ABU A DUHU CHAPTER 2

ABU A DUHU CHAPTER 2

              Www.bankinhausanovels.com.ng 

Soyayya ce me qarfi yashiga tsakanin bayin Allahn biyu, se de kash iyayen azra sunce bazaayi auren su yanzu ba.. dole dole se tahada degree dinta..

Haka ya haqura yace to zai jirata , dan yanzu ne ma azra take shekara na biyu a jami’a+

Azra da haitham sun zama love birds shaquwa me tsanani yashiga tsakanin su.. azra ba ta da wani magana da yawuce na haitham dinta shima haitham din haka.

Kwanci tashi ba wuya inji bahaushe…

Yau gashi azra zata gama degree..

A cikin shekaru ukun nan masoya  da dama sunsha kawowa azra hari Amma azra tayi biris tace inba haitham ba ita bata ganin kowani namiji da gemu..

Ta bangaren haitham kuwa kullum yana zarya a gidansu azra, shi ke coaching dinta a karatunta, dangi duka ba Wanda baisan haitham ba, shima ta bangaren en gidansu ba Wanda baisan azra ba, da anyi masa maganar har yanzu baiyi aure ba da de uzurinsa Bai samu matar aure ba.. Amma yanzu uzurinsa daya tilo ne wato azra bata kammala

karatu ba.. to gashi Alhamdulillah azra tagama karatu ta lafiya lau.. gobe iyayen haitham zasuje Nema masa auren azra..Yau ne iyayen haitham suka ce zasu zo Neman auren azra tinda ta gama karatu kuma Sun gaji da ganin dan nasu haka ba aure, shekaranshi 35 kenan, ya gama bsc.dinsa a fannin biochemistry sede yafi maida hankali akan kasuwanci kuma Alhamdulillah kasuwanci ya Amshe shi.  Dan tuni yagama Gina tangamemen gidansa a new G.R.A..

Iyayen haitham sunzo sun koma se de da kagansu zakaga rashin walwala a tare dasu..

+

Me ke faruwa??? Inji haitham?

Ganin mahaifinsa ne Awana abdu yace haitham munje nema ba a bamu ba.. dama haitham baka da tabbacin za a baka yarinyar nan shine kuma dan wauta ka tsaya jiranta?? Me yake damunka??

Haitham da yake Jin maganan nasu kamar a mafarki, ya ce Alhamdulillahillaziy ahyana ba’ada ma amatana wa ilaihin nushur..

Ya Allah kasa mafarki nake… Awana abdu ne yace to majnunu azra.. bude idonka da kyau  kadai ji abinda muka fada maka. Kamaidamu yara munje tangal tangal anmaidomu..

A firgice haitham ya tashi yadau mota se gidansu azraCikin sauri ya aika a kirawo masa Azra.  Sede kash an dawo masa da mummunar ansan da yaqara dagula masa lissafi.  wai Abba yahana azra fitowa..+

Kan yajuya Sai ga abban nan da Kansa.. yace haitham,

Haitham ya duqa har qasa yagaidasa yace na am Abba..

Abba yace haitham ba wai na hana ka auren azra bane, Sai dai kayi hakuri dama ban ce namaka alqawarin zan baka ita bane, kayi hakuri yayana mahaifinta babba kenan ya yanke hukuncin hada auren ta da dan uwanta.. bawan Allah kayi hakuri azra ba rabonka bane.. cikin tashin hankali yayi sallama da baba yafice se de uku uku yake ganin hanya.

Ji kake rammmmmm…motarda haitham ke tuqawa ne ya bugi wani bishiya.. Sai innalillahi wa inna ilaihi rajiun mutane wasu na salati.. wasu na cewa ai dama giya yasha dole yayi irin hatsarinnan( kaji en adam Abu a DUHU basusan me musabbabinsa ba Amma har sunyi conclusion ai giya yasha.. Allah yashiryemu)..

Haka nan wasu su kadaine shi aka kaishi asbiti bangaren taimakon gaggawa.  Atake kuwa aka bashi kukawa na mussaman, yaji mummunan rauni a ka, yakuma samu Karaya a hannu..

Likiticin sunyi iya qoqarinsu sun ceto rayuwarsa Sai de har yanzu Bai farfafo yadawo hayyacinsa ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *