘yarsa.
Itadai Rahma batace komaiba, saima wasa da zoben hannunta datakeyi, amma har zuciyarta bataji dad’in maganar ‘Yar uwartaba, aganinta aii d’a na kowane, kuma shida gidansa tahanashi ajiye Wanda yakeso?, itafa har zuciyarta tana k’aunar Nawal, kuma yanda zata rik’e ‘ya’yan cikinta haka zata rik’e Nawal.
Yana zaune abakin gado yana danna laptop Nawal tashigo.
Lah papa bakayi barciba?.
Bobo yad’ago yana kallon d’iyar tasa, banyi barciba babyna ya akayi?.
Na cema momy zanzo wajenka, shine ta ce, ” a’a wai nabarka kagaji zakayi barci naje d’akinmmu na kwanta.
To miyasa bakije kin kwantaba?.
Ai bata ganniba nikuma na gudo nan, ammafa karka gaya mata.
Murmushi yayi Dan ganin yanda Nawal tazaro idanu saikace wata babba, to shikenan bazan fad’aba yanzu ya za’ayi?.
Ta ce, “papa barci zanyi.
To zoki kwanta, kan gadon tahawo ta kwanta, kwantar da kanta tayi kan k’afarsa daya tankwanshe, tana kallon rubutun dayakeyi a laptop suna labari, dahaka barci ya d’auketa, yagyara mata kwanciya dankar wuyanta yay sanyi.
Afalo kam safna da Rahma suna hira, dukda safna dauriya kawai takeyi, Dan zuciyarta na cikeda tsanar Rahma, dakuma haushin tashin bobo Afalon, Dan bata gaji da ganinsaba.
Tamik’a mata sak’on ummi gashi inji ummi.
Rahma takar6a ta na dubawa, miye kuma ummina tabani?, safna ta ta6e Baki ta ce, ” zata kiraki tamiki bayani, kinga bari nawuce, safna tafad’a tana mik’ewa.
Kai auntuna tun yanzu?, Rahma tai maganar tamkar zatayi kuka.
Kenifa banason iyayi, dama kika samu Nazo shine zakimin Ta6ara.
Sanin halinta yasa Rahma tai saurin fad’in yi hak’uri aunty Safna wlhy nayi kewarkune sosai. Dan ALLAH yaushe zaki dawo?.
Kallonta kawai safna takeyi, zuciyarta na raya mata yarinya karkiyi farincikin sake zuwana, Dan waywayowata gidannan ba alkairi bane ba agarekj, bazan ta6a barmiki bobo ba, abayama kuskurene da rashin sani, amma ayanzu kam sai Inda k’arfina ya k’are, bobo nawane nikad’ai…..
…
Ta6ata Rahma tayi aunty mikike tunani haka?.
Ajiyar zuciya Safna ta sauke, ta k’ak’aro murmushi, karki damu zandawo kwannann.
Cikeda farinciki Rahma tarungume safna.
Kayan kwalliya ta had’a mata hadda wasu k’ananun kaya masu k’yau da aka saka mata alefe, safna takar6a ko godiya babu ta tafi.
Har bakin mota tarakata, saida taga fitarta sannan tadawo ciki.
Batanemi su Bobo ba tahau gyaran gidan, da shirin girkin dare.
Safna kam tana fita saitaji hawaye sunabin kumatunta, abinda takesonyi tun d’azu amma sukak’i zuwa, gangarawa tayi gefen titi tasamu guri tai farking, kifa kanta tayi a sitiyari tanata rabzar kuka tamkar ranta zai fita, sai surutai takeyi kamar Sabuwar kamu.
Wlhy Rahma bazan barmiki Shiba, wlhy saidai idan ki mutu na mallakesa, kota halin k’ak’a saina rabaki dashi, idan ban samesaba mutuwa zanyi, Rahma miyasa zakimin haka ki auri abinda nafiso fiyeda komai arayuwata?, wlhy saikin barmin bobona, saikin barmin…..tasaki wani wahalallen kuka.
(Ni bilynku na ce, “kaga wani salo, Safna kinyi sake Rahma ta dafe.)
Cikin matsanancin kuka Safna ta kira basira ta zayyane mata komai, ita kanta tarazana sosai danjin labarin, safna ta ce, “baseera miye mafita?, kibani shawara, wlhy kwakwalwata na gab da tarwatsewa nashiga uku baseera namutu.
Kinga safna ki kwantar da hankalinki, gobe idan ALLAH yakaimu zamu koma wajen malam.
Baseera muje yanzu please.
A’a kiyi hak’urin goben, wlhy yau Abbana yana gida, kuma yasan banida lectures d’in yamma, baza’a barni na fitoba, kiyi hak’irin giben saimuje da sassafe.
Shikenan safna tafad’a jiki a sanyaye.
Motar taja tanufi gidan, Dan kukan datayi yad’an rage mata wani abun.
……
Rahma tagama komai tak’ara saka turaren wuta, jin kwala kiran sallar la’asar yasata nufar d’akin bobo danta tadashi, kwankwasa k’ofar tayi dukda tasan yana barci, bata jira amsaba tashiga da sallama.
Hakan tayi dai dai dafitowar bobo daga wanka, yana d’aure da fad’in tawul ita k’ugu zuwa guywa, hannunsa rik’e da k’arami ya ratayo a wuyansa.
Da sauri Rahma tajuya zata fita tana fad’in ashema ka tashi.
Eh natashi, ina zaki? Kizo kid’auki yarinyarki gatanan tamin barci ad’aki.
Rahma tajuyo kanta ak’asa, Ashe nan tazo?, nazata tana d’akina?.
A’a tana nan dama ta ce, “karna gaya miki gudowa tayi.
Murmushi kawai Rahma tayi tad’auki Nawal tafice abinta.
d’an murmushi yayi danganin yanda take Sinne kai da had’e hanya, yasan danta gansa babu kayane.
Tana falo yafito sanye cikin blue d’in wando da jar Riga, yayi k’yau sosai, Dan dama bobo akwai gayu gakuma tsafta, uwa uba k’yawun haiba.
Yad’an kalli Rahma, bara naje masallaci, daga nan zan wuce gidansu Ammi.
To ALLAH yatsare. Saika dawo.
Amin yafad’a akan la66ansa, yafita yanamaijin dad’in addu’arta gareshi.
Rahma tayi shiru tana mamakin yanda bobo kan sakata cikin al’amuransa ayanzu, komiye dalilin hakan?.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Safna tadanna uban hon, babu shiri baba mai gadi yabud’e mata gate, aguje tashiga gidan, tai farking, handbag d’inta kawai tad’auka tayi cikin gida, anan tabar kayan da Rahma ta bata, ALLAH yasota ma ummi na d’aki babu kowa afalon.
Ta fad’a saman gadonta tana kuka, wlhy saina raba wannan auren, Dan bobo nawane nikad’ai, bazan ta6a zuba ido ina kallonsa amatsayin mijin k’anwataba, saina mallakesa kota halin k’ak’a, konawa zan kashe kuma koyaya iyayenmu zasu d’auki lamarin itadai saita mallaki bobo.
Haka taita kuka har aka kira magriba, dama batayi sallar la’asarba, kuma da alama magribar ma babu niyya.
Ummi takalli agogo waini ina safna tamak’alene har yanzu shiru?.
Talatu mai aiki ta ce, “Hajiya aita dawo tun d’azu.
Kai talatu da gsk?.
Wlhy kuwa Hajiya.
Hankalin ummi ya kwanta takoma d’aki dama ko lazimi bata kammalaba tafito.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Bobo kam koda yay sallar la’asar saiya nufi gidansu, bayan sun gaisa da maigadi yashige ciki.
Yakashe motar yafito, cikin kasaitarsa yanufi cikin gidan, afalo yatarar da khursiyya da khairiyya suna kokawa akan gyale.
Tsaki yayi yana daka musu tsawa, kai dallah miye haka?.
Da sauri suka nutsu.
Ya ce, ” Ku wad’anne irin shashashune?, kun kirma amma kunacin k’asa.
Yaya gyalenefa na ajiye zansaka gobe idan zamuje gidanka, shine ta d’auka wai zata fitadashi yanzu……
Karya take Yaya…
Katsesu yayi suduka, kumun shiru dallah, hannu yamik’a yakar6i gyalen, batareda yak’ara tankasuba ya haye saman Appa.
Saida yaje k’arshen benen sannan yajuyo ya ce, “idan kun gadama kucigaba da fad’an harna sakko, yay shige warsa.
Khursiyya ta tura baki baba, hankalinki ya kwanta ya kwace duka, tobake kika jaba cewar khairiyya.
Kardai Ku fasa, kuyi tayi harya dawo kune zakuci dukan banza tunda kunsan halinsa sarai, Ammi ce mai maganar tana fitowa daga kicin, Ashe duk abinda sukeyi tana jinsu.
d’akinsu suka koma, kowa tana zum6ura baki gaba, Ammi ta girgiza kai tana nufar saman Appa itama…………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 27
Appa yatashi zaune yana murmushi, oyoyo babana nida Ammi.
Shima bobo dariyar yakeyi, yaje dafda Appa yazauna tamkar zai shige jikinsa.
Appa yamik’a masa hannu su gaisa, amma saiya nok’e ya ce, “ina yini Appa.
Dariya Appa yasakeyi, mukarram bakaso musamu ladan musabahane?, mirmushi yayi batareda yace komaiba, Appa yakamo hannun bobo yahad’e danasa yana fad’in ya iyalin?.
Suna nan lfy Appanmu, sunama gaisheku.
Muna amsawa. yau baka je aiki bane?.
Naje Appa, amma nataso dawurine saboda d’akko Nawal a school.
Ok, to ina direbanta?.
Wai bayajin dad’in jikinsa, shine nacemasa yahuta kawai.
ALLAH yabashi lafiya to.
Amin.
Assalamu alaikum.
Wa’alaikisslam. Appa da bobo suka amsawa ammi sallamarta, bobo yamik’e da sauri yakar6i kayan hannun ammi, kai Amminmu da kanki?, miye amfanin wad’ancan yaran?.
Dariya tayi tazauna, to mukarram inbanyiba wazaiyi?, hidimar mijinace fa.
Murmushi bobo yayi, shiyyasa kullum yakeson Amminsa haryau baiga macen datakai amminsu iya tattalin mijiba, gashidai sun tsufa amma har yanzu suna tattalin junansu tamkar yara…….
Ammi tak’atsema bobo tunani da fad’in mukarram ga abinci.
Firgigit yadawo da kallonsa Kansu, Ammi mikikace?.
Tunanin mi kakeyine?.
Bai 6oye musuba yafad’a musu abinda yake tunani, Dan akwai fahimtar juna da shak’uwa tsakaninsu da iyayensu.
Daga Ammi har Appa dariya sukayi danjin firicin bobo, ammi ta ce, “toga abinci azuba?.
A’a ammi nima matana tacikamin ciki da girkinta mai dad’i.
hhhhhh d’an bantan uba, ashedai gaskiyar Hamza dayace kanason matarka, babanafa akwai iya taku.
Dariya sosai bobo da Ammi sukeyi danjin zancen Appa, appa ya ce, ” naji dad’i sosai wlhy, ALLAH yak’ara Baku zaman lfy da zuri’a tagari.
Kansa ak’asa ya ce, “amin.”
Hira sukacigaba dayi, Appa yanacin abinci, bayan ya kammala ya ce, “mukarram!.”
Yanda Appa yakira sunan nasa yasan tabbas maganar muhimmiyace, shima cikeda girmamawa da nutsuwa ya ce, ” na’am Appa.
Appa yagyara zamansa, yanamai tsurama bobo ido, mukarram mike tsakaninka da Alh sunusi Dala?.
Ajiyar zuciya bobo yasauke, cikin nutsuwa yayma Appa bayanin tun farkon tsintar muheebat dakuma abinda yake faruwa a yanzun.
Appa ya girgiza kai alamar gamsuwa, ya ce, “ina alfahari daku sosai ‘ya’yana, ngd ma ALLAH dayayiku masu hankali dasanin darajar d’an Adam, lallai kaburgeni sosai babana, kuma Nagoya maka baya d’ari bisa d’ari ka kwatoma yarinyar hak’k’inta, “I’m proud of you my dear son”.
ALLAH yatsare minku aduk inda kuka tsinci kanku.
Amin Appa mungodema ALLAH dasamunku amatsayin iyaye nagari, bamuda abin biyanku saidai muyita binku da addu’a har k’arshen numfashinmu.
Ammi dai sai murmushin jin dad’i takeyi.
Appa yacigaba da fad’in dama abinda yasa kaji namaka maganar yaune Alhaji Sadiq muna hira yake bani labarin furucin Alh sunusi akanka, todaya fad’i sunanka shine yagano d’aya daga cikin ‘ya’yanane, shine yasameni yake gayamin nasaka ido kar a cutarmin dakai, Dan Alh sunusi bashida imani ko kad’an.
_(nasan har yanzu baima San kai d’ana bane shiyyasa yake rangwanta maka, Dan bama shiri sosai nidashi, siyasa tasakashi d’aukar gaba damu nida Abban Ammar)_
amma kadage da addu’a muma zamu tayaka, ALLAH yana tareda mai gsky kaji my son.
Murmushi bobo yayi, ya ce, ” karka damu Appa wlhy daidai da second 1 banta6ajin tsoro ko Shankar Alh sunusi ba, ni duk sanda yay wani abunma k’aramin k’aimi yakeyi.
Daga Ammi har Appa dariyar sukayi, sukace to ALLAH yak’ara tsareka auta, fira sosai yasha da iyayensa, saida suka dawo daga sallar magriba sannan yay musu sallama zai tafi.
Appa ya ce, “gobe idan ALLAH yakaimu yanason ganinsu su duka, yanaso su tattauna akan maganar auren su khursiyya.
To Appa ALLAH yakaimu lfy.
Amin bobon Ammi.
Dariyar bobo yayi yafice sai gida.
+
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Bayan isha’i ummi tashiga d’akin safna danganin ko lfy?, akwance take tana chart itada baseera dawasu k’awayensu a group sunata zugata akan bobo, Dan tuni sunsan labarin bobo.
Jin motsin tahowar mutum yasata tura wayar a k’ark’ashin filo, danbata buk’atar kowa yagane halin datake ciki.
Azaune ummi tasameta tana duba takardunta na makaranta.
Ummi ta ce, ” o aini nazatama bakida lfy ne?, kimdawo baki nemeniba bare naji labarin autana.
‘Yar dariyar basarwa safna tayi, lah ummi wlhy fitsarine yakoroni shiyyasa banshigoba, daga baya kuma namak’ale ad’aki dankarki lik’amin girki.
Dariyar ummi tayi, ta ce, “malalaciyar banza, ke koma auren akai miki yanzu aii mijin yabani, babu abinda kika iya sai kwalliya.
Safna ta ce, ” kai ummi, aidai nasan Kodan k’yawuna mijin ya zauna dani.
Baki ummi ta ta6e ta ce, “keni rabani da shiriritarki Yakika ganomin autata?.
Tana nan tak’ara k’iba, cewar Safna tana ta6e baki.
Alhmdllh ummi tafad’a cikeda jin dad’i, ALLAH yak’ara baku zaman lfy autana, har hankalina ya kwanta aii wlhy.
Itadai safna batace komaiba har ummi tafice.
Raka ummi tayi da harara kamar ba uwartaba.
STORY CONTINUES BELOW

Na ce, ” ALLAH yashiryaki Safna.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Sai bayan isha’i bobo yashigo gidan, farking yayi Inda yadace, yafito yanufi cikin gida cikin takun gayunsa da k’asaita, hannunsa rik’e da ledoji.
Rahma da Nawal suna zaune afalo suna homework.
Dagudu Nawal taje ta rungumesa, Yaya sama da ita yana sumbatar kumatunta, d’iyar momy ya gida?.
Ta ce, “my papa lfy, ledan hannunsa tak’ar6a, ya ce, ” zaki iya kuwa baby?.
Lah papa momyna ta ce, “niba raguwa bace, ko momyna?..
Rahma ta ce, ” hakane my dear keba raguwa bace.
Tad’an kalli bobo ta ce, “sannu da zuwa.
Yauwa ya amsa yana mata munafukin kallon nan NASA k’asa², d’akinsa yanufa yana fad’in kid’an kawomin ruwa.
Rahma tad’an turo baki gaba, mutum ace kullum fuska a d’aure kamar wani soja?, azuciyarta take wannan maganar.
Tamik’e tana cigaba da mitarta azuciya, to miye nacewama nakai masa ruwan sha d’aki?, sabon salo wai gaida uwar miji akasuwa, dahakadai tad’auki ruwa da cup tasaka a k’aramin filet tanufi d’akinsa.
Harya cire kaya dagashi sai gajeren wando, yana zaune abakin gado yana waya da ya Hamza.
Ta turo k’ofar tashigo da sallama, tai saurin kauda kanta Dan ganinsa babu kaya, aiko tazame zata fad’i suuuuuuuu.
Da sauri yatareta tafad’o jikinsa, saurin kallon inda tafad’a tayi, karaf suka had’a ido, kallon juna sukeyi cikin kallon ido cikin ido, da sauri Rahma ta lumshe idanunta danbazata juri kallon cikin idonsaba.
Shikam aituni tsigar jikinsa ta tashi, shima yalumshe nasa fararen idanun yana murmushi, haka kawai yatinci Kansa anishad’in kasancewarsu haka.
Rahma tafara yunk’urin tashi daga jikinsa, duk kunya ta lullu6eta.
Cikin muryar nan tasa mai sanyi da amo ya ce, “sorry.”
Itama ahankali ta ce, ”ngd, har yanzu yak’i bata damar tashi daga jikinsa, saima k’ara rik’eta dayayi.
Wayarsa aka kira, suduka suka kalli wayar, Rahma tayunk’ura ta zame jikinta, tiren hannunta yakar6a Wanda ALLAH yatsare babu abinda yazube, tomiya tsorataki?, yay maganar yana watsa mata wani shi’umin kallo.
Azuciyarta ta ce, ”Kaine mana, amma afili saitace babu komaifa.
Murmushi kawai yayi Dan yasan ganinsa datayi babu rigane ya razanata.
Batayi auneba taji anjamata hanci, matsoraciya kirage tsoronnan naki.
Dad’an gudunta tafice daga d’akin.
Murmushi yayi yana girgiza kai, afili ya ce, “k’uruci dangin hauka.
Falo tadawo tabud’e abinda yakawo musu, gasashshen namane da ice-cream, tana cikin dubawa yafito sanye cikin wando 3½ da k’aramar riga tashan iska, yau da alama babu karatun jarida babu danna laptop Dan wayoyinsane kawai ahannunsa.
Kujerar dasu Rahma ke jingine ya zauna, Nawal ta ce, “papa zomiyi game.
Baga shinan kinayi da momyn kiba, Nawal tayi shiru dantaji haushi.
Yakalli Rahma wai INA bak’uwar takin?.
Tafa wuce gida tun d’azun.
Baice komaiba, Wayarsa yad’auka yafara charting Wanda saiyayi kwana uku bai hauba.
Rahama ta ce, ” azuciyarta ana nandai da hali.
Ta daure ta ce, “papa akawo abinci, yad’ago yana kallonta, shikam mamaki take bashi idan tace masa papa, ya ce, “zuwa anjima.
Daganan kowa yay shiru shi yana danna waya, sukuma suna game.
Ajiye wayar yayi yana kallonsu batareda sun saniba, Nawal tafi Rahma iyawa sosai, Dan suna ‘Yar tseren motocine, amma tuni Nawal ta tserema Rahma, yashagala sosai akallen nasu, can Nawal tayi winning, Rahma ta ce, ” bata yardaba, sai dariya da murna Nawal takeyi.
Nawal tamik’ama bobo handle d’inta, papa kar6i handle d’ina kuyi da momy naje nayo fitsari.
Babu musu yakar6a, tanufi d’akinsu da gudu, shikuma yasakko k’asa kan carpet Kusada Rahma, har jikinsu nad’an gogar juna.
Kad’an Rahma tad’an muskuta suka fara, anutse kowa ke controling d’in motarsa, saidai awannan karon Rahma tafi bobo iyawa.
Dariya ta kufcema Rahma Dan ganin yanda bobo kek’ara k’aimi, shima dariyar yafara yana k’ara gudu danson wuceta amma yakasa, Nawal tafito taje bayan papanta tad’ane tana kallonsu, dariya sosai sukeyi kowa yana Nuna kwarewarsa, Nawal tana k’ara zugasu, momy gooo karki bari papa yakamaki, idan sukayi kamar zasuyi karo Nawal tabuga k’ara tamkar wad’anda suke agidan kwallo, bobo yana ganin Rahma zata masa game over sai kawai yafara k’ok’arin kwace handle d’inta, nanfa suka kaure kokawa suna dariya, itama Nawal tad’aresu tana dariya wai momy tafi papa k’arfi.
Sun shagala sosai wajen tumurmusar juna, hardai Bobo yasamu nasarar kwace handle d’in Rahma, ya ce, “saidai kar kowa yayi winning, dadai nayarda na d’auki game over.
Rahma tarik’e ciki tana dariya, cikin dariya ta ce, ” wannandai game ta fin k’arfice, miyasa zaka karaya dawuri haka?, hhhhhh.
Tsayawa yayi cak yana kallonta Dan dariyar tayi mata bala’in k’yau, jiyake kamar karta daina, yalumshe ido ahankali yabud’e akan Rahma data fara tsagaitawa da dariya tana d’aukar d’ankwalinta daya fad’i can gefe wajen kokawa.
Shi saima yanzu yalura da bak’in gashinta sid’ik irin Wanda ake kira roba roba d’innan, Dan yacika kan dam, ta d’aureshi kamar acuci, dukda bata saka masa mai amma sai kyalli da shek’i yakeyi, ahankali yakai hannu yakama gashin nata mai d’an tsawo babu laifi, Dan dazata cire ribom d’in to zai sauka harkan kafad’arta.
Jin hannunsa cikin gashinta yasakata dawowa hayyacinta, tayi saurin matsawa tareda d’aura d’ankwalinta.
Murmushi shima yayi, yatashi yakoma bisa kujera shida Nawal.
Itakam duk kunya tarufeta, mik’ewa tayi zata gudu d’aki, muryarsa ta dakatar da ita.
Abamu abinci muci ko babyna?.
Da Sauri Nawal ta ce, “eh momy yunwa mukeji.
Dole Rahma tadawo tagabatar da abinda yakawo, zata tafi d’akinta yay saurin rik’o hannunta, cikin sauri tajuyo, aranta tace waishi baya ganin Nawal mai shegen wayau da surutu.
Hannunta tashiga k’ok’arin kar6ewa, shikam yasake mata hannu, ina zaki? yafad’a adake.
Ganin yanda yay magar saita kama kanta, kanta ak’asa ta ce, ” d’aki.
Abincinfa?.
Nak’oshi.
Ashe zanmiki d’ura.
Da sauri ta ce, “tom zanci.
Murmushi yayi, itakuma tadawo ta zauna, babu yanda zatayi dole tasaka hannu sukaci naman a filet d’aya su uku.
Dad’i Nawal taketaji, Dan haka idan tad’ako nama tasakam Rahma abaki saita sakama bobo shima abaki, cikeda nishad’i sukecin naman, bayan sun gama aka dawo kan ice-cream, babbar roba d’aya sukesha su uku.
Rahma dukta kasa sakin jikinta, saboda kunya, bobo yana kula da ita amma ya share, yad’auke kansa yana maida TV wajen labarai.
Nawal tad’ebo ice-cream tabama bobo abaki, takuma d’ebowa tabama Rahma.
Shima bobo yad’ebo yabama Nawal, Yakuma d’ebowa yanufi bakin Rahma, k’asa tayi da kanta wai ita kunya, muryarsa kasa² kamar mai rad’a ya ce, ” zan zuba abakina sannan nakama bakinki najuye miki, kuma agaban Nawal komai zai faru.
Babu shiri Rahma tabud’e baki yazuba mata ta shanye.
Nawal ta ce, “momy kema kibamu to.
Babu yanda Rahma zatayi tunda an rutsata, ta d’ebo tabama Nawal, takuma d’ebowa amma takasa d’agowa.
Cikin shagwa6a bobo ya ce, ”baby kinga momyn ki ko tak’i tabani ni.
Lah momy kibama baby karyayi kukafa.
Bak’aramar dariya abin yabama Rahma ba, wai k’ato dashi yanama ‘yarsa shagwa6a, tana k’umshe dariya tad’ago tabashi shima, shikuma yad’aga mata gira.
Kanta ta tura cikin cin yoyinta Dan abin yabata matuk’ar kunya.
Hakadai suka riski wannan dare cikin nishad’i, bayan angama labarai suka tafi d’aki, shima yatafi d’akinsa cike da kewarsu, da mamakin Kansa a yau, yana Abu tamkar bashiba.
Wani 6angare na zuciyarsa ya ce, ” kafad’a tarko ne…………..
*_Happy juma’at Mubarak my lovely fan’s._*
❤❤❤❤💋💋💋💋💋💋💋
luv you all my fan’s
💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 28
Washe gari Safna sukayi sammakon tafiya wajen malam da’u, yauma dai k’arya tashirya ma Abba da ummi harta samu damar fitowa da sanyin safiyarnan.
Ak’ofar gida suka had’u Baseera tabud’e tashigo.
Kallon safna take cike da mamaki, Safna kinga kuwa yanda idonki ya kumbura?, amma dai kinyi kuka?.
Humm baseera kenan, aii jiya kukan jijine kawai banyiba wlhy, amma fa yanda naga rana haka naga dare, nayi nadamar zuwa gidan banzar yarin yarnan jiya, Dan dabanjeba dabanyi gamo da abinda zai dameniba, amma kuma hakan alkairine Dan koba komai naga farin cikina, nakumasan Inda zan sameshi yanzu, ta k’are maganar da share hawaye.
Kiyi hak’uri kibar kuka, komai zai daidaita nasan aikin malam da’u saikinyi farin ciki.+
“nikam na ce, “shi d’in banza, shima ga ALLAH yake nema”.
Mtsoooooow!!.
Suna tafiya sunad’an hirarsu, baseera ta ce, ” amma ummi bata saniba ko?.
Kai yazanyi tasani, kinsanma kuwa yanda takeji da shegiyar Rahma d’innan yanzu, kenifa inaga duk cikinmu ummi tafison Rahma ayanzu.
Kai Safna aiiko bazakice hakaba, duk gidannan babu Wanda akaima gata sama dake, kitunafa, ummi tabamu labarin tunkan tayi aure take addu’ar ALLAH yasa tahaifi mace haihuwar farko, amma ALLAH saiyabata maza, bayan ummi ta haifi ya Shaheed da ya Munneer taso haihuwar mace sosai, saikuma haihuwar tatsaya ma gaba d’aya, saida ya munneer yay shekara 7 sannan ALLAH yabata cikinki, kullum itace addu’a da sallar dare, har umara sukaje itada Abba saboda ALLAH yabasu ‘ya mace.
ALLAH mai k’yauta da k’ari aka silli6oki duniya, gatadai kinshashi fiye da kowa agidan, abinda kikeso shi ake miki, shiyyasa kika taso ‘yargata ta6ararriya, wlhy tsiyar dakikeyi agidanku Inda Rahma takeyinta datuni tashiga wani hali.
Amma harzaki bud’i baki kice anfison Rahma, duk Wanda yasan tarihin gidanku to bazai yarda da maganar kiba wlhy.
Shiru Safna tayi, Dan tasan gaskiya Baseera tafad’a.
Da hakadai suka k’arasa gidan malam da’u.
°*°*°*°*°*°*°*°*°*°*°
Tunda tatashi take hidimar gyaran gidan, bayan tahad’a breakfast tayima Nawal wanka tashiryata tsaf cikin kayan makaranta, tsaf yarinyar tafito tamkar kasaceta ka gudu, dama ga k’yau d’an asali, tana girma kamaninta nasake fitowa da mahaifinta.
Rahma ta kalli agogo 7:6am, ta ce, “baby bara nayi wanka nima kafin papa yafito.
To momy, Nawal tayi maganar tana k’ara gyara igiyar takalminta.
Cikin d’an lokaci k’alilan tayi wankan tai shirinta cikin siket da riga ‘yan kanti, d’an tsaki tayi Dan ganin rigar batada tsawo, aranta tace yanzu kanayin kuskuren d’aga hannu sai anga cikinka, da wannan mitar aranta suka fito falo.
Harta zauna a dinning itada Nawal saikuma tamik’e Dan hangen labulen windown Kusada su ya nannad’e.
Wani d’an kujera dake gefe wadda Bobo kan zauna idan baya buk’atar hayaniya ta janwo ta taka Dan tsawonta bazai kaiba, hawanta keda wahala koma labulen bata gyaraba tadai mik’a hannu zata gyara taji takun fitowarsa kwass kwass, tsintar kanta tayi da k’urama hangar tahowarsa idanu.
Ya salam tafad’a yayinda bobo yabayyana, sanye yake cikin wando dariga farare tas, ya d’ora rigar suit jaa mai laushi, takalminsa agogonsa duk jajayene, sai zabga uban k’amshi yakeyi, sajen nan yakwanta luf luf sai shek’i yakeyi.
Tashagala sosai akallonsa batareda tasaniba, shima gareshi hakan take, tsaye yake k’yam tamkar andasashi, idonsa nakan farar fatar cikinta data bayyana sakamakon d’aga hannu datayi zata gyara labulen daya nannad’e.
Ganin ya motsa yasa ta firgita, abisa tsautsayi kukerar tad’an goce tayi baya kamar zata fad’i amma tayi nasarar rik’e k’arfen window.
Ahankali yatako har inda take, fuskarsa babu yabo babu fallasa, baya murmushi bakuma a d’aure takeba, ahankali yayi maganar tamkar bayaso ko ammasa dolene.
Mikike kallo haka? Dahar kike shirin fad’uwa?.
Turo baki Rahma tayi, danta gaji wlhy, gashi Idan ta ce, “zatayi yunk’urin sauka fad’owa zatayi, Dan kad’an k’afarta take d’ofane akujerar.
Yanda ta turo baki cikeda shagwa6a saita k’ara burgesa, dama ga kwalliyarta ta tafi dashi, yad’an lumshe idanunsa ya bud’e akanta, bazakiyi maganaba ko?, Ashe zan barki kifad’o d’iyarki tamiki dariya, yayi maganar yana kallon Nawal da hankalinta baya kansuma gaba d’aya, wasanta takeyi da cokulan da Rahma ta ajiye a dinning.
Dawo da kallonsa yayi ga Rahma, cikin sanyin nan NATA tareda shagwa6a ta ce, ” ALLAH hannuna zai karye please help me.
Wani k’asaitaccen murmushi yayi tareda ajiye jakar aikinsa, yatura hanuwansa duka biyu a aljihu, idan na taimakeki kedami zaki biyani?.
Shiru tayi tana kallonsa, can kuma ta ce, “mikake so nabaka amatsayin ramako?.
Yad’an d’age kafad’a yana ta6e baki, nikomi kika bani fine.
Ta marairaice murya tamkar zatayi kuka, ALLAH nagaji zan fad’o.
Kauda kansa yayi gefen Nawal yana murmushi, ganin har yanzu hankalinta baya kansu yad’auke kai. Matsowa yayi Kusada Rahma tareda zare hannunsa daga aljihu ya tallafota, daga ita harshi lumshe idanu sukayi, tallafota yayi tamkar jaririya, ahankali yabud’e idonsa akanta, amma ita har yanzu nata alumshe suke, yakalli k’irjinta dayayi d’as a pink d’in rigar, ajiyar zuciya yasauke sannan yadireta ak’asa, saiyanzu tabud’e idanunta masu matuk’ar burkitashi, thanks tafad’a tana k’ara juya idanun.
Shi ganima yake tamkar da gayya tamasa haka, lumshe idanu kawai yayi yana jinjina kai Dan bakinsa yayi masa nauyi, cikin salonsa ya ce, ” nawafa?.
Ta ce, “me?.
Ramakona mana, kokin manta da yarjejeniya mukayi.
Kauda fuskarta tayi gefe Dan bazata juri kallonsaba, mikaso to?.
Abu biyune kawai, kuma marasa wahala.
Kafad’a inji idan zan iya.
Nafarko dai gyaran d’akina, Dan yayi datti, nabiyu kuma….. Saikuma yayi shiru, tajuyo tana kallonsa miye na biyun?.
Wani murmushin basarwa yayi, murya kasa k’asa ya ce, ” kiss me”.
Idanu tazaro, saikuma tajuya zata gudu, da Sauri yadamk’o hannunta, tsayawa tayi cak amma takasa juyowa…..
Momy papa!!!!. Zanyi latti fa…..
Muryar Nawal ta riski kunnuwansu, da Sauri yasaki hannun Rahma, itama tayi Saurin k’arasawa ga Nawal.
Break fast tashiga had’a musu, Bobo yak’araso dinning d’in, kujera yagyara tamkar zai zauna yakai bakinsa Kusada kunnen Rahma, kitabbata idan nadawo saikinyi, inba hakaba zanmiki abinda yafi kiss.
Kafin tad’ago yaja kujera ya zauna.
Dukta daburce, itafa mamaki bobo take bata cikin ‘yan kwanakinnan, tamkar bashiba, awaje idan kagansa dolene kaji tsoronsa da masa kallon mutum mai Girman kai da tsabar shariya, amma daka zauna dashi nad’an wani lokaci saika fiskanci shi mutumne mai sauk’i da iya zama da mutane, tasauke ajiyar zuciya tareda tura musu abincin kowanne agabansa.
Sunacin abinci yana mata munafukin kallon nan nasa, dukta takura awajen, adaddafe dai aka kammala suka mik’e.
Takama hannun Nawal suka fice shikuma yana binsu abaya har wajen mota.
Rahma ta rissuna taima Nawal kiss akumatu kamar yanda tasaba, itama Nawal Tamata, bobo yak’araso yana fad’in saura ni.
Shiru Rahma tayi tamkar bama tajishiba, bata ankaraba taji yabata summba (kiss) akumatu, dasauri tad’anja baya tareda lumshe ido, saikuma tajuya dagudu zuwa cikin gidan.
Murmushi yayi tareda binta da kallo harta shige ciki, shima yabud’e mota yashiga yana murmushi.
Saida yafara ajiye Nawal amakaranta sannan yanufi wani waje.
Adaidai wani k’ofar shago yatsaya, batareda yafitoba, yamik’a hannu ta windown shagon aka mik’o masa wasu takardu.
“banga fuskar wayeba nima.”
burka motarsa yayi yay gaba yana bin karatun alkur’anin dake tashi amotar ahankali.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Su Safna sun samu shiga wajen malam da’u, bayan gaisuwa ta labarta masa yanda komai yafaru tundaga randa suka bar wajensa, duk cikin matsanancin kuka takeyin bayani.
Shima Kansa malam da’u yarazana dajin batun na Safna, amma dayake yana son cin kud’i saiya dake abinsa.
Ya ce, “toke yama akayi haka tafaru dake kika kamu dason mijin k’anwarki?.
Safna tashare hawayenta, cikin rawar murya ta ce, ” malam katuna da labarin farko Dana Baka, saikuma kahad’a Dana yamzu zakagane bansan *_“ABADUL-MALEEK”*_ BOBO me iyayena sukaso na auraba, sai yanzu daga baya.
Jin jina kai malam da’u yayi, ya ce, “lallai kinyi Sake yarinya, amma zanyi iya bakin k’ok’arina Dan ganin kin mallakesa, Dan naga itama bata sonsa shima haka, Dan haka zamuyi nasarar rabasu cikin sauk’i, kid’aukama kinzama matarsa kawai.
Wasu kayan tsubbunsu yabata, yamik’a mata wani ruwa a ‘Yar jarka, ga wannan duk yanda zakiyi to kiyi Dan yasha abunnan, wannan kuma acikin abinci, sau uku zakiyi duka, Indai har yaci Yakuma sha tozaice ke yakeso, kuma zai saki k’anwarki.
Wannan kwallin kuma kiringa sakawa a idonki, kiyi k’ok’ari kuma Ku kalli juna ido cikin ido.
To malam ngd sosai Safna tafad’a tana washe baki, to amma malam duk tayaya zanyi wannan aiki nida ba gida d’aya mukeba?.
Malam yayi dariya, kekam saikace ba maceba, kiyi duk yanda zakiyi ki aikata, wannan yarage naki, nidai nagama nawa.
Tunda suka baro gidan malam babu mai magana da wani tsakaninta da baseera, kowa da abunda yake sak’ama zuciyarsa.
Safna dai tunaninta nakan yanda zataci nasarar ciyar da BOBO wad’an nan magungunan.
Amma zata gwada wata dabara tagani.
*_(“ni bilyn Abdul na ce, ” hummmmm, muje zuwa Safna.”)._*
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Jikake keyyyyyyyyyy yaja wani wawan birki da k’arfin tsiya Dan ganin wasu zaratan samari majiya k’arfi agabansa, sai faman huci suke suna mummurd’ewa, alamar jin karin k’aimi akan burinsu.
d’an tsaki yaja tareda cije le6ensa na k’asa, afili ya ce, “wad’annan k’ananun karnukanfa nawaye?.
“na ce, ” hummmmm.”
Murfin motar yabud’e cikeda Isa yafito, kuma fuskarsa tana nuna alamar hankalinsa kwance yake, yarufe murfin sannan yajingina ajikin motar, hannayensa yatura cikin aljihun farin wandonsa, ya hard’e k’afafunsa biyu dake sanye cikin Jan takalmi sau ciki mai k’yawun gsk, idanunsa sanye da siririn farin gilas, yad’an karkace kansa gefe yana k’are musu kallo d’aya bayan d’aya, shi dariyama suka bashi, Dan haka yasaki wani lallausan murmushi mai birkita ma’abocin kallonsa Wanda Ammar yasakama suna murmushin mugunta, Dan yafi bomb had’ari.
Cikin muryarsa mai taushi da amo ya ce, ”yan samari halan lafiya dai?.
Zaratan samarin suka k’ara babban k’aro k’irji gaba had’eda hura hancinansu danjin furucin BOBO maicikeda rainin wayo.
d’aya daga cikin samarin ya ce, “lafiya idan kabamu abinda muke nema, amma babu lafiya idan kace zakayi kuskuren hanamu.
Tofa, yafad’a yana k’ara sakin lallausan murmushi, lokaci d’aya kuma yahad’e fuska tamkar hadarin gabas, yasaka d’anyatsa d’a yajawo gilashinsa k’arshen hanci, saikuma yasakeyin murmushi, Yakuma gyara tsayuwarsa, ya ce, “to yan samari miye buk’atar taku?.
Kallon juna sukayi Dan aganinsu yaji tsoro, nafarkondai yasake yin magana, d’an uwa takardun dake cikin motarka Daka kar6a yanzu muke buk’ata.
‘Yar dariya yayi akaro na farko, yakai hannunsa na dama ya shafa lallausar k’asunbarsa ya ce, ” tofa, aikin babbane Ashe, hannunsa yacire daga aljihu, yatako ahankali yak’araso har Inda suke, yakuma binsu da kallo d’aya bayan d’aya, sannan yamaida kallonsa akan mai maganar, Wanda nake k’yautata zaton shine ogansu.
Cikeda Isa ya ce, “yan samari bayan takardu mikuke buk’ata?.
Wata mahaukaciyar dariya babban yasaki, saida yayi mai isarsa, BOBO na tsaye yana binsa da kallo, shima yakalli BOBO cikeda izza ya ce, “d’an saurayi konace matashin lauya bama buk’atar komai bayan takardunnan dai, sukad’ai sun wadatar damu…………..
Kafin yarufe baki yaji wani shegen naushi akumatunsa na haggu.
Tuni oga yazube ak’asa a sandare, BOBO yabishi da kallo yana murmushi tareda shafa gemunsa na gayu, ‘yan samari har wannanma bakwa buk’atane????.
Gaba d’aya sauran zaratan samarin sukayo kan BOBO, wani juyi yayi akansu saiga biyu ak’asa.
����♀sum sum nakoma bayan motarsa namak’ale kafin a maujeni���� kurasa mai d’akko muku rahoton kuma.
Tabd’ijan masu karatu nifa azatona a film kawai ake irin wanga Abu, Ashe afilima anayi, cikin ‘yan mintuna saiga ‘yan samarin nan kwance ak’asa gaba d’ayansu.
Daga mai karyayyen hannun saimai karyayyar k’afa, saimai zubabben hak’ori.
Amma gwarzon naku ko zoben dake yatsansa bai fad’iba barema ayi zaton yaji ciwo.
Yataka hannun wani yana tsaki mtsowwwwww shashashu k’ananan karnuka kawai…. Uban waye ya aikoku gareni??, Ku karnukan farautar wayeeeee!!!!!!?. Yay maganar cikin k’araji!!!!!…………..
” wayyo masu karatu, tsawar BOBO tarazanani, tuni nakwasa da gudu na6uya bayan wata bishiya, inaga kuyi hak’uri kawai zuwa gobe idan nasamu nutsuwa saina idabaku rahon yanda BOBO yak’are da karnukan farautarnan kamar yanda yake fad’a musu……..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 29
*_Assalamu alaikum. Happy new Islamic year 1439AH. Wish you all the best in this new Islamic year. Amen thumma Amen._*
4⃣8⃣
Mota yakoma yad’auki d’aya daga cikin wayoyinsa, sai hura hanci yakeyi, bugu biyu akad’aga, ad’an kausashe ya ce, “Ammar ina buk’atar yaranka.
My guy lfy kuwa?.
Mtsooowww wasu wawaye aka turomin, so nad’an koyar dasu zaman tarbiyya ne.
Murmushi Ammar yayi, Dan yasan waye abokin nasa, okey kabani 15m. Katsal.
Baice k’alaba ya yanke wayar, cikin motar yakoma ya zauna, amma murfin abud’e yake, k’afafunsa duk suna k’asa.
Mintuna kad’an saiga motar police, tuni aka yayibi karnukan farauta acewar BOBO aka watsa amota.
Bobo yakalli police d’in ya ce, ” kukaisu asibiti, abasu kulawa ta musamman, zuwa gobe kuma natsincesu a Stations, yana gama fad’a yashige motarsa.
Suma ‘yansan Dan mota suka shiga, harya tada mota wani police ya kwankwasa MASA, sauke gilas d’in yayi yana kallon matashin police d’in batareda yayi maganaba.
Umm yaya dama cewa nayi kozamu fara rakaka inda zaka tukunna.
Fararen idanunsa yad’ago, wad’anda ahalin yanzu sukad’an canja kala zuwa jaa, no karka damu Musadiq kuje kukaisu asibiti, sune keda buk’atar taimako baniba, saidai zuwa gobe kutabbatar da sunk’ara cin ubansu, harsai sunfad’i wanda yaturosu.
d’an murmushi Musaddiq yayi wanda daga gani akwai sanayya tsakaninsa da bobo, ya ce, “ok yaya ALLAH ya tsare.
Shima bobon murmushi yayi tareda jinjinama musaddiq sannan yaja mota yay gaba.
Musaddiq yabi motar da kallo yana murmushi, shidai arayuwarsa yana k’aunar ya Abdulmaleek domin mutumin kirkine, yanzudai kalli anturo mutane dansu cutar dashi, yakuma sassanbad’esu amma saboda adalaci ya ce, ” akaisu asibita abasu kulawa ta musamman, (ALLAH sarki aunty Ni’ima, ALLAH yajik’anki, inama kina darai har yanzu, daduk gidanmu sainace kinfi kowa dace da miji nagari).
“araina na ce, “kenan k’anin marigayiya Ni’imane shi?.”🤔
+
Guri yasamu yay farking cikeda tak’ama yanufi office d’insa, sai rissinawa ma’aikatan wajen suke suna kwasar gaisuwa, ransa a6ace yake danhaka ko amsa musu bayayi, hannu kawai yake d’aga musu.
Sakatariyarsa ta jinjina kai, aranta ta ce, ” yau kuma boss afusace akazo?.
Zama tayi bayan yashige, turare tad’auka tak’ara fesama jikinta tareda k’ara gyara fuskarta, sannan tanufi office d’in.
Kamilu masinja yata6e baki yana fad’in yarinya wahala bata ishekibane, nasan ko matan duniya sun k’are wlhy oga bazai sokiba.
Ahankali ta tura k’ofar tashiga, yana zaune akan kujerarsa ta alfarma, kwance yake acikin kujerar idonsa alumshe yanad’an lilawa ahankali, tabishi da kallo zuciyarta na zungurarta da wani Abu, a zuciyarta ta ce, “ALLAH ya mallaka minkai amatsayin mijina.
Na ce, ” hummm.”
K’arasawa tayi Inda firij yake, tad’akko drinks da cup tanufi inda yake.
Saida tagama tsiyaya lemon sannan ta ce, “oga ga abinsha ko kana buk’ata?.
Baice mata komaiba, saidai yabud’e idanunsa dasukayi d’anja Dan 6acin rai.
Waye yazo nemana?, yafad’a cikeda karsashi.
Tuni takama kanta, cikin d’ari² ta ce, ”mutum 3 sunzo nemanka amma biyu sun had’u da yalla6ai Kamal.
Ya ce, “d’ayanfa?.
Ta had’iye yawu kuut, d’yan Ra’is ned’an gidan…….. Hannu yad’aga mata alamar baya buk’atar k’arin bayani, yay mata nuni tatafi.
Tafiya take cikeda salo tana juya mazaunai, hartakai k’ofa ya ce, “k zonan.
Cak tatsaya k’irjinta na dukan uku², ahankali tajuyo saitaga bama ita yake kalloba waya yake dannawa, jiki a sanyaye tace sir gani.
Idanunsa akan waya ya ce, “k sau nawa zan fad’a miki karki sake zuwamin nan da k’ananun kaya office?.
A zuciyarta ta ce, ” danka k’yasane, amma afili saitace sorry sir zan kiyaye.
Tsaki yaja, har yanzu idonsa nakan waya ya ce, “wlhy daga yau kika sake banzar shiga kikazomin office abakin aikinki, 6acemin anan!!!!.
Dasauri tafice Dan atsawace yay maganar.
Yay kwafa tareda fad’in stupid gal kawai.
Waya ya d’auka yakira kamal, bugu d’aya ya d’auka, kamal kana office ne?. Eh Abdulmaleek, ka isone?.
” eh yanzu na k’araso”.
Okey ina zuwa.
Laptop yajawo yafara danne dannensa, bayan wasu ‘yan mintuna saiga kamal, hannu yabashi suka gaisa, sannan ya zauna.
Wai ina ka mak’alene?.
Laptop d’in gabansa ya ture gefe, yadafe tebir yana kallon Kamal, kabari kawai d’an uwa inacan an ritsani za’a kashe.
Ban ganeba?, kisa kamar ya?.
Ajiyar zuciya bobo ya sauke, ya CE, “wlhy kuwa kamal, wasu k’anan karnukan farauta aka turo waisu kar6i takardu a hannuna, nasandai bai wuce aikin wawayennan ba.
Suwa kenan?.
Ra’ees da babansa mana, Dan babu wasu takardu ahannuna saina kes d’insa, kuma sakatariyata tace yazo nemana.
Kwarai kuwa d’azu Nazo danmuyi magana baka nan, to ayayin shigowata mun had’u, zaifita nikuma zan shigo.
Humm, kamal lokaci yayi dazan fito naci uban mutanen nan fa.
A’a Abdulmaleek karkayi haka, har yanzu munada sauran bincike kaima kasani.
Hakane, amma wlhy natsanesu.
Wlhy nima hakantake, yanzudai bara naje, inada wata shari’a anjima kad’an, idan mungama zan dawo.
Okey saika dawo to.
Tunda kamal yafita yabar office d’in bobo yafad’a duniyar tunani, tunanin Rahma ya kanainaye zuciyarsa gaba d’aya, haka kawai yarinyar tana birgeshi, ko kad’an batada damuwa.
Murmushi yayi tareda kauda tunaninta yamaida hankalinsa ga tuno Wanda zai iya turo masa ‘yandaba, yamik’e Dan har yanzu ransa a6ace yake, wani wawan huci yafurzar tareda naushin iska, waini za’a turoma ‘yan daba yafad’a cikin k’araji, yacije le6ensa yana gyad’a kai humm zanyi maganin koma wane d’an iskane.
K’arasawa yayi gaban firij ya tsiyaya lemo akofi yakoma jikin windown office d’in na gilas ya tsaya, hannunsa d’aya a aljihu d’aya rik’eda kofin.
Ahankali yakai kofin bakinsa yakur6i lemon, idonsa akan mutanen dake fitowa awasu bak’ak’en jeep, Alhaji Abdurazak yafad’a yana gyad’a kai tareda ta6e baki, yad’anyi shiru alamar tunani, amma miyasa tunanina bai kawomin kai acikin wad’anda zasu iya turamin ‘yan daba ba?.
Yasaki murmushin nan nasa na mugunta.
Sakatariya taturo k’ofar da sallama.
Bai juyoba amma ya amsa sallamar.
Ta ce, “sir…….
Hannu yad’aga mata, ya ce, ” kice yashigo.
Tad’an zaro ido Dan abin yabata mamaki, bayau Alhaji abdurrazak yafara zuwa office d’innan ba, kuma duk sanda yazo oga baya bashi damar shigowa, Amman yau tunkan tafad’i ko waye yace yashigo, kuma tasan yagansa ta inda yake tsaye, kai lamarin da mamaki.
Itadai haka tak’arasa tasanar da Alh Abdurrazak, shima abin yabashi mamaki amma saiyayi tunanin ko bobo yaji tsorone.
Bobo yana tsaye baikuma juyoba har Alhaji ya zauna, saida yaja tsawon Minti biyu sannan yajuyo, taku yakeyi cike da isa harya k’araso mazauninsa.
Abin ya harzuk’a Alhaji amma saiya dake.
Bobo dake lila kujerarsa ahankali, idonsa akan alhajin ya ce, “Alhaji mike tafe dakaine?, yay maganar cikin salonsa na isa.
Alhaji yacije le6en jin haushi, saikuma yayi murmushi Barrister nazo maka da Business ne.
STORY CONTINUES BELOW

Bobo– hummm wane irin business?.
Alhaji– Akan aikine.
Bobo— miyasa saini?.
Alhaji– saboda ka cancanta.
Bobo– kayi kuskuren fahimtar hakan.
Alhaji– miyasa kayi gaggawar yanke hukunci?.
Bobo– saboda hakane yadace, kuma nasanka nasan kaina, bamu dace da had’a business ba.
Alhaji– a’a Barrister ka saurareni.
Bobo– mizaisa na saurareka?.
Alhaji– Saboda nayimaka bayani yanda zaka aminta dani.
Bobo yayi murmushin rainin hankali, Alhaji miyasa kakeson takuranine?.
Kayi hak’uri maganata mai muhimmancice tasha banban data baya Barrister.
d’an kafeshi da ido bobo Yayi, dayin tunani na second 20, yalumshe idonsa ya ce, ” INA saurarenka.
Murmushi Alhaji yayi, azuciyarsa ya ce, “dole ka saurareni aii, yagyara zama yana fad’in Barrister dama akan maganar yaron aboki nane Alhaji sunusi dala, nawa kakeso mubiyaka ka lalata shari’ar?.
Bobo bai amsa masaba, hasalima hankalinsa yana kan bodyguard d’in Alhajin dake k’ok’arin zarar wata takarda da bobo ya ajiye akan Derk’s d’insa. Murmushi bobo yayi ya ce, ” mai gadi zaka saidama mai k’osaine?.
Dasauri bodyguard d’in yacire hannunsa Yakuma matsa baya.
Bobo ya girgiza kai yana maida kallonsa ga Alhajin, INA saurarenka.
Alhaji da haushi yakashe, jiyake tamkar yasa aharbe MASA bobo Dan haushi da tsanarsa dayayi, yazaro sigari yasaka abaki, dasauri d’aya daga cikin bodyguard d’in yakunna leta zaisakama alhajin….hannu bobo yad’aga masa, yatashi tsaye tareda rankwafowa akan tebir d’in yasaka yatsunsa biyu yazare sigarin bakin Alhajin yana girgiza kai, sorry Alhaji ba’a shamin sigari a office, saboda yana lalata lafiyar maisha da mai shak’ar warin.
Ya ajiye masa kusadashi akan tebir d’in, gata nan idan katashi tafiya zaka iya d’aukar kayanka, Yakoma ya zauna.
Wani Abu ya danna yay k’ara saiga sakatariyarsa da Sauri tashigo, bai kalletaba ya ce, “kawoma Alhaji abin sanyaya mak’oshi Dan yana buk’ata.
Okey sir, tafad’a cikeda girmamawa.
Alhaji kam ya k’ame azaune, lallai yak’ara tabbatarwa yaron nan d’an iskane, amma zasu gyaramasa zama, a fusace Alhajin yamik’e yakar6i lemon da sakatariya tamik’o masa yay jifa dashi, kofin yadaki bango ya tarwatse.
Wata dariyar rainin hankali bobo yayi, yamik’e yana tafa hannayensa wooow! Alhaji ammafa ka burgeni, kaga yanda kayi d’innan haka nayima yaranka Nima d’azu da safe, saidai banbancin d’ayane, kai Kofi kafasa, nikam mutane na jibga.
Aburkice Alhaji yake kallon bobo kuma atsorace, amma saiya danne yahad’e fuska tareda Nuna bobo da d’anyatsa, kai k’aramin tantiri kashiga hankalinka, yaro kai k’aramin naman dajine idan yanzu mukaso saimu hallaka ka tamkar yanda muka hallaka………haba Alhaji mikakeson fad’ane haka?.
Bodyguard yay saurin Tatar numfashin Alhajin.
Bobo yayatura hannayensa a Aljihu yana murmushi, ya ce, ”no no no mai gadi, Daka barsa yak’asa fad’a kaga ya ragemin nauyin bincike, amma babu laifi hakanma ngd sosai yak’are maganar da d’aga fad’a yana ta6e baki, aii kobai fad’aba nasan yanaciki.
Yakuma gyara tsayuwa, yataka daf da Alhaji ya tsaya, ya ce, “Alhaji kakirani k’aramin naman daji.
Bakayi k’aryaba, tabbas ni naman dajine mai amsa suna *_ZAKI_*, ni zakine bana 6arnar banza, ammafa duk sanda naji yunwa kowa Shiga hankalinsa yakeyi, Ku saurari fitowata Dan duk sanda naji yunwa saina lak’umeku amatsayin abinci mafi Girman k’an k’anta darashin daraja…………
Kai!!!!. Alhaji yakatse bobo atsawace, yanunashi da d’an yatsa Abdulmaleek Aliyu kataka a sannu zakinma yanada nasama dashi ko’a cikin dajin.
Dariya bobo yayi ya ce, ” hakane Alhaji akwai manya manyan namun daji adokar daji, wad’anda sukafi zaki Girman jiki harda shekaru, amma girmansu baya hana zaki ya kacaccalasu aduk sanda ya harzik’o, barema idan yanakan ganiyar k’uruciyarsa, Dan haka Alhaji abdurrazak bulama Ku saurari matashin zaki yana nan tafe gareku, zaka iya barmin office kuma ka saurari sammaci, Dan zan maka ka akotu kaida karnukan farautarka, inason bin ba’asin bibiyar numfashina da kukeyi…….
Fuuuuu Alhaji yafice batareda yaji k’arshen zancen bobo ba, jiyake idan yakara minti d’aya a office d’in zuciyarsa zata bugane kawai.
Wani wawan tsaki bobo yaraka Alhaji dashi.
_(Na sauke nannauyan numfashi Dan ganin anrabu lafiya bobo baikai dukaba, danni yanzu tsoronsa nakeji)._
*_bayan kwana uku._*
Yau tsawon kwanaki uku safna tanata sak’awa da kwancewa, kullum Neman hanyar dazai kaita gidan Rahma takeyi amma tarasa gaba d’aya, tayi wujiga² saboda rashin mafita.
Ganin babu yanda zatayi yasa tasaki jikinta tanata harkokinta, agefe kuma kullum saita turama bobo message.
Tunbaya kulawa har yaudai yaymata replay, wani uban tsalle tazuba Dan dad’i, tad’ane gado tanata tsalle abinta.
Ganin yayi mata replay yau yasa tak’ara masa wani massage d’in na kalamun soyayya masu dad’i, amma har dare babu amsa, data kirama saiya katse kiran yakashe wayar duka.
Lamarin ya Sosa ranta amma saita dake, tana fad’in k’ila baya kusada wayarne.
Nidai araina na ce, “hummm.
*_kotu_*
Ayaune kuma su bobo suka koma kotu.
Bobo bai k’asa aguywa ba yakawo manyan hujjoji da shedu masu k’arfi wad’anda suke nuna haneef ya aikata fad’e ga muheebat. Ciki kuwa harda muheebat d’in kanta, wadda ya sulaiman yayma aiki ayanzu haka tana magana.
Bobo yak’arasa kusada muheebat ya ce, ” muheebat kotu tanasonji miya faru dake aranar 16/8/2017?.
Muheebat matashiyar yarinya mai wayo, tagyara tsayuwa, idonta na zubda hawaye ta ce, “yaya aranar data kasance 16/8 mama ta aikeni shagon Haleedu domin nasayo mata sabulun wanka.
Fitowata kenan Haneef yafito daga gidansu da mota…………..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 30
Kamar yanda yasaba duk sanda yaganni yakanyimin murmushi aranarma haka yamin.
Nad’aga masa hannu nima ina murmushi.
Ya ce, “min heeban baba ina zakije?.
Kasancewar alokacin bana magana namasa nuni da shagon haleedu da hannu.
Yayi dariya tareda kamo hannuna, amma saina nok’e saboda inna ta hanani, ganin haka yasa yad’akko alawar dayakan bani kullum idan zani makaranta.
Nikuma namik’a hannu zan kar6a saiya jawoni gaba d’aya cikin motar, daga wannan lokacin ban sake sanin inda nakeba sai a asibiti, wannan kad’ai nasani.
Murmushi bobo yayi tareda juyowa ga alk’ali, ya ce, ” yamai shari’a wannan hujjar kad’ai ta isa tabbatarma kotu cewa haneef ya aikata keta haddi ga heeba, abin lura anan shine haneef yadad’e yana k’ullama yarinyar gadar zare tahanyar bata alawa, ganin bazaici nasara tasauk’iba shine yasaceta tareda shak’a mata wani Abu harta rasa hankalinta, yaje ya aikata yanda yakeso da ita, awashegarin ranar yazo bakin titi nesa da anguwarsu ya jefar da ita dankar aganeshi, saidai kuma yamakaro Dan angansa harma aka d’uki number motarsa.
Dan haka ina rik’on wannan kotu mai adalci datayi dubi da d’unbin shedunmu kuma da maganganunsu ta kwatoma wannan ‘Yar yarinya hak’inta.
She data tak’arshe itace zuwan Alh Abdurrazak abokin Alh sunusi office d’ina, yamai shari’a INA buk’atar tv, babu 6ata lokaci aka kawo TV, wani kaset bobo yasaka Wanda yayi copy d’insa daga computer office d’insa, duk abinda yafaru tsakanin bobo da Alh Abdurrazak saida suka gani.
Tuni jikin Alhaji sunusi yay sanyi, yasan yau d’ansa yatafi saidai wani ikon ALLAH, amma tunda sunbama Alkali kud’i k’ila ya ku6ta.
Bobo yay shiru tareda kafe alk’ali da ido tacikin gilas.+
Jikin alk’alifa yay sanyi, yasan tabbas duk abinda bobo yafad’a gsky ne, saidaifa matsalar yaci kud’in Alh sunusi tareda masa alk’awarin zai ku6utar da Haneef, gefe kuma ga bobo yasan Barrister AAA hamshak’i sarai bashida sauk’i, kuma zai iyayin komai danyaga yakar6ama yarinyar hakkinta, azuciyarsa ya ce, “gaba kura baya damisa kenan.
Dandanan ji6i yajik’e alk’ali dukda yawan fankoki dake bada iska acikin kotun, asaitinsama akwai guda d’aya da aka aje danshi kad’ai sai abin yabama bobo dariya, Dan haka ya murmusa tareda yin wata inkiya da yatsu biyu wadda alk’aline kawai yasan miyake nufi, kuma yasan abinda bobo zaiyi inhar ya danne shari’ar, yashare gumi yana maida kallonsa ga lauya mai kare haneef, ya ce, ” lauyan Wanda ake k’ara kokanada abin fad’a?.
Girgiza kai lauya yayi ya ce, “a’a.
Alk’ali yamaida Kansa ga k’aton littafinsa yana dubawa.
Gaba d’aya ran Alh sunusi ya6aci, jira yake kawai yaji hukuncin daza a yanke, lallai yaci burin saiya koyama bobo hankali inhar d’ansa yashiga cikin garari……..
Bai rufe bakiba maganar alk’ali ta dakatar dashi.
Bayan Alkali yayi surutansa asashe nakaza zuwa kaza anyankema haneef d’aurin shekara 14 agidan yari, datarar nera miliyan d’aya da rabi domin inganta rayuwar yarinyar da karatunta.
Wani ihu haneef yakurma, saida aka rik’eshi, sai d’urama bobo zagi yakeyi.
Shikam bobo ko’a kwalar rigarsa Yakama hannun heeba suka fice yana murmushi jin dad’i da samun nasara.
Awaje yatsaya har aka fito da haneef, yaja gilas d’insa k’asa yana kallon haneef fuskarsa d’auke da murmushi.
Ya ce, ” haneef sunusi dala, so ina fata yanzu ka shaida wanene Abdulmaleek Aliyu Abdulmaleek hamshak’i, yanzu idan kafito saikayi takunka da sand’a gudun karkayi gamo dani Dan ruwaneni inhar nabayyana saina cinye gari, yay kasa² damurya zanyi missing naka my lovoly haneef bye aci gabza lfy..
Yaygaba batareda yajira amsar haneef ba.
Daga Alh sunusi har haneef ido sukabi bobo dashi, haneef ma kuka yakeyi, Alhaji sunusi kam ALLAH kad’ai yasan miyake kitsama zuciyarsa.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*
Bobo yakwashi su muheebat sai gida, sai saka masa albarka iyayenta sukeyi, har gida yakaisu, inna tashimfid’a masa tabarma ya zauna.
Cikin nutsuwa ya ce, “baba inaso kuyarda kubini can gida wajen iyayena kamar yanda nabuk’ata d’azu da safe, saboda gsky zamanku bazai yuwu anan anguwarba yanzu, na tabbata Alh sunusi bawai ya hak’ura baneba, to Dan haka nama iyayena bayanin komai, kuma sun bani izinin yau idan anyankema haneef hukunci to nawuce daku can gidan kud’an zauna nawani lokaci har abubuwa su daidaita.
Baba yagyara zamansa, ya ce, ” abdulmaleek kana ganin bazamu takurasu ba?.
A’a wlhy baba babu wani takurawa ka kwantar da hankalinka.
To shikenan mungode ALLAH yayimaka albarka ya azurtaka da yara nagari, ya albarkaci iyalinka da zuri’arka.
Amin baba ngd, yanzu Abu nagaba kuma shine idan kun koma can heeba zata cigaba da karatunta, za’a canja mata makaranta, kud’in da kotu ta kar6a mata kuma sai a ajiye mata a account harzuwa nangaba idan ta mallaki hankalin kanta saitayi abinda takeso dasu, yad’ago yana kallon idris da fuskarsa ke cikeda farinciki, dama kullum burinsa yaga tilon k’anwarsa tana karatu, amma yanayin rayuwa ya hana hakan.
Mungode ya Abdulmaleek.
Murmushi bobo yamasa ya ce, “karka damu, inaso naji kai INA katsaya anaka karatun, mikuma kakeyi yanzun?.
Matakin secondary nagama yaya, yanzu kuma ina aikin direba agidan su Rahma matarka.
Bobo yajinjina kai ya ce, ” babu damuwa kabani takardunka insha ALLAHU zan nema maka makaranta.
Baba d’aya su baba da inna da idris heeba suka kaure da godiya ga bobo inna harda kukan farinciki itada baba.
Bayan sun had’a ‘yan kayansu masu muhimmanci bobo yakwashesu sai gidan Appa.
STORY CONTINUES BELOW

Tarba akayi musu ta mutunci dan ansan da zuwansu.
Su inna sun yaba da kirkin wad’annan mutane darashin k’yamar talaka, 6angaren da aka gyara musu aka saukesu.
Bayan gaishe², bobo yamik’e yana fad’in Ammi bara nad’anje gidan sai zuwa anjima zan dawo, nasan su yayama Duk zasu shigo yau.
To mukarram ALLAH yakaimu, agaidamin d’iyata da Nawal.
To ammi zasuji, ina tagwayenkine?.
Yo basuna gidankaba.
Ayya aiban saniba bara najeto.
Agurguje yafito yashiga mota sai gida.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Su Rahma duk suna zaune suna kallon wani India film, sunyi mugun shagala akallon film d’in Dan ana zuba soyayya ne.
Bobo yashigo da sallama amma basujiba, tsayawa yayi yana musu kallon mamaki, TV yakalla danson ganin miya d’auke hankalinsa, shima shiru yayi yana kallon yanda mata da mijin suke zabga soyayya mai k’ayatarwa.
Kamar ance Rahma takalleshi tad’ago, baya tayi da Sauri tareda zaro ido, cikin Rawar murya ta ce, “sannu da dawowa.
Khairiyya da khursiyya suka d’ago alokaci d’aya suma suna kallonsa.
Amamakinsu saisukaga yayi murmushi tareda fad’in lallai yarannan gaba d’a film yatafi da imaninku ko sallama bakwaji ko?.
Wlhy Yaya bamusan kashigoba sannu dazu.
Murmushi yayi tareda nufar d’akinsa.
Khairiyya ta kalli Rahma, auntynmu yaufa mijinki yana cikin nishad’i wlhy.
Rahma tad’anyi murmushi, nimadai nakula da haka khursiyya, komiye yasakashi nishad’i?.
Dariya sukayi gaba d’aya, Rahma ta tashi dukda zuciyarta na dukan Tara Tara Dan kwana uku kenan baya cikin wata walwalar kirki, amma yau gashi yashigo musu cikin nishad’i, ruwa ta d’auka da cup tanufi d’akin.
Ahankali tayi Knocking kamar bataso. Yana kwance akan gado fuskarsa cikeda nishad’i, yau jinsa yake sakayau dashi, jin Knocking d’in k’ofa yasashi juyawa tareda amsawa, ya ce, ” shigo mana.
Rahma tashiga a sanyaye tareda yin sallama a can k’asan mak’oshinta.
Fararen idanunsa yad’ago yana kallonta, yad’an lumshesu sannan yabud’e akanta, hakan yayi daidai da rank’wafowarta zata ajiye masa tiren agabansa, wani nannauyan numfashi ya sauke yayinda idanunsa sukayi tojali da k’irjinta daya bayyana saboda wuyan rigar babbane.
Itakam dabatasan miyakeyiba ta tsiyaya ruwa akofi tad’ago zata bashi, kallo d’aya tayi. Masa ta kauda kai Dan ganin yakafeta da mayun idanunnan nasa masu hasken tsiya.
Ya lashi le6ensa nak’asa tareda kar6ar kofin tamkar wani soko, tana bashi takama hanya zata fice yay saurin damk’e hannunta.
Gabantane yafad’i amma bata juyoba, shima baiyi maganaba hasalima ruwansa yake sha idonsa kuma akan TV dake manne abagon d’akin, sunkai minti uku ahaka sannan ya ajiye kofin hannunsa yadawo da kallonsa kanta, bayanta yakebi dakallo aransa ya ce, “yarinyar tanada sura mai k’yau saidai tacika yarinta….. Mutsu mutsun kwacewa da takeyine yadawo dashi hayyacinsa, yakuma rik’e hannun nata sosai, cikin muryarnan tasa mai sanyin dad’i ya ce, ” jimana.
Maganar tabama Rahma dariya wai jimana saikace Wanda yaga budurwa a hanya, shiru bata juyoba danhaka shikuma yamik’e, haryanzu hannunta yana cikin nasa, yamatso daf da ita hartanajin saukar numfashinsa akan bayanta, tad’an runtse idanunta Dan idanhar bobo yakusanto ta takanji tsigar jikinta tana tashi….
Bata k’are tunanin nataba taji yarungumota ta baya, yazagayo da hannayensa duk biyu saman cikinta, jikintane yakama rawa cikin rawar murya ta ce, “pls kayi hak’uri su khursiyya suna jirana a falo.
Murmushi yayi tareda kawo bakinsa Kusada kunnenta muryarsa tayi low sosai can k’asan mak’oshi ya ce, ” wato su khairiyya sunfi mijinki muhimmanci ko?, yanda yay maganar akunnenta sai duk ta dabarbarce, tajuyo akid’ime, kallo d’aya tamasa gabanta yafad’i, Dan ganin fuskarsa ta canja hartayi d’anja, hakama idanunsa sunyi ja, girgiza kai tayi tana fad’in bafa haka nake nufiba, munayin girkine Dan Nawal takusa dawowa daga school.
Baki yad’an ta6e yana jinjina kai, idonsa akanta ya ce, “aikinga anraba kenan, su khairiyya sukula da Nawal, kekuma ki kula da baban Nawal ko?.
Rahma tak’ara kasa da kanta, shikuma yayi murmushi tareda saka yatsunsa biyu yad’ago ha6arta, lumshe idanunta tayi, shikuma yashiga Raba idanu bisa k’yak’yk’yawar fuskarta, muryarsa ta canja Dan akasalance yake magana, ya ce, ” Abu d’aya zakimin nabarki ki tafi.
Da sauri tabud’e idanunta ta ce, “minene?.
Gira yad’aga mata yana wani kasa k’asa da idanu, kibiya bashin danake binki na kiss, dankinsanfa ni bana mantuwa.
Zaro idanu Rahma tayi, ta marairaice fuska kamar zatayi kuka, Dan ALLAH kayi hak’uri wlhy bazan iyaba.
Yakuma narke murya to saboda mi?.
Inajin kunya.
Kunya kuma?.
” eh”.
Lallai kinada aiki, dole ki shirya zama mara kunya kuwa indai kina taredani, danni mutumne dabayason kauce², sak nake kuma komai nawa sak yake, inaso da sauri shiyyasa nakasance mai sauri, inaso da k’arfin zuciya shiyyasa nakasance mai dakakkiyar zuciya, inayi da yak’ini shiyyasa nakasance mai nasara, inayi da ikilasi shiyyasa ubangijin al’arshi yake taimakona adukkan al’amurana, kizama jaruma sai duniya tasanki, kizama mai gaskiya sai azzalumai suji tsoronki, kizama mai zuciya saiki kasance mai k’arfi, kizama mai hak’uri saiki ganki dayawan riba, kizama mai tunani saikomai naki yazama namasu hikima da k’yak’yk’yawan tunani, Abdulmaleek nakowane amma bakowa bane na Abdulmaleek, ‘yammata karki tsaya kallon ruwa kwad’o yamiki k’afa, kizama mai jarumta dankiyi nasarar maida jiyana da yau da gobena duk suzama naki kekad’ai da ‘yayanmu.
Yana gama fad’ar haka yasumbaci kumatunta tareda sakinta yashige bathroom.
Kamar sokuwa haka Rahma tabishi da kallo harya shige, sai juya maganganunsa takeyi aranta da k’arfin tunani da kwanji, amma kaf tarasa fassara ko guda d’aya aciki, tama rasa inda maganganun suka dosa, takai tsawon minti 6 awajen tsaye amma takasa fasa koda magana d’aya aciki, takuma kasa barin wajen, shikuma har yanzu bai fitoba.
Ahankali tafice tamkar munafuka, tunda tafito su khairiyya kebinta da kallo suna k’unshe dariya, tazauna tana binsu da kallon mamaki, khursiyya tamatso Kusada Rahma tana shinshina jikinta, dariya sosai khursiyya takeyi, Rahma ta ce, “wai miye abin dariya?.
Cikin dariya khursiyya ta ce, ” a’a babu komai nadaiji kinata zuba k’amshin turaren ya Abdulmaleek ne.
Da sauri Rahma ta shinshina kayanta, ilai kuwa kamshin turaren bobo takeyi, da sauri tamik’e tashige cikin kichin, khursiyya da khairiyya suka shek’e da dariya harda tafawa.
Itadai Rahma tana kichin itama dariyar takeyi k’asa², lamarin bobo yana bata mamaki wlhy………….
💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 31
Tana cikin kichin zaune danta kasa fitowa, jitake kamar su khairiyya sunsan miya faru, ihun Nawal ne yasakata fitowa dole, tasaki su khursiyya tanufo Rahma da gudu tarungumeta tana murnar ganinta, tana cikin cire mata uniform bobo yafito sanye cikin farar jallabiya, Shima Nawal taje ta rungumesa, yad’agata sama yana fad’in babyna yaushe kika dawo?.
Papa yanzun nan.
Toya school?.
Lafiya lau my papa.
To masha ALLAH sauka naje masallaci yafad’a yana direta k’asa, ya kalli Rahma datun fitowarsa tayi k’asa da kai, ya ce, “bara naje sallah.
Saika dawo tayi maganar kanta ak’asa.
Baice komaiba yafice.
Yaudai haka Rahma tawuni atakure Dan duk inda tayi idon bobo yana kanta, ko kunyarsu khursiyya bayaji.
Bayan sallar isha’i yashirya zai maidasu khairiyya Nawal tamak’ale wai saitaje, harsun fita yaturo Nawal takira Rahma itama tazo su tafi.
Murna tayi sosai Dan dama tsoro takeji wlhy.
Abaya ta tararda su khursiyya, dole tabud’e gaba tashiga, har Nawal zata shigo gaban ya ce, ” takoma baya, Rahma tadaure ta ce, “pls kabarta muzauna aii zai ishemu.
Baice komaiba yatada motar, saida yafita daga gidan sannan ya ce, ” kina ‘Yar lukutarnan ne kujera d’aya zata isheku?.
Da sauri tajuyo tana kallonsa, amma shiba ita yake kalloba, idonsa nakan titi, d’an harara tamasa tareda murgud’a bakinta…..
Babu zato ya ce, “nikikema murgud’e da harara?.
Kanta tadafe Dan batasan yana kallontaba, aranta ta ce, ” kai mutumin nan ya iya munafikin kallo wlhy, afili kuma ta ce, “nifa ban hararekaba, tak’are maganar da turo baki gaba.
Murmushin gefen baki yayi batareda yace komaiba.
Tunda suka shiga harabar gidan sukai karo da motoci reras, wannan alamace ta basawan gidan duksun zo kenan, shima guri yasamu yay fakin suka fiffito.
Yana gaba suna biye dashi, da sallama suka shiga falon daya k’awatu da haske.
Ya sulaiman ya ishaq ya Hamza duk suna gidan, hannu bobo yashiga basu suna gaisawa, su Rahma ma suka gaishesu tareda hayewa sama Dan gaida Ammi.
Ya Hamza ya ce, ” kace tare kuke gaba d’aya, bobo dake k’ok’arin zama ya ce, “yana iya baby tamak’ale saitazo, nikuma bazan iya barin Rahma ita kad’aiba shine na ce, kawai tataho mu tafi.
Ya ishaq ya ce, ” kai bobo banwani yardaba, kaid’innan baban soyayya.
Murmushi bobo yayi ALLAH Yaya kunyi bala’in sakamin ido agidannan amma babu komai dukzan ramane.
Dariya sukayi gaba d’aya ya sulaiman yad’an daki kafad’ar bobo yana dariya, autan Ammi barsu kaji, sumafa suna soyayyarnan…….
Sakkowar Ammi daga sama ta tsaida dariyar tasu, bobo yarissina ya gaidata, bayan sun gama gaisawa ta ce, “tom kutaso Appan naku yakammala.
Gaba d’aya suka mik’e abin sha’awa da burgewa, cikeda fara’a Appa yatari matasan samarin ‘yayan nasa, suma duk suka zauna suka zagayesa, Ammi ta ce, “to akawo abinci ko?.
Kowa ya CE, ” a’a.
Appa ya hararesu bangane a’a ba, tuni nak’icin abinci saboda nasan zakuzo shine yanzu zakuce wani A’a.
Dariya sukayi sukace to akawo ko kad’an suci.+
Tare sukaci abinci da Appan su, bayan sun kammala sukashiga tattauna abinda yakawosu, dama akan bikinsu Khursiyyane, antsaida sati hud’u kacal, dama shi Appa haka yake saka bikin yaransa bayaso danisa d’innan, anan take suka tsara komai data dace, kowa yad’auki abinda zai iyayi, Appa sai sakamusu albarka yakeyi shida Ammi, daganan hira sukad’an k’ara ta6awa sannan suka mik’e zasu wuce, bobo ya ce, “Ammi ina yarannan muwuce.
Suwaye yara? Ya ishaq yatambayi bobo.
Rahma da Nawal.
Lah matarka kakecema yarinyar? cewar Appa.
Dariya sukayi gaba d’aya, bobo kam murmushi kawai yayi, ya ce, ” Appa yarinyace mana shekarartafa 17.
O Dan shekararta 17 saika ringa cemata yarinya?, to aii yanzu tagirmi wannan sunan, cewar ya Sulaiman.
Bobo yaturo Baki gaba nidai kunga tafiyata saida safe, suduka dariya suka saka harda Appa da Ammi shidai yayi tafiyarsa d’akin Ammi, a can kuwa yasamesu sunata rubuce² itadasu kahiriyya yana shigowa suka 6oye, kallonsu yayi ya ce, “mikuke 6oyewane?.
Babu komai Rahma tayi maganar dasauri tana mik’ewa, yasan basuda gsky amma yayi fitowarsa yak’yalesu, azatonsa ko tsare tsaren biki sukeyi.
Rahma tad’auki Nawal datayi barci, saida taje tagaida Appa tamusi sallama sunata sakamata albarka sannan ta iske bobo aharabar gidan shida sauran ‘yan uwansa.
Mota tashiga tajirashi, bayan sun kammala kowa yashiga mota sai gida.
Tunda suka tafi babu mai magana, daga Rahma har Nawal barci sukeyi, dahakadai suka k’arasa gida, harya kashe motar yafito babu Wanda yamotsa, yaduk’o yana kallonsu Yoshi yanzu yama zaiyi dasu?, d’an tsaki yayi yad’auki Nawal yanufi cikingida, har d’akinsu yakaita ya kwantar bisa gado sannan yadawo, azatonsa zai Tatar Rahma ta tashi amma INA barcinta taketa shek’awa da Alama kuma yanamata dad’i.
Aransa ya ce, ” kegaki orobo amma sai son d’auka.
STORY CONTINUES BELOW

(Nikam bilynku nayi dariya araina, koyaushe tagaya masa tanason d’auka?.)
Itama d’aukarta yayi, yarufe murfin da k’afa sannan yanufi cikingida, sunkusa zuwa k’ofar falin tasak’alo hannayenta awuyansa, kallon fuskarta yayi yaga har yanzu barcinta takeyi, dak’afa yatura k’ofar yashiga, itama yadireta akan gadon, saidai yazo mik’ewa amma tak’i sakar Masa wuya Dan haryanzu hannayenta suna nan asak’ale, tsayawa yayi yana kallon fuskarta dad’an bakinta, sosai yake k’are mata kallo, yana kallonta amma bakamar yau dayake mata kallon k’urullaba, aransa ya ce, “babu laifi yarinyar k’yak’yk’yawace.
Sunkai minti hud’u ahaka, yakai bakinsa kamar zaimata kiss, komi yatuna? saikuma yafasa yad’an kalli gefen da Nawal take kwance, cikin dabara yazare hannanu NATA wai duk ak’ok’arinsa nakar ta tashi, him baisan Rahma dashegen nauyin barciba kenan.
Yacanjama Nawal kayan barci, yatsaya yana tunanin yanda zai canja na Rahma, zama yayi gefen gadon, yasa hannu ahankali yazuge zip d’in rigar atamfar dake jikinta, cikin dabara yasa6ule hannun Riga d’aya, Yakama k’arfen bra d’inta yacire…. Aiikamar ance tafarka tamik’e zumbur, ganinsa zaune kusada ita gakuma rigarta har Anfara cirewa yasakata d’an zaro ido, cikin muryar barci ta ce, ” malam lfy?.
Lafiya k’alau malama yafad’a yana mik’ewa, baijira cewartaba yafice abinsa, itakuma tabishi da kallo tana muci muci da idanu.
Na CE, “humm kwadaiji dashi.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
*_Bayan kwana Biyar_*
🅱🅾🅱🅾 yana kwance yana barcinsa kasancewar weekend ne, sama sama yaji kamar ana wak’ar.
_“happy birthday to you, happy birthday, happy birthday, happy birthday to you…”._
Tashi yayi zaune aransa ya ce, “birthday kuma?, tonawa kenan?, ihun Nawal dayaji yasakashi mik’ewa da sauri yanufo falo.
Tofa, yafad’a yana rik’e k’ugu tareda tsayawa kallon Rahma da Nawal, Rahma tanata zubama Nawal wani Abu mai k’yalk’yali itakuma tana tsale, yabi falon da kallo shima yasha decoration d’in balam balam.
Saikuma wani kati mai k’yau anrubuta…
*_“happy birthday my luvly Nawal, rice 100 may ALLAH bless you abundantly…… I luv yau so much”_*.💝
Murmushi yayi yataka ahankali har zuwa inda suke tsaye, yatura hannayensa duka a aljihu yatsaya yana cigaba da kallonsu.
Nawal ce tagansa, cikin farinciki ta ce, ” my papa today is my birthday.
Murmushi yayi yadurk’usa k’asa tareda bud’e mata hannayensa, tazo tashige ya rungumeta, sorry my habibaty gaba d’aya namanta yau birthday d’inki, amma kigodema ALLAH daya baki momy tagari d’iyata, wannan yak’ara nunamin baki tareda maraicin rashin uwa, wasu ‘yan hawaye suka mak’ale masa agefen ido.
Jiyayi ana goge masa, yad’ago ido yana kallonta, dasauri tamatsa baya saboda kunya, yayi murmushi tareda mik’ewa tsaye shida Nawal, k’arasawa yayi inda Rahma take daf da ita tamkar zai shige jikinta, cikin wata sassanyar murya yace my Cute ngd sosai ALLAH yabaki lada mai tarin yawa, ALLAH yakaimu ranarda zaki haifamin k’annen Nawal agidannan……
Da sauri tad’ago takalleshi, yad’aga mata gira… Aii saita shek’a da gudu tabar waje, tabashi dariya sosai Dan haka ya murmusa.
Nawal ta ce, “papa miyasa momy tagudu?.
Murmushi yayimata ya ce, ” babu komai, jeki tashiryaki yau yawo zamuje tunda ba’a shiya miki wani bikiba.
Sosai Nawal take tsalle za’a yawo.
Bayan kamar minti30 Rahma tagama shirya Nawal cikin kaya masu k’yau, falo suka fito suna jiran boss, babu dad’ewa shima yafito cikin k’ananun kaya, sunbala’in MASA k’yau sai zabga k’amshi yakeyi.
Rahma ta ce, “masha ALLAH, ALLAH yayi halitta awajennan, duk azuciya take maganar shiyyasa harya k’araso kusada ita bata saniba.
Namiki k’yaune?, yay maganar acikin kunnenta.
Da sauri tad’ago tad’an murmusa tana jinjina masa kai tareda rufe fuskarta da tafin hannu.
Shima murmushin yayi, yakuma fad’in aiini nakine ‘yammata, kiyyiata kallona harki gaji.
K’ara rufe fuskarta tayi Dan maganganunsa kunya suke bata, kutashi mutafi time nadad’a k’urewa.
A’a kuje kaida Nawal ni akwai abinda zanyine.
d’an harararta yayi ya ce, ” ban ganeba?.
Rahma ta marairaice tamkar zatayi kuka, ALLAH akwai abida zanyi, gobe idan ALLAH ya kaimu masake fita tare.
Baice komaiba danyaji haushi, azatonsa batason zuwane kawai, Dan haka yakama hannun Nawal afusace suka fice daga falon.
Binsu da kallo Rahma tayi tana murmushi, ta ce, “ayya dadyn Nawal kayi fushine?, saikuma ta jinjina kai ta ce, ” zaka huce idan kadawo kaga miya tsaidani.
Bobo sai zagayawa da Nawal yake wajajen shak’atawa na musamman, duk inda suka giftta sai an kallesu kuma sai an k’yasa bobo Wanda in ba kasaniba bazakace d’iyarsa bace Nawal, zaka d’auka irin d’iyar yayansace kokuma k’aramar k’anwarsa, bakowa yake yarda bobo yata6ama aureba bare akai ga haihuwa.
‘Yammata marasa hak’uri kam har magana suke masa, wasukuma suyima Nawal kodan yatanka, amma ko kallo basu isheshibama.
A6angaren Rahma kam suna fita babu dad’ewa saiga Khursiyya da khairiyya sun iso damasu decoration, nandanan aka share harabar gidan suka fara aikinsu, tsaf suka gyara ko ina yad’auki k’yau, suka jere kayan kid’ansu..
Haba zuwa k’arfe biyu ai gida yafara cika da yara, matansu ya sulaiman da yaransu duksun iso, tare suketa hidimar had’a abinci, ga kayan rabonan ank’ukkula, zuwa k’arfe hud’u duk Wanda suka gayyata ya iso gidan.
Awannan lokacin kuma bobo da nawal suna can sun lodo kaya daya sayama Nawal sun kamo hanyar dawowa gidan, dukda abinda Rahma ta masa da safe saiyaji baiji haushintaba sosai, tun awaje yakebin motocin da akayi fakin awaje da kallo, aransa ya ce, “k’ila wani gidanne a anguwar sukayi bak’i, yay hon maigadi yalek’o, ganin shine yasa yak’araso wajen mortar batareda yabud’e masa gate ba.
A’a yabaka bud’emin gate ba kuma?.
Aii oga wlhy babu wajen fakinne aciki.
Kamar ya babu wajen parking?, mike faruwa acikin Gidan?.
Mai gadi yad’an Sosa kai Dan Rahma ta ce, ” karya fad’a masa, ya ce, “saidai kashigo kagani oga.
Bobo yagirgiza kai kawai batareda ya tankaba yanemi waje awaje yay fakin suka fito shida Nawal, wayoyinsa kawai yad’auka amotar Yakama hannun Nawal suka nufi cikin gidan, bin ko ina yake da kallon mamaki yajinjina kai tareda nufar cikin gidan, suka shiga falon nanma shiru babu alamar akwai mutane awajen, baigama tunanin mike faruwaba yaji yara suna tafi dafad’in.
*_“happy happy birthday to you, happy happy birthday to you…… Saikuma gasu Rahma suma sun fito”._*
Aibaisan sanda yasaki lallausan murmushiba, dama abinda Rahma tashirya kenan shiyasa tak’i binsu?, jiyayai tak’ara girma da daraja azuciyarta. lol
Na ce, ” hummm gaba gabadan bobon Appa.
————————
Daganan aka shirya Nawal cikin kaya masu k’yau, shima ogan kwalliya yakuma ci, aka fara gudanar da biking birthday d’in Nawal.
Masha ALLAH komai ya k’ayatar abin burgewa.
Wajen bada cake Nawal tacuro tasakama babanta tasakama Rahma, tabi sauran iyayen matansu ya hamza dukta basu, su khairiyyama haka, daganan aka fara cashiya.
Biki dai bai tashiba sai gab da sallar magriba.
Masu tafiya suka tattafi, akabar yaransu ya hamza kawai da matansu, bayan isha’i suma mazansu suka iso, saida sukaci sukasha akasha hirara zuminci sannan kowa ya kwashi family nasa sai gida.
Bobo ya tsarama kansa wani Abu yau, amma saiyaji wai agidan su khursiyya zasu kwana, ba k’aramin haushi abin yabashiba amma saiya dake tunda bashida yanda zaiyi.
_bayan kwana hud’u_
Duk burin da bobo yaci akan Rahma ya rushe Dan har sannan su kursiyya suna gidan, doledai yad’aga k’afa.
Ranar Litinin da safe su khursiyya suka koma gida abinsu, shima bobo yafita aiki, Nawal kuma tana makaranta sai Rahma kawai agidan.
Tayi aikinta tagama komai tsaf, 1:30pm tana zaune afalo tana kallo wayarta tayi wringing da sauri ta kalli wayar bak’uwar no. ce, shiru tayi Dan yau tunda tatashi gabanta ke fad’uwa, har wayar ta yanke bata d’agaba aka sake kira, ganin babu dacewa arashin d’aukar yasa ta d’auka tunda batasan ko wayeba.
Sassanyar muryarsa tadaki kunnenta, ta sauke ajiyar zuciya wadda yajita har yatsan kafarsa, yad’an lumshe idanunsa yabud’e tareda jingina da kujerarsa, ahankali yake d’an lulita, ya ce, ”matsoraciya da kinzata waye to?.
Murmushi tayi ta ce, “nifa ba tsoro najiba, baki yata6e tamkar yana gabanta ya ce, ” dama zancemikine kid’aukko babynki a school yau aiki yamin yawa a office bazan samu damar d’akkotaba.
Okey babu damuwa.
So zaki iya deriving d’in ko?.
Eh zan iya.
Okey tom ALLAH ya tsare, saina sake kira…….
d’if ya kashe kafin tayi magana, murmushi tayi kawai tamik’e tacanja kayanta.
d’akinsa tashiga Dan key d’in motarta yana hannunsa, tagama dube dubenta bata ganiba, sai wani na jar motarsa a durowar gefen gadon, shita d’auka tafito.
Tashiga motar daketa tashin k’amshi, tana mamakin turaren da Bobo yake amfani dashi haka, komai nashi Yakama k’amshin turarensa, mai gadi yabud’e mata gate tafice.
Tafiya take ahankali saidai wani Abu mai kama da tsoro yana ta6a zuciyarta Dan tunda tafito daga gida take gani kamar wata bak’ar mota nabinta abaya, ajiyar zuciya tayi dataga motar kamar ta6ace, dahakadai tak’arasa makarantar su Nawal ta d’akkota.
Labarin makaranta Nawal keta bata, amma itafa hankalinta yafara tashi Dan yanzuma k’ara ganin motar d’azu takeyi.
Sunzo daidai danja ta rik’esu saikawai taga anbud’e motarsu anshigo, atsorace takalli bayanta saitaga wasu zaratan samari majiya k’arfi zaune tamkar motar gidansu, d’aya yanunata da bindiga, d’ayan kuma yatoshe bakin Nawal.
ga Motar bak’in Gilas ce, nawaje baya ganin naciki……………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 32
Babu dad’ewa aka basu hannu, tuni jikin Rahma yajik’e da gumi dukda AC dake aiki amotar, jikinta sairawa yakeyi, duk addu’ar datazo bakinta karantawa takeyi.
Dakansu suke nuna mata hanyar dazatabi, sunyi nisa sosai datafiya awata hanyar k’auyen da Rahma batasan ko inaneba, wayartace tayi wringing harzata d’auka Wanda yake rik’e da bindiga yadaka mata tsawa, kina d’agawa zan tarwatsa kanki.
Janye hannunta tayi da sauri akan wayar, Wanda yake rik’eda Nawal ne yad’auki wayar, saidai kafin yad’aga ta katse, wata uwar dariya yashek’e da ita Dan ganin sunan daya kira Rahman, *_dadyn Nawal_*.
Wani gida suka kaisu, zuwa sannan Nawal tayi barci, Dan sun shak’a mata wani abune, Rahma tarungume Nawal tana kuka maiban tausayi, aranta tana tunanin misukayima wad’an nan mutane dazasu kawosu nan??.+
Bobo kam hankalinsa yafara tashi Dan ganin yayima Rahma kira wajen 10+ amma bata d’agaba, dukda d’umbin aikin dake gabansa haka ya tureshi yabaro office d’in.
Makarantar su Nawal yafara zuwa, auntyn su ta ce, “aii tund’azu bayan yakira kamar yanda ya ce, ” momynta ce tazo ta d’auketa, to babu dad’ewa tazo ta d’auketa…..
Bai tsaya yagama saurarentaba yayo waje, daga nan gidansa yanufa, tun a gate yatambayi mai gadi, amma ya ce, “basu dawoba.
Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un kawai yake ammabata azuciyarsa, amma dukya birkice, da sauri yaciro wayarsa a aljihu yakira khursiyya, itama ta ce, ” basu zoba, Abu kamar wasa dukya rewad’e dangi dakira amma kowa amsa d’aya yake bashi *_basu zoba_*.
Cikin rawar jiki yakira Appa yaturo masa number Abbansu Rahma.
Cikin girmamawa ya gaidashi, tareda masa bayanin shine, Abba ya ce, “ALLAH sarki Abdulmaleek ngd ALLAH yayimaka albarka, ya su Rahma d’in?. Tun anan jikin bobo yayi sanyi, murya asark’e ya ce, ” dama ita zantanbaya ko sunzo nan gidan?.
Kai A’a gsky Rahma batazoba, kunyi da’ita zatazone?.
A’a Abba dama…… Nan yafad’a masa yanda akayi.
Abba yaja numfashi, to mud’an k’ara hak’iri zuwa d’an anjima mugani kota biya wani wajen, dukda dai nasan wannan baya d’aya daga cikin halayen Rahma, tabbas da Safna cema bazan damuba Dan nasan tanada rawarkai, amma Rahma kam batada wannan halin.
To abba. Kawai bobo yafad’a ya yanke wayar, kuma kiran Number Rahma yayi amma ank’i d’auka, yadafe Kansas tamkar zai FASA ihu, yana nan tsaye ak’ofar gate saiga ya ishaq da ya Hamza, suka tambayi yanda akayi yasanar dasu.
Ya hamza ya ce, “kasanarda Ammar ne?.”
Girgiza kai kawai bobo yayi danya kasa magana, ya Hamza yakira Ammar yayamasa bayanin kimai, salati ammar yashiga yi, bai tsaya 6ata lokaciba yabaza yaransa ki ina.
Al’amarifa kamar wasa hardare babu wani bayani, zuwa yanzun labari yakarad’e dangi, bobo kam dukya fita hayyacinsa, sai kuka yake tamkar mace, shidama haka yake akwai jarumta amma Abu kad’anne ke karya azuciyarsa.
Duksun dawo daga sallar isha’i, suna zaune afalo gidan Appa zugum², harda Abban Rahma da Umminsu, momyn ya Kamal da dad d’insu Ameera ihsan ya Muneer ya shaheed duk suna gidan Appa, Safna CE kawai babu, dantana makaranta abin yafaru, bayan tadawo mai gadi yashaida mata komai, yad’ora da fad’in ‘yangidanma duk suna gidan surukan Rahma d’in.
Safna ta ta6e Baki ta ce, ” kaga baba bud’emin gate nashiga nahuta tukunna, Dan bazan iya zaman jigum jigum ba wlhy tunda ba mutuwa akace sunyiba.
Maganar tata tarazana baba mai gadi, bayan yabud’e mata gate yabi mortar da kallo yana jin kina kai, aransa ya ce, “lallai yau nakuma shaidawa yarinyarnan batada mutumci ko kad’an, inbanda rashin mutumci d’an uwanka uwa d’aya uba d’aya ya6ata kanuna rashin damuwarka, kai ALLAH dai ya k’yauta to.
Safna dai bamatasan yanayiba Dan tuni tashige cikin gida abinta, sai wata fara’a takeyi wadda nadad’e ban ganiba daga gareta.
🤔araina Na ce, ” safna Kodai kidai??.
*_3days_*
Tsawon kwana uku kenan da 6atansu Rahma, Abu tamkar wasa, zuwa yanzu kam aii kowa yajigata, Appa yabaza rok’on ALLAH amasallatai, hakama gidan redio Dana TV, social media ma haka, amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa, kuma tun ranar ba’a sake samun number Rahma ba.
ALLAH sarki bobo acikin kwana ukunnan Yayi wata uwar Rama, ko abinci bayasonci sai ammi ta tsareshi tamkar yaro tabashi abaki, shima lauma hud’u zuwa Biyar zaice yak’oshi, saitata lalashinsa sannan zaiyarda yak’ara kad’an.
STORY CONTINUES BELOW

Nikaina yabani tausayi k’warai da gsk😥.
Yanzuma suna zaune afalo Ammi tana lalla6ashin sa akan yasha shayi amma sai yatsine baki yakeyi, ya mararairaice murya tamkar zaiyi kuka, ALLAH Ammi nak’oshi.
A’a mukarram kadaure kasha koda kad’anne, kaga rabonka da abinci tun jiya da yammafa, komai na rayuwa hak’uri yakeso, Addu’a suke buk’ata daga garemu kaji, ALLAH ya ku6tar mana dasu idan suna Raye.
Hawaye suka ziraro bisa kumatunsa, Ammi ta share masa..
Yana shirin yin magana sukaji sallmar ammar, suka amsa, yashigo ya zauna.
Ammi yarissina yagaida sannan yabama bobo hannu suka gaisa🤝, cikeda tausayi Ammar yake kallon bobo.
Ka kwantar da hankalinka Abdulmaleek insha ALLAHU za’a gansu, yanzu inaso naji time d’in Daka kira Rahma kafin tatafi d’aukar Nawal?.
Wayoyinsa yakwaso dukya yamik’ama Ammar Dan yanzun bayason yawanyin magana sosai.
Bincike sosai Ammar yakeyi a wayoyin Bobo yanayi yana waya da office d’insu, bayan sun kammala yabama bobo wayoyinsa, ya ce, “kabar wayiyinka akunne daga yanzun Duk Wanda yakiraka zamu gani, zakuma mu iyabi ta wannan hanyar dangano ko waye.
Jinjina kai kawai bobo yayi batareda yayi maganaba.
Ammi ta ce, ” Ammar karinga yima abokinka fad’a yaringa cin abinci jibifa yanda yaketa ramewa.
Ammar ya ce, “kik’ara hak’uri Ammi insha ALLAHU zai ringaci yanzu yana cikin rud’anine.
To ALLAH yasa Ammi tafad’a tana mik’ewa tabasu waje.
Haka Ammar yatsare bobo yad’ansha shayin da soyayyen dankalin sannan yaymasa sallama yatafi.
Tafiyar Amma babu dad’ewa saigasu ya Hamza sudukansu.
Guri suka samu suka zauna suna k’ara kwantarma da bobo hankali, yana kwance saman doguwar kujera yana jinsu, badai ya iya cemusu komai amma sunsan yana saurarensu, wayar bobo tafara wringing yayi burus da ita tamkar baijiba harta tsinke aka sake kira, ya ishaq ya ce, “kad’auka mana, 6ata fuska yayi tamkar zaiyi kuka amma baice komaiba, ganin wayar tana niyyar tsinkewa ya sulaiman yay saurin d’auka ya ce, ” hello.
Muryar data daki kunnensa CE tasakashi mik’ewa zumbur yana fad’in Rahma Rahma……. Kuna ina ne?…..miya faru daku?……..
Aiikafin yafarga bobo ya warce wayar, muryarsa har rawa take ya ce, “Rahma Ku……..
Bai k’arasaba wata muryar takatseshi da fad’in ba ita bace ta cancanta tabaku amsar tambayoyinku mine nan.
Ku suwaye!!!?, Bobo yay maganar Afusace.
Daga canma aka Daka masa tsawa, kai malam karka d’aga mana murya.
Bobo ya ce, ” kaga bawannan bane damuwata, miyasa kuka kamamin matana da d’iyata?, misuka muku?, waye yasakaku?, mukuke buk’ata?, idan kud’ine kufad’i konawane za’a Baku, pls karku cutar dasu.
A’a a’a muba kud’i muke buk’ataba domin anrigaya an biyamu, kai kanka muke buk’ata, inkuwa bakazoba tom ran ‘yarka da matarka zaizama fansar ranka amaimakonka.
Bobo yarintse idonsa tareda cije le6ensa, saboda 6acin rai yagaza cewa komai.
Daga can akace haba zaki kardai ace ka tsorata?, hhhhhhhh, bai kamata kaji tsoroba, munbaka daganan zuwa jibi idan bakazoba tom zaka tsinci gawar matarka da ‘yarka, idan kuma kana buk’atarsu darai tom fine sai ka fanshi ransu.
Saidai zuwan naka yanada sharad’i, wlhy koda wasa kada kayi gangancin zuwa da police zamu gane, na biyu saika taho zamu ringa fad’a maka hanya,, na uku idan ka 6ata mana lokaci zamu kacaccala matarka da ‘yarka mu watsar, gashi kasakejin muryarta.
Kafin bobo ya ce, “wani Abu saiyaji muryar Rahma cikin kuka tana fad’in dadyn Nawal karkazo pls, Dan ALLAH karka bada ranka akanmu, insha ALLAHU zanfanshi rayuwarku dagakai har Nawal, Nawal tana buk’atar mahaifi tunda tarasa uwa pls karka salwantar mata da ranka, Dan girman ALLAH karkazo, I luv you so much my Abdulmaleek.
I luv you too my cute Rahma na, bobo yafad’a da saurin Baki,….kafin yakuma cewa wani Abu suka kwace wayar, cikin k’araji sukace kai wawa harka samu damar yimana soyayyane??.
Wlhy kacika mana baki sai munmata fad’e hhhhhhhhhh dama gata daga gani zata bada feeling.
Kaiiiiii!!!!!!!!!! Wawa, Bobo yadaka masa tsawa, wlhy kabari zuciyarka takuma kissima maka wani Abu akan matata saina tarwatsa kanka da bullet, na rantse maka da ALLAHn daya halicceni saina shayar dakai gidauniyar azaba, tabbas ni *_Zakine_* kujira zuwan zaki gareku, saina lak’umeku!!!!!!!!!, yanda yayi maganar cikin tsawa harsu ya ishaq da Ammi Appa su khursiyya duksun tsorata da yanayinsa, gabad’aya jikinsa yayi jajur abinka da fari, gashi jikinsa dukya mimmk’e, hakama jijiyoyinsa duksunyi rud’u², yay jifa da wayar, da sauri ya Hamza ya cafeta.
Kowa yasan kuma ransa ya6aci kenan, k’arasawa yayi gaban Appa da Ammi yana yawaye ya ce, “iyayena kusamin Albarka zanje nataho dasu yanzun nan da kaina.
Yanda yake magana dukya basu tsoro da tausayi, Ammi ta ce, ” mukarram kayi hak’uri Ammar yazo kutafi tare, kai yagirgiza mata ya ce, “Ammi kedai sakamin Albarka kawai, basu musaba suka dafa kansa tareda saka masa Albarka da k’yak’yk’awar addu’a.
Ya mik’e afusace zai fice, ya sulaiman yay saurin shan gabansa, wata irin hankad’awa bobo yayma ya sulaiman yay taga taga zai fad’i ALLAH yasoshi ya ishaq nakusa yarik’eshi yafad’o jikinsa.
Bobo kam kota kansu baibiba yayo waje, yana fitowa ammar yashigo gidan, da sauri yatsayar da bobo, badan yasoba yatsaya yana kallon ammar dayaci wanka cikin shadda harda babbar Riga, wani d’an guntun tsaki bobo yayi danshi Ammar d’in yabashi haushin kwalliyar dayayi.
Ammar baice masa komaiba yamik’o masa babbar Riga ta shadda.
Galala bobo yatsaya kallon Ammar, wannanfa? yafad’a yana huro hanci.
Kaga kasaka mutafi, Dan mungano Inda suke tasanadin wayar dakukayi yanzu, kasandai babu yanda za’ayi muje kai tsaye dole saimun canja kama gudun karsu San da zuwanmu su cutar dasu.
Bobo yanajin haka yakar6i babbar rigar shaddar yasaka shima harda hula, duk abinda ke faruwa su Appa Ammi ya sulaiman ya ishaq ya Hamza khursiyya khairiyya duksun futo sunajinsu.
Appa ya ce, ” ALLAH yayi muku Albarka yayi taimako.
Amin suka amsa.
Bobo da Ammar dawasu police uku suka shiga mota d’aya, su ya ishaq ma mota d’aya, saikuma mota biyu itama duk police ne aciki amma da kayangida Dan kowa shadda yaci tamkar zasu d’aurin aure, ganin haka shima Appa saiya shiga motar su ya Hamza, su khursiyya sukace zasuje suma, AMMAR ya ce, “suyi hak’uri su zauna suyi ta musu addu’a.
Ammi ma kuka takeyi, hakadai suka fice.
Amota Ammar yake sanarma bobo yatura mutane biyu amashin dansuyi gaba.
Jinjina kai bobo yayi Dan har yanzun ransa a6ace yake Musamman idan yatuno da maganar wawan nan wai Rahmar sa zata bada feeling, wlhy saiya cirema d’an iskannan hak’ora….
Da sauri yashige cikin wata gona ya6oye bayan bishiya, boss gafa wasu motocinan har guda hud’u suna zuwa.
Akwai motar ‘yan sandane?.
A’a gskiya wad’annanma duk wankan shadda sukayi.
Mtsoooww kaiwane irin wawane, bana gayamaka akwai wani d’aurin aure daza’ayi acikin k’yauyen damuke ba, na tabbata wannan d’aurin auren sukazo, angayamaka su wawayene dazasu taho tun yanzu?, ko ka manta yanzu muka gama waya dashi?, nasan saisunyi shiri sosai kafin su ce zasuyi gigin zuwa, tabbas nasan zuwa gobe saisunzo nan Dan haka karka damu da wad’annan motocin.
Okey boss nafahimta, yafad’a yana gyad’a kai tamkar k’adan gare.
Yana yanke wayar yaji anshak’eshi tabaya, ido ya zazzaro waje Dan mamaki, shikuma wannan daga ina haka? Yaya maganar azuciyarsa.
Wani wawan naushi musaddiq yabama guy d’in tareda k’ar6e wayar, a ina suke?, musaddiq yatambaya yana k’ara shak’eshi.
Zan zan zan fad’amaka kaga sakeni Dan ALLAH karka kasheni.
Wani wawan mari yasake bashi, fad’amin ahaka, cikin Rawar baki yasanarma musaddiq, shikuma yakira su Ammar yafad’a musu.
Musaddiq yakuma fad’in kunawane aka baza Dan kawo rahoton zuwanmu?.
Mu mu mu mu goma shabiyar ne.
Murmushi musaddiq yayi, yad’auki waya yakira sauran ‘yan uwansa yace su bazu akwai sauran mutum goma sha hud’u.
_(ALLAH sarki musaddiq bayan Ammar yaturosu amashin su biyu, sunyi shiga k’auye kamar ‘yan k’auyen gsk, shikuma yazagaye yakuma samun ‘yansanda goma suka taho batareda sanin Ammarba, shine yanzu yakira su dansu bazu adajin)._
Su bobo kam sunatabin hanyar kamar yanda waya take nuna musu, suna zuwa daidai wani wajen mararraba wayar tatsaya wannan alamune na sun iso wajen.
Mutum biyune suka fito suka k’arasa ga wani matashin saurayi dake tsaye yana kallonsu, da alama shima yana cikin mutum 15 da’aka baza Dan kawo rahoto, Dan kallo d’aya Ammar yay masa yagane bashida gsky.
d’an saurayi Dan ALLAH tambaya Muke?.
ALLAH yasa nasani yay maganar yanata zazzare idanu.
Wani hanyar k’auye muke nema da ake d’aurin aure.
Ajiyar zuciya saurayin yayi tareda wale baki, ya ce, “to to zan nuna muku, yana motsawa danufin nuna musu hanya d’ansanda d’aya yanuna masa bindiga, kana motasa zan tarwatsa kanka, ina kuke 6oye dasu?.
Yawu saurayi ya had’iye ya ce, ” zan nuna muku yanzun nan….
K’asa yay da bindigar yanda baza’a ganeba yatasashi gaba, suma su bobo suka fiffito, amma sun rarrabu.
Su Rahma suna zaune tana rungume da Nawal suka farajin k’arar harbin bindiga, da sauri takali Wanda yake tsaronsu, duk taron ‘yan iskannan shikad’aine mai bindiga ahannu, ganin yana barci Dan tund’azu yake lodama cikinsa wuywuy, mik’ar da Nawal tayi ahankali daga jikinta, cikin sand’a tak’arasa inda yake him akujera zaune, tamik’a hannu ahankali zata d’auki bindigar saiya motsa, tayi saurin ja baya tamak’ale ajikin bango, zamansa yagyara yakoma barci, takuma kai hannu zata d’auka Nawal ta ce, “mo…… Da sauri Rahma tayi mata alamar tayi shiru, lek’awa tayi ta window saita hango k’artai biyu suna zuwa aguje, takuma hangawa d’ayan gefen ta hango uku, innalillahi tashiga ambata dantasan yau saidai ALLAH kam.
Hannun Nawal takama da sauri suka shige bayin d’akin taisaurin buga k’ofar tarufe dak’yar….
Adaidai lokacin ogan yafarka yamik’e zumbur yanufi hanyar bayi, shigowar yaransa biyu da gudune yadakatar dashi.. Oga oga wlhy ‘yan sandane……
Basu k’arasaba sauran ukun suka k’araso suma, ‘yansanda wajen hud’u suna take musu baya, harbi ogan yayi, yasamu d’ansanda d’aya ak’afa, suma suka fara harbi, nanfa aka fara musayar wuta, suma ‘yan sandan suka samu nasarar Harbin mutum d’aya acikin ‘yan iskan.
Ana cikin haka bobo yak’aso wajen, tuni duk sun cire Babar riga, bullet yak’arewa oga, ‘yan sanda biyu kuma sun sami harbi, ga yaran oga sun k’aru Ashe sunada yawa, danbe aka fara tsakanin bobo dasu dansu Ammar sunacan nesa da wajen shikad’aine saikuma ‘yan sanda biyu anharbi biyu.
Hummm masu karatu yaufa inashan kallo😳.
Dukan juna sukeyi sosai Dan suma gardawane majiya k’arfi babu abinda bobo zai nuna musu, gashi sunfisu yawa, sun daki juna duksun galabaita, kowa yaji ciwo sai sukaji k’arar harbi, gaba d’aya suka juyo Dan ganin Wanda yay harbi daga cikin d’akin, Rahma ce tsaye abakin k’ofa ta harbi Wanda yake k’ok’arin sokama bobo wuk’a ta baya, shikuma yana can hankalinsa nakan ogansu dasuke cin uban juna.
Gaba d’aya sukayo kanta, ALLAH yabata sa’a takuma harbin wani ak’afa shima yazube, gani suka itama anyi kutubal da ita tadaki bango goshinta yafashe yafara jini.
Adaidainan su Ammar suka k’araso da sauran gayyar ‘yan sandan, dakuma ‘yan dabar da aka kamo.
Hankad’a Rahma musaddiq yayi da sauri Dan hango Wanda yabugata da bango yayo harbi.
Fiyyyy bullet d’in yawuce tagefen hannunta, harya d’an ta6ata, tayi taga taga zata fad’i ya ishaq yay nasar rik’e hannunta.
Gaba d’aya anyi nasarar kamasu, Nawal tafito dagudu daga inda Rahma tasakata ta 6oye, bobo yadurk’ushe k’asa tareda bud’e mata hannunsa tafad’a jikinsa, yarungumeta tsam yana hawaye.
Papa yaushe kukazo?, wad’annan mutanen sunata dukan momyna, papa niko inata kuka ina kiranka, momyna ta ce, “su kasheta subarka da rai, kuma tana hana su dakeni..
Kowa kallonsu yakeyi cike da tausayi, bobo yad’ago ido yana kallon Rahma dake tsaye agefe itama tana kallonsu tana hawaye, murmushi yayi mata tareda mik’ewa tsaye, yaware mata hannayensa alamar itama tazo……………..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 33
Kafad’a ta d’an nok’e tana girgiza kai dantanajin kunyar mutanen dake wajen.
Tayi k’asa da kanta tana kallon k’asa, bata ankaraba taji an rungumeta, ahankali tasauke ajiyar zuciya, shima ajiyar zuciyar ya sauke, cikin kunnenta ya ce, “haba my cute bakiyi missing d’inaba ko?.
Batace komaiba saidai yanajin alamar murmushin datakeyi.
Ya sumbaci wuyanta, Ya hamzane dayaga bobo na Neman ruftawa gakuma Appa awajen sai ya k’araso inda suke, ya ce, ” baban soyayya kuzo muje gida saikuyi ko?.
Da sauri Rahma tazare jikinta, bobo yad’an kalleta sannan yadawo da kallonsa ga ya Hamza, Yaya karfa kazama….. Hummm kodayake baradai nayi shiru kawai.
Dariya ya Hamza yayi ya ce, “a’a fad’i karta kasheka.
Um um bazan fad’aba narufa maka asiri dai, my cute kona fad’a miki?.
Girgiza kai Rahma tayi tana murmushi.
Ya Hamza ya ce, ” karki damu Rahma cemasa yafad’a mana, nima saina tona aii yanzunnan.
‘Yar dariya bobo yayi Yakama hannun Rahma suka tafi, ya Hamza yabiyosu abaya suka tafi.
Yanzun ya Hamza da bobo da Rahma amota d’aya suka tafi, Nawal kam tana wajen Appa, tunda bobo yarungume Rahma Appa yakama hannun Nawal sukabar wajen yana murmushi.+
Suna zuwa gida asibiti aka wuce dasu Rahma, Alhamdllh babu wata matsala saidai ‘yan raunukan da Rahma taji, ya sulaiman ya dubata tareda basu magunguna sai gida.
Tunkan su iso gidan yacika da dangi, su Rahma suna shigowa dangi suka rungumesu anata kuka, bayan gama murnar ganin juna Rahma tashige d’akinta tayi wanka tayima Nawal.
Aka kawo musu abinci sukaci sukasha magani sai barci.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Haba ummi yazakice bandamu da 6atan su Rahma ba?, ‘Yar uwatace fa, Dan ALLAH kibar fad’a kadama wani yaji zata gskyne.
Oh da k’yarya nakeyi?.
A’a ummi nidai bance kina k’aryabafa.
Banza ummi tayi da ita, tajuya zata fita.
Safna ta marairaice murya ummi toyanzu mikikeso nayi dazai sakaki farinciki?.
Kafin ummi tabata amsa sukaji sallamar baseera.
Tarisina ta gaida ummi, cikin fara’a ta amsa sannan tafice.
Ummi na fita basira tamatso Kusada safna, k’awata mike faruwane wai naga ummi akanki?.
Mtsoooww kibari kawai akan 6atan Rahma ne…….. Takwashe komai tafad’a mata.
Baseera tazunguri safna kefa banzace miyasa bazakice zakije kizauna da ita harta samu lfy ba, daganan basaiki gwada sa’arkiba kema.
Kai hakanefa baseera, wlhy banyi wannan tunaninba ma, duk kaina yakulle baya kawo wuta.
Aikin 6urrr inji tusa, kinga tashi maza ki shirya.
Gudu gudu sauri Sauri safna tashirya kayan dazasukai fiye da sati d’aya, tad’auki duk abinda zata buk’ata ta shirya sanan sukanufi d’akin ummi.
Tana zaune da Alana tana wayane da wata ‘Yar uwar tata Dan tana bata labarin 6atan Rahma dakuma dawowarsu yau.
Tsayawa sukayi harta gama, takalli safna da akwatin kekuma INA zaki da kaya haka?.
Ummi zanje gidan Rahma na zauna danna ringa taimaka mata har jikinta ya daidaita, naga baikamata ace anbarta da dangin mijiba tamkar batada kowa.
Baki ummi ta washe ta ce, “kai naji dad’i wlhy safna ALLAH yayimiki albarka, aihaka akeso, kuma tahakane zuminci ke k’ara dank’o.
Ki gaisheta muma insha ALLAHU gobe zamuzo mu dubasu.
ALLAH yakaimu ummi, saikunzo safna tafad’a tana murmushi.
To saimunzo, baseera kigaida mutanen gidan.
To ummi zasuji.
Safna da baseera suka fito sai gidansu Rahma, sanda suka iso mutane duksun tafi, daga Ammi da inna sai khairiyya da khursiyya suka rage, har k’asa su safna suka durk’usa suka gaida su Ammi.
Safna ta ce, ” Ammi inasu Rahman?.
Murmushi Ammi tayi ta ce, “aii har yanzu barci sukeyi safna, yawajen su Maman taku?.
Lfy lau suke Ammi, suma saigobe idan ALLAH yakaimu zasuzo.
To ALLAH yakaimu lfy.
Inazaku haka da akwati? Ammi tayi tambayar tana kallon safna.
Safna tagyara zamanta tana k’ara marairaice fuska tamkar mutuniyar kirki, Ammi dama canayi bara nazo na zauna da ita harta samu k’arfin jikinta, Dan baikamata atakura su khairiyyaba ga bikinsu yana matsowa.
Murmushi Ammi tayi ta ce, ” lallai kinyi tunani Safna, ALLAH yay miki albarka.
Bobo dake bakin k’ofar Rahma yana niyayyar fitowa yatsaya sauraren tattaunawar Ammi da safna.
Ransa a 6ace yakalli Ammi suka had’a ido, yaturo baki gaba, murmushi Ammi tamasa tareda yimasa magana da idanu, wai karyace komai.
Kauda kai yayi yana d’an sassauta turo bakinsa, shifa wlhy yatsani yarinyarnan, amma shine yanzu za’ace tazauna taredasu mtsoooww yaja siririn tsaki.
Takowa yayi ahankali zuwa cikin falon, jin k’amshinsa da takunsa yasaka safna da baseera juyowa, kan ubancan kai, aii ba safnaba har baseera yau saida tashiga rud’ani.
Dukda yad’an rame amma k’yawun haibarsa na nan, kuma yak’ara haske sajennan yakwanta luf luf, sai k’amshin turarensa ketashi afalon mai sanyin dad’i, har yazauna Kusada Ammi idon baseera da safna na Kansa, baseera ta ce, “a ranta lallai dolene safna ta haukace,” Ashe haka guy d’in ya had’u masha ALLAHU.
Bobo yay d’an guntun tsaki Dan baya son kallo, ganin bazasu daina kallonsaba shikuma sun gundureshi, saiya katsesu dafad’in yakuke?.
Dandanan suka dawo hayyacinsu danjin saukar muryarsa mai ratsa jiki da 6argo.
Cikin in ina suka gaisheshi, ya amsa da lfy, tamkar yanda yasaba.
Khursiyya da khairiyya suka fito saga kichin bobo ya kallesu, harkun mammala abincin?.
Ya Abdulmaleek ai yau abinda kafiso muka dafa zakacidai ko?.
Murmushi yamusu tareda gyad’a kai kawai.
Suma dariyar sukayi suna mai farincikin ganin yayansu yau acikin farinciki, khairiyya ta CE, ” Yaya tunda aunty Rahma tadawo yanzu saika Dage dacin abinci kayi k’iba.
Harara bobo yasakar musu yana fad’in Ammi wlhy yarannan sun rainani.
Ammi da inna suka tuntsure da dariya, inna ta ce, “Abdulmaleek aiko kura da ‘ya ‘yanta take wasa a daji, ammi ta ce, ” wlhy kuwa inna.
Ammi takalli su khairiyya ta ce, ”kutaso heebba mutafi gida hakannan ko?, tunda kungama aikin, fuska suka shagwa6e, khursiyya ta ce, “Ammi wai kina nufin harda mu?, harararsu ammi tayi hardaku mana, tunda ga safna nan tazo kukuma basaiku koma gidaba, dama ga hidima fall cikinku, dasafe saikuringa zuwa ko?.
Su saima yanzu suka kuladasu safna dake zaune.
Ammi takallesu tareda fad’in kuna 6ata mana lokacifa gakuma Deriver yana jiranmu.
d’akin Rahma suka shiga sunata zum6ura baki, haryanzu su Rahma barci sukeyi abinsu.
Hibba dake barci suka d’akko suka fito, suna son yarinyar sosai, yanzu haka komai NATA Yakoma d’akinsu, har anmaida mata suna Autar Ammi.
Har mota safna da bobo suka raka ammi.
Bayan su Ammi sun tafi shima bobo ficewarsa yayi batareda yasake ko kallon indasu safna sukeba.
Suma cikin gida suka koma suka Shiga d’akin Rahma wadda har yanzu suna barci.
Suna nan zaune har aka kira magriba baseera tamik’e zata tafi, bayan Safna tarakata k’ofar gida tashiga adaidaita, baseera tana k’ara jaddada mata karfa tayi wasa da damarta, tayi k’ok’i kimai ta aiwatar yanda yadace.
Safna ta ce, ” karkiji komai insha ALLAH zanyi k’ok’ari.
Okey sainajiki k’awar rai da rai.
Dariya safna tayi ta ce, “hakane my sweet baseera, suka tafa mai adaidaita yaja suka wuce.
Safna tana Shiga gidan ta Tatar Rahma ta tashi, tayi farinciki daganin ‘Yar uwarta danhaka ta rungumeta, aunty safna yaushe kikazo?. Tun d’azun Nazo kina barci ya jikin?. Da sauk’i saidai jikina yana ciwo tayi maganar tana yatsine fuska, to sannu auta cewar safna, kai kawai Rahma tad’aga mata.
Ta ce, ” aunty safna yasu ummi?.
Suna nan k’alau suncema a gaisheki gobe zasuzo, tom ALLAH yakaimu lfy, Yakuma naji gidan shiru?.
Kowa yatafi saini kad’ai, Nima zan zauna anan ne harki samu sauk’i.
Lah da gsk?.
Eh mana safna tafad’a tana murmushi, Rahma tana juya baya safna ta galla mata harara.
Itakam rahma dabatasan tanayiba ta rungumeta tanamai farincikin faruwar hakan.
Bayan anyi sallar magriba bobo yadawo gidan, kaitsaye d’akin Rahma yanufa, har yanzu suna zaune da safna suna hira, safna tana hirarne kawai amma jitake tamkar ta shak’e Rahma tamutu.
Sallamarsace tasakasu d’agowa suduka tareda amsawa, suna had’a ido da Rahma yay mata murmushi, ya jikin? Yafad’a cikin sassanyar muryarsa, Rahma tai k’asa da kai sannan ta ce, “da sauk’i.
To Alhamdllh, kinyi sallah ko?.
Rahma ta girgiza kai alamar a’a.
Miyasa?, kobak’yayine?.
Girgiza kai Rahma tasake yi cikeda kunya, mik’ewa tayi tashiga bayin.
Harta Shiga bobo yana binta da kallo, saida tashige sannan yajuya yafita.
Safna tabishi da kallo zuciyarta na suya, jibi Dan ALLAH yama nuna tamkar baisan da ita ad’akinba, tayi k’wafa da fad’in zakazo hannuna ai.
Na CE, ” hummm.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Yau kwanan su Rahma 2 da dawowa, dangi kam kullum sunata tururuwar zuwa dubasu damusu jaje, A6angaren bobo kuwa kulawa yake basu ta musamman, dai dai da abinci saiyace shine zai bata abaki, itakuma taita zame zame, wata shafta sai anzo shan magani, saida lallashi da mazurai takesha.
Ran safna na 6aci, Dan aganinta wani abunma bobo yanayi da biyune, Dan haka take k’arajin tsanar Rahma aranta, kullum kuma zuciyarta tana k’ara nunkuwane wajen son Raba Rahma da bobo kota halin k’ak’ane.
++++++++++
Yau tsawon kwanan safna hud’u agidan amma takasa aiwatar da burinta nasakama bobo magani, Dan ko abinci bayaci taredasu saidai a d’akinsa, kuma su khairiyya suna gamawa zasu d’auki nasa sukai d’akinsa, itakam har yanzu bata ta6a shiga d’akinsaba.
Bobo kam bak’aramar tsana yayima safna ba, Dan sai yanzun yakejin Kalmar bata sonsa azuciyarsa, kuma dukkan take takenta yanzu yana lura dashi, takan bashi dariya wlhy Dan ganin yanda take nuna masa alamomin so.
Yaukam bobo yana cikin damuwa Dan yana buk’atar kasancewa da matarsa, tunda yanada lfy, sai juye juye yake agado, jiyake d’akin yayi masa girma, ya kalli agogon dake manne abangon d’akin 1:5pm na dare, yad’anyi tsaki tareda mik’ewa.
Wani story book yad’auka da filo yafito harabar gidan, wasu kujeru yanufa masu k’yau dake k’ark’ashin wata rumfar bunu, handky d’insa yasaka yashare kujerar da tebirin sannan ya zauna, yad’ora k’afafunsa bisa tebird’in.
Duk abinda bobo keyi akan idon safna ne, murmushi tasaki sannan ciki sand’a tafito dankar Rahma taji motsinta.
Kai tsaye wajensa tanufo……….💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 34
Jin motsin takun mutum yasakashi d’agowa, dararan idanunnan nasa masu haske yasauke akanta, wad’anda ayanzu sukad’an canja kala zuwa jaa.
Da sauri takauda nata idon Dan bazata juri kallonsaba, lokuta da dama idanunsa suna saurin rikita mata lissafi.
Lafiya dai?, bobo yay maganar fuska ad’aure.
Yanayinsa yasaka jikinta yin sanyi, danya d’aure mata fiye da kullum, amma saita fuske, ta ce, “kayi hak’uri inaso muyi maganane Dan ALLAH.
Idonsa yamaida ga littafin tareda jan d’an k’arami tsaki, da hannu yanuna mata wajen zama batareda yad’agoba.
Safna tagyara kujera tareda d’aukar handky d’insa dake gefen k’afarsa ta goge kujerar sannan tazauna.
Shikam cigaba yayi da karatunsa.
Saida tayi masa kallon tsaf, sanye yake da kayan barci wandonsa iya guywa sai k’aramar riga mara hannu kayan duka jajayene sunyi bala’in haska farar fatarsa, aranta ta ce, ” kai guy d’in nan yahad’u tako ina, komai nasa maik’yawune, kowacce irin sutura yasaka takan zauna daidai da tsarin hallittarsa, kallidai yanda kayan barci suka masa k’yau, shiyyasa idan yad’auki ainahin dressing yake rikita kwanyar mata……..
Jin tayi shiru saiya d’ago idanunsa yana kallonta, saiyaga tak’ura masa ido, k’ara d’aure fuska yayi fiye da d’azu, ina saurarenki, yayi maganar cikeda karsashi..
Tuni safna tashiga hankalinta, ta tattaro nutsuwarta guri d’aya, tawani lankwashe murya tamkar wadda take agaban mijinta.
_“ya Abdulmaleek Dan ALLAH da farkodai ina mai neman gafararka.”_
Idonsa nakan buk ya ce, “dakikaimin mi?, ince sai anma mutum laifi ake bashi hak’uri?, nikuma bakiminba.
Tunda yafara maganar tak’urama bakinsa idanu, Dan inbaka kasa kunnenkaba bazakaji abinda yake fad’aba, itama kanta Dan darene gari yayi tsit shiyyasa takejinsa, ahankali yake maganar kuma muryarsa cikin wani yanayi, mai lurane kawai zai fahimceshi ko kuma fahimtar halin dayake ciki.
Ahankali tasauke ajiyar zuciya tareda gyara zama, takuma marairaice murya can k’asan mak’oshi ta ce, “namaka laifi my Boboo!,”.
yanda tafad’i sunan nasa tareda jansa cikin salo saida yad’ago Jan idonsa yakalleta, baidaice komaiba yamaida idanunsa yalumshe.
Wani murmushi safna tasaki sannan tacigaba dafad’in nikuwa namaka laifi Dan ance na aureka amma nak’i, alokacin bansan kai baneba wlhy dabazan k’iba.
Ya maleek tunranar Dana fara ganinka a school d’inmu nakamu da sonka mai tsanani.
Da sauri yad’ago kai yana kallonta, saidai yakasa furta komai Dan mamakinta.
Tacigaba, wlhy sonkane yahana nayima iyayena biyayya dakuma rashin sanin kaine mijin dasuka za6amin.
Saidai randa ummi ta aikoni wajen Rahma nashiga matuk’ar rud’ani danadamar bijirema iyayena, lallai ranar zuciyata yayi tamkar zata fashe……
Bobo yakatseta da fad’in no wonder shiyyasa kikamana pretending wai kina jin juwa koma mine?, yafad’a yana yatsine fuska tamkar yaga wani tutu.
Safna tasakko tatsugunna agabansa tana hawaye, Dan ALLAH my boboo kataimakeni ka aureni?.
Wata uwar harara bobo yajefeta dashi, cikin kaushin murya ya ce, “bakida hankaline?, kokin manta nid’in *_MIJIN K’ANWARKI NE!!?._*
Itama cikin d’aga murya ta ce, ” inacikin hankalina kuma INA kan sani, Maleek nasan bakason Rahma, itama batasonka, Niko ina Sonka…….
Da Sauri yakatseta dafadin ubanwaye yagaya miki?.
Tazaro manyan idanunta, ta ce, “zamankune yafad’amin, Dan wlhy ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba baku ta6a had’a shimfid’a da Rahma ba, wannan yana cikin dalilin zamanka anan gurin, idan kuma nayi k’arya karantse mini da ALLAH kata6a had’a shinfid’a da ita, nikuma indai kayi zan hak’ura dakai nabar mata.
Harara bobo yasakar mata, to ina ruwanki?.
Tayi wani murmushin mugunta, daruwana maleek harda d’an tsaki, domin kuwa Sonka nakeyi, sokuma mai tsanani, Dan ALLAH kasaki Rahma kamaye gurbinta dani, wlhy namaka alk’awarin maka biyaya, zankuma cire maka duk wani kunci da damuwar dake tare da kai….
Cikin tsawa bobo ya ce, ” Dallah malama yimin shiru, yay murmushin nan nasa na munguta sannan yasauke k’afarsa k’asa, Yakuma gyara rungumar fillonsa yana kallonta, ya ce, “yarinya bakida abinda zaki iya mayemin gurbin my cute dashi, dantafiki komai wlhy, k’yawun sura ilimin addini iya zama da mutane hankali nutsuwa k’yak’yk’yawan tunani uwa uba hankali, yoni nayi canjinki da Rahma aina fad’o wlhy nakuma ci baya arayuwata, kisa azuciyarki dama can ALLAH yarubuta Rahma CE matata bakeba, ubangiji yagwada kine kawai danyaga k’arfin imaninki, amma saikika Nuna masa kinfisa wayo, to wallhy kisani kullum godema ALLAH nake dakikace bazaki aureniba, mahalliccina maisona da nasara yabani Rahma amadadinki, zuciyarki tadaina shirya miki k’aryar zan iya rabuwa da Rahma, wlhy yaudararki kawai takeyi, nida Rahma mutu karaba takalmin kaza.
_Yay k’asa da murya tamkar mai rad’a, ya ce, “Rahma sai Abdulmaleek, Abdulmaleek kuma sai Rahma k’yak’yk’yawa mafi k’yawu acikin mata._
Yafigi filonsa da littafi yay cikin gida yana ‘Yar dariyar mugunta.+
STORY CONTINUES BELOW

Durkushewa Safna tayi awajen tana kuka, wlhy baka isaba saika saketa ka aureni kokak’i kokaso, danni kad’ai ALLAH ya halicceka shiyyasama yakashe matarka tafarko yabarminkai, k’arya kake kace Rahma CE k’yak’yk’yawa acikin mata, ko makaho yashafa yasan nafita k’yau, kuma kaima kasani, boboo wlhy saika rabu da rahma, kuma muzuba nidaku d’an halak kafasa, daga yau zamu saka k’afar wando d’aya daku, saina addabi rayuwarku wlhy, duk cikin kuka take sambatunnan, saida tayi mai isarta sannan tamik’e, wlhy *_Abdulmaleek_* saina mallakeka koda ta hanyar kashe Rahma ne.
😳munga banu, safna!!.
Tabd’ijan masu karatu akwaifa Marsala, safna kuwa tanada hankali?.
Muje zuwa danjin yazata kaya.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Haka bobo yakwana tunanin maganganun Safna da yadda zai 6ullo musu, tabbas yayi kuskure dayake barin Rahma tana kwana d’akinta tun zuwan Safna, d’akinsa yadace tana kwana aii, haka yayta juye juye da tunani har asubahi baiyi wani barcin kirkiba.
Itamadai Safna haka tafaru gareta, batayi barcinba kwana tayi tunani.
Sai bayan sunyi sallar asubane barci yakwashesu suduka biyun dayake weekend ne.
Rahma da Nawal ne kawai keta kaikawo agidan, suka gama had’a break fast suka gyara gidan tsaf.
*_10:6am_*
Bobo yatashi, yagama komai na al’adar rayuwarsa sannan yafito falo cikin dogon wandon jins blue da farar t-shirt mai gajeren hannu, sai zabga uban k’amshi yakeyi.
Rahma da Nawal suna zaune afalo tana ma Nawal kalba, da gudu Nawal taje ta rungumeshi tana fad’in my papa ina kwana.
Lfy lau baby yafad’a yana rik’e hannunta sukazo suka zauna.
Rahma ta gaisheshi ya amsa amma fuskarsa babu walwala.
Azuciyarta ta ce, “boss yaukuma muskilancin ne yamotsa?, afili kuma ta ce, “ga break.
Yad’an kalleta, atausashe ya ce, ”kawomin tea kawai.
Mik’ewa tayi tahad’o masa tea mai k’auri takawo masa, ya amsa yana binta da kallo, ahankali ya ce, “ngd, itama d’an kallonsa tayi takauda ido.
Yana shan shayi yana kallon film d’in dasuke kallo wani India film yakula Rahma tanason film d’in India komiyasa?.
Safna tafito itama, Rahma ta kalleta aunty harkin tashi?.
Saida tad’an ta6e baki sannan ta ce, ” eh natashi.
Takalli Bobo dayayi tamkar baima san da shigowartaba kuma yanajinsu.
Ta ce, “ina kwana?.
K’ara d’aure fuska yayi sannan ya ce, ” lfy.”
Rahma bataji dad’in yanda ya amsama auntyn ta gaisuwaba amma yaza yayi.
Takalli Safna dake zaune tana kallon bobo ta gefen ido, aunty gafa break.
Uhum kawai safna tace mata.
Haka akaita zaman kurame afalon, saidai Nawal daketa surutunta, shi bobo yanayine saboda Safna, itakuma Rahma tanajin haushin yanda yake share ‘Yar uwarta, itakuma safna suduka haushi suke bata.
Shima yalura da Rahman amma sai itama ya shareta.
Bayan takammala abincin Rana tajere a dinning tak’ara gyara gidan tsaf, dama Safna bata tayata, saidai idansu khursiyya sunzo, to sukuma yanzu sunk’ara zama busy Dan bikinsu baifi saura 12days ba.
Rahma tanufi d’aki zatayi wanka, Dan Nawal nawajen dadynta.
Yaukam ALLAH yabama safna sa’ar zuba magungunanta acikin abincin bobo, bayan tagama takoma falo ta Fiske abinta.
Mintuna kad’an Rahma tafito cikin doguwar rigar material ja, kayan yayi mata k’yau sai zabga k’amshi takeyi.
Ta kalli safna dake zaune afalo, aunty bara nakirasu muci abinci ko?, tawuce batareda jiran amsar Safna ba.
Baki safna ta ta6e tareda raka bayan Rahma da harara.
Yana kwance rigingine Nawal tana gefensa tana barci, idanunsa na kallon p,o,p d’in d’akin da alama yana duniyar tunanine.
Rahma tashiga d’akin da sallama, shi baima jitaba sai k’arar rufe k’ofar yaji, yad’ago kai yana kallonta, tamasa k’yau kwarai da gsk, idanunta suna k’ara narkar dashi akanta……
Takatse masa tunani dafad’in dadyn Nawal gafa abinci yana jiranka.
Bai tankaba amma yatsura mata ido tamkar zai cinyeta.
Tasake maimaita masa sannan yay ajiyar zuciya, dama inason ganinki yafad’a yana yunk’urin tashi, saida yazauna sosai sannan yanuna mata bakin gadon alamar ta zauna.
Tad’an zauna nesa dashi kamar mai tsoron wani Abu.
*_RAHAMA!!._*
taji sunanta har cikin kwakwalwarta, Dan ya iya fad’ar sunan.
Yakuma fad’in _Rahama!._
Itama akasalance ta ce, “na’am.
Yagyara zamansa sosai yana fuskantarta, tsareta yayi da mayun idanun nan nasa ya ce, “inaso daga yau kidawo kwana d’akin nan.
Cikin sauri tad’ago takalleshi, hanjin cikinta ma saida suka yamutsa danjin furucinsa.
Fuskarsa babu alamar wasa Dan haka tamaida kanta k’asa, muryarta na rawa ta ce, “saboda mi zandawo kwana d’akin nan?.
Ya ce, ” saboda ni *mijinki* ne, umarni nake baki ba shawara ba, kuma daga yau nakeson ki fara.
Bata iya cewa komaiba Dan yau yakoma mata ainahin *_Abdulmaleek_* data fara gani ranar aurensu.
Shima baisake cewa komai yamik’e yashiga bathroom.
Tana nan zaune tamkar gunki harya fito daga bayin yacanja kayansa zuwa shadda milk colour d’inkin boda yayi k’yau masha ALLAH.
yad’auki Braun d’in takalmi yasaka agogoma haka, yafesa turarurrukansa tareda kwasar wayoyinsa da key d’in mota, saina dawo yay maganar yana k’ok’arin fita, itakuma tabisa da kallo tamkar sokuwa, ganin zai fice daga d’akin ta ce, “abincinfa?.
Tsayawa yayi amma bai juyoba ya ce, nak’oshi yay gaba abinsa.
Safna tana zaune afalo yafito, tamik’e da sauri tasha gabansa…………..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 35
Wani kallon sama da k’asa yamata ya ce, “bani hanya.
Ta ta6e bakinta tareda fad’in aidama zan baka, amma inaso na tunatar dakai maganar jiya.
Ya watsa mata harara amma baice komaiba.
Murmushin ko a jikina safna tayi, ta ce, “Nasan bakason Rahma, Dan dakana sonta bazaka fice batareda kaci abincin taba.
Tsaki yayi cikin nuna razanarwa da kaushi ya ce, “dallah bani hanya kokuma wlhy yanzunnan namiki abinda har jikokin jikokinki saisun samu labari, banza jahila kawai.
Ganin gaba d’aya kamaninsa Sun canja tamkar zai daketa yasa tabashi hanya tana murgud’a baki da yin k’unk’uni.
Ficewa yayi yana Jan tsak’i, adaidai lokacin Rahma tafito, amma bataga abinda yafaruba.
Itakam Safna bak’incikine yarufeta da fargaba, kardai ace mutumin nan yak’icin abincin nan, lalai daya cuceta.
Rahma takatse mata tunani, auty Safna lfy kuwa?.
Safna taja numfashi tana wani kicin kicin da fuska, lfy lau mikika gani?.
Rahma ta ce, “a’a nagadai kamar bak’ya cikin nutsuwarkine?.
Cikin masifa safna ta ce, ” to k’alau nake, tatashi tabar wajen.
Rahma tagirgiza kai, Dan indai dasabo tasaba da halin yayar tata.
+
%%%%%%%%%%%%
Sai dare bobo yadawo gidan, Nawal taje dagudunta ta tarosa.
Rahma da Safna suka masa sannu suma, ya amsa fuska ad’aure, d’akinsa yawuce itama Nawal tabisa.
Itama Rahma tamik’e tad’auki ruwa tabi bayansu, Safna taja tsaki tareda mik’ewa tashige d’akin Rahma.
Rahma ta shiga d’akin da sallama, saidai bayanan yashiga wanka, Nawal ce kawai take zaune tana wasa da wayarsa, ta ajiye ruwan ta ce, “Nawal zomuje ki kwanta.
Nawal ta nok’e k’afad’a tareda kwa6e fuska, ta ce, ” um um momy ni ad’akin papa zan kwanta,
Rahma tayi tayi amma Nawal tak’i Dan haka ta k’yaleta takoma d’akinta.
Bata dawo d’akinsaba sai 10:34pm, yana zaune yana danne dannen laptop tashigo, Nawal kam tayi barci.
Takai minti 3 da shigowa sannan yad’aga kai yakalleta sau d’aya yamaida kansa ga laptop, ki d’auki Nawal kikaita d’akin ki mana, yay maganar cikin nutsatstsiyar murya.
Rahma ta shagwa6e murya ta ce, “Dan ALLAH kabarta anan mana.
Yanda tayi maganar yasa dole yad’ago yana kallonta, tawani narke fuska, saiyaji wani Abu ya mintsini zuviyarsa, yad’an lumshe idanunsa harda yin wanid’an murmushin gefen kumatu, Wanda itakanta Rahma bataga yayibama, ya ce, “yaza’ayi ta kwana anan? aitayi girma da kwana tare da mu, in dama babu kowa a d’akin saikice anbarta ita kad’ai, amma tunda dakowa acan zata kwanta, yamaida kansa yacigaba da aikinsa abinsa.
Haka tad’auketa badan tasoba tanufi d’akinta da ita, Safna tana zaune tana danna waya Rahma tashigo tacanjama Nawal kaya sannan tagyara mata kwanciya.
Ta kalli safna, aunty Safna saida safe.
Safna takalleta cikeda mamaki, cikin yatsine fuska ta ce, ” ina zakije? Kike fad’in saida safe?.
Cikin d’anjin nauyinta Rahma ta ce, “d’akin dadyn Nawal”.
d’akin dadyn Nawal kuma?, tofa sabon salo kenan wai gemu akafad’a, yaukuma?.
Rahma dai batace komaiba tafice abinta.
Har yanzu yana gaban laptop, tashigo tazauna akujerar d’akin.
Yad’an kalleta bayan yakalli agogo, sannan yamaida kansa kan aikinsa.
Bayan kamar minti biyu ya ce, bakijin barcine? Kobakiga agogoba?.
Murmushi kawai tayi batareda tace komaiba, ya ce, ” kije ki kwanta abinki wannan aikin Nawal k’areshi ba yanzuba.
Dukda zuciyarta cike take da fargaba hakan bai hanata tashiba, gadon tahau amma dagacan gefe ta kwanta, tayi addu’oin ta, shiru tayi tamkar tana barci, amma duk motsin da bobo yayi sai gabanta ya fad’i, ganitake tamkar kanta yayo.
Dukda Rahma ba yarinya bace mai yawan kwaramniya kuma batada yawan surutu dan haka bata cika shiga cikin k’awayeba, bare ayi firar aure da ita, k’awayenta basa wuce basma ihsan, to amma ana koya musu wasu abubuwan a islamiyya, kuma takan d’an ta6a karatun hausa Novels idan tagani awajen Basma ko ihsan, wad’an nan dalilan yasa tasan wasu abubuwa da yawa akan zaman takewar aure, saidai yanda taga bobo yayi burus da lamarinta yasakata sakin jikinta sosai da manta sirad’in daren farko, saikuma gashi zuwan safna nashirin jamata…..
Hakadai taita tunane tunane har barcin gsky yay awon gaba da’ita.
Shikam bobo dabaima san tanayiba hankalinsa nakan aikinsa dan zuwa gobe idan ALLAH yakaimu yanada wata shari’a.
STORY CONTINUES BELOW

Ad’akin Rahma kam Safna takasa zaune takasa tsaye, wato saboda tayi magana jiya shine yau yagayyaci Rahma kwana d’akinsa? Yanaso yanuna mata maganarta ba gsky baceba kenan.
Tacije le6enta tana hawaye, aiko ya kusanceta saiya saketa ya aureni narantse, Dan INA sonsa sanda banta6ama wani mahalukiba aduniyarnan, tafashe da kuka.
Waya tad’auka takira Baseera, can aka d’auka ko gaisuwa bata tsaya sunyiba ta CE, “baseera inacikin matsala.
Wace irin Marsala kuma k’awata?.
Baseera duk shawarar dakika bani na aiwatar jiya, nasameshi namasa magana, shine ya CE, ” yau Rahma taje d’akinsa ta kwana, yanzun haka zancen nan danake miki tanacan.
Baseera ta sauke ajiyar zuciya safna ki kwantar da hankalinki babu abinda zai mata, nasan yayi hakane Dan kawai ya 6ata miki rai, Rahma d’in nawa take dahar zai kusanceta Indai yanada tausayi……
Safna tayi saurin katseta, Baseera bazaki ganeba, sufa mazan yanzu babu ruwansu dawani k’ank’antar mace, kema kuma kinsani, balleshi d’an hutu yana ganin komai yana tafiya daidai arayuwarsa,, kinsan dolene yabuk’aci mace aii.
Hakane Safna, amma kilura da wani Abu had’asu akayi kowa bayaso, kinga kuwa bazaije mata gaba gad’iba kasancewarsa mutum mai d’aukar kan tsiya, towaima na tambayeki?, kin aiwatar da aikin malam kuwa?.
Na aiwatar jiya, amma d’an zafinkan baiciba, canta had’osu shida ita yafito d’aki rai a 6ace daga nan yafice, Dan jiya abincin safe kawai yaci agidan, inda ALLAH yasoni baduka nazuba bama.
To aii da sauk’i, yanzun ga shawara d’aya dazata kawo miki nutsuwa harki samu barci, kisamu kota window ne kilek’a su, kiga halin dasuke ciki.
Kai baseera wannan ba shawara baceba, idan naje Nagano abinda zaisaka zuciyata bugawafa?.
Karki damu, insha ALLAHU bazaki ganoba.
Bayan sunyi sallama safna tayi tamaula tanufi bayan d’akunan, cikin ikon ALLAH window d’akinsa abud’e take, da sand’a taje wajen, bobo tahango abakin gadon zaune yana danna laptop, Rahma na kwance nesa dashi tarufa da bargo tana barci.
Wata sassanyar ajiyar zuciya tasaki sannan tajuya, cikin kwanciyar hankali tayi barcinta.
“Hummm kunjifa saka kai awahala masu karatu, ALLAH yarabamu da aikin Dana Dani.”
Marak’isiyya ta ce, “aunty Billy muma muje mukwanta, bobo ne kawai yajuri Rana dare yana danna laptop.”
Na ce, “aikinsan mutumin na Madeena kamar k’arfe yake, baya gajiya da aiki.”
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Yau tsawon kwanan Rahma uku da fara kwana d’akin bobo, amma ko alama baita6a kawomata wani Abu sa6anin hankalintaba, Dan haka tafara sakin jikinta sa6anin da datake barci a d’arare.
Tana zaune tanayin addu’ar barci yafito daga wanka, dagashi sai tawul saikuma k’arami dayake goge sumarsa, da sauri Rahma tashafa addu’a ta kwanta.
Yay murmushi tareda fad’in gsky Rahama kinada sonkai kulum saidai kima kanki addu’a amma banda ni.
Murmushi tayi sannan ta ce, “kaima ina maka aii.
Anya kuwa my cute?.
ALLAH kuwa da gsk nakeyi.
Toshikenan na yarda yay maganar yana saka kayan barci, tsaf yagama shiryawa yasaka turare sannan yazauna abakin gadon, yad’auki wayarsa yana dubawa Dan d’anzu ankirasa yana wanka, khairiyya ce Dan haka ya kalli agogo sannan yakirata, bugu biyu ta d’auka, ta ce, ” ya bobo ina yini?, lfy kawai ya ce, “yad’ora da fad’in k miye nakirana adarennan?.
Kayi hak’uri Yaya nakira number Anty Rahma ne akashe dama da’ita zanyi magana.
Miya faru?.
Babu komaifa, somuke muju kozatazo gobe idan ALLAH yakaimu d’in.
yaran nan nakula kunefa kuke son koyama matata bakin yawo, yanzu inbanda son gantali mizata muku giben?.
Ayya Yaya wlhy shirye shiryefa mukeyi, kuma kaga yanzu Ammi tahanamu fita ko ina.
d’an k’aramin tsaki yaja ya ce, ” ALLAH yakaimu, baijira cewartaba ya yanke wayar yama kasheta gaba d’aya.
Juyowa yayi yana kallon Rahma wadda tai muk’us adole ita barci takeyi, yay murmushi komaidai wayon amarya sai ansha manta, nasan idonki biyu, idan baki juyo kimin addu’aba zakisha mamaki yau.
Da sauri tajuyo.
Yako tuntsure da dariya kekam anyi matsoraciya anan, to amin Dan barci nakeji.
Azuciyarta ta ce, “yaukuma babu latsa laptop.
Amma afili saita turo baki, cikin shagwa6a ta ce, ” nafa yimaka tun d’azun…..
Murmushi yayi tareda jawota jikinsa yamatseta sosai, suduka suka sauke ajiyar zuciya, jikin Rahma harya fara rawa, hakama k’irjinta sai dukan uku uku yakeyi har bobo yanajin bugawarsa, murmushi yayi Azuciyarsa ya ce, “yazanyi da matsoraciyar nan nikam?.
Jin tana mutsu mutsun kwacewa yasakashi k’are matseta tareda tallafo kanta, kissing d’in wuyanta yafarayi, daddyn Nawal pls kayi hak’ur…….
Bai bari tak’arasaba yahad’e bakinsa danata, sosai yake wasa da harshenta da jikinta, ganin yana Neman wuce gona da iri tafara haure haure da k’afarta tana mintsilinsa.
Saida yayi mai isarsa sannan yasaketa yana maida numfashi.
Da sauri itama tamatsa gefe tana maida numfa, saida yanutsu sannan cikin murya mai taushi amma asark’e ya ce, ” kizo kimi Addu’ar inba hakaba namiki abinda yafi haka.
Babu shiri tajuyo tamasa addu’ar tashafa masa kamar yanda yabuk’ata,, shikam sai dariya yake k’asa k’asa wai matsoraciya.
Shiru tamasa tana tunanin hali irin na maza, Dan itakam wannan *_SABON AL’AMAREE_* yazarce wayonta.
Safna kam hankalinta a kwance yake yanzun, tunda malam da’u yace mata aii babu abinda zai shiga tsakanin Rahma da bobo tunda basusan junansu, acewarsa yaturo wani aljani dazai dinga gadinsu karsuji sha’awar junansu ma bare har wani Abu yashiga tsakaninsu.
Hummm kaji masu jayayya da hukuncin ALLAH.
######
DA SAFE haka Rahma tatashi tanamai tsananin jin kumyar Bobo, Sam tak’i yarda su had’a ido.
Safna tana lura dasu, Dan haka ko awajen break tayi kicin kicin da fuska tanata harare harare, babu Wanda yakula da ita, bobo idonsa nakan matarsa, itakam Rahma tamaida hankalinta wajen bawa Nawal abinci abaki dankarta makara, dahakadai aka gama break, bobo yad’auki Nawal suka fice, Rahma tarakasu har wajen mota, tafiyarsu babu dad’ewa itama Safna tatafi makaranta.
Har gabda magriba safna bata dawo daga makarantaba, hankalin Rahma dukya tashi, gashi takirata amma yak’i wucewa, duk halin datake ciki bobo nakula da ita ammadai baice komaiba.
Bayan yayi shirin masallaci yafito, afalo ya iske Rahma tanata safa da marwa, yay mata kallon tsaf, kamar zai wuce saikuma yajuyo, wai lfy kuwa?.
Yatsine fuska tad’anyi, wlhy aunty Safna ce har yanzu bata dawoba, gashi nakira wayarta tak’i hucewa, dan ALLAH kozakad’an gwada kiranta? muji…..
Yanda tayi maganar saita bashi tausayi, baice komaiba yazaro wayarsa a aljihu, harzaiyi amfani da family layinsa saikuma yafasa daya tuna wazai kira, layinsa dakowa yasani na office yay amfani dashi, ido yad’ago yana kallonta alamun tafad’a masa number.
Tafad’a shikuma yana sakawa, cikin mamaki sosai yake kallon number dan ana kiransa da turo masa message da ita, basarwa yayi yakirata Dan bayaso Rahma tafahimci komai, cikin sa’a kuwa yana kira tashiga, bugu biyu tad’auka jikinta har rawa yakeyi Dan ganin Wanda yakirata.
Cikeda salo tace assalamu alaika, sanin muhimmancin sallama kawai yasakashi amsawa, murya adak’ile ya ce, “kina inane?.”
Wani sanyin dad’i Safna taji, takuma kashe murya can k’asan mak’oshi, wlhy moto nane yad’an samu matsala kozakazo ka taimakeni…….
Baibata amsaba yakashe wayar gaba d’aya, ya kalli Rahma ya ce, “tace tana zuwa motantane yasamu matsala amma angyara.
Hummm kunfaji bobo da k’arya🤣.
ita kam safna yana yankewa tayi saurin kallon wayar, ranta yad’an 6aci amma saita danne takirashi, jin wayar akeashe yasa tayi zaton ko bashida caji.
Babu dad’ewa kanikawan data kira suka iso, mukullun mortar tabasu tatari adaidaita tayo gida…………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 36
Ana cikin sallar isha’i safna ta shigo gidan, babu kowa afalon sai k’arar TV tawuce d’akin Rahma suna sallah itada Nawal.
Da sauri tadawo baya dan tanada tabbacin Rahma bata gantaba, kai tsaye wajen abincin kan dinning tanufa, ta bud’e abinci tayi barnad’e barbad’enta tamaida tarufe sannan tanufi d’akin.
Zuwa sannan sun idar da sallah, Rahma ta ce, “kai aunty har hankalina yatashi wlhy, naga dare yafarayi kuma nakira wayarki tak’i tafiya.
Safna ta ce, ” ayya my lil motatace tasamu matsala gashi wajen babu network.
To ALLAH ya kiyaye gaba.
Ummi takiraki kuwa?.
A’a safna tafad’a cikin kallon Rahma, miya farune?.
Babu komaifa d’azu bayan tafiyarkine takirani wai Abba yanata fad’a yakamata ki koma gida tunda nasamu sauk’i, shine nace suyi hak’uri ayi bikinsu khairiyya saiki koma ko?.
Numfashi safna ta sauke, azuciyarta ta ce, “su ummi fa kuna k’ok’arin 6atamin aiki, amma zanyi k’ok’ari acikin ‘yankwanakin dasuka ragemin nayi duk abinda yadace, afili kuma saitayi murmushi haka yayi Rahma, abinda tafad’a kenan kawai tamik’e zata shige bayi.
Bobo yak’arasa shigowa d’akin Dan tund’azun yana bakin k’ofa tsaye yana sauraren firar tasu.
Safna dake k’ok’arin shiga bayi tajuyo tana kallonsa, suna had’a ido tasakar masa wani lallausan murmushi, ya Bob ngd fa da d’akkoni ALLAH yabar zuminci tak’arashe maganar da d’aga masa gira…..
Bobo kam ya daskare atsaye miyarinyar nan take nufi?, agidan uwarwa nad’akkota d’in?…..
Rahma madai kallon tuhuma take masa, Dan duk abinda Safna tamasa akan idonta, tuni idonta yaciko da kwalla saboda kishi, ita kanta batasan tanada kishi mai zafiba kamar haka, ta had’iye wani Abu mai d’aci daga mak’ogoronta, mik’ewa tayi tafice daga d’akin kawai.
Da sauri yajuyo yabi Rahma da kallo harta fice, Nawal ma dabatasan bikin da akeba tatashi tabi bayan Rahma, daidainan Safna tafito daga bayi, murmushin mugunta tasaki sannan ta tako ahankali har zuwa gabansa, my jaan rago baya zama gwani, nasan kaima kana sona, amma bansan mike hanaka nunawaba?, so karka damu ni bana tsoron Rahma zan fahimtar da ita ta kurman bak’i, idan bata ganeba zan mata fassara.
Tunda tafara maganar kallonta kawai yakeyi, yama rasa wane mataki zai d’auka akanta, kafin yafarga tafice abinta, haka shima yabi bayanta tamkar soko.
A dinning suka tarar da Rahma da Nawal sunacin abincinsu, bobo yaja kujerar dake kusada Rahma ya zauna, itama safna tazauna akusa dashi suka sakashi tsakkiya, tunda suka fito ko Inda suke Rahma batama kallaba, abincinta kawai takeci.
Safna taja filet tafara zubama bobo abinci, tunda yafahimci shiitake zubamawa saiya d’auki cokali kawai yafaraci acikin filet d’in Rahma.
Abin yak’onama Safna rai, amma saita dake tafaracin abincin data zuba masan, Rahma kam koda bobo yasaka hannu a abincinta bata kulashiba, shikam mamaki take bashi Dan baita6a ganin fushintaba saiyau.
Bayan sun k’are cin abinci bobo yamik’e zaitafi d’aki, Safna tai saurin cewa ya Bob maganarmufa ta d’azu?, kosai ka kaini makaranta gobe?.
Juyowa yayi yana kallonta kamar zaiyi magana saikuma yafasa yajuya yatafi.
Rahma tayi saurin share hawayen dasuka cika mata ido, ita tama kasa fahimtar inda maganganun Safna suka dosa, kuma takasa fassara yanayin fuskar bobonta bare tagane mike faruwa?.
Hakadai takama hannun Nawal suka koma falo, kallo takunna musu sukeyi dukda ita hankalinta baya a wajen, hotunan mutane kawai take kallo, amma bata fahimtar komai.+
Safna kam tana d’aki tanata zuba tsallen murna Dan dad’i aikobabu komai tasaka rud’ani atsakaninsu, gashi kuma yau bobo yaci abinci da maganin data zuba, tadaka wani tsalle tareda fad’in saini Safna ikon ALLAH, k’adangaruwar baking tulu nake, akasheni akar tulu, abarni na 6ata ruwan, takuma tuntsurewa da dariya.
Na ce, “hummm safna kenan ba girin girin badai tayi mai.”
Bobo madai yana d’akinsa, sai safa da marwa yakeyi, yamarasa tunanin dazaiyi akan Safna da kaidinta, ganin Kansa ya tushe yad’auki waya yakira Ammar.
Cikin zolaya Ammar yad’aga wayar, kaga barrister dodon ‘yan iska, mijin Rahma baban Nawal ya yadai my guy?.
Numfashi Bobo ya sauke tareda fad’in Ammar ajiye wasa gefe inaso muyi maganane.
To inajinka Ammar yafad’a cikin gyara nutsuwarsa.
Ammar wata matsalace agidana nakeson kanemamin hanyar maganinta danni kaina gaba d’aya ya kulle.
Ammar ya ce, “kaida Rahma ne.
A’a no Rahma batayimin komaiba yayartace Safna.
Haba bobo tokai miya had’aka da safna kuma?, bayan kai yanzu mijin k’anwartane.
Hakane Ammar ni mijin k’anwartane, amma yarinyar tana Neman shigowa rayuwata, yakwashe kaf abinda Safna tamasa yafad’ama Ammar, yanzun zancennan danake maka nadawo daga masallaci na Tatar tana barbad’a magani a abincinmufa, amma bata ganniba, Rahma kuma suna d’aki itada Nawal suna sallah.
Ammar yaja wani gwauron numgashi, lallai yarinyarnan hatsabibiyace, to amma kunci abinci?, a tomizai hana, sammu yakanyi tasirine da izinin ALLAH, Dan haka zuba maganinta bazai hanani cin abinciba nikam.
Hakane Abdulmaleek, ammafa natayaka murna da aurenka bai kasance da yarinyarnan ba wlhy.
Aikodai nima haka naketa godema ALLAH akullum Ammar, Dan nasan da itace matar tawa nasan saita rabani da Nawal.
Wlhy kuwa zata iya. ni yanzu hanya d’aya nake ganin mafita kuma maganin yarinyarnan.
Da sauri bobo ya ce, ” minene?.
Maganinta d’ayane Wanda zata gane lallai kamata nisa fintin kawau shine kayi k’ok’arin kusantar matarka, ka ajiye batun Barin Rahma sainan gaba, Dan wlhy Idan kayi sake sai shaid’aniyar yayarta d’in nan taci galabar rabaku nan gaba, Dan kuwa 6arakar ta hango har take iya tunkararka kasaki ‘Yar uwarta ka aureta, inhar tabud’e ido taga Rahma daciki, tom dolene tasakama zuciyarta salama ko itace shigabar jaheelai ta duniya, kuma yakamatama ta tattara takoma gida tunda su Rahman sun sami sauk’i.
Duk abinda kafad’a gsky ne Ammar, saidaifa gsky Rahma yarinyace.
Ammar yay dariya to abokina yaza’ayi, yaran k’auye da’akemusu aure shekara 12/13 fa?.
Hummm kai asuma mazan yarane shiyyasa.
Wata dariyar shak’iyanci Ammar yasaki cikin dariya ya ce, “kaikuwa gaka k’ato ko?, so kabimusu yarinyarnan ahankali wlhy Dan nasanka sai a slow.
Kai d’an iska saida safe, dankasamu nafad’a maka sirrina shine zakamin wulak’anci.
Hhhhhhh haba angon Daren yau maida wuk’ar mana.
Murmushi bobo yayi tareda yanke wayar yana fad’in kai Ammar mafa d’an iskane wlhy.
Jiyayi zuciyarsa yayi wasai kamar anyaye masa damuwarsa, mik’ewa yayi yashiga bayi ya salla wanka tareda d’auro alwala, bayan fitowarsa yad’an shafa mai da turarur rukansa yazira doguwar Riga ya zauna yana jiran shigowar Rahma.
Jareda yad’auka yana karantawa, saidai lokaci lokaci yakan kalli agogo, tun yana saran shigowarta harya fara mamakin miya hanata zuwa Dan 11:47pm, yad’anyi tsaki tareda gyara kwanciya yamaida Kansa ga jaredar, sai yakasa cigaba da karantawa, wayarsa yajawo yakirata amma bata shigaba yakumayin tsaki, afili yace mi yarinyarnan take nufi danine?.
Ganin wankin hula zai kaishi dare yasakashi mik’ewa yafito, fitilir falo yakunna Dan har ankashe alamar sunma kwanta kenan, le6ensa yacije yanufi d’akin Rahman.
Nanma fitilar akashe take saida ya kunna, yakai dubansa ga gadon Safna da Nawal ne kawai kwance suke barci, ad’an kid’ime yafara baza idanu, can yahango Rahma zaune akan sallaya tana karatun alkur’ani mai girma, ajiyar zuciya yasauke ahankali.
Itakam Rahma tun shigowarsa tana jinsa amma ko d’agowa ta kalleshi batayiba.
Ahankali yataka har inda take, wani d’an tsugunnon gayu yayi agabanta, ido tad’ago ta kalleshi, kallo d’aya tayi masa ta kauda kai, wani d’an murmushi yayi mai had’eda ta6e Baki, yay wani k’asa da murya yana mata kallon nan nasa na k’asan ido, Sayyada yau baza’a bani shayibane?, konayi laifine?.
Idanunta dake cike tabda hawaye tad’ago suka had’a ido, tai saurin juya k’wayar idonta Wanda yabama Hawayen damar zubowa, alkur’anin ta ajiye tamik’e batareda ta tanka masaba tafice.
Shima mik’ewa yayi yana murmushi azuciyarsa ya ce, “yammata kwantar da hankalinkima yanzun bada dad’ewaba zakiyi kukan mai dalili.1
Ficewa yayi yakoma d’akinsa.
Itakam tana kichin, bayan tadafa masa shayi tad’ora atire tareda yanka lemon tsami kamar yanda tasaba, d’auka tayi tanufi d’akinsa.
Yana zaune abakin gado yajingina da fuskar gadon yana latsa waya tashigo, idanunsa yad’ago yana kallonta, itakam ko Inda yake bata kallaba taje saman dirowar gefen gado ta ajiye tiren shayin, batareda ta tanka masaba takama hanyar juyowa, da sauri bobo yarik’e hannunta, cak tatsaya amma bata juyoba, yawani narke murya can k’asan mak’oshi, miyake damunki?.
Hawayene suka k’ara zubo mata akumatu, dama Rahma akwai arhar kuka, ganin bazata amsashiba yajawota tafad’o jikinsa, mutsu mutsun kwacewa tafara amma yay mata nagartaccen rik’o, hannunsa yasaka yakama ha6arta yarike yanamai fuskanto da fuskarta gareshi my cute kishi ko?.
Da sauri tad’ago idonta dayay ja tana kallonsa, ya akayi yagane asirin zuciyarta, ita kanta tana mamakin yanda ta nuna kishinsa ayau, wani 6angare na zuciyarta ya ce, “kin kamu da sonsane, da sauri ta ta6e baki.
Bobo yamatso da fuskarsa gabda tata tamkar zaimata kiss murya k’asa k’asa ya ce, ” miyasa kike ta6e Baki?, kobaki yardaba kina kishina?.
K’ok’arin mik’ewa tafarayi tana fad’in shayinkafa zai huce.
K’ara k’ank’ameta yayi, cikin salon maganarsa ya ce, “aii shayi yagama aikinsa daga yau, saidai idan nasha da marmari amma badan damuwaba, daga yau kece zaki zama shayina.
Da sauri ta kalleshi saikuma ta kauda kai yayinda suka had’a ido, bata fahimci Inda zancen nasa yadosaba amma taji aranta akwai shak’iyanci aciki.
Yunk’urawa tasakeyi zata tashi, ta ce, ” tonaji kabarni naje nacigaba da karatuna.
Ayya aynanma karatu zamuyi kuma jira kigani, tashi kiyi alwala kizo.
Dukda gabanta yafad’i amma saita dake Dan batason rud’a kanta da zargin abinda ba hakaba.
Inada alwatafa. Tayi maganar kamar zata fasa kuka.
OK tom tashi muyi sallah, bata musa masaba tamik’e suka hau sallaya, shine yajasu jam’i, raka’a hud’u sukayi kafin daga bisani yafara kwararo addu’oi Wanda ita bama tata6a zaton ya iyaba, daganan yadafa kanta yay addu’a da *Annabi tsira da amincin ALLAH su tabbata agareshi* ya koyar damu, yayi musu addu’oi sosai sannan suka shafa tareda mik’ewa.
Da sauri Rahma takama hanyar ficewa, bobo yay azamar shan gabanta, idanu tad’ago tana kallonsa, yad’aure fuska tamau tamkar bashine yagama lalla6ataba yanzun, k miye haka wai?, yaushe raini yashiga tsakaninmune?.
Yanda yacanja mata lokaci d’aya saitaji tsoransa yak’ara kamata, murya na rawa ta ce, “kayi hak’uri zanje nacanja kayane.
Hannunta yakama zuwa gado, karki damu bama saikin canjaba yay maganar yana k’ok’arin zame dogon hijjabin dake jikinta.
Idanu kawai Rahma ta runtse, zuciyarta sai faman bugawa takeyi da k’arfi…………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 37
Daga ita sai zani d’aurin k’irji, ya ajiye hijjabin gefe shima yazauna yana kallonta, yayinda itakuma taduk’ar dakai k’asa idanunta cike da kwalla.
Tashi yayi daga bakin gadon, yajawo d’an k’aramin tebir na gilas dake gaban kujera ya zauna a agabanta suna fuskantar juna, saida yay mata kallon tsaf sannan yasaka hannu yad’ago ha6arta.
Idanunta talumshe, kwallan datake mak’alewa suka zubo, yad’an lumshe ido yabud’e akanta, murya k’asa k’asa ya ce, “wai miye damuwarkine?, shin kukan nan bazai k’arebane?, kokuwa ban cancanci sanin matsalarkiba?.
Girgiza kai tayi alamar a’a.
Ya ce, ” nafison kimin maganar da bakinki.
K’ara matso hawayen tayi muryarta na rawa ta ce, “babu komaifa.
Ya ce, ” amma kike yin kuka?, kinga fad’amin kinji my cute.
Yanda yaymata maganar cikin muryar lallashi saitaji sanyi aranta, wannan yabata kwarin gyuywar kallonsa, ta d’an kauda idonta sannan ta ce, “Dan ALLAH ya Abdulmaleek miye had’inka da aunty Safna?.
Tabashi dariya kwarai da gsk, amma saiya dake, yad’an tsura mata ido nawani lokaci kamar mai nazarinta, batareda yabata amsartaba yamik’e tsaye, doguwar rigarsa yacire yarage dagashi sai gajeren wando.
Itadai satar kallonsa takeyi da mamaki, tamasa tambaya amma yashareta yacigaba da harkar gabansa.
Fita taga yayi, bayan kamar minti 3 saigashi d’aukeda fresh milk da cup, sake zama yayi akan tebir d’in, yatsiyaya fresh milk a cup, itadai tana kallonsane kawai, saida yacika kofin taf sannan yamik’a mata, girgiza kanta tayi ahankali ta ce, ” nak’oshifa.
Yanzu d’inma baitanka taba, saidai yakai kofin saitin bakinta, yanda yatsareta da mayun idanunsa wad’anda ayanzu suka sake canja kala yasata dole tabud’e baki tasha, haka yayta bata tanasha badan tanasoba, data janye bakinta saiya had’e fuska dole nacigaba da kar6a, ahaka dai harta shanye tas, shima zubawa yayi yana sha yana kallonta, itadai kanta na k’asa tana wasa da zoben hannunta.
Bayan yagama yamik’e ya ajiye cup da kwalin fresh milk adurowar gefen gadon, bayi yashiga yayi brush, ya umarceta itama dataje tayi, sanin datayi akwai sababbin brush a bayinsa dayakan ajiye yasa batayi musuba yashiga, aiko tararwa tayi ya ajiye mata sabo a Leda, tad’auka ta6are tayi brush abinta sannan tafito.
Abakin gado ta iskeshi zaune yana kashe wayoyinsa, yad’ago ido ya kalleta, hau gado ki kwanta mana ko bakyajin barcine?.
Kaita jinjina masa alamar eh.
Murmushi yayi ya ce, “karkidamu kwanta barcin zaizo, ko kin manta gobe kunada hidima agidan Appa.
Tunowa da gobene zasuje gidan Appa Dan k’arasa shirye shiryen bikinsu khursiyya yasakata hayewa gadon, saidai gabanta sai fad’uwa yakeyi, Dan ita lamarin bobo yau tsoro yake bata wlhy.
Hakadai ta kwanta tamkar wata munafuka ta k’udundune waje d’aya, yad’an kalleta ya girgiza kai sannan yagyara kwanciyarsa shima.
Kwanciya yayi sosai tareda Jan bargon ya lillu6e kamar yanda tayi, jawota yayi jikinsa, yay mata k’yak’yk’yawar runguma wadda ita kanta saida taji yarrrrr, daurewa tayi tadake Dan bataso tanuna masa tsoronta afili, saidai tamakaro Dan tuni bobo ya harbo jirginta.
Jitai yana mata wasu abubuwa sa6anin hankalinta, tunda take dashi bai ta6a mata hakaba, tuni k’irjinta yafara dukan Tara Tara.
Hawaye tafarayi ahankali kuma tafara sheshshekar kuka wadda tadawo dashi hankalinsa, cikin muryar kuka ta ce, “Dan ALLAH kayi hak’uri, d’an murmushi yayi sannan yajuyo da ita suna fuskantar juna dukda dai acikin duhu suke, cikin wata irin murya dabata ta6a jinsa da itaba yake maga, cikin kunnenta ya ce, ” plss Rahma ki daure ki mallaka min kanki, karki manta nata6a fad’a miki inaso da sauri shiyyasa nakeyi da sauri, inaso na numa duniya ked’in dabance kuma kin cancanta, sannan kuma kinmini tanbaya d’azun tom yanzufa zanbaki amsar tambayaki, amma kafin sannan kema zan tanbayeki, Rahma kina kishi nane?.
Tambayar yabata kunya Dan haka taisaurin sinne kanta ak’irjinsa daketa tashin k’amshi mai saka zuciyarta nutsuwa, yanda take fidda numfashi ak’irjinsa saiyakejin dukkan ga6o6in jikinsa sundaina aiki, yasa hannayensa duka ya rungumota sosai tareda mannata da k’irjinsa bayan ya zame zanen data d’aura.
Wata wawuyar ajiyar zuciya suka sake gaba d’aya, bai zauna 6ata lokaciba yafara bata hot kisses masu rud’ar da sabon shigarsu, masukuma k’ara k’aimi ga Wanda yasaba, to a6angaren Rahma dai rawar jiki take masa, ganin yanda tarikice masa ya lalubi kunnenta cikin sark’ewar murya ya ce, “my cute kinutsu bazan cutar dakeba, duk Wanda aka kira jarumi to kitabbata yakasance mai jarumtarne, Nima nakai mak’urar tik’ewar dabazan iya hak’uriba plz helf me my life…..
Kuka Rahma tafarayi ahankali, damasa magiyar yayi hak’uri Dan ALLAH, amma ina hankalin mutumin naku yagushe, bayajinta ko kad’an, k’ok’arin Isar da sak’wanni kawai yakeyi.
Bata ankaraba taji yafara addu’ar saduwa da iyali kamar haka.👇🏻
*_“Bismillaahi, Allaahumma jannibnashaid’ana, wajannibshaid’ana maa razak’tana”._*
Rahma ta kwalla k’ara data sakani kwasa aguje nayo waje, bobo yagama aiki, shima dukda baya cikin hayyacinsa saida yay nasarar saka tafin hannu yarufe mata bakinta.
Afalo na rak’u6e tamkar Minafuka, kukan Rahma danake jiyowa Nima yasakani hawaye, babu sunan Wanda bata kiraba ya taimaketa har Nawal yau saida Rahma takira amma babu mataimaki sai ALLAH.+
STORY CONTINUES BELOW

Safna cikin barci taji kamar Rahma tayi k’ara amma daga baya kuma saitaji shiru, d’an tsaki tayi tareda gyara kwanciyarta .
Safna lol🤣😜.
Nakai dubana ga agogon falon k’arfe 3:34am araina nace dukdai rashin imaninsa ai yanzu ya sarara mata, cikin sand’a na nufi d’akin amma sainaji k’ofar gam😒mutuminku fa yarufe k’ofa dankar naga 6arnar daya tafka, inagadai yana tsoron kar ‘yan gidan billy ladan suji labarine sufad’ama Safna, dantanada masoya awanga gida lol.😘
Ta kafar mukulli nasamu na d’an lek’a, kunsandai bilynku akwai d’an Karen naci, lallashi na hango bobo nayi, saboda kukan wahala da Rahma takeyi, sai saka mata albarka yakeyi da kalaman soyayya masu sanyin dad’i, _wad’anda ba’ayima ballagazar mace adaren farko, ALLAH dai yarabamu damasu halin akuyoyi._😏
Saida yaga barci ya d’auketa, Wanda nakeda tabbacin barcin wahalane, ahankali yazame kanta daga cinyarsa yamaida saman filo, yajawo bargo Yakuma lullu6eta sannan yamik’e.
Fuskarsa cikeda annuri yanufi bayi domin tsarkake jikinsa.
Hak’ura nayi nadawo falo nakwanta, ko barci awa biyu nasamu nayi, kar bobo yafito yace nacika sa ido.😏🤥.
*_washe gari._*
K’arar bud’e k’ofarne yatadani da asubahi, bobone naga yafito daga d’akinsa sanye da jallabiya, abinda yaban mamaki shine kwankwasa kofar d’akin Rahma dayayi, bayan kamar minti biyu Safna tabud’e k’ofar.
Kallo d’aya yaymata yakauda Kansa Dan sanye take da rigar barci iya guywa.
Ganin bobo tsaye yasakata d’an zaro ido my jaan lfy kuwa?.
Wani murmushin mugunta naga yamata Wanda ita bata fahimci hakanba saima wani dad’i data ratsa zuciyarta, azatonta aikin malam yafara tasiri.
ya ce, “pls auntynmu kid’an dafa mana ruwa tunda ‘yan nefa sund’auke, Dan ALLAH maid’an yawafa bara naje masallaci.
Duk da taji wani iri dayace mata aunty, amma saita kauda tunanin aranta ta d’akko na fara’ar dayamata tamaye gurbinsa dashi, aranta ta ce, ” to komi zaiyi da ruwan zafi oho?.
Nidai bilynku nace hummm.
Ruwan zafin Safna tanufi kicin tad’ora sannan takoma d’aki danyin sallar asuba.
Saida gari yad’anyi haske bobo yashigo gidan, hakan yayi daidai da fitowar Safna daga kicin d’aukeda boket dake cike daruwan zafi yanata turiri.
Ya ce, “yauwa auntynmu sannu da k’ok’arifa, lallai wannan jiyya dakikazo tayi amfani Dan yanzune zakiyi jiyyar gsky.
Cikin rashin fahimtar kalamansa Safna take kallonsa, ta daure ta ce, ” wai batada lfy ne?.
Kibari kawai batajin dad’in wlhy, Dan adaren jiya girma ya risketa, baijira cewartaba yad’auki boket d’in yanufi d’akinsa yana murmushinsa.
Binsa Safna tayi da kallo cikeda so da k’auna azuciyarta ta ce, “to wane kuma irin girmane yariski Rahman?, komi yake nufi oho, shidai bazaima mutum magana sak ba saidai amurd’e tak’are zance da ta6e baki had’eda d’aga kafad’a alamar sudai suka sani.
A d’akin bobo kuwa yanacan ya had’a ruwa maid’an zafi abayi, bayan yagama yafito tareda nufar gado Inda Rahma ke kwance tana barci, zama yayi abakin gadon kusada ita, sai faman mirmushi yakeyi, yakai hannu yana shafa fuskarta ahankali, aransa ya ce, ” lallai d’an Hakim Daka raina shike tsonemaka ido, kullum yanama Rahma kallon yarinya k’arama saigashi adaren jiya tabashi dukkanin farin cikin daya dace, lallai shikam yakasance mai sa’a..
Ahankali Rahma tabud’e idanunta dasuka kumbura saboda kuka, takai dubanta ga bobo dake zaune kusada ita yana shafa fuskarta, aranta ta ce, “dubi yanda yake farinciki babu ruwansa bayajin ciwon komai, amma ni ganinan ko motsawa banasonyi saboda azaba……. d’ago idon da bobo zaiyi suka had’a ido da Rahma, da sauri tamaida nata ta lumshe.
Cikin muryarnan tasa mai dad’i ya ce, ” aina ganki, Ashe kin tashi?.
Itadai shiru tayi bata tankaba.
Yad’an murmusa tareda janye bargon datake ciki.
Da sauri tazabura zata tashi, saikuma takoma ta kwanta tana fad’in wayyo zafi.
Saurin tallafota yayi zuwa jikinsa, yasaka hannu ya share mata hawayen dasuke zurara, cikin tausayawa ya ce, “sorry my cute ALLAH yay miki albarka kinji, lallai kinci sunanki Rahma, _Rahmar ALLAH_ nagodema ALLAH daya azurtani da samunki alokacinda banyi zatoba, Rahma kingama mallakata da komai nawa, ked’in wata abuce mai daraja daga cikin rayuwata, nabaki dukkan ragamata kijani inda kikeso kikuma yi yanda kikeso dani, daga yau *Abdulmaleek* nakine ke kad’ai da yaranmu, ina rok’on *_Ubangin Al’arshi ya albarkaci rayuwarmu ya saukar da albarka da soyayya nagartacciya mai tsafta arayuwarmu._*
Rahma wlhy bamma San Kalmar dazanyi amfani wajen gode mikiba, saidai inaso kisaka aranki *_Abdulmaleek_* yana sonki da k’aunarki marar adadi, I luv you so much my cute, I luv you, I luv you, I luv you 4ever, yak’are maganar da sumbatar goshinta💋.
Wani murmushine yasu6ucewa Rahma Wanda bata shirya yinsaba.
Bobo ya rungumeta, acikin kunnenta ya ce, ” lallai murmushinki ya nunamin kin kar6i soyayyata ngd sosai.
Sunkutarta yayi sai bayi, jin asakata cikin ruwan zafi ga wani rad’ad’i daya ratsata yasakata k’an k’ameshi tana fad’in wlhy da zafi.
Kinga yi hak’uri wannnan zafin dakikeji zai daina, idan baki shiga ruwanba akwai damuwa kinji, cikin lallashi da kalamai masu dad’i wad’anda Rahma bata ta6a tunanin bobo yanadasuba yake mata.
Cikin hikima da dabara yagasata, saida ya tabbatar taji dad’in jikinta sannan yafito yabarta dantayi wankan tsarki.
Katifar yajuya Dan dukta d’an 6aci da jini, yacire zanin gadon ya sauya wani.
Babu dad’ewa itama tafito daga bayi, sai duk’ar dakai takeyi saboda kunya.
Shi dariyama tabashi, abin sallah yashinfid’a mata, tasaka doguwar Riga da hijjaf tayi salan, shikuma yana zaune abakin gado yana jiranta.
Tana idarwa tayi addu’a, d’an kallonsa tayi fuska a marairaice ta ce, “bacci nakeji”.
Da sauri ya ce, ” zoki kwanta abinki my cute, ai yau ranarkice ke kad’ai.
Tashi tayi tacire hijjab ta kwanta, shima yaje bayanta ya kwanta tareda rungumota jikinsa.
Wata ajiyar zuciya tasaki, muryarta na rawa ta ce, “Dan ALLAH kayi hak’uri wlhy akwai wahala…..
Tabashi dariya amma saiya gimtse, ya ce, ” matsoraciyata kwantar da hankalinki kinji, barci zamuyi ni babu abinda zan miki.
Dukda bata yarda dashiba amma tad’anji dad’i.
Zuwa ‘yan mintuna barci yakwashesu suduka………….
💃✈ _jirgin so zaya tashi ked’ai ake jira ‘Yar gata Rahman bobo kece da sarauta._😂😂
*Yau ranarkuce masoya Rahman bobo*❤❤❤❤😘🙋🏼
. 人
. (___)
. ┃口┃
. ┃口┃
. ┃口┃
. ┃口┃. 人.
. ┃口┃. .-:”'”””;-. 人
. ┃口┃(*(*(*|*)*))(__)
┃ – ┃║∩∩∩║. |口||┃
. ┃┃┃┃┃┃┃┃┃┃. |三||┃
. ┃┃┃┃┃┃┃┃┃┃. |三||┃
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
Its another yaomal jumu’ah! May Almighty Allah make it easy for us, purify our mind, put joy in our hearts , increase our iman, elevate us beyond our expectations.(Amin thumma Amin.)
Juma’at mubarak.🕌🕌🕌💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 38
*_8:30am_* Nawal tasakama Safna kuka ita wajen momynta zataje.
Ita kanta Safna abin mamaki yake bata Dan ganin har tara saura Rahma bata fitoba, kota manta Nawal zataje makarantane?, dukda dai bobo yace mata batada lfy, amma yakamata ace tafito aii, jitai ranta yakuma 6aci, wata zuciyarta ta ce, “idan kin kwantar da hankalinki aii bobon yakusa zama naki gabad’aya…….
Nawal ta girgizata, aunty naje wajen papa na tambayesa momyna.
Safna tad’aga mata kai alamar eh.
Bugun k’ofarne yasakashi farkawa, bobo yaja d’an tsaki sannan ya yunk’ura yatashi da k’yar, sakkowa yayi daga gadon yanufi k’ofar, wayene yay maganar dad’an haushi.
Nawal ta ce, ” papa nice.
K’ofar yabud’e mata tashigo sannan yamaida yarufe.
Papa ina momyna take?.
Bobo yanuna mata gado da hannu, da gudu taje ta haye Rahma dake barci, momyna zan makara a school kitashi ki shiryani, kuma yunwa nakeji.
Bobo yad’an zaro ido Shifa yama manta yau akwai aiki.
Baby ya haka? Kosai kin tada momyn nakine?.
Rahma tabud’e idonta ahankali, ganin Nawal akanta yasa ta yunk’ura ta tashi zaune, Nawal kin tashi?.
Eh momy tund’azu natashi nake nemanki momy yunwa nakeji, kuma ba’amin wankan tafiya school ba.
Bobo dake tsaye yana kallonsu cikeda sha’awa yakamo hannun Nawal yana fad’in kinga kibar momynki batada lfy kinji, makaranta kuma tunda yau juma’a ki hak’ura kawai dankin makara Tara saurafa.
Kai Nawal tad’aga MASA, tamaida kallonta ga Rahma, momy kanki keyin ciwo?.
Murmushi Rahma tayi tareda satar kallon bobo, ta ce, “kaina keyin ciwo amma na warke.
Momy sorry, Nawal tafad’a kamar zatayi kuka.
Murmushi Rahma tayi tareda jawo Nawal jikinta ta rungume, karki damu babyna nawarke aii, tashi muje namiki wanka…..
Bobo yakatseta dafad’in no kwanta ki huta bara namata wankan, itada safna saina saukesu gidan Appa suje suwuni.
Da Sauri Rahma tad’ago tana kallonsa, ta kwa6e fuska tamkar zatayi kuka, cikin muryar shagwa6a ta ce, ” nifa?.”
Zama yayi kusada ita yakamo hannunta yarik’e anasa, kinga kibarsu sutafi tunda bakida lfy, Nima bazan dad’e awajen aikinba zandawo gida muyi zamnmu.
Nidai ALLAH inason zuwa kumafa ni lfy ta k’alau, Rahma tayi maganar tana hawaye.
Murmushi yayi yashare mata hawayen, itadai Nawal tana kallonsu, ganin papanta na sharema momyn ta hawaye itama tasa hannu tana goge mata, ta ce, “papa”.
Bobo ya ce, ” Na’am.
Papa kabar momy taje itama kaga tana kuka.
Shafa kan Nawal yayi tareda fad’in baby aina barta, kutashi Ku shirya idan mukaje can saimuyi breakfast.
Sakkowa sukayi, Nawal ta ce, “momy muyi wanka a bathroom d’in papa.
A’a baby muje namu.
Bobo ya ce, ” saboda kina guduna.
Ahankali yayi maganar yanda Nawal bazatajiba, Dan yakula yanzu dole su iya bakinsu agaban parrot d’innan.
Babu yanda Rahma ta iya dole suka Shiga bayinsa, bobo yabi Rahma da kallo Dan ganin yanda take tafiya dad’an d’ingishi.+
Acikin ‘yan mintuna suka gama shiryawa tsaf harda Safna, fitowarsu falo babu dad’ewa saiga bobo yafito cikin ash colour na shadda d’inkin zamani yayi k’yau sosai, Safna tashagala da kallonsa kuwa, jitake tamkar ta rungumeshi amma babu damar hakan.
Rahma tanufi kichin danta rufe k’ofa, bobo yabita da kallo dantayi MASA k’yau dukda dogon hijjabine har k’asa ajikinta, tafito tanufosu safna ta ce, “waike lfyarki kuwa kike tafiya haka?.
Cak Rahma tatsaya amma takasa cewa komai, bobo dake latsa waya yad’ago yakalli Rahma sannan ya maida kallonsa ga Safna ya ce, ” bana fad’amiki batada lfy ba.
Okey namantafa, Safna tayi maganar cikeda rainin wayau, Dan ita bata yarda Rahma batada lfy ba.
Bobo ya maido kallonsa ga Rahma my cute badai haka babynki zata Fita babu d’ankwaliba?.
Rahma takalli Nawal dake zaune akujera tana wasa da filoliwa ta ce, “nabata gyale bansan INA ta ajiyeba, Nawal ina mayafinki?.
Nawal tad’ago tana kallonta, ta turo baki ta ce, ” momy nibanason gyalen Nafi k’yau ahaka.
Tsawa bobo yadaka mata zakitashi ki d’akko kosaina zanekine?.
Da Sauri Nawal tamik’e zatayi kuka, Rahma tarik’e hannunta kinka fad’amin bakison wancanne na canja miki wani?.
Kai Nawal tad’aga mata tana satar kallon baban ta.
Bobo ya harareta Yakama hangar Fita dama Safna tafita, to kinga bisu naje nad’akko miki.
Bobo yak’arasa ga mota yabud’e yashiga, wuf Safna tabud’e gaban itama tashige, k’ala baice da itaba saima k’ok’arin tada motar dayakeyi, Nawal tabud’e baya tashiga tana satar kallonsa Dan bataso yadaketa.
Babu dad’ewa saiga Rahma tafito da farin siririn gyale ahannunta, takulle k’ofar falon tanufosu, tunda ta taho ioon bobo na kanta jiyake wata k’aunarta nak’ara ratsashi, ga wani k’yau na musamman dayaga yau tak’ara masa.
Koda tak’araso taga Safna agaban motar batako kallesuba takama k’ofar baya zata shiga.
Bobo ya ce, “dawo gaba.
Kallonsa Rahma tayi, yanda yaymaganar babu wasa afuskarsa kuma ba ita yake kalloba, a ranta ta ce, ” to a INA zan zauna?, afili kuma saitayi shiru tana kallonsa.
Ya ce, “bakijini baneba?.
Ta ce, ” naji amma a INA zan zauna?, badan Nawal dake motarba dasai yafad’i abinda zai saka Safna FASA binsu amma ALLAH ya taimaketa bazai iya kowace maganaba agaban d’iyarsa.
Duk abinda ke faruwa Safna nagaban mota ta kacire kamar motar mijinta.
Bobo yawatsama Rahma wani kallo, muryarsa cikeda gargad’i ya ce, “madam kina 6atamin lokacifa kuma kinsan office zanje.”
K’ofar Rahma takama tabud’e Safna tad’ago ta kalleta suka kalli juna, badai ta ce, “komaiba amma fuskarta tanuna alamar bak’inciki.
Rahma tadaure ta ce, “aunty kifito kikoma baya Dan ALLAH.
Cikin masifa Safna tabud’e Baki zatayiwa Rahma magana, saidai kuma komi tatuna saita FASA ta fito, tad’an bangaje Rahma tabud’e baya tashiga.
Itama Rahman gaban tashiga.
Bobo yagirgiza kai kawai dama yayima Rahman hakane danyafi son taringa takwatarma kanta ‘yanci awajen Safna.
STORY CONTINUES BELOW

Ahankali yake tuk’in tamkar bayaso, wayarsace tafara wringing, yad’auka yana fad’in malam miye nawani kirana da farar Safiya?.
Dariya ammar yayi, ya ce, “ho d’an duniya basaika nunamin ka girmaba aii.
Shima bobo dariya yayi ya ce, ” ALLAH Ammar bakada mutumci, yanzu nan nine kakecema sai yanzu na girma?.
Hhhhhh eh mana, kaima Kasan hakane.
Bakomai zan rama, yanzudai miye na kirana?.
Dama zan tambayrkane ko kana office?.
Kabari kawai wlhy namakara, yanzudai INA hanyar zuwa gidan Appa, amma daganan office d’in zan wuce.
OK to kabiyo tanan mana idan bakada wani uzuri.
Kai nifa Kasan banason zuwa office d’inka, wannan masu bak’ak’en kayan daka wani baza suyita kallon mutum.
Hhhhh toka had’une shiyyasa suke kallonka, Inda basu sankabama bazasu barka ganinaba ehe, ato bara nayi zamana Idan kamatsu kazo office kasameni.
Hhhhhh to yi hak’uri na Ammi kodayake yanzu kazama na Rahma.
Dariya bobo yayi ya yanke wayar, baikai ga ajiyewaba kiran Ya Sulaiman yashigo, yad’aga suka gaisa.
Bobo ya ce, “yaya dama wlhy INA niyyar kiranka, magani nake buk’ata.
Maganinmi bobo?.
Ummm saidai Nazo, inafata kana asibiti.
Eh, amma kai kana ina?.
Gani zanje gaidasu ammi, OK nima yanzu nabar gidan babu dad’ewa nida ya ishaq da Hamza.
Ayya tosaina shigo.
Okey, ina jiranka.
Bayan ya ajiye wayar yakalli Rahma kad’ain ya kauda kai, murya k’asa k’asa ya ce, ” gara naje na k’ar6o miki magani wannan tafiyar taki tadawo daidai, damma kinki hak’ura ne amma yanzu haka zakije gidan Ammi kina tafiyar ‘yan kaciy……
Bai k’arasaba yay saurin rufe bakinsa da hannunsa yana dariya.
Rahma taturo baki gaba, yakuma kallonta yashek’e da dariya.
Ba Rahmaba har Safna da Nawal saida suka kallesa, suna had’a ido da Safna ta madubi ya gimtse fuska.
Aranta ta ce, ”zakazo hannune malam.
Itakam Rahma ta ce, “mugu d’an masa sai ALLAH yasakamin aii.
Da hakadai suka k’arasa gidan AMMI.
Safna da Nawal suka fice, Rahma na niyyar fita bobo ya kulle motar, juyowa tayi tana kallonsa shima ita yake kallon, ya ce, “yadai ‘yammata namiki k’yaune?.
Kauda idonta tayi daga kansa, ta ce, ” Dan ALLAH kabud’emin.
Aidama zan bud’e miki, sonake nacemiki kiyi k’ok’ari koyaya kid’an gyara tafiyarki inba sokike kowa yasan miya faruba.
Kallonsa tasakeyi, saikuma tayi k’asa da kai tana turo baki gaba, nifa wlhy zafi nakeji awajen.
Shiyyasa nace ai kiyi zamanki sai gobe amma kikak’i, amma babu damuwa bara na kar6o miki magani wajen ya sulaiman, yanzudai muje ciki, amma idan kinje kiyi kwanciyarki ki huta kinji.
Batace komaiba takama k’ofa zata bud’e yarik’o hannunta haba tawan ko sallama babu?.
Tokai bazaka shigaba?.
Jawota jikinsa yayi yana fad’in zan shiga mana, amma ai bazan dad’e ba, k’ok’arin saka k’wayar idonsa yake anata itakuma tak’i basa dama, saima talumshe idanunta gaba d’aya, wani murmushi yayi Wanda har tanajin sautinsa, jin bakinsa kan nata yaskata saurin zabura, amma ina tamakaro yarigada yayi nasarar cafkar harshenta.
Na ce, “humm bara nakoma daga waje najiraku.”
Ak’alla sunkai minti biyar sannan naga Rahma tayi saurin fitowa tana murmushi, shima bobo yafito yana dariya, gaba tayi abinta hartana had’awa dad’an gudu, bin bayanta yayi yana fad’in matsoraciya kawai.
Ak’ofar falo tatsaya ta daidaita nutsuwarta sannan tashiga.
Gaba d’aya yaran suka taso suka tareta, itama tahad’asu tarungume tana dariya, Rahma akwai San yara shiyyasa duk inda taje saikaga yara suna sonta.
Bobo yana shigowa suka saketa suka nufeshi, zama Rahma tayi suka gaisa da su aunty Rasheeda, aunty ummy, aunty sameera, khairiyya da khursiyyama suka gaisa.
Bobo yak’araso shima suka gaisa su aunty Rasheeda suna tsokanarshi, Rahma dai mik’ewa tayi tanufi d’akin Ammi itada khairiyya.
Bobo ya ce, “ALLAH idan baku daina matsaminba saina saka mazanku sun k’ara aure.
Da sauri aunty Sameera ta ce, ” a’a Abdulmaleek wlhy nikam nabari yi hak’uri, tashi yayi yana murmushi ya ce, “waiku mata miyasa kuke tsoron kishiyane?.
Aunty Rasheeda ta ce, ” jeka katambayi Rahma, d’akin Ammi yanufa yana fad’in ai ita bata tsoron kishiya.
Dariya suka saka gabad’aya shikuma yashige d’akin Ammi da sallama.
Ammi ta ce, “a’a mukarram d’ina kaine?.
Wlhy nine Ammi wad’ancan ‘ya’yan naki duksunbi sun rainani, nakusa daina musu dariya.
Dariya Ammi tayi ta ce, ” kunfi k’asa aii.
Shima dariyar yayi sannan yagaida Ammi cikin girmamawa, yanayi yana satar kallon Rahma dake zaune kusada Ammi suna ware wasu kaya itada khairiyya.
Ya ce, “Ammi yunwa nakejifa.
Kallonsa Ammi tayi tana dariya, haba mukarram aii gwauro aka sani da zama da yunwa, murmushi yayi shima, ya CE, ” Ammi nima tawa matarce babu lfy.”
Ayya, Ammi tafad’a tana kallon Rahma, nima tunda tashigo nake kallonta duk naganta sukuku babu walwala sosai, ga idonta sund’an kumbura, mike damunta?.
Sosa kansa yayi yana fad’in em…em.. Ammi zazza6ine.
Dariya Ammi tayi ta ce, ” mukarram magana da in ina kamar mara gsky.
No Ammi inada gsky kawai inaso natuna sunan zazza6inne.
To ALLAH yabata lfy kunje asibitine?, a’a ammi jiya da daddare zazza6in yasameta, dama yanzu zanbiya tawajen ya sulaiman na kar6o mata magani.
Okey to Aida tayi zamanta agida tahuta ko.
babu yanda banyi da ita tazaunaba amma fir tak’i wai itadai saitazo, yayi maganar yana kallon Rahma.
Tana jinsu amma tashare kamar batasan zancen da akeba, Ammi ta ce, “khairiyya jeki had’omusu break fast ko, suma su Safna haka.
To Ammi khairiyya tafad’a tana mik’ewa.
Ammi da bobo suna ‘Yar hirarsu khairiyya takawo break fast, bobo yalangyare wai saidai Ammi tayi feeding d’insa.
Rahma tad’ago ta kalleshi saiya yimata gwalo, Ammi na kallonsa, danhaka tayi murmushi had’eda girgiza kai, koba komai tasan d’anta yasamu farinciki daga matar tasa,.
Rahma d’auke idonta tayi daga kansa tana d’an murmushi, aranta ta ce, ” Indai ta6arace kaganta salo salo ga daddyn Nawal, wani abunma idan yayi saiya baka dariya wlhy.
Ammi kam dakanta tabama bobo abincin yaci, saida yak’oshi sannan yamik’e, AMMI bara nad’anje office naga mike tafiya.
To ALLAH yabada sa’a yatsareka babana.
Amin ammina.
Ya kalli Rahma, ya ce, “my cute nawuce.
ALLAH yabata kunya amma saita dake ta ce, ” ALLAH yabada sa’a, ameen yafad’a yana fita, idon ammi kawai yahanashi mata kiss.
Afaloma yamusu sallama yafice.
Da sauri Safna ta tashi tabi bayansa………………1💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 39
Bobo dabaisan Safna nabinsa abayaba yabud’e mota yashiga, harya tada motar yaji ana kwankwasa masa gilas.
Sauke gilas d’in yayi ahankali Dan atunaninsa Rahma ce kosu khursiyya, had’e fuska yayi Dan ganin safnace, baice komaiba ya kauda kai daga kallonta.
Rik’e k’ugu tayi tanamai jifansa da shu’umin kallo, cikin narkewar murya ta ce, “haba my jaan wai miyasa kakeson wulak’antanine?, aiko bakomai ance kaso mai sonka, yanzu Dan ALLAH abinda kamin agaban Rahma d’azun yadace?.
Tsaki yaja tareda yatsine fuska tamkar Wanda yaga kashi, ya ce, “ke awa? dabazan miki abu agaban Rahma ba?.
Ya nunata da d’anyatsa wlhy kifita hanyata, karki yarda kibari na nunamiki asalin colour d’ina, ina d’aga miki k’afane saboda ‘Yar uwarki, amma zakisha mamaki idan kikacigaba da bibiyata…….
Kafin ta ce, ” wani Abu yaja motarsa yafice, dama tuni mai gadi yabud’e masa gate.
Hawaye suka kwararo afuskar safna, wani d’an lungu tasamu dagacan baya ta zauna, saida tad’anyi kuka sannan tad’auki waya takira baseera, bata d’agaba takuma kira nanma haka, ajiye wayar tayi tazabga tagumi cikeda damuwa.
Su Rahma suna ciki basusan bikin da akeba, bayan sungama ware kayan da ammi tasakasu suka dawo falo wajen sauran ‘yan uwansu suna hira, saidai hankalin Rahma yana kan tunanin ina aunty Safna?, gashi batason tashi Dan gudun karsu fahimci halin datake ciki, tasan ko kowa bai tanka tafiyartaba sai aunty Rasheeda tayi magana, Dan tun d’azu take binta da kallo, itakam idan antambayeta batasan amsar dazata bayarba.
Da sauri Safna ta kalli wayarta ganin Baseera CE yasa tad’auka da hanzari, ko gaisuwa bata tsaya sunyiba ta ce, ”kekam baseera ina kika Shiga haka inata kiranki tun d’azun?.
Safna muna lectures ne, kinsan ba’a d’agama sir hamza waya idan yana lecture, waimi yahanaki zuwa school yaune?.
Wlhy babu komai hakanan naji banason zuwa.
Lallai kinyi wauta Dan wlhy sir hamza yayi test yanzu.
Ke babu damuwa aii ina gidansu, kinsan ankusa bikin k’annenesu nextweek, to muna gidan ana shirye².
Hummm ALLAH yasa yad’aga miki k’afa to, Dan wlhy ya CE……..
Da sauri Safna ta katse baseera kenifa bawannan bane damuwata, nakirakine muyi magana.
To inajinki baseera tayi maganar tana zama kusada zeenat data fita harkarsu tuntuni dantaga sunyi nisa basa jin kira, idanma zasuyi k’ulle k’ullensu basaya akusada ita.
Safna ta ce, “baseera wlhy inacikin matsala.”
Matsala kuma kamar ya?.
Safana tafara zayyanama baseera abinda yafaru tundaga Daren jiya da motarta ta lalace harzuwa abinda bobo yamata yanzunnan.
Jinjina kai baseera tayi sannan tad’an kalli zeenat dake karatu amma hankalinta na Kansu kuma tanajin duk abinda safna ke fad’ama baseera awaya, baseera ta ce, “lallai safna bakida wayo wlhy, keyanzun harya sakaki dafa ruwan zafin Gaza Rahma amma ki Gaza ganewa?, kumafa k’uru k’uru yafito yace miki Rahma tagirma amma duk Baki ganeba.
Safna tad’an ta6e baki baseera ban… bangane kema mikike nufiba aii.
Tsaki baseera taja tana fad’in aikin banza, asheke zaman banzama kikeyi agidan, ayanzukam kid’auka bobo yamiki nisa wlhy dankuwa adaren jiya ya angwance kenan…..
Agaban safna yafad’i cikin masifa ta ce, ” baseera karki k’ara 6atamin rai kema banason fatan tsiya, taredakefa malam da’u yacemana yaturomusu aljani dazai hana ya kusanceta.
Baki baseera ta ta6e ta ce, “wannan zancekam yazama labari tunda bobo ya aikata hakan ajiya, saidai kuma kujira result d’in ciki.
Kuka wuy wuy safna tasaka tana kuran tashiga uku bobo yaci amanarta itakam rayuwarta tazo k’arshe garama tamutu ta huta.
Tsaki baseera tayi tareda yanke wayar tana fad’in ‘Yar wahala keni nagaji da matsalolinki, wlhy da bobon zaice yana sona nimafa sonshi nakeyi harma nafiki Dana kula yamin nisa saina hakura, amma nakula ke kinkasa ganewa *_” ANNABI”_* yafaku, haba Dan ALLAH ayi mutum da tosashshiyar basira, idanma bakisaniba kisani dagani har malam da’un cin k’ud’inki kawai Mukeyi babu wani aiki dayake miki Dan tun farko yafad’amin komai wlhy, ya ce, “kwata kwata babu aure tsakaninki da bobo Dan bazaima sokiba.
Zeenat tayi galala tana kallon baseera wadda da alama tamanta tana wajen shiyyasa taketa sakin zance babu (,) babu (.).
Ganinfa da gsk tamanta tana wajen yasaka zeenat zungurar ta baseera kinsan mikike fad’a kuwa?.
Figigit baseera ta kalleta saikuma tafara Kame kame au.. au.. Ummm zeenat dama kina nan?, Dan ALLAH kinji minake fad’a?, pls kirufamin asiri maganarnan tatsaya dagani saike Dan ALLAH, kitaimakeni Zeenat wlhy su6utar bakice.
Girgiza kai kawai zeenat tayi tamik’e tabar mata wajen Dan wlhy yau bak’aramin tsoro baseerar tabataba, lallai maganar Sajna gsky CE datace *_wata k’awar tafi guba_*, itakam yau ta shaida akan baseera, idan bata mantaba baseera CE tasaka safna ahanyar bin malami da bokaye, amma Ashe tanacan tahad’a baki da bokayen sunacin dunduniyar safnar, ALLAH ma ya k’ara, aiduk Wanda baiji bariba yaji hoho, babu irin nasihar da bataima safna ba amma tak’i saurarenta daga Bayama daina mata magana tayi wai bata k’aunarta, toga baseerar datake d’auka tana k’aunarta d’in nan tajefata arami mai zurfi kuma mai duhu, aii duk Wanda yagagara yima iyayensa biyayya to yanatareda gamon wahala, to ita baseera CE gamon wahalarta kuwa.
Ganin baseera tanufota yasakata saurin yin gaba.
Da gudu baseera tacimmata kuwa.+
STORY CONTINUES BELOW

A6angaren Safna kuwa baseera tana Yanke wayar tAk’ara sautin kukanta, tama rasa wane irin sambatu zatayi?, amma jitake Duk duniya babu Wanda ta tsana kamar Rahma arayuwarta, jitake zata iya kashe Rahma wlhy, afili ta ce, “wlhy natsaneki Rahma, natsaneki tsana irin wadda banta6ama wani mahalukiba, Rahma kin cuceni kedasu Ya Shaheed munafukai kawai, duk bakwa sona nimakuwa natsaneku bana sonku harma ya munnir d’in dasu ummi dukna tsaneku, kuka take Rurus da sambatu.
Zeenat Dan ALLAH ki saurareni pls.
Mizaisa na saurareki baseera?, aini yanzu kinfi k’arfina wlhy, keba k’awar rayuwa bace, tunda har kika iya cin amanar safna data d’auki sirrinta Dana gidansu tabaki duka, tonikam sai yaya kenan?, ALLAH abin tsoro kema baseera dole aji tsoron kaidinki, kecefa kika jefa rayuwar Safna a halinnan amma Ashe kina gefe kina cin dunduniyarta, haba baseera miye ribarki Dan ALLAH?, tundaga sanda iyayen safna sukace sun mata miji kika Shiga kika fita kika kanainaye rayuwarta, kin hana afad’a mata gsky bare ta fahimta, saboda son zuciya irin naku yanzu kun koma danku 6ata rayuwar auren k’anwarta, haba baseera kashe aurefa ba abin wasa bane, *_”ALLAH ne ya halatta aure da saki, amma shikanshi bayason sakin aure, duk sanda igiyar aure ta katse sai al’arshin ubangiji ta girgiza saboda kad’uwa, shaitan yakanyi farinciki awannan rana saboda yaraba aure, shin kuma kunaso kuzama daga jerin shaid’anu?.”_*
Wlhy kuji tsoron ALLAH kutuba tun kuna da dama, idan kuka bari damarku ta su6uce kunci amanar kanku, kutuba tuba na gsky ALLAH zai iya yafe muku *_”domin shi gafurun rahimunne, kuma maji6incin al’amuran bayine.”_*, kuma godema ALLAH daya fargar daku da wuri Dan yana sonku da rahmarsane.
Tunda zeenat tafara maganar baseera kuka takeyi, tabbas ta tafka babban kuskure kuma sharrin shaid’anne, wlhy tayi nadamar halayenta, tarik’o hannun zeenat tana hawaye ngd sosai zeenat kin tunatar dani abinda ban saniba kuma ngd wlhy kinsamu ladana Dan nayi nadamar abinda na aikata, kuma daga yanzu insha ALLAHU zan tuba, zan samu Safna na warware mata dukkan k’ulli, amma inaso ki taimakamin da nuna mata hanya itama, Dan inaso yanda natuba na dawo hanya itama ta tuba ta gyara kodan mugudu tare mu tsira tare.
Jinjina kai zeenat tayi tana murmushi had’eda sharema baseera hawayenta, karki damu ‘Yar uwa ngd Nima dakika fahimceni kika kuma gane abinda nake nufi, ALLAH ya yafe mana gabad’aya ya kar6i tubanmu, ALLAH yasa mufi k’arfin zuciyarmu, ina fata yanda kika fahimta da wuri ALLAH yasa Safnama ta fahimta d’in.
Ameen zeenat ngd.
Karki damu muje Dan sir koba hakabane,😜 yakusa Shiga mana, muje muk’arasa lecture d’in muwuce gida.
Jinjina kai baseera tayi tana murmushi suka kama hannun juna suka nufi holl.
😁 _wlhy abinda yaburgeni kuma yamin dad’i masu karatu, ALLAH yasa safna itama ta fahimta kamar yanda baseera tagane kuma ta tuba.🙏🏻ameen._
Su Rahma duk suna kichin suna aikin soya cincin d’in gara, amma jitake zazza6i yana neman rufeta, ga k’asanta yana mata zafi har yanzu ko motsi bata sonyi ma, Ammi dake kallonta tun d’azun ta ce, “Rahma yaya dai?.
Murmushi yak’e Rahma tayi ta ce, ” babu komai Ammi.”
Aunty Sameera ta ce, “kai Rahma bakida lfy gsky, tun d’azun nima ina lura dake, aunty Rasheeda ta ce, ” wlhy nima nakula tundama tashigo batada walwala kamarma tana d’ingishi, kokinji ciwo ak’afarne?.
Shiru Rahma tayi kanta ak’asa, jitake duk kunya ta isheta, itakam bobo yaja mata, yanzu hakama kowa yagane abinda yafaru……..
Ammi CE ta katse mata tunani dafad’in tashi muje kisha magani.
Ahankali Rahma tamik’e tana duk’ar da kai, duk sukai mata sannu amma banda safna, azuciyarta ma sai tsinema Rahma takeyi.
Kama hannun ta Ammi tayi suka nufi d’akinta, ta zaunar da ita abakin gado sannan itama ta zauna tana fuskantarta, kallonta take cikeda nazari, ita kam Rahma kanta na k’asa tana wasa da zobenta.
Rahma kodai fad’a kukayi keda mukarram d’in?.
Girgiza kai Rahma tayi ta ce, “a’a Ammi bamuyi fad’aba.”
To mike damunki?.
Ammi babu komaifa k’afatace kemin ciwo, shuru Ammi takumayi tana kallonta, zuwa can ta ce, “fad’uwa kikayine?, a’a, to ciwo kikaji kenan?.
Eh, Rahma tafad’a cikeda kunya, ga hawaye suncika idonta taf, bata fata ammi tasake tambayarta wani Abu kuma bayan wannan Dan batasan mizataceba kuma.
Ammi ma batasake cewa komaiba Dan sai yanzu tafahimci komai, amma tayi mamakin hak’urin mukarram dahar ya iya barin Rahma har zuwa yanzun, dawani yagaya mata bazata yardaba, amma gashi tagani da idonta, koda yake tasan duk cikin ‘yayanta babu Wanda yakai mukarram kawaici saidai zuciya da masifar tsiya.
Bayi tashiga tahad’a ruwa mai zafi tareda magunguna masu k’au cikin wad’anda takema su khairiyya gyara, fitowa tayi tana fad’in Rahma taso kigani.
Rahma tamik’e tamkar wata muna fuka tanufi Inda ammi take tsaye, bayi ammi tanuna mata da hannu, kishiga ruwa na nan aroba kicire kayanki saiki shiga ruwan, amma saikin daure Dan yanada d’an zafi, idan yahuce kikuma Tarar wani ga maganin nan ajiye aroba saiki kuma shiga kinji, shima saiya huce insha ALLAHU k’afar zata daina ciwo sannu, nima idan k’afata na ciwo dashi nake amfani.
Sanyi Rahma taji aranta Dan duk tunaninta Ammi taganene, amma dataji tace itama dashi take amfani idan tana ciwon k’afa saitaji dad’i, risinawa tayi Tanama Ammi godiya.
Ammi tayi murmushi tana fad’in aii babu godiya tsakaninmu Rahma, kud’inma ‘ya’yanane, matsayinku d’aya dasu mukarram araina.
Murmushi Rahma tayi tashige bayi tanamai jin k’aunar tsohuwar aranta, itama jinta take tamkar umminsu.
Ammi tana niyyar fita saiga ya hamza da bobo sunshigo d’akin da sallama.
Baya ammi takoma tana musu sannu, suka gaisheta sannan suka zauna abakin gado, shi boboma kwanciya yayi, Ammi ma zamatayi saman kujerar d’akin tareda jawo k’atuwar ledar dasu bobo suka ajiye, miye kuma anan?.
Ammi d’unkunanmune wlhy muka amso cewar bobo dake kwance male male agado.
Ammi tayi murmushi a alallai manyan yayye sun shirya, harkun kama d’inkinku ahannu?.
Ya hamza yay dariya to Ammi aigara haka, inba hakan mukayiba aiki cud’e mana zaiyi, Dan kinga daga yau babu hutu, sauk’inma banida lectures gaba d’aya satin nan, boboma nashi mai sauk’ine tunda zai iya d’aukar Hutu, ya sulaiman da ya ishaq nedai babu dama.
Hakane amma aii ansamu sauk’i tunda gaku, ALLAH dai yayi muku albarka.
Ameen Ammin mu.
Ammi appa bai dawoba?.
Eh bai shigoba, k’ila yau a can zaiyi sallar juma’a Dan yacemin sunada meeting.
Okey nima bara naje gida nayi wanka to kafin su ya ishaq su taso.
To shikenan saika dawo.
Bobo ya ce, “saika dawoto, bara nayi barci kona minti30 ne, plz idan kadawo katadani.
Humm ALLAH ya shiryaka kaikam, to kana nufin bazakayi wankan masallaciba?.
Ah zanyi mana, nikasan inada kaya anan gidan, to Dana tashi zand’an watsa ruwa na shirya, kafinma ad’akko yara school amusu wanka ashiryasu aina d’an huta.
Dariya ya hamza da Ammi sukayi, ya hamza ya ce, ” Ammi wannan autan naki bansan yaushe zaisan yagirmaba?.
Bobo ya ce, “babu wani auta, kana ina ammi ta tureni daga sannan kujerar ta d’ora hibba.
Yanda yay maganar cikin shagwa6a yasaka Ammi da ya hamza yin dariya, ya hamza yafice yana fad’in bara na dawo sai azauna shari’a.
Ammi ma mik’ewa tayi tafice zuwa kichin tana dariya.
Bobo yagyara kwanciyarsa yana murmushi, arayuwarsa yanason rayuwar irinta gidansu, Inda ace hakane akowane gida toda zuminci bai lalaceba, ALLAH yak’arama amminsu da Appa tsawon kwana.
Na ce, ” ameen.
Lumshe idanu yayi dansonyin barci, baisan Rahma tana d’akinba.
Itakam tanad’anjin hirarsu sama sama, daga baya taji shiru duk zatonta sunfita gaba d’aya.
Tamik’e daga cikin ruwan da ammi tahad’a mata Dan har ya huce, wani takuma had’awa kamar yanda ammi ta umarceta, tasake shiga, nanma takai minti 15 aciki ruwan yana ratsata, yanzukam taji dad’i sosai, harma jitake wajen yabar zafi, wanka tayi kawai tafito.
K’arar bud’e k’ofarne yasaka bobo bud’e ido ahankali ya sauke akan Rahma.
Sosai yakuma bud’ewa Dan yayi mamakin ganinta, dama tana band’aki tun d’azun amma tayi muk’us kamar babu kowa?.
Shiru yayi bai motsaba Dan yakula batama gansaba.
Aiko Da gsk Rahma bata kula dashiba, tasa k’aramin tawul tatsane jikinta, jinta take wasai yanzun kamar iska zata d’auketa, kujerar madubi taja ta zauna tana mai fad’in kai ALLAH yabiyaki Ammi, Ammi uwa tagari, dabadankeba k’ilan saina had’a sati ina fama dazafin wajennan Dan wlhy ciwo yakemin, ALLAH yak’aramiki tsawon Rai Amminmu Dan zuciyata kullum k’ara k’aunarki takeyi wlhy.
Murmushi bobo yasaki danjin furucin Rahma ga mahaifiyarsu, jiyayi sonta yak’ara nunkuwa azuciyarsa.
Itadai hidimar shafa manta takeyi harda yaye yawul Dan ko kad’an hankalinta baikai akanshiba, tsaf tagama sannan tad’an gyara fuskarta dukda bawata kwalliyar kirki tayiba amma tayi k’yau.
Kayan su data d’akko ta d’auka tasaka, tayi d’as cikin siket da rigar na farin material mai d’igo d’igon bak’i.
Bobo dai yana kwance yana kallon ta cikeda k’auna, baimasan sanda yafurta woow my cite kinyi k’yau.
Arazane Rahma tajuyo tana kallonsa, tako wage baki zata tsala ihu Dan ita azatonta aljanine yay shigar siffar bobo yazo mata.
Da sauri bobo yajawota yarufe mata baki da lallausan tafin hannunsa……………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 40
“K!, ‘yammata karki taramin mutane mana, bobo yay maganar yana mai matse Rahma ajikinsa.
Sotake ta kwace kanta amma yak’i bata damar haka, ganinfa kamar da gsk atsorace take dashi yahad’e bakinsu waje d’aya, wata sassanyar ajiyar zuciya Rahma tasaki saidai har yanzun jikinta baibar k’yarmaba, saima k’aruwa dayayi Dan ayanzun ta shaid’a lallai bobone, to amma baya gudun Ammi tashigo tagansu?, kokuma wani daga cikin matan yayyensa.
Mintsininsa take amma yak’i sakinta, dole tahak’ura tazubama sarautar ALLAH ido wadda ta girma ta d’aukaka, daga kiss yafara kauce hanya, ayanzukam bazata iya jurewaba musaman idan ta tuno da azabar datasha adaren jiya wadda har safiyar yau wajen namata rad’ad’i, iya k’arfinta take turesa amma mutumin naku ko gazau sak’wanni kawai yakai son isarwa cikin nuna k’warewa.
Hawayene suka fara zurara akumatun Rahma Dan ayanzu kam batada wata hanyar ku6ta saidai kuka dan shikad’aine yarage mata………
Da gudu khairiyya da khursiyya suka shigo d’akin suna kwala kiran aunty Rahma! Aunty Rahm………
Suduka maganar tamak’ale amak’oshi Dan ganin abinda yafi k’arfinsu.
Shima da sauri bobo yabar abinda yakeyi yad’ago, yayinda Rahma ALLAH yabata nasarar mik’ewa daga jikinsa.
Bobo ya k’ank’ance idonsa dasukayi jaa yana kallonsu khairiyya dasukayi tsuru², yasan tabbas idan yayi magana saiya fallasa asirin muryarsa, to amma bazai iya k’yale yarannanba.
Rahma tara6a tagefensu khursiyya zata fice yace karki fita.
Cak tatsaya cikeda mamakin wannan k’arfin hali irinnasa.
shikam kallonsa yamaida akansu khairiyya ya ce, “ku bakuda hankali Baku iya sallamabane idan zaku shiga waje?.
Yaya wlhy bamusan kana nanba munzata ita kad’aice Dan ALLAH kayi hak’uri bazamu sakeba.
Le6ensa yacije yama rasa mizaice musu, tsaki kawai yayi dallah kutashimin kai shashashu, haka za a kaiku gidan miji kunama mutane shirme.
Da sauri sukayi waje, suna fita khursiyya tarufe bakinta da hannu ta shek’e da dariya, itama khairiyya dariyar tasaka, suka tafa suna cigaba da dariyarsu, saidai sukayi mai isarsu sannan khairiyya ta ce, ” kai ya bobo an iya mazuran rashin gsky, nakulafa yama rasa mizaice manane shine ya koromu, dariya suka kama tuntsurewa da ita.
Khursiyya ta ce, “yar uwa yau naga ruwan soyayya, dama irinsu ya Abdulmaleek akwai iya soyayya, amma akwai dai mazuran tsiya, badan karyaci ubanaba wlhy saina koma naga mi akeyi yanzu.
Idanu khairiyya tazaro ta ce, ” tabd’i wlhy badaniba, kingama tafiyata baza’a kaini gidan miji da karyayyar k’afaba, haka kawai su sunacin tasu soyayyar da allura ni akaima mijina jiyya yakasa nunamin.
Rahma dake bayansu ta ce, “ALLAH ya shiryaku wlhy.
Da sauri suka juyo ganin Rahma yasasu nufowa gareta harsuna ‘Yar rigerigen tambayarta ya aikayi tafito?.
Hararar wasa tamusu ta ce, saiya fito yaritsaku wlhy.
Da sauri suka bar wajen itakuma tabi bayansu tana murmushi.+
Tundaga wannan lokacin Rahma bata sake bari sun had’a hanya da bobo ba har dare lokacin tafiyarsu yayi.
Bansan miya faruba Ammi tace safna tayi zamanta anan danta tayata wasu ayyukan.
Ina kallon bobo yayi wani murmushi mugunta, Rahma dai batace komaiba, Safna kam jitayi tamkar tafasa ihu Dan Bak’inciki.
Rahma ta ce, “ina Nawal mutafi.
Kinga d’iyata kuyi tafiyarku tunda weekend za’a shiga kuma dukan yaran nan za’a barsu.
Jiki a sanyaye Rahma ta ce, ” to Ammi saida safe.
ALLAH yakaimu d’iyata kinji.
Tunda suka fita bobo yake wata ‘Yar dariyar mugunta k’asa² itadai Rahma batace dashi k’alaba saidai jikinta duk yayi sanyi.
Da kansa yabud’e mata motar tashiga, shima yazagaya yashiga, har suka fice daga gidan baikuma cewa k’alaba, bayan yahau babban titi yana tuk’i ahankali yad’an juyo ya kalleta ya ce, “matsoraciya har an hau network d’in tsoronne?.
Shiru tamasa kamar batajiba, murmushi yayi yasaka hannunsa d’aya yakamo nata yana murzawa, d’ayan kuma yana tuk’i dashi, batace masa komaiba bakuma ta hanashi abinda yakeyiba.
Wai baza’amin maganaba ne my cute?.
Idanunta tad’ago ta kalleshi ganin hankalinsa nakan titi yasa takauda kai, miye kuma kike kallona?, bobo yay maganar har yanzu idanunsa atiti.
Nifa ban kallekaba, Rahma tafad’ad’a kamar zatayi kuka.
Humyim yarinya zaki maganane, ainasan hanyar dazansaki maganar bara mu Isa gida dai kigani.
Gaban Rahma ne yafad’i, saikawai hawaye yafarabin kumatunta, aranta ta ce, ” wlhy ka k’aramin irinna jiya mutuwa zanyi.
Karya kwana yayi yashiga layin gidansu, anguwar shiru babu kowa sai haushin karnuka, yay hon mai gadi yabud’e masa gate bayan sun gaisa yashige ciki damotar.
Yana tsayawa ko kashewa bata tsaya yayiba tayi wuf tafice, sauri sauri gudu gudu tashige ciki bayan tabud’e k’ofar falon, kafin yak’araso harta shige d’aki ta kulle kanta.
Tabama bobo dariya danhaka yashige d’akinsa yana wata ‘Yar dariya.
Tana Shiga d’akin tadafe k’irji tanama kanta dariya, wata zuciyarta ta ce, “kai Rahma akwai tsoro?, yo badole naji tsoroba, wlhy nabari mutuminnan idani zaiyi, afili tayi maganar Tanana kanta dariya.
Wanka ta shiga bayan tagama ta d’auro alwala tafito, shirin barci tayi sannan tahau abin sallah tayi shafa’i da wutiri, tayi addu’ointa tamik’e, aranta tana fad’in yaudai ba’a nemi shayin k’addaraba.
Gado tahaye ta kwanta hankalinta kwance taja bargo ta lullu6a.
STORY CONTINUES BELOW

Shimadai bobo yana Shiga d’akinsa wankan yashiga, yay shirin barci tsaf, duk abinda yakasance al’adarsa yagudamar sannan yajawo laptop akahau aikin k’a ida.
Har wajen k’arfe d’aya yana gaban laptop sai biyu saura yad’ago yana kallon agogon dake d’akin, mik’a yayi tareda hamma, yarufe laptop d’in yamik’e, dirowar gefen gado yabud’e ya d’au key da wayoyinsa yakashe fitilar d’akin yafice.
d’akin Rahma yanufa yasandai yanzu tayi barci, ahankali yabud’e k’ofar yashiga yamaida yarufe, kallonta yayi kwance akan gado ta k’udindine abargo, aransa ya ce, ” yarinyar nan sai abarki, gakida bargo na gsky mai laushi kin 6uge da shiga bargon bogi.
Wayoyinsa yazube adurowar gefen gadon yahau yakwanta ahankali, bargon ya janye yashige ciki tareda rungumeta a faffad’an k’irjinsa mai yalwar k’amshin turare.
Ahankali yasauke ajiyar zuciya tareda lumshe idanu, Alhmdllh yafad’a azuciyarsa.
Rahma kam dabatasan yanayiba takuma gyara kwanciyarta sosai a k’irjinsa, ahankali tarink’a sauke numfashi mai d’umi ak’irjinnasa.
K’ara lumshe idanu yayi yana mai lashe la66ansa da k’yar ya iya control d’in Kansa yay barci.
_washe gari_
Da asuba Rahma tariga bobo farkawa, jinta kamar ajikin wani Abu yasakata saurin bud’e idanu, ganin bobo yasakata zare k’yawawan idanunta, aranta ta ce, “to yaushe yashigone?, mutum tamkar aljani?, k’yak’yk’yawar fuskarsa tazubama idanu, aranta ta ce, ” mutumin nan akwai sirrin k’yau, babu Abu mafi d’aukar hankalinta ajikin bobo kamar Sajensa, tanason sajensa sosai danya k’awata sirrin k’yawun fuskarta, ahankali talumshe idanunta tareda kai hannu bisa k’yakykyawar fuskarsa tana shafa sajensa daya kwanta luf luf yanata tashin k’amshi mai dad’i kamar yanzun yasaka masa turaren.
Tunda tafara shafa masa fuska yafarka, ta k’asan ido yake kallonta, aransa ya ce, “ALLAH yabani magulmaciyar mata, anasona ana kaiwa kasuwa, Rahma tajanye hannunta tana murmushi Dan duk zatonta bai tashiba, k’ok’arin zare jikinta tafara daga NASA, jin haka yasa bobo k’ara rungumota, acikin kunnenta ya ce, ” guduwa zakiyi kibarni?.
Shiru tayi wai ita a adole barci takeyi, ya ce, “humm nizakima pretending? Bayan kingama shafemin fuska kina shauk’i?.
Rahma ta cusa kanta ak’irjinsa tana dariya k’asa k’asa, shima dariyar yayi ya ce, ” oh ni dama matana ta iya gulmar soyayya saikace matar k’auye?.
Itadai luf tayi ajikinsa Dan kunya.
Jin ana kiran assalatu yasashi yunk’urawa yatashi da ita ajikinsa, to madam pretending tashi muyi sallah.
Zame jikinta tayi daga nasa batareda tad’ago ta kalleshiba, shimadai mik’ewa tayi yashiga bayinta ya d’auro alwala, Inda take ya iso yana gyara hannun rigarsa daya nannad’e saboda alwala, sunkuyowa yayi yasumbaci kumatunta sannan yafice yana fad’in saina dawo.
Batace komaiba saidai tasaci kallonsa tagefen ido tana murmushi, yana fita tatashi itama Dan d’auro alwala.
Saida yaje d’akinsa ya canja kayan barcinsa zuwa doguwar Riga sannan yafice masallaci.
Saida gari yayi haske sannan bobo yadawo, lokacin Rahma ma tana zaune akan sallaya tana addu’a bayan ta k’arasa karatun alkur’ani.
Zama yayi suka shafa addu’ar tare.
Kan Rahma ak’asa ta ce, ”ina kwana?.”
Bazan amsaba saikin kalleni.
Murmushi tayi tareda rufe idanunta da tafin hannu, kamata yayi yamik’ar tareda zare hijjabin sannan yajata suka zauna a bakin gadon, my cute wai ita wannan kunyar bazata raguba haka?, nafa rage kusan 60% acikinta amma ank’i nunamin hakan.
Murmushi tayi kawai batareda tace komaiba, ya ce, “idan kinaso nakaiki gidan Appa yau saikin kalleni, yafad’a yana tsura mata mayun idanunsa.
Ahankali tad’ago k’yawawan idanunta masu kasheshi ta sauke akansa, kallon ido cikin ido sukema juna, suduka sunshagala cikin shauk’in so, bobo yad’an lumshe idanunsa yabud’e ahankali, cikin muryarsa mai dad’i ya ce, ” ina k’aunarki dayawa Rahma, tabbas da ubangiji bai sauya al’amuraba danayi asarar rashin kasancewarki matata, ALLAH na gode maka dakamin wannan k’yauta.
Rahma talumshe fararen idanunta, ta ce, “nice na cancanci gidema ALLAH ya *_Abdulmaleek_*, kaid’in namijine mai wahalar samu acikin maza, zanta godema ALLAH har k’arshen numfashina da kasancewarka mijina, Nawal d’iyata, tabbas kai alkairine ga rayuwata, hawaye yafara bin kumatunta na dad’i……
Ganin haka yasaka bobo fara bata Sumba ako ina najikinta, saida ya yamutsata San ransa, itakam dukda tsoron dake cikeda ruhinta haka tadake zuciyarta tana kar6ar sak’wanninsa.
Rungumeta yayi yana sauke numfashi asarek’e, muyi barci yafad’a ahankali yana gyara mata kwanciya.
Shiru tayi kamar tana barcin, shikam bobo mintuna kad’an barcin yay awon gaba dashi, ganin barcinsa yayi nisa tazare jikinta ahankali tamaida masa filo a madadinta.
Ficewa tayi domin had’amusu breakfast.
Cikin ‘yan mintuna ta kammala komai ta gyara ko ina yad’auki k’amshi, abayinsa tayi wanka sannan tadawo d’akinta, mai tashafa tayi ‘Yar kwalliya yau harda jambaki tasaka, aiko tayi k’yau tamkar kasaceta kagudu.
Siket dariga tasaka na atanfa fara da adon jajayen fulawoyi.
Masha ALLAH nafad’a araina Dan babu k’arya Rahma tahad’u.
Kum tad’auka tana taje kanta, wani d’an ruwa daya d’id’d’iga asaman gashin yafara tsalle harya sauka akan fuskar bobo.
Bud’e ido yayi ahankali yasauke akan Rahma dake tsaye agaban madubi tana faking d’in gashinta da jan ribom.
Lumshe ido yayi yabud’e yana murmushi aransa yace masha ALLAH.
Itakam dabatasan yanayiba tad’auk’i d’ankwali ta tayi d’auri mai k’yau na zamani, tad’auki ‘yan kunne jajaye tasaka sannan takuma feshe jikinta da turarenta.
Juyowa tayi danufi fita saitaga idon bobo akanta, hannu tasa tarufe fuska tana ‘Yar dariya, shima mik’ewa yayi zaune yana murmushi, yatako ahankali zuwa gabanta, hannunsa biyu yasaka yarik’o k’ugunta, muryarsa anarke ya ce, “beautiful Lady kinyi k’yau sosai, shine kikamin wayau ko?.
Girgiza masa kai tayi haryanzu hannunta nakan fuska.
Ya ce, ” to bud’e fuskar naga kwalliyar tawa ko?, akunyace tacire hannunta, woow my beautiful wife kwalliya namiki k’yau amma bak’yasonyi, todaga yau haka nakeso aringa tsantsaramin wadda zata ringa hanani fita office.
Yabata dariya Dan haka tatuntsure da dariya, shima dariyar yayi tareda rungumeta, bayan sund’an sarara ya ce, “to muje nima kimin wankan.
Idanu tazaro waje ta ce, ”rufamin asiri.”
Asirinki arufe yake aii, shima yafad’a yanad’an zaro ido kamar yanda tayi.
Murmushi yayi, shikuma yafita yana fad’in tom bara naje nayi my cute, amma next time bazan d’aga miki k’afaba.
Murmushi Rahma tayi tareda d’aga hannunta sama tana fad’in ALLAH ngd maka daka daidaita al’amurana alokacin dabanyi zatoba.
d’akin tahau gyarawa cikin lokaci k’alilan takammala takoma falo tazauna jiransa yafito.
Shima baid’auki lokaci mai tsawoba yafito cikin k’ananun kaya wando 3½ da k’aramar Riga tashan iska duk farare tas, yasaka Jan silifas ak’afarsa, sai zabga k’amshin turarensa yake na alfarma.
d’agowa tayi tana kallonsa, yasakar mata murmushi itama ta mayar masa tareda mik’ewa, a dinning suka yada zango, tazuba musa abincin tana k’ok’arin zuba nata yarik’e hannunta tareda mata magana da ido.
Zama tayi danta fahimci inda yadosa, indai tak’aice muku dakansa yabata abinci itama tana basa, haka sukaci suka k’oshi tagyara wajen suka dawo falo suka zube.
Rahma takalli bobo ta narke murya, wai bazamuje gidan AMMIN ba?.
Ido d’aya ya kanne mata, ya ce, “a’a yau zamu huta agida musha soyayyarmu my cute.
Baki taturo kamar wata bebyn roba.
Zamewa yayi yakwanta bisa kujera yana murmushi.
Sallamar da akayice takatsema bobo maganar dayayi niyyar yi……
Rahma ta amsa tana maida kallonta ga k’ofa, ta ce, ” kushigo.
Zeenat da baseera suka shigo da sallama, mik’ewa Rahma tayi taje ta tarbosu cikin farincikin ganunsu, zeenat ta ce, “oh ni Autar ummy amare.
Hannu Rahma tasa tarufe fuska tana fad’in kai aunty zeenat, baseera ta ce, ” Yar lukutar ummi kin k’ara kibafa, aunty baseera kema hadake ko?, Rahma tayi maganar cikeda shagwa6a.
Dariya sukayi tareda k’arasawa cikin falon, baseera da zeenat suka kalli juna Dan basuyi zaton bobo yana nanba.
Zama sukayi suna gaisheshi, baiko kallesuba ya amsa da lfy amma fuskarsa asake, mik’ewa yayi yana fad’in yakuke?.
Sukace lfy lau wlhy.
Fita yayi harabar gidan danya basu waje, dandanan Rahma tacika musu gaba da kayan ciye ciye, ta zauna suka gaisa.
Zeenat ta ce, “nibanji motsin mutuniyarba.
Wai aunty safna?.
Sukace eh.
Lah tana gidansu ya Abdulmaleek aii, a can takwana wlhy. Dama tunda naganku nasan zuwantane tunda Baku ta6a zuwaminba.
Dariya sukayi baseera ta ce, ” a’a dama gunki mukazo ko zeenat, gyad’a kai zeenat tayi tana dariya.
Daganan hira sukashigayi, bayan kamar minti30 suka mik’e tareda alk’awarin suma zasu halarci bikinsu khairiyya d’in.
Godiya tamusu tarakosu har harabar gidan, bobo nasaman mota zaune, suka masa sallama sannan suka tafi.
Dirowa yayi daga saman motar idonsa akan Rahma, batayi auneba taji yad’auketa cak kamar jaririya yanufi cikin falon da ita.
Direta yayi saman doguwar kujera suna dariya, yakwanta tareda d’ora kansa saman cinyarta suna kallon juna, ya ce, “wad’an nanfa daga ina?.
K’awayen aunty Safna ne?.
Baice komaiba, saima ya kauda zancen da d’akko wani daban……………..
1
“Dan ALLAH duk masoyina yamin addu’a acikin sallarsa, ALLAH yabiyamin buk’atata ta alkairi, yakuma azurtani da abundana nake buri na alkairi.”
💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 41
Wunin ranar gaba d’aya haka bobo da Rahma suka kasheshi asoyayya da tattalin juna, dukda Rahma tanad’anjin kunyar bobo har yanzu.
Ganin shiru basuzoba Ammi takira bobo tana tambayar ko jikin Rahmar ne har yanzu?.
Cikin Sosa kai na jin kunya ya ce, “a’a ammi taji sauk’i bamuzoba daine kawai, sai gobe idan ALLAH ya kaimu.
Murmushi Ammi tayi ta ce, ” toshikenan ALLAH yakaimu goben tunda dai lfy Alhmdllh, ka gaishemin da ita
To Ammi zataji.
Rahma dake kwance ajikinkinsa ta ce, “ya Abdulmaleek ko kunya bakajiba Dan ALLAH.
Murmushi yayma tareda fad’in kunyar wa zanji?.
Ta Ammi mana.
Nanma murmushin yasakeyi batareda yace komaiba.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Shirye shiryen biki ya kankama sosai, hidima akeyi babu kama hannun yaro.
Rahma da bobo kan sai godiyar ALLAH, soyayyarsu suketa zubawa kamar babu gobe, amma dai baisake mata komaiba Dan yana tausayinta sosai, kuma bobo ba irin fitunannun mazan nan baneba, tattalikam tana shansa, azuciyarta har mamakin bobo takeyi Dan bata ta6a tunanin yanada sauk’i hakaba, ada tana masa kallon muskili masifaffe.
Amma yanzun data k’ara kusanci dashi saitaga Bahaka bane, dukda yanada fad’a amma sai anta6oshi yakeyi.+
Safna kam abin duniya ya isheta, k’iri² Ammi tahanata komawa gidansu Rahma, kayantama ranar gabad’aya bobo yakawomata gidan Ammi, bak’aramin 6aci ranta yayiba dantasan wannan Duk shirin bobone.
Yau tunda safe take tsumayensa amma yak’i zuwa gidan kamar yanda yasaba, suna zaune itadasu khairiyya dake had’a kayansu saboda daga gobe shagalin biki zai fara.
Kad’an kad’an saita lek’a window d’akinsu khairiyyar Dan daganan ana hangen Wanda zaishigo gidan, ta kalli agogon hanunta tareda yin tsaki.
Khursiyya ta ce, “aunty safna lfy kuwa?.
Murmushin yak’e tayi tareda wayancewa ta ce, ” wlhy ya Abdulmaleek nake jira sonake nakar6i sak’o awanjensa.
Su khairiyya basu kawo komaiba aransuba sukace ayya k’ila yanacan yana shan sharafin soyayarsama, kinsan su ya Abdulmaleek sai addu’a, k’ila kuma bazaizo gidanba saiya tashi daga aiki Dan wataran haka yakeyi.
Dammmmm safna taji gabanta yafad’i, azuciyarta ta ce, “soyayya kuma?, wani kululun bak’in ciki yatokare mata mak’oshi ta had’iyeshi dak’yar, zamewa tayi takwanta visa gadon su khursiyya tana sauk’e ajiyar zuciya wadda su bama sukulaba hankalinsu nakan rigima akan wani wandon jins dakowa ya ce, ” yanaso sukahau kokawa, can ALLAH yabama khursiyya sa’ar kwacewa daga hannun khairiyya ta sambad’a da gudu zuwa waje.
Itama khairiyya ta take mata baya tana fad’in wlhy baki isaba saidai kowa yahak’ura mu badashi, daidai zasushiga d’akin Ammi bobo yashigo falon da sallama.
Sanye yake cikin suit blue, komai na jikinsa blue ne amma banda belt da takalmi dasuka kasance jajaye, dressing d’in bak’aramin feeting d’insa yayiba, masha ALLAH.
hannunsa yatura cikin aljihun wandonsa yajingina da kujera yana kallonsu khairiyya daketa zagaye falon batareda sunkula dashiba.
Ganinfa bamasu gansaba yasakashi daka musu tsawa, kai!!! Wane irin iskancine wannan?, zaku maida mana gida filin polo?.
Can suka tsaya suna mazurai, yacire hannunsa daga aljihu ya nunasu Ku nakula kafin kubar gidannan saina ta6a lfyar jikinku?, dannaga wani tashen iskanci kukeji yanzu?, to ubanmiye ya had’aku?!!.
suduka saida sukad’an razana da tsawar dayayi, sukad’anja baya khairiyya ta CE, “Yaya wandonefa nad’auka shine ta kwace tagudo.
Tsaki yayi ya ce, ” wandon nawaye?.
Da Sauri khursiyya ta ce, “nawanefa, itama khairiyya ta CE, ” Yaya k’arya takeyi nawanefa.
Kansa yadafe Dan suna Neman samasa ciwonkai ma wlhy…
Ammi tafito ta ce, “miya faru kuma tom and Jerry?.
Suduka suka nufi Ammi suna mata bayani…..
Hannu Ammi tad’aga musu ta ce, ” ainagaya muku kubar sayen Abu guda d’aya saboda gudun irin wannan ranar to gashinan kun saya kuma yanzu bawaje d’aya zaku kasanceba sannan kowa yanaso.
Khairiyya tayi kwalkwal zatayi kuka, Ammi tafasan Nafi son wandon kuma nace ta d’auki rigar nitabani wandon amma tak’i yarda.
Hannu bobo yamik’a ya ce, “kubani wandon….
Jikin khirsiyya na Rawa tamik’a masa, yana kar6a ya haura saman Appa batareda yasake maganaba.
Khairiya tafara hawaye tana hararar khursiyya Ammi ta ce, ” wlhy ALLAH yabaku sa’a kunsandai halin mukarram sarai ba bak’oku bane, idan darabon saiya zaneku kuna a amare kukuka sani, idan kunason kanku da arzik’in toku kama kanku danni babu ruwana wlhy, tana gama fad’a itama tahaye saman Appa.
Jiki asanyaye suka koma d’akinsu, Safna ta kallesu tana fad’in kukuma lfy INA wandon?.
Baki Khairiyya ta turo ta ce, “bataja ya Abdulmaleek ya kwaceba.
Zumbur safna tamik’e tana fad’in yazone?.
Basu tanka mataba Dan duk haushinsa ya ishesu.
Itama bata saurari amsa daga garesuba tafito falon, jin k’amshin turarensa daya tafi yabari yasakata murmushin jindad’i, tasan yanzu yana wajen iyayensa danhaka tafito harabar gidan.
Ganin motarsa yasakata k’ara sakin wani murmushin, bud’e gaban motar tayi tashige Dan bai kulleba.
STORY CONTINUES BELOW

Shikam yanayanacan gaban Appa suna magana.
Appa ya ce, “Mukarram tunda Alhaji sunusu dala yabada hak’uri miyasa bazaka hak’ura dakaishi koti ba, bakamar yanda kayi niyya tun farko ba?.
Appa idan na k’yaleshi to bansan mizaimin agaba ba, badan ALLAH ya tak’aita wahalabafa nasan yaransa zasu iya kashe Rahma da Nawal alokacin nan, Amma shine yanzu zai dawo yana ‘Yar murya wai ayi hak’iri, naga da ko magana baya maka amma dayake yanzu yasan miya shirya shine zaizo yay maka dad’in baki akan kahanani kaisa kotu?.
Hakane mukarram amma ni aganina duk bak’in halin mutum idan yay nadamar kuskure dayayi to yanada k’ayau agafarta MASA tunda ALLAH ma muna MASA laifi kuma idan muka rok’eshi saiya yafe mana, amatsayina na mahaifinka INA rok’ama alhaji sunusi gafara agareka da iyalanka, daga nan idan yasake yunk’urin cutar dawani namu saika d’auki matakin daduk yadace bazan hanakaba saidai na taimaka maka akan hakan.
Shikenan Appa zan yafe MASA to amma Alhaji Abdurrazak fa?, na tabbata tare sukayi k’ulle k’ullen sacemin mata da ‘ya.
Eh nasani Dan yafad’ami. Shinema yazugashi akan suyi hakan, to amma wani nacin arzik’in wani aii, to shima Alhaji Abdurrazak yaci arzik’in Alhaji sunusi.
Shikenan Appa zanfad’ama Ammar karsu tura maganar kotu dama sonake agama bikinnan sannan mushiga kotu, tunda hakane zan fad’a MASA najanye amma akwai shari’ar damukeyi da Alhaji Abdurrazak akan kisan Barrister Lawan Usman D/tofa, da ake zargin su suka saka akasheshi akan wata shari’a daya tsaya da lauyansu kuma yasamu nasara.
Ranar dayaje office d’ina danyimin gargad’i kuma yaso tabbatar min dahakan saidai bodyguard d’insa yak’atseshi.
Ajiyar zuciya APPA yasauke ya ce, “a’a wannan bazan hanakaba kam Dan waccan shari’ar daban wannan daban Dan haka saidai nace ALLAH yabaka Nasara, Yakuma k’ara kareka daga Sharrin mak’iya da azzalumai, ALLAH yamuku albarka kaida sauran ‘yan uwanka.
Ammeen Appa, bobo da Ammi suka amsa.
Daganan wani zancan suka d’akko.
Bobo yakalli agogo tareda mik’ewa, Ammi Appa bara nashiga Office time na wuceawa kuma inada shari’a yau k’arfe 11:30.
To ALLAH yabada nasara jarumin babammu.
‘Yar dariya yayi yana k’ok’arin fita, to kugaidamin inna da Baba Dan bazan samu shiga wajensuba nayi latti.
To zasuji idan sun fito.
Ficewa yayi da hanzari, abakin k’ofa yaci karo da Idris tareda ya sulaiman zasu shigo.
Tofa kukuma daga ina haka?, bobo yay maganar yana mik’amusu hannu, gaisawa sukayi cikin musabaha.
Ya sulaiman ya ce, “yanzu nashigo muka had’u da idris zashi gaida su Ammi.
Bobo ya maida kallonsa ga idris, ya karatu idris?.
Alhmdllh yaya komai normal munata fama.
To ALLAH ya taimaka, ni bara nawuce nayi latti.
To ALLAH ya tsare yabada sa’a.
Ameen ngd.
Ya sulaiman ya ce, ” yauwa idan katashi kuma Kannada lokaci plss kad’an biyo ta asibiti dama inason ganinka.
Okey babu damuwa saina shigo.
Okey saina ganka shima ya sulaiman yafad’a suna nufar ciki shida idris, shikuma bobo yafito.1
Motarsa yanufa hankali kwance yabud’e yashiga yana fad’in masha ALLAH yanzu kuma sai office.
Idan ka gama dani ko?……..
Da sauri bobo yakalli gefensa dan son ganin waye?.
d’aure fuska yayi tareda fad’in miyasa kina shigarmin mota?, wama yabaki izinin shiga?.
Wani murmushi Safna tasaki tareda k’ara lafewa cikin kujerar tana shak’ar k’amshin mortar da turaren bobo, tayi far da idanunta tana kallon k’yak’yk’yawar fuskarsa, aibasai anbani izinin shiga motar mijina ba, tayi maganar tana d’an d’aga gira.
Kauda kansa yayi daga kanta tareda k’ara had’e fuska, ke banason k’aramin iskanci fitarmin amiota.
Safna ta marairaice fuska harda hawaye, cikin muryar kuka ta ce, “Dan ALLAH ka saurareni wlhy magana nazo muyi kuma mai muhimmancice.
d’agowa yayi yakalleta haryanzu fuskarsa ad’aure take, ganin tana kuka saikuma tabashi tausayi, bayason mutum yashiga damuwa akansa, yad’an huro iska daga bakinsa tareda kallon jan agogon fatar dake hannunsa 8:45, batareda ya kalletaba ya ce, ” nabaki minti5 Dan inada abinyi.
Hawayen fuskarta ta share ta ce, “wlhy minti5 yamin kad’an pls ka k’aramin.
d’agowa yayi yad’an kalleta saikuma ya kauda kai, saidai ki hak’ura kuma saina taso daga aiki Dan yanzu haka nayi latti, so idan nadawo zanzo nan saiki sameni amma ki tabbata magarki tanada muhimmanci, kuma ki tabbata itace magana tak’arshe dazata shiga tsakaninmu daga ita kifita arayuwata, ina d’aga miki k’afane saboda banaso nazama silar rushewar zumincin iyayenmu, sannan bazan iya wulak’anta jinin Rahma ba, dan itama bata wulak’anta jininaba.
Batareda yasake kallontaba yatada motarsa, ya ce, ” sai anjima.
Jiki a sanyaye Safna ta bud’e motar ta fito, hakan yayi daidai da fitowar ya sulaiman da idris.
Suduka cikin mamaki suke kallon Safna da kuma motar bobon.
Bobo dake kallonsu ya sulaiman ta madubi yad’anja tsaki, dama abinda yake gudu kenan, ganin ya sulaiman kamar yanufoshi yaja motar da sauri yabar gidan Dan bayason tambaya, musammanma akan safnar.
Cak ya sulaiman ya tsaya yabi motar da kallo har bobo yafice daga gidan, kallonsa yadawo dashi akan Safna dake ida share hawayenta.
Rissinawa tayi tana gaisheshi sannan tara6a ta gefensa zata wuce.
Jimana ya sulaiman yafad’i yana kallonta.
Safna tatsaya harya k’araso gabanta suna fuskantar juna, lfy kuwa mike faruwa?.
Babu komai safna tayi magana muryarta nad’an rawa, shiru ya sulaiman yay yana kallonta da nazarin yanayinta, yad’an gyara tsayuwarsa yana sauke numgashi, ya ce, “keba yayar Rahma bace?.
Yayartace, cewar Safna.
To amma miya had’aki da Abdulmaleek? har kike kuka?.
d’ago ido tayi ta kalleshi, bazata iya kallon idonsaba Dan yana mata kamada na bobo, tayi shiru batareda ta iya cewa komaiba.
Ganin bazatayi maganaba ya ce, ” to shiga cikin….
Da sauri tawuce batareda ko juyowaba.
Shima binta yayi da kallo cikin mamakin miye tsakaninta da bobo?, bai zargi komaiba Dan yasan bobo dodon matane, bazai ta6a zarginsa da fasik’anciba, amma tabbas akwai wata ak’asa tunda har bobo yafice daga gidan Dan bayaso suyi magana.
Yabud’e motarsa yashiga zuciyarsa cike da waswasi, shima ficewa yayi da zummar zai tambayi bobo inhar sun had’u.
STORY CONTINUES BELOW

++++++++++
a6angaren bobo kam yana fita office yanufa kai tsaye.
Sakatariyarsa ta gaishesa cikeda salo kamar yanda ta saba, babu k’arya yau wankan bobo yakasheta, datanada dama har pic zata masa.
Turare tad’auka tafesa tareda k’ara kallon kanta amadubi, komai daidai, tagyara zaman siket d’in material d’inta da rigar, shima mayafin aka sake salon yafawa sannan. Tanufi office d’in.
Masinja Kamilu dake la6e yana kallonta Dan yasan dolene indai oga yashigo saitayi gyare gyarennan ya tuntsure da dariya yana fad’in kai iska na wahalar da maikayan kara, kedai awahala zaki k’are yarinya, mutum kamar wannan aii kasan matarsama abar kalloce, tomizai tsaya kallo ajikinki wannan karfata.
Itadai Sakatariya Madeena😂😜 dabatasan masija nayiba tanufi office d’in cikin takun k’asaita da salon yanga irinta d’aukar hankali.
Bobo na zaune akan kujerarsa ta alfarma yana rubuce rubuce sakatariya tayi sallama.
Bai d’agoba amma ya amsa mata, yad’ora dafad’in waye yazo nemana?.
Lissafa masa tafarayi daga k’arshe ta ce, “ad’arare sai Alhaji sunusi da la..
Tak’are maganar da in ina.
Dukda haka bai d’agoba sannan baice komaiba itakuma baice tatafiba.
Araina na ce, ” mulki kenan.”
Yakai kusan minti 4 yana rubuce rubucensa saida yagama sannan yad’ago yana linke takardar.
Mik’a mata yayi, tamatso tareda rissinawa takar6a.
Yamaida bayansa yakwantar ajikin kujerarsa yana d’an lilawa kad’an, idonsa akanta ya ce, ke yanzu dakikayi shigar mutunci bakijin kinfi kima a idon mutane ba?, amma da ko kunya bak’yaji kisakko kananun kaya kina tallar jikinki ga jama’ar gari da sunan wayewa, wannan ba wayewa bace shashancine, ki kama kanki sai miji nagari yaganki yasoki, shigar banza babu abinda yake jawomuku sai mazan banza suyita bibiyarku dankoba ‘yan iskanbane tofa kallon ‘yan iska irinsu suke muku, ki kiyaye banason shashanci.
Kaita gyad’a duk kuma sai jikinta yayi sanyi, ta ce, “sir ngd ALLAH yak’ara girma da d’aukaka yatsareka daga sharrin mak’iya.
To amin, ALLAH yasa mudace yafad’a yana d’agowa daga kwanciyar dayayi akujera, yanuna takardar hannunta, wannan takardar kibama Kamilu yakai office d’in Barrister Kamal Abubakar, yatsaya yakaranta yabasshi Reply yakawo min.
Okey sir madeena sakatariya yafad’a tanad’an rissinawa cikeda girmamawa.
Hartakai k’ofa tajuyo sir baka buk’atar wani Abu?.
Kai bobo ya girgiza mata yana jawo laptop d’insa daga cikin jakka.
Itama ficewa tayi tana fad’in OK sir.
Tana fita ta tararda Kamilu zaune akujerar dake gefen tebir d’inta, fuska ta had’e dantasan gulmace ta kawoshi.
Ilaikuwa kallonta yayi yana ‘Yar dariya, madee ince dai yau andace oga ya k’yasa?.
Harararsa tayi tareda fad’in ban saniba magananne ni dalla kar6i oga ya ce, ” ka kaima sir Kamal, kuma kajira yabaka Reply ka kawo masa.
Mik’ewa yayi yakar6i takardar, to madee bara naje nadawo muyi magana, tunda har yanzu oga yak’i k’yasawa nisaina taya.
Wata uwar harara tawatsa masa, kaidai shashashane Kamilu, yoko mazan duniya sun k’are aibanga abinda zanyi da sakaren namiji irinkaba.
Tab yarinya aii ba’a fuska ake gane sakaran namijiba.
Tsaki tayi tareda mik’ewa wlhy zanje nafad’ama oga baka tafiba.
Da sauri yawuce a’a Madeena rufamin asiri Dan ALLAH, wannan zakin faman yanzu saiya hau kaina aii.
raka bayansa tayi da harara, taja tsaki tazauna tana mita.
Bobo yakalli wayarsa dake wringing ganin Ammar yasashi d’aukar wayar da hanzari, gaisawa sukayi tareda tsokanar juna kamar yanda suka saba.
Bobo ya ce, “dama kobaka kiraniba zan kiraka.
To miya faru angon Rahma?.
Murmushi bobo yayi, ya ce, ” so inaga anjima zanshigo gidan saimuyi magana atsanake yanzu time d’ina k’urarrene nanda ‘yan mintuna kad’an zanshiga wata shari’a.
Okey babu damuwa to saina ganka, nima inada ganawa da Governor nanda minti 10.
Hummm mutumina kuna sha’aninkufa, idan kukayi wasa duk ad’aure zakuje lahira Dan daku ake mulkarmu ak’asarnan.
Dariya Ammar yayi ya ce, “masheranci aii kaima ad’auren zakaje indai hakane.
Can abakinka d’an fatan tsiya sai anjima.
Yanke wayar sukayi suduka suna dariya.
Harzai ajiye wayar saikuma yafasa yakira Rahma.
Tana zaune afalo ita kad’ai tana kallon wani India film, takalli wayarta dake wringing, ganin sunan dake a screen d’in yasakata murmushi, *_Nurulk’albee_*, d’auka tayi muryarta can k’asan mak’oshi tace amincin ALLAH ya tabbata agareka ya *_Nurulk’albee._*
Wata sassanyar ajiyar zuciya bobo yasauke, murya akasalance ya ce, ” kema amincin ALLAH ya tabbata agareki my *_Nusfulhayat_*. Ina fata kina cikin k’oshin lafiya da kuzari?.
Alhmdllh sai godiyar ALLAH kam.
Wani k’asaitaccen murmushi yasaki Wanda hartanajin sautinsa akunnenta, ya ce, “nagodema ALLAH da kika kasance cikin k’oshin lfy, kinga kenan yau za’a kar6e ni 100/100 abani kulawa ta musamman awajen barci.
Kamar tana gabansa tafara buga k’afafu cikin shagwa6a ta ce, ” nidai a’a wlhy inajin tsoro kuma har yanzu wajen akwai zafi.
Yanda take masa magana cikin shagwa6a yasaka jikinsa yin sanyi, k’ara lafewa yayi acikin kujerar yana shak’ar kamshin turarensa dana office d’in, yakuma narke murya can k’asan mak’oshi haba my Angel kedai kincika tsorone kawai, amma yau kwana hud’u ace haryau anajin zafi?, kodai ana gudunane?.
Hannu tasaka tarufe fuska wai ita kunya kamar tana gabansan, nidai Dan ALLAH kabarmin wannan maganar banaso.
‘Yar sassanyar dariya yayi harda shashsheka wadda tasaka Rahma shagala tana saurarensa, ya ce, “shikenan idan nadawo gida zamuyi aii, kafinma nadawo kisaka d’iyarki tayi barci, ummuch💋 yamannama wayar kiss, batareda yajira amsartaba ya yanke Kiran.
Lumshe ido Rahma tayi tana murmushi, afili ta ce, ”kai maza sai’a barsu sudai ko kunya basaji?.
Shimadai a can murmushi yayi, yamik’e yana had’a takardu, yad’auki k’atuwar rigarsu ta lauyoyi tareda hular yarik’e sannan yad’akko siririn farin Gil’s d’insa yasaka yafice domin gabatar da shari’a……………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 42
_5:12pm_* bobo yamik’e tareda harhad’a takardun dazai buk’ata agida, yacire laptop d’imsa daga caji yasaka a jakka, bayan yagama had’a komai yakashe kayan wutar office d’in sannan yad’auki rigarsa ta lauyoyi ya sak’ala ahannu, yarataya jakar aikinsa akafad’a yafito.
Da sauri Kamilu yataso yana fad’in oga kafito?.
Nafito kamilu, zan wuce gida kuma.
Kamilu ya washe baki tareda kar6ar key d’in hannun bobo ya kulle k’ofar, fitowa sukayi har wajen mota yarakishi, Dan tuni sakatariya Madeena tana gida, k’arfe hud’u da rabi yake sallamarta ita.
Saida yashiga motar sannan yad’ago yana kallon Kamilu, to kashigo muwuce mana Dan naga garin kamarma hadarine.
Dariya Kamilu yayi yabud’e mortar yashiga yana fad’in oga ai damunar tafara kankamane, nanda ‘yan satittika zakaga ruwa yafara wadata.
Murmushi kawai bobo yayi danyasan surutun Kamilu baya k’arewa, ahankali yake Murza kan motar yana kuma sauraren karatun alkur’anin dake tashi amotar cikin k’ira’ar shriek Abdurrahaman sudes, har k’ofar gida yakai Kamilu yamik’a masa kud’i yana fad’in gashi asaima uwargida kaza.
Cikin washe baki Kamilu yakar6a yana godiya, wannan dalilin yanasakashi k’ara ganin kimar ogan nasu, kwatakwata bashida k’yankyamin talaka bare girmankai irinna alhazan birnin nan, gashida alkairi kullum baya gajiyawa.
Har bobo yafice daga anguwar Kamilu natsaye yana kallonsa, saida ya6acema ganinsa sannan yashiga gida cikeda farinciki.
Ganin hadarin nak’ara tasowa yasaka bobo k’ara gudun motarsa cikin ‘yan mintuna k’alilan ya Isa gida, guri yasamu yay parking sannan yakwashi tarkacensa yanufi ciki, zuwa sannan anfara yayyafi.
Rahma tana kichin Dan k’ok’arin had’a abincin dare taji ana kwankwasa k’ofa, fitowa tayi da hanzari dakuma tunanin wanene haka? Acikin hadarinnan.
Batayi gaggawar bud’ewaba saida ta ce, “wayene?.
Jin haka yasa bobo niyyar tsokanarta, ya mak’e murya kamar mace ya ce, ” nice hafsat Xoxo budurwar bobo.
Gabantane yafad’i gakuma wani k’ululn bak’inciki aranta, cikin masifa ta ce, “ai bayanan saiki koma sai sanda yadawo kizo.
Pls madam ki taimakeni ruwafa na jik’ani.
Yo ya kasheki mana, Rahma tafad’a ak’ufule tareda juyawarta kicin.
Magana yasakeyi yaji shiru, ga ruwa yafara jik’ashi, da Sauri yanufi baya yaduba ko k’ofar kichin abud’e take ta baya, yana turawa tabud’e, yashigo da hanzari Dan tasowar wata iska mai sanyi.
Da sauri Rahma tajuyo dansan ganin waye, ido tad’an zaro waje Dan mamaki, sannu dazuwa tayi maganar a cunkushe Dan tuna abundana yafaru yanzu tsakaninta da Xoxo.
Dariya tabashi danganin kishi k’uru k’uru kwance afuskarta, amma saiya gimtse ya ce, ” yawwa.
K’arasowa tayi inda yake tsaye takar6i jakarsa da rigar, sai wani kakkauda kai takeyi.
Lfy kuwa?, naganki haka?.
Lfy lau tafad’a tana nufar cikin falo.
Binta yayi da kallo yana murmushi, zame rigar suit d’insa yayi danta d’an jike yaja kujerar dake kicind’in ya zauna yana cire takalminsa.
Rahma tadawo kichind’in ganinsa azaune yasata binsa da kallon mamaki, dukda yaji shigowarta amma bai d’agoba saida yagama cire takalmin yad’ora k’afarsa fara Sol Asama.
Rahma ta ce, “azuciyarta, hummm jik’afa kamar ba’a takata ak’asa……..
Bobo yad’ago shima yana kallonta, nikam Nusfulhayat wana ganin ak’ofar falo tsaye kamar mace?.
Baki Rahma taturo gaba, ta kauda kanta gefe, nima bansaniba.
Ido yazaro waje bakisanibafa kikace?, datazo batayi Knocking bane?.
Hawayen datake mak’alewa suka zubo akumatunta, cikin shagwa6a ta ce, ” bakai tazo nemaba, kuma ta ce, “budurwarkace ita.
Yaso ya shek’e da dariya amma saiya dake, yamik’e da Sauri yana fad’in amma kika barta awaje ruwa na dukanta, yanzunan cute sokike kifara korarmin ‘yammatane?, kwasar takalmansa yayi ahannu yawuce cikin falon.
Rahma taduk’e kanta ajikin cabinet d’in kicin tana kuka.
Shikam bobo d’akinsa yanufa yana ‘Yar dariyar farincikin ana kishinsa Ashe?, kayansa yacire yafad’a wanka.
Itakam Rahma saida taci kukanta ta more sannan tad’ago tacigaba da girkin, jitake dama batayi MASA girkinba, tsaf ta kammala komai tajere a dinning sannan tagyara kichind’in tsaf.
Dubanta takai ga agogon falon, ganin lokaci yayi nisa tanufi d’akinta ta tatada Nawal dake barci Dan magriba ta k’arato, hannunta taja zuwa bayi tawanke mata fuska sannan suka dawo falo tabata ruwa…….hummm ni shinema yau ko ruwan ba’a baniba bare akula dani, maganar bobo tadaki dodo kunnenta.
Da Sauri Nawal takwace hannunta taje tarungumeshi tana fad’in my papa oyoyo.
Shima d’aukarta yayi yad’aga sama, my baby INA kika shigane bangankiba?.
Papa barci nakeyi yanzu momyna ta tadani magriba tayi.
Oh ‘yargatan momynta yafad’a yana sumbatar kumatun yarinyar.
Rahma dai tana tsaye tana kallonsu cikeda sha’awa, hannunsa yasa yakare fuskar Nawal sannan yad’agama Rahma gira, kauda kai tayi tanad’an murgud’a baki.
Ya ce, “Niko?.
Nidaifa banceba ehe, itama tafad’a kamar badashi takeba.
Murmushi yayi sannan yadire Nawal, baby sauka nasha ruwa tunda an hanani.
Da d’an gudu Rahma taje gaban firij tad’akko ruwa da cup takawo MASA.
Bobo yayi dariya tareda fad’in ashedai ana tsoron kishiya.
Gaba tayi tashige d’akinta tana tura baki, shikuma yazuba ruwa a cup yasha yana dariya.
Nawal ta CE, ” papa yaushe zamu tafi gidan Ammi?, gobene bikinsu aunty khursiyya.
Saida ya shanye ruwan sannan ya ce, “jekiyi sallah idan nadawo masallaci zan sanar miki.
d’akin momynta tanufa shikuma yadoshi hanyar fita, yabud’e sannan yad’an lek’a, ruwa akeyi sosai Dan haka yahak’ura yajuya d’akin Rahma dansuyi jam’i.
Shigar tasa tayi daidai da fitowar Rahma daga bayi, da alama alwala tayi, baice da ita komaiba ya gyara shimfid’ar sallayar, itama ganin haka yasa tagane abinda yake nufi.
Yana gaba suna baya itada Nawal yajasu jam’in magriba.
Bayan sun idar Rahma ta d’akko alkur’ani tana koyama Nawal, shima yana zaune yana kallonsu cikeda jin dad’i, har lokacin sallar isha’i yayi suka mik’e domin gabatarwa.
Saida yamusu doguwar addu’a sannan kowa yamik’e suka fito falo.
Bobo yazube saman kujera yana fad’in wash ALLAH na, Nawal tazauna kusadashi my papa bakada lafiyane?.
A’a baby nagajine kawai……. ga abinci fa….Rahma takatse musu zancen tana kallonsu.
Fararen idanunsa yad’ago yana mata wani shu’umin kallo, ta kauda idonta daga kansa shima saiya ta6e baki.
Nawal tamik’e shikuma ya ce, “nidai nagaji bazan iya hawan dining ba.
Yanda yay maganar ashagwa6e saiyabama Rahma dariya, dinning tanifa tana murmushi, komai saida suka sakko dashi tsakkiyar falon.
Tana niyyar zuba abincin taji ya ce, ” kihad’amana a filet d’aya kawai, batace k’alaba tacigaba da zuba abincinta, bayan tagama ta tatura gabansa.
Gyara zamansa kawai yayi yafara cin abincin atsanake, Rahma azuciyarta ta ce, “guy d’innan komai yahad’a, cin abincinsama abin kallone.
Hakadai suka gama cin abincin anutse, daganan aka koma kallo, Nawal najikin papanta kwance yana shafa kanta ahankali.
Tuni barci yad’auketa, yakalli Rahma dake kwance a 2sita tana game da wayarta, momyn Nawal zoki d’auketa tamin barci ajiki.
Mik’ewa Rahma tayi domin d’aukar Nawal amma saiya jawota ta zauna akusadashi, hannunta yarik’e gam sannan yashiga k’ok’arin janye Nawal daga jikinsa cikin dabara.
Rahma ta turo baki gaba, yatsu biyu yasa ya d’alli bakinta, da sauri tasaka hannunta awajen Dan zafi, cikin shagwa6a ta ce, ” wayyo bakina.
Habawa yarinya nagafa kamar kinfara rainani, bobo yay maganar yana matseta ajikinsa.
Shinwai ni sa’ankine?.
Da sauri Rahma ta ce, “a’a dantaji zafin d’allar mata baki dayayi. Ya ce, ” to miye kiketa wani kumbura fuska?, nifa babu komai kaina yake ciwone.
Ayya my Angel sorry, namiki kamu?.
Kai tad’aga masa alamar eh.
Ahankali ya kwantar da ita acinyarsa, maimakon yamata kamunkai saitaji bakinsa akan nata, tabud’e baki zatayi magana yasamu damar zira harshensa……+
STORY CONTINUES BELOW

🚶🏻♀baya najuya musu karsuce nacika saka musu ido.
Saida aka d’auki tsawon lokaci sannan na juyo Dan inada tabbacin komai ya kammala.
Raham nagani tana cusa kanta acikin bobo suna dariya, da alama wani abun yafad’a mata taji kunya.
Ya ce, “kinga tashi muje mu kwanta, mik’ewa tayi cikin jin kunya, ta d’auki Nawal takai d’akinta, kayan barci ta canja mata itama ta canja, tana k’ok’arin hayewa gado saiga Bobo yashigo sanye cikin kayan barci shima.
Kallo d’aya tamasa ta kauda kai, shima baibi ta kantaba yamatsa kusada Nawal yamata kiss akumatu sannan yaja bargon yarufeta yana fad’in saida safe d’iyar albarka.
Itadai Rahma batace komaiba Dan harta kwanta agefen Nawal, jitayi anyi sama da ita, tafara wutsil wutsil da k’afafu wayyo ya Abdulmaleek kabarni barci nakeji, nidai yau bazanbar Nawal ita kad’aiba, pls kabarmu mu kwanta.
Bai sauraretaba har yakaita d’akinsa yadire agadon, tana k’ok’arin tashi yasa k’afa ya danneta, wayoyinsa yad’auka ya kashe sannan shima yahaye gadon yakwanta tareda jawota jikinsa.
Itakam tuni tafara kuka zuciyarta cike fal da tsoro, jin yafara mata abinda hankalinta bazai d’aukaba tafara kuka tana zame zame.
K’ara matseta yayi ajikinsa yana k’ara rud’a jikinta da sakwanni wad’anda sukeyin tasiri ajikinta da zuciyarta, amma kuzarinta na k’ok’arin turesu domin ku6tar kai.
Ina mutumin naku baiko saurara mataba Dan tuni jikinsa da ruhinsa sun Lula duniyar begen aika aikar dayakeyi, da zafifi yake aikamata sak’wannin soyayyarsa, kafin tafarga yad’auki hanyar mallakarta daga ita har zuciyarta Dan tuni itama tabada kai dukda d’unbin tsoro da fargaba dasuka kanainaye ilahinrin lungun da sak’on zuciyarta.
_Hummm masu karatu nima bara naja camryn 🚶🏻♀k’afafuna nanufi wajen angona kuma sarkina mamallakin zuciyarta da ruhina_ *_{Abdus’salam)_* d’ina adon zuciyata😘😂.
_washe gari_
Hummm yaukam na iso amakare Dan natarar har Rahma tagama tsaftace ko ina na gidan, takuma had’a breakfast mairai da lafiya.
Zaune na isakesu a dinning suna karyawa, Rahma da bobo dasun had’a ido saisu sakarma juna murmushi, bobo kam harda d’aga mata gira, takan kauda kai tana murmushi Dan gudun kar Nawal tafahimci wainar da suke toyawa.
Bayan sunci sun k’oshi suka mik’ewa tareda yin hamdala ga sarkin sarakuna mai k’yauta da k’ari.
Bobo yad’auki jakar aikinsa ya rataya, yaukam sanye yake cikin wani farin yadi mai laushi, Wanda akaima ado da bak’in zare, rigar dakad’an tawuce d’uwawunsa amma yayi d’as aciki kamar kazauna kayita kallonsa,
_Hummm karkuma ka kalla k’ilu tajawo bau, Rahma ta ce, “kana kalan mata miji🤥, my Xoxo ki kalleshi kad’an keda Rano_o😎.
Rahma tasakama Nawal jakarta abaya sannan tad’auki d’an kwandon abincinta suka fito, itama Rahma sanye take da shadda ruwan k’asa mai turuwa zani da Riga, tasaka farin hijjabi har k’asa Asama.
Saida suka fara sauke Nawal a school sannan Bobo yad’auki hanyar gidan Appa.
Juyowa yayi ya kalleta hayateena awajefa zan saukeki dannayi latti.
Itama kallonsa tayi sannan ta kalli agogon motar ta ce, ” k’arfe 7:34am yanzu”.
Eh nasani, sonake naje office dawuri yau, nayi duk aikin dazanyi zuwa 4 nadawo gida mukasance tare.
Hannu Rahma tasa tarufe fuska tana ‘Yar dariya, ALLAH kana bani kunya.
Murmushi yayi idonsa atiti ya ce, “tom nadaina baki kunya Nusfulhayat d’ina mai kuka, yaya Dan ALLAH kabini ahankali, daddyn Nawal wlhy yauma a kwai zafi, wayyo ummina kizo ki cecen………..
Bata bari yak’arasaba tasaka MASA kukan shagwa6a.
Ohh sorry my cute nadaina fad’a, cikin dariyar shak’iyanci yay maganar.
Maigadi yabud’e masa gate yashiga, ko gama tsayawa da motar baiyiba tafice tayi cikin gida.
Binta kawai yayi da kallo yana murmushi, afili ya ce, “wato idan ka auri yarinya k’arama tana maka ta6ara kaima saika zama ta6ararre, ya shafa sajensa daya kwanta luf, yad’an lumshe ido yana fad’in ALLAH yak’arama ANNABI daraja da fadila da Wasila.
Rahma kin mallake *_Barrister Abdulmaleek Aliyu Abdulmaleek hamshak’i_* gaba d’ayansa da komai nasa, kin mantar dani damuwata gabad’aya, ya ALLAH kak’ara mana soyayyar juna, kakuma nisanta shaid’an daga garemu.
Na ce, ” Ameen bobon Rahma.
Fitowa yay shima yanufi cikin gidan, babu kowa afalon sai kamshi dake tashi da sanyin AC.
Shiru yay atsaye yana nazarin gidan, sallamar Baba hansai mai Aiki yasakashi juyowa, ta ce, “a’a Alhaji kaine agidan.
Murmushi yamata sannan yarisina ya gaisheta, baba hansai masu gidan basu tashi bane?.
Khairiyya da khursiyya sun tashi tun d’azu, amma banga Ammi ba gsky.
Okey bara to nawuce office kawai saina dawo.
To Alhaji bazakaci komai bane?.
Ahhh baba nidanake da mata, ai tuni nafita agandu.
Dariyar jin dad’i baba hansai tayi, ta ce, ” to madallah Alhaji, ina Nawal da mamanta?.
Nawal na makaranta, mamanta kam tana nan cikin tare mukazo, kud’i yazaro a aljihu yamik’a mata yafice.
Itakuwa tarakashi da k’yawawan addu’oi.
Rahma kam koda tashigo taga falon babu kowa saita wuce d’akinsu khursiyya, cikeda ihun murnar ganinta suka tashi suka ruk’unk’umeta, akan gado suka zube suna dariya.
Daga nan hira suka farayi.
fitar bobo badad’ewa safna tafito daga bayi, dama tana wanka sanda Rahma tashigo.
Rahma ta gaisheta, da k’yar ta amsa, itakam batabi takantaba Dan abunda su khairiyya suke nuna mata ya d’auke hankalinta.
Khursiyya ta ce, “aunty Rahma wai waya kawokine?.”
Ya Abdulmaleek mana Rahma tafad’a tana dariya.
Kai yana ina?.
Inaga yakoma Dan yace dama bazai shigoba sauri yakeyi.
Ajiyar zuciya Safna ta sauke aranta ta ce, “yagama guje gujensa yazo yasameni daram.
Sudai su Khairiyya dabasusan tanayibama hirarsu suketa zugawa suna kwasar dariya kamar wasu k’awaye……………..
*_💃🏻Taka rawar gani akalla kome kayi kanka duniyace, mai jimirin zama cikinta, shike zuga kansa d’an magori._*
(zancenka haka yake nura m inuwa😎).💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 43
Sai wajen k’arfe biyar su bobo suka dawo gidan, kamar had’in baki suka dawo kusan lokaci d’aya suduka hud’un, bayan kowa yafito daga motarsa suka gaisa cikeda k’aunar juna.
Ya Hamza ya ce, “lallai gida yafara kar6ar bak’i irin wannan hayaniya.
Dariya sukayi gabad’aya, ya ishaq ya ce, ” tokumu k’arasa ciki..
Cikin falon suka nufa suna ‘Yar hirarsu da dariya.
Na ce, “masha ALLAH, biki ya kankama Dan falon yad’an cika da bak’i wad’anda suka iso yau, ga hayaniyar yaransu ya ishaq daketa wasa da yara sa’anninisu bak’i.
Su bobo suka rissina suna kwasar gaisuwa, kowa kallonsu yake cikeda sha’awa, bayan gaisuwa aka ta6a ‘Yar hira da tsokanar juna, shidai bobo banda murmushi babu abinda ya iya, dama haka yake ko tsokanarsa kakanni sukeyi iyakarsa murmushi, amma baya iya maida murtani, saidai ‘yan uwansa idan suna kusa su kare masa.
Yanzuma wata ‘Yar tsohuwa ke tsokanarsa, ta ce, ” mai sunan Alhaji wai kaidai kana nan babu canji?, maganama wahala take maka bare dariya?.
Nanma murmishi kawai bobo yayi kamar yanda yasaba baice komaiba.
Ya sulaiman ya ce, “Hajiya iya aii maganar Abdulmaleek tsada gareta saikin saya da kud’i.
Yo sule mizanyi da maganarsa nikam barema na siya, wannan sai matarsa dai amma baniba.
Dariya suka saka gabad’aya falon.
Bobo Yakama gemunsa nagayu yana shafawa fuskarsa cikeda murmushi, ganin zasu saka rayuwarsa gaba yamik’e ya haye saman benen, aiko suka rakashi da dariya, ya ishaq ya ce, ” Hajiya iya kinga kin koreshi?.
Isahaqa ai dankar yayi maganane yatashi, nibansan halinwa mai sunan Alhaji yakwasoba?, tunda nake ban ta6a ganin muskilin mutum irinsaba, mifa zan iya k’irga maganarsa mai tsawo danaji atsawon rayuwata, mutum kulum dund’un dunkum, sai murmushi shima idan ya gadamar yi.
Dariya aka sakeyi, su ya Hamza suka mik’e suna dariya, suma sama suka haura, cikin dariya da zolaya ya Hamza ke kiran Dund’un Dunkum! Kana inane?.
Bobo dake zaune kusada Ammi yaturo bak’i gaba, ammi kingansu ko?, wlhy nasan dani suke.
Murmushi Ammi tayi kafin tabashi Amsa su ya sulaiman suka shigo d’akin suna dariya dacigaba dakiran dund’un Dunkum.
Ya Hamza ya kalli bobo haba Dund’un Dunkum ya munata kira kaki amsa mana?.
Hararsu yayi cikin sigar wasa, ya ce, “halan faratun tsohurcan ce tafad’i sunan nan?.
Ammi dake k’unshe bak’i tana dariya ta rankwashi kan bobo, mukarram k’aniyarka wace faratun?..
Uhhhchch bobo yafad’a Dan zafi yana dafe kai, wayyo Ammi ALLAH da akwai zafi.
aidama dankaji zafin namaka tayi maganar tana k’ara kai masa wani rankwashin.
Da Sauri ya kauce, su ya ishaq suka saka dariya, gefe bobo Yakoma yana turo bak’i kamar wani k’aramin yaro, sai shafa Inda Ammi ta rankwasheshi yakeyi.
Sudai su ya hamza dariya suketa masa.
Ana cikin haka Appa yashigo d’akin da sallama, duk cikin dariya suka amsa harda ammi, Amma banda bobo dake gefe zaune ya shagwa6e fuska.
Tofa dariyarmi kuma akeyi uwa da ‘yayanta?, Appa yafad’a yana zama abakin gadon Dan duk su ya Hamza suna ak’asan kafet ne zaune.
Bak’i bobo Yakuma turowa ya shagwa6e fuska kamar zaiyi kuka, Appa nifa sukema dariyarnan.
Kai kai kowa ya saurara, yazaku tasamin babana a gaba kuna dariya?, haba Ammi harda ke?. Babana zonan naji miya faru?..
Tasowa bobo yayi yazo yazauna kusada k’afafun Appa, yad’ora Kansa bisa cinyarsa, Appa yasaka hannu yana shafa kan bobon dayawani narke kamar yayayye.
Babana mikayi ake maka dariya haka?.
Appa ba Hajiya iya bace tacemin wai Dund’un Dunkum shine suka tasani gaba da dariya, ita kuma Ammi Dan nacema Hajiya iya ‘Yar fara shine tarankwasar min kai, kumafa kaina harya fara ciwo.
Shima Appa sunan yabashi dariya wai Dund’un Dunkum, amma saiya gimtse saidai yayi murmushi, yacigaba da shafa kan bobo kaga mukarram d’ina barsu duksai na Rama maka, kowa saimun za6i suna sannan musaka masa.
d’agowa bobo yayi yana dariya shima, aii Appa harnama tanadi sunan dazan saka musu sai ranar deener zan fad’a idan za’a gabatar da manyan yayye yakare maganar dayimusu gwalo.
Appa yasaka dariyashida Ammi, sukam su ya ishaq kowa ya tsaya da dariyarsa suna hararar bobo Dan sun San zai iya aikatawa sarai.
Ya sulaiman ya ce, “haba bobon Ammi garadai kafad’a anan komai ya wuce.
Hum’im ban yarda da wayonba a can zan fad’a dankuji ehe.
Kaga sulaiman barsa yafad’a d’in , ALLAH yakaimu muma aisaimu fad’a, muce INA yayansu Amarya Dund’un Dunkum.
Appa ka gansuko?, bobo yay maganar cikeda shagwa6a.
Yanzunkam kowama saida yadara harsu aunty Rasheda dake k’ok’arin shigowa Dan gaida Appa, dama duk suna tsaye tun d’azun sunajin diramar family d’in, kowa sai kunshe bak’i take tana dariya dankar ajisu, zuwa yanzun sun kasa rik’eta Dan haka suka sheke da dariya suduka suna shigowa cikin d’akin.
Ya Hamza ya ce, “ALLAH bobo kaji kunya, wai yaushene zaka daina shagwa6ar nan takane?, Rahma kina fama gsky.
K’asa Rahma tayi da kanta tana dariya, Dan maganar ya Hamza tabata kunya.
Bobo ya kalli Rahma dake dariya tana to she bak’i da hannu, ba k’aramin birgesa tayiba.
Safna ma dai yau ba abarta abayaba Dan dariyar takeyi, ba k’aramin birgeta shagwa6aar bobo tayiba.
Saida aka tsagaita da dariya su Rahma suka gaida Appa, ya amsa fuskarsa wasai.
Mik’ewa su Aunty Sameera suka fara da zummar Fita su basu waje.
Appa ya ce, ” a’a INA zakuje kuma?, kuzauna ayi hirar zumunci asamu ladan juna, komawa sukayi suka zazzaauna cikeda kunya da k’aunar sirikan nasu masu kamala da dattako.
Hira aka cigaba dayi cikin farinciki har aka kira sallar magriba kowa ya mik’e mazan suka wuce masallaci, sukuma kowa yayi alwala sukayi agida.+
STORY CONTINUES BELOW

Basu dawoba saida akayi isha’i.
Safna dake la6e ajikin motoci tayi saurin rik’o rigar bobo.
Da Sauri yajuyo dansan ganin waye?, ganin Safna yasashi saurin zare ido, ya maida kallonsa gasu ya ishaq yaga babu Wanda yajuyo harma sun shige falo, hamdala yayi azuciyarsa dabasuga aika aikar da Safnar tayiba.
Juyowa yayi yana kallonta fuska a gimtse ya ce, “sakarmin Riga.
Babu musu tasaki Dan gizagon fuskarsa yabata tsoro, ta marairaice fuska kamar zatayi kuka ta ce, kacika “alk’awari.
Yagane mitake nufi amma dukda haka saiya yatsine fuska ya ce, ” alk’awarin mi?, ke nifa kin addabawa rayuwata.
Safna ta marairaice fuska saiga hawaye sharrrr, ta ce, “bobo kana wulak’antani saboda ALLAH ya jarabceni da Sonka ko?, pls ka taimakeni ka taimaki rayuwata, wlhy sonka zai kasheni Abdulmaleek, bana iya barci, Sonka yana neman haddasa k’iyayya tsakanina da ‘Yar uwata, Dan ALLAH karda kayadani Abdulmaleek wlhy Sonka zai halakani, inasonka INA Sonka fiyeda son dAnakema kaina….. Takasa k’arasawa saboda kuka dayaci k’arfinta.
Shikam tsayawa kawai yayi yana kallonta, zuwa yanzu tafara basa tausayi, jiyayi zuciyarsa tana shawartarsa daya taimaketa koda da nasihane k’ila tagane ta farka daga nannauyan barcin daya d’auketa.
Yad’an lumshe idanunsa yabud’e akanta, kinga tashi yafad’a cikin muryarsannan mai dad’i da amo.
Safna ta tashi tsaye tana share hawayen fuskarta.
A can ciki kuwa saida su ya sulaiman suka zauna sannan sukaga babu bobo.
A’a INA Abdulmaleek ya tsaya?, cewar ya ishaq.
Kasansa shida baba mai gadi yanzu haka yana can.
Ammi ta ce, “Rahma jeki kira mijinki yazo yaci abinci tukunna saiya tafi suyita hirar.
Akunyace Rahma tamik’e, zata fita Appa yafito shima daga d’akinsa, ya kallesu ya ce, ” a’a INA mukarram d’in?.
Gashi can antafi kiransa wajen baba mai gadi.
To Aida kun k’yalesa babu dad’i suna hira kuma akatsesu, shima bazaiji dad’iba malam salen, daga yau kar a k’ara haka kunji?.
Insha ALLAHU Appa baza’a sakeba suka had’a baki wajen fad’a.
Rahma kam tana fita domin kiran bobo, harta kusa tsakkiyar gidan saita hango safna da bobo tsaye safna tana masa murmushi, badai ta hango fuskar bobo ba Dan ya juyasaiata baya, Dan haka batasan shi miyakeyiba, amma wata zuciyarta tana shaida mata shima murmushi yakeyima safna, tsayuwar sojan badakkare tayi, bata gama farfad’owaba ta hangosu sun nufi hanyar lambun gidan, jitai hawaye nabin kumatunta, yaukam abinda take zargi ya tabbata, inhar bobo da Safna ba soyayya sukeyiba a6oye mizaisasu ware kansu alambu kuma arin wannan lokacin?.
Ta share hawayenta tareda cije le6enta da k’arfi, juyawa tayi takoma cikin gidan, ta daure ta ce, “yana tareda baba suna hira awaje.
Appa ya ce, ” kinga Rahma barsa kawai, idan sun gama yazo yaci abincin.
Jinjina kai tayi cikin ladabi ta ce, “to Appa.”
Amma azuciyarta saitace aibama saiyaci abinciba soyayya zata k’osar dashi, d’akin su khairiya tashige tashiga bathroom tasha kukanta San ranta, zuciyarta sai tafarfasa takeyi Dan bak’in ciki, jitake gaba d’aya yau tatsani bobo dakomai nasa.
Haka tasha kukanta, bata fitoba saida taji aunty ummy na kwala mata kira tazo suci abinci, wanke fuskarta tayi tafito tana murmushin yak’e, ganinan aunty ummy wani abune yashigarmin ido shine nake cirewa.
Ayya sannu yafita ko?.
Eh ya fita aii ruwa naita sakawa.
To sannu, muje muci abinci ko.
To kawai tace mata suka fito falon k’asa inda kowa yake har Ammi, mazan ne kawai babu suna sama tareda Appa.
Aunty Sameera ta ce, “a’a INA safna wai?.
Da sauri Rahma ta ce, ” tana waje tana waya, aii muci abincinmu kawai wannan ba yanzuba, idan tafara waya sai ALLAH.
Dariya sukayi gaba d’aya, aunty rasheeda ta ce, “wlhy kubarta ta soye abinta, itama muje musha biki, tunda tak’i bobon mu, madai gani ko guy d’in nata yafishine haka?.
Babu Wanda yace komai saidai anyi dariya, harda Rahma datayi na yak’e, tasan sarai habaici aunty Rasheeda tayima Safna, amma bataga laifintaba tunda itama ga aunty Safnar can suna cin dunduniyarta itada mijinta datad’auki so ta d’ora masa ayanzun.
Hakadai sukecin abincinsu, Rahma tanacine kawai badan dad’iba, amma jitake kamar tana cin magani.
Safna da bobo kam suna lambu zaune, bobo ya d’aure fuska kamar bai ta6a dariyaba Dan ganin yanda Safna takafeshi da idanu tamkar zata cinyeshi.
d’an tsaki yaja yana kauda kai daga kallinta, ke kinga inada abunyifa nazo nan nazauna, kuma matata banaso taduba bata ganniba Dan haka miye maganar taki?.
Dukda maganarsa ta 6atama safna rai, musamman dayace bayaso matarsa taduba taga bata nan amma saita danne ta matso hawaye tana shashshekar kuka.
Hannu ya d’aga mata, kinga ba kuka na tambayekiba fa malama.
Share hawayenta tayi, ta durkusa agabansa guywa ak’asa tana cigaba da hawaye, Abdulmaleek pls kasamo mana mafita, nidai nasan kaima kana sona, idan zaka iya daurewa wlhy ni bazan iya jurewa ba ka taimaki rayuwata karta salwanta akan sonka.
Wani murmushin mugunta bobo yayi, ya ce, “tabbas ina sonki amma so na ‘yan uwantaka, irin Wanda nakema khursiyya da khairiyya.
So na gsky irin na soyayya da tsan tsan k’auna da begen juna, mai ratsa jijiya da ruhi da 6argo mutum d’aya tak nakemashi, itace Rahma, my Nusfulhayat d’ina, farin cikina uwar ‘yayana, sarauniya mai sarautar dukkan zuciyata da duk abinda ke cikinta.
Safna kamar yanda na gaya miki wannan zaman shine zai zama zama na k’arshe tsakanina dake, kuma itace zata zama magana ta k’arshe tsakanina dake wadda ta danganci wannan, zan baki shawara kuma zan miki nasiha, idan kin d’auka kin huta, idan kin watsar ke wahala, nidai ALLAH yagani nafita hak’k’inki amatsayina na d’an uwanki musulmi.
Zamansa yagyara yana mai k’ara tattara nutsuwarsa waje d’aya.
Cikin murya mai nuna muhimmancin maganar dazaiyi ya ce, “Safna!.
d’agowa tayi tana kallonsa amma bata tankaba.
Ya ce, “Safna ina d’aga mini k’afane saboda darajar Rahma amma nakula ke bakisan zuruba.
Zan baki shawara ta k’arshe atafiyamu Dan inaso mugudu tare my tsira tare…………..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 44
Ina mai baki shawara amatsayina na mijin k’anwarki, ki nutsu kinemi miji kiyi aure kidaina wahalar da kanki akaina.
Amatsayinki na wadda tayi kuskure abaya yakamata kiyi zaman gyarashi yanzu, sannan ki d’auki sona dakike ik’irarin kinayi ki jefar dashi gefe ki tsarkake zuciyarki, ki daina biyema k’awayen banza suna sakaki a hanyar hallaka na bin bokaye…..
Cikin matuk’ar mamaki Safna take kallonsa, azuciyarta ta ce, “a ina yasan wannan?.
Kamar yasan tunanin datake yayd’an murmushi tareda jinjina kai, yacigaba da fad’in kina mamakin ina nasani ko? Humm hakan babu inda zai kaiki wlhy saidai kiyita komawa baya arayuwarki, Safna babu abinda ke cutar da rayuwarki sai son zuciya, to son zuciya kuma facin zuciyane.
Na tabbata ALLAH ya jarabceki da sonane saboda hakan yazamarma masu hali irinnaki ishara.
Da’ace su Abba basuda Rahma dasunji kunya awaccan ranar dakika nuna musu basu isaba, saboda k’ok’arin kunyatasu dakikayi akan dalilinki mara tushe.
Shin alokacin kinada tabbacin sake ganina?, kokuwa idan kin ganni kinada tabbacin zan kar6i soyayyarkine?, amma saboda son zuciya kika bijirema iyayenki akaina, wannan itace jarabawa tafarko dakika fara fad’uwa arayuwarki.
Safna iyayenmu sunfi kowa sonmu Dan haka bazasu cutar damuba, idan baki saniba zan fad’a miki ayau, tunda nake banta6a za6ar matar aureba da kaina.
Matata ta farko ma iyayenane suka za6amin, dukda banasonta amma nayima iyayena biyayya nakar6i k’yautarsu da hannu bibbiyu, biyayyar danamusu ban bijireba sainaci riba, daga ni’ima har Rahma sunzamemin alkairi arayuwata, wadda na tabbata da auren soyayya nayi bazanci riba hakaba, kema na tabbata dakinma iyayenki biyayya dakinyi gamon katar da abinda kikeso, amma kinga sakamakon da bijirewar taja miki yanzu, saidai sharri shaid’an dana zuciya sun danneki kin kasa ganewa bare kiyi nadama harki nemi afuwar iyayenki.
To inamai tabbatar miki idan baki gyaraba haka zakiyita fad’uwa ak’asa, ki k’are rayuwarki a bibiyar tamu rayuwar, gashi mukuma kullum farincikine ke k’ara baibaye rayuwarmu saboda albarkar iyaye dake bibiyarmu.
_amatsayinmu na ‘Ya’ya wad’anda iyayenmu sukasha wahala wajen haihuwarmu, rainanmu, karatunmu, tarbiyyarmu, basa son kukanmu, kulada lafiyarmu daduk wani motsinmu, amma ayayin damuka girma muka mallaki hankalinkanmu lokacin daya kamata mu share hawayensu, amma sai suka nemi wata alfarma agaremu muka bijire musu, saboda mu muna ganin mun waye su mutanen Dane, mukuma ‘ya’yan zamani wad’anda boko tagina, shin kuwa muna ganin ALLAH zai k’yalemu kuwa?, aganina babu abinda ‘ya’ya zasuyi aduniya su biya iyayensu akan hidima da d’awauniyar dasukayi dasu suna k’anana._
Akwai inda zaka iya bijirema iyaye kaci riba, shine idan sunce kasa6ama ALLAH, wannankam ba’a yarda kamusu biyayyaba.
Idanfa ta gsky da tsarin addini za’abi, iyaye akace suza6ama ‘Ya’ya mijin farko, idan kuma k’addara ta gifta hartayi zawarci to wannan tanada ‘yancin za6ama kanta akaro na biyu tunda ta mallaki hankalin kanta.
Safna kije ki tsugguna ga iyayenki kinemi gafararsu na tabbata insha ALLAHU ko yayane saikinji sona yaragu azuciyarki.
Inhar iyaye na fushi dakai tom dolene kaita tsintar kanka cikin asara, bafa zaka sami sassauciba harsai sun janye fushinsu akanka, tokema ki gwada ki gani insha ALLAHU zaki dace…….
Shashshekar kukan Safna ne yakatsemasa dogon bayanin daya d’akko, d’ago k’yawawan idanunsa yayi yana kallonta, ya ce, “ba kuka zakiyiba inhar nasihata tashigeki, nadama zakiyi, kuma ki d’auki hanyar gyarawa.
Cikin shashshekar kuka safna ta ce, ” duk abinda kafad’a gsky ne, amma wlhy akowane dak’ika na rayuwata k’ara sonka nakeyi, narasa yanda zanyi nacireka araina, ina sonka so bana wasaba.
Tabashi tausayi kwari da gsk, Dan haka cikin taushin murya ya ce, “kiyi hak’uri Safna, kimik’a lamarinki ga ALLAH shine zai taimakeki, na tabbata shaid’an nak’ara hura wutar sonane azuciyarki Dan kawai yaraba zumincin dake tsakaninki da ‘Yar uwarki, Yakuma cigaba da 6atar dake acikin duhuwa kikasa rok’ar gafarar iyayenki bare harkici riba a rayuwarki.
Zan tayaki da addu’a ALLAH yacire miki sona azuciyarki kema yabaki miji nagari maisonki fiye da komai amadadina, nabaki kwana uku kije kiyi tunani kuma kiduk’ufa da addu’a Nina zan tayaki.
Jinjina kai Safna tayi cikin sanyin jiki, ga hawaye sha6e sha6e afuskarta, yazaro farin handky d’insa daga aljihu sai tashin k’amshi yake yabata.
Hannu biyu tasaka takar6a tareda fad’in ngd ya Abdulmaleek, ALLAH yabiyaka da mafificiyar nasara, yasakama rayuwarka da mafificin alkairi.
Jinjina mata kai yayi tareda lumshe idanunsa fuskarsa d’aukeda murmushi Wanda bata ta6a ganin irinsaba daga gareshi.
Itama mayar masa da murmushin tayi, tashare hawayenta da handky d’in.
Gaba tayi yana binta abaya gabad’aya saiyaji tabashi tausayi Dan baiyi tunanin zatayi sanyi dawuri hakaba.
Cak safna tatsaya tanabin mutanen Dake tsaye da kallo a harabar gidan d’aya bayan d’aya.
Da Rahma suka fara had’a ido, tunda take bata ta6a ganin ‘Yar uwarta Rahma hakaba, ta tamke mata fuska tamau kamar batasan miye dariyaba arayuwarta, juyawa tayi da kallonta ga sauran saitaga ya ishaq da matarsa ya Sulaiman da mayarsa ya Hamza da matarsa, wannan ya tabbatar mata sunfitone dazummar tafiya k’ila anata Neman bobo, gaba d’ayansu takula kallon tuhuma da tsana suke mata, k’asa tayi dakanta idonta cikeda hawaye, batason su maidata ruwa, tanason kowa ya fahimceta kuma ya k’aunaceta, juyawa tayi ta kalli bobo, shikam hankalinsa kwance yake, Dan fuskarsa da murmushi ya ce, “oh kunata jirana ko?, bara nama su Ammi Sallama mu wuce…….
Baijira amsar kowa acikinsuba yayshige warsa falon.
Sum sum safna itama tayi yunk’un tafiya Dan tsorata da kallon tsana dasuke mata kuma harda ‘Yar uwarta a ciki, da Sauri aunty Sameera tayi yunk’urin Tarar safna amma sai Yaya ishaq yad’aga mata hannu alamar tabarta.
Ganin haka yasaka safna saurin shigewa falon sukaci karo da bobo dake fitowa, kallonta yayi d’an murmushi ya ce, ” karfa komai yadameki nida kaina zan warware musu k’ullin kinji.
Kanta ta d’aga Dan koba komai taji sanyi tunda bobo yafara nuna mata kulawa, saida safe tafad’a a sanyaye.
ALLAH yakaimu yay maganar yana fita, Itakuma tahaye sama zuciyarta na k’ara k’arfafata akan karta bari dalilin wasu tubanta ya ruguje.
Koda bobo yafito saiya Tatar ya ishaq nagaya musu karkowa yatada maganar sai bayan biki, suna ganinsa kowa yagyara tsayuwarsa kamar basa maganar komai.
Shima bai nuna musu yaji komaiba yabasu hannu sukayi musaBaha kowa yashiga motarsa, hannun Rahma Yakama saita fisge..
Cikin d’an mamaki yakalleta ta kauda kanta gefe, k’ara damk’ar hannunta yayi yatura amota, Duk abinda ke faruwa ‘yan uwansa suna kallonsu amma babu Wanda yay yunk’urin yin magana.
Yana turata amotar yamaida yarufe, shima yazagaya yashiga suka fice kowa Yakama hanyar gidansa.
Tunda suka fice agidan Rahma tafara shashshekar kuka, baice da ita komaiba dukda kukan NATA na ta6a zuciyarsa, tsayawa yayi wajen wani gashin kaza yasaya sannan yadawo motar, gefen Rahma yakalla saiyaga tayi barci, girgiza kai kawai yayi yatada mortar yay gaba.
Bayan sun gaisa da maigadi yashiga cikin gidan yay fakin Inda yadace, baitadasuba sai kawai ya d’auki Nawal yakai cikin gidan, yadawo Yakuma d’aukar Rahma, yana tafiya yana kallon fuskarta daduk yayi jurwayen hawaye, lallausan murmushi yasaki ahankali ya ce, “my Nusfulhayat sarakan kishi, Ashe kema rigimammace?,…da wannan tunanin yakaita d’aki itama, yadawo yakwashi tarkacensa yay ciki.
Bai tadasuba amma cikin dabara yasauya musu kayansu zuwa na barci, yamik’e yanufi d’akinsa, shima wankan yayi sannan yazauna yaci naman ya k’oshi yad’ora da ruwa mai sanyi, yay hamdala ga ubangiji ya mik’e Yakoma d’akin Rahma.
Shima gadon yahaye yakwanta a bayanta tareda rungumeta, hannu yakai danufi shafa fuskarta amma amamakisa sai yaji hawaye sha6e² wasu na korar wasu.
Tashi yayi zaune ya kunna fitilar d’akin yana mai kallon fuskarta, yakai tsawon minti 6 ahaka, amma har sannan kukan takeyi kuma idonta arufe ruf.
gyarama Nawal kwanciya yayi, itakuma Rahma yad’auketa cak yay waje, duk abinda yakeyi tana jinsa amma tak’iyin koda motshin kwarai.
Koda ya direta asaman gado saiya kuma dawowa yakashema Nawal fitila yasake yimata addu’a, Yakoma Inda yabarta anan yatarar da ita, yagirgiza kai kawai yakashe fitilar tareda hayewa gadon.
Jawota yayi jikinsa yarungume, cikin taushin murya ya ce, “my Nusfulhayat!.
Shiru Rahma tayi kamarma batasan da wata halittaba awajen, yakira sunanta yakai so hud’u amma ko motsi batayiba, ajiyar zuciya ya sauke tareda k’ara k’ank’ameta ajikinsa yana aika mata da wasu sakwanni cikin nutsuwa da kwarewa.
K’arfin kukan Rahma ne yak’aru, tad’an fara mutsu mutsu ganin haka sai kawai ya manne bakinsa da NATA……..+
STORY CONTINUES BELOW

Hummm saida safenku bobo.
Washe gari tunda yadawo sallar asuba bai Tarar da Rahma ad’akin saba, yata6a k’ofar d’akinta yaji gam. Kyaleta yayi yatafi d’akinsa yakwanta.
Rahma kam tana zaune tana jinsa, saida taji shiru alamar yakoma d’akinsa sannan tafito tahau hidimar gyran gidan da had’a breakfast, fuskarta dukta kumbura saboda kukan datayi, yanzun haka tana aikinne babu ko d’igon walwala atattare da ita.
Bayan ta kammala aikin tsaf tayima Nawal wanka tamata shirin makaranta, itama wankan tashiga, batawani dad’eba tafito, ‘Yar kwalliya tayi cikin atanfa zani da riga takama hannun Nawal suka fito falo.
Bayan sun hau dinning ta had’a musu breakfast, Nawal ta kalleta cikeda shagwa6a momyna ina papana?.
Kallonta Rahma tayi da zummar mata magana saiga bobo yafito cikin shigar gayun zamani ajin farko.
Dukda tana fushi dashi ita kanta saida ta yaba, kauda kanta tayi daga kallonsa, yad’an ta6e bakinsa afili ya ce, “gulma.
Tana jinsa kuma tasan da ita yake amma ta share kamar batasan yana yibama.
Sumbatar kumatun Nawal yayi, itama yabata nasa tayimasa, ta gaisheshi, fuskarsa cikeda murmushi ya amsa, yak’arasa inda Rahma take, muryarta can k’asa ta ce, ” ina kwana?.
Bai amsaba saida ya sumbaci kumatunta, acikin kunnenta ya CE, “inafata kintashi lfy?, sarauniyar zuciyata.
Batako kalleshiba tacigaba da bama Nawal break abaki.
Shima baikuma cewa komaiba yad’auki cokali yasaka a abincin nasu yanaci, shayin gaban Rahma yajanyo yafara sha, yitayi kamar bata gansaba har suka kammala suka mik’e.
Yauma saida suka fara ajiye Nawal a school sannan yakaita gidan Appa, yanda tashareshi babu magana shima haka ya shareta, saidaifa idan yafaki idonta saiya kunshe baki yana dariyar mugunta, itadai batamasan yanayiba.
Agurguje ya gaisa da mutane yafice Dan zuwa office, bayaso ya had’u da yayyensa ko d’aya.
Gaba d’aya yinin Ranar haka Rahma tayisa sukuku babu walwala, kuma ko kad’an bata kula Safna bare shiga sabgarta.
Dukda Safna bataji dad’in hakaba amma taso ace Rahma ta fahimceta, saidai zatayi hak’uri har shi dakansa ya kwance kullin kamar yanda yagaya mata ajiya.
Ammi taso fuskantar wani Abu amma hidimar saukar bak’i ta d’auke hankalinta gabad’aya, saidai dukda haka saida ta tambayi Rahma gameda kumburin fuskarta, sai Rahman tace tayi zazza6ine jiya da daddare.
Ammi Tamata sannu dukda bata yarda da abinda taceba, amma tabar komai sai zuwa bayan biki.
*_4:15pm._* na yamma aka fara gudanar da kamu wanda ya k’awatar da jama’a, amare sunsha k’yau masha ALLAHU kamar kasacesu ka gudu, dangin angunan sunzo kuma suntaka rawar gani ta burgewa, taron yakasance na mata zallah Dan haka babu su bobo awajen bama su dawo daga aikiba.
Can na hango Rahma tasha k’yau cikin doguwar rigar material blue sun nad’a farin d’ankwali, ankone itada matan su ya Hamza, sunyi k’yau sosai dukda dai yau Rahma bata cika walwalaba amma tana iyakar k’ok’arinta Dan ganin tarage damuwar fuskarta.
Abinda yak’ara mata dad’ima shine zuwansu Basma da ihsan da aunty Ameera, Anty Naja’atu matar ya Muneer, aunty haleema matar ya Shaheed duk sunzo mata, ganinsu yasakata sakin jikinta tanamai jin dad’in ganinsu.
Alhmdllh kamu ya k’ayatar kuma antashi lfy kowa yakama gabansa.
Mutane basu ida barbajewaba su bobo suka dawo, rarraba ido yashigayi danson hango matarsa amma yakasa ganinta.
K’awayensu khairiyya sai fad’in kai guy d’innan ya had’u sukeyi, wau su khursiyya sumusu jagora wajensa.
Khursiyya ta ce, “Ku yanafa da mata wlhy kubari babu ruwana, wlhy ya Abdulmaleek d’an hayak’ine, idanma kuka cigaba da yawan kallonsa sai rankowa ya6aci awajennan Dan haka ku kama kanku.
Wata ta ce, ” amma ba gidannan yakeba?, Dan ban sanshiba.
Dariya khairiyya tayi ta ce, “to k’arewar gidannanma shi muke bimawa, dagashi saimu.
Cikin mamaki sukace amma dai wasu sun rasu a tsakaninku?, kumafa mudai bamu sanshiba, kai ‘yan biyu kuji tsoron Allah.
Hhhhhh lallai baku yardaba kenan?, to yagirmemu sosai Dan Ammi ta ce, ” wajen ahekara 12 yabamu, bayan shi harma ta fiddarai da haihuwa saigamu mun wuntsilo, abinda yasa Baku sanshiba bashida hayaniyane, kuma bakowace sabga bace zaku ganshi aciki, shinefa wanda kukazo bikinsa wata biyar dasuka wuce baya.
Idanu suka zaro, Zainab kabeer ta ce, ”wlhy bamu ganeshiba kinsan da daddare muka Ganshi awajen deener, masha ALLAHU, ina matarsa?.
Tana nan bara zaku ganta aii.
Bobo dabaisan sunayiba yahaye saman mota yazauna Dan bayason shiga falon saboda duk matane, harabar gidan tad’anfi k’arancin mutane tunda an ragu, Taufiq babban d’an ya ishaq yakira, ya ce, “my son ina auntynka?.
Taufiq ya ce, “uncle aunty Rahma?.
Eh, ita.
Yanzu naganta itada heebba sunshiga falo.
Yauwa jeka kiramin ita to.
To uncle.
Babu dad’ewa saiga Taufiq yadawo ya ce, ” uncle tana zuwa.
Okey my son, yanzu kuma sai ina?.
Uncle muna tarene nida abokaina.
Kaima gayyan kayo wajen taron mata?, maimakon kabari sai ranar d’aurin aure ko gobe wajen brother’s Night.
Uncle aii duk zasuzo shima.
Dariya bobo yayi ya ce, “to na mata.
Shima Taufiq tafiya yayi wajen abokansa yana dariya.
Na ce, ” masha ALLAHU yaron yafara zama saurayi, su bobo ankusa ajiye surukai, lol.
Yana zaune awajen yana latsa waya saiga Rahma tafito.
Kamshin turarenta kawai yaji yad’ago.
Kallo d’aya tamasa ta kauda kai.
Murmushi yayi yana kallonta, ya ce, “kai my Nusfulhayat kinyi k’yaufa, kamarma kece amaryar wlhy.
Ganin ta kauda kai ya ce, “madam har yanzu fishinne?.
Batace komaiba itadai, kuma fuskarta asake take gudun kar mutane su fahimci wani Abu.
Ya ce, ” my Nusfulhayat yunwafa nakeji, gashi duk mata agidan nama rasa yanda zanyi.
Murmushi mugunta tayi ta ce, “ina Safnar tabaka abinci?, ko sak’one naje nafad’a mata?.
Kallonta yayi ido cikin ido, tai saurin kauda kanta Dan bazata juri kallon cikin idonsaba, shima murmusawa yayi ya ce, ” idanma kinyi hakan ai babu laifi, yadiro daga saman motar, ki kaimin falon su inna munacan nidasu ya Sulaiman.
Baijira amsartaba yawuce…………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 45
Binsa tayi dakallo tana k’unk’unai, amma baijitaba Dan yayi gaba abinsa.
Safna tana dagacan saman kujera tana kallonsu, hawaye suka cika mata ido taisaurin saka handkyn daya bata jiya tagoge, ta Yanke shawara yau zatabi su Ameera sutafi gida, Dan inhar tana ganin bobo bata tunanin sonsa zai ragu azuciyarta barema ayi tunanin fita gaba d’aya, amma idan tayi nesa dashi k’ila taji sauk’in zuciyarta, Dan insha ALLAHU tayi tuba na gsky kenan.
Rahma tahad’a musu abincin Wanda dama tun d’azu ta tanada domin su, ihsan da Basma ne suka tayata d’auka zuwa 6angaren inna.
Duk sunacan harda Ammar dawasu mutum biyu dabata saniba, bayan sun ajiye suka gaidasu, idanun bobo nakan matarsa, itama tasaci kallonsa ganin idonsa akanta yasa ta kauda idonta tareda Jan hannun su ilham suka fice.
………………………÷
Bayan sallar isha’i su anty Hafsat sukace zasu wuce, Safna data gama had’a kayanta tamik’e itama, kallonta kawai Rahma takeyi amma batace komaiba, su dama su aunty Ameera tafad’a musu zata bisu Dan gidan yacika damutane kuma Rahma anan zata kwana itama, basu kawo komai aransuba sukace eh gara kawai tatafi gida.
Har harabar gidan tarakasu saida suka Shiga mota taga fitarsu sannan takoma ciki.
Amota Safna cikin dabara take share hawayenta, wata zuciyarta tana fad’a mata anya zata iya daurewa kuwa?, da sauri ta ce, “insha ALLAHU zan iya.+
.+.+.+.+.+.
Tafiyarsu Safna babu dad’ewa sosai bobo yashigo falon, wasu kallo sukeyi wasukuwama harsun kwanta, yagaidasu sannan ya haura sama, afalo yatarar dasu zaune sunata kulla kayan rabo, zama yayi yana fad’in wai Kodai yau anan zamu kwanane?.
Kallonsa ammi tayi, ta ce, ” nidama zaku barsu su kwanan Aida yafimin, idan bamu gamk’ullin nan yauba nasan zuwa gobe gidannan zai d’inke da mutane.
Kansa yashafa yana d’an murmushi Ammi sudai gama kawai saimu wuce ko zuwa 12 ne.
Hararsa Ammi tayi cikin wasa, ta CE, “fin k’arfi za’a nunamin akan ‘ya’yana?.
A’a Ammi mu mun isane.
Hira sukaitayi har su ya ishaq suka shigo suka had’u gabad’aya sukayi k’ullin sannan kowa ya d’auki matarsa sukai gida.
Biki yacigaba da kankama cikin farin ciki, komai yana tafiya yanda yadace, washe gari da safe akayi k’unshi, zuwa yamma gida kam ya d’inke da bak’i na nesa Dana kusa, su Rahma kam aii ko ganinsu ba’ayi Duk sun zama busy, to barema su bobo manya manyan yayye.
Da daddre k’arfe takwas aka fara d’ibar mutane zuwa wajen brother’s night dasu bobo suka shirya, abokansu sosai suka gayyato, taron ‘yammata da samarine kawai saikuma irinsu bobo masu mata, amma babu yara bare tsofaffi.
Taro yak’ayatar kam masha ALLAH, amare da angwayensu ansha k’yau abin sai Wanda yagani, su bobo suntaka rawar gani irinta manyan yayye, ko INA yashiga yana mak’ale da matarsa abin zak’yk’yau da burgewa, ‘yammata kam dayawa sun k’yasa, saidai ganinsa mak’ale da matarsa yakansa sushiga taitayinsu.
Alhmdllh dahaka taro yatashi lfy kowa Yakama gabansa.
_washe gari_
Aka d’aura auren khairiyya Aliyu Abdulmaleek hamshak’i da angonta Ahmad m sadiq, sai Khursiyya Aliyu Abdulmaleek hamshak’i da angonta Zaharadden usman Aliyu.
Masha ALLAH d’aurin aure yatara d’unbin jama’a nanesa Dana kusa ‘yan siyasa da masu mulki, ‘yan kasuwama ba’a barsu abayaba.
To khairiyya da khursiyya saimuce ALLAH yasanya alkairi yabada zaman lfy da zaman hak’uri.
Hummmm abun mamaki wai harda alhaji sunusi dala a ‘yan d’aurin aure, (araina nace su alhaji sunusi anji yaji🌶🤣 ahanun bobonmu😎😂😜) aiko bobo sai antaya MASA kallon banza yakeyi.
Shidai baimasan yanayiba.
Bayan kammala d’aurin aure su bobo sukaima anguna jagora zuwa cikin gidan, shidasu Yaya ishaq duk wankan farar shadda sukayi, masha ALLAH daka gansu kaga ‘yan uwa jini d’aya.
Har cikin falon suka Shiga anata gaisawa da ‘yan uwa da abokan arzik’i, bakin anguna yak’i rufuwa hakama su ya sulaiman suna cikeda farin cikin yau k’annensu sunyi aure.
Tunda sukashigo falon bobo yaketa baza ido domin hango Nusfulhayat d’insa, rabonsa da ganinta tun jiya bayan sun dawo daga faty.
Ganin duk d’unbin taron Matan falon bai Gantaba har sama dasuka haura aka gaisa dasu ammi nanma bata nan baimaga Matan yayyensaba ko d’aya.
Sakkowa yayi yabarosu a can, wayarsa yaciro a aljihu yafara kiran number ta amma bata d’aukaba, yana nan tsaye yanad’an waige waige saiga Nasiba zata shige itada wasu ‘yammata, Nasiba ta gaidashi ya bobo ina yini.
Juyowa yayi danson ganin wanene, oh Nasiba dama kinzo?.
Wlhy nazo jiya Yaya, tunda nazo bangankaba kaida ya sulaiman, amma naga ya hamza da ya ishaq.
Muna nan muma munyi busy ne da yawa, Dan ALLAH ko kin ganemin Rahma?.
Aunty Rahma, naganta anan baya itada umminta da Ammi dawasu mata, saidai ban saniba ko sun koma ciki.
Kai a’a bata ciki, amma ummi da Ammi nagansu aciki.
Okey bara na duba maka ita.
Ok thanks.
STORY CONTINUES BELOW

Gaba sukayi ‘yammatan sukace kai Nasiba wannan guy d’infa?.
Dariya Nasiba tayi ta ce, “shima yayanmu ne.
Ya sunansa?, Dan munsan bobo ba sunan yanka bane.
Hhhhh kukam miye damuwarku da sunansa?, wannanfa ba irin mazannane masu sauk’in samuba, wlhy yanzuma bak’aramar sa’a mukayiba dahar yay doguwar magana……
Hangen Rahma datayi yasata cewa yauwa gama aunty Rahman can bara nakirata nadawo.
Basuce mata komaiba tanufi Rahma dake tsaye itada aunty Ummy hannunsu d’auke da fillatai masu yawa.
K’arasawa tayi wajensu da sallama, cikeda fara’a suka amsa mata, Nasiba ta ce, ” aunty Rahma ya Abdulmaleek kam yana nemanki.
Rahma tad’an marairaice murya, wayyo ALLAHna shikuma Dan ALLAH mizan masa yanzu?.
Hararta aunty ummy tayi, takar6i fillatan hannunta tana fad’in zauna Jan aji wata ta k’yasa miki miji, kinga jeki ina nan ina jiranki.
Cikin kunya Rahma tajuya suka tafi itada Nasiba, Nasiba ta ce, “aunty Rahma ALLAH kirage kunyar nan, mazannanfa sunfison surunga ganinka ido atsaye kana basu kulawa, barema irinsu ya Abdulmaleek ‘yan Hutu.
Itadai Rahma mirmushi kawai tayi amma batace komaiba.
Tunda suka dosa yake k’are mata kallo cikeda k’auna, kwalliyarta ta tafi dashi kwarai da gsk, sanye take cikin atanfa zani dariga, zanin Rafa siket yabi jikinta da k’yau kamar siket, kwalliyarta daidai misali tayi d’as da ita…….
Saida sukayi sallama sanan yadawo hayyacinsa, yay firgigita yana murmushi.
Nasiba ta ce, ” to Yaya gata nan.
Yau Nasiba sannu da k’ok’ari.
Yauwa yaya Nasiba tafad’a tana juyawa cikeda jin dad’in yau ya bobo yamata doguwar magana.
Tana tafiya bobo yamatso daf da Rahma tamkar zai shige jikinta, baya tad’anja tana fad’in mutanefa na kallonka.
Baki yata6e yana fad’in ina ruwana dasu, nifa kema kad’ai nake gani awajen.
Fararen idanunta tajuya tana gyara tsayuwa, itafa haushinsa takeji idanma bai saniba…. K’yass k’yass taji ana d’aukar hoto, d’agowar nan dazatayi aka k’ara mata, Ammar tagani abayan bobo d’aukeda camera, bobo yay masa alamun jinjina sanan yamatsa Kusada ita aka d’aukesu tare, bata ankaraba taji hannayensa biyu bisa k’ugunta, da sauri tad’ago suka kalli juna aka d’auka, gira yad’aga mata.
Bak’aramar kunya abun yabataba Dan haka tajanye jikinta tamatsa gefe Dan kunya, ga mutane sai kallonsu sukeyi, wasu naganin sun dace, wasu kam kishi yahanasu ganin dacewar.
K’awayen Nasiba sikace kar dai itace matarsa?.
Dariya Nasiba tayi ta ce, “eh mana, aii itace yace na nemo MASA.
Kai ammafa itama ta had’u, amma yarinyace sosai yamata yawa, saidai kuma tamore sosai dasamun wananan miji na garari, wata acikin k’awayen Nasiba tafad’a tana kuma k’arema Rahma da bobo kallo da Ammar keta kestasu hotuna.
Ana cikin haka amarema suka fito dasu ya Hamza aka cigaba da hituna harda sauran jama’ar wajen, bobodai duk inda zaka gansa yana manne da Rahma, ita dai duk kunya ta isheta, haka aka gama hituna hardasu Ammi da umminta Dan itama tunda safe tana gidan.
Haka aka cigaba da gudanar da biki awanan yini Alhmdlh kowa kagansa yana tareda walwalarsa.
*_6:30pm_* d’unbin jama’a suka raka amare d’akunansu, sundai sha kuka tamkar zasu shid’e, Ammi ma tasha kuka sosai na rabuwa da ‘yan autocinta wad’anda suka kasance su kad’ai mata.
Appa da yayyensu duk sun musu fad’a yanda yadace, hakama dangin uwa Dana uba kowa yamusu daganan aka kwashesu sai gidajensu, Anfara kai khairiyya tunda itace hassana, sanan akai husaina khursiyya.
Bayan kamar awa d’aya ‘yankai amare suka dawo kowa yafara shirin tafiya dinner da anguna suka shirya.
*_8:30pm_* aka fara tururuwar tafiya wajen dinner faty d’in data tara d’unbin jama’a na 6angare uku Dan had’ewa akayi domin sauk’ak’ama mutane wahala.
Masha ALLAH amare sunsha k’yau kamar babu gobe, sunyi kwalliya cikin kaya iri d’aya, farin material doguwar Riga, annad’e musu kawuna da golden d’in gwaggwaro, idan kagansuma saika Gaza ganesu abin sai Wanda yagani.
Can nahango su Xoxo su Deejerh kakus, su Sa’adatu sa’ad, zulaihat, mamn haneep, mamn sultan, Maryam zuntu, miss Ayush, deexerh, hawwa, kai idanfa naita lissafosu saina cika muku page d’in taf dasunayen masu karatu, ammafa har wad’anda ban ambataba na k’yallosu awajen.
Har Anfara gudanar da shagali hankalin amare atashe Dan basuga walk’iyar kod’aya daga cikin yayensuba bare matansu, amma yaran duk dangi sunzo dasu, su Nawal ma suna tare dasu daga kai amarya ba’a koma dasuba.
Tsayuwa wasu motoci yasakani gwalo idanu dansan ganin suwaye acikine?.
😳tofa masu karatu manyan yayyene.
Hummm tuwon girma miyarsa nama muka fad’a nida Maman ussy, sai baza ido muke muga wankansu.
Chaiiii!, namuku na IBO, wankafa aka d’auka iya wanka awajennan dankuwa kowa yahad’e cikin shiga ta alfarma shida matarsa, ya ishaq ya sulaiman ya Hamza, oga bobo duk sanye suke cikin wasu dakakkun shaddoji milk colour, sunsha d’inki ‘yan ubansu, komai najikinsu iri d’ayane, takalmi hula agogo kai komaidai.
Suma su aunty Rasheeda Anty sameera Anty ummy, Rahma sanye suke cikin less milk da d’igon Silva, sun nad’a d’aurin d’ankwali kalar Silva, suma komai nasu iri d’ayane, cikin hall d’in taron suka dosa kowa rik’eda hannun matarsa, shigowarsu kallo Yakoma sama, kowa yabawa yake azuciyarsa, guri na musamman da aka ware musu suka zauna.
Kai yanzu ran khairiyya da khursiyya yay fes.
Dagananfa al’amura aka fara gudanarwa cikin farinciki.
Awajen lik’i kam manyan yayye sun ajiye tarihi suda matansu, abindai saimuce sambarka.
Dahakadai taro yatashi lfy, anguna sukad’auki amarensu suka maida gida, suma su bobo kowa gidan Appa yamaida matarsa Dan yauma anan zasu kwana.
Washe gari aka gudanar da walima dawuri Dan ‘yan nesa su sami damar tafiya.
To dagadai yau biki yatashi, zuwa dare kuma gidan yarage hayaniya Dan mutane duksun ragu.
Sai bayan isha’i su Rahma suka bar gidan amare, kowa mijinta yaje yad’auketa sai gida.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Washe garima dai su Rahma saida suka koma gidan Ammi, suka gyara duk Inda aka 6ata suda ‘yan aiki, duk kuma abinda aka aro aka maida.
Sudai su bobo kowa Yakoma kan aikinsa, hakama yara duksun koma makaranta, sai dare kowa yazo yakwashi iyalinsa, daganan kuma sai juma’a kowa ya huta.
Ammi da Appa sai sakamusu albarka sukeyi da jinjinama k’ok’arinsu, sun taimaka an rufama juna asiri anyi angama lfy cikeda farinciki.
Babu abinda kake ganin afuskar ‘ya’yan na Appa da matansu sai murmushin jin dad’i.
Dahakadai kowa yay gida.
Safna…………..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 46
wai masu karatu ina Safna?._
ALLAH sarki rayuwa, duk wanan shagali da ruguntsumi da’ake fama Safna nacan tana fama da ciwo batareda kowa yasaniba.
Babu yanda Ummi batayi da itaba akan tashirya suje wajen bikin amma tak’i ta ce, “kanta namata ciwo.
Ummi bata d’auki zancen ciwon nata serious ba dantasan halin Safna sarai da d’orama kai ciwon k’arya idan batason yin Abu.
K’yaleta tayi ta cigaba da jerangiyar zuwa bikin, yayinda Safna ke jiyyar zuciya Dana ruhi, zuwa yanzu tayi ALLAH wadai damai hali irin nata yafi sau dubu, tabbas tagane illar bijirema iyaye dazama akan ra’ayin rik’au, idan tatuna ranar data tuburema iyayenta batason auren dasukayi shirin yimata takan tsani kanta dadukkan rayuwarta, lallai zuwa yanzu tagane sharri zuciya dana k’awa, Dan baseera ta taka rawar ganin wajen zurma rayuwarta ga halaka.
ALLAH sarki zeenat dama kin fad’amin zanyi nadama, amma na k’aryataki, nak’i yarda da zancenki lokacin Sharrin shaid’an Dana zuciya suna d’awauniya dani, sai yanzu nagane ke mai k’aunatace da gsy, kece k’awa abar alfahari agaren……tarushe dawani kuka maiban tausayi.
Da sauri ummi tak’araso gareta tana fad’in Safna lfy kuwa?.
Tashi tayi zaune da sauri tak’ank’ame ummi tana kuka, ummi wlhy nayi nadama, yanzu zan canja, dan ALLAH ki gafarceni keda abba dasu ya munner, wlhy nayi nadama bazan sakeba……..
Takuma rushewa da kuka yayinda numfashinta ke sama yana k’asa, k’irjinta tadafe tana fad’in wash ummi zan mutu, ummi k’irjina zai fashe..
Arazane ummi take girgizata tana kwala kiran Safna! Safna!!, ke Safna!!!.
Ina Safna tayi nisa batajin kira, numfashinta yatsaya cak da aiki, afirgice ummi ta ce, ” nashiga uku ni sa’adatu mizan gani haka?, wayar safna ta raruma jikinta sai rawa yake takira abba, yana d’agawa tafashe dakuka mai tsuma rai, abban shaheed ka taimakeni kada safna tamutu dan ALLAH.
SHIMA cikin mamaki ya ce, “safna kuma?, miyafaru da safnar?.
Abba Shaheed nidai kataho gida wlhy safna bata numfashi gabad’aya wayyo ALLAH na safna karki mutu, munyafemiki dan ALLAH karki tafi kibarni wayyo safna….
Surutai da sambatu kawai ummi ke zubawa.
Cikin lokaci k’alilan saiga abba da likita harda ya munnir, ai ganin Safna sharaf kamar gawa doctor ya ce, ” sud’auketa kawai atafi asibiti, jikinta yawuce adubata agida.
Ya munnir yasa6eta batareda yabarima likita ya k’arasa fad’aba.
Agaggauce suka isa asibiti.
Taimakon gaggawa aka shiga bama safna wadda saidai abinda ALLAH yayi kawai, dan kwance take sharaf babu alamar numfashi.
Masu karatu nimafa atsorace nake😟, safna saidai wani abu ga ALLAH.+
Su Abba sai safa da marwa sukeyi ak’ofar d’akin da’aka sakata, ummi kam banda hawaye babu abinda take shar6ewa, Abba da ya muneer sai hak’uri suke bata.
*…………………………..*
Awanan lokacin kam Rahma nagida itada Nawal da direba yad’akko yanzu Daga school.
Bayan Tamata wanka sukadawo falo, Nawal nagefenta zaune tanacin abinci itakuma tana duba buks d’inta taga ko anbasu homework
Nawal ta ce, “momy!.
Na’am babyna, miya farune?.
Nawal tayi ‘Yar dariya, momy auntynmu ce ta ce, ” wai bankai mata kayan bikiba, shine nace gobe zan kaimata, aizaki bani nakai mata ko?.
Murmushi Rahma tayi tareda d’agamata kai, zan baki my sweety na insha ALLAH.
murna Nawal tafara, itakuma Rahma tana kallonta tana dariya.
Bayan takammala cin abincin ta koya mata homework, suna kammalawa suka fito harabar gidan suna shan iska, Nawal tanata wasanta cikin ‘Yar motarta, ita kuma tana zaune tana karatun book awaya dansu Basma sun sakata groups na Novels.
Jin k’arar bud’e gate yasa tad’ago tana kallon hanyar gate d’in dukda basosai take hangowaba amma taga kamar motar bobo.
Agogon dake manne ahannunta ta kalla _4:15pm_ afili ta ce, “lfy kuwa Nurulk’albi?.
Bobo yay farking a inda yadace sanan yafito, sanye yake cikin k’ananun kaya, blue d’in wandon jins da farar Riga mai dogon hannu, yayi k’yau tamkar yanzu yay kwalliyar, jakar aikinsa yad’auka ya rataya sanan yakwashi wayoyinsa, harya nufi hanyar falon saiya jiyo dariyar Nawal da Rahma abaya.
Dawowa yayi yanufi inda yakejin dariyar.
Nawal naganinsa ta tashi da gudu ta taroshi, rungumeta yayi yanamai farincikin ganinta, ya ce, ” baby ya school?.
Lfy lau papana.
Masha ALLAH, amma yau ba’aje islamiyyaba?.
Kanta ta d’aga.
Ya ce, “miyasa?.
Shiru tayi Dan tama manta abinda yasa yau bazasu islamiyarba.
Ganin haka yasaka bobo d’agowa yana kallon Rahma, sauke idonta tayi daga satar kallonsa, idonsa yalumshe yana murmushi, afili ya ce, ” gulma.
Kallonsa tayi tana turo baki Dan tasan da ita yake, fuska akumbure ta ce, “sannu da zuwa”.
Bakinsa yata6e ya ce, ” bazan amsaba, aiba haka ake tarar mijiba.
Idanu tad’an zaro tana kuma satar kallon Nawal.
Shima Nasal d’in ya kalla saikuma yamaida kallonsa ga Rahma, gira yad’aga mata yana wani murmushin gefen baki.
Tashi tayi tak’araso gareshi, tamik’a hannu nufinta yabata jakarsa, maimakon yayi haka saiya mik’a mata kafad’arsa duka.
Nawal takuma kalla taga takoma wajen motarta, d’an kad’a idanunta tayi sanan tasaka hannu tazare jakar.
Bak’aramar kasala tasakarma boboba data kad’a idanunta, yalashe la66ansa sanan yamatso daf da ita ya manna mata kiss akumata.
Ja baya tayi da Sauri, harma taso bama bobo dariya saboda yanda ta razana kamar wani maciji ya ta6ata amma yadake.
Ra6awa tayi ta gefensa tawuce, binta yayi da kallo harta shige.
Yakalli Nawal daketa wasanta da mota, ya ce, “baby kijirani yanzu zanyi wanka nadawo.
To my papa, Nawal tayi maganar hankalinta awasa.
Ciki shima yanufa.
Yana shiga d’akinsa Rahma na niyyar fitowa, Ra6awa tayi tagefensa zata fice yay saurin shan gabanta, k’ara kaucewa tayi nanma ya tareta, tad’ago ido tana kallonsa saitaga fuskarsa ta canja yakomamata ainahin bobo nada data sani ada.
Jada baya yayi yajingina da k’ofar, ya hard’e hannayensa ak’irji yazuba mata mayun idanunsa, k’asa tayi dakanta gawani tsoro yana shigarta, jitai miyasama take masa haka?, kodan taga yanzu ya sake mata yana wasa da ita?.
Kallonta yake daga sama har k’asa, shifa ganin yakema tak’ara MASA k’yau da haske, yad’an lumshe idanunsa yabud’e, murya a tausashe ya ce, ” Rahma!.”
Kanta tad’ago ahankali tana kallonsa, ganin ya zuba mata idanunsa da awanan munafikin kallon NASA k’asa k’asa yasa tamaida idanunta tana wasa da zoben hannunta.
Yakuma fad’in Rahma!.
Na’am ta amsa kanta asunkuye kuma muryarta tana rawa.
Ya ce, “miyeni awajenki?.
Tambayarsa tabata mamaki Dan haka tad’ago tad’an kallesa ta maida kanta k’asa sanan ta ce, ” mijinane.
Ajiyar zuciya ya sauke sanan ya warware hannayensa yatako ahankali zuwa gareta, jin k’amshin turarensa yak’ara kusantota yasakata rumtse idanu, nanma tsayawa yayi yana k’are mata kallo, saikuma yasaka hannunsa yad’ago ha6arta, kalleni yay maganar akasalance.
K’ara rumtse idonta tayi Dan bazata iya kallon nasaba.
Yakuma cewa My Nusfulhayat kalleni.
Girgiza MASA kai tayi alamar a’a.
Ya ce, “miyasa?.
Batace komaiba amma tagyara tsayuwarta.
Bobo Yakuma narke murya can kasa tamkar mai rad’a ya ce, ”kina fushi da mijinki ko?, saboda kina zarginsa dacin amanarki yakeyi?.
Hawaye suka ziraro daga idanunta, ahankali suke silalwo visa kumatunta, yad’an cije le6ensa yanamai k’ara tsura mata idanu.
Matsota yakumayi, yasak’alo d’ayan hannunsa kan k’ugunta, ahankali yad’ora bakinsa visa nata, cikin Sauri da rawar jiki tabud’e idanunta saidai tamakaro Dan haryayi nasarar zira harshensa aciki, kissing nata yake cikin kwarewa danuna zalama.
Itakam tun tana yunk’urin kwacewa harta hak’ura tamik’a wuya Dan tuni ga6o6in jikinta sun saki, da wanan damar yayi amfani wajan cud’anyata San ransa, ganin tsayuwa tana Neman gagararsu yad’auketa can sukayi gado.
🚶🏻♀sum sum nafito wajen Nawal.
Soyayya sosai Bobo yasha, saida nutsuwa tazo musu sanan Yakuma jawota jikinsa yarungume, muryarsa can k’asan mak’oshi ya ce, “Rahma da gsk kina zargin mijinki da cin amanarki?.
K’ara kwanciya tayi luf visa faffad’an k’irjinsa tana shak’ar daddad’an k’amshinsa, muryarta nad’an rawa ta ce, ” nifa ba zarginka nakeyiba.
Ya ce, “to miyasa kike 6ata rai idan kinganni?, miyasa kuma Safna tatafi gida batareda nasaniba?.
Idonta ta rumtse tareda sauke sassanyar ajiyar zuciya, wlhy bani nakori aunty Safna ba, kuma bansan abinda akai mataba tatafi, nidai naganta da kaya kawai.
To miyasa baki hanata tafiyaba?, Ko kuma ki sanarmin?.
Inatsoron kartamin masifane, kuma gashi acikin mutane Muke.
Huci yafitar daga bakinsa, yasaka hannu ahankali yana shafa kanta, suduka sukayi shiru nad’an lokaci, jin shirunta yayi yawa yad’ago yalek’a fuskarta saiyaga barci yakwasheta.
Maida kansa yayi ya kwanta shima ya lumshe ido amma ba barci yakeyiba yafad’a duniyar tunanine kawai, tundaga randa Appa yay masa maganar auren Safna harzuwa canjamasa da akayi da Rahma, bikinsu, rayuwarsu tanesa nesa, har zuwa yau dasuka zama Abu guda, yad’anyi murmushi dantuna darun Rahma, yasan kishine kawai kecin zuciyarta, jiyayi yak’ara k’aunarta nikin baninkin, yad’ago ahankali yana kallon fuskarta, ahankali take sauke numgashi ak’irjin nasa, fusakarta tayi fayau gawani annuri namusamman datake fitarwa, shiru yayi yana sauraren yanda Nawal take buga k’ofa tana kiran momy! papa!.
Tashi yayi ahankali da Rahma ajikinsa, cikin hikima yazameta daga jikinsa ya kwantar da ita tareda kara mata filo, kafin yagyara mata kwanciyarma harta gyra kanta tareda jawo filo tarungume.
Murmushi yayi yana mai kallon k’yak’yk’yawar fuskarta, azuciyarsa ya ce, “ragguwa da anta6aki sai barci.
Jin Nawal takuma bugawa yamik’e yad’auki tawul yad’aurama k’ugunsa sanan yanufi k’ofar yabud’e.
Tana tsaye abakin k’ofar, ya ce, ” baby miya faru?.
Papa ina momyna?.
Saida yajuya yakalli Rahma sanan yadawo da kallonsa kan Nawal, momynki tana aikine jeki kijirata afalo kinji d’iyar albarka.
Kanta ta jinjina, ta ce, ”papa nakalli cartoon?.
Eh babyna jeki saka MBC 3 kigani, muma yanzu zamu fito.
Tafiya tayi abinta tana murna, shima yamaida k’ofar yarufe harda saka key.
Bathroom yashiga yay wanka, dama Rahma tahad’a masa ruwan wanka, bayan yagama k’alk’ale k’alk’alensa yafito.
Kujerar madubi yaja yazauna, yana cikin shafa mai yaga Rahma yatashi afirgice tana sambatar aunty Safna! Aunty Safna!!, Dan ALLAH karki mutu, A’uzubillahi minashshaid’anirrajim!, sai jikinta ke rawa, da Sauri. Bobo yamik’e yaje yajata jikinsa yarungume, yana kiran my Nusfulhayat nutsu kinji, mafarki kikeyi ba gske bane, nutsu.
Hawaye tafara zirarwa, a’a my Nurulk’albi Dan ALLAH ka kaini na ganta, kacemin bata mutuba, wayyo aunty Safna karki tafi ki barni………
Kafin tarufe baki wayar bobo tafara wringing, dak’yar tayarda ya janyeta daga jikinsa yatashi yad’auki wayar, gabansane yafad’i shima Dan ganin sunan ya Shaheed 6aro 6aro akan screen d’in wayarsa.
Haka kawai yasamu zuciyarsa dayin rawa, dakuma k’ok’arin gaskata mafarkin Rahma, shiyyasa ba’ason barcin la’asar yafad’a azuciyarsa yana kallonta.
Ganin kallon dayake mata saita sake fashewa da kuka, cikin muryar kuka ta ce, “yan gidammune ko?, namasan zasu fad’amin aunty Safna na tarasune kawai…… Tasaki kuka maiban tausayi da tsuma zuciyar mai saurare.
Kiran ya Shaheed ne yakuma shigowa, jiki a sanyaye yad’aga yakara akunne, muryar ya Shaheed kawai dayaji yasaka zuciyarsa karaya, bayan sungaisa ya Shaheed yasanarma bobo abinda nikaina banjiba.
Cikeda tashin hankali ya ce, “ya Shaheed gamunan zuwa, koda suka yanke wayar.. Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un kawai bobo ke iya ambata, Rahma tataso ta warce wayar, ganin sunan Wanda yakirashi yasakata fashewa da kuka, matsowayayi Kusada ita ya ce, ” addu’a Safna take buk’ata yanzu agaremu Rahma, kinga tashi kiyi wanka muje.
Kasa tashi tayi, saishine ya d’auketa yakai bathroom yaymata wankan dakansa, dak’yar yasamu tayi wankan tsarki sanan suka fito, d’akinta yaje yad’akko mata wasu kayan, babu zancen shafa mai zirawa kawai tayi, shima yasaka doguwar riga kawai yakama hannunta suka fito.
Afalo suka d’auki Nawal sai gidansu Rahma.
Amotama sai kuka take, shima yakasa lallashinta Dan duk arud’e yake, tuk’i kawai yakeyi cikeda damuwa…………..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 47
Ganin yanufi wata hanya daban yasa Rahma tsura masa idanunta dasuka k’ank’ance saboda kuka, yana kallonta tagefen ido kuma yakula magana takesonyi amma takasa, shima bai iya cemata komaiba, gudu kawai yake shararawa, ganin sunshigo cikin asibitin Rahma takuma yarda mafarkinta ya tabbata, guri bobo yasamu yay fakin kowa yafito jiki a sanyaye, banda Nawal dabatasan wainar da’ake toyawaba, cikin asibitin suka shiga kowa da abinda yake sak’ama zuciyarsa, Rahma takan share hawaye lokaci lokaci.
A Reception suka tsaya bobo yakira ya shaheed.
Babu dad’ewa saigashi yazo, Rahma tana ganinsa tafad’a jikinsa tana kuka, cirota yayi daga jikinnasa yana fad’in haba Autar Ummi bakisan kin girma bane?, kinga share hawayenki kinji.
Cikin shashshekar kuka ta ce, ”yaya waye bashida lfy?.
Ya ce, “safna CE.”
K’ara share hawayenta tayi ta ce, “yaya nasamma aunty Safna tarasu ko?.
Idanunsa yazaro ya CE, “haba auta wayace miki tarasu?, a’a tana nan da ranta har yanzudai tana tareda doctor’s ne.
Ta share hawayenta tana kallonsa, to yaya miya sameta?.
Muma bamu saniba Rahma saidai idan likitoci sun fito muji.
To muje kokin manta bake kad’ai baceba?.
Ita saima yanzu ta tuna tare suke da bobo Dan haka takalli Inda yake tsaye rik’eda hannun Nawal dake kuka tunda taga Rahma na kuka.
Da sauri tazo taja Nawal jikinta ta rungumeta tana lallashi, bobo dai da ya Shaheed suna tsaye suna kallonsu.
Ganin abun bana k’are bane yasa bobo matsawa kusada ita ya CE, ” yakamata mu k’arasa ko.
d’agowa tayi ta kalleshi saikuma takama hannun Nawal suka shiga ciki.
Acanma tana ganin su Abba taje tafad’a jikinsa tana kuka, dak’yar ya lallasheta tayi shiru, bayan sun gama gaggaisawa suma sukabi sahun ‘yan zaman tagumi.+
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Har akayi sallar magriba likitoci nakan Safna, su bobo dasu Abba suka nufi masallacin cikin asibitin, sudai su ummi da matansu ya Shaheed duk suna nan zaune jigum jigum, Nawal kam tuni tayi barci, ummi taciro d’ankwalin kanta dayake yanada girma tabama Rahma ta ce, “ta Goya Nawal, amsa Rahma tayi tacika umarnin ummi, gama goyon babu dad’ewa saigasu ya Muneer sun dawo daga masallaci, hakan kuma yayi daidai dafitowar doctors d’in kowa yana yarce gumi, da Sauri kowa yanufesu yana tambayar halinda safna take ciki, duk zame jiki sukai suka gudu akabar doctor Kaleel kawai, kallonsu yayi d’aya bayan d’aya yana share gumi, ganin duk ‘yan gidane ya sauke ajiyar zuciya, ya ce, ” Alhmdllh munsami nasarar ceto ranta, yanzu haka tasamu barci, yanzuma za’a wuce da’ita d’akin Hutu danhaka Ku kwantar da hankalinku alhaji, komai yazo da sauk’i aii alhaji, sauran bayani kuma sai zuwa gobe idan ALLAH yakaimu.
Alhamdllh suka fad’a gaba d’aya, godiya sukaima doctor Kaleel sannan yawuce office d’insa.
Tafiyarsa babu dad’ewa aka gunguro Safna a d’an gadon marasa lfy, kwance take sharkaf tana barcin wahala, cikeda tausayi da addu’ar samun lafiya suka bita.
Zuwa yamzu fuskokin kowa garage damuwa bakamar d’azunba.
Bobo yamatso kusada Rahma ya ce, “My Nusfulhayat ki sauketa mana, aii yanzu Nawal tawuce goyo karkizo k’irjinki yana ciwo.
Girgiza MASA kai tayi ta ce, “bafa tada nauyi ALLAH.
YA munnir dake kusadasu yana jinsu ya ce, “aidama gida kuka tafi tunda anga yanda jikin NATA yake.
Abba ya ce, ” gaskiyarka muneer, Abdulmaleek kutafi gida hakanan, kuma su Muneer kud’auki iyalanku Ku tafi gida saboda yara dakuka bari..
Rahma ta turo baki gaba cikin shagwa6a ta ce, “Abba nidai anan zan kwana gsky.
A’a auta bazai yuwuba, idan anbarki kin kwana anan mijinkifa, bobo yad’an shafa Kansa idonsa ak’asa ya ce, “Abba abarta ta kwana Indai Dan tanine babu wata matsala.
A’a a aiba hauka akeba Cewar ummi dake Harar Rahma.
Abba ya ce, “kutafi gida kinji auta, ALLAH yay muku albarka gaba d’aya, gobe idan ALLAH yakaimuma aii ranace ko.
Bobo ya ce, ” to Abba bara muyi sallar isha’i, Dan komun tafi a hanya zata riskemu.
Eh gsky ne to kubari ayid’in.
STORY CONTINUES BELOW

Bayan sallar isha’i badan Rahma tasoba suka fito gaba d’aya harsu ya Shaheed da matansu domin tafiya gida.
Abba da ummi kad’ai aka bari a asibitin zasu kwana.
Har yanzun Nawal tana bayan Rahma agoye saida zasu Shiga mota bobo ya taimaka mata ta sauketa ya kwantar da ita a sit d’in baya sannan suka Shiga mota kowa yanufi gida.
Babu maima wani magana harsuka Shiga cikin gidan, bayan mai gadi yabud’e musu suka Shiga, bobo yay fakin suka fito, harzata d’auki Nawal ya ce, “tabari ya d’auketa, bata Musa masaba tabari ya d’auketa suka Shiga cikin gidan.
Har d’akinta yakai Nawal ya kwantar, ita kuma tashiga wanka.
Shima d’akinsa yanufa yacire doguwar rigarsa yasaka kayan barci, fitowa yayi yanufo dinning Dan yunwa yakeji.
Rahma tafito wanka ta rama sallolinta sannan tanufo falo domin d’aukar Abu.
Ganin bobo zaune a dinning yatuna mata dabaifa ci abinciba Ashe, jitayi yabata tausayi, tak’araso Inda yake tana fad’in sorry Nurilk’albi muntafi ko abinci bakaciba.
Murmushi yay mata ya ce, ” karki damu o, kina arikicannan ta’inama zaki tuna da cikina.
Marairaice fuska tayi tamkar zatayi kuka, ta ce, “pls kamin afuwa.
Ayya my Nusfulhayat karki damu ai nasan bakiyi da niyyaba.
Itama murmushin tamasa.
Ya CE, ” babynkifa?.
Tana barcinta har yanzu.
OK tom zoki zauna muci abinci, Nima yunwace ta addabeni shiyyasa ban nemekiba.
d’an yatsine fuska tayi tareda ta6a cikinta ta ce, “nikam na k’oshi.”
Kamo hannunta yayi, yajawota ta zauna saman cinyarsa, shima hannunsa ya d’ora akan cikin nata yana shafawa ahankali, haba my Nusfulhayat kinaso ki haifamin babyna d’an k’aramine?, nifa k’atoto nakeso Wanda Nawal zata d’auka da k’yar.
Kallonsa tayi tad’an juya idonta dasuka kummbura saboda kuka, tasaka hannu tarufe fuskarta tana fad’in Nurulk’albe baby kuma?, a INA?.
Hannunta ya janye ya d’aga mata gira, ya ce, “acikinki mana.
Tad’an zaro ido tana tura baki gaba ta ce, ” nidai kabar fad’a.
Ya ce, “miyasa?.”
Since kanta tayi ak’irjinsa cikin sassanyar murya ta ce, “wlhy inajin kunya.
Tabashi dariya Dan haka yay murmushi mai sauti tareda d’agota yana fad’in Ashe kunyarnan har yanzu ban gama fiddataba?, shikenan nadaina tashi muci abincin.
Girgiza masa kai tayi.
Ya ce, ” pls ko kad’an kici.
Yunk’urawa tayi zata tashi, ya maida ita ya zaunar, no yizamanki kawai.
Badan tana son cin abincinba ya matsa mata, dakansa yarink’a bata shima yanaci, tana zame zame damasa ta6aradai har sukaci da d’an yawa sannan suka mik’e, ya taimaka mata suka gyara wajen tsaf sannan kowa yanufi d’akinsa.
Harta kwanta ta rungume Nawal taji motsin shigiwarsa shima gadon yahawo, suka saka Nawal a tsakkiya, yamusu addu’a ya shafama kowa sannan yahad’asu yarungume sai barci..
Nima dai homajeep d’in k’afafuna naja natafi wajen my Abdul d’ina nabar Rahma Dana itama.😜
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Washe gari bayan sunyi breakfast Rahma tabisu, yasauke Nawal A school sannan suka nufi asibitin.
Har cikin yashiga shima, yatayata d’aukar kulolin kayan breakfast d’in Data had’o musu, ahanya suka had’uda Abba zai fita, suka rissina suka gaisheshi, cikeda fara’a ya amsa musu, Yakoma yimusu bangajiyar jiya, suma suka tambayeshi yamai jiki?, ya ce, “a dasau kam Dan tana nanma zaune yanzu haka.
Alhmdllh suka fad’a atare.
Ya ce, “kuk’arasa ciki to, nima zanje gidane na shirya nawuce kasuwa.
Saika dawo.
Da sallama suka shiga d’akin, Safna tana zaune akan gado tajingina bayanta da filo, hannunta manne da k’arin ruwa.
Ummi na zaune agefenta tana had’a shayi, d’agowa sukayi gaba d’aya suna amsa sallamar, Safna kallo d’aya tamusu ta kauda kanta.
Ummi ta tashi tareda turama bobo kukerar tace ya zauna.
A’a ummi kiyi zamanki, zanma wuce wajan aikine, rissinawa yayi ya gaidata da tambayar maijiki, ta ce, “jiki Alhmdllh tunda gata azaune hartana magana.
Ya ce, “ALLAH yak’ara sauk’i.
Ameen ummi tafad’a tana fita.
Rahma dake Kusada Safna tsaye tana tambayarta yajikin?, da k’yar ta amsata, Rahma dai bata kawo komai arantaba duk zatonta zafin ciwone.
Ummi nafita bobo ya kalli Safna, ya ce, ” antynmu ya jikinki?.
d’ago manyan idanunta tayi ta kallesa, ahankali ta ce, “da sauk’i.
Ya ce, ” ALLAH yak’ara sauk’i, yasa kaffarane.
Amin tafad’a a saman la66anta.
Shiru nawani d’an lokaci, bobo yakalli agogon hannunsa sannan yakalli Rahma, my Nusfulhayat bara nawuce ko, kinsan yau k’arfe 10 zamushiga shari’armu dasu Alhaji Abdurrazaq.
Itama kallonsa take tana d’an murmuahi ta ce, “to Nurulk’albi ubangiji ALLAH yabada nasara, yakuma d’oraka akansu.
Lumshe idanunsa yayi yana murmushi, ahankali yabud’e akanta ya ce, ” ngd sosai da addu’arki gareni my Nusfulhayat.
Murmushi kawai tamasa batareda tace komaiba.
Yamatso daf da ita, bata ankaraba taji kiss akumatunta, d’an zaro ido tayi tana kallonsa, shikuma yad’aga mata gira sannan yamik’a mata kumatunsa wai tamasa kiss, hannu tasaka tarufe fuskarta tareda fad’in kai Nurulk’albi nidai a’a gsky.
Dariya yayi ya ce, ” shikenan aii, ya kalli Safna da bak’incikin abinda sukeyi agabanta tamkarma sun manta da ita ya tokare mata mak’oshi.
Auntynmu ALLAH yak’ara lfy fa, bara natafi office time natafiya, sai dai ganinki yasa matana takasamin adawo lfy.
Murmushin yak’e Safna tayi Wanda duk Wanda yagani yasan tabbas na yak’ene, ta ce, “a’a nikam babu ruwana..
K’ofar yabud’e zai fita sannan yajuyo ya kalli Rahma yakashe mata ido d’aya yafice.
Murmushi Rahma tayi tana girgiza kai.
Safna tazame ta kwanta idanunta cikeda kwalla.
Ahaka ummi tashigo ta samesu, sai yanzu Rahma tasami damar gaida ummi.
Ummi takama hannu Rahma suka zauna ta ce, ” autana ina d’iyar takine?.
Tana makaranta ummi, saida mukama ajiyeta sannan muka wuto nan, ALLAH sarki aii yarinyar tanada Shiga rai wlhy, gatada wayonta masha ALLAH.
aii ummi saima kin zauna da Nawal wlhy, yarinyar batada damuwa ko kad’an…..
Haka sukaita hirar Nawal, Safna tana kwance tana jinsu amma tayi shiru, da k’yar ma ummi tasata ta tashi tayi breakfast da kayan Rahma data kawo.
Ummi saiyabama girkin Rahma takeyi itakuma tanatajin dad’i, Safna dai batacemusu k’alaba har doctor yashigo yaduba jikinta yacire k’arin ruwan.
Fitar doctor babu dad’ewa saigasu ya muneer da matansu, suma basu dad’e dazuwaba saiga ‘yan gidansu ya Kamal, harma dashi ya Kamal d’in, saikuma ga Appa Ammi da inna, nanfa akashiga gaishe gaishe datambayar mai jiki.
Zuwa azuhur asibin yacika da dangi, sunata tururuwar zuwa ganin Safnar, haka suka kasance da dangi, kowa yaga Rahma saita burgeshidantakuma yin bul bul da ita, ga wani k’yau da murjewa data k’ara na musamman.
Aunty yahanasu Maman Basma ma cewa tayi ‘yata kodai nasamu jikane?, irin sannan k’yau haka?.
Hannu Rahma tasa tarufe fuskarta, aiko mutanen d’akin sukaita mata dariya, mamansu ihsan ta ce, “wlhy yaha nimadai tun d’azu nake kallonta, Abdulmaleek yarik’e mana ita da k’yau, ALLAH dai yak’ara baku zaman lfy.
Akace amin.
Duk firarnan da akeyi Safna jitake tamkar ta had’iyi zuciya tamutu, duk saima taji tatsani ‘yan cikin d’akin.
Na ce, ” Safna aiduk Wanda baiji bariba to zaiji hoho.😜
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Haka Safna tacigaba da jiyya kullum dangi na jerangiyar dubata, su ya ishaq dukansu sunzo da matansu suma, Rahma kullum acan take yini, bobo yakaita idan zayi aiki, idan kuma yataso yabiyo tanan su wuce gida.
Zuwan bobo asibitin bak’aramin tada hankalin Safna yakeyiba, duk sanda yazo saitayi kuka a6oye shiyyasa ta k’agarama a sallamesu su koma gida.
Cikin kuwa ikon ALLAH yau doctor yabasu sallama, ba k’aramin farinciki Safna tayiba Dan har fuskartama saida tanuna, to suma dangi kowa yayi farinciki damata addu’ar k’ara samun lafiya.
Haka suka rankaya suka fito domin tafiya gida, akuma daidai wannan lokacinne motar bobo tashigo asibitin, fitowa yayi ya iso garesu, yarissina yamik’a gaisuwa gasu ummi tareda fad’in lfy dai naga kun fito?.
Rahma ta ce, an sallamemu aii.
Murmushi yayi yana kallon safna, a lallai auntymu yau sai kwanan gida ko?.
Dariya akayi itakuma Safna tad’anyi murmushi.
Abba ya ce, “Rahma to kibi mijinki kuwuce gida ko.
Rahma ta marairaice fuska tamkar zatayi kuka, amma batace komaiba.
Dafata ummi tayi ta ce, ” kije kinji autata ainasanki akwai biyayya…….
Bobo ya katse ummi da fad’in ummi ki barta kawai muje muyima auntynmu rakkiya har gida.
Kallonsa Rahma tayi tanaijin farinciki, haka suka rankaya suka tafi.
Bak’aramin farin ciki Rahma tashigaba data ganta yau agida, aiko haka taita yawo lungu da sak’o nagidan babu inda bata shigaba, itace har gidansu ya Kamal, sai bayan isha’i bobo yad’auketa suka tafi, dama Nawal tana gidansu Appa.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Rayuwa mai gudu da sauri, sakwanni sunata tafiya, mintuna sunata sauri, awoyi NATA gudu, akwana atashi babu wuya wajen ALLAH, Alhmdllh jikin safna yayi sauk’i sosai saidai abinda ba’a rasaba, shimadai jiyyar zuciyane narashin bobo.
Bayan sallamota ma Rahma tad’an zazzo ganinta dukda dai bata cika sake mataba amma bata damuba………….💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 48
Kasancewar yau weekend bobo yana gida, yanzu ma haka yana kwance bisa gadonsa dagashi sai wando 3½ da t-shirt mara nauyi, gefensa Nawal ce kwance tana barci, sai Rahma dake d’an kai kawo atsakar d’akin tsakanin dirowa da gado, kayan bobo damai wanki yakawo take shiryawa, kad’an kad’an takan yamutse fuska da cije le6enta, bobo daketa binta da kallo tun d’azun danba k’aramin tafiya dashi dressing nata yayiba, sanye take da jins blue yasha adon duwatsu daga saman cinyarta saikuma Riga pink t-shirt ta mata, kanta babu d’ankwalli tadaiyi farking nasa da pink d’in ribom, gashin yaywani Tim atsakkiya saboda kasancewarsa roba roba, yad’an lumshe idonsa yana shak’ar kamshinta daya baza d’akin, dukkuma motsin datayi saiya bigi hancinsa.
Rahma dake gyara linkin wasu kaya ta ce, “oga me wannan kalonfa?.
d’an murmushi yayi yana k’ara gyara kwanciyarsa har yanzu idonsa akanta, murya akasalace ya ce, “my cute zokiji wata magana mana.
‘Yar dariya tayi tareda nok’e kafad’a ta ce, ” nak’i wayon, nakula yau sokake kawai mushiririce agidannan batareda nayi aikin komaiba, kallifa agogo har 12 tayi amma banshiga kicinba, mikakeso muci da rana?.
Wata Narkakkiyar dariya yayi sannan Yakuma juya kwanciyarsa zuwa gareta Dan yanzun takoma jikin dirowa.
Ya ce, “to aii Indai dan tanine yau kiwuni ajikina kina bani ni’imtaccen k’amshinki ina shak’a tareda jin d’umin lallausar fatarki sannan naringa kallon k’yawawan idanunnan naki fararen wad’anda sai antara mata dubu ake samun mace d’aya mai irinsa, hakan kawai ya wadatar dani kuma zai k’osar dani fiyeda abincin dazanci.
Yabama Rahma dariya, Dan haka dariya takeyimasa sosai harda wata shashsheka mai d’aukar hankali dakuma kashe jiki, aikodai idanma tarkone Rahma keson d’anawa to tayi kamu, Dan kuwa tuni bobo ya narke agadon yana binta da wani shu’umin kallo, itakam dariyarta tacigaba dayi batareda tasan tarkonta Yakama zaki ba, kayan dasuka rage ta ida kwashewa tasaka adirowa, ganin yana niyyar sakkowa daga gadon yasata fita ad’akin dad’an gudunta, dariya tabashi yazauna abakin gado yanayi.
Itakam kichin tanufa domin d’ora girkin rana, Abu naga tasamu tarufe hancinta sannan ta kunna gas, yau wajen kwana biyu kenan batason kamshin gas d’innman, idan zatayi girki saita to she hanci shima a daddafe take gamawa, yau kuma ga abun yana Neman had’e mata biyu Dan cikinta ciwo yakeyi yana daurewane kawai.
Ruwan shinkafa tafara d’orawa sannan tabud’e firij tad’ebo naman kaji zata wanke, wani wuntsilawa da cikinta yayi ya tilasta mata rik’e murfin firij d’in, tadafe cikinta jitake tamkar tafasa kuka.
Daidai nan bobo yashigo kichind’in da zummar tayata aikin dan dama duk weekend tare suke aikin gidan, haka zaita tayata tana hanashi, amma saiyace yana koyi da ANNABIN ALLAH ne, Dan wannan sunnace mai k’arfi, tun tanajin kunyar idan yana tayata suyi bak’i harma yanzu tasaba abin yazamemata jiki.
Ganin takifa kanta tayi shiru yasa bobo fad’in lfy kuwa my Nusfuhayat?.
Bata iya basa amsaba saidai tad’aga MASA hannu, da Sauri ya iso Inda take, tabaya ya rungumota yana k’ok’arin juyo da ita, aijitayi tamkarma yak’ara mata ciwonne, tai saurin k’adandaneshi tana fad’in wayyo ALLAHna dadyn Nawal cikina, wayyo kamar ana tsitstsinkamin hanjina, da Sauri yazame abinda tarufe hanci dashi, aiko tana shak’ar k’amshin gas d’in sai yunk’urin amai, da gudu ta fisge jikinta daga gareshi ta arce waje, shima take mata baya yayi.
Abayin dake falon taja birki amai tafara zazzagawa kamar zata amayar da kayan cikinga, bobo dukya rud’e yarik’eta sai sorry yake mata.
Saida tagama yataimaka mata tawanke jikinta shikuma ya wanke Inda ta 6ata, cak yad’auketa suka nufi falo, zaunar da ita yayi ajikinsa yana fad’in sorry my cute duk-ya rud’e tamkar zaiyi kuka, cikinne yak’ara murd’a mata takuma k’ank’amesa tana kuka.
Shima sosai ya tallafota jikinsa, tuni ya janye hannunta daga kan cikin ya maye gurbin wajen danasa yana shafawa ahankali, can azab ta isheta takuma k’ank’amesa tana ambatar sunan ALLAH, tare suka k’arashe da bobo Daka gansa kasan yana cikin damuwa.
Ganin abun NATA k’ara gaba ya ce, “my Nusfulhayat Kodai asibiti zamuje?.
Da Sauri ta girgiza MASA kai tana cije le6e, hawaye da gumi kam sun jik’e fuskarta sharkaf dukda da AC dake aiki a falon.
Hijjab d’inta datakan ajiye afalo Indai tasan k’ananun kayane ajikinta, gudun kar bak’ yazo yasa takan ajiye, bobo yajawoshi yana share mata gumi da hawayen dasukaima fuskarta ado, wata damk’a data MASA yasakashi fad’in uchch my cute, ita batamasan yanayiba takanta take kawai, wayarsa yad’auka yakira ya sulaiman, ko gaisuwa bai tsaya sunyiba yafad’a MASA abinda ke faruwa, da Sauri shima ya sulaiman ya ce, “ganinan zuwa to.
Cikin mintuna k’alilan ya sulaiman ya iso gidan, har yanzu Rahma tana jikin bobo, kai tsaye cikin gidan ya sulaiman yashigo.
Bobo yad’auki hijjab d’inta yasakamata, hakan yayi daidai dashigowar ya sulaiman, basu tsaya ko gaisuwaba yashiga dubata, ‘yan tambayoyi yafara mata wad’anda duk cikin kuka da zafin ciwo take amsa masa.
Ya sulaiman yabama bobo wata kwalba, Abdulmaleek kakaita tayo fitsari mugani…..
Aibaima bari ya sulaiman ya k’arasaba Yasureta sai bathroom d’in dake falon, fitsari tayi a ‘Yar kwalbar sannan suka fito, nanmadai d’akkota yayi dukda tanata nok’e nok’e wai bataso yabarta zata iya da kanta, bai saurareta yasunkuceta suka fito.
Saman doguwar kujera ya direta sannan yamik’ama ya sulaiman kwalba.
Ya sulaiman yayi gwajin ciki, ganin abinda tsinken yanuna yad’ago yana fad’in Alhmdllh, fuskarsa cikeda murmushi.
Bobo dake binsa da kallon mamaki ya ce, “yaya lfy dai?.
Jinjina kai ya sulaiman yayi ya ce, “congratulations my lil bobo, Nawal tasamu k’ani ko k’anwa.
Rahma jitayi cikinta yak’ara juyawa Dan tsoro, shikam bobo Baki ya washe tareda d’aga hannu sama ya ce, “Alhmdllh ala kulli halin”, yataso suka rungume juna shida ya sulaiman, ya sulaiman dai sai dariya yake masa.
Nandai yarubuta maganin dazata buk’ata sannan yamata allura wadda saida akasha fama tayarda akayi, sai sinne kai take Dan kunya tak’i yarda su had’a ido da bobo barema ya sulaiman.
Cikin mintuna kad’an barci ya d’auketa.
Ya sulaiman yakalli bobo, Abdulmaleek kamarfa k’auri nakeji.
Da Sauri bobo yamik’e yana fad’in ya ilahi wallahi na manta tad’ora girki.
Cikin hanzari ya sauke tukunyar datasaka ruwan zafin shinkafa harya k’one kamas shine tukunyar tafara k’auri.
Kashe gas d’in yayi yafito.
Ya sulaiman yamik’e, Abdulmaleek bara nawuce gida.
Kai yaya tun yanzu?, koma ‘Yar hira bazaka tsaya ayiba?.
Dafa kafad’ar bobo yayi sorry bobon Ammi zanje wajen antynka kasan irin wannan ranarce kawai mukeda damar kasancewa da iyali.
Murmushi bobo yayi ya ce, ” hakane kam yayana.
fita sukayi suna dariya, saida bobo yaga fitarsa sannan yadawo gida.
d’aukar Rahma yayi yamaida d’akinsa, shima yakwanta suka hau barci abinsu.+
STORY CONTINUES BELOW

…………………………….
Haka rayuwar tacigaba datafiya, Rahma tanata shan laulayi Dan cikin NATA maisa laulayine, cikin ‘yan kwanaki dukta rame, bakomai take iya Ciba, yanzu hakama tadaina girki Dan batason k’amshin gas ko kad’an, kullum daga gidan Ammi ake kawo musu abinci safe da yamma Dan darana tana gidan AMMI, idan zaitafi aiki saiya ajiyeta can, idan kuma yataso yabiya ya d’auketa, daga shi har Ammi tarairaya suke mata ta musamman tamkar zasu maidata ciki, Appa ma ba’a barsa abayaba, duk abinda Rahma tace tanaso saiya siyo mata shi, kamar yanzune za’a haifi jikan farko agidan, ita wani lokacinma har kunyar kanta takeji, amma yazatayi badasonta take sakasu wata wahalarba tsirface kawai irinta ciki.
Nawal kullum idan tadawo makaranta tana nane da Rahma, maganarta bata wuce yaushe zaki haifomana babyn momy?.
Rahma takanyi dariya tacemata bayanzuba da sauran lokaci.
Wata sa in takanyi dariya wataran kuma kuka ta ce, ” itafa dawuri take so ahaifamusu sabon baby.
Idan Ammi ko bobo suna kusa ake diramar sukanyi musu dariya…….
…………………………….
Safna na kwance afalo ita kad’aice yau agidan, Abba yana kasuwa, ummi kuma tana gidan aunty yahanasu mamansu Basma, taje saka ranar auren Basma da akeyi yau.
TV take kallo amma bata fahimtar komai a film d’in dukda sonsa datakeyi tamkar mi.
Ta gyara kwanciyarta tareda kai dubanta ga hotonta itada Rahma sannan suna yara, sunyi matuk’ar k’yau duk sunyi murmushi, takuma kai dubanta gawani k’aton hoto Wanda yak’awatu da k’yau, kauda idanunta tayi tanamai share hawayen dake ziraro mata akumatu.
Dubana nakai ga hoton danson ganin suwaye ajiki?, hummm Rahma CE da bobonta sunyi masifar k’yau, hoton and’aukeshine aranar mother’s day, tanasanye da bubu shikuma bobon suit, tad’anyi k’asa da kanta yayinda bobo ke kallonta yana murmushi, ya munner agefensu yana bama Rahma wani Abu.
Masha ALLAH nafad’a azuciyata danba k’aramin k’yau sukayiba, dolene Safna taji 6acinrai, tamayi k’arfin hali databar hoton Agalon, kodayake tana tsoron ummi ne kawai nasani.
Sallamar da ake kwad’awane yasakata mik’ewa tana tsaki, k’ofar tanufa tabud’e, ganinsu zeenat da baseera yasakata k’are tamke fuska, tayi hakane saboda baseera.
Basuji komaiba gameda canjawar tata Dan sunsan halin kayansu.
Cikin falon suka bita, kowa yanemi gurin zama batareda tabasu izinin hakanba.
Itama tsanar baseerar datayi bai hanata had’o musu abin motsa bakiba kamar yanda tasaba, koba komai aii harda mai k’aunarta Zeenat.
Zeenat takalleta cikeda tausayawa ta ce, “Safna yak’arin k’arfin jiki?.
gyara zamanta tayi ta ce, ” da sauk’i Zeenat, aina warke.
Baseerama ta mata ya jiki, adak’ile ta amsa mata.
Zeenat takuma fad’in wlhy mu bamusan bakida lfy ba, mundai kwana biyu bakije school ba toshime mukace bara muzo muga ko lfy?, munshigo anguwar muka had’u da yaya kamal yake fad’a mana harma asibiti kika kwanta.
Safna tad’anyi murmushi wlhy kuwa zeenat har asibiti na kwanta yau kwana hud’u da sallamomu.
ALLAH yasa kaffarane.
Ameen.
Daga nanan sukayi shiru nad’an lokaci, Zeenat takatse shirun da d’akko zancen bobo.
Baki Safna ta ta6e saiga hawaye.
Arud’e zeenat da Baseera suka k’arasa gareta suna lallashi, dagananma har Zeenat ta zayyanemata yanda sukayi da Baseera a kwanankin baya, dakuma Nuna mata tayi nadama, itama suka Shiga mata nasiha da lallashinta da nunamata muhimmancin iyaye da had’arin bijire musu, baseera ta durk’usa har k’asa tana Neman gafarrar safna.
Ta ce, “tayafe mata, ALLAH ya yafemusu baki d’aya, daganan zeenat tak’ara musu nasiha itama, saikuma suka koma hira tamkar basune sukasha kuka yanzunba.
Anan suka wuni zubur suna k’ara kwantarma da Safna hankali dakuma k’ara bata shawarwarin yanda zata nemi gafarar iyayenta.
Saida ummi tadawo suka gaisa sannan suka tafi gida.
%%%
Da daddare bayan Abba yadawo suna zaune afalo shida ummi saiga ya Shaheed da ya munner.
Safna dake kwance ad’aki tamik’e tanufo falon Dan ganin ga dama tasamu na Neman gafarar iyayenta da ‘yan uwanta.
Tunda tafito kowa yamaida kallonsa gareta, ganin tanata ra6e-ra6e Abba ya ce ” safnata miya farune?.”
Tana tsaye saiga hawaye suna zirara akumatunta, ya munner sarkin tausayi yatashi yaje yakamo hannunta, zaunar da ita yayi kusada k’afafun Abba.
Abba yadafa kanta yana fad’in haba safna mike damunkine wai a ‘yan watanninnan?, kodai har yanzu jikinne mukoma asibiti?.
Kanta ta girgiza tana share hawaye, cikin shashshekar kuka ta ce, “Abba Dan ALLAH Ku yafemin Kozan samu sassaucin son Abdulmaleek dake son hallakani, wlhy Abba nayi nadamar abinda na aikata, nayi kuskuren bijiremuku akan abinda wayona bazai bani shiba, Abba narantse muku *_NAYI NADAMA_* (sabon buk d’in pertymerh xarah) Dan ALLAH Abba kujanye fushin dakukeyi dani kozan samu ubangijina yabar fushi dani………….nanta shiga basu labarin yanda akai tagane Abdulmaleek shine Wanda take so alokacin data bijire musu, tafad’a musu komai danganeda shawara da muguwar k’awa tabata, saidai ta6oye sunan kowacece kuma batafad’i zuwa gidan malami da bokayeba…….tarushe dakuma mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Tabasu tausayi sosai Dan haka suka shiga lallashinta, Abba ya ce, ” munyafe miki Safna domin kuwa ALLAH ya nuna miki kuskurenki tuntuni nadamace dai kika gagara yi saboda sharrin shaid’an, to ayanzunkam ki tabbatar kinyi tuba na gskya Wanda babu kome a aikata wani laifin makamancin haka.
Kanta tad’aga tana fad’in ngd Abba ALLAH yak’ara tsawon kwana da ikon cigaba da rik’emu, ta rarrafa gaban ummi tana kuka da Neman gafararta, ummi tajata jikinta tarungumeta, nayafemiki safna domin idan nace bazan yafemikiba bansan kuma wane irin gararin rayuwa zaki fad’aba nan gaba, nayafemiki ki kwantar da hankalinki kema ALLAH zai baki miji nagari domin Abdulmaleek yamik’e nisa ayanzu, shid’in mijin k’anwarkine.
Nanma kanta ta girgiza ta ce, “nahak’ura ummi tuntuni, saidai har yanzu inajin sonsa azuciyata, jinake tamkar kullum ana k’aramin sonsa, ummi ta6a k’irjina kiji, tayi maganar tana kamo hannun ummi tad’ora asaitin zuciyarta.
Ummi ta jinjina kai danjin bugun zuciyar Safna dake fita da k’arfi, tabata tausayi sosai, dama doctor Kaleel yafad’a musu zuciyarta tana barazanar kamuwa daciwo Ashe dalin son *_Abdulmaleek_* ne.
Lallashinta ummi taitayi da kwantar mata da hankali, suma su ya Shaheed da ya munner dukata rok’i gafararsu sunkuma gafartamata, tareda alak’awarin tayata da addu’a.
Nasiha sosai sukai mata mai ratsa jiki da jini.
Tundaga ranar Safna tazama wata shiru shiru amma har yanzu son bobo na nan mak’ayale da zuciyarta saidai Alhmdllh yaragu bakamar daba dayaso zame mata ciwo.
Yanzukam kulawa ta musamman iyayenta suke bata da k’arajanta ajikinsu, hakan nak’aramata kwanciyar hankali da k’aunarsu, haka rayuwar tacigaba da shurawa har ayau ranar wata juma’a da iyayenta sukazo mata dawata magana ta had’ata aure da yaya kamal, (Brr….kamal Abubakar, yayansu Ameera kuma abokin aikin bobo)……………..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 49
Safna tak’ara k’asa da kanta amma bata iya crwa komaiba.
Abba ya kalli ummi itama kallonsa takeyi, ya Shaheed ya ce, “Safna ke muke saurare, shin akaro na biyu kin amince da auren Kamal?.
d’ago idanunta dake cikeda kwalla tayi, ahankali ta jinjina kanta, muryarta na rawa ta ce, ” na amince iyayena, amma Dan ALLAH ina Neman wata alfarma agareku.
Abba yayi murmushi, kinemi kowace iron alfarma agaremu Safna, insha ALLAHU zamuyi miki inhar batafi k’arfinmuba.
Hawayen dasuka fara gangarowa visa kumatunta ta share, ta ce, ”Abba Dan ALLAH inhar ya Kamal baya sona to kuyi hak’uri kucanja min da wani, ahalin danake yanzun ina buk’atar mai sona dazai iya d’aukar duk wani Abu daga gareni kasancewar halin dana tsinci kaina acikj.
Gani nayi gabad’aya sunyi murmushi, ya muneer ya ce, “ki kwantar da hankalinki Safna, Kamal dakansa ya CE, ” yana sonki, kuma shine ya tuntun6i iyayenmu da maganar, abinda yaragemiki kawai shine krma ki koyi sons a, kema kifara k’ok’arin fidda *_”ABDUL-MALEEK”_* daga cikin zuciyarki, ki koma yimasa kallon mijin k’anwarki kuma d’an uwanki.
Jin jina kanta tayi tana murmushi mai had’eda kuka, ummi tajawota ta rungume Rana saka mata albarka, suma su Abba fuskar kowa ka kalla saikaganta wasai cikeda farinciki.+
Bak’aramin kuka Safna tashaba ayau, tasan yanzunkam bobo yamata nisa har abada, zeenat takira away a ta zayyane mata komai, shawara tak’ara bata tareda kwantar mata da hankali, nasiha sosai tamata mai ratsa jiki, hakanne yad’an k’ara rage mata damuwa.
Itama ummi tashigo takuma mata nasiha, zuwa yanzun hankalinta Yakima kwanciya, Dan koba komai kowa yana tausaya mata kuma yana lallashinta, zuwa yamma Kamal yazo gidan, jitayi tamkar tafasa ihu amma babu yanda zatayi haka tashirya tafito gurinshi.
Atsakar gida ta iskeshi visa farar kujerar roba, gakuma wata an ajiye kusadashi alamar tatace, sallamarta yasakashi d’agowa saga latsa wayarsa dayakeyi, murmushi yamata tareda amsa sallamar tata.
Tayi k’asa da kanta, gurin zama yanuna mata yana fad’in bismillah, Safna tad’an jawo kujerar bays sannan ta zauna, idonsa akanta ta ce, “ina yini.
Murmushi yayi sannan ya amsa, yad’anyi k’asa da muryarsa sannan ya ce, ” nifa banason sanyin nan dakika kowa, Madison ganinki tamkar safnar da mai tsiwarnan darashin Baron kota kwana, solon sanyi na Rahma be amma ba Safna taba.
d’an murmushin yak’e tayi Wanda yafi kuka ciwo, wato had yanzu kowa nakuma nunamata Rahma tafita k’yawawan halaye kenan, kwallah suka cika mata ido amma tayi jarumtar hanasu sauna visa fuskarta.
Kamal yad’an tsura mata idanunsa zuciyarsa cikeda nazarinta, tabbas ya yards da maganar bobo Safna tanada k’yau idankuma aka Shiva lamarinta za’a iya canja mata rayuwarta Mara k’yau zuwa mai k’yau, insha ALLAHU zaiyi k’ok’ari wajen canjata d’in, tabbas ada yaso Rahma run tana k’aramarta domin k’yawawan halayrnta sine suka dunkareshi darashin yin sure da wuri yana jiranta, alokacin dayayi shirin mik’a buk’atarsa ga iyayensu said auren Safna yatashi cikin gaggawa, yayi shirurune had akamala biking Safna da bobo asannan sannan yakaowo maganrsa da Rahma, saidai kasha al’amura said sukayi uyin wahainiya Auden Yakima kan Rahma, yashiga bak’inciki da tashin hankali awannan lokacin harya kasa halartar taro ko d’aya data tarurrukan auren Rahma da bobo, bak’aramin yak’i da zuciyarsa yayiba wajen bats hak’uri harta hak’ura yacigaba da rayuwarsa Lamar da.
Awata rana saiga sak’on takarda masinjan bobo yakawo office d’insa, sak’9n takardar yana k’unshe da shawara data bobo akan yanemi auren Safna domin tanada 6oyayyun halayr Wanda saita samu mai jagorantarta akan hanya mai k’yau zasu fito.
Da farko bai d’auki maganar taxa serious ba, saidaga bays yazaina yay nazari sosai tareda k’arin k’arfin guywa da bobo kebasa aduk sands suka had’u, saikuma yaji yakamu Dawson Safna d’in, saidai kuma bayason tad’auki halin sanyi irinna Rahma Dan hakan zai iya jawowa son Rahma yaringa motsa NASA harya aikata wani Abu ga Safna a madadin Rahma, shikuma Sam bayason tagane yama ta6a son Rahma d’in a baya, wannan me yasa yamata magana akan komawarta safnarta taxa mai tsiwa………..
Jin yayi shiru gashikuma yadasa mata idanunsa ko k’yaftawa bayayi yasakata fad’in ya Kamal mikake tunani?.
Firgigit yayi yana murmushi, yagyara zamansa ya ce, “nayi zurfi akogin sonkine my Safna, INA data kema kin kar6eni amatsayin masoyi na had abada, inaso mutaru nidakr mushare hawayen juna my mantar da kanmu munta6a son wasu abaya, mutaru mugina sabuwar rayuwa maicike da abubuwan sha’awa ga al’umma.
Kallonsa tayi cikeda mamaki, asaninta ya Kamal baita6a budurwaba Dan bata ta6a jin hakan abakin kowaba, NASA daurewa tayi ta ce, ” ya Kamal damage kata6a soyayya?.
d’an murmushin takaici yayi sannan ya ce, “nata6ayin makauniyar soyayya abaya domin ba’asan inayiba, wadda nayi Dan it a batasan nayiba harta su6ucemin, amma ayanzu kid’auka babu it a araina saike kad’ai kuma INA Neman taimakonki mutaru muk’ara karfin ginin soyayyar kodan mugudu tare my tsira tare, Safna nami alk’awarin share mini hawayenki inhar INA numfashi, kuma zan nuna mini soyayya da k’auna iya iyawata.
Hawayen dasuke zirara akumatunta ta share, cikin rawar murya ta ce, ” ngd ya Kamal amma Dan ALLAH INA rok’onka kayi hak’uri daduk halin dazaka ganni had zuwa lokacin da komai zai daidaita mugina ni’imtacciyar rayuwa Lamar yanda kabuk’ata.
Murmushi yayi tareda mik’a mata hanky d’insa ya ce, “karki damu my sweery na, mijinki ya fahimceki kuma zaimiki dukkan uzuri kinji.
Kanta ta jinjina tana murmushi tareda share hawayenta da hanky d’insa, sunyi ‘Yar hira duk akan yanda biking Nash zai kasance, sannan yamata sallama yatafi………
STORY CONTINUES BELOW

.*.*.*.*.*.*.*.*..*.*.*.
Rahma kwance visa gadon Ammi tana sharar barci bayan tagama con d’anwaken filawa Wanda ayanzu yazame mata abinci akoda yaushe, haka take wuni barci tamkar kasa, saidai idan lokacin sallah yayi ammi ta taxa ita tanayi kuma wata sa in zata 6ingire akan sallayar, yanzu haka kosu bobo batasan sundawo saga masallacin juma’a bama.
Matansu ya ishaq gaba d’aya suna falo tareda yaransu, sai kuma wasu bak’i dangin Appa dasukazo musu bangajiyar biki dansu basu sami Samar zuwa bikinba.
Appa da ammi dasu bobo kam suna falon appa ana shari’a.
Su ya Hamza me suna kai maganar ganin bobo da Safna dasukayi ana jibi auren su khursiyya.
Shine appa yake kallon bobo cikeda alamar tambaya, Mukarram kafad’a mana gsky mike tsakaninka da ita?.
d’an cije le6ensa yayi cikeda 6acinrai, bai ta6a zaton ‘yan uwansa zasu zargesa da wani mummunan abuba bare harsh kawo maganar ga mahaifansu, tuni idonsa yad’an sauya kala, duk said a ya kalli ‘yan iwan NASA sannan yafara zayyane musu komai fake tsakaninsa da safna, tundaga farkon had’uwarsu had zuwa ganin dasuka masu aranar, yad’ora da fad’in saidai gsky kunbani mamaki Dan banta6a zaton zaku zargeni da Abu makamancin hakaba, raina ya6aci bazan 6oye mukuba, danni ko’a mafarki bazan ta6a zarginku da aikata Abu makamancin haka Mara k’yauba..
Gaba d’aya sai jikinsu kuma yay sanyi, sungane gsky basu k’yautaba, kosu kad’ai ya Isa sumasa maganar basai sunzo gaban iyayensuba, amma sumafa sunada hujjarsu nayin hakan.
Yunk’urawa bobo yayi yamik’e danufin barin wajen, da sauri ya Hamza dake kusadashi yaruk’o hannunsa, bai juyoba baikuma kwace hannun nasa saga rik’on Yaya Hamza ba.
Ganin haka Appa ya ce, ”mukarram dawo kazauna.
Itadai Ammi batace komaiba binsu kawai takeyi da kallo.
Baya bobo yadawo ya zauna danshi mutumne dabaya k’etare maganar iyayensa komaiba kuwa son dayakrma Abu sukace yabarsa to zai barsa, Duke kuma k’in dayakema Abu sukace yayi to zaiyi inhar bai sa6ama shari’aba, zan iya cewa wannan tarbiyyar yaran guidance gaba d’aya Dan kunsan halayensu d’ayane suduka.
Inda yakeda Yakima ya zauna, nasiha Appa yashiga yimusu, sannan yanunama kowa kuskurensa dagasu had bobon, gaba d’aya kuma said jikinsu yayi sanyi, ganin nayi suna mik’ama juna hannu suna musabaha, duk kuma suka bama bobo hak’uri daneman afuwarsa shima hak’urin yabasu saboda kasa fahimtarsu dayayi, saga nan hira mai dad’i sukacigaba day I kamar basuba, said a aka kira sallar la’asar sannan suka mik’e zuwa masallaci.
…………………→
Koda suka dawo masallaci sai duk suka zauna afalon k’asa har Appa.
Bobo dai daya wawwaiga yaga babu Nusfulhayat d’insa saiya mik’e, harya kama k’arfen benen zai haye Ammi ta ce, ”mukarram sai ina?.”
Kunyace takamasa yad’an sosa kansa umm Ammi zand’an duba abune.
Ammi ta hararesa zakaje duba Abu kokuma zakaje tada Rahma me.
Dariya kowa yakeyi danganin yanda bobo ya Sosa k’eya alamar an harbo jirginsa.
Ammi ta ce, “to dawo kazauna, nibansan miyayake tsolemaka idoba idan Rahma tana barci saikayi yanda kayi katada it’s, bayan kuma kasan barcin nata na lalurane.
Dawowa yayi yanad’an zum6ura baki, yaje Kusada k’afafun Appa ya zauna.
Kansa Appa yashafa yana murmushi ya ce, ” babana yaushe ka koyi k’arya?.
Lah Appa bafa k’arya nayiba nafad’ane kawai ba daidaiba.
Nanma dariya sukayi, ya ishaq ya ce, “ALLAH ya shiryaka Abdulmaleek.
Amin babban Yaya bobo yafad’a yana dariya.
Rahma dake niyyar sakkowa takoma da baya, tun d’azu ta tashi tayi sallar la’asar, sanda bobo ke k’ok’arin hawowa it’s kuma tana niyyar sakkowa, jin maganar da Ammi take masa yasata la6ewa, duk abinda ke faruwa itama tanaji tana dariya dagacan.
Kangado takoma tad’auki waya tana chatting abinta Dan tanajin kunyar fita falon k’asa.
Ganin lokaci yaja ammi ta ce, ”hibba taje ta tado Rahma.
Mik’ewa tayi tana fad’in to Ammi.
” araina na ce, “yarinyarnanfa tafara zama ‘Yar budurwa, to yanzu tana samun kulawa yanda yakamata gasu ammi, ga karatu tanayi a tsadajjiyar makaranta, komai tasamu na fannin rayuwa itada iyayenta da yayanta Idris.
Akeance hibba ta tartar da ita tana chart, Rahma tad’ago tana kallonta da murmushi, itama hibba murmushi takeyi, ta ce, ”anty!, ammi ta ce, ” kitashi hakanan lokacin sallah na k’urewa.
Mik’ewa Rahma tayi tana fad’in ainama tashi tuni nayi sallah muje kawai hibba.
Koda suka fito falon Rahma ta rissina tagaida Appa da Ammi, ta Haida su ya ishaq, idon bobonta na kanta, yitayi tamkar baya gansaba harta zauna sannan tad’an sack kallonsa, har yanzu shima ita take kallo, tad’an murgud’a masa baki, nuna kansa yayi waishi?. Saida tad’an faki ido sannan tamasa gwalo, kansa yagirgiza alamun zata gane kurenta idan tazo hannunsa.
Duk abinda sukeyi Appa na lura dash, murmushinsu na many a kawai yayi yana girgiza kai.
…………………………°
Alhmdllh komai yana tafiya yanda yakamata, Rahma anata jan ciki, masha ALLAH tak’ara k’yau abinta, soyayyakam itada bobonta sai Wanda yagani, tarairayarta yake tamkar kwai acokali.
Ana cikin haka kuma aka saka bikin Safna da ya kamal wata d’aya kacal, za’a had’a bikinsu Dana Ameera, bak’aramar murna Rahma tayi dajin sannan labariba, haka taita rok’on bobo saiya kaita gidansu.
Aiko dolensa yakwasheta itada Nawal yakaisu suka wuni, lokacin dasuka Isa basu iske Safna agidanba yana gidan ya Shaheed, sai yamma tadawo ta iskesu, ta amshesu babu yabo babu fallasa, Rahma sarkin hak’uri kuwa farincikinta ta nunama Safna sosai, tareda fatan ALLAH yakaisu susha Niki.
Safna dai batace mata k’alaba harta k’araci murnarta tabarta.
Sai bayan isha’i Bobo yadawo yad’aukesu, safna har kuka tayi bayan tafiyarsu, dayansu ita bobo yazo d’aukafa, dayanzu itace d’auke da cikinsa, amma rashin biyayya ga iyaye yaja mata😭……………💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 50
BAYAN WATA →1
Bikin su safna ya kankama, anata hidima dakai kawo, yau takasance ranar kunshi suna tsakar gida itada Ameera da k’awayensu irinsu zeenat baseera da sauransu, masu k’unshine har uku sukema k’awayen amaren, saikuma Basma datakema Ameera da Safna harma angama ma Ameera yanzu safna akeyimawa, hira da barkwanci aketayi irinna taron k’awayen amarya.
Duba nakai ga fuskar safna, kadaran kadahan take, bata d’aureba sannan kuma bata saka baki cikin hira da dariyar k’awayen nasu.
Rahma ta fito daga cikin falon hannunta d’aukeda filet na d’anwake dayasha yaji, sanye take dajar atanfa zani da Riga, rigar fitet ce wannan yabama matashin cikinta damar fitowa d’as, bak’aramin k’yau cikin Yamataba, gashi yakaramata fari da ‘yar k’iba masha ALLAH, ga atamfar takuma haska k’yawun halittar jikinta.
Da yawan ‘yammatan wajen bak’aramin birgesu Rahma tayiba, taja kujera ‘Yar tsigunno tazauna tana fad’in kai aunty Ameera k’unshinfa yabada ma’ana tafad’a tana k’ara lek’a k’afar.
Murmushi Ameera tayi ta ce, “da gsk auta?.
Wlhy kuwa yau duk kunfito amarenku keda aunty safna.
To mungode, ke sai yaushe za’a miki naki?.
Saita gama muku ‘Yar wulak’ancin idan ta gadama, nikoma zan iya jure zaman?, Rahma tayi maganar tana hararar Basma.
Dariya Basma tayi ta ce, ” karki damu uwar uku dolene namiki kodan ya Abdulmaleek yagani.
Rahma ta d’akama Basma duka a baya ‘Yar fatan tsiya ukun lfy?, nama haifi d’ayan mana, saidai ke ALLAH yasa Ranar damuka kaiki ki samo mana biyar nasan Yaya Salman bazaiyi wasaba.
Basma dake shafa wajen da Rahma ta doketa ta ce, ”Mara kunya wlhy Rahma kin fetsare.
Dariya Rahma tayi tanacin d’anwakenta dayaji uban yaji sai faman sheeeee! Take da baki saboda zafin yajin, ta ce, “kibari zan fad’amiki yanda akayi na fetsare.
Anty Ameera ta ce, ” ALLAH ya shiryeku yarannan, yanzufa Rahma saitace ta girmemu ko?.
Dariya duk ‘yan wajen keyi, wata acikin ‘yammatan amaren ta ce, “eh mana tunda tarigaku shiga daga cikin itace babba yanzu.
Dariya suka kuma shek’ewa da ita wasu harda tafawa.
Safna dai fuskarta tamau babu alamun annuri, dan ita hirar tasu ba burgeta takeyiba.
Wayar Rahma yafara Wringing, d’auka tayi tana murmushi, cikin wata sassanyar murya da kowa bayajinta awajen harsu Basma ta ce, ”Assalamu alaika ya Nurulk’albi.
Bobo dake zaune a office d’insa sanyin AC da k’amshin turarensa na ratsashi yalumshe idanunsa yana wani murmushi na musamman tamkar yana gabanta ya ce, ” wa’alaikissalam my Nusfulhayat, ina fatan kina cikin nagarta da aminci da k’oshin lafiya keda babyna?.
Murmushi mai sauti Rahma tayi cikin salonta ta ce, “Normal Muke, kaima muna fatan kasancewarka cikin kuzari da jarumta irin na ma’aikacin kwarai mai k’ok’arin kare hak’in al’ummarsa?.
Alhmdllh my Nusfulhayat duk abinda kike hasashe agareni ALLAH yasaukar da ni’imarsa agareni musamman dakika kasance mai yawan tunatar dani waye ni akowane dak’ik’a na rayuwata.
Masha ALLAH Rahma tafad’a murya anarke.
K’ara lumshe idanunsa yayi dak’ara lafewa cikin kujerar yanad’an lilakansa akujerarsa alamun yanajin dad’in yanayi da hirar dasukeyi, ya ce, ” mikikecine haka kiketa faman shan yaji?.
Dariya mai Narkar da zuciya Rahma tayi ta ce, ”canki mana.”
Shiru bobo yayi yanad’an nazari, zuwa can ya ce, “tom saidaifa muyi da sharad’i?.
Hummm sharad’in mi?.
Idan na canka dai-dai to yaufa babu k’orafi awajen barci, dannaga wani guduna akeyi yanzu.
Dariya mugunta Rahma tayi ta ce, ” nayarda Dan nasan bama canka zakayiba.
Shima dariyar yakeyi ya ce, “kardai ki cika baki.
Batace komaiba saidai tayi murmushi.
Shima shiru yayi yana tunanim mizaice?.
Rahma tayi gyaran murya.
Ai kamar ta zurgud’a masa allura ya ce, ” d’anwake kikeci.
Shiru Rahma tayi, shikuma shirun datayi yabashi damar tuntsurewa da dariya yana fad’in naci gari, yarinya yau ki shirya babu d’aga k’afa.
Kukan shagwa6a Rahma tasaka masa tana fad’in itadai bata yardaba.
Dariya su Basma suka saka mata har bobo na jiyosu.
Safna kam tsaki taja ta na kauda kai.
Rahma tajuya baya danjin suna mata dariya, jin dariyar dayake mata shima yasa tadage akan bata yardabafa.
Shima dagacan cikin dariyar ya ce, “ahaf ‘yammatana ai babu hanyar ku6ta, kima shirya tarbata Dana tashi daga office zanbiyo mutafi gida nasha Amarcina yanda yakamata.
Da sauri ta ce, ” banida lfy fa.
Karki damu inada magani, yana gama fad’a ya Yanke wayar yana cigaba da mata dariyar mugunta.
Ameera tarik’e ha6a oni auta d’an koyamin shagwa6ar nan mana nima na iyata, Rahma tarufe fuskar tana dariya, Ameera ta ce, “yo ALLAH kanama mijinka wannan shagwa6ar ai babu inda zai fita, shiyyasa ya Abdulmaleek baya ganin kowa saike kad’ai.
Tashi Rahma tayi tabar wajen suna mata dariya.+
STORY CONTINUES BELOW

K’arfe *_5:6pm_* bobo ya iso gidan, ak’ofar gida yatsaya yakira wayarta, alokacin Rahma ta na zaune kusada ummi tana zubamata shagwa6ar wai k’irjinta na ciwo, ummi tashafa kanta tana fad’in auta saidai hak’uri, ba’a Raba mai cikin da irin wad’annan k’ananun ciwuwwukan harsai anhaihu suke dainawa.
Baki tad’an turo sannan tazame ta kwantar da kanta bisa cinyar ummi.
Ummi ta ce, ” sannu autana.
Kanta tad’aga cikin salon shagwa6a.
Dariya ummi tamata tana fad’in auta Abdulmaleek yana fama da wannan shagwa6ar taki, kekiyi Nawal tayi gakuma baby zaizo.
Hannu Rahma tasa tarufe fuskarta tana dariya.
Ana cikin haka kiran bobo yashigo, akunyace tad’auka tasa akunne batareda tayi maganaba.
Bobo ya ce, “kifito muwuce ina mota.”
Cikin muryar kamar zatayi kuka ta ce, “wayyo ALLAH tun yamzu?.
Haba my Nusfulhayat gobe idan ALLAH yakaimufa zaki dawo, nima atausayamin mana.
Baki takuma zun6urowa tamkar zatayi kuka, shikuma dagacan ya ce, ” inajiranki, ya Yanke wayar batareda yajira cewartaba.
Lalla6ata ummi tashigayi Dan taji wayar dasukayi, mik’ewa Rahma tayi tashirya tanatama ummi shagwa6a harda ‘yan kwanlanta, tayima mutane sallama tafito, cikin mota ta iskeshi, koda yashiga sallama kawai tamasa ta zauna tajuya masa k’eya.
‘Yar dariya kawai yayi yatada mota suka tafi, shima baice da ita k’alaba har sukayi nisa, tuk’insa kawai yakeyi yanabin karatun alkur’anin dake tashi amotar cikin suratul Nurr.
Itama Rahma tayi shiru tanabin karatun ahankali cikin k’ira’ar shiek Abdurrahman sudies, takula bobo yanason karatunsa.
Koda sukaje gida bata tsaya jiransaba tabud’e motar tafice abinta, binta yayi da kallo yana wani shu’umin murmushi, shima fitowa yayi yakwashi tarkacensa ya take mata baya.
Afalo ya isketa kwance akan 3sita, tana ganinsa tafara cije le6e.
Dariya tabashi Dan yasan sarai pretending ne datasaba masa a ‘yan kwanakinnan, baisan miyasa yanzun batason yara6eta dasunan auratayyaba.
Yi yayi kamar bai gantaba yawuce d’akinsa, harya kai k’ofa ta ce, “wai Nurulk’albi yaushe zaka d’akko mana Nawal ne?, wlhy nayi kewarta gidan babu dad’i kuma.
Bakinsa yad’an ta6e cikin zolaya ya ce, ” sai randa momynta tabar guduna, baki ta turo shikuma yashige d’akinsa yana murmushi.
Itama mik’ewa tayi tanufi d’akinta, suduka kowa wanka yashiga.
Bobo yana fitowa ya tsane jikinsa ya zira jallabiya yafito, d’akin Rahma yad’an lek’a, daga bakin k’ofa ya ce, “My Nusfulhayat natafi masallaci.
Kanta kawai tad’a masa tana cigaba da tsane ruwan jikinta, Dan fitowarta kenan daga wanka itama.
Bai shigoba sai bayan isha’i, tana zaune afalo daga ita sai wando na jins pink iya cinyarta tasaka best fara tas sai tashin k’amshi takeyi.
Kallo d’aya bobo yamata ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya, sannu tamasa, ya amsa yana lumshe idanunsa, d’akinsa yanufa, mintuna kad’an yafito dagashi sai gajeren wando da best, hannunsa d’aukeda laptop da wayoyinsa, zama yayi kusada ita yasaka hannu afilet d’in kayan marmari datake sha.
d’ago ido tayi tana kallonsa, yad’aga mata gira tareda kanne idonsa d’aya.
Kauda kai tayi gefe tana murmushi, zuwa can kuma ta ce, ” Nurulk’albi serious ina kewar babyna fa.
Hannunsa na haggu yasa yatallafota zuwa jikinsa, yankan abarba yad’auka yasaka mata abaki, ya ce, “nima ina kewarta my cute amma haka zamu hak’ura tak’arasa hutunta a can, kullum k’orafin mama ba’a kaimata Nawal Hutu, shiyyasa wannan karon nace taje ta musu kwana biyu, tokuma gashi sun rik’e mana ita, d’azuma sunzo office d’ina itada musaddiq, kiyi hak’uri kinji, data kammala hutun zata dawo garemu, Nawal batada wata uwa aduniya sai ke kinji.
Kanta tad’aga tana masa murmushi, yacigaba dabata fruit d’in yana fad’in har andaina fushin?.
‘Yar harararsa tayi cikin sigar wasa, ta ce, ” aikasan bana iya fushi dakai Nurulk’albi, soyayyarka ta mamaye dukkan jikinna da 6argo ruhina da jinina, wad’an nan matakan tsaron daka gark’ame ilahirina jikina dasu basa Barin masarautar zuciyata dogon fushi dakai, inasonka dayawa bobona, har zuciyata tanayi tamkar zata faso daga k’irjina zuwa gareka musamman alokacin data nisanta da ‘Yar uwarta.
My zumana kai namusamman ne, kai jarumine acikin jarumai, kai gwanine acikin gwanaye, kazama zaki acikinsu, tutar nagarta na hannunka kad’agama sauran maza saidai subika abaya kosunaso ko BASA so kuwa…..
Wani sanyin dad’ine yaratsa zuciya da 6argon bobo, yad’uki filet d’in kayan fruit d’in ya ajiye saman Santa tabir, k’ara matsota yayi jikinsa yashiga nuna mata zallar k’auna da zazzafar soyayya mai cikeda alfahari gaduk macen data sameta ga mijinta, sunkai rabin awa yana Abu d’aya, Rahma kam tana k’ara harhad’o hanyoyi da gudummawa na taimakonsa, sun lula basajinkira, gabansu kawai suke hange amma ba bayaba, saida suka nutse bisa tirbar soyayya kowa yakuma yarda da jarumtar nagartacciyar soyayya daga d’an uwan nasa sannan suka tsagaita tareda tsurama juna shu’umin kallo kowa na zubda kwallar farinciki da ni’imtaccen so tsaftatacce kuma gawurtacce.
Rungumeta Yakuma yi yana lashe dukkan hawayen dake zirara bisa kumatunta tareda shiryamata nutsatstsin kalamai masu nisan kiwo ga ballagazar mace.
Bayan ya sarara itama talashe nasa tas suna mai k’ara dulmiya cikin farinciki da nutsuwar kasancewa tare tamkar kowane ma’aurata dasuka kasance cikin inuwar aure.
Bayan shud’ewar mintuna kamar ashirin suka 6ararraje a tsakkiyar falon, Rahma najikin bobo kwance suduka idonsu nabisa laptop d’insa dayake danne-danne da’alama yana aikin daya shafi office ne, Dan gaba d’aya daga ita harshi sun maida nutsuwarsu ga abinda yakeyine..
Sunkai tsawon awa biyu ahaka kafin bobo yad’ago idonsa visa k’yak’yk’yawar fuskar Rahma dake barci tun d’azu.
Murmushi yayi yana fad’in kasa kenan, kedai yanzu ba’a hira dake, da amfara saiki 6ingire barci, aiko zama kitashine Dan yau bazan iya jurewaba.
Kwanciyarta ya gyara mata wai tak’ara samun barci kafin yagama, haka yacigaba da aikinsa lokacin-lokaci yakan kur6i lemon data ajiye masa.
Yaja lokacin mai tsawo yana aikinsa da Rahma lafe ajikinsa, zuwa can yad’aga kai yakalli agogo, d’an zare idanu yayi danganin shabiyu harta wuce, agurguje yak’arasa abinda yafara, ya rufe laptop d’in yad’auki Rahma zuwa d’akinsa, saida ya ajiyeta sannan yakoma d’akinta yad’akko mata kayan barci yakwashi tarkacensa yakoma.
Kayan barcin ya canja mata shima yasaka nasa sannan ya haye gadon, mugunta irinta bobo bai k’yaletaba saida ya tada ita ya raya sunna sananan…….😎.
______________________
Biki yayi biki, yau aka gudanar da kamu daya k’ayatar aharabar gidansu Safna, anhad’eshi gaba d’aya itada Ameera, komai ya k’ayatar damutane, zuwa gab da magriba aka tashi.
Daga nan ancigaba da gudanar dabiki su Rahma amarori k’irjin biki danma ciki namata cikas bata iya komai yanda yakamata.
Ahaka aka wayi gari yau asabar safiyar d’aurin aure, Kujiba-kujiba su Rahma aketa sha Dan annan takwana, dak’yar bobo ya yarda ta kwana saida Ammi ma tasaka baki sannan, aiko gidan Ammi ya kwana wai bazai kwana gidansu shi kad’aiba kewa ta isheshi, dariya Rahma taitayi masa shikuma yana hararta.
*_2:30pm_* dai-dai aka d’aura auren Safna bilal Basheer mai Gold & Kamal Abubakar Basheer, sai kuma Ameera Abubakar Basheer & Hafeez Lukman sa’eed.
d’aurin aurene daya Tara d’unbin al’ummar Annabi, Appa dasu ya Hamza ya ishaq ya sulaiman bobo Ammar Musaddiq idris duksun halarci taron d’aurin auren.
To saimuce ALLAH yasanya alkairi safna da Ameera da ya Kamal da hafeez, duk ALLAH yabaku juriyar zaman ibada da hak’uri Wanda akasan ma’aurata dashi.🤓
Bayan gama d’aurin aure su bobo abokan ango suka shigo tareda anguna domin d’aukar hotuna, bak’aramin tashin hankali Safna tashigaba da ganin bobo, jitake tamkar tad’ora hannu aka tarushe da ihu amma babu dama, sai satar kallonsa takeyi, shima yana kula dahakan shiyyasa yakoma can gefe nesa da inda take tsaye da k’awayenta.
Cikin ikon ALLAH ma saiga Rahma ta fito daga falon itadasu aunty ummy matansu ya Sulaiman, k’arsowa sukayi wajen suna gaisawa da angunan, Bobo yakamo hannun Rahma yana fad’in woow my Nusfulhayat kinyi k’yau, nakuma gode miki dakika saka gyale bakifito harabar gidanan hakaba.
Murmushi tamasa ta ce, “Murulk’albi na nasanka da kishi Dan haka zanyi k’ok’arin toshe duk wata hanyar da kishinka zai motsa.
Lumshe idanunsa yayi yana murmushi jin dad’in furucinta, zungurarsa ya Kamal yayi kai malam agabanfa jama’a kuke.
Dariya bobo yayi ya ce, “d’ansa ido miya kawo idonka kammu?, kabar amaryarka can kataho nan neman gulma, halan Ammar ne ya cinnoka Dan nasan yashahara sosai awannan 6angaren.
Ammar dake jinsu ya ce, ” indai har na shahara tokuwa kai ka gawurta fitsararre.
Duka bobo yakai masa, Ammar yakauce yana fad’in abin kunya bobo agidan surukai saika nuna hali?.
Rahma dake dariya ta ce, “Nurulk’albi kabar Yaya Ammar zamu ramane.
Hakane my Nusfulhayat saiyazo gidanmu zamu tararmasa.
Dariya sosai ake musu, ‘yammata dayawa sun k’yasa matasan samarin k’yawawa masu wadataccen ilimin addini Dana boko.
Dayawan ‘yammatan wad’anda suka San labarin bobo abakin safna sukan tayata jimamin rasasa Dan babu k’arya guy d’in yahad’u tako ina, hotuna akayi kowa sotake taga tafito kusada bobo amma Rahma takasa ta tsare tana manne dashi ako ina ko ‘Yar kunyar nan tata yau ta tureta gefe gudun kar wad’annan manyan ‘yammatan dasuka FItA wayewar boko Suyi mata suruf bahana da Nurulk’albi d’inta.
Bak’aramin kishine ya turnuk’e safna ba, amma haka ta daure tadake akayi hotunan aka gama su bobo suka tafi.
Shagalin biki yacigaba da gudana acikin gida……….. .💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 51
Zuwa dare aka halarci dinner faty daya tara d’unbin al’umma, ita Ameera ankaita gidan mijinta tund’azu, dagacanma suka taho dinner d’in, safna kam sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu tunda angon d’an gidane.
Amare da angwaye kam sunsha k’yau matsa ALLAH, fuskokinsu duk cike suke da annuri da akasan amare da anguna nayi aranar bikinsu, balaifi awannan karonma safna tad’an saki jikinta.
Sai hange-hange da lek’e-lek’e nakeyi amma ban hangomuku Rahma da bobo ba saboda cikar da wajen yayi.
Sai awajen lik’i ALLAH yabani nasarar sauke idanuna kan Rahma da bobo dasuketa zubama su Safna lik’i, Rahma taci ado cikin less yellow riga da zani buba kamar d’inkin yarabawa, ta nad’e kanta da blue d’in d’ankwali sark’arta ‘yan kunnenta dakomai blue ne, bobon tama sanye yake da shadda blue sai maik’o da d’aukar ido takeyi, shikam komai ajikinsa blue ne, sai kamshi suke zabgawa tamkar sune amarya da angon.
Tunda suka fara musu lik’in idanun safna da Kamal akansu kowa da abinda yake tunani, sukam sai zabga murmushi sukeyi hankalinsu kwance, ganin kud’in dasuke zazzagarwa mawak’i yafara wasasu tamkar sukad’aine a hall d’in taron.
Safna dai data kasa daurewa saida tayi kuka, kular da bobo yayi yasashi kama hannun Rahma sukabar wajen.
Inda sukeda suka koma suka zauna, awajen bada cake ma safna saida suka had’a ido da bobo, murmushi yamata kawai yana masu tafi, murmushi nasa ya sanyaya zuciyarta Dan haka itama tayi.
Araina na ce, “safna kinada aiki wlhy, yakamata kihak’ura hakanan.🤓+
Rahma tanarke ajikin bobo tana yatsine fuska, tallafota yayi sosai zuwa jikinsa ya ce, ” my Nusfulhayat ya dai?.
Shagwa6e fuska tayi, Nurulk’albi barci nakeji.
Idanunsa yad’anzaro waje, barci kuma?, bafa agama ba.
Takuma yatsine fuska nidai wlhy nagaji hayaniyarnan tama isheni.
Kingani ko, saidafa nace kiyi zamanki karkizo kikak’i, to gashinan tun ba’aje ko’inaba harkin gaji.
Tab, nazauna agida wata ta manne maka, inacan nikuma sagaga da baki.
Dariya tabashi amma saiya gimtse, yay nufin zolayarta, my cute nifa mijin mata hud’une, kumafa inada sha’awar k’ara aure.
Zame jikinta tayi daga nasa, amamakinsa saiyaga tamik’e zata bar wajen, da sauri yaruk’o hannunta yana fad’in sorry my hayatee wasa nakeyifa, dagake aii babu k’ari, dukda haka bata saurareshiba, su ya hamza dake kusadasu kowane da matarsa suka shiga musu dariya, Ammar ya ce, “karki yarda Rahma dad’in bakine kawai yanada budurwa.
Hararsa bobo yayi ya ce, ”tod’an had’i kuma tunzurata…….
Baijira cewar ammar ba yabi bayan Rahma da sauri Dan har takama hanyar barin hall d’in.
Su ya ishaq da mamansu sai dariya suke musu.
Da Anty yahanasu sukaci karo itama zata fita, a’a Rahma lfy ina zakije haka da sauri?.
Saurin saisaita kanta tayi, Anty wlhy nagaji barci nakeji.
Aidama rigimar kice tasa kikazo, mujeto nima gidan zani nagaji……
Dai-dainan bobo yak’araso yarissina yagaida aunty yaha, Anty yaha ta ce, “ko tare zaku tafine?.
d’an Sosa kansa yayi yana murmushi.
Dariya aunty yaha tayi tareda fad’in kaga koma kayi zamanka saimuwuce tare tunda nima gidan zani.
To shikenan Anty saida safe.
Har waje yarakasu, har suka tafi Rahma bata yarda sun had’a ido da bobo ba.
Dariya yayi bayan tafiyarsu ya ce, ” humm my Nusfulhayat kishinki na burgeni da k’ara tsundumani a lodin k’aunarki.
Juyowa yayi zai koma, daidai zai Shiga sukayi karo dawata k’yak’yk’yawar budurwa, suduka kowa jadabaya yayi, sorry my guy, yarinyar tafad’a cikeda yanga.
d’aure fuskarsa yayi baice komaiba yara6a ta gefenta zai wuce.
Da sauri tasha gabansa tana fad’in pls jimana.
Tsayawa yayi yana kallonta saidai fuskarsa babu alamar yasan miye dariya, tamkar bashine yagama dariyaba yanzu.
Tagyara tsayuwarta tana wani far da idanu, ni sunana Anisa Ahmad Sa’eed, so atak’aice ana cemin neesa, k’anwace ga angon y Hafeez.
Wlhy tunjiya awajen launch kaketa birgeni bansamu damar maka magana bane sai yanzu, pls ina fata zaka kar6i tayina?, tayi maganar tana tsura masa ido da langa6ar da kanta gefe.
Yamutse fuska yayi yana mata wani kallon rainin wayo, baice da ita k’alaba yara6a tagefenta yawuce.
Binsa tayi da kallo tamkar zata FASA kuka dan bak’inciki, Dama saida Anty laura ta ce, “kartazo Dan daga ganinsa zaiyi Girman kai, kuma taga kamar yanada mata, amma tak’i azatonta kodan k’yawun da ALLAH yay mata dolene bobo ya saurareta saigashi ya bud’a mata k’asa a ido.
Jiki asanyaye takoma cikin hall d’in, amamakinta saita hangoshi yana dariya shidasu ammar, shagala tayi sosai tana kallonsa da addu’ar ALLAH ya mallaka mata bobo amatsayin miji.
” Araina na ce, “humm.”
STORY CONTINUES BELOW

Dahakadai taro yatashi, ango Hafeez yad’auki amaryarsa Ameera suka tafi, shima ya kamal yad’akko safna sukayo gida, su bobo da sauran jama’a kowa yay gida.
Sanda suka iso tuni Rahma tayi barci a falon Abba dama a can takwana jiya.
Washe gari aka kai safna d’akinta itama bayan anyi walima.
Masha ALLAH gidan yayi k’yau, su ummi sunmata gata irina iyayen kwarai, kowa ya yaba kam saidai mak’iyi.
Tom daganan taro yatashi kowa Yakama gabansa, Raham ma bobo yazo ya d’auketa sukai gida abinsu.
_____________________
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, Rahma anata rainon ciki, suma su khairiyya da khursiyya an gamu, Dan jiya agidansu Rahma da Nawal suka wuni, sunjajje musu yawo, aiko bak’aramin farinciki sukayi da hakanba, suntarbi su Rahma tamkar su goyasu, ansha hira zuwa dare bobo yaje yad’akkosu.
Su safna amare anata shan amarci, sosai ya Kamal yake k’ok’ari wajen mantar da Ita bobo, rayuwa sukeyi mai dad’i, itama kuma tanata k’ok’arin faranta MASA dukda har yanzu idan son bobon yamotsa takansha kukanta a6oye, amma tana iya bakin k’ok’arinta danganin tacireshi azuciyarta.
Ameerama dai ba’a barsu abayaba sunata shan soyaya itada hafeez d’inta.
Sai masu gayya da aiki bobo da Rahmarsa soyayace tsantsa ake zubawa agidan cikeda kulawa da tarairayar juna, yanzukam sai abinda yay gaba wajen kulawar da bobo yake bata musammam da cikinta yashiga wata Tara na haihuwa, datace wash, zaice miya faru?, wani lokacin har tsokanarshi takeyi saita langa6e tana zuba shagwa6a, dataga yarud’e saita saka MASA dariya, yakace haba yarinya zan ramane baridai ki haihu.
Awannan tsakaninne yasamu nasarar shari’arsu da Alhaji abdurrazak, yanzu haka an Yanke musu hukuncin d’aurin rai da rai agidan yari, Dan ba wannane karo nafarko dasuka saka yaransu yin kisaba.
Mutane sai yabama k’ok’arin bobo sukeyi, yak’ara girma a idon al’uma, kowa k’ara k’aunarsa yakeyi Dason tarayya dashi, hakama iyayensa da ‘yan uwansa kowa alfahari yakeyi dashi.
Gama sharia’ar babu dad’ewa yak’arasa ginin gidansu idiris harsunma koma amma ambarma ammi hibba kamar yanda ta buk’ata, babansu idris yayi murna yasakama bobo albarka harbabu adadi.
Su Rahma sunsha bikin Basma Wanda dak’yar bobo yabarta take zuwa saboda cikinta yatsufa sosai ga cikin yayi girma masha ALLAH.
Bayan kammala bikin da kwana biyu Ammi tazo hargida zata tafi da Rahma takoma gidansu Dan ta CE, “bata amince tabarsu sukad’ai agidaba ga haibuwa yau ko gobe.
Rahma dai tayi murna da haka amma bobo tamkar zaiyi kuka, daga k’arshema shima shirya kayansa yayi Yakoma gidan Appan, Ammi dai ta CE, ” shiyya sani Rahma cedai bazata bayarba sainanda wata hud’u.
Idanu bobo yazaro yace ammi wata hud’ufa kikace?.
Eh Ashe kajini?, sainan da wata hud’u lokacin baby yayi kwari, d’iyata ta huta sosai.
Shiru yayi kamar zaiyi kuka.
ammi sai kunshe dariya take, Rahma dake zaune Nawal na matsa mata k’afafunta dasukeyin fishi, itakam kasa daurewa tayi ta tuntsure da dariya.
Hararta bobo yayi tareda yin kwafa yatashi yafita.
Saida yafita sannan ammi tayi dariya itama.
Da Appa yadawo tabashi labari shima dariya yayta k’yalk’yawltawa, ya ce, “wai da gsk shima yahad’o kaya yadawo nan gidan?.
Wlhy kuwa Appan ishaq karkaji wasa, yana nan tsohon d’akinsa kwance yanzu haka yana barci.
Appa ya ce, ” kai mukarram kayan shirirta, shi koyaushe zai gane yagirma ne?. To ALLAH yak’ara had’a kawunansu shida ita dakuma sauran ‘yan uwansa da matansu gabad’aya.
Amindai Ammi tafad’a cikeda farin ciki.
______________________
Rahma tana kwance itada Nawal akan gado, Ammi na zaune bisa sallaya tana addu’oi bayan ta idar da nafila datakanyi akowane tsakar dare, yanzu itama ad’akin take kwana saboda gudun kar Rahma tafarka da ciwo cikin dare.
Agogo Ammi takalla 2:54am, filo tajawo daga saman gadon ta ajiye akan sallayar tazame ta kwanta, barcine yakwasheta, akuma daidai lokacin Rahma tafarka dawani matsanancin ciwo, amma saboda jarumta irin tata takasa magana saidai cije le6e da hawaye daketa sharara.
Zuwa wani lokaci takasa daurewa, ahankali ta daddafa tasakko daga gadon tadawo k’asa ta duk’usa tareda d’ora kanta bisa gadon tana murk’ususu.
Abin tamkar wasa sai gaba gaba yakeyi, can taji bayanta da k’ugunta cikinta ko ina yarik’e, wani wahalallen kuka tasaki tana fad’in nashiga uku ummi zan mutu, wayyo bayana cikina k’irjina zasu cire……..
Afirgice Ammi tafarka, ganin Rahma durkushe tana kuka Takuma rud’ewa, Rahma yadai?.
Ammi cikina, bayana, ko ina ciwo zan mutu Ammi kuyafemin.
Bazaki mutuba Rahma, runk’a addu’a, akid’ime ammi take maganar, ga waya a hannunta tana kiran bobo…..
Shima azaune yake, tun d’azun yafarka saboda mafarkin Rahma dayayi tana kuka dakiran sunansa, tund’azu yakeson ya lek’a d’akin yaganta amma yanajin kunyar had’uwa da ammi, ganin damuwa zata masa yawa yatashi yad’auro alwala yazo yay nafilfili yanzu haka yana zaunene yana karatun alkur’ani, ganin kiran ammi yasashi d’aga wayar da hanzari…….
Zumbur yamik’e danjin ammi tana fad’in yafita da mota gasu nan fitowa, Alkur’anin ya ajiye yafigi key yay waje da sauri, mota yaje yagyara fakin sannan yadawo ciki, afalo yagamu da Appa d’auke da Nawal zai kaima ‘yan aiki ita, wuceshi yayi yatarbo Ammi dake rik’eda Rahma tanata kuka.
Aii baijira cewar Ammiba yad’auki Rahma gaba d’aya yay waje da ita, ammi kuma d’akinta takoma ta d’akko kayan daza’a buk’ata, cikin mintuna k’alilan Ammi da Appa suka fito, bayan Ammi tashiga Kusada Rahma, shikuma Appa yazauna Kusada bobo, a 360 bobo yaja motar sai asibitin ya sulaiman.
Koda suka isa cikin gaggawa aka kar6esu, dandanan doctor Fa’iza takar6i haihuwar Dan ya sulaiman akwai kunyar surukuta tsakaninsu.
Har zuwa 4:46 Rahma bata haihuba, anatadai shan tata6urza, aii bobo dayaga abin bana k’are bane sai kawai yadanna kai cikin d’akin, duk maganar da ya sulaiman yake masa bai saurareshiba.
Inda take kwance yak’arasa, tana ganinsa tafara mik’a masa hannu tana kuka dakiran sunansa, Nurulk’albi ka gafartamin zan mutu, wayyo ALLAH dadyn Nawal nima mutuwa zanyi kamar Anty Ni’ima.
Dukda arikice yake shima haka yake shafa kanta yana fad’in a’a My cute bazaki mutuba, insha ALLAHU lafiya zaki haihu……..kafin tabashi amsa wani sabon ciwon yazo.
K’ank’ameshi tayi sosai tana wani wahalallalen nishi.
Aiko bobo yaji rik’onnan na Rahma, sai jije le6e yake shima kamar mai Nak’udar.
Cikin ikon ALLAH saiga jariri yafad’o yana tsayyara kuka, cikeda murna doctor Fa’iza ta ida ciroshi tana fad’in Alhmdllh, saikuma sabuwar nak’uda, mik’ama Nurse tayi jaririn takuma kar6ar sabon baby daya kunno kai.
Ai Rahma na sauke wannan kaya saitayi lakaf ajikin bobo.
Ahargitse yake kiran my Nusfulhayat!, my cute!, momyn Nawal!!.
Katseshi doctor Fa’iza tayi da fad’in sir babu abinda yasameta tana hutun wucin gadine.
Doctor Fa’iza bafata numfashi.
A’a yalla6ai tanayi kalli k’irjinta kagani, kallonkuwa yayi saiyaga tana sauke numfashi ahankali.
Dukda bai samu nutsuwa dukaba yaji dad’i, ko sauraren ‘ya’yan baiyiba dukda yana cikin matsanancin farincikin zuwansu duniya, amma ta mamansu yakeyi yanzu, bayan shigewar mintuna Rahma tad’aga idanunta dasuka k’ank’ance tana kallon bobo, murmushi tamasa.
Cikin farinciki yarungumeta yana fad’in Alhmdllhi Alah kulli’halin, sai yanzu d’unbin farincikinsa yafito fili.
Tuni labari yakaigasu Ammi, anhaifi twins namiji da mace.
Dan dad’i Appa har rungume ammi yayi, ya sulaiman sai kauda kai yayi yana dariya.
Cikin ‘yan mintuna aka gyara baby’s da mamansu, bobo yad’akkosu yafito dasu wajensu ammi, bakinsa yak’i rufuwa yaukam.
Had rige-rigen d’aukarsu ake tsakanin ya sulaiman dasu Ammi.
‘Yan gata sun iso duniya, yara masha ALLAHU basuda maraba da yayarsu Nawal, dakuma mahaifinsu Abdulmaleek bobo.
To saimuce ALLAH yaraya ‘yan dugwuy-dugwuy iyalan baba.
Sai karfe 8pm sukabar asibitin, aka rankaya zuwa gidan Appa, zuwa sannan labari yabaje dangi, sanda suka Isa gidan Appa cike yake dasu anty rasheeda, har and’ora ruwan wanka.
Innar su hibba tayima Rahma cikakken wanka, tanata zille-zille da zame-zame har aka kammala, yarama anmusu, annad’esu cikin fararen kayan sanyi masu laushi sai barcinsu sukeyi.
Rahma tafito daga bayi Dan tuni inna tafito tabarta tana k’imtsa kanta.
Zama tayi tashafa mai tashirya tsaf cikin atanfa sabuwa dal, itakad’aice ad’akin mutane duk suna falon k’asa har jariran.
Abincin da Anty ummy ta ajiye mata tazauna taci, shayine mai kauri da farfesun ‘yan ciki, saikuma soyayen dankali, citai kad’an sanan tahaye gadon ta kwanta sai barci, dama barcin bai ishetaba…………..💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 52
Falon cike yake da dangi, bobo yashigo da sallama hannunsa d’auke da leda babba, gaisawa suka shigayi da mutanan falon anata masa barka, cikeda farinciki yake amsawa, mutane dayawa dabasa ganin dariyarsa yau har mamaki sukeyi yanda yaketa yak’e hakwara.
Ammi dake fitowa daga kichin ta ce, “yauwa mukarram kadawo?.
Eh ammi nadawo.
A’a yanaganka da ‘Yar leda?, sauran Kayanfa?.
Mik’a mata ledar yayi yana fad’in wlhy naje zan sayo saina tadda ya ishaq awajen yana siya, shiyyasa najuya nasiyo wad’annan kuma.
Ayyo aiban saniba, to ina yayan naku yanzu?.
Acan nabaroshi, amma nasan yana hanyar zuwa shima.
To shikenan ALLAH yakawoshi lfy.
Ameen, Ammi ina Rahma d’in?.
Tana d’aki kwance tana barci, kasan jiya bawani barcin kirki tasamuba, kaima aii yakamata kaje kad’an kwanta kona awa biyu kasamu kayi.
Shafa kansa yayi yana murmushi, wlhy Ammi ni namafa daina jin barcin.
Dariya ammi tayi, lallaikam murnar zuwan kishiya da miji yasa idonka bushewa kenan?.
Dariya sosai bobo yakeyi, ya ce, ” ammi aii k’yautar ALLAH daban take, wlhy ko’a mafarki banta6a zaton Rahma zata iya haihuwar yara biyuba yanda nake mata kallon yarinya karama.
Itama ammi dariyar tayi, mukarram aii ikon ALLAH kenan, Ubangiji mai hikimane, amma gsky koni bankawo Rahma tana d’auke da cikin yara biyu bane, ALLAH dai yarayasu akan turbar addinin islama.
Amin ammi, bara nalek’a Rahman kota tashi?.
To, ammafa Indai barci take karka tada ita kaji nagaya maka.
Karki damu ammi, bobo yay maganar yana haurawa sama.+
Cikin barci Rahma taji ana shafa kanta, ahankali tamotsa, jin k’amshin turarensa yasakata bud’e idanunta ta sauke akansa.
Murmushi yamata murya a sanyaye ya ce, “my Nusfulhayat kin tashi?.
Kanta tad’an jin jina tana murmushi, yunk’urawa tayi zata tashi yataimaka mata, ta zauna sosai amma tana jingine ajikinsa, Nurulk’albi yaushe kashigo?.
Sumbatar kumatunta yayi idanunsa cikin nata ya ce, ” tun d’azun ina zaune ina gadinki aii.
Tofa saikace wata sarauniya?.
Aikinfi sarauniya awajena Rahma, Ubangiji ALLAH yayimiki albarka, tabbas ke Alherice arayuwata, shigowarki Rayuwata kin yalwata alkairi mafi daraja agareni, inason yara sosai Rahma, inaso yara fiye dazaton mai tunani, saigashi tashi d’aya ALLAH ya albarkacemu da samun biyu, Rahma yanzu nine da yara har uku?, kai ALLAH na gode maka godiya Mara adadin kididdiga, lale dake yasanyin idaniyata.
Dad’i da farinciki duksun yalwatu afuskar Rahma, takuma narkewa ajikinsa, ngd my Nurulk’albi, ina rok’on ALLAH ya tsawaita rayuwarmu domin miyita bauta masa da kuma kasancewa tare har abada.
Ameen my cuty na.
Amma Dan ALLAH ina neman wata alfarma agareka.
Gyara zamasa yayi Yakuma jawota sosai ajikinsa ya rungumeta, kitambayi Duk abida kikeso agareni insha ALLAH zanmiki shi inhar bai sa6ama ALLAH ba.
Murmushi tamasa ta ce, “inason asakama macen sunan marigayiya aunty Ni’ima Dan ALLAH kamin wanan alfarmar, idan kamin haka zanyi farinciki sosai.
Tsura mata idanu yayi nawani d’an lokaci, har jikinta yafara sanyi ko bazai aminceba, amma saitaji ya rungumeta tsam yana bata Sumba takowane 6angare ajikinta.
Ammi dake tsaye tun d’azun tana kallonsu ta kauda kai tana murmushi, dama tabiyo bayansane danta tada Rahma tabama yaran nono, Dan sunfara kukan yunwa.
Jin maganar dasukeyi yasa tatsaya bata shigoba Dan batason katsesu saga farincikin dasuka tsinci kayinsu.
Saida bobo yagama bata hot kisses sanan yad’agota yana kallonta, ALLAH yamiki albarka shine abinda yaketa maimaitawa, cikin raunin murya ta ce, ” my Zuma kayarda kenan?.
Jinjina mata kai kawai ya iyayi yana murmushi, ahankali ya ce, “Rahma nazama naki, kinrigada kin dabaibaiye komai daya shafi rayuwata, aduk duniya daga iyayena saike acikin jerin Abu mafi Girman muhimmanci a tafiyar rayuwata, sai kuma ‘yan uwana wad’anda suka zama jigogi kuma matakan tsaro agareni, ‘ya’yana sanyin idaniyata, ALLAH ngd maka daka yalwatani da wad’annan ni’imomi naka badan Nafi sauran bayiba kabank, badan nakasance mafificiba acikinsu, badan wayonaba, badan iyawataba, badan k’arfinaba ka yalwatani ka azurtani ka ni’imtani, ka suturtani, ka ingantani, ka d’aga darajata acikin bayinka, ya ALLAH yanda kamin wanan k’yauta aduniya ka Albarkaceni dasamun mafiyinta alahira……. Hawaye suka zuraro akumatunsa, Rahma tasa hannunta tana share masa.
Yacigaba da fad’in ya ALLAH karka jarabceni da kasancewa acikin masu butulci agareka, ya ALLAH karka jarabceni dagacikin masu sa6onka, ya ALLAH karka jarabceni daga cikin marasa godiya agareka, ya Ubangijin Al’arshi ma’abocin Rahma da gafara, ka gafartamin dukkan kurakuraina nida zuri’ata data musulmai baki d’aya, ya ubangijina kak’ara imani da tsoronka azuciyata, ya ubangijina katsare harshena daga sa6amaka komai ribar hakan agareni, ya Ubangijina ka tsare idanuna daga kallon haramun komai farincikin da hakan zai sakani, ya Ubangijina katsare k’afafuna daga zuwa inda haramun yake komai d’aukakar da hakan zata jamin, ya Ubangijina katsare gangarjikina, zancena, numfashina, furucina, daga afkawa tarkon shaid’an la’ananne nida dukkan zuri’ata data musulmai baki d’aya, ALLAH ka k’arama annabi daraja da fadila da Wasila, ALLAH yasa munacikin al’ummar da zaiyi alfahari damu muda zuri’armu baki d’aya, ALLAH yasa munacikin wad’anda zasu amsa kiran cetonsa awata rana mai cikeda rud’ani da hargitsi, ya ALLAH idan katashi d’aukarranmu kad’auka munacikin imani da tsoronka bacikin shagaltuwa da duniya da abinda ke cikintaba.
Ameeen Rahma tafad’a tana k’ank’amesa hawaye sharkaf da fuskarta saboda addu’ar mijin NATA ta ratsa dukkan sassan jikinta da 6argon jikinta.
Ammi ta share guntun hawayenta itama sannan tamusu sallama.
Da Sauri Rahma ta tashi daga ajikinsa tamatsa gefe kanta asunkuye saboda kunya.
Shima k’asa yayi da kai yana Susa k’eya.
Sunbama ammi dariya amma saita gimtse.
Fuskarta d’auke da murmushi ta ce, “Rahma kintashi?.
Kan Rahma akasa ta ce, ” eh ammi natashi tund’azu.
Kodai mukarramne yatadaki?, dannasan halinsa sarai.
Girgiza kai tayi cikeda kunya tana murmushi.
Ammi tayi dariya, to tunda kintashi bara nakawosu ki basu abincinsu tun asuba yara basuci komaiba sai ruwan zam zam da Zuma aketa basu……
fita ammi tayi, bobo ya kalli Rahma baki bud’e, my cute wai kinanufin basuci komaiba yarannan harfa 12 tawuce?.
Shagwa6e fuska tayi Nurulk’albi wlhy ina gama wanka na kwanta saboda barci danakeji sosai………
Kafin ya ce, “wani Abu Ammi tashigo d’auke da yaran ahannunta.
Bobo ya kar6i macen, saida yasumbaci goshinta sanan yamik’ama Rahma ita.
Cikeda kunyar Ammi ta kar6a Dan ita saima yanzu zata gansu tunda sukazo duniya, jitayi k’aunar yaranta tana ratsa dukkan sassan jikinta, Aranta Ta CE, ” ALLAH sarki haka iyayenmu sukeji akanmu, ALLAH ka k’aramana k’aunar iyayenmu dakuma taimaka musu iya iyawa Dan bazamu iya biyansuba…..
Ganin tayi shiru ammi ta ce, “Rahma bata tasha mana.
Ajiyar zuciya Rahma tasauke, idanunta Akan k’yak’yk’yawar jaririyar daketa bud’e baki alamar tana Neman abinci, ga idanu kyar masha ALLAH, (Yaran yanzu haka ake haihuwarsu da wayensu, saidai fatan ALLAH yatsare manasu damu kanmmu).
Tana saka mata abaki yarinyar tafara sha, da sauri tacire tana fad’in wash da zafi.
Daga bobo har Ammi dariya suka saka mata, Ammi ta ce, “haka zaki daure kibasu, daga baya zaki daina jin zafin.
Tasowa bobo yayi yadawo Kusada Rahma, ita kunyama yabata ga Ammi a zaune kan kujerar madubi, bobo ya ce, ” kinga kidaure mana, kokin manta wahalar jiya tafi wannan.
K’asa-k’asa yay maganar yanda ammi bazatajiba, ita tunima tad’auke kanta daga Kansu tana kallon baby boy d’inne Wanda take kallo amatsayin tarihi ya maimaita kansa, Dan tamkar bobo yana jariri haka take kallon yaron.
Rahma takuma sakama yarinyar, tana kamawa tacire tana yarfe hannu dafad’in shiiiii wlhy da zafifa.
Tabama bobo dariya amma awannan karon saiya dake, dakansa yasakama yarinyar akaro na uku, Rahma tarik’e hannunsa ga zafi ga kunyar Ammi data lilli6eta, kallon Ammi tayi sannan takalli bobo tamkar zatayi kuka, ammifa na kallonka Dan ALLAH kasaki zan bata da kaina.
Ammi shima ya kalla yana murmushi, to aii bamu Ammin takema kalloba, hankalinta nakan angonta sabo fil.
Dole Rahma tahak’ura har babyn tad’ansha amma sai matse baki takeyi da yarfe hannu harta sha da yawa.
Ammi takatsesu da fad’in to abarta haka shima maigida yasamu yasha.
Sosai kunya ta lilli6e Rahma, Ashe Ammi na kallonsu amma ta sharesu.
Ammi tamik’ama bobo Namijin, itakuma takar6i macen, akafad’a tasakata tana shafa bayanta danson tayi gyatsa.
Shikuma bobo yad’ora ma Rahma beby boy acinyarta, yanzuma haka yasaka masa shima abaki da kansa, Rahma nakukan zafi-zafi, ana cikin haka saisukaji sallama, ammi dake tsaye ta amsa, Safna tashigo cikin ‘Yar fara’a, rissinawa tayi yagaida ammi, ammi ta amsa mata cikeda fara’a da tambayarta mai gidan?.
Yana nan lfy Ammi, Ashe ansamu k’aruwa?, ALLAH ya raya.
Ameen Safna, yaukam kunyi ‘ya’ya gasunan masha ALLAH, ammi tafad’a tana mik’a mata baby gal dake hannunta.
K’ar6a Safna tayi cikeda sha’awar babyn.
Rahma ta ce, “Anty Safna sannu da zuwa, tana maganar tanad’an yarfa hannunta.
Dariya Safna tayi, ke lfyarki kuwa?..
Zafi wlhy, Dan ALLAH kabarshi haka Nurulk’albi wlhy yak’oshi.
Bobo yad’ago yanama Safna sannu dazuwa, ya ce, ” wannan k’anwar taki akwai ragwantaka.
Zama Safna tayi abakin gadon tana dariya, Ammi tafice abinta dama.
Bobo yacirema babyn nono abaki yana dungure kan Rahma, raguwa kawai.
Eh naji babu komai koma miye kufad’a, anjima kuma saiku nemi abinci awajen jaruma.
Dariya bobo yayi ya ce, “koda k’arfin tuwo aii sai anbamu ‘yammata.
Rahma ta ce, ” shikenan k’arfinku yabaku to.
Kizuba ido mana zaki gani aii.
Safna dai dariya take musu, Dan yanzu Alhmdllh son bobo yaragu sosai azuciyarta saboda k’ok’arin da ya Kamal yakeyi wajen mantar da ita hakan.
Tal’ek’a fuskar baby boy dake hannun bobo, masha ALLAH yaran duk kai suka biyo kaida Nawal.
Cikeda farinciki ya ce, ” ko auntynmu?.
Wlhy kuwa, Safna tafad’a tana dariya, ta kalli Rahma dake gefe tana jiyyar kanta, auta next time saiki haifa mana mai kama dake.
Idanu Rahma tazaro Anty safna ban fito daga magagin wannanba amma kike zancen wata, yanzu kam saidai ku.
Kallonta bobo yayi yana dariya, my Nusfulhayat aikema nanda next year nakeason ki k’ara haifo wasu biyun.
Narke fuska tayi tamkar zatayi kuka, Dan ALLAH my Zuma kudainamin fatannan wlhy akwai wahala.
Dariya safna da bobo suka saka mata……….adaidai nan kuma khursiyya da khairiyya suka shigo dagudunsu, rungume Rahma sukayi suna murna, suduka suka haye gadon khairiyya tazauna Kusada bobo tana amsar baby, itama khursiyya na hannun Safna ta amsa, sai dad’i sukeji sunata k’ank’ame yaran.
Khairiyya ta ce, “yaya, su ya Hamza suna kirankafa.
Mik’ewa yayi yana fad’in lah sunzo gidanne?.
Eh yanzu suka shigo suma.
Fita yayi yabarsu sunata hirarsu da dariya.
Safna sai kallon yaran takeyi cikeda sha’awa, dayanzu itace ta haifesu, dayanzu ita bobo yakema wanan tattalin, ya ALLAH kaciremin son bawan ALLAHnnan gaba d’aya, nima namaida hankalina ga mijina kodan tattalina dayakeyi.
Duk a zuciyarta takeyin maganar.
STORY CONTINUES BELOW

To nimadai na amsata da Ameen, Dan yanzu tausayi take bani.
_bayan kwana uku_
Aka kawo kayan barka, bobo yataka rawar gani, kayan sai sambarka a keyi, Appa da Ammi ma ba’a barsu abayaba suma da nasu, Rahma sai fad’in kayannan sunyi yawa takeyi, jitake k’aunar mijinta da ‘yan uwansa nak’ara ratsata.
Haka akaci gaba da kar6ar bak’i yan barka har zuwa ranar suna.
Yara sunci sunansu, Namijin sunan Appa yaci, wato Aliyu haidar, macen kuma Ni’imatullah.
Za’a ringa cemusu Shareeff da Shareefa, to saimuce ALLAH yaraya Aliyu & Ni’imatullah.
‘Yan uwan Aunty Ni’ima sunji dad’in wanan karamci daga Rahma, Appa ma sai albarka yake saka mata, hakama sauran dangi.
Suna yak’ayatar alhmdllh abin sai Wanda yagani, naga tarin masu karatu awanan suna masha ALLAH.
kwalliya kam Ranar Rahma tashata, kamar kasaceta ka gudu, awajen yin hotunama bobo sai yabawa yakeyi, shima yaci wankan shadda sai k’yalli da k’yawun haiba kefita agareshi.
K’yaututtuka kam sun samu bila adadin, gadon Ammi damk’am yake da kaya iri-iri.
Zuwa dare taro yatashi mutane kowa yakama gabansa, sai su Ammi kawai, da Rahma bobo Nawal hibba, Appa da ‘yan aiki, saikuma shareeff da shareefa.
Bayan Rahma tafito wanka tashirya kanta cikin kayan barci.
Tana zaune ak’asa shayi takesha, yayinda Ammi takeyima Shareeff da shareefa shirin barci, Nawal da heeba suna zaune kan gado sai k’irga kayan jariran da aka samu sukeyi da turame.
Da sallama bobo yashigo d’akin shima sanye yake da kayan barci, zama yayi Kusada ammi yana fad’in Ammi shirin barci kukeyine?.
Shirin barci mukeyi mukarram, suma sun gaji yakamata su kwanta su huta ko.
Gsky ne ammi.
Mik’a masa Shareeff tayi tana cigaba da shirya shareefa, umm my sweet dady, yau kunsha hayaniya ko?…….. Nawal ta ce, “papa!.
Na’am Mamana miya faru?.
Kaga kayasu baby’s d’inmu dayawa.
Nagani kuwa, kunyi goshi, nawa kuka k’irga?.
Papa bamu gamaba’ai cewar hibba.
To kudage mugani nawa muka samu.
To papa.
Dubansa yamaida ga Rahma, ohni ‘yammata dankina shan shayi saikiyita shama mutane k’amshi?.
Murmushi Rahma tayi ta ce, ” aibanaso kace zakashane.
Ummyim aina ganoki, Ammi ALLAH nima yunwace takoroni nakasa kwanciyafa.
Dariya Ammi da Rahma sukayi, ammi ta ce, “Ashe da gskyar Rahma datak’i yimaka tayi.
Humm ammi kibarta aii zan rama.
Mik’a masa shareefa tayi, to rik’eta nasamo maka abinci.
Kar6arta yayi yana sumbatar kumatunta, my beauty na.
Rahma takallesu cikeda sha’awa, yanda yaketa wasa da yaransa abin birgewa.
Babu dad’ewa Ammi takawo masa abinci, ta d’auki yaran shikuma yasakko yanacin abincin, heeba da Nawal suka sakko suna murna dafad’a musu adadin kayan.
Sudai su Rahma sai dariya suke musu.
Ammi ta kwantar da yaran ad’an gadonsu sanan tafice wajen Appa.
Rahma takalli bobo daya ture filet d’in abinci, wai harka k’oshine?.
Alhmdllh my Nusfulhayat nak’oshi.
A dama bayunwar dakake fad’a kakejiba.
Haka kikacedai, amma kinsan ALLAH, tun safe damukayi break nidasu ya sulaiman bankuma samun nutsuwar zaman cin abinciba har awajen waleema, Ammar nata fama dani nazauna naci amma nakasa, lokacinma banajin yunwar saboda d’awainiyar mutane, kai my cute mutane sunmana halacci wlhy, yanda kikasan mun Tara taron bikifa, sandasu Ya ishaq sukace za’ayi walema kamar yanda akeyi duk sanda aka haihu canayi kawai abarsa tunda lokacin haihuwar Nawal anyi, Dan gani nake mutane bazasuzoba.
Amma suka dage sai sunyi, wai yanzuma yadace suyi tunda wanan ne karo nafarko da’aka haifa mana twins a family.
Saiga mutane tamkar anbusa k’aho.
Dariya Rahma tayi ta ce, “Zumana aikai mutumin muranene kowa zaiso halartar taronka, gakuma gayyar su ya Hamza.
Hakane my Nusfulhayat, kumafa Appa shima yayi tasa Walemar da safe.
Kai haba?.
Wlhy kuwa my cute.
Tab lallai mungodema ALLAH sosai, ALLAH yasakama mutane da alkairi dansuyi rawar gani, jibifa kayan da’aka Tara mana.
Nagani wlhy, ALLAH yabar zuminci dai.
Amin.
My Nusfulhayat yaushe kuma zamu koma gidanmu?, tunda angama suna.
Wata ‘Yar dariya Rahma tayi tana hayewa gado, ta ce, ” sai bayan arba’in.
Shima dariyar yayi danbai d’auki maganar tata serious ba, tashiyayi yana fad’in haba yarinya kima canja shawara dai, gaban gadonsu shareeff yaje yamusu kiss sanan yayma Nawal dasuke kwance agado idata hibba, Rahma dai duk tana kallonsa.
Gabanta ya iso ya durk’usa ak’asa yana kallonta, itama kallonsa takeyi, batayi auneba taji bakinsa cikin nata.
Kissing nata yake sosai danba k’adamar kewarta yayiba.
To itama daga gareta hakane, sosai ta taimakeshi suke faranta ran juna, jin tahowar Ammi d’akin yasaka Rahma saurin k’wace kanta, suduka duk maida numfashi sukeyi a wahale.
Ammi tashigo da sallama, kasa bobo yay da kansa Dan bayaso suhad’a ido da ammi, ya tabbata saita gane halin dayake ciki.
Ra6awa yayi tagefenta yafice kansa asunkuye, itadai Ammi ta kalleshi ta kalli Rahma dake kwance akan gado tayi luf ita adole barci takeyi.
Saida yakai gab dazai fita sanan ya ce, “Ammi saida safe.
ALLAH yakaimu Ammi tafad’a tana binsa da kallo harya ida ficewa.
Kallonta ta maida ga Rahma, ta ce, ” kidai dage kibiye masa keda kikeda la6u6un jarirai, wannan dalilin yana d’aya daga cikin abinda yasa na maidoki gabana, dannasan halin mukarram ko kad’an bashida hak’uri akan abinda yakeso.
Rahma dai tayi luff kamar ruwa yacinyeta, sai fad’in take a zuciyarta My Zuma kabani kunya yau wayyo ALLAH na.
Ammi ta shige bayi tana cigaba dayima Rahma fad’a…………….😂💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 53
Alhmdllh abubuwa nata tafiya yanda yakamata, su Rahma harsunyi arba’in, yara sunyi 6ul-6ul dasu abin sha’awa da birgewa kamar subani, bak’aramin gyara Ammi takrma Rahma ba awanan zaman wanka, aiko ko ita kanta tasan taji gyara Dan fatarta tayi wani k’yau da laushi, kuma zammm takejin kanta.
Bobo nata fushi Dan yaso sukoma gidansu tuni, ammi ta ce, “saidai yakoma shikad’ai su Rahma dai ba yanzuba, wanan dalilinne yasashi fita harkar Rahma gaba d’aya, shi adole fushi yakeyi da’ita, daga gaisuwa babu abinda yake had’asu, saikuma yad’auki yaransa kokuma yazauna ad’akin yana musu wasa, ada Rahma tashiga damuwa da sauyin nasa, amma da Ammi ta zaunar da ita tana lallashinta da nuna mata itama tafita harkarsa da Kansa zai dawo gareta, daganan sai Rahma tasami nutsuwa, wani lokacinma har dariya yake bata idan yana shan k’amshi, musamman idan takamashi yana satar yimata kallonnan nasa k’asa-k’asa, dasun had’a ido saiya gimtse fuska, kokuma yakwashi yaran yabar mata d’akin.
Ita kanta ammi bobo yana bata dariya, data kasa daurewa har Appa tabama labari, shima yaci dariya ya ce, ” babana na kaina.+
Bayan kammala arba’in suka fara zaga dangi.
Gidansu tafara zuwa, bak’aramin farinciki Abba da ummi sukayiba daganin jikokinsu, anan tawuni sai dare oga yazo yad’aukesu abisa matsawar Appa, Dan ya ce, “dolene yakaita ko ina takeso.
Haka suke tafiya amotar babu mai tanka wani.
Washe gari kuma gidan ya ishaq sukaje suka yini saidare yaje yad’akkosu, daganan kullum akwai gidan dazasuje su yini, haka sukaita zaga dangi, sunje gidan ya sulaiman, gidan ya Hamza, gidan ya Shaheed, gidan ya muneer, gidan Ammar, gidan aunty yahanasu, gidansu marigayiya Ni’ima, gidan khairiya da khursiyya, gidan Ameera, gidan Basma, kai babu Inda basu zagaba, gidan Safna ne k’arshen zuwa, tabar gidan Safna k’arshene dantasamu suje weekend yakaita tunda safe tawuni sosai..
Aiko ayau Asabar suka Isa gidan, cikin farinciki Safna ta tarbesu, har mamaki Rahma tayi, sai nan-nan takeyi dasu, tamkar tagoyasu Rahma, cikin mutunci suka gaisa da bobo, Wanda shima canjawar safnar kebashi mamaki.
Itakam zuwa yanzun zuciyarta fes, kallon bobo takeyi amatsayin d’an uwa kuma mijin k’anwarta, bayan haihuwar Rahma tak’ara dukfa da addu’a, takuma k’ara Neman gafarar iyayenta, suka kuma k’ara jaddada mata sun yafe mata suna kuma k’ara tayata da addu’a ALLAH ya daidaita lamuranta.
Wad’annan abubuwanne suka taru suka k’ara taka rawar gani wajen inganta farincikita dakuma jin son bobo yafita fit azuciyarta, saidai tana ganin girmansa damasa soyayya irinta ‘yan uwantaka tamkar su ya munner, soyayya mai tsafta kuma ingantacciya suke gudanarwa itada mijinta, wani bala’in sonsa takeji ayanzu haka, shima soyayya yake nuna mata irinta ‘yangatan mata kamilallu, dankoba komai yana alfahari da safna, cif tazo MASA a cikakkiyar budurwa shiyya 6areta aleda, dama baita6a kallonta dawata illaba saita tsiwa.
Su Kansu Rahma da bobo yau sunsha kallo, danba kunya safna da ya Kamal suke narka soyayya agabansu.
Rahma taji dad’i sosai dataga ‘Yar uwarta tak’ara kwantar da hankalinta, aiko yau sosai takejanta ajikinta, su shareefa kam ai tamkar ta lashesu Dan so da k’auna, wuni sukayi ahannunta, tad’auki wanan ta ajiye ta d’auki wannan, haka suka wuni cikin farinciki da k’ara k’aunar juna.
Su bobo na fita sallah Safna taja hannun Rahma suka shige k’uryar d’aki, magunguna tad’akko tabama Rahma, tanata mata bayanin yanda zatayi amfani dasu, Rahma tarufe fuska yana fad’in kai aunty Safna ALLAH kina bani kunya.
Dukan wasa Safna tayima Rahma, kai auta gulmarki tayi yawa wlhy, idan kina tareda ya Abdulmaleek aii idonki rufewa yakeyi amma saikina gabanmu kice wata kunyar gulma, dama sabodake na had’asu, jiyannan nakecema my heart yakaini gidan Ammi nakuma gano yarana, ya ce, “nabari sai ranar Sunday, to ashema kuma hanya, ‘Yar uwa k’ara gyara kanki ya Abdulmaleek yaji zammm danya k’ara rik’e manake d’amm, safna tak’are maganar da d’agama Rahma gira, dariya suka saka harda tafawa tamkar wasu k’awaye, Rahma ta ce, ” ALLAH yabarminke auntyna, suka kuma kashewa da dariya.
STORY CONTINUES BELOW

😂wayyo masu karatu dad’i tamkar yakasheni, nasan kumafa yau hakan take agareku musamman masoyan Safna, luv you so much safnarmu😘👍🏻.
Sosai tahad’a ‘Yar k’anwar tata Dan acewarta batada kamarta aduk fad’in duniya, sukad’aine mata agidansu sukashe su rufe abinsu, hira sukayi sosai ad’akin harsu bobo suka dawo basu saniba.
Abubuwa sosai safna tahad’ama Rahma harda sabulai na gyaran fata, Rahma sai dad’i takeji da k’ara k’aunar ‘Yar uwarta, yanzukam sunzama tamkar yanda take buri tun farko, saidai fatan ALLAH yak’ara had’a Kansu waje d’aya.
Sai bayan isha’i suka fito zasu tafi, shareef da shareefa suna hannun Safna da ya Kamal, Rahma tashiga Kusada bobo ta zauna sanan Safna taziro mata shareef da ledar kayanta, my sweet lil gasu karfa ki tsaya Sanya Dan da zafi-zafi ake dukan k’arfe, abinda Baki ganeba to naji kira.
To my aunty godiya nake sosai ALLAH yabar zuminci saikinzo d’in.
Bobo dake kallonsu sun burgeshi sosai, cikin zolaya ya ce, “auntynmu mi muka samune haka?.
Dariya Safna tayi ta ce, ” k’anina abin sirrine aii.
Lalala yanzunan auntyna dake za’a had’eminkai?, Kamal zoka ganemin nan.
Dariya ya Kamal yayi idonsa akan safna, tad’aga MASA gira, shikuma yasakar mata lallausan murmushi, bobo ya ce, “Kamal sai magana akeyi agabana adunk’ule bana gane komaifa.
Cikin dariya ya Kamal ya ce, ” kaikuma ga rashin hak’uri, aisaika kwantar da kai kaji Inda bakin zaren yake, kokuwa my Angel?.
A to my heart gaya MASA dai.
Rahma dai dariya take musu, bobo ya ce, “shikenan idan tayi wari aii maji, cikin dariya Rahma ta ce, ” aibama zatayiba.
Dariya suka kwashe da ita su duka, safna takuma gwargwad’ama Rahma magana akunne suka kuma tafawa suna dariya.
Bobo ya ce, “Kamal bara kaga nagudu da my Nusfulhayat d’ina kafin matarka tak’ara zugemin ita.
Nanma dariya suka kumayi sosai, daganan sukayi sallama bobo yana mota suka tafi, zuciyar bobo k’al da farincikin Safna tasaki jikinta yanzun komai ya wuce, gashi sun had’e Kansu itada ‘Yar uwarta, dama fatansa kenan akullum.
A can kuwa su bobo na tafiya safna ta narke ajikin ya Kamal wai saidai ya d’auketa bazata iya tafiyaba, dariya yayi ya ce, ” my Angel kemafa shagwa6a66iyace tafad’a a ji, d’aukar kayansa yayi tamkar jaririya suka shige gidan suna dariya, asaman doguwar kujera ya sauketa suna cigaba da dariyarsu, cikinta yashafa yana fad’in Nima yaushe zaki bani nawa babyn my Noor?.
Ido d’aya safna takshe masa ta ce, “ayanzu hakama ina zaton kasamu, Dan kwanakin preod d’ina sun wuce kobaka lissafi?.
Cikin farinci ya k’ank’ameta yana fad’in kumafa hakane my Angel, soyayya mai tsafta kuma nagartacciya yashiga Nuna mata, safna ma tana bashi gudummawa saida suka soyu sanan suka tashi adarennan sukaje pharmacy, tsinken gwajin ciki suka siyo, aiko suna gwadawa sukaga tanada ciki, wayyo zokaga murna da farinciki awannan gidan, tun adaren suka fara bazama dangi.
Safna Rahma tafara kira wadda harsunje gidan tuni, tagama shirin barci kenan kiran safna yashigo, ta guntsa mata abin farincikin daya samesu bayan tafiyarsu, tsalle Rahma takeyi harta bama safna dariya, safna ta CE, ” kai lil ya bobo nashan fama, har yanzu ana nan ana gwada halin k’uruciya.
Kai aunty nid’in?, Rahma tafad’a cikefa shagwa6a.
Eh mana.
Bubbuga k’afafu Rahma tafarayi ak’asa ita adole ba haka bane, bobo daya shigo yanzu yakwantar dasu Shareef yatsaya yana kallonta, suna had’a ido yakauda kai yana ta6e baki, shi adole ba kallonta yakeyiba, Ra6awa yayi tagefenta ya fice, Rahma tabishi da kallo yana turo baki gaba.
Bayan fitarsa Rahma ta ce, “wlhy Anty d’azun namanta muyi wata magana, tamkar zatayi kuka take maganar.
To inajinki auta miya farune?.
Zayyane mata abinda ke faruwa tsakaninta da bobo tayi.
Dariya safna tayi ta ce, ” kema ki shareshi, kedai kita amfani da magungunan nan, na tabbata duk randa kuka koma gidanku yakashe amarci insha ALLAHU saiya dawo dakansa yana Neman shiri da lalla6arki, kuma zakice Nina fad’a miki.
To shikenan aunty na ngd ALLAH yabar zuminci ya saukeki lfy kema, ki Haifa mana yaranmu ‘yan uku.
Kai auta rufamin asiri ‘yan ukun lfy.
Dariya sukayi gaba d’aya, Rahma ta ce, “I luv you so much my sweet auntyna.
Luv you more my lil sisina, ALLAH yak’ara kauda shed’an atsakaninmu, Yakuma k’ara had’akanmu waje d’aya muzama taintsiya mad’aurinki d’aya, asuba tagari my heart yana jirana nabashi d’umin jikina, gwauruwa arungumi fillo lfy… d’if ta Yanke wayar, tabar Rahma da dariya.
Kai Anty safna ALLAH ya shiryaki, Nima aii nakusa tashi daga Layin gwagwaren, ALLAH INA k’ara godiya Daka daidaita mana komai cikin sauk’i, ALLAH ka k’ara ninka salatinka ga annabi Muhammad tsira da aminka su k’ara tabbata agareshi.
Sumbatar yaranta tayi ta tamusu addu’a dukda papansu yamusu, gado tahaye tamusu addu’a itada Nawal tareda rungume Nawal dake barci, itama ta sumbaci kumatunta, har yanzu zuciyarta yana k’ara k’aunarta tanajinta tamkar su Shareefa, bak’aramin tausayi yarinyar Take bataba saboda rashin uwa, amma tayi alkawarin zamema Nawal uwa har abada, bata fatan ranar dazatazo ta banbanta soyayyarta dasu shareeff.
*_BAYAN KWANA UKU_*
bayan kwana uku da zuwa gidan aunty Safna Ammi tashirya Rahma tsaf da shirin maidata d’akin mijinta, nasiha sosai Ammi da Appa sukai musu tareda fatan alkairi agaresu, sosai Rahma tasha kuka Dan ko babu komai tayi sabo da zama gidan sosai ayanzu, amma babu yanda ta iya.
Zuwa dare bobo yakwashesu sai gidan, ko a mota kuka Rahma taitayi, bobo yana kallonta amma baice da ita k’alaba.
Koda suka Isa gidan saitaga komai tsaf, angyara gidan sosai, wanka kawai tayima yaran tamusu shirin barci, Nawal na kwance bisa gado tanatama su shareef wasa, sosai yarinyar take k’aunar yaran, komai tasamu ta ce, “na Shareef da Shareefa ne.
Rahma dake tsaye agaban madubi tana shirin barci ta ce, ” babyna bazakiyi barciba?, gobefa idan ALLAH ya kaimu akwai school.
Momy nidai bazanjeba zan zauna gidan taredasu Shareff.
A’a babyna to idan bakison zuwa makaranta suma idan sunyi girma aii bazasuje ba ko, ki kwanta kiyi barci abinki da antasoku bakina tareda suba.
To momy bara suyi barci sannan nayi.
Dariya kawai Rahma tayi batace komaiba.
Bobo dake tsaye abakin k’ofa yanajin hirarsu ya ida shigowa cikin d’akin, ta madubi Suka had’a ido da Rahma, batace komaiba haka shima bai tankaba yahaye gadon wajen yaransa.
Lalla6a kayansa yaytayi harsukai barci suduka ukun sanan yagyarama Nawal kwanciya, yamata addu’oin barci ya shafa mata, suma su Shareefa ya kwashesu zuwa d’akinsa, itadai Rahma da kallo kawai tabishi, ad’an gadonsu yasakasu yamusu addu’oi suma, Rahma na zaune abakin gado tana addu’oin barci danta k’udiri aniyar bazata bishi d’akinsaba.
Batayi auneba taji anyi sama da ita, ciccila k’afafunta takeyi tana fad’in wayyo dadyn Nawal Dan ALLAH kabarni ALLAH barci nakeji.
Bai sauraretaba yadireta agadonsa, ganin zata addabi kunnensa da surutu ya had’e bakinsu waje guda, zallar soyayya mai tsafta yashiga aika mata, hummm lallai bobo uayi missing d’in Nusfulhayat d’insa, itamafa mutuniyar taku muk’us kakeji, tuni tafara maida murtani……..🤰🏻😜.
Hummmm yaukam ansha fama Dan sabon ango da amarya suka koma, ranar kam Rahma ta murzu ta shaida bobo yayi kewarta sosai Dan bai d’aga mata k’afaba har gabannin asuba ana Abu d’aya.
Washe garima dak’yar ta lala6ashi tatashi tahad’a musu breakfast.
Wankama tare sukayi, nanma saida suka kashe juna da soyaya sanan akayi wankan suka firo, ta shiryashi tsaf cikin shirin office, sanan ta tata Nawal itama tamata wankan shikuma yataimaka mata da shiryata, tayima su Shareefa suma duk shine yashiryasu.
Gaba d’aya suka d’unguma zuwa dinning shi yana d’aukeda shareef nawal tana d’aukeda shareefa, Rahma kuma tashiryama kowa breakfast agabansa sanan ta kar6i sharifa ahannun Nawal danta samu nutsuwar cin abinci.
Bayan gamawarsu yad’auki Nawal suka tafi, aka bar Rahma itadasu Shareefa kawai…..
Haka rayuwa taciga da tafiya musu wataran Zuma wataran mad’aci, yaransu sunata k’ara samun girma da kulawar iyayensu.
Soyayya kam Rahma da bobo ba’a cewa komai sai sambarka.
To ALLAH yacida ‘yan bayan haka irinsu o e😂…….bandai fad’i sunaba bare ace nace😜🤸🏻💖ABDUL-MALEEK!!💖
(BOBO)
Bilyn Abdull ce
Pg 54
*_BAYAN WASU SHEKARU…._*
Abubuwa sun faru da dama, ciki harda haihuwar Safna, tasamu d’iyarta mace wadda taci suna khadeeja, bayan ita takuma haihuwar Abubakar sadiq, yanzu haka tana goyon mace Asma’u.
Soyayaya itada ya Kamal d’inta ko sai abinda yay gaba, komai yawuce tamkarma bai faruba saidai tashin zance.
Su khairiyya da khursiyyama duk sun haihu, yanzu suma yaransu uku uku.
Anty Ameera ma yaranta biyu.
Hakama Basma tanada biyu.
Anyi Auren zeenat da baseera suma harda tsarabar ciki.
Itama ihsan k’anwar ya kamar ansha bikinta da musaddiq k’anin marigayiyya aunty Ni’ima, Wanda sun had’une ranar bikinsu Safna suka shirya Kansu.
*_bara nalek’a muku gidan bobo naga wace waina ake toyawa kuma._*🤓.
Tundaga harabar gidan naked’anjin hayaniyar yara, nak’arasa falon saina tadda Rahma kwance saman doguwar kujera idonta akan TV, gefe kuma Nawal ce zaune itada Shareeff da Shareefa tana koya musu homework, saikuma yara biyu dake fad’a duk maza wad’anda ak’alla zasukai shekara hud’u da kuma 5½, d’an shekara hud’unne Kebin d’an shekara Biyar suna zagaye falo yana fad’in nisaika bani abuna, nisaika bani abuna.
Nawal datazama ‘yammata Dan ayanzu tana ss2 a Secondary ta ce, “Farhan wai bazaka bashiba, ALLAH natashi saikayi kuka, kabashi kazo kayi homewook d’inka.
Wanda aka kira Farhan ya ce, ” yo Anty Nawal nawanefa shi kulum kulum saiyayta yima mutane rigimar banza sai anbashi Abu, yaje d’akin papa yad’akko NASA mana…..
Kafin Nawal tace wani Abu bobo yafito daga d’akinsa sanye cikin jallabiya fara da alama ma alwala yayo……ya ce, “a’a Farhan mike faruwane haka?, momy kina zaune kina kallonsu sunata faman fad’a idan wani yazame yafad’i yaji ciwo fa?.
Yatsina fuska Rahma tayi ta tashi zaune tana fad’in wlhy bazan iyaba Nurulk’albi, ni takaina nakeyi, idan nabiyema Farhan da Shureim gidanan wlhy sainamusu mugun duka, Dan ALLAH gobe idan ALLAH yakaimu ka kwashesu ka kaima Ammi weekend kokuma anty Safna nikam nahuta koda na kwana biyune.
Dariya tabashi da tausayi, tunda tasamu cikinnan yake bata wahala, hargashi yashiga wata na hud’u amma bata hutaba, yay saurin rik’o Shureim dake bin Farhan suna zagayashi, d’aukarsa yayi yana fad’in haba Abbana miyasa kakeda rigima?, yanzu kai ina naka jirgin yake?.
Papa nawafa baya tashi sama yanzun……. Papa wlhy k’arya yakeyi, d’akinkafa yakai ya 6oye jiya dadaddare ko Anty Nawal?.
Shareefa ce mai maganar tana Harar Shureim daketa turo baki gaba.
Kallonsa bobo yayi ya ce, ” Abbana wai da gsk aunty Shareefa takeyi?.
Girgiza kai Shureim yayi alamar a’a ba gsky bane.
Farhan ya ce, “ALLAH papa da gsk Anty Shareefa takeyi d’akinka yakai ya ajiye.
Dire Shureim bobo yayi, Yakama hannun Shureim da Farhan kunga kuje kuyi alwala mutafi masallaci lokacin sallar la’asar yayi, Ya Shareeff atashi idan mundawo acigaba da homework d’in tunda babu islamiyya yau.
Mik’ewa Shareeff yayi, araina na ce, ” like father like son, gaba d’aya yaron kamarsa d’aya da bobo sosai har d’an Karen muskilancin na bobone, idan baigadamaba sai agama wanan shaftar bazai sakama kowa bakiba, haka yake bashida hayaniya ko kad’an.
Rahma tabishi dakallo tana girgiza kai, miskili kafi mahaukaci ban haushi, wai yaronnan duk abinnan da akeyi bamu isheshi kalloba?.
Dariya bobo yayi ya ce, “k’yawun d’a…..
Rahma ta ce, ” yagaji ubansa.
A to kingani, bashida lokacin yahaniyarku ne, baby kuma kutashi kuyi sallah.
To papa Nawal da Shareefa suka fad’a suna mik’ewa.
Nawal ta ce, “momy haryanzu bakijin yunwar?.
Wlhy babyna inajin yunwar amma bana sha’awar cin komai.
Langa6e kai Nawal tayi kamar zatayi kuka momy kidaina zama da yunwa dukfa kin rame.
Daga bobo har Rahma dariya sukayi, bobo ya ce, ” to momy ba’aso ki ramefa kullum anfison ganinki Orobo.
Nanma dariya sukayi, Nawal ta ce, “momy bara nayi Sallah Nazo nadafa miki wani abun, to baby jekiyi.
Nawal nabarin wajen bobo yadasama Rahma mayun idanun nan nasa cikeda so da k’auna, my cute Kodai wajen ya Sulaiman zamu komane?, yakuma duba minke?.
Murmushin k’arfin hali Rahma tamasa, a’a Zumana bama saimun komaba, yanzu babu Inda kemin ciwo saidai kasala da d’acin baki.
To shikenan my Nusfulhayat, amma inaga wannan karon uku zaki Haifa mana shiyyasa cikinnan ke baki wahala da yawa, dama gashi kin huta dayawa ga Shureim da shekara hud’u aduniya.
Wayyo zumana dainamin fatannan, idanma ALLAH yasa na haifi mace ai hakama sun ishemu maza uku mata uku Alhmdllh.
Ido yad’an zaro tab my cute saura shidda kenan 12 nakesofa, kuma duk daga gareki………
Kafin tabashi amsa su Shareeff suka fito kowa yayi alwala, bobo ya kalli Shareeff babana koma ka canja wanana wandon, koma ka saka dogon wando dai kokuma kasaka jallabiya.
Papa jallabiyoyina duk sunyi dattine.
Rahma ta ce, ” ba saida nace jiya kad’akko Ashiru ya wankeba tunda zayyi wankin papanku.
Momy ALLAH nibanjiba.
Yaza’ayi kajini tunda kamaida kanka dud’um dunkum, mutum sai muskilanci…….
Bobo yakatsesu da fad’in to yanzudai kasaka dogon wando gayican za’a kabbara sallah.
Juyawa yayi mintuna kad’an yadawo suka tafi masallaci, Rahma ma tashi tayi tanufi d’aki Dan gabatar da sallah.
Hajara mai aiki tazo tagyara falon kafin su dawo, su Farhan sukuma 6atawa.+
STORY CONTINUES BELOW

_____________________
Rahma kwance ajikin bobo, kasancewar yau weekend yana gida, ahankali yake shafa kanta tanad’an lumshe ido dansan yin barci amma k’iriniyarsu Farhan ta hanata.
Tajuya kwanciyarta tana d’anyin tsaki, bobo ya ce, “yayadai my Nusfulhayat?.
Yunk’urawa tayi ta tashi zaune tana turo Baki gaba, Dan ALLAH Nurulk’albi ka iza k’eyar yarancan islamiyya daga nan idan sun dawo suwuce gidan Ammi wlhy surutunsu na damuna, Nawal da Shareeff kawai nake buk’ata.
Dariyace taso kuccema bobo saboda yanda Rahma ke maganar kamar zata FASA kuka, daurewa yayi ya gimtse, ya ce, “kai my cute bak’aramin masifaffiya cikinnan yamaidakiba, da bakiyima yaranki fad’a ko Abu sukaimiki saidai kimusu nasiha da sakamusu albarka, amma yanzu dukkin canja. Miyasa?.
K’ara shagwa6e fuska tayi ALLAH banason hayaniya yanzu Nurulk’albi.
Amma indai Shareefa da Farhan da Shureim suna gidanan sai sun saka mutum ciwonkai.
To Shareeff fa?.
Wanana shi bashida damuwa shida Nawal.
‘Yar dariya bobo yayi ya ce, ” amma jiya kika gama cemasa dund’un dunkum ko?, Hajiya iya takawo muku Sara ALLAH dai yajik’anta.
Ameen, amma Kasan miskilancin Shareeff fa harso yake ya zarce naka, yaronnan bayason yima kowa magana agidanan, idanfa kaji yana doguwar hira to dakaine.
Lumshe idanunsa yayi yana murmushi , ya ce, “d’an gado kenan my cute saiya zarta….
Buga k’ofarne yasa bobo yin shiru batareda yak’arasaba.
Shurein ne yake kuka yana buga k’ofa da kiran papa! Momy!.
Tashi bobo yayi yaje yabud’e MASA k’ofa, Abbana miya farune?, Yayi maganar yana d’aukar Shureim dake sanye da kayan islamiyya.
Papa ya Shareeff ne idokeni a zuciya.
Kaikai azuciyafa Abbana?.
Eh, shureim yafad’a yana d’aga kai.
Fita bobo yayi dashi, Rahma dai dariya take musu, ta kwanta tana fad’in ALLAH yashiryaka Shureim a INA ake ganin zuciya dahar za’a doketa?.
A can kuma bobo ya iske Shareeff ad’akinsu yana had’a littatafansa na islamiyya acikin jakka.
yana ganin papansu ya yarissina yagaidashi cikeda girmamawa, Shareefa ma dake gyaran gadon su Shareeff d’in tazo tagaida papansu, suduka sanye suke da Uniform d’in islamiyya lemon green.
Bobo yazauna akujerar d’akin yana fad’in ina Farhan da Anty?.
Papa suna d’akinmu, wai Farhan ne baiga hularsaba.
To ina aka ajiye?.
Papa shiyya ajiye da kansa, waikuma ya manta.
ALLAH yasa aganta to.
Yaya Shareeff mi auta yamaka ka dukesa azuciya.
Dariya Shareefa takeyi, Shareeff kam murmushi yayi, araina na ce, “masha ALLAH yaronnan bashida maraba da bobo tako ina.
Papa littafina na Fiqhu ya yaga min, shiyyasa na rankwashi kansa, Dan yakiyaye a gaba, amma ni bandaki zuciyarsaba.
Shureim Ashe kaji laifi kayima Yaya shiyya ya hukuntaka.
Nawal da Farhan suka shigo da sallama, suma gaida dadynsu sukayi, ya amsa yana tambayar anga hular?.
Eh papa anganta, Ashe cikin kayan Shareefa yasaka.
Mik’ewa bobo yayi ya ce, ” to kuyi sauri Ku k’arasa lokaci na k’ure muku.
Afalo ya iske Rahma tafito, a’a momy bakiyi barcinba?.
Hummm inani ina barci?, aii inaga saidai idan basawan gidan sun tafi islamiyya kuma.
Zama Kusada ita yayi yana dariya.
Mintuna kad’an duk yaran suka fito.
Duk suka gaida Rahma, murmushi tamusu tana amsawa, tareda tambayarsu sun tashi lfy?.
Kowa ya ce, ”lfy lau momy.
Baby anhad’a wanki waje guda ko?, basai ashiru yazo Yata jiraba.
Lah momy harma yafara wankewa, yaga akwai wuta shine yace bara yayi kafin su d’auke.
Amma yayi dabara, anhad’a da kayan nan na Farhan daya had’a musu daud’a agidan Abba ko?.
Eh duk nahad’a dasu.
To adawo lfy.
Suduka kowa yazo yasumbaci kumatun iyayensu, suma suka sus sumbacesu sanan aka fita ana fad’in sai andawo.
Ajiyar zuciya Rahma tayi ta ce, “kai gidan haryayi dad’i.
Dariya bobo yayi ya ce, “aizasu dawone.
Amma kafin sudawo nahuta.
Ya ce, ” idan nabarkiba, yayi maganarne yana d’aga mata gira.
Murmushi tayi ta ce, “Zumana kafa girma.
Hhhh girma kuma?.
Eh mana, kallifa yaranka biyar, koyanzu aka aurar da Nawal zama zatayi ga Shareefa ma tana neman kamota atsawo, yarinyarnan ni bammasan inda takwaso jikinnanba?, sainagama kamar tafi Shareeff k’iba.
Zamewa bobo yayi yakwanta yad’ora kansa saman cinyarta, jikin ya Hamza takwaso aii kobaki kulaba?.
Kumafa hakane wlhy Nurulk’albi, da jikin jiddahn ya Sulaiman da jikin Shareefa, amma duk tsayonka suka kwaso, jiba Nawal da Zainab d’in ya ishaq harfa rankwafawa yarannan sukayi.
Wlhy hakane my cute, jiya danaje gidan ya ishaq naga Zainab cewa nayi kawai suna kammala Secondary amusu aure itada Nawal, ni idan tanima za’abi harda Sumayya yaran duk sun zangame fa.
To aii girman ne babu wahala, mustapha da Sageer gasunan subasuyi tsawoba bakuma su gajarceba har Shareeff naneman finsu tsawo, amma Ahmad da Kamal d’in ya hamzama duk kune, ALLAH dai yaraya manasu baki d’aya.
Ameen my cute, ALLAH ya saukeku lfy kuma, yafad’a yana shafa cikinta.
Murmushi tayi ta ce, ” Ameen my zumana, kasan kuwa jiya muna waya da khairiyya takecewa tanason fita takasa saboda laulayi nace mata ainida ita babu maraba, da k’yar na iya zuwa sunan Basma, shine take dariya wai Anty Safna da khursiyya sunfimu dauriya, ranar bikin taufiq da heeba sai aiki sukeyi tamkar bamasu tsohon cikiba.
Dariya yayi ya ce, “dafa gsky khairiyya wlhy, wanan cikin duk yamaidake raguwa, amma cikin Shureim wasuma saida yafito sukasan kinada cikin aii.
Tab kaidai danba ajikinka yakebane, amma cikin Shureim ma nasha zaz6in rana, wata sa’infa kamar jira kana fita aiki su Nawal suka tafi makaranta sai zazza6i yarufeni, ga son jikin tsiya har k’agara nake kadawo najini kwance ajikinka.
Hhhhh mage kenan.
Wlhy asanan namafi mage, cikin Farhan nedai kam bansha wahalaba sosai da cikin daya zube bayan haihuwar su Shareeff, shi saidama nayi 6arin nasan inadashi kamanta.
Inafa zan manta my cute, kai ranar narud’e dayawa, dayanzu yaranmu shida ga na 7.
Dariya Rahma tayi ta ce, haka ALLAH ya tsara, wad’annanma daya bamu mungode masa, wasunacan suna nema basu samuba.
Hakane kuma my cute d’ina, ALLAH dai yaymiki albarka kinji.
Ameen Zumana tafad’a tana sumbatar kumatunsa.
Lumshe idanu yayi yana murmushi, ahankali yabud’e akanta, my cute tashi mutafi d’aki.
d’aki kuma Nurulk’albi?, mizami yo?.
Lada zamu samo mana, yad’aga mata gira, dariya sukayi gaba d’aya…
STORY CONTINUES BELOW

_____________________
Duk suna zaune afalo, Shareeff da Shareefa na game dasuka had’a da TV, Rahma tana gyarama Farhan kumba Dan gobe idan ALLAH yakaimu Monday, Nawal kam tana note, Shureim najikin bobo yana barci bayan angama masa gyaran k’umba.
Jisukayi ana kwankwasa k’ofa, suduka suka kalli k’ofa, bobo ya ce, “Shareeff tashi kaga waye.
To papa, Shareeff yamik’e tareda ajiye handle d’insa yanufi k’ofar yabud’e.
Kallon mutumin yake d’an kimanin shekara 40+, yarissina ya gaidashi.
Mutumin ya amsa cikeda murmushi yana k’arema Shareeff kallo, tabbas da ace d’an Adam yana komawa baya zuwa k’uruciya dayace bobone agabansa.
Ganin kallon da mutumin yake masa yasashi fad’in uncle kana Neman waye?.
Murmushi yayi ya ce, ” yaro ina Neman mahaifinkane, Dan daga ganinka kai jinin *_Abdulmaleek bobo_* ne, babu inda ka banbanta dashi, yaro miye sunanka?.
Sunana Shareeff.
Masha ALLAHU d’ana Shareeff, kacema mahaifinka Haneeff Sunusi dala ne yake sallama dashi.
Jinjina kai Shareeff yayi yajuya domin isar da sak’o ga papansa.
Shareeff yanaga ka dad’e?, wayene?.
Papa ya ce, “sunansa Haneeff Sunusi dal…….
Aii kafin Shareeff yak’arasa Rahma da bobo duksun zaro ido waje, bobo yace cemasa yashigo.
Yakalli su Nawal yace kusaka hijjabanku, ak’idarsace wanan indai wani bak’o namiji zai shigo koda Ammar ne, ko ‘ya’yan su ya ishaq to dolene su Shareefa su saka hijjabai, dama tuni Rahma tasaka nata..
Da sallama Haneeff yashigo, bobo ya amsa cikeda fara’a da mamakin canjawar haneeff, yazama babban mutum harda gemu,haneeff ya zauna cikeda fara’a yanabin yaran da kallo, masha ALLAH Abdulmaleek ka Tara zuri’a kam.
Dariya bobo yayi yabashi hannu suka gaisa, Rahma ma ta gaidashi, su Nawal kowa ya gaidashi, sannan suka tashi suka koma d’akinsu.
Dandanan Shareefa da Nawal suka cika masa gaba da kayan motsa baki.
Bobo ya ce, ” haneeff dama zaka iya tunawa dani?.
Dariya Haneeff yayi ya ce, “Abdulmaleek kai basoyine dabaza’a manta dakaiba, kakafa tarihin dabazai gogu a duniyaba, tundaga lokacin Dana tsinci kaina gidan yari lokacin da abubuwa suka fara nisa, addini da ake koya mana ya hudani saina tabbata kai masoyine na hak’ik’a domun kataimaki rayuwata, k’ila dabaka saka ankamaniba har naje wannan gida da yanzu rayuwatama ta lalace, bazan mori komaiba, amma yanzu kalleni nazama babban malami acikin gidan, jiya jiya nafito amma nace tabbas sainazo na ganka, naje office d’inka sai akacemin aii tuni katashi, sunmin kwatancen office d’inka na yanzu, dakuma super market d’inka, to naje super market d’innne aka bani address d’in wannan sabon gidan naka, shine nazo.
ALLAH sarki haneeff kar ka damu kanka aii komai yawuce, ya bayan rabuwa?.
Sai godiyar ALLAH kam, ya iyalinka?.
Dariya bobo yayi ya ce, ” gasunan lfy lau, haneeff yabama Rahma hak’uri daneman gafararta akan kamasu da mahaifinsa yasa akayi alokacin, yad’ora dafad’in nazo Neman yafiyarkune dakuma heebba Dan ancemin tana wajenka.
Hakane tana tareda mahaifanane, yanzu hakama tayi aure wata d’aya daya wuce.
Da sauri Haneeff ya ce, “wata aure?.
Yaron yayanane Taufiq d’an wajen Yaya ishaq.
Haneeff yashare hawayensa yana fad’in ALLAH sarki heebba ALLAH ba azzalumin sarki bane, ALLAH yabaku zaman lfy, Abdulmaleek Dan ALLAH ina rok’on alfarma kahad’ani damijinta danna rok’i gafararsu.
Wlhy babu damuwa haneeff zan had’aku, yaunema kawai baizo gidananba amma kullum saiyazo ya gaishemu, inagama yau wani uzurinne yahanashi.
ALLAH sarki.
Daganan hira sukayi, bobo yakirasu Nawal duk yanunama haneeff su.
Kaga wanan Nawal ce, itadai nasan bazaka mantataba, itace wadda aka kama tareda momynsu, saikuma ‘yan biyu Aliyu da Ni’imatullah, muna kiransu Shareeff da Shareefa, sai kuma Muhammad Farhan, sai Bilal munakiransa Shureim gashinan yana barci.
Masha ALLAH ubangiji ALLAH ya rayamanasu akan turbar addini, yatsaresu daga sharrin shaid’am da gur6atattun abokai.
Ameen ya ALLAH, tokai kuma sai yaushe zakayi auren?…
Hummmm Abdul kenan, wacece zata yarda ta auri tsoho.
Kai habadai aii zama bazai yuwu hakaba, yakamata kayi aure, yakuwa Alhaji?.
Dad yana nan ciwo yahanashi komai, sai yawon asibiti, yanzu hakama daga wajensa nake, harma yace yananeman afuwarka abisa abinda yafaru abaya Dan ALLAH ka yafe masa.
Ayya wlhy komai ya wuce, aibansamma yadawo k’asarba, kwanaki munje muda Appa da ya ishaq da ya Suleiman da ya hamza dubashi, sanan yana tsaka da ciwon nasanma bai ganeniba.
Yanzu bara mushirya saikamana jagora mudubashi Dan ALLAH.
To shikenan.
STORY CONTINUES BELOW

Cikin ‘yan mintuna suka shirya, gaba d’aya har yaran sukaje asibitin.
Bak’aramin tashin hankali su bobo suka shigaba da ganin Alhaji sunusi dala, dukya yamushe tamkar bashiba.
Yana kuka yana rok’on gafarar bobo dasu Rahma.
Bobo yace ya yafemasa.
Alkairi yamasa sosai sanan suka fito kiwazuciya cikeda k’arajin tsoron ALLAH.
Daganan gidan Taufiq sukaje haneeff yanemi gafarar heebba da Taufiq, duksun yafe masa.
Daga nan gidan Ammi suka biya suka gaishesu.
Amma da Appa tsofaffin kirki sunji dad’in zuwan ‘yan jikokinsu, nan suka zauna akasha hira da dariya har yamma sanan sukaje gidansu Rahma nanma suka gaida ummi da Abba, suma sunji dad’in ganin ‘yan jikokinsu, agidan Safna aka yada zango itama danata family abin sha’awa, sai dare suka dawo gida bayan bobo yabiya dasu shopping kowa takwaso abinda yakeso, suka dawo gida cikeda farinciki da k’aunarjuna.
Kowa d’akinsa yanufa danyin shirin barci.
Rahma na tsaye gaban madubi tana d’aure igiyar rigar barcinta bobo yashigo, tabaya ya rungumeta, yana dad’in amincin ALLAH ya tabbata agareki uwar ‘ya’yana.
Juyowa tayi suna fuskantar juna, itama cikin kashe murya ta ce, “kaima amincin ALLAH ya tabbata agareka uban ‘yayana.
Murmushi mai kashe zuciya bobo Yamata, yakuma manneta sosai ajikinsa, ya ce, ” I luv you so much my Nusfulhayat.
Luv you more my Nurulk’albi na zumana.
d’aukarta yayi cak yahaye gado da’ita suka shiga nunama juna zallar k’auna maicikeda farinci na har abada, tamkar sunyi shekara basa tare…….
🚶🏻♀sum sum nafito domin nabarsu haka suma su shak’ata nima nahuta, masu karatu kuma Ku huta.
Tammat bi hamdullh.
_Alhamdullahi Ala kulli halin, ina mik’a d’unbin godiyata ga ALLAH mad’aukakin sarki daya bani iko da damar kammala wanan littafi mai suna Abdulmaleek bobo, babu abinda zance da masoya saidai godiya domin kun nunamin d’unbin k’auna, ALLAH yabar zuminci ngd ngd ngd har babu adadi._
*_inad’anso naja hankalin masu karatu a wanan ga6ar._*
_bai k’yautu amatsayinka na Wanda ka6ata lokacinka harnawani tsawon lokaci kana bibiyar littafiba ace baka ammfani dakomaiba acikinsa, saidai kawai ka karanta kayi farinciki, ko tausayi, ko bak’in ciki ka kakka6esu anan katashi batareda kad’auki wani muhimmin abuba ka gwada wa rayuwarka Dan ganin amfaninsa, aganina indai hakane gara karka 6atama kanka lokaci waje karantawa kuwa._
*_ni yanzu ba alfahariba bana karanta littafi na 6ata lokaci na a banza, kumani babu ruwana ko yau kika fara rubutu to zan karanta littafinki, idan soyayace alittafin yak’unsa tofa saina d’auki wasu abubuwan nagwada ga mijina naga shin sunada amfani?, idankuwa wani abune sa6anin hakan tofa shima saina gwada, idan Wanda yakamata ka gudane to zan gujeshi kuwa, idan Wanda zai amfanenine bana sanya wajen yinsa, to kuma haka nake fata Ku kasance._*
_littafin Abdulmaleek yakunshi abubuwa dayawa, soyayya, muhimmancin biyayya ga iyaye, muhimmancin sanin hak’in ‘ya’ya mata dakuma kwato musu hak’insu, musamman akan fad’e da ayanzu babu abinda ake cin mutuncinmu dashi kamar fad’e, awani fannin muma Matan munada laifi saboda shigar banza damukeyi dasunan wayewa, wani kuma lokacin ana cutar damune musaman ga k’anan yara wad’anda bazasu iya kare kansuba, kuma bayan an keta musu haddi basuda wani tsayayye dazai tsayama raayuwarsu bare k’wato musu hak’k’insu musamman idan ‘ya’yan masu kud’ine suka aikata ta’asar, sai muhimmancin zuminci, littafin Abdulmaleek yanuna muku muhimmancin zuminci musamman idan kukayi dubi da family d’in Alhaji Aliyu Abdulmaleek hamshak’i abinsu abin birgewa da ban sha’awa, babu mummunar ak’idarnan irinta uwar miji ko uban miji ga surukansu, Rayuwar bobo abar alfaharice gakowane matashin saurayi Dan zaiso yakasance Jan wuya mai gasky da Kare hak’in d’an Adam, bobo bashida tsoro kuma bashida kwad’ayi shiyyasa yazama dodon azzalumai, ayanzukam samun irinsu bobo k’alilanne acikin al’umma, zakaga duk tarin dukiyar mutum hangen k’ari yakeyi takowacce hanya, saikuma k’awaye, idan bakayi gamo da k’awayen kwaraiba tuni za’a zirmaka karuguza tarbiyya da iyayenka suka dad’s suna ginaka akai, Safna taso tafad’a wanan tarkon akan hud’ubar baseera, amma da taimakon zeenat tagane gsky harma baseerar, saikuma hak’uri duk rayuwar dababu hak’uri acikinta saika sameta cikeda damuwa, hak’uri babban jigone dake Jan zaren rayuwar d’an Adam, idan bakada hak’uri ibadar da ALLAH ya hallicceka Dan ita bama zakayiba, saboda rud’anin duniya mai shagaltar da bayi, da Rahma batayi hak’uriba da bata samu boboba, da Safna tayi hak’uri data samu abin Sonta bobo, amma tabijire aganinta iyayenta sun cutar da rayuwata, wanan matsalar tana taka rawa acikin al’umma, idan iyaye suka za6ama ‘yayansu miji sai ace zasuyi musu auren dole, gsky hakan bai daceba mufa ‘ya’ya yakamata mu runga tunawa da d’awainiyar da iyayenmu sukayi damu wadda bamuda abin biyansu duk duniyarnan, wannan biyayyar dazamu ringa musu itace me sakasu acikin farinciki da alfaharin sumafa sun haifa, idan har d’a bazai iya share hawayen iyayensaba alokacin dasuke kwaranya to aii banga amfanin haihuwaba kuwa Dan batayi ranaba, hattara ‘ya’ya mugyara, fushin iyaye akanmmu babban masiface, kungadai halin hau da Safna tashiga Wanda koda wanan kad’ai aka barka kashiga taskun rayuwa._
_wasu sunsha fad’in na matsa rayuwar Safna dayawa, ba haka bane, inaso Ku gane muhimmancin iyaye da gujema fushinsu, Inda Safna tama iyayenta biyayya data samu abinda takeso alokacin dabatayi zatoba._
_Ku kalli rayuwar bobo mana, shifa namijine amma bai bijirema iyayensaba, dukan aurensa biyu za6insune, kuma idan kuka duba duk yaci ribar gamon katar da mata nagari, to albarkar iyaye ta taka rawar gani wajen samun haka agareshi._
_so masoyan Safna ina mai baku hak’uri sosai, muma muna k’aunarta, munsata a wanan fagenne Dan kugane kuskuren abinda tayi kuma Ku gyara, gamasu sha’awa kuma karsu aikata._
*_idan kuma kuka d’auki soyayyar bobo da Rahma kowacce mace zatayi fatan mijinta yanuna mata irin haka, to hattara samari saikuyi koyi danmu mata ‘yanson soyayyane, wlhy ko mace bata sonka idan kanuna mata soyaya saitayi sanyi tamik’a wuya, mukuma mata bafa zuba ido zamuyiba, muma saimuna taimakawa danamu salon sannan za’a had’u agina ingattaciyar soyaya irinta aure._*