AHUMAGGAH CHAPTER 10

AHUMAGGAH CHAPTER 10

Acikin motar nasu ma a matse take,Banda jahan data matsa sai ta raka su babu abunda take daga ido tagani wanda zai sauya mata radadin datake ji azuciyan ta+ Khaldun baya ma kula su ba dan baima hade mota daya dasu ba shikadai ake jansa ana shi motar yana biyo su daga baya Da suka isa airpot taga lallai jahan tafiya zatayi ta barta dashi bata iya boye fargaban ta ba sai ta dai daure ta yi mata magana sosai akan subaya. Jahan dai ta saurarae tane amna ita kanta bata gane komai daga abunda tace ba gani take kamar bahiyyan tana cikin tension,aure babban al’amari ne and this whole thing is new for her ahakan dai ta barshi ta shiga lallabata da maganganu masu sauki Tace kar ki damu da subaya.. .she is very emotional, hala idan batayi hakan ba bazata iya rabuwa dake ba ne..i know how much she cherish you ni zan kula maki da ita and da ta sauko ita zata zo miki first visit a abuja! Ok? Hakan yasa taji dan dama dama jahan ta bata wani warm and cormfoting hugs…sannan ta damka ta hannun shi with her eyes directly odering him ta take care of her . A haka suka bar kano suka dauki jirgi zuwa garib abuja,kowa na harkan gaban sa bata kallon inda yake shima baima san da ita ba . Da suka isan ma Awani private lodge mai tarin sojojin navy na da kasa ya fara sauka sai ya aje ta a wani daki ita daya yayi gaba abunsa Anan tayi ta zama tana juye juye Babu abinci babu ruwan sha babu komai kuma Bata sake ganin sa har sai chan data gaji ta dan fito ta aika a aka kawo mata abu tasa abakin ta Anan take ganewa ashe ma meeting yake yi da chief security adviser un behalf of sub marine security operation na kasa Tabe baki kawai tayi ta koma ciki,snack din da aka kawo din tasa abaki taci sosai dan shi ya dan bata karfin giwa har tayi wanka tayi sallah sannan ta cire kayan jikin ta tasauya da wani simple material gown baki mai laushi, dan karamin roll dinshi ta yafa tayu zugum yanayin bakaramin daukar pale mood din ta yai ba Ta na zaune a hakan jin kadan sai ga wayar ta na kara,ganin jahan ne yasa ta dauka da wuri tana mai sauke ajiyan zuciya … sunyi magana ba mai yawa ba,anan ma koda ta tambaye ta akan subaya jahan ce mata tayi ai subaya ta fita a gidan dan itama ta dawo bata same ta ba Haka dai suka kare wayar,cikin ranta cike da tunani kala kala,tunowa da cewa dija na abujan yasa tayi hanzari daukar wayar zata kira taji Just as she was about to call,sai ga budewar kofar shi Kashe wayar tayi da sauri ta dago sabida jin shin akanta datayi bazata ya dan buga mata zuciya,baice mata uffan ba itama haka Suna hade ido ta kau da nata sai taga har yanzun fushi yakeyi,and she just can stand his furious looks. Ko gama juya maganan batayi ba taji voice dinshi yana cewa “Inkin ga dama sai ki fito,..am leaving now… Ta dago kai kafin ta ansa shi har ya bar wajen,tabe baki kawai tayi ta mike kayan ta kawai ta daga ta fito dashi waje masu aiki suka karasa sawa a booth dinsa Duka a bayan seat suka zauna Tana daga gefen sa kanshi na kallon dayan side din ta waje She just wonder whats wrong with her own sa’ood amma haka kawai yanxun itama take kallon shi da abunda ya gaya mata jiya.. Cheap,i hate you Tayi siririn asirtaccen tsaki. A haka Har suka kai bakin wani katafaren gini irin ginin gidan jahan sak amma yadda aka tattale shi da uban kwalliya zaka san kwanan nan ma aka shige shi The house is full of law and oder . kowanni maid namiji da na mace suna sanye ne cikin wani yadin atamfa blue da dankwalayen su yadin fari kamar kuyangan gidan sarkin gabas wanda Dinkin ne kawai Yake banbata su da kuma matsayin su. Da haddadiyar GTR din su ya tsaya tun kafin su sauka akayi anoucing isowar su achan sashen jahan khatun ,her majesty dilshad khatun din ma tana cikin gidan,itama tazo zaman wucen gadi ne dan wannan karo ne na farko da suka taba banbanta gida da kasa tsakanin ita da yarta jahan khatun Dan haka babu tantama The atmostpher is filled with reams of oficiality and Royal sophiscation. Kowa na dar dar, juya kai ta glass bahiyya tayi tana kare ma ta wajen gidan kallo Dayaga ta bashi bayan alaman hankalin ta bai wajen sa wabi takurarren tsaki yaja bai bari ya sake juyowa ba yace mata Ke,sanda ta waigo a razane ta daga ido tana kallon daurarren fuskan sa Wani warning taji yana kashe mata yana cewa saura kije ki gaya ma wani cewa ke matar aure ne,sake maimaita kalman ure nothing but my maid din shi ya sake buga mata zuciya ta tsaya duban shi ranta a dan bace har ya sa kafar sa ya fita bata ko tanka masa ba Cikin ranta tace Kar nace ni matar ka ce?Akan me…inji dai ance nan ma gidan naku ne..to ai muddin auren nan ya auru i think yan uwan ka ma sun sani Ita tayi tunanin hakan ne amma Ko kadan bata san jahan ma tace kar khal da alhaj hamood su fadi auren yanzu da wuri ba Jahan tasan halayen su dilshad sarai,zasu iya daukar dumin da zaisa a cutar da su duka, sai ta yanje shawarar cewa to su bar komai a rufe har sai an hadu gaba daya awaje daya sai a warware maganan Kowa dai acikin su na dan fargaba Musamman akan alkwarin saood da junnut,duk dama sunsan dan saood ya aure bahi ba haramun bane Anma ko kadan basu so ace dilshad tana musu kallon kamar sun hade kaine sun ketare dokan ta Toh Da shike dukan su ayanzu kowa nada nashi uzurin kusa,alhaj hammod sai yace ajira khal yana dawowa daga mission din shi shima zaizo har kano ya taho da su jahan Aarah abuja sai ayi maganan Yanzu dai a matsayin Su yasu suka san abunsu Awajen subjgan aarah auren sirrin akayi ma khaldun saood da bahiyyah. khaldun tuni ya fita a motar ya barta ciki yana takawa security sukayi yuuu suna biyo bayan sa ana taka mashi baya,shika dai yasan abunda ke damunsa dan bai ko daga ido ya kalle kowa ba Cikin takun sa na kasaita da jan aji ya nufi wani part na daban wanda ma ba a asalin main house din bane Ita kuwa bahiyya Tun daya tafi ya barta a motan ta rasa mezatayi guda daya,dan Leken shi takeyi har ya bace ma ganin ta,kafin ta farga sanda taga yan mata biyu sanye da unirfom agaban ta suna mata fadan ci kamar zasu cinye ta Ure welcome ur highnesss… Wannan ya rike nan wannan ya ja nan A Tun bata son daga kai har suka fara bata takaici cikin ribibin gaisuwar nasu tuni aka Rabata da duk wani kayan ta aka kai side din khal da bata ma sani ba To da ta fito sarari babu wani bayi mata She was quiet confuse on where to go strght ahead,sai ta yanke hukuncin bin inda taga ya shige in dazu,kowani gyara mayafin doguwar gown din tan batayi ba ta rike sauran a hannu tana takawa ladaf ladaf cikin tsarin da bazakace wani abu yana damun ta ba Gaban katoton golden gate din ta isa bayan amsa gaisuwa batace da kowa uffan ba ta shiga daga ciki,kallo ta kare ma wajen aranta tana mamaki sai taga a ta Wajen ne dai kawai akwai security amma tana sa kafarta cikin farfajiyan gida taga shiru ne babu kowa sai lafiyayyar fili da home street layout masu tsananin fallasa tsafta Tana daga ido wani sharbeben kuma boyayyen mansion ne ya bayyana mata kansa,amma da alaman ya bata baya dan babu kofofin dayayi kama da na shiga Dan juyi take yi tana dan kifta idanun ta…”Wowww…zuciyan ta dake bugu slowly ya fada gashi wajen ya dada yankewa da tsitttt babu ko kuda sai tarin qamshin garden flowers da sanyin pure breeze Ta dan duba setin mansion din ko zata ga doors bata gani ba hakan yasa ta tabbatar nan ta baya ne ko maybe tayi missing hanya. Kaamil daga chan saman benen yana amsa waya shiya fara hangota tana tunani tana dan dube dube. Wani irin dakatawa yayi ya kare mata kallo sosai Maids sunce masa khaldun ya iso da wata yarinya dama shima sauri yake ya je site dinsan su gana…but seeing this angel rogjt now akasa yasa ya kashe wayan sa da sauri Ya sauko a guje ya bullo ta kofar main gate dake kasanr benen da bata lura dashi din ba har ya shiga asalin cikin gida “Jayyyyy…jaaay..junnuttttt..junnut..ya shiga kwalla mata kira yana cewa kizo kizo kizo Yadda ya zaburo yake kwala mata kiran tana chan sama ne amma Sanda taji ta tsorata A gurguje take kokarin saukowa tun kan ta karasa cewa menene! Ta ji ya cakumo hannun ta feeling so excited yana dan dariya Yace mata junnut ques what,? Batace komai ba Sai ta tsaya kallon shi tana turo baki ” mutumin ki is around kuma yazo mana da wata kyakkwar angellllll. . Ke kinga kyauun ta? U know what!i just cant wait to meet her kema fa dole ne muje yanzun ki ganta Dan dariya junnut tayi tace what nonsense kay,yanzu akan wata yar mace kake kwalla min kira! Tace hmm ai nasan ruwa bata tsami a banza,. But Murnan jin ance khal dinta is arond ma kawai ya sa mata dadi da nishadi So ita Bata damu da yarinyar da yake magana akai ba amma danta biye ma shirmen nashi sai ta bashi hannu suka sauko tare har waje suka shigo ta dayan mansion din Suna surutu suna takowa daga matakalan dake cahn sama basu ma lura ba1 Da kuwa har sun zo zasu wuce inda kaamil yake tsaye dazun da ya hango ta,sake ganin ta awajen da yayi yasa ya dawo baya sai ya jawo junnut baya itama yace heyyy heyy Look at her,gata chan wallhy har yanzun bata bar wajen ba Da sauri junnut ta waigo,suka isa ta Jikin balcony stand suka kama dukan su suna lekowa kasa amma sai basu ga fuskan ta da kyau ba A lokacin bahiyyan itama ta juya tana magana da maid din da ta kai mata kaya ne akan ko zata kaita masaukin ta da khal maids din kuma ta turje akan doka ne basu shiga side din sau biyu saida cikakken izinin sa Bahi sai ta rasa me ma zata ce ma maid din ta saduda ta kaita,gashi ya hana tace ita matar sa ce sai kwana take mata sabida bata san ko ina ba Ganin haka yasa junnut ta dan ja tsaki tace nikam mu tafi kawai…. Look how She is just talking to a maid bana tunanin tana da aji u know i really miss him ni shi nake son gani ba wata babe ba…. Shikuwa kaamil ba yadda ya iya ne kawai amma haka kawai tunda yagan ta yaji zuciyansa yana ta zumudi1 yace ok ok muje mana junnut sai ta shiga gaba…Aikuwa suna juyawa wani karamin short gesture ya wuce walau ta idanun ta ya nuna mata kamar barin gefen fuskan bahiyya Wani dum dum taji a zuciyan ta atake taji tana neman tsayawa chak Kaamil da ke gaba sai zame sai yaga junnut ta dakata sai yace ke ya haka?mu tafi ba basauri kike ba? Ko kula shi batayi ba ta koma kan step din da gudu again tana dada kare ma bayan bahiyyar kallo,bata san me ya sata ba kawai sai taji bakin ta ya furta bahiiiii? “The feeling was so increasing…sai ta dada cewa Bahiyyyahhh…ita ma bahi tuni jikin ta ya bata kamar wani abu na daban zai faru amma sai ta basar aikuwa 2secnd bata kara ba ta juyo not looking up ita dama environment din tafiye kallo cos har yanzu bata lura da mutane achan saman ba Da junnut taga ita dince Wani electric shock ne taji ya bi jijiyan ta agigice ta ware idanun ta,..asif she was dreaming in a broad day ligh Atake jikin ta ya fara rawa dakan shi Tana wasu irin kakarin kukan murna mamaki ya sa kaamil ya dawo gaban ta yana ta binta ido Sosai ta kafe ido tana kare ma bahi kallo dan ta tabbatar ba mafarki takeyi ba. bahiyya tana juyi zata bi bayan maid din itama dan ta nemi mafita makanta A haukace Junnut ta wani daka tsalle in clean exctiment takarkrewa tayi ta kwala kira bahiyyyahhh…bahiii. Kamar wanda zata cire magwagoron ta Jin karar yasa bahi ta dakata Wani rassss kanta ya buga Tuni ta waigo a tsorace dan ba tantama ta gane muryan junnut din ta ne Da ta waigo bata ga kowa ba Sai ta yi saurin lumshe idanun ta ta rike kirjin ta dake faff gaff da sauri duk abunda take yi alokacin junnut na sama tana kallon ta Hawaye ne suka wanke fuskan junnut Wani birkicewa tayi cikin murmushin murna da ko kaaamil bai taba gani akan fuskn ta ba Sai ya riko hannun ta a slow. …yace junnut dama kinsan ta ne,..batayi saurin amsawa ba sabda ta wani lumshe idanun ta data itama She saw how bahi is reacting righ now ta kuma gamsu cewa lallai bahiyya bata mance da amana ba. Kamar wance ta haukace ta xabura ta tsala ihun murna tana kuka at same time,after five years of silence and pain,tuni tabi ta kankame sa tana cewa kaamil bahiyya ta ce fa,..she is mine…what im i even waiting for… Jin sautin ihun da murnan junnut ya dan dada jan hankalin bahiyyar sai ta shiga zulumi tana dan dube dube har wani abun naso yace mata ta dube sama amma tana daga kai taga babu kowa nan ba dan Tun kan kaamil yayi gaining balance ya rike junnut ta ture sa ta arce aguje tana saukowa she dint even know when ta zubdar da takalman kafafun ta Bata tsaya ba sanda ta iso kasan ta ganta da kyau atsayen Lokacin ita kuwa Bahiyya har tagaji da dube dube ta dauka ko kunnen ta ne kawai yake neman haukatar ta sai ta juya zata fita One good step ta dora sai ta taji muryan kuma still a kusa da ita,. Cikin sanyi ake kiran ta Bahiii…bahiyya.. Duk da daukewa chak datayi bai hanata wani irin waawan juyowa Sai charaf suka hade idanun su su,wani irin shock ne ya debe su na mamakin ganin juna da kuma mamakin irin wajen da suka hade ayanzu Sunfi minti ashirin a haka har kaamil ya karaso wajen suna ta kalloin junan su Wasu rikitattun hawayen kewa mamaki da kauna duka ya wanke fuskan su Junnn….nut???..bahi ta fada da kyar muryan ta kamar zai rabu da jikin ta dan rawa Wani kasallalen murmushi junnut tayi tana dan kokarin share tears din tace yess yess nice bahiyya…. please come ….sai ta ware arms dinta duka biyu ta fashe da kuka…1 Da wani irin force of atraction suka taho jikin juna aguje suka kankame kansu cikin wani irin mugun shauki. Dada kankame juna sukeyi juyi juyi bakajin sautin komai sai na muryan su Kaamil yayi still ya nade hannun shi a gafe shikam yana kallon su in total confusion har sanda abun ya dan sake su A hankali bahiyy ta zare jikin ta dago junnut din tana kallon ta hawaye ne masu nauyi ke sauka akan maraitaccen fuskan ta ta dora hannun ta ta shafa fuskan junnut din gently…murya na rawa tace junnut ashe kece…ya ilaaahi…..dont tell me this a dream..sai tayi saurin sake ta ta juya mata baya tana lumshe idanun ta.. A hankali junnut ta karaso ta wani kwnto akan gadon bayn ta tarre da knkame ta ji kawai tayi ta zagaye jikin ta tsam da hannun ta cikin yanayin shauki ta rungumo ta baya.. Tace ba mafarki bane kawata nice ….junnut dinki ce…. I missss you soo much bahi,..banyi tsammani zan ganki anan ba. .nor now What are doing here Sai ta juyo da bahi suna kallon juna kowannen su na kokarin controling emotions dinsa.. Dan ajiyan zuciya bahyy ta sauke tace Nima yanzu nazo… Bansan nan wajen ba…i came with.. Junnut tace its ok,ko waye ya kawo ki yau dai bazan dena gode masa ba Cos he brough me back to bein who i am when i use to be with you Come,Meet my brother …sai ta jawo hannun ta zuwa gaban kaaamil wanda ya dade yana ta kallon su kansa adaure. . Acikin nitsuwar da baisan junnut dashi ba tace Kay..wannan itace zuciya ta..bahiyya ta.. my best and childhood friend infact my blood sis… Sai Ya danyi smile a hankali yana binsu da kallo Yace yeah i can see that.,ure welcome zuciyar junnut ….ya mata murmushi itama ta mayar mashi…i love this ur bonds fa,. Like ouchhhh junnut kece?…ai saura kiris kusani kuka .. Yanayin yadda yayi maganan cikin shaukin kwaikwayo da unserious feeling sanda suka danyi masa dariya suna jin kunya Zo muje ciki…ta ja hannun bahiyyar suka fara fita gaba daya daga shashen Kaamil shima yana tahowa yana binsuu da ido yana wondering irin yanayin shakuwar su Bai taba sanin junnut zata dawo wata daban lokaci guda ba sanda yau yagan ta da wannan yarinyar! Those innocent tears,the bonding and pure respect,its get to him har brain dinshi yaji lamarin su Yace kai wannan yarinyar She must be very speacial one…junnut tana matikar kaunar ta…gata kyakkwa Uwa sarauniya Su kuwa tafiya suke rike da hannun juna junnuta tana cewa Nan gidan mom dina ne kanwar mahaifiyata muma ai jiya muka dawo kasar nan,,yanzu dai bana so na cikaki da surutu kinga kakata na nan lets go and meet them first kafin naji lpyar ki ko? Murmushi bahiyya tayi suka wuce basu sake tsayawa ba sanda suka shiga wata albarkatcciyar waje mai mugun dauke hankali Thy are two colours that speak of royalty.. “purple and black” Ko ina ya dauki white wall with dark edges,daga gani ba tanbaya tasan nan kam ba arziki bane kawai harda mararin sarauta Bayi da maidens na ta kaikawo junnut na rike da hannun ta har suka kai gaban wata hamshakiyar mata dake kime akan wani jahilar royal puple chair mai haddaden golden grown crown head Ganin ta ma kawai ya isa gaban ka ya fadi sau dari,dan haka bahiyya ta zame hannun ta a slow ta dan ja da baya tana kallon yadda junnut da kaamil suka isa gaban ta. Ur majesty.. Grand ma …matar cikin mulki da nuna isa mai sanyi tayi murmushi ta dan shafa kansu Junnut tayi nuni da bahiyyya,at same time tana gayyatar ta tayi gaisuwa…har kasa kuwa ta rusuna ta gaishe da dilshad . .wanda tsaban son ta san wacece wannan din ya sata dasa mata kasaitatun idanun ta Grand ma wannan itace bahiyya,kawata ce tun muna gida chan tare da ammah Tun kan Dilshad tace ohhh sai sukaji muryan jahan khatun akansu alaman ta shigo ne unxpected ,Aina kuma lika samo ta…ta fada da wani irin muryan da bai nuna saukin kai… A dan tsorace bahiyya ta juya ta kalle ta,sai taga suna mugun kama da junnut din,babu bata lokaci ta rusuna tayi gaisuwa Wani kallon sama da kasa tayi mata kallon raini da kaskanci kafin ma ta amsa cikin wuyar ta.. Haka kawai taji yarinyar bata mata ba musamman tasa idanun hasada da kallon baki isa ba.. Nan junnut ta shiga basu labarin ta sosai,she was so excited amma sukam abun bai wani dara su ba Kaaamil ne ma yace musu ai da khaldun tazo gidan sannan dilshad tadan wayance suka dena bata cold looks shi sai ya zame ya fita zuwa site din khaldun din dan kuwa yasan ko nan ma dukan su awajen jiran sa sukeyi Junnut kuwa tuni taja bahiyyya takai ta chan sama dakin ta,its a very big apartment on its own, kalar tsarin kaya duniyan da aka zuba mata ido bazai iya tantancewa ba . A kan sharbaben tufted and heavy matress din ta suka baje,after so much conversation and happy moods.. Nan junnut take ce ma bahiyyan ai jiya suka dawo nigeria daga persia, kuma dama tana so ne idan sun huta sai taje neman ta a kaduna wajen ummah surbajo Duk abunda junnut ke ciki arayuwa na ci gaba da cikar burin ta sanda ta ayyana ma bahiya step by step,har labarin hilda bahi taji amma bata gaya mata komai akan khaldun ba Bahiyya ma ta bata labarin yadda destiny yayi da rayuwan ta zuwa gidan jahan Aarah,har junnut ta gane cewa ashe jahan Aarahn da bata taba gani ba itace uwar rikon bahiyyar ta Duk dama taji labarai munana akan jahan Aarah daga wajen su dilshad,amma sai yau taji tana son ta da bahi ta gaya mata yadda suka rike ta da amana da son gaskiya. Ashe kina london? Ai dana sani da wallhy nima chan zan koma Bahi tayi dariya tace ai na gama,shiyasa ma kika ganni anan Junnut tace nikam ban gama ba ina ganin ma kamar ban fara ba…ina first degree ne yanzu….my mum tace zanyi masters kafin nan musan nayi.. .i still wanna be that girl kinganne,irin matan nan dai da idan babu su babu duniya,kuma babu sha’ani..tana ta zuba Bahiyya tana kallon ta tana murmushi chan tace junnut Har yanzu baki ko zanca ba,Ure still that mrs ambitiuos girl.. Wani rau da ido junnut tayi ta mike tsaye tana wani juyi cikin jin dadai,tace look at me bahi ke yanzu bakijin dadin yarda rayuwar muya dawo,?ki kalli fatar jikin ki..duk dama yanzu naga kin kere ni a kyau but i do have evrything im dreaming of saura kirissssssss sauran ma jira n suke yi. Bahi tace Allah ko? Wani dariyan sukayi suka dan tafa Junnut bata damu taji maye alakan bahi da khal ba tun dama taji ance mahaifiyar sa ce tayi adopting din bahi ne ….she just assume thy are con-curent siblings babu wani connection For the main time Bahiyya taji ta cikin sabon yanayi,tace lallai Allah shike yadda yaso..if not bazata taba kawo cewa yau zata ga junnut din ta ba Anan junnut ta rike ta dam hira kala kala…kowa na fadan nashi damuwar Sirri biyu ne a tsakanin su,bahi bata fadi tayi aure ba ke junnut bakice kinada mijin aure ba Sannan A duk damuwar du da suka tada haka ma bata gaya mata ko kadan daga labarin zaman ta mai muni daya shafi sadat ko khal achan gidan Ba She was just awwed dayadda taga junnut ta dawo,ga guntun skirt cinya awaje,ga wasuxuka zukan nails da sukaji red tinted curtex..tasan dai junnut tana da dogon gashi irin nata amma kuma attchement ne akanta ayanzu. Sunfi awanni suna magana non stop,haka junnut ta matsa har bahiyyar ta yi amfani da bathrum din ta tayi wanka cikin nishadi da kewar juna suka zauna akayi serving dinsu abinci suna ci suna hira Bangaren khal kuwa gaba daya ya rasa meke masa dadi game da yawan tunanin bahiyya,..he wish zai iya jin ya tsani bahiiya amma its not feeling like it.. Yanzun haka fushi ma yake yi dakansa amma shikan sa bai sani ba He look down and angry,dandanin murmushi babu a fuska Side din dama nashi ne shikadai just like yadda yake agidan jahan mahaifiyar sa Yanzu ma Kiran ta ne ya tuno masa da cewa bahiyyar bata fa biyo bayan sa ba,. He was like ohon mata inma taje wani abu ya same ta shi babu ruwan sa. Wanka ya fada ya sauya kayan sa zuwa simple long sleev shirt da trousers,yana famar combing kansa agaban mirrror saiga kaaamil ya shigo Ba yabo ba fallasa suka gaisa.. Shikam ya rasa meyasa yaketa famar zumudi akan bahiyya… Not too long ya fara zubaa ma khal labarin duk abunda ya faru Shida baiso yanajin maganan ta amma wannan ba karamin buga masa zuciya yayi ba.. So bahi and junnut are best friends!! Ya maimaita wannan maganan a brain dinshi yafi sau goma.. Witout showing any major concern,ya amsa tambayar kaamil dake neman sanin hadin shi da bahiyyar. Sai kawai Yace masa shima hadota da ita akayi,acewar sa jahan Aaarahs adopted doter ce Kaamil was like wowww …kace ma yar uwata ce Ko kula kaaamil baiyi ba dan kuwa Ba karamin zafin yake jin aransa ba musamman inyana tuno ranar daya zage yake bada kaamil din labarin ta Cikin zuciyan shi cewa yake She is the twinkle i wanna show you..but not anymore …not eva.. I bet im not the guy Nayi nadaman bude zuciyata ma wata yarinya kuma sai ta san dawa take yi Tare suka fito dag sashen nashi kaamil na taka nashi zasu je suyi gaisuwa agaban su dilshad Hira sukeyi kadan kadan,nan yake jin cewa ai bahiyyar tana can wajen junnut so bai wani damu ba Isar su ya fada yayi gaisuwa,cikin so gata da nuna kaunar su suke tarairayan sa Shima sosai ya nuna jin dadin sa game da dawowar su nan nigeria… Musanm ma zuwan ita kakan nasu dan ita tassa shi har ya mata alkwarin cewa zai daga tafiyar sa dan ya mata kwana biyu. Dan itama tafiyar zatayi nan d wata guda Hira sukayi mai tsayi tsakanin su su hudu,basu ko kawo maganan junnut ba bare bahiyya Most of their talks is eida politcal or official har dare yayi kowa ya watse zuwa site dinsa To Kiraye kirayen jahan din ne yasa bahi ta dan matsu dataje taga inda suka sauka da mijin nata.. Ga Junnut ma ta gama sarai zasu kwana tare amma sai ta ki sam Duk dama yaune rana na farko da junnut ta taba mancewa da shafin khal kawai dan taga bahiyyar ta Nan ma da kyar suka rabu,Har nite gown mai kyau ta sa ta tasa dan dole tayi mata kwalliya ta zaunar da ita ta dada gyara mata kai tun anan suka fara musun yadda kowa yayi wayewar sa Junnut cant beliv that bahi har yau batayi irin budewar idon da ita tayi ba,…a haka dai ta hakura ta shirya akan zata raka ta zuwa site din khal Wanda ko rabin shiga basuyi ba jahan khatun ta raba su da kira She just dont like the girl,sosai ta raina kurwan bahi..wani gani gani take mata Tana mata kallon kaskanci da rainin wayo Cikin ranta tace hala ma yar bola ce aka dauko aka laka ma miji na dan tunda akace mata daga wajen jahan Aarah ta fito ta ji yarinyar sam bata mata ba Ko yanzun ma ta dade tana kallon su daga sama Kyaun bahiyyya har yana dan raxana ta. Haka kawai takejan tsaki,tsaki irin na hassada da nuna kyashi, badon ma khal ya bada oder lallai bahiyyar dashi zata zauna a site dinshi ba da chan wajen gidan baki zata sa akaita and she tot that wannan kawancen nasu a wajen ta is baseless aganin ta junnut din ta bazata taba hada hanya da kaskantatun kawaye irin wannan yar ba Bahi kuwa tsoro ma take ji in taga irin kallon d jahan khatun keyi mata .gaba daya bata do su cika hade idanun su Datakira junnut din ko ta dan hada ta da maid,haka bahi ta lallaba dakanta ta isa Akan gobe da safe duka zasu hadu Tafiy takeyi tana gode ma Allah tana kuma jin fargaban haduwar ta da khaldun Ashe wai yau ne first weding nite dinta? Tsaki ne ya kufce mata haka kawai bata san dalilin shi ba,dawowar junnut rayuwan yau ma kawai ta yasata taji wani sabon karfin gwia da karfin zuciya Wajen shiru babu kowa,amma da shike the same design ne da gidan su,babu tantama ta san wani kofar ya kamata ta shiga ta same shi Tana tabawa kuwa taji damm alaman an kulle da lock ta ciki Nan Tayi tsaye tana knocking almost 1 tana abu daya amma bata ji am bude ko an bada izinin a shigo ba Yana jin ta dan Yana zaune akan gadon sa ne yayi shiru yana fama da tunani kala kala aransa sa with each pain dayakeji shima so yake ya mata wani abunda zata ji abunda shima yake ji Ganin ta tsaya har taji ba dadi tuni Ranta ya baci ga bacci ga tsoro,chan dai wani abu ya sa ta ta zaga ta baya..aikuwa tana bullowa anan ta hango shi ta plain glass wall dake hango kan gadon sa direct wanda ya bada wajen mermaid world look mai gaba daya.. Wowwww tace aranta tana ware sleepy eyes din ta da kyau….daga dakin nashi zaka iya jan glasss ka bullo cikin backyard din room din wanda aka kawata shi da wasu marayun flowers masu gamshi da tsari gawata shekikiyar blue water pond mai shape din kwakwa white swan ne suke shawagi aciki Bata ma damu da kallon cikin room din ba tukuna ta tsaya kare ma wajen kalllo Sanda ya ishe ta sannan ta iso gaban glass wall tana kallon ciki tana neman ja dan ta shigo. Its heavy ..nauyin shi yasa ta kasa motsa shi…gashi yana da yawa sosai…2 coners ya rufe… Anan Wani zuciyar na ce mata ta masa magaña hala zai jita, but Ganin ya diro akann gado yana dosowa ta inda take yasa ta dakatawa daga kokarwar da takeyi da dooor din ta tsaya kallon shi.. Wani irin kallo suke ma juna ta glasss din as he was coming vwry closer fuskan sa babu alaman rahma.. In yana ganin ta Zuciyar sa taba masa wani irin zafi Son ta yafi rikita masa tsarin yanayin sa fiye da abunda ke tsakanin ta da subaya Ita kuwa kyau ya mata sosai,duk dama tana yar tsama da shi but ta shagala tana kallon sa cikin wani yanayi…he look soo handsome and gentle acikin white pjams din shi da bai saba sabawa ba Sai taga ya kama draw open din She tot bude mata kofar xaiyi sai ya dauke kansa tana gani yana danna wani abun god knows meyayi ma kofar amma tabbass dada kullewa yayi Yana gamawa Ko sake kallon ta baiyi ba ya koma yayi kwanciyar sa tana tsaye tana kallon shi Kwanciyar sa yayi kamar baisan da wata ba Looking at her straight in the eye ya danna wata remote tuni taga wasu shegun drapery curtain marasa nauyi suna haduwa da kansu suna neman mata katangan karfe daga kallon sa She was like,kai ka aika na zo amma ka kulle ni awaje “Wai meye nayi masa haka?cikin ranta ta furta kanta a mugun kulle…to ina zanje na kwanta gashi ko ina yayi shiru gashi batasan kowa ba Da ta tuno da junnut har ta kama hanya zata sauka chan tsoron haduwa da jahan khatun sai y dakatar ta da ita. Anan ta dawo ta nemi waje bakin pool din ta zauna cikin wani irin zurfin tunanin da vata san ya akayi yaci mata awowi ba.. ….sanyi da rairayi sune suka fara rtsata waje ya dada yayi tsit tun bata so har Ta dan jingina kanta ai kuwa batayi minti biyu ba wani bacci mai nauyin tsiya ya tafi da ita.. Da asubhain fari ta farka a firgice,dan kuwa tsaban sanyin daya ratsa ta ji take kamar hancin ta ya toshe don bata iya numfasshi da kyau Wajen ta dada karawa kallo wani irin tsoro na shiga ranta,da wuri ta mike ta koma jikin kofar still baija curtain din ba . Kamar zatayi kuka ta koma gefe ta tsaya,haka ta dinga jeka ka dawo tana leke ko zai ma ji ajikin shi,amma sai taga har gari ya waye bai waiwaye ta. She was sad and confused,dan haka tayi timing lokacin fitar sa sallah haka ta hakura ta zago yana fita ta shiga dakin Ta bincika ashe ma ba anan aka aje mata kayan ta ba To where is my room?…ko dama daya kawo nin banda daki ne… Lallabawa tayi cikin dabara irin na mata ta dauro alwala ta gabatar da sallahn safiya,bai shigo ba sai ta fice ta shiga duba kayan ta dakuna uku ne asite din da kyar ta samo wanda kayan nata ke ciki Ohh Ahamdullhi,ta fada tana zama agefen sharbeben bed din,aranta tana cewa ai da ta san haka ne da ko kadan bazata kusa da inda yake ba Nan tayi wanka ta saka normal material gown na wata lush material Mayafin shi tayi rolling akanta sannan ta samu damar fitowa Allah ya taimaka ta gane hanyar dakin junnut toh babu bata lokaci ta nufi wajen its 8.00am inthe mrning amma tayi knocking shiru Sai can anjima aka zo aka bude mata kofar,…junnut din ne atsaye sanye da wata figigjyar nity alaman ma bata ko tashi a baccin ta ba bare tayi sallah Da har ta dago da fuskan rashin mutunci but dataga bahiyar tane tuni ta ware ta jawo ta ciki Bayan Kare ma dakin kallo bahi tace “Kar kice min baki ma tashi? Kinsan karfe nawa ne kuwa yanzu Junnut tace Ohhh bahi,I know….nifa bana tashi sai 10 ….dokace… Dan ma kene wallhy Da sassafen nan mai takurani ai sai angan shi Haka suka tsaya musu,bahi is shock again dajin yadda junnut take nuna bata wani damu da sallan safiya ba,abun ya dan daga mata hankali Is this part of wayewar?koko wani abu ne daban ya juya mata kan junnut din ta. Anan dai suka karace zaman su,har junnut tayi wanka ta shirya suka ci first breakfast which is always a hot coffe Ko wani fresh prepared juice . Gamawar su keda wiya aka aiko da cewa su fito main parlour After like 30 minutes suka fito Tafiya sukeyi atare bahiyya nakan korafi akan kayan da junnut ta sa Wani cross fold half gown ne mai tsiririn hannu,daga wuya zuwa nonuwar ta gaba daya abude suke Infact wani sabon gyaran gashin dokin ta zuba shi ta baya platinum kamar wata lady gaga ,kafarta yaci ubar 5inches sandal ga make up bakin ya haska da red matte lipstick tsadadde Tace bahi Nidai ki kyale ni da wa’azin kin nan,babu abunda zaki fahimta Thank god Agidan mu kika sauka,we will definatley sort it Kema dole zaki dena wannan dresing din Bahi har kallon ta take Intana magana tana juya mata ido cikin kadadi,dan kuwa wani tsaban rigima junnut ta ke ji dashi A dai dai zasu shiga fadar wasu maids suka taho kowa na binsu da gaisuwa Mamakin yadda junnut take binsu da kallon wulakanci da kaskanci still yasa bahi mamaki most time sai Tace junnut why? Ita kuwa junnut Sai ta juyo tadan mata ido irin Shusssh dont say anything gaban wayannan kaxaman zasu raina ni. Haka ta ja ta suka shiga cikin palour Dilshad ne a babban kujeran ita daya sai jahan khatun gefen ta Kaamil da khaldun suma a kujera daya suka zauna duka sanye suke da suit din valentino garavani Wani kallon ya kare ma hannun junnut dake rike da na bahiyya ayayin da suka durkufa suna gaisuwa Sai yanzu ya amince da zancen kawancen nasu ya lura duk yadda su dilshd suke bada cold attitude ma bahi junnut bata gani dan kuwa da alaman yau a sama take jin kanra Ga khaldun ga bahiyya ga junnut Duk wani kwarewer kwaliyar junnut mashi tayi Anma Da shike kaamil ne a kusa da shi sai ta koma inda bahiyya take itama ta zauna babu avunda take sai kallon shi Baimaa kula ta ba bahi kam da bata son daga kai She remain queit for some moment Bata dago ba sanda taji jahan khatun tana tambayar sa directly akan ta Bai wani bata lokaci ba ya mata bayanin cewa adopted doter mum dinshi ne..duk da ma bai shiga deep ya mata bayanai ba bangaren bahiyya tasha mamakin sa So he is serious about this secret weding stuff? Wato bazai fada ma familishi ni matar sa bace ko?. Junnut ce tayi masa introducing bahi as kawarta good kawai yace kaamil na dan saka musu baki Cikin haka sai taji junnut din tana kawo masa hirarrki tana masa tambayoyi wanda bata gane gansu ba Baicika son amsa shirmen ta ba amma sabida ya zantar da abunda ke mind dinshi agame da bahi ya sa ya dan sake yana biye mata har su jhan khatun suka ji dadi aransu Toh Bayan sun fita falon zaaje cin abincin safiya To shi khal baya cin abinci da kowa kowa yasan da haka. Junnut kuwa ganin an ragu sai ta jawo shi ta kuma jawo bahiyyar har gabansa tace nasan kinsan shi ko?bahi tayi karamin yake tana kauce ma kallon dayake mata…duk dama bai sake fuskan sa ba Tace dama zan gaya maki tun jiya but no time…i just want to u to oficially meet my future husband tayi nuni dashi tace shine wannan….Ina gama schol Shi zan aura we are engaged Da Wani irin kallon bazata mai tafe da bugun zuciya bahi ta kalle ta tace you…rrr future husband?…bata san sanda muryan ta yayi rawan ba1 junnut tace eh tana gyada mata kai tana murmushi Wani zufa take taji na saukka mata ta ciki Da kyar ta iya furta mata congrats dan Wani mugun faduwan gaba da wani irin ciwon kai su suka taso mata idanun ta dakansu suna rufuwa ,da kyar ma ta bar zuciyan ta harya barta ta daure ta dago ido ta kalle shi dan taga reaction dinshi ko zataji yace wani abu Suna kuwa hade ido Ya dauke kansa ya zame ya bar wajen Junnut tace mata shall we? Ganin idon mutane akansu yasa ta danne firgicin dake idanun ta suka tafi kan dinning din Bata wani iya cin abincin ba,duk dama kaamil is tryn his best yaga ta sake Bayn sun kammala kaamil yayi excusing dinsu ya tafi wajen khal ita kuma junnut ta ja bahi sukaje daki Bata lura da yadda bahi ta sauya atake ta dawo shiru shiru jikin ta a sanyaye ba Zama tayi tana bata labarin engagement din ta da khal from the start tana gaya mata yadda ma tafara son shi tun bata gansa a reality ba Abu daya ne bata gaya mata sabida bayan hilda da kaamil bata so kowa yasan damuwar ta akan khal All she want now shine ta bayyana shi wa bahi ta sigar da zata san tayi dace da cikakken namiji So she lied alot akan yana matukar son ta,har zuwan ta gidan shi a us ta shafa mata Cahn dai data ga kamar bahi tayi sanyi sai Tace bahi kina tamin shiru,ko dai mijin nawa baiyi maki bane Bahi dake jin kanta kamar acikin wuta bata ma iya yin kwakwarn murmushin ba,da kyar tace mata yayi Junnut kuwa sai labari take tana dada gwada shi …..dan shiruuuu bahi tayi cikin rudanin zuci,ganin bazata iyaba tace junnut pls can you excuse me? Tun kan junnut ta bude baki ta tambaye ta ina zata je tayi sauri ta isa bakin door ta bar dakin site dinsun ta nufa cikin sauri tana shiga dakin ta ta zube akasa wani irin azaban kuka ne ya kufce mata mai dauke da radadin kishi da zafin soyayya. Wani shakurarren kuka mai kakarin rudewa ta fashe dashi duk jikin ta sai da ya dauki rawa.. Dafe kirjin ta tayi cikin numfasawa tana furta innalihhi wa inna ilaihi rajiun Tsaban bugu catake zuciyan ta zai fito daga kirjin ta,ji tayi kwalwwlkta na ce mata komai ma mafarki ne. Dan Har yanzu Ta kasa yarda da cewa abu daya suke so ita da junnut din ta,”dama ashe har sa’ood yana son wata?…to what about me?i truly loved himm hala shiyasa yake wasa da hankali na, bai ma taba jin nayi masa ba,..but why junnut…why my besfriend, meyasa zuciyata ta zata so abunda kike so kuma yake sonki. Dan pause tayi tana jan numfashi idanun ta gaba daya sunyi jazir..yace ya aure ni,amma yaki yace ni matar sace?..,bisa ga abubuwan da junnut tace mata ayau..ba tantama ta kawo cewa maybe suna matukar son juna…maybe he dosnt even want hurt junnut for my sake.. Kuka kawai takeyi tana birgima akan floor cikin tsananin tausayin kanta Tayi ta maganganu daban daban amma bakin ta ya kasa furta mata mafita guda daya akan lamarin What is even upseting her more bai wuce wani azaban wutar kishin sa datake ji ba…abun ya mata yawa har taba mamakin kanta Ji takeyi kamar bazata taba iya hakura da son shi ba Dan ance junnut zai aura,bai fi damun ta kamar yadda junnut din take bada labarin sa ba Ayanzu Wani Haushin sa takeji kuma tasan son shi da mummun kishin san suke tada mata haka Takune kanta tayi akasa a tsakar dakin cikin kunci ta ta kife kanta da gwiwa feeling so lost and confused Tunani takeyi ko zata iya rayuwar ta acikin su a haka? Beside bata san me yasa ya aure tan ba Wasu hawayen ke sauko mata,sad and trembling voice dinta yake cewa In har junnut ce ka zaba tuntuni why did u marry me?wai ko ce masa akayi ne ina sonshi yake neman wulkantani?… To wazai fada masa sirri na?…is that why he call me cheap…in zata iya tunawa babu wanda yasani daga sadat dai sai su jasmine su kadai suka san yadda take kaunar khaldun Tace gaskiya bazan iya hada miji da junnut ba,tunda yace ai ba so na yake ba why not ni ka sake ni na koma gida nayi rayuwa ta?..But can she? a take wani zuciyar yace mata meyasa bakiyi tunanin haka tuntuni ba sanda kikaji maganan kishiya,kin amince kin zama matar sa duk da abunda yake gaya maki,to kenan zaki sadaukar da mijin ki sabida yayi alkawari da wata? Dan Shiru tayi tana duba da lamarin can ta jingina kanta da bango slowly ta runtse idanun ta.. Tasan dai har yanzu khaldun shine abu mafi soyuwa aranta wanda take ganin kamar rabuwa dashi abu ne wanda zai iya mugun azabtar da ita. Sannan A Duniya tasan junnut ta fi karfin komai awajen ta,not even a guy that is mistreating her feeling,bisa ga maganganun junnut na dazu a yanzu kam ta amince khal ba ta ita yake ba,to ita ma me zatayi da shi? Gani take kamar itace matsalan yanzu data kwallafa shi aranta Tace Ko ma ta fada ma junnut komai ne dan suyi shawaran yadda zata rabu mata dashi kowa ya huta?. Ayanzu gaskiyar ta shine Tasan bazata iya hada kishi da junnut din ta ba kuma tasan bazata taba iya daurewa akan soyayyar shi ba… What a strange world..tayi ta juya tunani,ta bada kwalwalta dalilai amma har yanzu dai bata gane komai ba Takance dama ace banyi aure shi ba da sai ince zan yanke wani hukuncin na daban Shiru dai tayi tana maganan zuci,a hankali tana sauke ajiyan zuciya…Ganin kamar numfashin ta na neman daukewa sai tayi saurin sulalewa ta mike kafafun ta akan floor din tayi tsam da idanun ta na aikin zubar da rudaddun kwallla A duk tunanin datayi sai take Jin kwakwaltar kamar shirme yake mata She is in extreme shock and pain,bata ma san lokacin da wani hutaccen bacci yayi awon gaba da ita ba. Bangaren khal kuwa haka kawai ransa ya bashi cewa duk inda bahi take ayanzu tana cikin rudani dan yasan bazata ji dadin abun ba Shikam yasan yana son ta,kuma Duk da abubuwan da yake faruwa har yanzu bai cire rai ba Yasan xai iya yuwa itama tana son shi,sanin hakan ne yafi tasiri aransa fiye da duk wani laifin datayi masa . kuma Yana da yaqinin da wata na dabance ba junnut ba da abun zai zo mata da sauki,but her best friend?. yasan is not gonna be easy for her to asimilite…toh a duk da yana tuno hakan amma yake tursasa zuciyan sa jin dadin da hakan ya faru da ita Gani yake wannan al’amarin shi zai rama ma kanwar shi azaban da ta dandana mata akan sadat somehow Dama shi da kaamil ne awajen to da junnut ta iso sai ya share su ya tsunduma kanshi gaba daya cikin tunanin bahiiyar sa baiya ma sauraran hirar su Kaaamil is so intrested in her,dan tun daya ganta zuciyar sa take faman harbawa Koda junnut tazo wajen ma hirar bahi kawai sukeyi Khal Jin tace ma kaamil ai hira sukeyi bahin tayi excusing dinta ta tafi tuni sai yaji zuciyar sa ta amsa Ba bata lokaci ya xame ya wuce bai tsaya ko ina ba sai site din sa sauri yake kamar wanda ake tunzira shi,bude kofar dakin ta yayi da sauri daga idanun shi ke dawuya ya hango ta dunkule akasa tayi laushi har abun tausayi hawaye sun gama bushewan su akan kuncin ta Dan karamin ajiyan zuciya ya sauke Ya dafe kansa….”Mixed feelings na damuwar ganin ta Ahakan da wanda yake so ya ji na dadi daya ganta hakan duk su suka dama zuciyan shi…” Kallon yanayin ta ya tsaya yi almost 20minut bai daga idon shi ba,dan kuwa ba sai angaya mashi meyafaru da ita ba jikin shi sosai ya bashi halin datake ciki Sai yace Duk dama amanar wata take shirin ci now she is jelous dan ance ina tare da kawar ta ..what is wrong with dis girl,ya dada kare mata kallo…xuciya nawa take da shi?Allah ya tsine ma zuciyar da zai so ni ya so wani wawa kamar sadat Daure fuskn sa ya dadayi Har wani kikkifta ido yake yana Kallon ta Shi sam bai fahimce ta *** Farkawan ta ke da wuya suka hade ido dashi amma bata tashi akan floor din ba ta lafe Wani kallo suka maida ma juna yana binta da wasu zafafan harara fuskan sa a daure Itama Hade rai tayi cikin jin kishin sa tana mutsuka ido tana dan turo baki a shagwabe sosai taji dadin ganinshi akanta…. “..Yace Whats all this?…baki da hankali ne zaki kwanta ma mutane akasa…will u get up before i crush you.. Wani share sa tayi,tana dan kau da kai maganganun da suke wanzuwa azuciyar ta su suka fi dauke mata hankali har ya tashi ya fita waje bata ma sani ba yana dawowa kuwa wani shahhhh taji ana gwaro mata ruwan sanyi tun daga kan tsakar kanta har cikin jikin ta A mugun fusace ta mike tana huci ruwan na bin fuskanta mikewa tsaye tayi zumbut har ta hayyako zatayi magana ya wani daka mata tsawa yace… “…Ina wasa dake ne da zanyi maki magana ki zauna ki namin shiru,ni sa’ar ki ne? Wani kuka ta fashe masa dashi Tace ina ruwan ka dani? Shiru yayi ya kure ta da ido tana famar komar da kukan amma Wasu sabbin hawaye ne suke sauko mata dan Tsaban fushi bata san sanda tace masa hakan ba.. Yace ohhhh,to doka ne ba a kwanciya min akan floor dina Duk randa kika sake kwanciyar sai na karya kafarki4 Ciikin kakarin kukan Tace ai ba dakin kaba ne sai ka fita.. Bai kulata ba yace ni dai na fada maki,kar na sake ganin ki a kasan flooor dina Unless u want me to trow out. ” wani harara ta jefa mashi A dan fusace ta dago cryn balls din ta cikin sanyin murya mai nuna firgici tace mashi throw me out now…ni wallhy nagaji..i just want to go home Ai ni bance ina son zama da kai ba Shiru yayi cikin hade rai yanajin ta sanda ta gama maganganun nata kafin ya matso kusa yasa hannu ya jawo ta Har gabansa kamar wanda yake shirin cakumo ta… “U aint going anywhere,gidan nan shine prison dinki.. Zaki ta zama dani har sai na auri kawar ki,she is the only one i want…2 ..ke Baki da amfanin komai,and dont you dare say ure my wife to her dan nikam nafi karfin ki Ko kallon shi batayi ba,A duk abunda yace “sai na aure kawar kin shiyafi mata zafi”hannun ta take shirin kwacewa ya ki ya sakar mata,..wani Cizo ta danna masa a hannun A mugun fusace ta shiga firgici zata kwace jikin ta daga nashi,shikuwa bai sake tan ba sanda ya gama karance duk wani hawayen dake sauka akan fuskan ta yasan wannan duk borin kishin sa ne…dan yau ne ranar daya fara jin tana maida masa magana cikin fushi da firgici Shikansa ayanzu ta gama ruda masa tunani,dan kuwa balain son shi da kishin sa yake hangowa a yanayin ta just like shikadai ne a zuciyan ta babu wani3 Cikin ranshi sai yace wai kam Ba sadat take so ba?meyasa take fushi dan ni nace zan aure kawarta,wato ashe ba dadi take iya ma wasu? Wani murmushin mugun ta yayi aransa yace ai Allah ne ya kama ki”da zan iya gaya maki laifin ki amma duk abunda zai faru dake shine dai dai ke..very stupid girl sai ya sake ta ya futa abunsa. Itakam Kuka ta cigaba dayi,daga nan tunda ta wanke fuskanta sai bata sake lekowa tsakar gidan ba Har sanda tayi kwana biyu masu kyau a dakin ta bata kuma kira kowa ba. Dama in bawai ta fito bane babu mai shigowa site dinsa dan haka bata sha mamakin da taga ko junnut bata leko ta ba Wani bin in ta zauna har mamakin kanta take yi sosai,a duk sanda taji zimman cewa zata yanke hukuncin gaya ma junnut komai toh wani azaban fargaban rasa shi da kishin sa shi yake saurin danneta Most times sai taga kamar ma babu amfanin soyayya ko auren da ke tsakanin ta da khaldun amma har yau ta kasa bari zuciyar ta ya cika furtawa mata hakan bare kuma ta kai maganan gaba Sosai sonshi yayi nisa acikin ranta har ya zame mata numfashi da abinci ma ruhin ta Washe garin yau bata jin daidai ajikin ta, amma sai ta daure ta fito dan su hadu da junnut din ta..hira kadan sukayi Junnut tace dana ga kwana biyu baki fito ba sai nayi tunanin na barki ki huta kawai Most time bahi sai dai tayi murmushi Dan inta kalle junnut bata iya daurewa …sai taga ko magana mai tsayi bata cika son yi da ita,..gaba daya ta dawo wata shiru shiru komai tana yi ne tana dan jan baya akai ita kuwa junnut sai rawan kai take xuba mata surutai Ita kuwa bahiyya A duk zumudin sake haduwa da aminiyar ta datayi bata kawo cewa cikin sauki zataji komai ya fita mata akai har haka ba.. Domin kuwa iya daurewa da nazari tanayi amma har yanxu bata gane kan komai ba sai ma dada rudewa da tunanin su yake sa takeyi Bangaren khaldun kuwa duk yana sa idon sa akanta a boye amma bata san da haka ba Aranshi Yakanji ya takura ma rayuwar ta akan junnut tunda yaga kishi na damun ta sosai.. amma idan ya kalle yanayin tarin hadarin son data ke masa a kwayar idanun ta sai yaji gaba daya jikin shi yayi sanyi da al’amarin..game da subaya da sadat yasan tayi ma zuciyar shi laifi..but he stil respect that kowani dan adam yana da ra’ayin shi akan wanda zaiso da wanda bazai so ba Yana matukar kaunar ta yar hanzu….He hate those tears …he feel that bazai iya cigaba da dauriyar ganin ta ahaka ba duk dama laifin datayi ma zuciyan san is still unforgivable. And Besides ya tsani raini,kuma Baijin zai iya cigaba da sai insa da ita bare ya gaya mata sirrin zuciyar sa Dan a kwana biyun ya lura yaga cewa gaba daya mood din ta ba adaida yake ba Hakan ya dada sawa yayi watsi da tsabgar ta bata ma ganin shi sosai a hidima gidan amma shi yana lura da ita sosai Kaamil da junnut din dai suke kokarin debe mata kewa duk dama kwata kwata yanzu mind din ta baya wajen su duka Ita ayanzu Tafi tunanin yadda zata fuskance al’amarin,shin zata daure ta gaya ma junnut komai ne koko zata nemi mafita ta wani wajen. Akan hakan ma ta kira dija yafi sau agirga amma ta kasa gaya mata asalin meke damun ta,gashi har yau subaya taki daukar wayar ta bare suyi magana,kuma duk sanda suka hadu da junut har ta kawo mata maganan khaldun din ta toh bata iya yin bacci mai dadi Wani bin ta dinga kuka kenan A Haka rayuwar ta kasance mata na har kusan sati biyu sannan ta fara jin sassauci aranta musamamman data gane cewa ayanzu bata da wani madogara face ta bar ma Allah komai. Idan tayi wani tunani sai taga kamar bazata iya zuba ido taga komai na tafiya a lullube ba,duk dama yanzu kam junnut ta cike mata brain da karerayi akan soyayyar su da khal But tunda ta dan aje hankalin ta waje guda ta soma lura da banbancin lafuzan junnut da na kaamil akan abun sosai sai ta fara gane cewa kamar abun duk daya ne babu wani banbanci. . dada nitsuwar datayi sosai yasa ta gane cewa wasu zantukan junnut din duka karya ne Hakan ya fara bata karfin gwiwa har ta dena jin karfin cutarwan lafuzan ta a zuciyar ta kusan kowani lokaci Gashi ta gama lura ayanzu kamar rayuwar su ya dada banbanta,dan babu yadda batayi da junnut ta dena saka guntayen kaya tana yawo agidan ba amma haka sam taki.. Ita tunda khal ya sa tayi islamiya a london ta gane cewa ko wata mace a duniya kamar sarauniya ce,yaanzu ita dakanta ma bata son cika barin jikin ta abude haka kawai… Junnut Takan dai ce mata bahiyyya ke kam bazaki taba wayewa ba,tunda kika zo gidan kike lullebe kanki kamar wata kwai…bazaki sa kaya kisha iska ba?wasu designers din are terrible Design dinsu is alwys revealing amma dan dai tasan su din ta saka bata damuwa da yanayin tsarin su Shikuwa kaaamil yanayin bambancin tarbiyan su yana daya daga cikin abunda yake sa shi yake jin bahiyya na burge sa sosai. Ya lura duk iya surutun junnut da tsiyar d zatayi ma bahiyya,bahi taki sam ta biye mata akan irin sabbin tsarin rayuwar da ta debo makanta. Ana cikin haka washe gari da safe bahi ta farka da niyyar zata kai ziyara ma dija dan kuwa tunda ta karbe adress din bata bude ba sai yau Sanye take da hot pink nitie ta sake suman kanta duka sun zubo mata a baya ganin safiya yayi yawa ba lallai akawo mata abincin akan lokaci ba yasa ta shiga private kitchen dinshi ta shiga dora indomie Wani irin hadin alfarma takeyi ma indomie yana ta zuba qamshi an shake shi da ingredient kala kala tamkar ba ciki za’a kaishi ba Tanayi ne tana tunanin masoyin ta,musamman take so ace yaci ko da zata ji dadi aranta for once Dan haka Bayan ta kammala tayi serving a plate sai ta gangaro tabiyo ta kofar dakinsa,tafi minti biyar a kofar dakin batayi knocking ba kuma bata ce uffan ba.. Har Fargaba yasa taji ta juya kawai ta bar wajen,one step ta kara sai taji kyat an bude kofar dakin daga bayan ta Wani gafff taji kirjin ta ya amsa,a dan sadade ta juyo ta gama daukawa shi zata gani kawai sai suka hade ido da junnut,… Saurin dakewa tayi ta tsaya…She cant hide the remorseful look dan ko murmushi ta kasa mayar mata,ita kuwa junnut sanda ta gama kare mata kallo sannan tace bahi?me kike yi anan haka..tayi mata maganan ne tana kallon dresing din ta Irin kofar dakin husban to be dina ne kike zuwa mashi da hot nity?4 Junnut Batayi tsammani ba sai taji bahi ta mayar mata da irin tambayar,tana cewa ke me yakawo ki nan din,im suprised..naga baki tashi da sassafe sai 10 ko… Tace ohhhhh dear,bari kawai khal ne fa..kinga wai miji zaiyi tafiya shine nazo muyi ban kwana kinga ma har ya tafi ya barni a dakin ban sani ba… Wabi shiru Bahi tayi dan bata san sanda ta daure fuskan ta ba,tana jin duk surutun junnut din amma bata sake cewa uffan ba Imagining takeyi cewa ita da suke shashi daya tayi kwana biyu kenan bata ganin sa amma sai yau junnut ne zata gaya mata cewa yayi tafiya? And what is chocking her up bai wuce cewa da junnut tayi tazo wajen sa har cikin dakin nasa ba. Ita sam bata ji dadin haka ba,duk dama bata taba ganin junnut a site din ba yau kishi ya sataji kamar dama idan tana daki junnut din takan shigo wajen sa ma bata sani ba. Wucewa kawai tayi ta nemi waje ta zauna cikin danne zuciya ta bude abincin ta fara ci a tsanake kamar bata damu ba,but Tsaban bata jin dai dai ko tayin abincin bata mata junnut din ne tagaji ta sa hannu suka karasa ci tare.. Da ta dan kawo hirar iyayen sun ne ma bahi ta sake nata fuska ta sa baki,.junnut ke cewa ai abincin bahin har yau babu maraban shi da na mahaifiyar ta… Bayan sun gama cin indomien,wayar junnut tayi kara sai ta fita tayi excusing dinta Daga nan wanka ta fada ta yi alwala tayi karatun qurani haka kawai dan ta rage zafin kishib datake ji aranta game da kawar ta wanda bata san da shi ba Wani bin takan rasa gane dalilin daya sa ta kwallafa gayen da bai damu da ita ba .. Tasan dai Allah yana jin kukan ta Amma rashin samun sassauci akan son data ke mashi yasa ta dadajin ta bar ma Allah komai Dan kadan ta tattale fuskan ta da make up,ta shafa turare marar karfi Riga da skirt tasa na plain ember sai ta dora kakkauran bakar kimono jacket ta rufe sumar kanta gaba daya da veil shima baki… Fitowar ta ke da wiya suja hade da kaamil,waya yake yi amma daya ganta sai ya dakata ya iso har inda take yana yaba dresing dinta Takan ji kunyarshi sosai duk dama most times dan yasa ta magana yake damun ta he has a great sense of humor ..ya iya barkwanci da salon sace zuciyar mata Ita kam bata jin komai akansa,ta kan dauka dai khal shine nadaban acikin yan uwanshi,subaya da kaamil duk taga basu da daure fuska Sai da suka zauna Tace masa ina junnut take? Sai yace mata tana daki tana shiryawa kinsan kawarta zata kawo mata ziyara Tace hilda? Yace ehh…thank god kinsan ta ai dana baki labarin ta bata da maraba da kawar ki .. Sa tayi murmushi batace komai ba… Yana ta kallon ta…chan yace mata yaushe zamuje…tace ina? Yace waje…i want to take you out….ko kin fiso kita zama a gida..gwara mu muna ganin mutane am sure babu ko irin maids din nan a shashen bro..aint u bored? A hankali Ta girgiza masa kai tace no am ok….cikin gwalo ido ya taso zaiyi magana to karar takalmin junnut ya dakatar da su. Duka suka maida kallon su kanta sai langwasa takeyi tasha white dolce and gabana suit ya mata kyau bana wasa ba Ita kanta bahi bata san ko kallon kishi tayi mata kona jin takaicin irin wayewar junnut din ba …right now she dosnt even look like a muslim girl. Tace me kuke fada baku jira ni ba? Kaaamil ya tabe baki.. .yace yawwa kizo kisa mun baki ko hajiya kawar ki zata amince muje mu sha iska. Zama junnut tayi tna kallon bahiyyar,cikin raha tace hajiya bahi… Bahi Tasan da lullubin ta take yi Sai sukayi Dariya…cikin shagwabben yanayi tace junnut ni fa ki kyale ni Wani dariya junnut din tayi tace nikam na shiga uku,kay kaga tun ban yi korafi ba harta gane me zance..kaga dai bahiiya sam taki ta dena shake jikin ta da kaya..nikam ko aure kike so ne..? Duka suka yu dariya…kaamil yace no its good like this nidai tayi min a hakan,chic nd beutiful… Junnut tace whaat tayi maka ahakan? Tabbb di..wallhy gwara ma ka cire “makan nan” she is mine…u have to pass trou me kafin ka isa gaban bahi Ita dai batace uffan ba,murmushin dake fuskan ta kaamil yake ta satan kallo suna musu da junnut akan ta,shi yana ta yabawa junnut kuma tana komarin gano asalin nufinshi akan bahiyya Har yace shi daga yanzu ma bazai iya kira sunan bahiyya ba cos he feel she is special…abun dai a wasa suka dauke shi. . Da kyar yasa su suka amsa akan zai kaisu shan ice cream sabida sudan zaga garin abuja su su sha iska Anan Sanda suka jira shi ya sauya dressing dinsa yayi kyau shima sosai.. Ba yadda junnut batayi da bahi akan ko jeans tasa ba amma taki sam Haka kawai take jin kamar in tasa ta fita mijin ta zai ganta da shi duk dama junnut ta gaya mata baya gari but she just cant…tasan ai baya son ganin ta hakan1 Su uku suka fito sunyi kyau kaamil yana tuja su a cikin wata katuwar bmw jeep formated. Junnut ce uwar surutu,kowa na ta fadan albarkacin bakin sa akan tsarin garin abuja har suka isa babban shoping mall,Inda kaamil da bahi suke zagawa suna hira jifa jifa Ita kuwa Junnut ta tsaya amsa wayar hilda ata bayan su. Bayan sun fito wajaje daban daban kamil yake ta yawo dasu suna zagawa suna nishadi ,selfies,swings..mad talks… Dan dariyar da tayi tayi Gaba daya sai ya sake jefa ta cikin wani halin tunanin khaldun Gashi ta fara ganewa Da alaman kaamil ya aje wani special request azuciyan shi game da ita duk dama bata yi saurin kawowa soyayya bane A fannin shi It seeems like tayi mashi sosai amma kamun kanta da banbancin ta dasauran matan daya saba gani yasa baida option din furtawa kai tsaye sai yake dai nuna mata a dan wasar da sukeyi Just for the fun…anma har ya fara kiran ta da suna”cupcake” .4 Junnut na dake dan lura takance dashi sai fa ka biya kudi sosai…wannan tsada gare ta. Su biyun sun gane so ne amma bahi bata dauki abun da tsanani ba… Toh Da sukaje amusement park ma abubuwan sun fi daga mata Hankalin ta Wani abun idan kaaamil yana mata Gaba daya tunanin khaldun shi yake dawo mata na tun ranar da yazo london ya cire ta acikin kuncin datake ciki na rana guda,wanda har yau takasa mancewa da shi. Har yanzu bata ga abu mai saurin yaye mata damuwar ta kamar shi ba.. “..Shikuwa kaamil in yaga ta bata shiru cikin tunanin tana kallon site dinshi yakan dauka ko ya burge ta ne sai yaji dadi aransa A haka har ta gaji da abubuwan dayake mata na neman burgeta,ta koma shiru ko tana yawan jan jan musu aji Basu sani ba ita yawon nasu a hakan tuno mata memories din khal kawai yake yi,she become all rosy acikin zuciyar ta har tanaji kamar babu abunda ya faru tsakanin ta dashi3 Wajen diving zasu ce,kuma shine last wasan da suka yi da khal lokacin dayazo london graduation din ta..! Takan tuno da yadda suka zauna daf da daf hannun shi akan nata with all the smiles on her face..sai taji kawai bazata iya sake maimaita hakan da kaaamil kowani namiji ba.. To daga cewa zata je washroom sai ta zame ta barsu..bata san ko ina garin abuja ba Da taimakon waya da adresss aka kaita har kofar gidan su dija Its a huge flat,a anguwa mai suna osokoro ba tantama tasan dija dama ba yar talakawa bace tun fil azal Dija ta nuna farin cikin ganin ta sosai sanda itama taji sabon nishadi ya mamaye ta,dan ma kar su junnut su neme ta sai ta sa wayar ta a silent Hira sukayi for 2hrs dan gidan babu kowa mahaifiyar dija busy woman ce yar kasuwa ce sosai Kuma mahaifin ta ya rasu da dadewa. Bayan sunci abinci sunyi dam, Da kamar zata gaya ma dija abunda suke ciki da kawar ta junnut but Ganin kirar su kaamil yayi yawa sai ta mike tace ma dija ni zan koma Dija tace ah’a kam..yaushe kika zo…ko oga ne yake ta kira naga kina ignoring calls dinki Tace ahh bashi bane..ai naji ance yayi tafiya ma..bata san ma hakan tace ba dija ta kure ta da ido tana jin mitar ta Sauke ajiyan zuciya dija tayi dan babu boye boye tasan bahiyya is not ok with her life har yanzu kuma agaskiya tana mugun son taga tana taimaka mata Tace ance maki baya nan kuma?ba auren kikeyi ba?dont tell me Har yanzu bakuyi setling issures dinku ba..? Sai tayi shiru… alaman ma ta rasa mema zatace Ma dijan2 Dija tace bahi?baki tambaye shi kinji laifin da kikayi masa ba ko? .. .kinsan dai haka kawai mutum bazai zanza maki ba..sooo wont u talk to him?ko kin masa shiru ne har yau kina ta famar wahalar dakan ki.. i know u enjoy doing that”mrs zurfin ciki…in zaki ji ni kiji ni, wata rana zaki kashe kanki am telling u Duk dama dija bata sa fushi ko fada akan maganan ba amma Wasu siraran hawaye taji suna neman taruwa cikin idanun ta,kuma gashi tasan bata da lokacin dogon magana shes sure duk inda su junnut suke ayanzu sun damu.. kawai sai ta mike tace dija, ni zan tafi kawai Idan ya dawo zan tambaye shi sai inzo miki we wll talk about it. Cike da nuna damuwa dija tace no way…babu wani jira a lamarin nan bahi Nidai kawai kice kin min alkawari zaki je yau din nan ko ta phone ne ki tambaye shi matsalar, if not bazan barki ki tafi ba sai kin gaya min komai.. Adan dame tace me zan gaya maki dija…ni wallhy bansan mena masa ba..he is angry at me..fada yake mun in na tambaye shi, and he said that wai gidan shi ne prison dina kuma saiya aure ta…wani hawaye ne suka sauko mata a bazata muryan ya har yana shaking Cike da mamaki Dija tace saiya aure ta?wacecce kenan Sai tayi shiru tana goge hawayen ta kamar dama bata so ta firta kalaman ta ba.. Dija ta sake maimaita tambayar tace Bahi dama akwai wata Ne bayan ke?.. Data dago ido ta kalle dijan sai taji kamar bazata iya boye mata komai ba Komawa tayi ta zauna a Slow ta dan kife kan ta akan gwiwar ta ta sake ajiyan zuciya.. Cikin sanyin jiki ta gaya mata halin data ke ciki bata rage mata komai ba… Tace dija junnut ce fa?..babban kawata.. aminiya tace..ta yaya zanyi zaman kishi da ita kuma fa cewa yayi zai aure ta mu zauna tare. Ni walllhy in ya aure ta bansan yaya zan yi da rayuwa ta ba Kar kiga yadda take son shi,kullum sai ta min tadin shi .. Wallhy yau ji nayi kamar na mutu dana ganta ta fito a dakin shi duk dama dai tace min wai baya nan I think bazan iya daurewa ba..dija, inajin kishin sa sosai har bansan ko zan iya sadaukar da son shi ma wata ba.. Dija sai ta bace shiru tana kallon ta…cikin zurfin tunani dan bata ma iya cewa komai ba “..Dama tasha jin labarin junnut a bakin bahi amma bata san complication din da zai zo ya shiga tsakanin su ba bake nan idan sun hadu. Gaban ta dawo ta dan rusuna ta riko hannayen ta tana mai tausaya mata har cikin ranta,its sadat before and now she has to deal with her love and her best friend.. Tace bahi,kinga abun da nake ji maki tsoron ko?.. Illar shirun da kikayi ta masa har kuka kai wannan lokacin baki matsa kinsan akan me yake fushi dake akai ba yanzu shi zai dada jawo maki hanyoyin daban daban na shan wahala.. U have to act fast Bahiyya,u need to talk to him ai mijin kine..nidai nasan bazaki iya zaman nan kina fada da miji kuma agefe ga kishiya ba,kishiyar ma kuma kawar ki,… …nidai am sure oga yana sonki kamar yarda kike son shi.. nifa tun time din da baki da lpya nagane irin son da kike masa shi yake maki But i think Something is wrong somewhere..kinyi kuskure da kika zauna baki matsa shi ya gaya maki ba..u cant go on like this..for how long? Indai kuma akan kawar kin ne kike ganin ya zanca,ni shawarar da zan baki shine ki nitsu ki bar ma Allah komai Pls Kar ki cutar da kanki wajen tunanin zaki bar mata abunda ranki yake so,everything is fair in love and war . Tana iya nata kema kiyi naki dan kuna son abu daya ai ba haramun bane.. ..gashi aure ne yanzu a tsakanin ki dashi ba wai ba…its happens..ki dauka ai bake kadai bace kike facing irin wannan coincedence din. Kiyi ta addua bahi..ki dage kinji …bahi tace toh dija.. Dijan ta sauke ajiyan numfashi Tce..yanzu muje in raka ki…ni wallhy jiki na duk yayi sanyi ..amma idan na yi tunani mai zurfi zamu karasa maganan kinji?. Bahi ta share guntun tears din ta dake shirin sauka tace its ok…a hankali ta furta nagane kuskure na . Dija tana ta kallon ta batace mata komai ba mikewa tayi sai ta dauki wayar ta tayi dialing number junnut,as expected bugu daya aka dauka…helllo. Da farko taji muryan junnut din sai kuma kaamil ya karbe wayar duk sun damu suna tambayar ta ina take… Tace na hadu da kawata ce amma gani nan zuwa…tana kashe wayar dija tace mata shikuma wannan din waye ne Bahi Tace kaaamil ne..junior bro dinshi He is nice Dija tace ayyyah..he sound very tense Bahi tayi murmushi tace inkin gan yadda yake min kamar dama yasanni.. Dija tace to why not ki dinga sakewa kina fita kuna hira da su? I hate when u isolate urself…ki dena cika ma kirjin ki damuwa kinji?ai Komai zai daidai ta3 Ta gyada kai,haka ta sa ta a mota ita tayii driving suka isa har inda su junnut suke,Dija ce ta fara sauka a motar… wajen is private so tana ganin su ta gane su,da wani irin sauri kamil ya taho dayaga Bahi na takowa agefen dijan…shi baima tsaya gaisawa ba ya shiga jefo mata tambayoyi kamar wacce tayi shekara da bacewa Yace cupcake meyasa baki ce zakije wani waje ba? Wallhy kin tsora ta ni…kar ki sake yin haka kinji ..We can go together ai,.ko baki son na kaiki da kaina ne? Duka suka tsaya kallon sa yana ta zuba,bahi na ta faman gyada mashi kai a duk abunda yace sabida fuskn sa bakaramin nuna damuwa yayi ba Wani kallon kallon junnut sukayi exchngin da dija cikin su kowa na jan aji babu wanda ya ce uffan ma wani Chan Junnut Tace itace kawar kin? Anan bahi tayi gyaran murya tace yes itace.. Dija meet junnut. junnut wannan itace kawata dana gaya maki …we met in london.. A hakan ma dija ita tafara miko hannu sukayi musabaha suka gaisa sama sama…tace ok…shall we? Nan dai sukayi sallama dija ta ja motar ta ta bar wajen suma suka gama hanyar gida,cikin ran junnut Kwata kwata dija bata mata ba.. Now she know why bahi is like that,taga itama dijan kayan mutunci ne ajikin ta harda lullubi Ita kuma intaga haka kallon kauyanci takan iya yi ma mutum Bayan kwana biyu har yanzu khaldun bai dawo ba..as usual wayar shi ma bata shiga Da safe bahi tana zaune a dakin ta sai taji knocking,a dan hanzarce ta sauko duk tunanin ta khal ne ya dawo zai dan duba ta..a Yanzu dai da suke yawan tattaunawa da dija a waya sai tafara jin karfin gwiwar fuskantar sa da tanbayoyin ta dan na musamman take so taji laifin datayi masa da abunda ya jawo auren su cikin gaggawa.. Budewa kofar ta ke da wuya sai taci karo da junnut su biyu daga bakin door..,wata figaggiyar halittar data gani abayan ta yasa ta kasa bude baki tayi magana kallon kallon suke jefa ma juna asace Har suka karasa shigowa dakin,sai taga babu abunda matar take bin ta dashi sai yatsine.. Junnut tace bahi kawata ce tazo.. Wanda nake gaya maki..to dama hilda turanci kawai take iya comunicating Sama sama suka gaisa da bahin,duk dama she cant help it sanda ta bata attitudes irin nasu na watsasun yan mata.. kamar taga wata kashi take kallon drsing din bahi maganan takan amsa shi dakyar tana yi tana wani daga mata kai “Da alama bahin ne bata mata kalar ta ba,musamman datagan ta all closed up ga dogon riga ga suma kanta duka acikin turban cap.. Kuma ta mata kallon sama da kasa bataga nails ko wani expensive fixtures ba,tuni sai wani rainin wayo ya shiga ranta game da ita. Dan ko da suka fita a site din korafi kawai takeyi ma junnut akan dama wannan ne kawar taki da kika ishe mutane da ita?,cewa tayi ita dai bazata taba hada hanya da bahi ba2 Junnut bata jin dadin furucin amma itama takance ai tayi bakin kokarin ta bahi dai haka ta zaba ma kanta… Duk dama sunsan ta fi karfin su a kyan gani amma gani suke kamar bata waye ba Acikin kwana biyun haka aka sha fama akan haka,hilda bori boro take nuna ta tsani bahi..a boye kuma jahan khatun takan saka baki tayi zugi idan hilda tana cacccakar bahi a gaban junnut din Sukam dama nasu yazo daya,hilda har da ce ma jahan ai ita kallon munafuka take yi ma bahiyya dan haka tana basu shawarar suyi hankali da ita Hilda is a chronic egoistic princesss Bata da da’a bata da saukin kai duk mugun halin junnut na kaskantar da dan adam sam bai kai nata ba So dawuri bahiyya taja layi makanta da yawan shiga harkan su,duk dama junnut takan nuna rashin jin dadin attitude din hildan akan bahiyayyr ta Amma abune wanda suke mata afili..dan ta ja mutuncin ta kawai sai ta dena neman junnut kwata kwata in ba ita tazo wajen ta ba abubuwan gaba daya ba kamar da chan ba,bahi ta dan sake jikin ta duk dama har yau abu mafi wuya a rayuwar ta agidan shine gaisuwar da suke kaiwa gaban dilshad da jahan khatun ga kuma hilda Ita dai bataga abunda ta tsare musu agidan ba amma jikin ta ya mugun bata cewa jahan khatun din nan bata kaunar ta. Dan ko gaisuwar nata a wuya take amsawa sannan tana yawan nuna banbanci tsakanin su da yayan ta Kwana biyu dayake bahi ta kan nuna kin amincewa akan yawan fita shan ice cream,sai ya zamto kaamil ya kawo saran video games,wani bin suyi su uku da junnut idan hilda na bacci wata rana su biyu Shikam He feel more happy with her Sometimes yanayin ta yana masa kama dana khaldun,thy r very lucky numbers and winners in nature Acikin sun ganin kamar sun fita wayewa a fuska amma idan suna abu sai suga tafi su nitsuwa da dabara Tuni hakan ya sa jahan khatun ta fara saka ido sosai akan kaamil Gashi yana yawan ambaton bahiyya Haka ma musamman in bahi taki fitowa dining to kaamil gaba daya baison zama shima1 To tun daga nan jahan khatun ta fara kai korafi ma junnut tana tambayar ta ko dai yarinyar bata da kamun kai ne? along with zugin hilda takance Aganin ta danta yafi karfin yabi wannan kaskantcciyar yarinyar,cewa ma take hala taga daula ne take so tayi seducing din dan gida ko zata tasami wuri, duk sun hana junnut sakat da maganganu Dan koda kunnut ta kare bahiyyar basu sauraran ta wani bin har fada jahan khatun take mata most time idan junnut ta bata rai akan abun da sukeyi ma bahi,hilda kuwa sai taji ta kara tsanan bahin sosai. Ranar da bahi ta cika wata guda ana neman sati kenan da zuwan hilda gidan Da safe kaamil shima baiya nan,bahin tagama waya da dija sunyi hirar su musamman akan hilda dake neman tsole mata ido a gidan har na wuce gona iri Ita tunda ta samu goyon baya daga wajen jahan khatun sai bata da wani buri da ya wuce ta ga ta kaskantar da bahi ta wulaknta ta To yawan share su d bahi takeyi tana abubuwan ta da kaamil yasa hilda bata samu dama ko sau daya akanta ba Amma a kwana biyu da kaamil baiya nan sosai hilda take zakewa tana gaya mata bakaken maganganu marasa dadi.. Toh Tana aje wayar dija sai ga kirar jahan Aarah,da sauri ta mayar kunnen,cikin nitsuwa da girmamawa ta gaishe ta,to dama ta dada mata magana akan shirun subaya, she tot ko amsar zancen xataji amma sai taji jahan na mata wani magana daban Tace bahiyyya ki shirya,hajy indirah tana hanya zata iso yau din nan,idan har akwai wani matsala sai ki gaya min Bahi tace ok maam…babu wani matsala Allah ya sauko da ita lpya Dan Hira kadan sukayi kafin ta kashe wayar.. Bangaren subaya kuwa jahan Aarah tayi har ta gaji,dan tun lokacin da akayi aurem bahi yau wata guda kenan amma babu wanda ya gane kan subaya. She is alwya queit,takan iya yin awowi tana shiru batace komai ba kamar wanda take cikin kunci ko rudani Har likita jahan ta kira,amma subaya taki sam ta bude ma kowa sirrin zuciyan ta Haka ma sadat yake fama da ita,a duk da iya shige da ficen sa wannan karon sabbin halayyar subaya yanasa shi tunani Rabon ta datayi wani dogon magana da shi tun ranar da ya dawo gidan ta nuna masa ya bata mamaki sosai akan lamarin sa da bahiyya.. Yaso ya dada cusa mata bakin ciki da cewa bai fasa auren ba.. amma sai yaga itama ta daure ta nuna masa cewa sam batayi tsammanin zai iya sa rayuwar cikin wannan hatsarin ba She become cold towards him,har da ya dauka ko fushin kishin ne,amma daga baya sai ya kasa gane ma yawan shirun ta akansa kwata kwata.. Anan gida abuja kowa Ko ina a site din bahiyya is crystal clean an tsaftace shi sosai,dan dokan aikin side dinsa ne anayi tun kan ma su tashi daga bacci so iya zaman ta anan maids din dake kula da ita ma basu taba bari taga fuskokin su ba.. Chan da yamma ta farka daga short siestar da tayi..,Wanka ta tashi ta tsala sai ta fito da wata dark maroon gown mai manyan hannaye da designing din silver stones..she wanted to look much presantable dan jahan ta sha gaya mata wacece hajiy indirah. 4.pm dot sai ga aika cewa bakin ta sun iso.. Kayan jikin ta ya haska ta sosai ya maida ta tamkar wata kasaitacciyar sarauniya,dan veil din rigar sharara ne kuma yana da dan fadi to instead of yafawa sai ta lullebe kanta d shi inda fuskan ta ma da kyar ake iya gani sosai Make up din ta is deep,dan har wani smoky eyess ta baza ma eye socket dinta ta zana light maroon eye shadows tabi layin eye liner ta da silver glitters..Ga wani uban qamshin wasu shegun mixed arabian scents daya mamaye ko ina ajikin ta yana kai sakon isowar ta tun kafin ta billo A nitse take saukowa kamar wacce zata je bada doka,bata sauri amma ayangace sautin takun ta ke bada tsarin sa mai dauke hankali Babu kowa a inda suka saukan sai masu aiki da yan kaikawo.. Daga site din khaldun sai wannan site din, so Data shigo faloun Bata sha mamakin ganin mata biyu data ke zaune akan kujera ba Fadin haduwar su fa tsarin yadda suke bazai fadu ba ,dan ko makaho yashafa ya gansu yasan yayi gamo da kyawan halittu masu ji da zunzurutun dukiya da kasaita.. Tun kafin bahi ta isa gaban su,dayan matan da tayi kama da yar shekaru 27 ta mike ta riko ta tana murmushi A hankaali kamar mai rada mata a kunne Tace…Gaban ki Alheri bayan alheri..farin wata sha kallo..bullowar ki baya bukatar sanarwa..farar tantabara,haske, zuciyar duniya.. Tana rike da hannun bahin Sai ta juya ta kalle hamshakiyar matar dake zaune tana binsu da ido tace ummmah.. wannan fah itace matar Aaaban din…. Murmushi kawai matar tayi..sai Tace Jeki kiyi gaisuwa mahaifiyar ku ce…aikuwa Da wuri bahi ta karaso gaban matar ta rusuna a nitse ta shiga gaishe ta Ita kuwa cikin saukin kai take amsawa tana saka mata albarka da manyan kalmomin yabo masu tsada Matar Sai kallon ta takeyi tana duban ko ina ajikin ta daga sama har kasa kamar wacce aka ce tazo tayi inspecting dinta Bayan sun samu daidaitawa,bahi ta cire kunya ta shiga asalin cikin gidan maids din For the first time tun da tazo sai yau ta bada oder aka kawo musu pleasantries to dama ita tayi abincin ta dakanta da abubuwan jika magwagwro Jin maids ta ce bahin ne tayi girkin dakanta yasa hjy indirah taji bahin ta dada burge ta Duka Suna ci duna dan mata tambayoyi…Wurin dirin hallita kwalliya da kyaun fiska duk hjy indirah ta bada marking.. A hakan ma sanda tayi korafi akan bata ga gwalagwalai masu yawa ajikin ta ba Tace kinsan wa kike aure kuwa?..to zakiyi kwalliya sosai dan bazamu zauna araina mu ba It seeem like matar no nonsence ce,zata kalle ka kuma ta fadi magana babu tsoro bare fargaba But ta manyan ta dan Akalla zata iya haurawa late 50s inma bata kai irin 59 din nan ba .. Dayan matar sunan ta murjanah she is 27yrs..itace yar hjy indirahn dan daga gani kamannin su zaka gane hakan Ita dai bahi bata bar wajen ba har suka kammala ciye ciyen su.. Nan hajya indirah ta nemi alfarman akan suje tare ta gaishe da tsohuwa dilshad.. Ba bata lokaci bahi tayi musu jagora to tafiya sukeyi bisa tsari..daga ka gansu kasan sunji duniya. Bahi na gefen aunty murja,ita kuma hjy indirah na gaba dadu. Adai dai gabar shiga falon sarauniya dilshad akayi wani gamon kicibis tsakanin hajiy indirah da junnut dan har junnut din ta dan buge ta sai da suka kalle juna. Maimakon tayi saurin cewa soryy a matsayin ta na karama kuma taga babbar mace ce sai ta takarkare ta watsa mata kallon banza mai shake da harara kamar yadda ta saba yi tana nnan jan tsaki .. Ai kuwa bata hankara ba taji wani saukan gigitaccen saukar tasssssss akan fuskan ta wani rauuu kunnen ta ya dauka,shock ya gauraye ta kamar waccr zata zube a kasa..6 wajen a take ya dauke shiru,tuni jahan khatun ta diro daga kan kujera ta iso bakin door din a hargitse Dai dai lokacin Hjy indira tana tambayar bahiyya tace wacce kuma wannan bushiyar? …”ehhh lallai kam…daga gani gidan nan babu manya acikin ta Wani mugun hada rai jahan khatun tayi kirjin ta na bugawa Ta wani dake tana kallon su Junnut na dafe da kuncin ta ta asa dagowa dan radadi Da zata karasa ciki Wani Kallon sama da kasa hjy indiran ta mata tace kin bace agaba na ko sai na taka ki..? “Cike da masifan daure fuska da nuna bacin rai jahan khatun ta tsare kofar,ta maida kallon ta take kan junnut din datayi rau da idanu takasa magana sai huci.. Cikin sautin muryan izza tayi kamar ta basar da presence din hjy indirahn sai tace Wai meke faruwa ne? “Ammah, wannan matar ce ta mare ni..junnut ta mayar da amsar muryan ta har na rawa tsaban fushi kamar zata fashe da kuka Hjya indiran ta nade hannayen ta cross arm ta zuba musu ido bata motsa ba… dan a lokacin Wani uban harara murja take bin junnut din da shi mai nuna fin karfi da iya barikanci so take taga iya gudun ruwan ta itama ta caccaka ta dan bata bari araina uwar ta ko kadan “…ita kanta jahan khatun tasan wacce hjy indirah dan haka sai tayi saurin kalmasa yanayin ta batace mata uffan din ba amma tabbas taji mugun haushin marin yartan da tayi a yanzu ..har cikin gidana?waye ma ya bata izinin zuwa min gida na…tsaki take fanar yi cikin ranta Tattaba fuskan junnut ta shiga yi tana kukkuni kamar wacce aka fasa mata kwai data dau shrkaru tana tattalawa.. To,kije daki..Allah zai saka maki… Ita kuma junnut fuuuu ta dau hanya har Saura kadan ta banke su ta wuce.. Hjya indira ta wani daka mata tsawa ta dawo da ita baya agigice..tace Ke?…come back here and look at me..saka idanun ki acikin nawa nace Ba shiri junnut ta jiyo a tsorace “Kinga nayi maki kama da saar ki ce da zaki buge ni bazaki iya budan baji kice min sory ba? Yadda hjya tayi maganan with daring and matured tone ya sa junnut ta nitsu dan dole, jikin ta ne ya fara rawa slowly sabida tsoro Rayin jahan khatun tuni ya dada baci…anan jahan khatun din ta yi saurin shan gaban junnut din cikin masifa tace….excuse me?..baza a sa min yata a gaba ana ci mata mutunci ba,metayi,? akan me?a gidana?wani takurarren tsaki taja a fusace sai ta dan juya kai tana maida kallon ta cikin palon da wani shakuratren voice tace… Mum Ina ganin kimar ki ne da wallhy babu wacce xata zo gidana ta dakar min yata nasa ido ina kallon ta… Hjy indirah Ta yi wani takaitaccen dariya taja siririn tsaki,bata tsaya amsa maganan ba dai kai tsaye ta kusa kai cikin falon ta isa har kusan gaban dilshad dake zaune tana jin duk abunda suke yi… Dukan su suka biyo ta yuuu kowa da yanayin sa,bisa tsari hjy indirah ta gaida dilshad khatun kamar ba ita ba.. Dilshad Tace indirah..Kece kuma da hayaniya ? Menene yarinyar tayi daxaki mare ta. Tuni hjy indirah ta dada daure fuska,tace ur majesty ai kya bari mugama gaisawa ko? Toh..matsalan su da ita kenan bata cika bada respect yadda suke so ba…tana gama gaisuwar kuwa tace murja tsuguna ki gaishe su duka..cikin nuna biyayya ma uwa murja ta fada tayi gaisuwa.. Junnut da bahi na gefe sukam basu ce komai ba Sai da akayi Nan ne hjy ta dago ta dube jahan khatun da irin kallo ni bade ke zanyi ba sai dai nayi da uwarki,..a tsanake ta fara cacakar su da magana cikin dabara da sanyin nuna ita bata shayin su Tace ur majesty kince nazo maki da hayani,to ni ba haka nake ba..ai aganina wata motsatsiyar belbela bata isa tace tayi muhalli ma shaho ba nan fa gidan hamood ne, shin ita wacece yar?a hakan ake kiwo agidan nan ma kasa baisan nagaba ba?to nidai babbace .kuma yaro ko ya yake akasa na yake…ni nazo gidan dana ne Kuma babu wanda ya isa ya sa min doka akan komai…Sai dai fa ayi hakuri ur majesty A fusace jahan khatun tayi saurin tarar numfashin dilshad data dago kamar zatayi magana… tace,..kinzo gidan hamood?toh wallhy baki isa ba yanzun nan zaki koma inda kika fito …nan dai gidana ne kije chan inda kika saba zuwa kiyi mulkin ki Hjy indirah…tace ke da Allah rufamin baki ..ko so kike in tuna miki hamood daban ke daban ne?to inkin manta lna zaman aure kike…dan haka kuma gidan hamood ba fadar uwar ki bane.. Ni jinin shi ne toh idan ban isa da gidan hamood ba sai kece bare yar aro kika isa da shi ko? A zafafe sarauniya Dilshad tace musu enough… Tuni tayi hannu ma yaran suka bace suka basu wuri… Fada ta shiga musu sosai kamar dattijuwar arziki… “Tace Abunda kukeyi har agaban yaran ma baza ku san kun manyan ta ba..?Idan sunji hakan.. nan gaba kuma ya zasu kalle ku bare mu da muka tsufa mukayi laushi Ana maganan yara kuma Me zai kawo gorantawa ? Ke indirah ki gaya mana meya kawo ki daga nan ayi sallama i think uve over stayed ur welcome …hjy indirah tace what? meya kawo ni fa kikace ur majesty..wani takaitaccen kallon rainin wayo ta musu tace “bakwanta nazo kamar yadda kowa yake zuwa”..nan da wata guda ma ina cikin gidan nan …ran jahana ya dada baci dan tasan duk gorin akan zaman dilshad agidan nan take yi.. Da kyar dai dilshad ta yi setling case din har jahan khatun ta yarda da cewa hajy indirah zata xauna a gidan for the main time a basu san asalin dalilin ta ba3 …a duk dama ran jahan khatun baiso ba tabbas aranta tana harsashen sabida bahiyya aka turo hjy indirah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *