ABINDA ZUCIYA KESO COMPLETE

 ABINDA ZUCIYA KESO COMPLETE

 da akayi yasa  mai gadi yafito da saurinshi daga dakinshi that is just beside the gate ya zare sakatan gate din ya wangale gate din sabida motar ta shigo, wangale gate din da akayi yasa wata yar budurwa da bazata wuce 25-26yrs ba da wani matashi ke zaune gefenta kan plastic chair yana sanye da bugaggiyar shadda milk duk suka dago

kansu suna kallon Gate din ganin wanda zai shigo ciki da alamun tadi sukeyi abunsu dan kowannen su na dauke da murmushi kan fuskarshi, motar gidansune ta shigo har zuwa inda ake parking motar yay parking, bude bayan motar akayi wata yarinya fara dake sanye da jean da t-shirt ne tafito ta tsaya tana turo baki tai kini kini da rai, white flat shoe ne na vine a yar karaman kafarta da dududu size dinta bazai wuce 37 ba yar kafar, sai pencil jean din jikinta daya tsaya mata a daidai idon sahu, kafarta na haggu sanye dawani hadadden leg chain daya kama yar faran wrist din kafan nata, yama kafan nata kyau sosai bana wasaba dan silver color ne, ba karamin kamata sky blue Jean din chinos din yayiba batada wani girman ass but is a lil bit bumpy saidai tanada wani mahaukacin hips curve, irin matan da ake cema cylinder shape kenan, wani white non logo t-shirt ne ajikinta yadin so soft fari kal babu ko single stain ajikin rigan, tasaka wani simple necklace mai hawa uku masu dauke da pendent din moon shape wanda the last one ya sauko har kasan wajen gab da cikinta suna walkiya, babu komi kan fuskarta batasa makeup ba, dan ficicin pink lips dinta sun bushe sosai sai manyan idanunta da kwayan idanun kenan mai ruwan toka ko kadan ba bakake bane, tanada cikan gira baki, sai dan karamin sky blue dan gyalen data yane kanta dashi da ana ganin almost rabin kitson ta yan fici fici kalaba masu kyau sosa, wrist dinta na haggu sanye da digital watch sai dayan wrist din tadaura wani fine simple bracelet daya karama little tiny hand din nata kyau, ko kadan bata da girman jiki, batada wani tsayin kirki badai gajera bace, sanan batada kiba kawai she is super portable, bata da girma kuma baxaka kirata karama ba. Kallon direban daya bude kofa yafito tayi bayan ya kashe motar, turo baki tayi tareda hararanshi cikeda tsiwa tace “kai Isa bazaka bani jakana ba ninagaji da tsayuwa” da sauri Isa direba yazo wurin cikeda girmamawa yace “sorry Autan Mummy, dan gyara na dauko miki to” matsawa gefe tayi tana kwafa tareda kama waist dinta da hannu daya tana jiranshi yadauko mata jakan ya bata, wani bagpack yadauko mata irin na yan matan nan da yan makaranta ke amfani dashi da ake goyawa abaya fari ya mikamata yana murmushi yace “yauwa to ungo gashinan nadauko miki Auta” hannu tasa ta fizge jakan kaman ana fada sanan tajuya ta tafara tafiya tana fita daga parking tent din tai cikin yard dinsu, das das take tafiya kaman bataso tayi hips dinta na juyawa gashi jean ne ajikinta abin looks so alluring to the eyes, tundaga nesa take ballama Ya Siddiqa dake kallonta cikeda takaicin ta harara, saida takaraso wajen taja wani mugun tsaki tace “bashi ko tara eh? Anwani kafe mutun da idanu kaman za’a tsotsemai jinin jiki, sa’ido dai sana’ar banza ne” tai wani fari da ido tai gaba abinta batare data gaida koda mutumin dake gefen Siddiqa ba, azuciye Siddiqa ta tashi daga kan kujeran zata bita da sauri Sadiq yarike mata hannu yace “me haka ina zaki? Ki barta yarinya ce bakigani ba” cikin fushi Siddiqa ta fizge hannunta tace “Baby wlh duk rashin kunyan ta tai dani ni kadai bazan ma tanka taba, amma tsabagen rashin kunya ta kallemu taja tsaki sanan tacemana sa’idawa, that’s an insult wlh saina fasa mata baki yau agidan nan” kafin yamayi magana ta fizge hannunta tai ciki tsabagen yanda kirjinta ke zafi yana tafarfasa sabida yanda Auta tamasu itada Sadiq rashin kunya haba mana, agaban wanda zata aura zata disgata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *