ABDULKADIR CHAPTER 11 KARSHE

ABDULKADIR





CHAPTER 11 KARSHE




Da wani irin sanyin gwiwa ta karasa bangaren ta, watakila har yanzun Waheedah batajin dadi, in baka da lafiya daman komai fita ranka yake shisa. Ko kuma taji haushine dan batai mata ya jiki ba, ita kuma sai lokacin tunanin yazo mata. A haka ta karasa bangarenta, ta samu AbdulKadir kan doguwar kujera a zaune. Karasawa tayi ta zauna a gefen shi, yanajin shigowarta, ran shi a bace yake, ga yunwa da yakeji kuma. Baisan me yasa sai yanzun yake jin haushin ta ba, dana kudin shi da ta kashe, da kuma na yau da ko kadan bata neme shi ba ballantana tasan bashida lafiya harya yini a asibiti. 22

Har yanzun yaga alama batasan waye shi ba, ko dan rashin Waheedah a kusa dashine yasa yake ganin komai ma bashida muhimmanci, yanzun da yasan ba zata barshi ba, ya samu natsuwar da zai fuskanci sauran matsalolin shi. Bayason kashe kudin da bashida dalili, komai nashi a kan tsari yake, sosai yakan yi tunanin abinda takeyi da kudi, kuma ba a dan zaman sun nan ya kula da idan ya ajiye kudi a wallet tana kwashewa ba, ko yazo yin kwana biyu, indai zai mata nata kwana dayan saita dibar mishi kudi. Idanuwa ya dauka ya saka mata yaga gudun ruwanta, yanzun ne ta gama kawo mishi wuya. 9

“Mu me zamu ci?” 6

Nuriyya ta bukata muryarta a sanyaye, dan sosai ta saka ranta a abinda Waheedah din ta girka. Sai takejin da wahala ta iya cin taliyar da ta dafa 8

“Ke ba mace bace? Baki dafa naki bane?” 12

AbdulKadir din ya bukata yana tsareta da idanuwa, duk da maganganun shi sun mata zafi, murmushi ta danyi 2

“Na dafa mana taliya”

Baice mata komai ba, ganin hakan yasata mikewa ta samu plate ta zubo musu taliyar, har miyar ta hade. Tare sukaci, AbdulKadir na rasa ranshi da yake a bace ne, ko taliya ce da bai cika so ba, ko kuma girkin ne bashida gabas, dan ko gishiri-gishiri na miyar ma baiji ba, sai wani daci-daci. Turawa kawai yayi, ita kanta Nuriyya da tana da wani zabi sam ba zata ci taliyar nan ba, sa ma ranta cin girkin Waheedah da tayi yasa taliyar kara fitar mata daga rai. Tana kai kwanon kitchen dakin baccinta ta wuce, ta dauki wayar ta. Tallar littafin Hauwa A Usman Jiddarh tagani na Saki Reshe, tana tunanin sarkakkiyar da take ciki na yanda za’ayi jarumin ya kasance gagarumin dan fashi.

Ba’a kai da fara shi ba, hakan yasata jan dan karamin tsaki, daman jiya littafin Fadime na Bingel ta maimaita dan sosai takejin dadin littafin, soyayyar da aka shimfida ciki na tuna mata dalilin da yasa ta auri AbdulKadir tun da farko, amman yanzun ta fara gajiya dan taci karo da abinda bashi take tsammani ba. Ganin babu abinda zata karanta yasa ta dauko system din ta, daman tana lallaba fina-finan da take dasune, tana budewa sai ga AbdulKadir ya shigo dakin, karasawa yayi kan gadon yahau yana saka hannu yaja system din

“Masoyi…” 2

Ta fadi tana kallon shi, bai mata magana ba yasa hannu yana kashe system din dauketa daga kan gadon gabaki daya ya dora kan drawer din da take gefen shi ya juyo yana tsura mata kananun idanuwan shi da suka sata yin shiru

“Ki kashe mana wuta”

Ya fadi, dan makunnin ba’ayi shi a kusa da gado ba, mikewa Nuriyya tayi tana zuwa ta kashe wutar ta dawo ta kwanta itama, sai dai ga mamakinta, juya mata baya AbdulKadir yayi da alamun bacci zaiyi. Wani abu taji yai mata tsaye a makoshi, batason ya sauke mata fadan shi, shisa ta hakura bata dauki system din ba, wayarta taci gaba da dannawa, tana ganin yanda status din kowa ya gauraye da maganar ganin wata

“Anga wata”

Ta fadi, AbdulKadir ya jita, surutunne ba zaiyi da ita ba yau, asalima niyyar azumi ya daura a zuciyar shi, sake gyara kwanciya yayi yana fuskarta, wayar da take hannunta ya fisge yana sakata a key ya ajiye a tsakiyarsu tare da fadin

“Ki kwanta Nuriyya”

Muryarta can kasan makoshi tace

“Banajin bacci wallahi, bakasan baccin da na sha ba yau daka fita” 10

STORY CONTINUES BELOW

Shisa bata neme shi ba, baccin ta yafi jin inda yake muhimmanci. AbdulKadir ya fadi a ran shi, zuciyar shi na kara jagulewa

“Bazan sake magana ba…”

Cewar AbdulKadir din cikin iko da gadarar shi da take bata mata rai. Gyara kwanciya tayi, ranta in yayi dubu a bace yake, batasan iya lokacin data dauka a haka ba har bacci ya dauketa itama. Su dukkan su baccin suke, shi AbdulKadir baccin daya kwana biyu baiyi bane ba, ita kuma Nuriyya baccin da batayi da wuri bane, ko ma da wurin ta kwanta shi yake tashinta sallar asuba, inba haka ba sai dai ta makara, dan in baya gari makara takeyi. Hakan yasa ko kiran sallar farko basuji ba, sunata bacci har karfe shidda saura. 1

Haske AbdulKadir yagani cikin idanuwan shi, kasancewar window din dakin baccin Nuriyya din daga waje yake, duk da wanda yake waje ba zai iya hango su ba, su da suke ciki zasu iya hango shi, haka gilashin window din yake. Amman bai hana hasken da yake nuna alamar gari ya waye shigowa ba. Murza idanuwanshi yayi da hannu yana kara runtsa su, kafin ya bude su cikin tashin hankali yana mikewa zaune babu shiri, hasken da yagani cikin dakin bai saka shi ya yarda ba, saida ya dauki wayar Nuriyya da take gefen shi ya danna, yana ganin shidda saura minti goma.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

AbdulKadir ya furta yana kai hannu ya jijjiga Nuriyya

“Ki tashi mun makara” 4

Ya fadi yana hasaso kalar yunwar da zaiji a yinin yau, dan shi azumi baiyi suhoor ba rayuwar shi na cikin tashin hankali. 4

“Nuriyya…”

AbdulKadir ya kira yana bubbugata, idanuwanta ta bude dakyar tanayin mika

“Dilla ki tashi karfe shidda fa” 1

Wata irin mikewa Nuriyya tayi tana kallon shi

“Karfe shidda? Shidda fa? Bamuyi Suhoor ba, baka tasheni ba”

Wani irin kallo AbdulKadir ya watsa mata yana jan tsaki

“Ban tasheki ba? Bake ya kamata ki tashi ba, ki dafa mana abinda zamuci, nine zan tasheki?” 5

Shagwabe fuska tayi, tanajin idanuwanta na cika da hawayen bakin ciki, duk yanda sukai zaman rashin mutunci da Anas yana tashinta lokacin azumi, tunda yaga randa batai suhoor ba ta zama abin tausayi, a kwance ta wuni shame-shame. Shine AbdulKadir zai sauke mata fada kamar akwai inda aka rubuta cewar ita ya kamata ta tashe shi dole dole. 7

“Kaima idan ka tasheni ai ba wani abu bane Masoyi”

Ta fadi wani abu na tokare mata wuya, kankance idanuwan shi AbdulKadir yayi

“Magana zaki fadamun?”

Ya bukata cike da neman ta furta wani abu ya sauke mata fadan shi, kai ta girgiza a hankali, hawayenta na kara taruwa, qwafa yayi yana sauka daga kan gadon ya wuce bandaki, abin na hade mishi waje daya, ga bakin cikin rashin suhoor ga asuba daya rasa, ga Nuriyya da zatai mishi kukan rashin dalili. Saida yadan watsa ruwa a gaggauce tukunna yayi alwala ya fito, bama shida kaya a dakin nata, dole sai yaje bangaren Waheedah. Nuriyya ya kalla da bata ko nuna alamar tashi ba

“Ke ba zakiyi sallah ba?”

Kafafuwanta ta sauko daga kan gadon

“Ba zakiyi wanki ba kuma? Bandakin ki baya shigar miki ido, me yasa bakya wankewa ne? Dakyar nayi wanka a ciki” 5

AbdulKadir ya karasa yana wucewa ta fice daga dakin. Wannan karin hawayen ta taji sun zubo. Wani malolon bakin ciki na tokare mata kirji, a haka ta dauro alwala ta dawo ta gabatar da sallar asuba. Tana idarwa ta koma bandakin, tasa tsintsiyar da take a ciki ta wanke shi sama-sama, ko omo bata saka ba. Ba zata fara karar da karfinta a bandaki tun yanzun ba, dan wani sharri ma, cikinta harya fara murdawa da alamar yunwa. Wani zaninta ta dauka ta hada duka kayan wankin da suke cikin bandakin ta kulle su, ta dawo ta cire zanin gadonta dan yayi dauda sosai shima takai bandaki ta ajiye akan wancen kayan wankin, zata fitar dasu tunda Waheedah ta dawo. 11

STORY CONTINUES BELOW

*

AbdulKadir kuwa dakin Waheedah ya wuce yana turawa wani kamshi ya cika mishi hanci, dakin a gyare yake tsaf. Ta sake zanin gado, ko ina tsaf tsaf, tana zaune kan gado ta mike kafafuwanta, ta goya Ikram ta gaba tana kwance akan kirjinta, hannunta daye rike da Qur’ani. Ba zaice ga kalar dinkin jikinta ta yanda take zaune ba, amman atamfa ce, ta daura dankwalin atamfar, fuskarta fayau babu kwalliya. Amman ta mishi kyau har zuciyar shi dokawa take. Sai da ta idar da ayar da take kan karantawa, tukunna ta dago idanuwa ta sauke su kan AbdulKadir din

“Ina kwana”

Ta furta cikin sanyin muryarta tana dan mishi murmushin da yaji zuciyar shi ta dan nutsu

“Wahee… Ya kuka tashi?”

Dan langabar da kai tayi

“Alhamdulillah…”

Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance mata

“Shine baki tashe mu ba? Mun makara, yanzun fa muka tashi, ko sallah banyi ba” 2

Ware mishi idanuwa Waheedah tayi, ita ba Suhoor takeyi ba, sai dai inta tashi tayi brush tasha ruwa, in tana da kankana ta dan sha dan samun ladan suhoor din, ko taci dabino wasu lokuttan, yau dinma hakan tayi. Zatai karya idan tace batayi tunanin duba ko AbdulKadir din ya tashi ba, tunda tasan yanda yake wahala idan baiyi suhoor ba, kawai dai ta tsinci kanta da share koma meye yake son yin tasiri a kanta 3

“Na dauka kun tashi, kasan ni ba Suhoor nake ba”

Kai kawai AbdulKadir din ya iya jinjina mata, ba sai ta fada mishi ba, yasan fushin da takeyi dashi ne, koya tashi Waheedah zata kara kiran wayar shi ta tabbatar da hakan, wahala take son yasha, kuma zai shata din yau ya sani. Kaya ya wuce ya dauka, yana ganin yanda Waheedah batace ya bari ta dauko mishi ba 5

“Ka dauki na kwana biyu ka wuce dasu Sadauki, inka dauki kaya kaje dasu bangarenta ka cire acan kabar mata acan, karka dawo mun dasu nan dan Allah” 10

Ta karashe maganar da rokon shi kamar yana da wani zabi

“Ki zo ki dauko mun to”

AbdulKadir yace kamar karamin yaro, Qur’anin ta ajiye tana tallabe Ikram ta sauko daga kan gado, kaya ta dauko mishi, riguna da gajerun wanduna, harda na ciki kala bibbiyu, tunda shi ba manyan kaya yake sakawa ba, yana dasu, in tayi magana kan ya saka bakinta ne zai tsini, ba zaisa ba, bayason manyan kaya. Hannun shi ta dago tana saka kayan a ciki, tayi mishi murmushi har hakoranta suka fito, idanuwa AbdulKadir ya kankance mata

“Ko turare baki fesa mun ba” 4

Kallon shi tayi

“Bafa kayi sallah ba, lokaci na wucewa kuma”

Wani irin shagwabe mata fuska yayi, ta wuce tana komawa tayi zamanta, tana daukar Qur’ani taci gaba da karantawa a bayyane da muryar data tsaya dai-dai kunnuwanta. Da kan shi yaje wajen mudubinta yana daukar turaruka ya feshe kayan dashi, ko inda yake ma Waheedah bata kalla ba, balle yai tunanin zatai mishi magana. Harya gama ya fice daga dakin, ta sauke numfashi tana cigaba da karatunta. Ko da ta idar, bata fita ba sai wajen karfe goma, da Ikram ta fita karta ajiyeta ta farka taita kuka dan wanki zatayi kafin su dauke wutar su.

Sai da ta fara share dakin wankin tukunna ta koma dakinta ta dauko jakar da suka dawo da ita da. Tana cikin firfito da kayyakin wankin sai ganin Nuriyya tayi kamar mikiya, ta diro dakin wankin, da katon zanin gado da alamar kayan wankine a ciki

“Lafiya?”

Waheedah ta tambaya tana tsare Nuriyya da idanuwa cikin yanayin da yasa Nuriyyar jin duk ta daburce, Waheedah din na mata wani irin kwarjini naban mamaki, dan ko babu fara’a a fuskarta bata hade girar sama da ta kasa haka.

STORY CONTINUES BELOW

“Ina kwana”

Nuriyya ta fadi saboda ta rasa abinda zatace kafin tayi saurin dorawa da

“Ya jiki?”

Sai da Waheedah ta kalleta na wasu dakika, tana sata jin duk ta tsargu, kafin ta amsa da

“Lafiya”

Tana cigaba da hidimarta, tsaye Nuriyya tayi mamaki duk ya gama cikata. Kayan wankin ta ajiye tana juyawa ta fice daga dakin. Wankin ta Waheedah tayi dan bashida yawa, ta kwashe ta zuba a wata babbar roba, Ikram tazo ta kwantar akan doguwar kujera tana saka pillow din ta tareta, dan yarinyar ta cika juye-juye, karta fado. Tukunna ta koma ta dauki robar ta fita bayan gidan inda igiyoyin shanya suke, ta shaya kayan ta dawo. Wanda Nuriyya ta ajiye ta kwashe tanajin nauyin shi, bangaren Nuriyyan da tunda ta shigo gidan zata kirga lokacin da kafafuwanta suka taka ta nufa, a tsakiyar falo ta ajiye mata kayan tana juyawa, dakin wankinta ta janyo ta saka mukulli ta rufe ta dauki Ikram suna shigewa ciki. 11

Nuriyya kuwa fitowa tayi dan ta kawo wata hijab da tagani da datti, taci karo da jibgin kaya ajiye a falo. Tsaye tayi turus tana kallon kayan cike da mamaki, ba rashin lafiya bace take damun Waheedah, wani hali na banza ne ta dauka da ba nata ba, dan bata santa dashi ba. Ranta a bala’in bace ta dibi kayan wankin tana komawa dasu ciki ta ajiye a tsakiyar bandakin, itama tana da injin wankin ai, bawai bata dashi bane ba, kitchen ta koma ta dauko ledar omo ta dawo tana kallon AbdulKadir da yake a kwance yana danna waya 10

“Masoyi…”

Ta kira shi muryarta na fitowa a karye, hakan yasa shi dago idanuwan shi ya kalleta

“Ya ake amfanin da abin nan?”

Dakuna mata fuskar shi yayi

“Wanne abu?”

Ya tambaya, yana sa kunya ta rufeta, dan ta tsani ace duk irin wannan abubuwan na gayu ita bata iya ba, muryarta can kasan makoshi tace

“Na wanki” 2

Mikewa zaune AbdulKadir yayi yana kallonta cike da rashin fahimta, hakan na sata sake fadin

“Injin wankin, ya ake amfani da shi”

Har lokacin kallon ta AbdulKadir yakeyi

“Da ina kikaje da kayan? Ba naga kin fita dasu ba”

Maganar shi nasa ranta kara baci

“Bangaren Waheedah…”

Ta amsa a taqaice tana kin mishi bayani, wannan karin fuskar shi ce dauke da tsantsar mamaki

“Me kike nufi da bangaren Waheedah?”

Kanta ta saddar kasa ganin irin kallon da AbdulKadir din yake mata

“Ita kika kai tayi miki wankin saboda baki da hankali?” 3

AbdulKadir yake fadi yanajin ranshi na kara baci fiye da yanda yake a bace, dan bai taba ganin irin wannan rashin hankalin ba, shisa ya sai mata nata injin wankin itama, yanda ma ba sai taje bangaren Waheedah din ba gabaki daya akan maganar wanki. Yana daukar abubuwa da yawa a rayuwar shi amman bayason raini

“Ajiyeta kikai da zaki kai mata wanki Nuriyya?” 2

Kanta ta kara saddarwa, hawaye na tarar mata cikin idanuwa a karo na biyu daga wayewar garin yau, ko kadan bata saba a sakata a gaba ana mata fada ba, ko a gida daman Baba ne yake mata fada in tayi wani abin, to sai tayi abu goma, Mama bata fada mishi ba. Ranta baci yake yi duk idan akai mata fada, balle kuma yanzun da take jin tayi girman da duk wannan abubuwan bai kamata ana mata su ba, ranta a bace tace

“Karka ce haka…”

Tunda shi ba zama yake gidan ba, kuma Waheedah din na wanke mata da, bai sani bane ba 2

STORY CONTINUES BELOW

“Dama can nake kaiwa, yaune kawai ta dawo dashi” 1

Sosai AbdulKadir yake kallon ta

“Wankin kike dauka daga nan, sai ki kai bangaren ta, sai ta wanke miki?” 2

Yayi tambayar yana saka Nuriyya jin kamar tayi wani laifine, wata yar dariya AbdulKadir yayi da ko kadan batada alaka da nishadi kafin ya sauko daga kan gado yana ficewa daga dakin ya doko kofar kamar zai karyata. Bangaren Waheedah ya nufa ko sallama baiyi ba yanda ya tura dakin yasa ta bude idanuwanta daga baccin daya soma fisgarta

“Wanki kike ma Nuriyya? Akan wanne dalili?”

Ya bukata yanajin yanda ranshi yakai koluluwa wajen baci

“Baka taba kula ba sai yanzun?”

Waheedah ta bukata a sanyaye, dan yana gidan Nuriyya take kwaso wankin ta kawo mata bangarenta, shisa ta dauka yasani. 5

“Karki amsa mun tambaya da tambaya, karki kara batamun rai Wallahi” 1

Yanda yai maganar da yanayin fuskar shi yasata sauke idanuwanta daga cikin nashi, akwai yanayin da tasan ba zata fara gwada hakurin shi a cikin su ba, yanzun na daya daga cikin su

“Ko ban sai mata engine wanki ba, akan wanne dalili zakiyi mata wanki? Ajiyeki tayi?”

Numfashi Waheedah ta sauke

“Ina azumi nikam”

Kankance mata idanuwa tayi

“Ni nace miki bana azumin ne?” 2

Kai ta girgiza mishi a hankali, tana jin murmushin da yake shirin kwace mata, tayi kewar rikicin shi

“Allah ya baka hakuri Sadauki, yanzun ai zata wanke abinta kaga, kuma menene dan na hada na wanke?”

Kallon da yai mata yasa ta yin murmushi

“Yi hakuri”

Tsaki kawai AbdulKadir yaja yana ficewa daga dakin, su duka biyun haukata shi suke sonyi yaga alama. Akwai halayen Nuriyya da yawa da yake kula dasu yanzun da baya ganin su da, dakin ya koma yana samunta inda yabarta, bandakin ya wuce ran shi a bace har lokacin, tsayen da Nuriyya taga yayi ne yasata bin shi, nuna mata yanda zatayi amfani da injin wankin yayi, bama komai tagane ba saboda a masife yake nuna mata komai, yana gamawa ya fice daga dakin, falo ya koma ya kwanta kan doguwar kujera yana huci shi kadai. Ga hanjin shi daya tattaru ya kulle waje daya. Bacci yake son yi, rana na karawa kuma, yana so yadan shiga kasuwa, dan ba zai ba Nuriyya kudin shi ba. Komawa dakin yayi ya dauko wallet da mukullin mota sai wayar shi ya fita daga gidan. 6

*

Dakyar ya dawo gida, har wani haske-haske yake gani yana gilmawa ta cikin idanuwan shi saboda yunwa. Ga makoshin shi kamar sahara, a bushe da kishi, a hanya ya tsaya yai azahar, kayan ma dakyar ya fito da su daga mota, daga dankali sai doya da cefane ya siyo, sai kuma kwai da dakyar ya samo shi. Ga kasuwar a shaqare, darajar watan azumi shisa duk wanda ya take mishi kafa in ya bashi hakuri ko amsa baya samu, amman da mutanen da zai mara Allah kadai yasan yawan su, duk da haka saida ya watsa ma wani me napep zagi, baiko juyo ba illa kara gudun napep din ganin wandon sojoji a jikin AbdulKadir din. 4

Yana shiga ya wuce bangaren Nuriyya ya ajiye kayayyakin a bangarenta, tukunna ya koma mota ya dauko apple din daya gani yana shiga dakin Nuriyya, a falo ya sameta zaune, ta kwantar da Ikram a kujera tana mata wasa, sallamar shi tasa ta amsa tana dago da kanta, fuskar shi ta kalla taga gajiyar da take tattare da shi, ledar ya mika mata tasa hannu tana fadin

“Sannu da gajiya…”

Kai AbdulKadir ya jinjina mata, yana kallonta, jira yake tace mishi zata hada mishi ruwan wanka ya watsa ruwa, ko batace haka ba, ta fada mishi wani abin, ta nuna mishi damuwarta kamar yanda ta saba, amman ta ajiye ledar apple din tana mayar da hankalinta kan Ikram 2

STORY CONTINUES BELOW

“Wahee nagaji sosai, kuma yau ana rana”

Hancinta ta hada dana Ikram din da take wangale bakinta da babu hakora, suna saka zuciyar shi cika fam da kaunar su, hankalinta na kan Ikram din tace 3

“Sannu, akwai rana kam, ni da nake cikin gidama inajin zafi”

Kallonta yayi, muryar shi da wani irin sanyi yace

“Nasan nayi laifi, nasani Wahee, ki horani ta kowanne fanni zan dauka. Amman wannan rashin kulawar banda ita, zuciyata ba zata dauka ba Wallahi” 3

Yanda ya karasa maganar ya sata yin shiru batace komai ba, tanajin shi ya juya ya fice daga dakin. Numfashi ta sauke me nauyi, sai taji wani irin kadaici ya danneta, kewar Fajr takeji, da yana nan da ya dameta da surutun shi, addu’a take a kasan ranta, Allah yasa AbdulKadir din yaje ya taho dashi, tunda ita ba zata iya kira tace a dawo dashi ba. Tana nan zauna aka kira sallah, ta tashi ta dauki Ikram suka koma daki. 1

AbdulKadir yana shiga dakin Nuriyya a kwance ya sameta kamar gawa, har saida ta tsorata shi ganin ko motsin kirki batayi 1

“Nuriyya…”

Ya kira, tana dago kanta dakyar ta kalle shi, dariya yaji ta kubce mishi 6

“Duk azumin ne?”

Ya tambaya yana zama gefen gadon, ta matsa mishi can, duniyar takeji ta hade mata waje daya, ga baqar yunwa da take addabarta, ga wankin da tayi akwai kayan da suke zuba, duk ta hade su da masu haske. Harta zanin gadonta yayi kampala-kampala, zaman gidan takejin ya gundureta, ga kuma fadan AbdulKadir din. Zama tayi tana tunanin rayuwar da ta tsarama kanta kafin shigowa gidan shi, da wannan da takeyi yanzun. Ga kuma Waheedah ta kara sawa komai ya kwance mata, mamaki takeyi tana karawa, babu kalar tunanin da batayi ba, ko wasu kawaye Waheedah tayi masu mugun hali da suka bata shawarar canza mata haka. 7

“Wallahi bakaji cikina ba, kamar an mun sata”

Murmushi AbdulKadir yayi, zuciyar shi yakeji tayi nauyi a kirjin shi. Kan gadon sosai yahau ya kwanta, idanuwan shi ya rufe yanajin gajiya sosai. Bacci yayi har la’asar dan saida Nuriyya ta tashe shi tukunna yai alwala ya fita masallaci. Sanda ya dawo sun kawo wuta, yai zaman shi a falo yana kallon namun daji a tashar discovery. Har wajen biyar kafin yaga Nuriyya ya fito daga dakin tana bin bango, shima yunwar yakeji. Kitchen ta shiga tana rasa abinda zata farayi, batama san abinda zata dafa ba, tunda bataga alamar Waheedah zatayi girki dasu ba. Ita yau ma ba zataje bangarenta ba, alkawari taiwa kanta. 11

Zama tayi ta yanki doya ta fere tana samu ta dora, tunda taga kwai, gara ta soya musu doya da kwai kawai. Bude fridge tayi taga babu lemo ko daya sai ruwa, falo tazo tana samun AbdulKadir din tace

“Masoyi bamu da abin sha fa a dakin nan, ko fanta ka siyo mana” 10

Yana rike da remote, hankalin shi nakan tv ya amsa ta da

“Banda kudi”

Yana cigaba da kallon shi, abinda ya zame mishi dole yayi shi zaiyi, tunda tai mishi barnar kudi zata gane kuskurenta. Tsaye tayi tana kallon shi cike da mamakin fadin bashida kudi da yayi, ranta a jagule takejin shi

“Me zamuyi buda baki da shi to?” 1

Har lokacin bai kalli inda take ba ya amsa da

“Nima ban sani ba” 1

Yana cigaba da kallon shi. Kitchen Nuriyya ta koma, ta cika kamar zata fashe, dan ta kashe dubu arba’in shisa yake mata wannan wulakancin, wayarta ta dauka tana duba account dinta taga babu abin arziqi a ciki. Kudin hannunta kuma bai wuce dubu hudu ba, shisa take karajin kamar batada lafiya, dan ta tsani taji babu kudin kirki a jikinta, in ba zai bata ba tasan zai ajiye, zata kuma diba idan ya ajiye. Dan tana bukatar abubuwa na ciye-ciye. Doyar ta sauke da tafasa daya tayi ta tace ta. Ko gishiri ta manta ana zubawa balle dan sikari tunda sabuwar doyace, ko ba sabuwa bama taste din nayin dadi na daban inka dan saka sikari. 3

STORY CONTINUES BELOW

Ruwa ta maka mata, ta dauki cefanen ta juye wajen wanke wanke ta gyara shi, jiri ma takeji saboda yunwa. Markadawa tayi duka ta juye shi a tukunya. Tana da danyar kaza a fridge ta daukota, ba zata iya wata wahala ba, itama ruwa ta saka mata ta wanketa, da kankara a jiki har lokacin ta dauketa tana zundumawa cikin kayan miyar tunda a yayyanke take, kankara ce tayi, zata narke in taji wuta, ta zuba ruwa kofi biyu, duk su hadu su tafaso tare sai tayi miyar da yawa ta saka a fridge, diba kawai zata dingayi. Mai ta dauko ta bulbula a kai, ta bare maggi ta zuba ta rufe tana komawa daki ta kwanta. 33

Mintina talatin ta ba miyar ta fito tana ganin ruwan ya tsane, jujjuyawa tayi ta sauketa tana kashe gas din. Doyar ta yayyanka ganin yamma tayi sosai, ta kada kwai ta zuba maggi, ta dora mai. Yar albasa ta dauka ta yanka cikin kwan tana tuna cewar bata zuba a cikin miya bama. Karamin tsaki taja tana kara dauko wata albasar ta yayyanka a plate ta bude miyar ta zuba a ciki ta mayar ta rufe, tukunna ta zuba doyar cikin kwan ta cakuda ta juye ta gabaki daya a cikin mai tana komawa gefe ta tsaya. Aikam ya fara tasowa yana zuba har kasa, gabanta yai wata irin mummunar faduwa, zuwa tai kashe gas din mai ya zubo mata ta saki ihun da yasa AbdulKadir shiga kitchen din da gudu. 13

Hannu yakai yana kashe gas din ya kama na Nuriyya zuwa wajen famfo ya sakar mata ruwa

“Mahaukaciya ce ke? Me kikeyi haka?”

Hannunta ta cire daga cikin ruwan tana yarfewa saboda azaba. Turo baki tayi kawai dan tanayin magana fashewa zatayi da kuka, batasan me yasa komai yake jagule mata ba haka. Shi kanshi AbdulKadir din ranshi yaji ya kara baci, kananun fada haka ba halayyar shi bane ba, amman a kwanakin nan jin shi yake komai ma na fada ne, ganin idan ya tsaya a kitchen din fada zai mata yasa shi fita kawai ya koma ya zauna inda ya tashi. Nuriyya doyar ta samu wani waje ta rage, tana rage man ma, ta sake kunna gas din, ta soya ta ciki da kwan jiki duk ya nadi mai, ta kwashe ta saka wadda ta rage din itama ta soyata, doyar nayin wajenta kwan ma yanayin wajen shi. Zuwa lokacin shidda harda kwata. 5

Dan AbdulKadir ya wuce daki dan ya daura alwala, yana so ana kiran sallah ya fara saka wani abu a cikin shi tukunna ya fita masallaci ko zai samu natsuwar yin sallah. Nuriyya kettle ta dauka da nufin dora ruwan zafi su sha shayi, shaf ta manta da man da ya zube a kitchen din, ga kuma ruwan da ta zubar dan ta cika kettle din, ta kuma takashi tana nufar inda socket zaiyi, ta taka man tana wata irin zamewa, sai da tai sama, kettle din ma tayi sama tukunna su duka suka sauka kusan a tare, kettle din a gefe da ruwan ciki daya mungule gabaki dayan shi, ita kuma aka mazaunanta tayi warwas a kasa. Ta dauki wasu dakikai tana sauke numfashin wahala kafin taja kafafuwanta ta mike. 27

Jikinta take kakkabewa duk ta nade ruwan a doguwar rigar dake jikinta, kettle din ta dauka ta tari wani ruwan, tana kokarin mayar da hawayen da suka cika mata idanuwa taf. Gabaki daya duniyar ta hautsine mata a cikin kankanin lokaci. Kettle din ta jona tana kunnawa. Sannan ta sa abin goge-goge na tsaye ta fara aikin goge kitchen din, tanajin kiris take jira ta fashe da kuka. Tana gama gogewa ta sake mayar da miyar kan wuta ta bata mintina biyar tukunna ta kashe, ko tayi ko batayi ba a haka zataci. 4

Tana nan tsaye ruwan ya tafasa, kettle din ta kashe kanta, ta dauko flask tana juyewa taji kiran sallah. Ta karasa ta rufe, ruwa ta dauko a fridge sai ga AbdulKadir ya shigo kitchen din, ya karbe robar daga hannunta yana budewa yai Bismillah ya kafa bakin shi, Nuriyya na bin shi da kallo harya sauke robar hadi da wani irin numfashi, ruwan ya mika mata ta karba itama tasha, yana dirar mata ciki da wani yanayi mai sanyi.

“Kibani wani abu inci in fita masallaci”

AbdulKadir ya fadi yunwa yakeji har kan shi na mishi ciwo. Kular doyar ta bude mishi, a tsaye ya saka hannu yana dauka ya saka a bakin shi duk da ta mishi zafi, yanajin ta kamar babu gishiri, kuma kwan bai kama ba, Waheedah harda tattasai take saka musu in zata soya. Baiyi magana ba, saboda yau daya ga azumi, bazai dora alhakin fadansu akan shaidan ba, asalin halayen sune zasu bayyana. Ficewa yayi daga kitchen din zuwa masallaci, jikin shi har kyarma yake sanda aka idar ya taho gida. Bangaren Waheedah ya wuce yana jin kamshin daya hade waje daya baisan kona menene ba, amman ya kara mishi yunwa. Kan darduma ya sameta a daki tana azkar ne da alama. 4

“Sannu da shan ruwa”

Ya fadi yana kallon yanda fuskarta tai wani sanyi. Murmushi tayi mishi tana idar da addu’ar ta

“Sannun mu”

Ta amsa shi tana mikewa ta ninke dardumar da take kai. Kallon ta AbdulKadir yake tayi yana kallo ta fita daga dakin, tana dawowa da apple a hannunta ta gutsura tana taunawa, Ikram ta dauka a gefen shi tana samun waje ta zauna, yarinyar ta gyarama zama itama a jikinta dan ta bata tasha, taci gaba da cin apple dinta, cikin shi da yaji yayi wata irin murdawa yasa shi mikewa, dan da alama Waheedah ba zata bashi abinci ba, ta daina son shi yanzun…!Kan kafet ya zauna yana jiran Nuriyya ta fito daga daki ta dauko musu kular doya. Ko yaji bata dashi, ta ajiye tana samun waje ta zauna tare da fadin +

“Masoyi ko yaji bamu da shi, in karbo mana wajen Waheedah?” 7

Tun kafin ta karasa AbdulKadir yake girgiza mata kai. Bada shi za’ayi wannan danyen aikin ba, ba zata ja mishi jangwam daga dan samun natsuwar shi ba. Kai Nuriyya ta rausayar tana sake mikewa, kofina ta samu guda biyu, a kitchen din ta hada musu tea ta fito dashi tana ajiyewa AbdulKadir na shi, dauka yayi ya kurba dan ya kora doyar da tai mishi tsayuwar mashi a makoshi. Yana dan bata rai jin kamar akwai abinda ya kamata ya kasance cikin shayin da babu, ya saba da Waheedah na saka kayan kamshi a shayinta, yanzun kam ruwan zafine sai madara da milo, ko lipton din ma bai samu a ciki ba.

“Wacce irin doyace wannan Nuriyya? Babu kwai fa”

AbdulKadir ya fadi yana saka Nuriyya hadiye doyar dakyar, gashi tayi mata wani irin salaf, shi baiga kokarin da tayi ba, ko da bata soyu kamar yanda ya kamata ba, sai ya duba kokarin da tayi yai shiru 1

“Na saka kwai ni dai”

Tai maganar tana saka AbdulKadir din kankance idanuwan shi a kanta

“Bana gani ne? Ya zaki cemun kin saka kwai? Kafafuwa yayi ya rabu da doyar kenan” 18

Yai maganar a fadace saboda yanda yaji zuciyarshi na tafasa, ga yunwa yanaji ta fitar hankali, amman rabon shi da abinci makamancin mai munin wannan tun wani aiki da yaje Makodi, shima wajen abinda duk ka samu shi zaka aunawa cikinka. Amman ko wannan din zakaji alamun gishiri a jikin shi. Ganin tayi shiru yasa shi jinjina kai kawai, bazai karar da dan karfin shi akan doya da kwai ba. Haka ya dauka yana turawa sai ya danna da shayin ya hadiye. Iya inda yaji cikin shi ya cika ya tsaya yana karasa kurbe ruwan shayin ya mike, dai-dai lokacin da yan nepa suka zabi su dauke wutar su.

Dogon tsaki AbdulKadir yaja, yayi niyyar ya biya ya siyo mai dazun, kwana biyune bai damu daya kunna gen din ba shisa. Daman indai ya biyewa Waheedah ba kunnawar zai dingayi ba, zatace ita babu abinda zatayi da wutar tana da charge, kuma tama fitilar ta ma, sai dai in ana zafine dan su kunna fankoki. Da fitilar wayar shi yayi amfani zuwa daki ya dauko ma Nuriyya tata wayar yana kunna maya fitilar ya ajiye kan kujera ya kama hanya yana ficewa daga gidan batare da yace mata komai ba. Tana jin shi harya fita bata dai dago bane ba, wani irin kunci naban mamaki ya cika zuciyarta fam, ba zata tuna ranar karshe da wani abu yazo wuyanta yai tsaye ba haka. 5

Har yunwar da takeji ta nemeta ta rasa, kwashe kwanonin tayi tana mayarwa kitchen, acan ta tsaya dakyar ta shanye ruwan shayin tanaji kamar zata kama da wuta saboda bacin rai. Shinkafarta data dora ta duba taga ruwan ya tsane, ta kashe gas din tana barinta a cikin tukunyar ta wuce dakin bacci, alwala ta sakeyi jin har ana kiran isha’i. A daddafe tayi sallah tana idarwa ta janyo wayarta tana bude whatsapp ta lalubo chat dinsu da Asma, ita kadai ce kawarta da zatace suna maganar komai a yanzun, kuma bazawara ce, a FCE suka hadu. Ita Nuriyyar ma ce ta manne mata saboda ganin yanda tafi kowa wayewa da kudi a ajin. Har suka zama kawaye, dan Nuriyya na bala’in so ace tana tare da manyan mutane. 3

‘Asma mutumin nan bashi da kirki wallahi, kinsan dai yanda azumi yake bani wahala ko da nayi sahur balle yau da muka makara, dakyar na soya doya kinji masifar da ya sauke mun’

Kafin kace meye Asma harta karanta sakon

‘Ya dauko miki yar aiki kema, kina auren mutum kamar wannan zaki zauna kina shiga Kitchen, ke banzar ina ce, narkewa zakiyi saiya dauko miki yar aiki” 2

Numfashi Nuriyya ta sauke, duk yanda zata misaltama Asma halin AbdulKadir din ba zata fahimta ba

‘Kika san magana nawa nai mishi? Taurin kan shi yafi karfina, yace ba zai dauko ba fa, kuma nasan ba zai dauko din ba’

STORY CONTINUES BELOW

Kawunan mamaki Asma ta turo mata tana dorawa da rubuto

‘Lallai ma, saiki zauna kina kwasar bakin ciki ai, shisa kinganni, auren nan ya gama fita kaina wallahi, tunda na tungule aurena na biyu naji ko zanyi wani ba nan kusa ba, bazan zauna wani katon banza na batamun rai ba. Ga mutane nan kaca-kaca suna lallabani, sha’anina kawai nakeyi. Kudi na shigomun ta ko ina’ 2

Shiru Nuriyya tayi tana tauna maganar, da gaskiyar Asma, kafin igiyar aure ta daureta da AbdulKadir free take jinta, babu nauyi ko tunanin kowa, inda take so nan take zuwa, amman yanzun tana iya tambayar AbdulKadir zataje waje ko baya gari yace ba zata ba, iya wannan ta kasa sabawa dashi, dan auren Anas mayafi take dauka in yana nan tace mishi ta fita, idan baya nan tayi gaba abinta. Balle kuma yanzun ga maganar girkin nan da sauran ayyuka, ta shiga wani irin matsatsi cikin kwanaki kadan da bata taba hangowa ba, ko kafin kwanakin nan, zasuyi waya da AbdulKadir, zasuyi chatting ko yayane, zaizo suyi hira tana kwance a jikin shi. Amman tanajin wani abu can kasan ranta da ta rasa menene.

Sai yanzun takejin farin cikine cikakke bata dashi, ba zatace ma ga asalin yanda yake ba, dan inta taba shigar shi a bayama ta manta. Yanzun ne kuncinta ya karu, rayuwar a cunkushe take jinta. Data dinta ta kashe batare da ta amsa Asma ba. Ta ja jiki ta haye gado ta kwanta, gara ko bacci ta samu tayi watakila zuciyarta zatayi mata sanyi-sanyi. Tana nan kwance taji shigowar AbdulKadir din ya wuce bandaki kan shi tsaye, ruwa ya watso ya fito ya saka gajeran wando dan baiga towel din shi ba 2

“Nuriyya ina towel dina?”

Ya bukata, kai ta dan dago, bata ganin shi sosai saboda ta kashe fitilar wayarta, tashi kuma ya ajiye a bandaki, tadan hasko dakin kadan. Sai da taji zuciyarta ta doka, dan tunda ta kwaso kayan daga wajen shanya, kulle su tayi a cikin zanin gado ta ajiye can gefe

“Magana nake dake fa”

AbdulKadir ta fadi a kule, saukowa tayi daga kan gadon tana kunna fitilar wayarta ta taka zuwa inda ta ajiye kullin kayan ta kama su taba kwancewa 1

“Ki mikomun gajeran wando da singlet”

Daukowa tayi, duk sun zama kamfala, musamman gajeran wandon da yake ruwan madara, mayar dashi tayi ta dauko mishi na kakin sojoji shima duk yayi rodi-rodi. Tana dunkule su waje daya ta karasa ta mika mishi, kamar hakan yan nepa suke jira da bugun agogo na alamun cikar karfe tara na dare suka kawo wuta, haske ya gauraye dakin, yana dai-dai da sauke idanuwan AbdulKadir akan kayan ya kuwa ware su yana bude kayan sosai. 7

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un” 2

Ya fadi yana jujjuya wandon shi

“Bansan akwai kaya masu zuba ba, na hada duka”

Kai AbdulKadir yake girgizawa

“Aikin ki kenan, kullum bakisan abu ba, ko yaushe uzurinki baki sani ba. Hankalin ki bai baki ba’a hade gabaki daya kaya wajen wanki ba? Idan kin hada wandon nan da sauran kaya, me yasa zaki hada farare da masu kala? Ke mahaukaciya ce?” 3

Ya karasa maganar yana kallon ta

“Kuskure ne kowa nayi”

Nuriyya ta fadi cike da gajiya

“Karki fara mun rashin kunya, wallahi karki fara cewa zaki fadamun magana Nuriyya, baki sanni ba ko? Bakisan halina ba har yanzun, shisa nake magana kina kokarin mayar mun”

Shiru tayi idanuwanta na cika da hawaye, gefen gado ta koma ta zauna, ta dauka yayi shiru, ai kamar lokacin ya fara fada, sai da yayi mai isar shi tukunna ya koma bandakin, ranta inyai dubu a bace yake, kwanciya tayi tana tsiyayar hawaye masu zafin gaske, ko kadan ba wannan rayuwar ta hango ba, bata saba ana mata fada ba, duk bala’in Anas ba koyaushe yake kulata ba, sai ta kaishi karshe, shima in yaga ta hayayyaqo mishi sai yayi shiru ya kyaleta koya fice daga gidan. Amman yanda AbdulKadir ya nuna yana gab da kwada mata mari shisa tayi shiru, ba sai kowa ya gaya mata ba zai dauki kaso daya cikin abinda Anas ya dauka ba. 5

STORY CONTINUES BELOW

Fitowa yayi har lokacin ran shi a bace yake ji shisa ya karayin wanka. Ya zagaya kan gadon ya hau yana kwanciya, baya Nuriyya ta juya mishi, tsintar kan shi yai da bai damu da hakan ba, Waheedah ce dai bata isa ta juya mishi baya ba kome yai mata, ko gajiya tayi da kwanciyar zata juya hannu sai dai suyi musayar waje. Ko a jikin shi take kuwa, sai dai in bacci yayi, daya tashi ya ganta saiya kamata ya juyata. 11

“Ki kashe mana fitila”

Ya fadi yana juya kwanciyar shi, yana jinta ta sauka daga kan gadon ta kaso fitilar ta dawo. Alarm ya saka a wayar shi ya ajiyeta gefe, Addu’ar bacci ya tofa a jikin shi yana lumshe idanuwan shi duk da alamun yunwa da yakeji.

*

Karfe uku da rabi alarm din daya saka ya tashe shi, sai da yayo brush da alwala tukunna ya tashi Nuriyya. Rigar kirki ya dauka yasaka a jikin shi, yana ganin yanda ta koma kamar Kampala itama, sallar nafila ya tayar yanayin raka’a hudu. Sai lokacin ma Nuriyya ta sauko daga kan gadon dakyar ta shiga bandaki ta wanko fuskarta, ta wuce kitchen. Mikewa AbdulKadir yayi yana fita shima ya nufi bangaren Waheedah ya tura hadi da sallama ya kuwa same shi a bude, kwan dakin ya kunna yana sakata runtsa idanuwanta sosai alamar hasken ya shigar mata cikin su, kafin ta bude su tana kankancewa akan AbdulKadir 4

“Nace ki dinga kulle kofa, bakyajin magana ko Wahee?”

Cikin bacci ta turo mishi bakinta da har lokacin da alamun janbaki ja, mika tayi, muryarta cike da bacci tace

“Na manta ne”

Hararta AbdulKadir din yayi yana sakata yin murmushi

“Kinfi so inta surutu kan abu dayane kawai”

Ya karasa ya dauki Qur’ani daman shi yaje dauka, ya tako yana kashe fitilar

“Kabar mun a kunne”

Waheedah ta fadi, sake kunna mata yayi yana jan numfashi kamar yana son zuqar iya kamshin da zai iya da yake cikin dakin kafin ya fita hadi da ja mata kofar. Dakin Nuriyya ya koma ya samu waje ya zauna yana bude Qur’anin shi ya soma karantawa cikin sanyin murya, yana wajen har Nuriyya ta shigo ta ajiye musu plate din shinkafa sai miya data zuba a wani kwanon, sai da AbdulKadir ya karasa shafin da yake karantawa tukunna ya rufe Qur’anin, su Hajja kawai yaiwa Addu’a sai iyalan shi da yan uwan shi, Yassar ne na farko. Janyo jikin shi yayi yana matsowa inda Nuriyya take zaune, yanayin shinkafar a idanuwan shi yaga kamar bata dahu ba, hakan yasa shi dan dibowa da cokali ya saka a bakinshi ya dan tauna yaji ta giri-giri 1

“Wallahi bazan ci shinkafa a tsai-tsaye haka cikina ya kumbura ba, bata dahu ba” 3

Ya fadi yana ajiye cokalin, kallon shi Nuriyya tayi

“Kici a bakin ki, da tun jiya kika dafa mana yanzun saiki yi warming kawai”

Plate din Nuriyya ta dauka tana mikewa da sauri ta fice daga dakin, dan duk wani abu na zuciyarta gaya mata yake ta juye mishi shinkafar sannan ta kwantara mishi farantin tangaran din saman kai kowa ma ya huta. 21

“Kece da asara Waheedah, danni bawai ya dameni bane” 15

Nuriyyar ta fadi a fili da bala’in bacin rai, da tayi tunanin kwantara mai faranti ya mutu duk su huta. Cikin tukunya ta mayar da shinkafar ta kara ruwa tayi tsaye. Idan ta koma dakin ya sake magana tanajin kome ya fito daga bakinta fada mishi zatayi sai dai in gabas zai saka kanta ya yanka yayi. Tagaji har cikin kasusuwan ta, ya fara fita daga ranta daga shi har auren, a wuya takejin su sun mata tsaye. Takai mintina sha biyar har saida ta fara jin kaurin shinkafar tukunna ta kashe gas din, ko ta dahu ko bata dahu ba haka zai hakura yaci, ko ya fito ya dafa wata. 2

Sake zubawa tayi ta dauka tana komawa dakin ta ajiye. Dan diba AbdulKadir yayi yana sakawa a bakin shi, tadan rissina ba kamar dazun ba. Duk da bata kai yanda Waheedah take dafa musu laushi ba, kallon shi Nuriyya takeyi tana jiran taji ya sake cewa bata dahu ba, dan tabbas wannan karin zata kwantara mishi farantin tangaran din. Sai taga baice komai ba, miyar ya dibo yana zubawa a gaban shi hadi da cakudawa, ba sosai yake son abinci mai zafi ba, hakan ne yasa shi baiyi saurin kaiwa bakin shi ba, ta riga shi zuba miyar ta juya ta diba ta saka a baki. Wani irin karni taji cikin kofofin da suka hada bakinta da hancinta, sannan miyar ta sauka cikin bakinta da wani dandano marar kan gado, tana taunawa dakyar ta hadiye.

STORY CONTINUES BELOW

AbdulKadir ta kalla daya ciko cokali tanajin kamar tace mishi karya ci, ya kuwa auna cikin bakin shi, lokaci daya yanayin fuskar shi ya sauya, bai tauna shinkafar ba ya hadiye yana wani irin sauke numfashi har lokacin bakin shi a gauraye yake jin shi. Mama na musu abinci marar dadi, amman yana ciyuwa, bakajin kamar zaka shaqe ka wuce lahira

“Kasheni kike so kiyi Nuriyya… Da raina kike so ki kasheni” 9

AbdulKadir ya fadi yana dorawa da 1

“Baki iya abinci ba, bansan ya akai ban taba sani ba sai yanzun… Wacce irin miyace wannan?” 7

Kai Nuriyya ta saddar kasa tanajin kunyar data shiga ta danne bacin ran da take ciki

“Shisa kike cewa in daukar miki yar aiki?”

Kai tadan daga mishi a hankali, kai AbdulKadir ya jinjina dan abinda ba zai taba yiwuwa bane ba, badan kar a tayata aiki ba, ko dan baya goyon bayan mazan da suke daukar ma matan su yan aiki ba, ko da babbar sallah yana ma Hajja magana a dauko ma Waheedah ta soya mata nama. Baiga dalilin da zaisa shi yaci abincin yar aiki ba

“Ki koya dan ni ba zanci abincin yar aiki ba”

Kallon shi Nuriyya tayi sosai, tana tunanin ta inda yake so ta fara koyon girki, kowa yake so taje ta samu ya koya mata

“Kafin ki kasheni dan Allah ki dinga mana mai da maggi” 10

AbdulKadir ya karasa maganar da sigar roko yana dorawa da

“Yanzun ma tashi zakiyi ki zubomun da mai…” 1

Batayi musu ba ta mike, numfashi AbdulKadir ya sauke yana jin komai ya birkice mishi, fada yaso yayi sosai, amman kananun maganganu ba halayyar shi bace ba, bai kuma saba komai sai yayi magana a kai ba, sun sami matsala da yawa yau Da Nuriyyar bayaso su kara samun wata cikin daren nan. Dan yasan halin sune, kome zai faru iya sune, babu shaidan din da zasu labe a bayan shi tunda watan azumi ne. Bai shirya sanin yana da halaye marassa kyau ba, gara tasan yanda zatayi ta koya, ya dai cika da mamaki, ya dauka koyayane mata sun iya girki tunda abune da sukeyi yau da kullum. 2

Da mai yaci kuwa yana mayarwa da ruwa ya mike, yanajin yanda idanuwan shi sukai zuru-zuru duk da bai kallo mudubi ba. Bacci suka dan koma kafin asuba. Sanda ya dawo masallaci Nuriyya harta sake komawa bacci. Shikam zama yayi yana yin azkar har rana ta fito ya mayar da sallah raka’a biyu ta nafila. Sai daya wuce dakin Waheedah yana samunta tana linke dardumar ta da alama itama sai lokacin ta tashi. Dan ita ta saba mishi da yin nafilar bayan asuba, ko kadan bata wuce ta, ta tunasar dashi tarin ladan da yake cikin hakan. 1

Yanzun harta zame mishi jiki, cikin sanyin muryarta ta gaishe dashi, ya amsa

“Kun tashi lafiya?”

Sai da ta fara jinjina mishi kai tukunna ta amsa tana dorawa da

“In kaje gida yau ka taho da Fajr”

Kallonta AbdulKadir yayi, sosai take kewar yaron nata

“Ni nace miki zanje gida ne? Ki kirasu a kawo miki shi”

Kai ta girgiza mishi

“Ni kunya nakeji ai”

Dan murmushi yayi

“Lallai yarinyar nan, nine sarkin rashin kunya ko?” 1

Dariya Waheedah ta tsinci kanta dayi tana girgiza mishi kai

“Haka kike nufi mana, ba zanje ba to, in kina kewar shine ki kirasu da kanki”

Ya karasa maganar yana juyawa dan bacci zaije yayi daman zai duba ya suka tashine.

“Dan Allah ka dauko mun yarona”

Juyawa AbdulKadir din yayi yana harararta ya fice daga dakin yaja mata kofa, dariya take sosai, har ranshi tasan harara ce yake ganin yanayi, amman idanuwan shi basuda girman da zasu juyu har suyi hararar, bata taba gaya mishi bayayi dai-dai ba. Sai dai tasha dariyarta kawai. Ikram ta dauka tana cire mata kaya, dan wanka zatayi mata, itama tayi, sai suzo suyi baccin. 3

STORY CONTINUES BELOW

*

Bacci yayi har wajen sha biyu sannan ya tashi, ya watsa ruwa ya fito yana zaune bakin gado, Nuriyya na kai tana danne-danne waya, dan group dinsu an turo wasu laces masu bala’in kyau. Kuma duk wanda yake cikin group din yace yana son guda daya, ita kadai ce batace a ajiye mata ba, dan taji Hajiya Kaltume mai siyar da kayan tace kudi hannu ne, ba zata bayar da bashi ba wannan karin, da sai ta dauka sai karshen wata. Gashi kowa sai magana yakeyi ita ba zata siya ba, tana ta kallon sune batasan me zatace ba, kar a rainata.

“Masoyi”

Ta kira cikin sanyin murya, tana saka AbdulKadir din kallonta

“Kaga wani lace” 1

Ta fadi tana nuna mishi wayar, kallo yayi yana jinjina mata kai

“Yayi kyau”

Ya amsa a taqaice yana daukar tashi wayar da take ajiye a gefe. Murmushi Nuriyya tayi dan taga alamar zatayi nasara

“Dubu arba’in da biyu”

Kai kawai AbdulKadir ya jinjina mata baice komai ba yaci gaba da danna wayar shi, da sauri tace

“In dauka zaka biya kudin?” 9

Dago idanuwan shi AbdulKadir yayi yana kallonta kamar bata da hankali 1

“Wai me kika daukeni ne Nuriyya? A bishiya nake tsinko kudi kome? Kin manta kudina da kika kashemun, kin sani saida na taba wasu dana ajiye dan wani abin, har kina mun maganar in sai miki abin dubu arba’in da biyu. Ina nagan su?”

Kallon shi take dan in jikinta zai zama kunnuwa ba zata taba yarda bashida su ba, da cayai mata ma bazai bayar ba sai yafi mata saukin yarda. Wayar shi AbdulKadir yaci gaba da dannawa yana nemo text din albashin shi ya ajiye wayar kan gadon yana turama Nuriyya data dauka

“Bansan kallon me kike mun ba, amman ni ba wasu kudi gareni ba, kinga albashina nan duk watan duniya, a ciki nake duk hidimata, katon gidan nan kudin allowance ne na wasu ayyuka, haka motata, bawai albashina bane, sukuma sai ayi shekaru ba’a same su ba. Idan ban taba fada miki ba yau kisani, ni bamai kudi bane, cikin layin masu rufin asiri ma a tsakiya za’a sakani” 4

AbdulKadir ya karasa yana mikewa ya fisge wayar shi daga hannun Nuriyya yana ficewa daga dakin yabarta a zaune gabaki daya jikinta ya gama mutuwa. Tabbas yau kallon kitse ake ma rogo ne ya tabbata a kanta, wannan albashin na AbdulKadir sam-sam bashi bane burinta ma hamshaqin mijin da take son aure 7

“Tafdin…” 1

Ta fada ranta a jagule, kwata-kwata yanda ta hango AbdulKadir ba haka yake ba. Daga halayen shi har kudin shi, ita da bata hango ckarta shekara daya a gidan batare da tayi motar kanta ba. Da wannan yagalgalallen albashin yaushe harya tara kudin da zai siya mata mota. Wani kunci takeji yana taso mata tun daga yatsan kafarta yana mata zaune a kirjinta. Harma fada mata yake shi ba kudi yake dasu ba dan karta sa ran zai mata wani abin arziqi. Har ranta take jin babu wanda ya cuceta sai Waheedah, babu babbar makira irinta, ita ta dinga nuna mata kamar tana cikin daular rayuwa, ita kuma ta dinga mata hidima kamar AbdulKadir din wani hamshaqin mai kudine, ita taja mata duk wannan abin da take ciki, dan ita ta haska mata AbdulKadir din taga kyallin shi harta kwadaitu da auren shi, amman da duk mintina take ganin abinda bataso a tattare dashi. 34

Gani tayi bakin ciki zai mata katutu, ga whatsapp din data bude harta private Hajiya Kaltume ta mata maganar siyan lace din nan, hankalinta ya kara tashi, hakan yasa ta janyo system dinta, drawer din gefen gado ta janyo ko ta saka earpiece dinta a ciki, taga wata leda da batasan ta ajiye ba, dagota tayi taga kudine a ciki, sai da zuciyarta tai wata irin dokawa, warware ledar tayi tana zazzago kudin kan gadon, ganin su tayi da yawa sosai, da sauri ta tashi ta saka mukulli ta kulle kofar ta dawo, kudine masu yawan gaske dan ba’a dauresu ba, hakan ya sata tunanin da alama ana zararsu ne. Tasan AbdulKadir din kan ciro kudi ya ajiye ana diba, dan tasha zara kuma bai taba ganewa ba tunda bai mata maganar ba.

Duk da zuciyarta na dokawa, wani abu kasan ranta na fada mata kar tayi, dubu arba’in da biyu ta kirga ta ware su a gefe, ko kwatar kudin bataga alama sun girgiza ba, tasan ba kirgawa zaiyi ba, da sauri ta gyaggyara su ta mayar cikin ledar tana nannadewa kamar yanda tagani ta mayar ta rufe drawer din. Wanda ta diba din ta mike ta samu jaka ta zuba su a ciki. Kafin ta zauna taji ana kwankwasawa, da yake ta saba dibar kudin Anas ko dar bataji ba, taje ta bude mishi kofa, baice mata komai ba ya rabata ya wuce. 10

‘Namiji munafuki’

Ta fadina ranta, daman akance namiji bazai taba nuna maka samun shi ba, yau ta kara yarda, yanzun ya nuna mata wani alert kamar mai gaskiya, jibi kudin da ta gano. Daman tanata tararrabi anya ace bashida kudin da take tunani. Tana kallo ya bude drawer din ya dauki ledar ya sake zuwa ya fice, dakin ta tura. Ta koma kan gado tana daukar wayarta taba Hajiya Kaltume amsa

‘Ni banda kudi a banki, Cash ne bansan ya za’ayi ba, gashi yau bazan fita ba, ni nake da girki’

Ba’ayi mintina biyu ba Hajiya Kaltume ta amsa ta

‘Kibani address din zan turo yaro yazo ya karba’

Tura mata tayi kuwa tana komawa kan gado ta zauna. Ko da kirgawa AbdulKadir yayi yagane an diba sai ta bashi hakuri, fadane zaiyi saita toshe kunnuwanta ta kyale shi, in aka kawo lace din ta daura a jikinta zai wanke mata haushin shi da zataji na dan wani lokaci. Ko mintina sha biyar ba aiba, taga kira yaron harya iso kofar gida. Kudin ta dauka ta saka hijabi ta leqa ta kai mishi, saida ya kirga a gabanta tukunna ta dawo gida, tana jin wani abu yadan kwanta cikin bacin ran data shiga. 9

*

“Hamma kasan fa bani da lafiya, gashi ana rana, ina azumi ka fito dani”

AbdulKadir ya fadi yana mika mishi ledar kudin da sun kai kwana goma a ajiye a wajen shi, dan Yassar din yayi cinikin mota zai sake wata, tashi nata bashi matsala, daya ciro kudin sai cinikin bai yiwuwa ba, yana jin qwiyar komawa bank ya kuma san halin shi, ko Hauwa yaba ta ajiye saiya bi ya karba ya kashe. Amman idan AbdulKadir dinne ba zai bashi ba sai dai ko in lalura. Yanzun ma dan yace ga motar an kawone an gama komai, kudinne kawai zai basu, tashi motar ma har wanda ya siya ya dauka tukunna AbdulKadir din ya fito da kudin. 7

Ya daukama dakin Waheedah ya ajiye, dan yaje yana nema, ta taya shi basu gani ba, kafin ya tuna dakin Nuriyya ya ajiye.

“Kai kamar ba soja ba”

Kankance mishi idanuwa AbdulKadir yayi

“Ina gida yanzun, kabarni. Kuma ma dan ina soja sai akace duk wahala in dinga jureta”

Kai kawai Yassar ya girgiza mishi yana karbar kudin ya basu. Suna tsaye aka kirga

“Dubu dari hudu ne babu arba’in da biyu”

Da mamaki Yassar yace

“Bangane ba”

Dan yasan kudin shiya ciro su da kan shi

“Eh babu dubu arba’in da biyu” 3

AbdulKadir ya kalla yana fadin

“Ka taba kudin nan ne AbdulKadir?”

Kai AbdulKadir ya girgiza dan baima ji me suke fada ba, hankalin shi nakan wayar shi da yake duba sako

“Me ya faru?”

Ya bukata yana mayar da hankalin shi kan Yassar din

“Wai basu cika ba, babu dubu arba’in da biyu”

Dagowa AbdulKadir yayi daga jikin motar shi

“A kara kirgawa dai”

Ya fadi saboda bayason abinda ya fara zuwa kan shi ya tabbata, sam bayaso, mutumin kuwa bai musu gardama ba, wannan karin duk a tare suka kirga kudin, babu dubu arba’in da biyun. Wallet din shi AbdulKadir ya zaro yana dauko ATM din shi ya mikama Yassar 1

“Kasan password din”

Wani irin kallo Yassar ya watsa mishi kafin yace

“Bana son iskancin banza da wofi”

Kai kawai AbdulKadir ya jinjina yana mayar da ATM din inda ya dauko shi, batare da yace komai ba ya bude murfin motar shi, ran shi ya dade bai baci ba irin haka.

“AbdulKadir me ya faru? Ka fito daga motar nan muyi magana”

Yassar ya fadi ganin yanayin fuskar AbdulKadir din, amman mukullin motar shi ya murza yana tayar da ita, duk maganar da Yassar din yake mishi baiji ba ya fisgi motar yana hawa titi…!Tunda ta gama baccin safenta ta gyara bangaren ta tsaf, sannan tayi wanka ta shiga kitchen. Dan wanke-wanken da take dashi tayi. Ikram na kwance cikin kekenta tana bacci. Fridge din ta duba taga tana da naman rago, kawai sai marmarin tuwon semo da miyar dan yar kubewa ya kamata. Fito dashi tayi dan ya huce, yayi kankara, ta dauki Ikram suka fito ta kulle kitchen dinta. Daki ta koma ta kira Naziru a waya tace yaje ya siyo mata danyar kubewa ya kawo mata in yazo sai ta bashi kudin. Hakan kuwa akayi, dadewar da yayi har bayan azahar yasa ta dauka ma ya manta dan tasan shiriritar shi.

Kitchen din ta koma ta samu kwando ta juye kubewar a ciki, tana da yawa, inta ajiyeta ma kafin ta sakeyin wani tuwon zata iya yin yaushi, gara tayi miyar ta saka a fridge. Tasan zata waiwayeta. Ajiyewa tayi ta wuce daki ta dauko wayarta ta dawo, Tafsir din Sheikh Albani ta kunna kan yanda zaka kara gyara ibadunka. Ta rage karar dai-dai kunnenta tunda ba earpiece ta saka ba, duk da ita kadai ce ta riga ta saba. In akwai abinda yake saurin sosa mata rai bai wuce tana zaune waje wani ya kunna waka ko wani abin ya kure sauti ba. Sam mutane basa tunanin ko wanda yake kusa dasu baya jin dadin su abinda suke saurara din, ko baya cikin yanayin son saurarar komai.

Wasu suna ganin ai karatun Qur’ani ne, musamman lokacin azumi, kuma zaka iya shiga hakkin wani, shisa aka saukaka da akai earpiece, ka saka kaji duk abinda kake so dai-dai kunnuwanka batare daka takura kowa ba. Kubewarta ta wanke tana dauko abin gogawa ta dauraye shima ta ajiye su gefe dan taga naman ya saki, gara ta dora shi ta dafa, har cefane ta dauko, lokacin ba wahala gare shi ba, gashi tana son dafa zobo. Aikinta take a nutse taga giccin AbdulKadir da wani irin sauri da ya sakata leqawa, yanayin tafiyar shi ya tabbatar mata da ranshi a bace yake sosai.

“Allah ya rufa asiri”

Ta furta a hankali tana komawa taci gaba da aikinta. AbdulKadir kuwa duk azumin da yake bai hana shi zira kai ta murfin mota yana ma mutane masifa a hanyar shi ta zuwa gida ba, dan gani yake sun tare mishi hanya, sun hana shi isowa da wuri, wayar shi ma da Yassar ya ishe shi da kira kasheta yayi. Ba zai tuna ranar karshe da yaji kunyar Yassar irin yanda yaji ba yau. Tunda can ma akan Yassar ne fara sanin yana iya jin nauyin wani dan adam haka, kan shi tsaye zai iya fadama Hajja abu, har Abba ma, koya tambaye su abu, amman Yassar saiya jima yana juya maganar kafin ya samu ya fito da ita. Lokutta da dama yanajin kamar shine ya kamata ya fito ciki daya da Yassar, su kwanta a mahaifa daya saboda kusancin da yake tsakanin su. 6

Sai dai haka Allah Ya kan tsara lamurra, wani lokacin ma sai kaga shakuwa a tsakanin mutanen da basu hada jini ba, Yassar na daya daga cikin abinda yake godema Allah da samu a duk sallar shi ta duniya tunda ya mallaki hankalin shi. Ta ina Nuriyya take so ya fara hada idanuwa da Yassar din? Me take so yace mishi bayan yau? Ta mishi abubuwa da yawa, kanana da manya da ya dauki idanuwa ya saka mata, abubuwan da duk ya tsarama kan shi ba zai dauke su a wajen macen da yake aure ba. Sai dai ita din ba Waheedah bace ba, yanajin ranar da duk zai waiwayi abinda tayi mishi da wahala alaqarsu ba zata samu tangarda ba, shisa yake kauda kai yana kyaleta. 1

Yau ne ta kai shi saman kanta ga ba jikin bango bama, da shi ta taba, da kudin shine, watakila ba zai ji abinda yakeji ba yanzun, da kudin ma na wani ne daban da yasan in ya mayar mishi zai karba duk abin zai zo da sauki. Kudin na Yassar ne, kuma ko jiya sai da yai mishi mitar bashi da kudi, yai ma Hawwa gyaran mota, yana so ya kara tara wasu kudin itama ya sake mata wata, zai iyayin abubuwa da dubu arba’in da biyun shi, ko kayan abinci zai siya ya ajiye, ko yayi hidimar sallah da take gaban shi cikin kwanaki kasa da talatin. AbdulKadir na da tabbacin bashi kadai bane yake tsara komai na rayuwar shi. Ciki harda yanda kashe kudin shi yake tafiya.

Bakin kofar dakin Nuriyyar ya tsaya yana rike da handle din kofar, idanuwan shi ya lumshe ko zai tuna wani dalili da yasa zuciyar shi doka mata tun daga farko amman ya rasa, ba halayenta bane, saboda baisan su ba lokacin da ya fara son ta, bai san su ba lokacin da zuciyar shi ta sake doka mata bayan ya rufe shafinta daga rayuwar shi. Baisan ko kadan cikin halayyarta ba lokacin da ya amince ma aurenta, halayenta sun fito mishi ne bayan ya aureta, a kasa da sati daya bayan ya aureta ya fara kula dasu, sun sake fito mishi bayan ta tare a cikin gidan shi, zama ya hada su, tana saka shi fahimtar dalilin da yasa mutane ke cewa zaka iya shafe shekaru da mutum ba kasan ko da kashi ashirin cikin halayen shi ba, saboda akwai boyayyayun halayen da ba mutum bane yake boye su dan kar a sani, basa fitowa ne sai zama na a kwana a tashi karkashin inuwa daya ya kama suke bayyana.

STORY CONTINUES BELOW

Auren Nuriyya yasa ka shi fahimtar abubuwa da dama duk da ba zama yakan yi yai tunani akan hakan ba. Akwai kuma dalilin da yasa akan auren Nuriyyar bayan ta tare Hajja ta kira shi a waya tana ce mishi

‘Soyayya ce take dibarka yanzun AbdulKadir, kuma ita kadai bata isa ta rike aure ba, akwai lokacin da zaku tashi ku duka ku nemi digon soyayyar nan ku rasa, wallahi idan har baku gina zaman ku akan abinda ya girmi soyayya ba, in kuka shiga cikin irin yanayin nan zai muku wahala ku samu dai-dai to. Ba zance maka kacokan zaman aure kan ginu akan halaye bane kawai, amman su din kan zama ginshiqi mai girma na zaman aure. Ga ka ga Nuriyyar nan, itama ga ta ga ka nan, ba baki zan maka ba, amman akwai halayenka da nake da yaqinin Waheedah ce kadai macen da zata iya jurewa’ 3

Bayason ya tsaya tunanin hakanne a baya, dan zai saka tunanin cewa sai da kowa da yake son shi yai mishi magana akan auren Nuriyya din yai biris da su, ko Yasir da ba shiga harkar juna suke ba sai dole sai da yace mishi

‘Da yawan lokutta mukan so abinda ba alkhairin mu bane ba, zaka iya son abu ka rayu babu shi, zaka iya kin abu ka rayu dashi AbdulKadir. Dan kana son yarinyar nan baya nufin in baka aureta ba wani abu zai sameka, da yawan lokutta mukan yi hakuri da abinda muke so dan zaman lafiyar mu’

Shima yai watsi da shi, kashe wayar shi ma yayi. Shisa duk wani karamin abu da Nuriyyar zatai mishi baya daga kai, yasan tunanin maganganun da kowa ya fada mishi kan aurenta ne zai danne shi. Ya kuma tsani kalaman dake biyo bayan dana sani na ‘Sai a wane ko wance suka fadamun ban ji ba’ wani lokuttan kuma sai kaji ana ‘Daman ance mun kaza da kaza’. Duk bayason wannan tunda ba zasu canza abinda ya riga da ya faru ba, shisa yau yake tsaye bakin kofar yana so ya tuna koma menene da zai saka shi yadan sauka daga dokin zuciyar da yake kai, ko da kuwa sharrin shaidan ne, amman azumi akeyi, babu wani shaidan a cikin abinda yake ji sai Nuriyya. Numfashi yaja yana fitar dashi da wani irin bacin rai ya tura kofar, a tsaye ya sameta tana linke hijab. Kan lace din da tayi saurin jefa hijab din sama idanuwan shi ya fara sauka kafin yaji kamar ta watsama wutar da take ci a zuciyar shi galan din fetir.. 1

“Me yasa?”

Ya tambaya muryar shi can kasan makoshi yana kafeta da idanuwa

“Me yasa me?” 4

Nuriyya ta tambaya tana son yin kamar bata fahimci abinda yake nufi din ba, duk da yanayin shigowar shi yasa ta gane yasan ta dibi kudin, ita tabarmar kunya da hauka akan nadeya. Tana bacci ma wayarta ta fara ihu, ta dauka taga Hajiya Kaltume ce tana fada mata yanzun za’a kawo lace din ma, dan ya iso, ta dauka sai dare. Ta karbo kenan ta shigo ta tsaya waya da Asma, ta manta shaf bata kulle kofar ta dauke lace din ba taji shigowar shi, da yasa zuciyarta yin wani irin tsalle, shisa ta jefa hijabin a sama tana fatan Allah yasa baigani ba. Tana kallon yanda yasa hannun shi ya dafe goshin shi yana runtsa idanuwan shi kafin ya sauke hannun yana ware su a kanta.

Sosai yake kokawa da duk wani abu dake zuciyar shi yana tuna mata da in ta manta akwai igiyar aure a tsakanin su da Nuriyya da ta hana mishi dukan ta saiya fitar mata da yanda ko a gaba ba zatai kokarin raina hankalin wani mai suna irin nashi ba, akwai azumi a bakin shi, watan Ramadan ne, wata mai albarka da yake cike da son yafiya da aikata alkhairai. Amman tafin hannun shi har kaikayi yake ya amsa tambayar rainin hankalin da tayi mishi akan kuncinta, marin da sai taga taurari

“Ki tauna maganar da zaki fadamun Nuriyya, Wallahi gab nake da wanka miki mari. Karki gwada wasan banzar ki a kaina yau, ba zai mana dadi ba. Me yasa kika daukar mun kudi?”

Kallon shi Nuriyya tayi tana jin zuciyarta na ci gaba da dokawa, bata taba ganin shi cikin irin wannan yanayin ba, amman a kasan tsoronta akwai yanda maganganun shi suka bata mata rai, taya zaice zai mareta tana matar shi, ita alkawari taiwa kanta daga ranar da namiji zai tabata ya taba auren shi tunda ita ba jaka bace da zai kamata yana duka.

STORY CONTINUES BELOW

“Wai wanne kudi?” 3

Ta tambaya tana karasa kwance sauran hankalin da AbdulKadir yakeji yana rike da kwakwalwar shi ya kuwa dauketa da wani irin mari da yasa tajin kamar idonta daya ya fado, da sauri ta saka hannu ta dafe idon tana lalubawa taji kwayar na cikin shi, wani irin numfashi take ja tana son kukan ya kwace mata ko zai rage mata radadin da takeji, AbdulKadir na kallon ta, wani irin dana sani yake ji yana shirin lullube shi, alkawari yaiwa kan shi da ba zai sake taba wata mace da zata kasance karkashin igiyar auren shi ba, saboda yanda addini ya haramta mishi hakan, yanda al’ada bata yardar mishi da hakan ba, amman Nuriyya ta saka shi ya karya alkawarin nan da azumi a bakin shi. 13

“Na fada miki ki tauna maganar da zaki fadamun baki jini ba, uban me yasa ni da gidana ba zan ajiye kudi inda nake so ba? Me yasa zaki dauka? Me yasa zaki daukar mun? Rashin hankalin ki bai fada miki kudin zai iya kasancewa ba nawa bane? Ban nuna miki salary dina ba Nuriyya?”

Ba sosai take jin maganganun AbdulKadir din ba duk da hargowar da yakeyi kamar kiris yake jira ya rufeta da duka

“Abinda nake miki bai isheki ba sai kin daukar mun kudi? Kin dauka ban san kina zarar mun ba duk idan na ajiye? Ban miki magana bane saboda ina guje mana zuwa inda muke yanzun. Kinsan kudin wa kika dauka? Kinsan kunyar da kika sakani a ciki? Me kike so in ce mishi? Ni na dauki kudin? Ko ke kika dauka? Me yasa zaki mun haka?” 2

Zuwa lokacin radadin da take ji ya fara yin kasa, sai hawayen bakin cikin da suke silalo mata suna busar da tsoron shin da takeji, tunda ba mala’ikan mutuwa bane ba, ta dauka yafi karfin dubu arba’in da biyu da har zai zauna yana mata tijara akan su

“Ni na dauka, saboda na tambayeka ka hanani shisa nagani na dauka, me yasa kai baka fadamun ka ajiye kudin ba? Me yasa kai baka fadamun ba naka bane ba?” 5

Nuriyya ta tambaya cike da tsantsar rashin kunya tana saka wani murmushin takaici kwacema AbdulKadir din

“Akan dubu arba’in da biyune zaka mareni? Ni ba jaka bace da zan zauna kana jibgata” 6

Kai AbdulKadir ya girgiza, idan yana ganinta a gaban shi, idan taci gaba da magana zai daketa saiya ji wani daga cikin kasusuwan ta yayi kara alamar karyewa, zai daketa sai ta kasa ko nishi balle alamar kuka, ballantana ta sami bakin da zata tsaya tana kallon shi cikin idanuwa tana mishi rashin kunya, zai zabar musu abinda zai fi musu sauki, muryar shi a hankali ta fito kamar yana dandana duka kalaman shi

“Kije gida Nuriyya, kije gidan ku ki dan huta, nima in huta” 13

Sheqeqe Nuriyya take kallon shi, tana jin auren shi yau kamar sartse a makoshin ta, bambancin su da Anas na bayyanar mata

“Ni babu inda zanje babu wata shaida, sai inje musu saqaqa ince me? Yaji na yo? Ka sakeni mana sai in tafi da Hujja” 7

Ta karashe maganar tana watsa mishi wani kallo kafin ta dora da

“Ni ba kai bane mijin dana dauka na aura, ba haka Waheedah take fadarka ba, ba haka take nuna ka ba” 3

Da mamaki AbdulKadir yake kallonta

“Kin aureni akan abinda Waheedah take fada ne daman?” 2

Dan sosai yake son ya kwantar da bacin rai ya fahimci maganganunta, amman su kansu tunzura shi sukeyi, ba shi ta aura ba, mijin Waheedah ta aura shine abinda take son fada mishi. 2

“Me zanyi da kai? Wallahi AbdulKadir ba kai bane mijin da nake burin aure, kudinka da halayenka basuyi mun ba, ba zan iya zama da kai da wannan bakaken halayen ba” 12

Nuriyya ta karasa maganar tana jin zugin da kuncinta yake na marinta da yayi, garama ya saukake mata auren shi, Asma tace mata da kyawunta ta zauna namiji na wahalar da ita, kuma gaskiya ne, in yau ta gama iddarta tana da tabbacin samarine zasu dinga mata layi. Numfashi AbdulKadir yake ja yana fitarwa idan taci gaba da magana tabbas zai datse igiyar dake tsakanin su, maganganun da take fada din na kara tunzura shi sosai da sosai, dan bai kara sanin yanda zuciyar shi take doka mata ba sai yanzun da take fada mishi maganganun da yasa shi jin kamar ita din bata taba son shi ba. Abinda take tunanin auren shi zai samar mata shi take so. Abinda taga kamar auren shine ya samarwa Waheedah shi ta biyo. 4

STORY CONTINUES BELOW

Lokutta da dama kuma ba mata kawai ba, har maza na wannan wautar, ba a karin mata ta biyu ba maza kanyi kuskuren nan, a ta farkon ma, da yawa kan dauka auren wata mace shine cikar farin ciki, idan har baka da farin cikin da kaine silar samarwa kanka shi, cikar shi zatayi maka wahala idan wani ya zama sanadin farin cikin ka, ko da zama na yau da gobe bai taba wannan farin cikin naku ba, rabuwa ta kaddarar rayuwa ko mutuwa kan iya giftawa, sai kayi yaya? Aure kan samar da farin ciki, amman baya nufin duka farin cikin naka zai zamana a zagaye da shi auren. Mata sunfi kowa yin wautar nan, musamman a zamanin da muka tsinci kan mu a ciki. 7

Zamanin da yasa idan mace ta samu jinkirin auren da ba laifinta bane za’a dameta da yawan surutai har ya sata jin yin auren ne kawai hanya daya ta samun farin ciki, a wasu lokuttan kuma idan yarinya bata tashi cikin wadata ba, bata kuma da wadatar zuciya sai ta dora ginshiqin aurenta da samun farin ciki akan auren mai kudi, wasu kuma hange-gange shine yake halakar dasu, kinga mace cikin rufin asiri, kinganta daga sama da mijinta suna cin me kyau su sha me kyau, sai wannan kyallin ya haska miki shi, sai kiga kamar ta samu duk wani abu da shine burinki a zaman aure.

Bakisan yanda zaman aurenta yake tare da mijinta ba, bakisan me take jurewa ba, bakisan shima me yake jurewa a zama da ita ba, zamantakewa ta tsakanin ma’aurata sirrine da yake a lullube, abinda idanuwanki suka gani baya nufi shine komai, zai iya yiwuwa mijin wadda kika kyalla idanuwanki a kai bashi bane abinda burinki yake bukata. Karki so mutum dan abinda kike tunanin kin ga matar shi ta samu a tare dashi, ko da zatonki ya zama gaskiya ba kida tabbas ke zaki samu irin wannan a tare dashi. Duk da wasu matan ma na da laifin ganin mijin su nasu ne su kadai, wasu kance ‘Ta auri mijin wata’. Dan kawai ta shiga a ta biyu. 3

Babu wani abu mijin wata daga lokacin da musulunci ya halarta karin uku bayan ke tun kafin wanzuwarki, mijinki nata ne itama. Wahalhalu da yawa mutane su suke dorama kan su ita, kwanciyar hankali baya zuwa idan baka neme shi ba. AbdulKadir ko kadan bai zaci ta aure shi da wata manufa da ta wuce ta son zama dashi kamar yanda yake son zama da ita ba, shisa ya juya yana ficewa daga dakin. Takawa yake dan ya fita daga gidan ya tafi wani waje, koma ina ne inda ba zaiga Nuriyya na wani lokaci ba kafin ta tunzura shi ya yanke musu hukuncin da su duka ba zai musu dadi ba. 1

Amman sai ta biyo shi, a falon Waheedah ta sake shi zai wuce ta gaban kitchen din shi tana kama mishi riga ta janyo shi saida ya juyo

“Nuriyyaa”

Ya sake kira cikin wani sabon kashedin, Waheedah taji takun tafiyar shi tun kafin ya fito, ta kuma ji muryar su dan tana hango kafar shi guda daya, da yake kujera ta saka ta zauna a kitchen din ta jingina bayanta da lokar kitchen din ta dora roba kan cinyarta tana gurza kubewa

“Ka dawo ka saukake mun wannan kaddararren naka, dan Wallahi ba zanje gidanmu babu wata shaida ba, ni dama nagaji da zama da kai…” 1

Numfashi AbdulKadir ya sauke ya kama hannunta yana banbarewa daga rigar shi yana fadin

“Kin gaji da zama dani right? Ki jirani Nuriyya, duk mu huta da rashin albarkar da take bin mu” 3

AbdulKadir ya karasa dan shi kan shi yanajin yagaji da bala’in nan, yanzun nan kuma yanajin rashin albarkar iyaye ce take bibiyar shi shisa a kasa da sati biyu komai ya jagule musu shida Nuriyyar, shima a gajiyen yake jin shi, maganganun kowa da suka fada mishi sun tabbata, hankalin su ya kwanta, sai su kalli idanuwan shi suyi mishi dariya su fada mishi da yaji maganar su daga farko da baizo inda yake ba yanzun. Dakin Waheedah ya wuce, Nuriyya na tsaye bakin kofar kitchen din Waheedah din tana girgije-girgije, ta wutsiyar ido Waheedah ta ganta, ko dagowa batayi ba, kubewarta take gurzawa a hankali tana bin karatun daya shigo na Suratul-Mulk cikin muryar Qari Sheikh Ghamdi da ke nutsar da abubuwan da batasan a tashe suke a tattare da ita ba.

Bata kalle su bane saboda basu bane a gabanta, saboda fadansu bai shafeta ba, asalima bata da alaka da shi. Nuriyya na nan tsaye AbdulKadir ya dawo da takarda a hannun shi, dayan da biro rike, fuskar shi kawai zaka kalla kasan ran shi a matuqar bace yake 1

STORY CONTINUES BELOW

“Gashi nan, na sake ki saki daya” 8

Runtsa idanuwan ta Waheedah tayi tana jiran taji ko zata girgiza tare da abinda ya girgiza daga kalaman sakin aure da AbdulKadir ya furta, asalima tana bude idanuwanta ji tayi kamar tare da sakin Nuriyyar ya dauke mata wani katon dutse daga saman kai. Nuriyya kuwa bata karbi takardar ba, kallon AbdulKadir din takeyi bata son sake hada wata hanya dashi ko ta wasa ce, wani auren zatayi na mai kudi inda ba za’ai mata tijara kan dubu arba’in da biyu ba

“Daka haifu cikin Hajja da ka karashe biyun ai, kaga duk sai ka hutar damu” 18

Sosai AbdulKadir yake kallon ta, a duniya babu wanda ya taba zagin shi haka, babu wanda ya taba kallon shi ya zage shi haka, saki daya ko uku, har a bayan zuciyar shi yanajin kamar yanda ya nuna babu wanda ya isa ya hana shi lokacin daya aureta, sai wata kaddarar da baiyi fata ba, haka yakejin yanzun ma babu wanda ya isa ya saka shi sake zaman aure da ita ko da su kadai suka rage a fadin duniya, saboda bayason gauraya yaran shi da matar da ta fada mishi maganganun da Nuriyya ta fada mishi. Takardar ya yaga yana komawa cikin dakin, ko mintina biyu baiyi ba ya fito da duka littafin a hannun shi yana dago kafar shi daya ya dora littafin a jiki yai rubutu ya yago ya mika mata.

“Na sake ki saki uku…na saukake miki gabaki daya kaddararren aurena Nuriyya” 17

AbdulKadir din ya karashe yana mika mata takardar da ta karba ta linke batajin digon dana sani ko daya, asalima wani irin sakat taji ta, tana kallon shi ya ajiye takardar da biron akan kujera ya taka ya fice daga gidan, ta dauke idanuwanta daga kan kofar tana kallon kitchen inda Waheedah take gurza kubewa kamar bata da wata damuwa a duniya, sai Nuriyyar taji shine abinda yai mata tsaye a makoshi, yanda Waheedah take nuna kamar bata da wata damuwa a duniya 2

“Zaki iya nuna farin cikin ki, ga mijinki nan nabar miki sai ki jika kisha” 5

Nuriyya ta fadi da wani malolon bakin ciki daya taso ya danne mata zuciya, amman inda take ma Waheedah bata kalla ba 1

“Banza wawiya kawai” 7

Ta kara fadi tana jan wani irin tsaki ta wuce ciki dan ta hada akwatunanta. Waheedah bata kulata bane duk yanda zuciyarta take tunzurata da tayi hakan, ta fada mata maganganu, ta gaya mata yanda ta ture amintar su ta aure mata miji, ta zageta kamar yanda take so, amman azumi takeyi, ita ko bata azumi ma batajin akwai wasu maganganu da Nuriyya zata fada mata da zai tunzurata kuma, babu wani abi a tattare da ita da zai bata mamaki, daga ranar da ta iya auren AbdulKadir bata kara bata mamaki ba. Taji maganganun Abba da yace mata karta taba bari bakin halin mutane ya canza kyakkyawar dabi’arta, ko jiya ta karajin wa’azin Mufti Menk akan mu’amala da mutane. 3

Sai dai wani lokacin zuciya bata da kashi, mutane basu da kirki, babu uzuri a cikin lamurran su, kai sai suyita maka rashin arziqi, idan ka ware rana daya kai magana akan hakan sai ace da hakuri aka sanka, ba’a tunanin yanda akwai zuciya a kirjinka kaima, babu wanda zai maka uzurin cewa kaima din fa dan adam ne kamar kowa, amman kai mutane sai su saka ransu a cewar yi musu uzuri ya zame maka dole. Yanzun dai ta zabi kin kula Nuriyya dinne, daga yau zata fara addu’ar yanda ta fita daga rayuwar su, ko a hanya kar kaddara ta sake hadasu da ita, mikewa tayi da kubewar da ta gama gurzawa tana ajiyeta ta share wajen ta wanke hannuwan ta, sai take jin iskar da take shaka ma daban take dirar mata. 1

Nuriyya kuwa data wuce daki ta sauko akwatinan ta ta fara hada kayanta, harda ghana must go ta zuba takalmanta da jakunkunanta a ciki. Sai da tagama hada kayan tsaf ta dauki hijab ta saka tukunna ta fita daga gidan, bakin hanya taje ta taro mai napep ta dawo, ta kula da kitchen din Waheedah din a kulle yake kamar bata ciki, munafukar ta fadi a ranta. Akwatinan ta dinga janyowa tana fitowa dasu tana loda wa mai napep din da ta ajiye a kofar gida, har maigadi yayi kokarin tayata fita da akwatin data fara fitowa dashi 1

“Na rokeka ne? Banason tsinanniyar gulma da bakin munafunci kamar baka gane sakina akayi zan bar gidan ba” 10

Cewar Nuriyya tana saka shi ya koma inda yake ya zauna, haka ta dinga fitowa da kayan tana dirka nishi, kayan kitchen dinta tazo da akori kura ta kwashe abinta dan ba barinsu zatayi ba, ko siyarwa tayi tai amfani da kudin, wani sama-sama take jin kanta da take alaqantawa da nishin da take saboda fito da kayan. Komawa ciki tayi dan ta dauko karamar jakarta. Tana daukowa ta fito ta ga wayam, babu mai napep babu alamar shi, rasa inda zata nufa tayi, titin haggu ko na dama, dawowa tayi tana turo kofar muryarta a karye take kallon mai gadin 30

“Dan Allah kaga inda mai napep din nan ya nufa?”

Wani irin kallo yake mata, daman kayan da zai tayata dauka dan ya zata matar gidance har lokacin, ba hurumin shi bane tsoma baki a al’amuran gidan AbdulKadir din, amman har ranshi ya tsani Nuriyya, saboda yasha ganinta ita da Waheedah din idan tazo gidan ta rakota, lokaci daya yaga ta shigo gidan a matsayin matar gidan, ko ba’a fada mishi ba yasan auren cin amana ne akayi, ga ta da wulakanci kuma, sai ya gaisheta ta watsa mai mugun kallo tana amsawa dakyar, ga aiken rashin daraja da take mishi. 3

“Tsinanniyar gulma da bakin munafunci bai barni na ga inda yai ba” 36

Kallon maigadin tayi hawayen bakin ciki na tarar mata a ido, kafin ya tura kofar har yana bige mata yatsun da take yarfewa dan azaba. Hawayenta na samun damar zubowa, gabaki daya sutturarta ce ya tattara yai gaba da ita, karyarta da mutuncin da take shiga kawaye na ganinta dashi duk ta silar kayan ce. Sai yanzun wani abu kamar guduma ya dakar mata tsakiyar kai,da asalin abinda barinta gidan AbdulKadir din zai haifar, ina zataje yanzun, bata manta kashedin da Baba yai mata ba, duk da watannin nan idan taje gida ta gaishe dashi yakan amsata babu yabo babu fallasa, ta ina zata fara? 5

“Na shiga uku na” 59

Ta fadi wasu sababbin hawayen na zubo mata…Baisan inda zai nufa ba, da duk dakika da yanda zuciyar shi take kara mishi zafi. Tsintar kan shi yayi a kofar gidan su. Aka bude mishi ya shiga da motar shi ciki, kan shi tsaye bangaren Hajja ya nufa, ya shiga babu ko sallama. Fajr da ya rugo ya rike mishi kafafuwa ya kama yana daga yaron cik ya sauke shi a gefe tare da fadin +

“Fajr kabarni nikam, ina Hajja?”

Shagwabe mishi fuska Fajr yayi

“Tana bacci”

Kai AbdulKadir ya jinjina ma Fajr din yana wucewa yabar shi a wajen. Dakin Hajja ya nufa ya kwankwasa, cigaba yayi har saida yaji muryarta dake cike da bacci ta amsa shi, tukunna ya tura dakin yana shiga. Kallo daya tayi mishi tagane a hargitse yake 1

“AbdulKadir…”

Ta kira cike da damuwa tana dorawa da

“Lafiyar ka?”

Kai AbdulKadir ya girgiza mata yana kallon ta kamar zai fashe da kuka, yanayin da yasa Hajja mikewa zaune.

“Me ya faru?”

Tsayen dai yake yana kara kankance mata idanuwan shi

“Kai mun magana mana AbdulKadir”

Takawa yayi ya zauna kasa yana dora kan shi akan kafar Hajjan kamar karamin yaro

“Hajja nayi kuskure…. Na sake biyewa zuciyata nayi kuskure babba”

Cikin tashin hankali Hajja tace

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…me kai ma Waheedahr kuma?”

Kai AbdulKadir ya girgiza mata

“Ba Waheedah bace ba, na saki Nuriyya…Hajja na saketa”

Numfashi Hajja ta sauke, duk da saki ba abin so bane, musamman ita mace data fahimci abinda hakan yake nufi. Amman zatai karya in tace bataji wani sanyi a kasan zuciyarta da tasan ba Waheedah bace ba. Tayi iya kokarin ta na ganin ta bata kasance cikin irin iyayen mijin dake daukar tsana ta babu gaira babu dalili sun dora akan matan yaran su ba, amman sam zuciyarta ta kasa aminta da auren AbdulKadir din da Nuriyya. Ko kadan bata son yarinyar, hakan dai ba zai hanata fada mishi gaskiya ba

“Subhanallah, me ya faru AbdulKadir? Cikin azumin nan? Yanzun ita tana ina?”

Kan shi ya kara kwantarwa a jikin cinyarta, kirjin shi zafi yake kamar ana hura mishi wuta. Maganganun Nuriyya sun ruguza wani abu a cikin zuciyar shi da baima san dashi ba. Komai yai mishi tsaye, ya kasa yarda cewar ya saketa din, duk da ko ba gabaki daya ya datse igiyoyin auren su ba, ta fada mishi maganganun da yake da tabbacin alaqarsu ta samu tangarda ta har abada, badai zai hana zuciyarshi jin zafin abinda ya faru ba.

“Bata so na, abinda aurena zai iya bata shi take so”

Ya furta muryar shi na fitowa da wani irin yanayi da yasa Hajja runtsa idanuwanta tana sake bude su

“Wannan kawai bai isa zama dalili ba”

Dago kai yayi yana kallon Hajja, kafadun shi yadan daga mata

“Na riga nayi, na saketa, saki uku Hajja, dalili ko babu dalili ba zai canza hakan ba”

Wannan karin ware idanuwanta Hajja tayi

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…. AbdulKadir saki uku? Idan Allah ya jarabceka da son ta kuma fa?”

Ta karasa maganar hankalinta a tashe, dan sam abin bai mata dadi ba, kome ya faru kuwa, duk yanda bata son shi da Nuriyyar. Murmushi yayi me sauti yana dan dafe kan shi da yake sarawa kafin ya sauke hannun shi yana kankance idanuwan shi akan Hajja, wanne soyayya kuma banda wadda yai mata tasa kafafuwa ta ture, itace mace ta farko da zuciyar shi ta fara dokawa, ita ce mace ta farko da ya fara tunanin zaman aure da ita.

STORY CONTINUES BELOW

Ba yajin akwai wata jarabta ta bangaren soyayyar Nuriyya da zai same shi ya bashi mamaki. Itace macen da yaso, sai dai ba ita bace macen da ta dace dashi. Yanda zaka so abu ya zamana ba alkhairinka bane bazai daina bashi mamaki ba. Inda yasan hakan zai faru, da yana da ilimin sanin abinda gobe zata haifar ba zai soma auren Nuriyya ba, ciwon da zaiji na hakan ba zai taba kai wanda yakeji yanzun ba. 1

“Magana nake maka fa”

Hajja tace tana saka AbdulKadir din mikewa tsaye

“Hajja ni kirjina ciwo yake mun, dan Allah kiyi hakuri…”

Ya karasa maganar yana zagayawa ya mika hannu ya dauko pillow daya daga kan gadon ta yana jefa shi a kasa. Sai daya cire takalman kafafuwa shi tukunna Hajja ta kula da su. Sabon shine shiga ko ina da takalma tun yana da karancin shekaru, bakinta har ya gaji da magana kan hakan. Yanzun ma da idanuwa take bin shi harya zauna kan kafet din dakin nata ya gyara pillow din shi ya kwanta

“AbdulKadir…”

Ta kira

“Hajja kunyar Hamma nake ji shisa nazo wajen ki…Allah zan tafi in baki barni ba” 3

Mikewa tayi, ta riga da tasan halin AbdulKadir din, duk da alamu sun nuna yana cikin hali, in ba da kanshi yake son yin maganar ba bazai yi ba. Yana jinta ta fice daga dakin, gyara kwanciyar shi yayi yana lumshe idanuwan shi ko kirjin shi zai rage zafin da yakeyi. Bacci yayi har la’asar, har yaje masallaci ya dawo yanajin kirjin shi bai daina zafi ba. Dakin Hajja ya sake komawa yai kwanciyar shi. Tana shigowa tagan shi tace

“Wai kai AbdulKadir ba zaka tashi ka tafi gidan ka ba?”

Sake juya kwanciya yayi

“Yanzun Hajja dan nayi aure shikenan bazan zo gida duk sanda nake so in kwanta in huta ba?”

Ya karashe maganar kamar zaiyi kuka, dan baiga dalilin da zaisa Hajja ta dinga korar shi shida gidan Abban shi ba, amman da Waheedah tazo babu wanda yace ta koma sai da yazo ya dinga binta yana bata hakuri

“Idan kuma yaji nayo fa? Sai ki koreni kice in koma?” 6

Dariya Hajja take da AbdulKadir din baiga dalilinta ba, dan shi da dukkan gaskiyar shi yake maganar da yakeyi din.

“Allah ya shiryamun kai AbdulKadir”

Hajja ta fadi har lokacin tana dariya ta fice daga dakin, sai da yagaji da kwanciyar tukunna ya fito zuwa falon yana zama Fajr na shigowa da nama a hannun shi yanaci

“Paapi kaga, Mami tabani”

Ya karasa maganar yana zuwa ya zauna a jikin AbdulKadir din

“Mami ta kyauta, ka gode”

Sake shigewa jikin AbdulKadir din Fajr yayi yana kwanciya sosai, yana sa AbdulKadir din fadin

“Kaifa ka cika son jiki Fajr, baka azumi zaka bini ka danne”

Baisan inda yaron ya koyi son jiki ba, gashi dan mitsitsi dashi abinda yake so shi zaiyi, maganar shi ba zata sa Fajr din ya sauka daga jikin shi ba, sai dai in dukan shi zaiyi. Amman wani ido ko magana ba ko yaushe suke tasiri akan Fajr ba, baisan inda ya kwaso halayen nan ba, dan shi ba haka yake ba. Anan ya zauna har aka kira sallah, dabino da kankana ya dan sha yayi alwala, Fajr na rigimar sai ya bishi 4

“Ka tafi dashi mana”

Cewar Hajja

“Baiga takalmin shi daya ba, har anyi raka’a daya”

AbdulKadir ya fadi yana zame hannun Fajr din daga cikin nashi, yaron na bude baki ya fara kuka, wani irin mari Abdul ya dauke shi dashi da yasa Hajja fitowa daga kitchen ta kama Fajr din

STORY CONTINUES BELOW

“AbdulKadir baka da hankali? Wannan ai sai ka ji mishi ciwo” 1

Ta karasa tana daukar Fajr da jikin shi ko ina ke bari, yama kasa fitar da sautin kuka. Ficewa daga gidan AbdulKadir yayi dan baida amsar ba Hajja, bayason kukan banza marar dalili, Fajr ya cika rigima har ta banza, inda Hajja tasan dukan da yake sha da ba zatai magana dan ya mare shi ba. Daya dawo masallaci ma ruwan shayi kawai ya iya sha, dan ko yunwar ma bayaji, tukunna yaima Hajja sallama ya sake ficewa ya shiga motar shi yana nufar gida. 1

*

Ba zatace ga iya lokacin da ta dauka a kofar gidan ba, zafin ranar da ake kwallawa shi yasa ta yanke hukuncin takawa zuwa bakin hanya ta tare wata napep din ta shiga zuwa gidan su. Lokaci zuwa lokaci take saka hannu tana share kwallar dake zubo mata. Bayan kayanta da aka gudu dasu, tasan akwai wani abin da yake nuqurqusarta da bata son tsawaita tunani a kai. Dari biyu ta ba mai adaidaita sahun tana wucewa ta shiga gida da sallamar da Mama ta amsa mata. Tana zaune kan kujera a kofar daki tana tsintar shinkafa.

“Ki dauko tabarma mana”

Mama tace mata ganin Nuriyya din na shirin zama kasa kan siminti, batayi musu ba ta shiga daki ta dauko tabarma tazo ta shimfida. Gaisawa sukayi, Mama taci gaba da tsintar shinkafarta batare da ta ko kalli inda Nuriyyar take ba, ballantana kuma tace mata wani abu. Gabaki daya jikinta Nuriyya taji ya kara mutuwa, wasu sabbin hawayen na kara zubo mata da ba zatace ga dalilinsu ba.

“Mama ya sakeni, AbdulKadir ya sakeni”

Ta furta wani abu na tasowa daga dan yatsan kafarta yana zuwa kirjinta ya samu wajen zama. Sosai yanzun abinda hakan yake nufi ke zauna mata, ga yunwar azumin dake bakinta data fara kulle mata ciki, ga shinkafar da taga Mamar na tsinta ta kuma tabbar da ita dince abincin buda bakinsu, sai dan kunu da kosai da ba kullum ake samu ba. Da yanzun tana daki a kwance da fanka in sun kawo wuta, komin ta lalace kuma akwai nama a fridge dinta, ko soyawa zata iya yi. Watanta kusan tara rabonta da shinkafar hausa. 3

“Allah ya rufa asiri ya kyauta” 1

Mama ta fadi tana mikewa da farantinta takai dan karamin kitchen din gidan ta ajiye. Itacen ta iza tana bude waken taga ko alamar dahuwa baiyi ba, shisa ta dora shi da wuri inta dafa saita ajiye. Anjima ruwa zata kara daya tafaso ta zuba shinkafa. Badan tayiwa auren Nuriyya da AbdulKadir din baki ba, amman har a kasan ranta taji alamun babu inda zaije, ko badan auren cin amana bane, Nuriyya na da son zuciya da son abin duniya da in batai wasa ba zai hanata zaman aure, dan zata cigaba da gina aurenta akan hakan, duk namijin daya gane kuwa da wahalar gaske yaci gaba da zama da ita.

Hidimarta Mama ta karasa ta shige daki tana barin Nuriyya anan zaune, ganin hakan yasa itama ta tashi tana komawa dakinta na da, yana nan yanda yake babu abinda ya canza, banda yan kayan sawa da aka ajiye. Ta kuma san na Mama ne, tunda ita bata da yara mata, nata duk mazane, dakin su kuma daban yake. Jakarta ta ajiye ta samu waje kan katifa tana kwanciya, a jikinta take jin banbancin katifar da ta gidan AbdulKadir. Wasu sabbin hawayen na sake silalo mata, musamman da tunanin Waheedah nacan kwance a daki tana jin dadin tabar mata gidan, sai taji wani malolon bakin ciki ya taso mata kamar zata hadiyi zuciya ta mutu ta huta. 7

Kafin yamma wani zazzabin tashin hankali ya rufe ta, banda tsinuwa da fatan tifa ta take mai napep din da yai mata dibar albarka babu abinda takeyi. Ga kuma tashin hankalin abinda zai faru idan Baba ya dawo gidan ya ganta, dan sosai kashedin shi yake dawo mata. Ita kam bataga inda zata fara zuwa ba a yanzun, bata da wani waje daya wuce nan din, haka ta wuni juye-juye. Ta kulla ta saka, hadi da addu’o’i kala-kala, cikin su harda na samun mijin da yafi AbdulKadir komai tana gama iddarta tayi aure inda zata huta ta shakata, amman tasan hakan bazai yiwu babu suttura ba. Ta yanke hukuncin siyar da duka kayan kitchen dinta, ta siyi kaya saita ajiye sauran kudin tana kashewa a hankali kafin ta samu garan da zata wanka.

STORY CONTINUES BELOW

Wannan tunanin shiya nutsar da ita har aka kira sallar Magriba, tukunna ta fito daga dakin tayi alwala tana sake komawa, sanda ta idar da sallah, Mama ta kawo mata kunu da kosai da taketa jin kamshin shi tana kwance, hakan ya tabbatar mata da ba siyowa akayi ba, Mama ta soya da kanta. Ci tayi dan ya mata dadi sosai, rabon da taci abu mai nutsuwar wannan tun girkin Waheedah. Tas ta shanye kunun ma da yasha kayan kamshi ta samu waje ta zauna, wata nutsuwa da koshine kadai ke samar da ita na saukar mata.

Tanajin sallamar Baba taji hanjin cikinta ya hautsina, komai ya tsaya mata. Tashi zaune tayi, daman dakin fitilar wayarta ce ta haska, itama kashewa tayi, tai zaune cikin duhun tanajin zazzabinta ya dawo sabo. Ba zatace ga iya lokacin da ta dauka a dakin ba kafin taji Baba na fadin

“Auren ta kaso? Shine kika barta ta zauna mun a gida? Ban gaya mata ta nemi wani wajen ba?”

Baba ya karasa maganar yana daga labulen dakin da Nuriyyar take ciki

“Fito….aina fada miki idan kika kaso auren nan ki nemi wani wajen, na fada miki bazan kaffarar rantsuwa ta ba”

Wani irin kuka Nuriyya take tunda Baba ya fara magana. Mama ce ta kama labulen daga hannun shi tana saukewa da fadin

“Aikam hakuri zakayi kai azumin kaffara saboda babu inda zataje” 1

Da matukar mamaki Baba yake kallon Mama, kai ta daga mishi, dan sosai iyaye suke wannan kuskuren, tasan bacin rai abune da ba’a iya guje mishi idan yazo. Amman bataga dalilin da zaisa iyaye su gindaya sharadi kan cewar idan yara suka tsallake su nemi wasu iyayen ko kuma su bar musu gida ba. Akwai dalilin da yasa Allah ya zabi ya basu amanar yaran, batace babu hakkin iyaye akan yaransu ba, amman akwai hakkin yara akan iyaye suma. Amana ce mai wahalar rikewa, amana ce da rikonta yake cike da kalubale kala-kala.

Amman korar yara daga gida da nufin son su gane kuskurensu ba hanyar gyara bace ba, lokutta da dama hakan baya janyo komai banda kara lalacewar su, ga fushin iyaye da ko basu koresu ba zaici gaba da bibiyarsu har sai lokacin da suka furta sun yafe ko suka kudurta a ransu, ga tangaririya a filin duniya batare da tudun dafawa ba. Ba mata kadai hakan yake faruwa dasu ba, har mazan, da yawa in basu fada sace-sace dan su sami abin ciyar da kansu ba, zasu fara shaye-shaye dan rage damuwa, da duk wani abinki da zai iya fin wanda yai sanadin korar su daga gida muni. Akwai kaddarar da take tafiya da son zuciya, kamar ta Nuriyya, halin da take ciki laifinta ne, amman hakan baya nufin ba kaddararta bace ba. 4

Da yawan mutanen da zasu zageta idan sunji halayenta marassa kyau su kansu basu wuce jaranta da irin kaddararta ba, bata saka musu baki a cikin al’amuran su, amman tana da yara, duk da maza ne, ba za’a hadu da ita ayi wannan kuskuren da Baba yake shirin yi ba

“Ina kake so taje? Idan tabar gidan nan ina kake so taje? Bazan maka magana akan cewa hannunka baya rubewa ka yanke ka yarda ba, saboda ban taba yarda da wannan kalaman ba, lokacin da azaba zata isheka, idan baka roki wani ya yanke maka ba, zaka sami wuka ka yanke da kanka, neman sauki abune mai ban mamaki”

Cewar Mama tana dorawa da

“Amman nasan yara amana ne a wajen iyayen su, nasan idan tasa kafa ta fita daga gidan nan ka gaza a rikon wannan amanar. Ban taba saka maka baki akan Nuriyya ba, yaune na farko saboda yau dinne nake ganin zakayi kuskure mai girma, in kuma ina da wani muhimmanci a wajenka zaka hakura kabarta tunda ba tada inda yafi nan din, babu kuma wanda ya wuce kaddara dagani har kai”

Jim Baba yayi yana tattauna maganganun Mama din, zuciyar shi na tafasa sosai, amman yasan gaskiya ce ta fada mishi. Babu inda Nuriyya take dashi da zataje, bakuma zai kyauta ma mahafiyarta ba, dan sunyi zaman da baya manta ta a duk daga hannuwan shi da zaiyi dan gabatar da addu’a. Wucewa yayi dakin batare da yace komai ba sai addu’ar neman shiriya da yake ma Nuriyyar a ran shi. Numfashi Mama ta sauke tana daga labulen tare da fadin

STORY CONTINUES BELOW

“Inya huce kije ki same shi ki bashi hakuri, sai a kira AbdulKadir din aji idan abinda zai gyaru ne”

Hawayen fuskarta Nuriyya ta share tana girgizawa Mama kai.

“Saki uku ne”

Labulen Mama ta saki tana girgiza kanta kawai. Addu’a ce kawai abinda ya rage tsakaninta da Nuriyya, alwalar isha’i ta daura ta shige daki kawai. Nuriyya kuwa kwanciya tayi, batafi mintina goma ba aka kawo wuta. Cajin wayarta ta saka ta fito tsakar gida ta wanke fuskarta ta koma tayi sallar isha’i. Sai take jin tadan samu natsuwa yanzun da tasan babu inda zataje. Baba bazai koreta ba, zata samu tasan yanda zatayi ta kwaso kayanta ta siyar dasu, dan batason shigowa da komai gidan sai kudinta da kayan sawa.

Lambar wayar telanta ta laluba tai mishi magana ta whatapp dan akwai kayanta wajen kala biyar da zai kai mata gida washegari, tayi mishi kwatancen nan gidan tace ya kawo mata, su zata samu tadanyi amfani dasu kafin taje ta kwashe kayanta ta siyar ta siyi wasu na kece raini. Ta kuma yanke hukuncin Asma ce kadai zata san aurenta ya mutu, itama dan ta tayata siyar da kayan kitchen dinne, sauran saita samu mijin da zasu girgiza da jin shi tukunna zata sanar dasu dan suzo biki. Biki zatayi na alfarma ba irin na AbdulKadir da akai tayi mata tsegumin ko yar walima batayi ba. Da wannan tunanin na sabuwar rayuwar da zatayi bacci mai karfi yai awan gaba da ita. 3

*

Yana shiga gida ya hango Yassar tsaye da waya a hannun shi yana dannawa, parking yayi ya fito daga motar

“Kai nake shirin kira, Waheedah tace mun ka fita tun dazun baka dawo ba…kar in sake ina maka magana kana kama hanya ka wuce, dan ubanka kasan yanda ka dagamun hankali? Yanzun ma machine na hau nazo”

Juya mishi idanuwa AbdulKadir yayi

“Na sha ruwa lafiya… Kai fa?” 3

Ya fadi yana saka Yassar din watsa mishi wani kallo

“Bana son iskancin banza… Me ya faru?”

Numfashi AbdulKadir yaja yana fitarwa, hadi da jingina bayan shi da motar shi, sosai yake jin kunyar Yassar din, muryar shi can kasan makoshi yace

“Dan Allah Hamma kayi hakuri, tun dazun naso inje amman kunyarka nakeji shisa na kasa zuwa…. Wallahi kunyarka nakeji har yanzun… Dan Allah kayi hakuri”

Kai Yassar yake girgiza mishi tunda ya fara magana, in duka kudin AbdulKadir ya kashe zai hakura da sake motar, idan fiye da hakan yake bukata zai siyar da motar ya bashi duka kudin, yafi karfin wani dukiya a wajen shi, ballantana dubu arba’in da biyu, shi ya biyo bayan shine saboda yaga yanayin bacin ran daya shiga

“Dan Allah ka daina wannan maganar AbdulKadir, kasan kafi karfin wannan kudin a wajena”

Kai AbdulKadir ya jinjina

“Nasani,amman ajiya kabani saboda baka son taba kudin”

AbdulKadir ya karasa yana kallon Yassar din

“Nikam kabar maganar kudin nan, kayi zuru-zuru, duk azumin ne?”

Kai AbdulKadir ya girgiza ma Yassar din

“Banajin dadi Hamma, kirjina ciwo yake mun”

Cike da damuwa Yassar yace

“Ko zamu koma asibitin ne? Kaga shisa suka so ka kwana rannan dan suga yanayin jikin, kuma baka shan magungunan ko?”

Numfashi AbdulKadir ya sake saukewa, kafin ya sauke muryar shi yana fadin

“Na saki Nuriyya… Saki uku”

Cike da rashin fahimta Yassar yake kallon shi dan kamar daga sama haka yaji maganar

STORY CONTINUES BELOW

“Bangane ka saketa saki uku ba, baka da hankali ne kai? Ina tunanin ka ya tafi? Rashin hankalin naka har yakai haka”

Kai AbdulKadir yake girgiza mishi

“Baka san me tayi mun ba Hamma, baka tambayi me tayi mun ba, kar kaimun fada bakaji duka abinda ya faru ba”

Sosai Yassar yake kallon AbdulKadir din, sam baiji dadin jin maganar ba, badan yana son Nuriyya ba, sai dan saki abune mai girman gaske

“Koma me tayi maka, shisa addini ya bada maslaha akan ka fita kabar mata gidan idan kaga zata tunzuraka, karka yanke hukunci sai ka samu nutsuwa ka sauka daga fushin daka dauka. Macece ita, ba ko yaushe take da hankali ba, komai ya fito daga bakinta fada maka zatayi”

Shiru AbdulKadir yayi, dan maganganun Yassar din ciwon da yakeji suke kara mishi, cikin taushin murya Yassar yaci gaba da fadin

“Nikam sam banji dadi ba, kuma baka kyauta mun ba Wallahi, na dauka munyi magana ta fahimta akan wannan zuciyar taka da rashin neman shawara”

Wani abu AbdulKadir ya hadiye da yai mishi tsaye a wuya

“Kayi hakuri”

Ya fadi yana sa Yassar din kallon shi, yanayin AbdulKadir din na karya mishi zuciya, da kaga alamun shi kasan yana cikin jimamin rabuwa da Nuriyya din, amman kaddarar suce tazo da haka. Da yawan lokutta mutane biyu kan hadu dan su koyar da juna wani darasi kafin kaddara ta raba hanyar su, hakan ne abinda ya faru da zaman AbdulKadir din da Nuriyya 1

“Allah yasa hakan shine mafi alkhairi”

Cewar Yassar yana dorawa da

“Karka saka damuwa sosai a ranka, babu wanda yake wuce kaddarar shi, yin aure da mutuwar shi lokaci gare su, Allah bai nufi zamanku zai tsawaita ba”

Kai AbdulKadir din ya jinjina

“Hakane Hamma… Nagode”

Sallama Yassar din yai mishi, babu yanda baiyi da ya sauke shi gida ba, amman yaki, cayai yaje ya kwanta ya huta, yana bukatar ya samu wadataccen hutu. Bai wani ja maganar ba, dan kan shi ciwo yake sosai, har bakin kofa dai ya raka Yassar din tukunna ya dawo yana shiga gida da sallama. Baiga Waheedah a falo ba, hakan yasa shi ya wuce cikin daki ya sameta a kwance. Kan gadon ya karasa ya dauki Imaan dake bacci yana sauketa kasa kan nata gadon, ya matsa sosai ya rungume Waheedah ta baya yana sauke wani irin numfashi da baisan yana rike da shi ba.

Hannunta ta dora kan nashi dake cikinta, tana lumshe idanuwanta, tana jin yanda zuciyarta ke bude mata duk wata kofa da ta taba son shi hadi da dokawa da karfin gaske, tana jin yanayin kaunar shi da kusancin shi da ita hakane kawai yake haifar da ita, tana jin yanda tayi kewar yanayin sosai.

“Sadauki”

Ta furta cikin yanayin daya manta rabon da yaji ta fadi, da sauri ya kamata yana juyo da ita, sosai yaji dadin hasken da yake gauraye da dakin, idanuwanta yake kallo yana ganin soyayyar shi a ciki, yana ganin yanayin daya manta rabon daya ganshi a tare da ita. Wata ajiyar zuciya ya sauke yanajin ciwon da yake ji ya rage mishi, rungumeta yayi sosai a jikin shi

“Nagode…” 1

Ya fadi batare da yasan dalilin yin godiyar ba, kawai ya tsinci kan shi da son yi mata godiyar ne. Dumin jikin shine taji kamar ya wuce misali, hakan yasa ta taba wuyan shi, tana sauko da hannunta ta saka cikin rigar shi tana taba jikin shi sosai

“Zazzabi kakeyi”

Ta furta tana dago kanta daga jikin shi tana kallon idanuwan shi da yake kara kankance mata

“Tashi ka sha magani”

Dakuna fuska yayi yana girgiza mata kai

“Ba zazzabi nakeyi ba, banajin dadine kawai”

STORY CONTINUES BELOW

Dan daga mishi girarta tayi duka biyun, duk da sanin dalilin rashin jin dadin nashi na saka wani irin kishi naban mamaki tsirga mata

“Shine zazzabin ai, kaci abinci?”

Kai ya sake girgiza mata

“Banajin yunwa, na sha shayi a wajen Hajja”

Wannan karin zame jikinta Waheedah tayi daga nashi

“Kaje gidan shine baka taho da Fajr ba Sadauki?”

Hararta yayi

“Nine bani da kunya ai, kije ki dauko shi da kanki”

Murmushi tayi kawai tana sauka daga kan gadon

“Karki wahalar da kanki, ni babu maganin da zan sha”

AbdulKadir ya fadi, komawa kan gadon tayi tahau tana saka hannunta cikin aljihun shi ta dauki mukullin motar shi, Hajja tace mata yana asibiti rannan, ta tabbatar an bashi magunguna, suna mota dan inya shigo dasu gida zata sa yasha. Aikam magungunan ta dauko a mota tana dawowa dasu dakin ta ajiye kan gado

“Bafa zan sha magani ba saboda lafiyata kalau”

Har lokacin batayi mishi magana ba, fitowa da magungunan tayi kala hudu, akwai paracetamol a ciki, shi kadai ta ballo guda biyu tana sakawa a hannunta ta mika mishi, akwai ruwa a roba kusa da ita data shigo dashi ta dauko ruwan, kunshin hannunta yake kallo, shiyasa shi karbar maganin yana hadawa da hannunta ya rike

“Ka sha dan Allah, shi kadai ne ai”

Dauke idanuwan shi yayi daga hannunta yana sauke su cikin nata

“Bazan sha ba gobe” 1

Yai maganar cike da tabbaci, kai kawai Waheedah ta daga mishi, tana kallon shi ya shanye maganin yana hade fuska kamar zai amai, sosai ya dakuna fuskar shi yana turo mata labban shi, murmushi kawai tayi, fushi yake dole saboda tasa shi yasha magani. Ko Fajr inta bashi magani da kuka da komai yake sha, ko AbdulKadir din yana nan baya tayata, ca zai mata magani bashida dadi. Tsaf halayen shi yaron ya kwashe. Bata matsa mishi yaci abinci ba, dan tasan in har da kanshi zaice mata bayajin yunwar to bazai iya cin abincin bane ba. Ita ta kashe musu fitilar dakin tukunna tahau gadon, duk da tana rike a jikin shi, ko kadan ya nemi bacci ya rasa, ita kanta ba baccin takeyi ba, rashin baccin shi ya hanata yin nashi, suna kwance har karfe uku kafin su tashi su karasa raya daren ta hanyar gabatar da sallolin nafila.

BAYAN WATA SHIDDA

Ba zatace ga lokacin da ta taba jin dadin rayuwarta irin watanni ukun nan ba, tana gama iddarta ta fara shiga gari yanda take so, satinta daya bayan rabuwarsu da AbdulKadir ta samu ta fita da rana ita da Asma sukaje gidan suka kwashe kayan kitchen dinta, bata samu AbdulKadir a gidan ba, sai Waheedah da sallamar su kawai ta amsa. Harda kayan abincin da suke kitchen din kaf ta kwashe tana tafiya dasu gida. Haka tace ma Mama cikin kudin kayan kitchen dinta ne data siyar. Da su ta siyi atamfofi da leshi, ta rage sauran da a kayan kwalam da maqulashe ta karar dasu. 1

Kwalliya takeyi ta kece raini, samari ne suke mata layi kala-kala suna mata hadarin kudi, sai yanzun tasan rabuwa da AbdulKadir din alkhairinta ne, sakayau take jinta, a watanta na biyu bayan tagama idda ne ta hadu da Saminu. Matashin saurayin da bazai shige shekara talatin da biyu ba, daga yanayin shi tasan bai taba aure ba kafin ya tabbatar mata da hakan, da wuri ta sanar dashi cewar ita aurenta biyu, nuna mata yayi duk wannan ba matsala bane ba. Dogone sosai mai kirar karfi, kusan da kadan zaifi AbdulKadir, sai dai nesa ba kusa ba, ba zaka hada kyawun Saminu da AbdulKadir ba. Saminu ya tsere mishi tun daga hasken fata da dogon hanci, wayewa kawai AbdulKadir zai nuna mishi. Da alamu Saminu baiyi karatun boko ba, dan turancin shi irin wanda akan tsinta a hanya ne. Yace mata dai shi dan kasuwa ne.

STORY CONTINUES BELOW

Yana siyar da atamfofi da leshi da suke kawowa daga Legas zuwa nan garin Kano. Rashin wayewar shi bai dami Nuriyya ba, saboda yana sakar mata kudi kamar baisan ciwon su ba, ga siyayya yana mata kaca-kaca. Mafarkinta ne yake shirin cika, dan a sati Saminu na iya zuwa da mota kala biyu, watan su daya cif da haduwa ta nuna tana so ya fito, yace mata babu wata matsalar komai. Wannan karin Baba da kanshi ya fadama Wakilan Saminu cewar Nuriyya ta taba aure har sau biyu. Sukace duk Saminu ya sanar dasu. Ko sadaki dubu hamsin suka bayar.

Kallo daya zakaiwa Nuriyya kaga tsantsar farin cikin dake fuskarta, ga sabuwar waya kirar infinix dal a kwali Saminu ya kawo mata. Yar walima tayi a gidansu Asma ta tara kawayenta aka ralle, tunda dubu dari Saminu ya bata dan yin hakan. Da kan shi yai mata maganar tarewa ta nuna mishi ita bata da wani kayan daki ba kuma tada kudin yi. Zuwa yayi da mota ya dauke su ita da Asma sukaje wani tsantsareren gida dakuna shidda, da komai da komai a ciki, yace ta duba idan yai mata. Ranar da suka dawo har Mama sai da ta kula da rawae kafar da Nuriyyar takeyi

“Ki dai bi komai a hankali Nuriyya…”

Cewar Mama, farin cikin da Nuriyya take ciki yasa ta fadin

“In shaa Allah. Nagode”

Ta wuce daki. A kwana biyun sosai ta matsama Saminu kan maganar tarewa, yace karta damu zaizo har gida ya dauketa ranar wata alhamis da tayi juyin waina gardamammiya da rayuwarta. Har gida Saminu ya shiga suka gaisa da su Mama, yayi musu siyayya sosai ta kayan ciye-ciye, ya kuma kara yi musu godiya tukunna ya fita waje yana jiran Nuriyya. Ta dauki jakarta da mayafinta a kafada Mama ta shigo dakin 1

“Nuriyya kinga kin samu mijin da alamu suka nuna yana sonki, dan Allah kibi rayuwar nan a hankali, kiyi hakuri da duk yanda zata zo miki…”

Kai Nuriyya take jinjina ma duk wata nasiha da Mama tayi mata badan ta jita ba, dan hankalinta nakan alkawurran da Saminu yayi mata, na cewar hajjin shekarar da ita za’ayi ta. A satin zasuje suyi hoto, a fara maganar biyan kudi. Tun a mota take fadin

“Kasan a jirgi kawai nake hango ni”

Dan ta gama fada ma su Asma da duk wasu kawayenta maganar zuwan su Hajji, group dinsu ma yanzun Hajiya Nuri suke kiranta, sunan da yake kara sawa kanta ya kumbura. Tunda suka hau titin unguwar su take kula da cikin kurna yake nausawa maimakon Rijiyar zaki inda gidan daya kaisu ita da Asma yake. Ganin suna barin cikin kurna suna nufar dan dinshe, unguwar da tafi tsana duk a cikin karamar hukumar dala yasata fadin 2

“Naga munayin dan dinshe”

Kai Saminu ya jinjina mata, dan shi din bamai yawan magana bane ta kula

“Zan amshi sakone” 1

Ya amsa ta a takaice, numfashi ta sauke mai nauyin gaske tana sake gyara zama cikin motar. Haka har suka karasa cikin dan dinshe, kusan karshen unguwar dan gidan da yayi parking ne karshe a unguwar sai wani gidan bulo daga gefe, unguwar shiru kamar anyi sata. Taso ta zauna a cikin motar yace mata ta fito su shiga tare, batason duk wani abu da zai bata mishi rai a daren su na farko yau, shisa ta fito, tadai cika da mamaki ganin ya zaro mukulli a aljihun shi yana bude gidan, bin bayan shi tayi. Karamin gidane dan karami, da dakuna guda biyu, bandaki sai dan kitchen dako kofa babu, sai karamin risho a ciki da yar tukunya daya tabbatar mata da cewar kitchen ne.

“Gidan fa babu kowa… Wanne irin sako zaka karba?”

Nuriyya ta fadi tana kallon shi, ko kulata baiyi ba ya tura dakin da yake a share tas, da katifa matsakaiciya an gyarata itama, sai kamshin kafur yake da alamar yanayin damuna yasa aka saka saboda warin raba. Zuciyarta taji ta kasa natsuwa da ta shiga dakin 2

“Ni dai ka dauki sakon da zaka dauka mu wuce”

Wani irin kallo Saminu yai mata da yasa hantar cikinta kadawa

STORY CONTINUES BELOW

“Babu sakon da zan dauka”

Ya karasa maganar yana samun waje gefen katifar ya zauna.

“Ki shigo malama kar sauro ya cika mana daki”

Cike da rashin fahimta Nuriyya take kallon shi

“Ki shigo sai in miki bayani”

Zuwa lokacin kafafuwanta har rawa suke, shiga dakin tayi tana kasa zama, dan zuciyarta dokawa take tayi da wani irin karfi da yake saka jikinta bari

“Wata hudu da suka wuce na shiga unguwarku wajen wani abokina muna zaune majalissa wajen mai rake kika zo kika wuce. Kina gifta mu naji kin kwantamun har kasan raina, lokacin na furta hakan. Ban bar majalissar ba saida naji kaf labarinki, aurenki da Anas da kuma mijin kawarki da kika aure. Cikin kasa da awanni biyu suka fadamun labarin da nasan kinfi karfina, saboda banida kudin da zaki gani ki saurareni”

Saminu ya karasa maganar yana mata wani murmushi da yasa tajin kamar an watsa mata ruwan kankara

“Sunana Saminu da gaske, kuma kamar yanda na fada miki dan asalin kauyen dan busai dake nan jahar Kano. Abinda baki sani ba shine ni bani da wasu kudi, mahaifinki yasan sana’ata ni direban babban mota ne, kudin duk da nayi miki hidima dasu, kudin da kikai tunanin ina dasu tsintar su nayi. Sai bayan na tsince sune tunanin inzo miki a matsayin attajirin me kudi yazo mun saboda kin manne mun a zuciya. Ko kadan bakiyi wahalar siyewa ba saboda abin duniya ne a gabanki, nan dinne gidan dana samu na gina a cikin sana’ar da nake… Kar kuma kiyi tunanin akwai wani tashin hankali da zakiyi da zaisa in sakeki saboda wallahi nasha banban da duk wasu maza da kika aura a baya, babu kalar tashancin da banci karo dashi ba, banje wajenki ba sai da nayi shirin zama dake a duk yanda kika so mu zauna” 4

Mayafinta Nuriyya ta sauke daga kafada tana wulwula shi cikin son fifita fuskarta da iska ta daina kai mata, bata taba sanin menene tashin hankali ba sai yau. Tunda Saminu ya fara magana take jin wasu notika na kwancewa a jikinta, cigaba yai da fadin

“Duk motocin da kikaga ina zuwa wajenki dasu cikin ragowar kudin da suka ragemun nake arowa, gidan dana kaiku na ubangidan wani abokin wasana ne da yake gadi na roke shi alfarma naje daku kika gani, naso inji babu dadi na yaudararki da nayi, sai naga mu dukan mu badan Allah muka gina dangantakar ba, ni dan son mallakarki, ke kuma dan son abinda nake dashi, zaki iya taimaka mun mu gyara zaman mu daga yau mu nemi yafiyar Allah” 1

Wannan karin dariya Nuriyya tayi da bata da alaka da nishadi, tana son wani yazo ya tasheta daga wannan mugun mafarki, dan a mugun mafarkine kawai zata auri direba, direban ma na babbar mota. 5

“Da gaske ina kasuwanci, tunda idan nakai timatiri legas ina dauko gawayi in dawo dashi nan in siyar” 3

Da kuka dariyar ta kwace mata, kafin tasa hannu tana goge hawayen ta ajiye mayafinta a kasa ta kalli Saminu tana fadin

“Wallahi karyar iskanci kakeyi, ni zaka yaudara? Saminu ni zaka yaudara? Sakina zakayi yanzun nan dan bazan taba zama da kai ba. Kaga na maka kalar matar da zata zauna a wannan akurkin kajin?” 2

Dariya Saminu yayi

“Saki? Ai wallahi gara ki fara sakawa a zuciyarki mutuwa ce abinda zata gifta ta rabani da aurenki” 1

Mayafinta Nuriyya ta tsugunna ta dauka tana jin yanda duniyar take jujjuya mata, shirin fita takeyi daga dakin, cikin zafin nama Saminu ya taso yana riko hannunta, juyowa tayi tana daga dayan da niyar sharara mishi marin da zaisa ya saketa a daren nan ta koma inda ta fito ya rike hannun yana hadawa da dayan yai mata rikon da takeji kamar zai karyata tukunna yasa dayan hannun nashi ya sharara mata wani irin mari da yasa ta jin wani gishiri-gishiri a cikin bakinta 2

“Na gaya miki duk kalar zaman da kike so muyi dake shi zamuyi, idan mutunci kike so zamu lallaba rayuwar mu, idan rashin mutunci kike so zan zauna dake dashi” 1

Kiciniyar kwacewa take tana auna mishi kalar zagin da in sun kwana a tafa yakanji karuwai nayiwa masu neman su. Shisa yasha alwashin kudin goron da akewa direbobi nabin mata bazai zamana cikin su ba, koba dan komai ba yana tsoron lahirar shi, duk tangaririya da wahalar rayuwar daya sha da saken daya samu sanadin mutuwar iyaye bai saka shi ya lalace ba. Iskanci zabine a kowanne yanayi duk da yakan zo da kaddara, amman akwai zabi a cikin al’amuran rayuwa. Wani marin ya sake dauketa dashi yana wurgi da ita kan katifar dakin ya fita yana kulle dakin daga waje, yanajin yanda take dukan kofar tana cigaba da auna mishi zagin dako a jikin shi. 1

Mota yake ya fito da kayayyakin Nuriyyar da suke ciki ya shigo dasu tsakar gidan, sai da ya dawo kofar gidan ya tsaya abokin shi daya roka alfarma yazo ya dauki motar mutane ya mayar musu ya iso, yabashi mukullin tukunna ya koma gidan ya kulle. Ya shiga ciki ya bude dakin Nuriyyar da ta fito, ya nuna mata karfi yana daukarta ya mayar da ita cikin dakin, bala’i ne take gani irin wanda take jin labarin shi, dan Saminu bai jira ya saka abin duka ba, da hannun shi yaci gaba da mata wani irin duka da ko lokacin da AbdulKadir yake tashen zane su a islamiyya bai taba mata irin shi ba. Tun tana samun bakin zagin shi tana kai mishi yakushi har ta galabaita, nishin kuka ma bata iya fitarwa, a haka Saminu yabi ta yana raya daren. 2

Zuwa safiya kallo daya zakai mata kasan tagama fita daga hayyacinta, a gida yai sallar asuba. Ko kazar daya siyo sai da safen yace mata tazo suci, kai kawai ta iya girgiza mishi dan dakyar ta iya samu tai wanka tayi sallah saboda ciwon da ko ina na jikinta yake mata, shine kawai abin daya tabbar mata da cewar ba mafarkin auren Saminu takeyi ba, da gaske ne auren shi tayi. 1

“Kalar duk zaman da kika zabar mana shi zamuyi Nuriyya” 1

Ya kara tabbatar mata lokacin daya fice daga dakin, kanta kawai ta hade da gwiwa wasu irin hawaye masu zafi na silalo mata, hausawa sunce babu inda son zuciya baya kai mutum, ko da wasa bata taba hango nata zai kawota cikin wannan bala’in ba, ko kadan idan sama da kasa zasu hade ba zatayi zaman aure da saminu ba Hannu hijab take gyarama Ikram, ta kasa rankwafawa saboda tsohon cikin dake jikinta. AbdulKadir sai kiranta yake, yace shi bazai shiga cikin gida ba, saida ta fito harabar gidan ma tagan ko motar bai shigo da ita ba, kofar gidan ta fito ita da Ikram tana tsammanin ganin motar shi. Amman ko alamarta babu, dan baima karaso ba duk yabi ya daga mata hankali kamar wani wajen tazo ba gida ba. 3

A shekaru uku zatace babu abinda ya canza musu banda samuwar karin cikin da yake jikinta, rayuwa suke a nutse da ba zatace a kullum cike take da farin ciki ba, suna samun matsalolin da basu fi karfin yin sulhu tsakanin su ita da AbdulKadir ba. Sai dai zuwa yanzun ta fahimci rayuwar haka take tafiya a ko ina, ta koyar da ita babu wani abu waishi dawamammen farin ciki, sai dai akwai farin cikin da kake samu ko yayane a cikin kowacce rana tunda zaka tashi da tarin dalilan da zaka godema Allah domin su.

“Waheedah…”

Taji muryar Nuriyya ta dirar mata cikin kunnuwa, daga ranar da ta kwashe kayanta rabon da ta sakata a idanuwanta, duk da lokutta da dama takanyi tunanin kotana wacce duniyar, juyawa tayi tana kallon Nuriyyar da rayuwa tasa tayi wani irin sanyi. Da hijab doguwa a jikinta, duk. Da ba wata shigar azo a gani bace a jikinta, ba’a wulakance take ba, dan har kasan ran Waheedah din taji dadin ganinta a nutse. Haka zuciyarta take, wanda suke nufinta da sharri ma da fatan alkhairi take binsu, dan a wajenta duka duniyar bata da wani yawa. Mu duka kuma yan cirani ne da muke haduwa da mutane mabanbanta a hanyar mu, burin kowa shine samun ribar da zai alfahari da ita idan lokacin shi ya cika. Shisa bataga dalilin da zaisa bata lokacinta akan abubuwan da ba zasu amfaneta ba. 3

Sosai Nuriyya taji dadin ganin Waheedah din, tun tana ganin auren Saminu kamar abu na wasa, kamar abinda ba zata tana yarda dashi ba, tun tana mishi rashin mutunci yana jibgarta harta fara saduda da lamurran duniya, dan taje gida Abba ya rantse wannan karin idan harta kaso auren Saminu ba zata zauna mishi a gida ba, Mama kuma tace ba zata bashi hakuri ba. Haka ta hakura ta koma, kullum rana sai Mama ta kirata a waya tayi mata nasihar da saida ya dauketa shekaru biyu bata jita ba, shima shekarun satar fita tayi batare da ta fadama Saminu ba, akai mummunan hatsari a gaban idanuwanta mota ta take mace da goyonta ko numfasawa basuyi ba.

Motar kuma ta kama da wuta haka direban ya fito yana ihu yanaci da wuta mutane na kokarin kawo mishi dauki, bata tunanin ta taba tsorota kamar yanda ta tsorata a wannan yanayin dan a gigice ta karasa gidansu da kafafuwanta kamar zararriya, tana shiga gida jikin Mama ta fada tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, gabaki daya duniyar bakomai bace ba, kana aikin banza kake cinye kwanakinka, sosai hatsarin ya tuna mata da kwanciyar kabarin da take jiranta, tarin tashin hankalin da yake cikin kwananta na farko ita kadai batare da taimakon kowa ba.

Ranar a gida ta kwana, duk da washegari Saminu zai dawo daga Legas. Samun shi tayi ta bashi hakuri kan irin zaman da suke, sosai kuma suka fahimci juna suka kuma nemi juna gafara. Data nutsu saita sami farin ciki a zama da direban data raina, direban da take ganin tafi karfin tayi rayuwar aure dashi a duniyar da bakomai bace, data nemi tana son ta gwada neman aiki da takardun NCE dinta bai musa mata ba, ca yayi ma akwai wani ubangidan shi zai mishi magana yaji. Cikin ikon Allah aka samo mata aikin koyarwa a wata primary ta mata da ke nan dan dinshen. Dai-dai karfin shi Saminu yake mata hidima. 1

Duk da matsala dayace take fama da ita yanzun, itace rashin haihuwa, banda wannan rayuwa take data sa tagane farin ciki bako yaushe yake zuwa da kudi ba, farin ciki kanzo idan ka samu wadatar zuciya da iya inda Allah ya zaunar dakai. Tayi nasarar ganin Anas sau daya tun bayan rabuwar su, ta kuma roki daya yafe mata, duk da har yanzun takanyi juyi da amsar daya bata

‘Na jima da yafe miki Nuriyya saboda bana son wani abu ya sake hadani dake, ciki kuwa harda tsayuwa gaban Ubangiji a filin tashin kiyama, wallahi na jima da yafe miki karki damu’ 3

Sosai takanyi tunani akan kalar rayuwar da tayi a baya, da mutane biyun da suka nuna mata kauna fiye da kowa a rayuwarta da yanda tayi amfani da wannan kaunar ta cutar dasu

“Nuriyya”

Waheedah ta fadi tana katse mata tunanin da takeyi

“Ki yafemun dan Allah, na cutar dake da yawa, wanda kika sani da wanda baki sani ba, ki yafemun Waheedah…”

Numfashi Waheedah ta sauke

“Babu komai, Allah ya yafe mana”

Wannan karin ajiyar zuciya Nuriyya ta sauke tana dorawa da

“Ki rokar mun AbdulKadir da ya yafemun shima”

Kai Waheedah ta daga mata tana hango motar AbdulKadir din

“Sai anjima…”

Tace ma Nuriyyar tana kama hannun Ikram din

“Ina Fajr?”

Nuriyya ta tsinci kanta da tambaya tana saka Waheedah juyowa ta kalleta cikin idanuwanta

“Na yafe miki Nuriyya, tun kafin ki tambaya, amman hakan baya nufin ina son sake kasancewa dake a rayuwata, babu wani abu da zai sake hadani kawance dake” 2

Kai Nuriyya ta jinjina ma Waheedah din, bata koji zafin maganganunta ba, ko itace a matsayinta abinda zatayi kenan.

“Nagode…”

Nuriyya ta fadi da wani irin yanayi a fuskarta

“Ina miki fatan alkhairi a duk inda rayuwa zata kaiki”

Waheedah ta fadi tana jan Ikram suka tsallaka inda AbdulKadir yayi parking din motar, Nuriyya kuma ta shiga gida. Bayan motar ta budema Ikram ta sakata a ciki, tukunna ta bude gaban ta shiga

“Kinsan sarai gobe zan tafi, shine zaki zo ki barni ni kadai” 1

Murmushi kawai tayi

“Nuriyya nagani yanzun ta shiga gida, tace ince ka yafe mata”

Shiru AbdulKadir din yayi badan baiji me tace ba, sai dan a shekaru uku yaune rana ta farko da maganar Nuriyya ta gifta a tsakanin su. Motar shi ya tayar yana wucewa dasu gida, bashida abin cewa yanzun ma, shisa ya zabi yin shiru, wanda duk zaiji labarin shi da Nuriyya zai san kaddarar zaman aure ce kawai ta gifta a tsakanin su, yanzun ta zama bayan shi, bayan da baya dubawa idan harya wuce, ya gama yafe mata duk wani kuskure da tayi mishi a dan gajeran zaman da sukayi. Shima fatan shi idan ya kuskure mata ya zamana ta yafe mishi.

Dan da Abbba ya kira shi yai sake mishi nasiha kan abinda ya faru din daya kira mishi ko da gaba zai tunanin kara aure saida hanjin cikin shi ya murda, yana addu’ar Allah yasa kaddarar shi ta zama da mata biyu ta kare daga kan Nuriyya, Waheedah ta ishe shi rayuwar duniya yana kuma fatan ta zama matar farko da zai nema idan ya tsallake duk wani mataki yayi nasarar shiga aljanna.

Suna karasawa gida an kawo wuta, Ikram nata tsalle ganin tv a kunne da tashar cartoon network da suka saka shun the sheep. Nan falon suka barta suna shigewa dakin su. Waheedah na cire hijabin dake jikinta, AbdulKadir ya taka ya hade space din dake tsakanin su, sai nishi take kamar tayi wani aikin karfin.

Hannun shi daya ya dora kan cikinta kamar abinda yake ciki hakan yake jira yayi motsin da taji har bayanta ya amsa tana runtsa idanuwanta ta bude su akan AbdulKadir da yake mata dariya

“Ke kam kamar ba matar soja ba”

Harar shi tayi

“Da zan iya dana cire cikin nan ka dauke shi kona kwana biyune”

Tsinin cikin bazai barshi ya rungumeta yanda yake so ba, hakan yasaka shi sakin hannunta ya zagaya yana rungumeta ta baya hadi da rada mata maganganun da sirrine a tsakanin su, hannu tasa tana dan ture shi hadi dayin dariya kafin ta dora hannunta saman nashi da ya ke kan cikinta tana lumshe idanuwan shi. ABDULKADIR din ta, sojan ta, Sadaukin ta. Bata same shi da sauki ba, kaddarar zaman su bata kawosu inda suke da sauki ba, bata da wani tabbaci akan yanda rayuwa zata kare musu, amman tana da yakinin indai suna tare da juna koya rayuwa zata hankade su koda sun fadi dayansu zai daga daya…! 1

DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *