AIKIN ZUCIYA CHAPTER 2 BY LU’UBATU ISA LAWAN

Shi ne mai bayar da hailuwa ga wanda ya so, a kuma lokacin da Ya so. Kuma ki sani Ubangiji dai ba a yi masa dole”

Naja ta yi murmushin Karfin hali ta ce,

“*Ina sane da hakan, kuma duk abin da ka fada gaskiya ne. To amma ai kana jin abin da mutane suke fada”

Ya girgiza kanshi, “Kada ki damu kanki da duk abin da mutane za su fada, balle har ki sanya abin a cikin ranki ya zo yana damunki.

Taso mu je na tayaki ki yi wanka ki huta, yauwa Didina, ko ke fa?”

Maimakon da suka shiga cikin daki ta nufi bandaki sai kawai ta haye kan gado ta kwanta, hakan da Nur ya gani ya sanya shi ya nufo gadon ya hau tare da janyota jikinshi, domin ya rarrashe ta.

Fuskarta ya gani jike da hawaye, ya ji tausayinta ya sake dirar mishi, ya sanya bayan hannu yana goge mata.

“Please Najnoor ki yi shiru, kin san bana son kukanki, don sanin kanki ne yana tada min zucita, taso mu je Lobina na yi miki wanka, don na lura yau ‘yan shagwabar ne suka motsa Naja ta mayar da idanunta ta lumshe gami da bude su tayi mishi murmushi.

“Sweetyna ka bar shi zan yi da kaina”.

“To shi ke nan, bara na koma falo na jira ki, tunda yau ba kya so na taya ki”.

Murmushi ta kuma sakar mishi, hakan ya yi dai-dai da barinshi cikin dakin. Ta nufi

bandali, tana fara zubawa jikinta ruwa ta ji wani sanyin dadi yana mamaye mata zuciya wannan ne ya ba ta damar ci gaba da gabatar da wankanta cikin kwanciyar hankali, ta kuma yi fatali da duk wata damuwa da ke cikin zuciyarta.

Tsaye ta ke gurin madubi tana shafa mai lotion a jilinta, gami da goga turaren gabbai daga bisani ta saka wata ‘yar doguwar rigar bacci mai hade da ‘yar ciki, sannan ta feshe jilinta da body spray, ta dauko cingam mai kamshi Apple tare ta jefa wa cikin bakinta tana tauna a hankali, ta nufi dakin baccin Nur.

A bakin kofar ta tsaya tare da sanya hannu ta yaye labulen dakin, kwance yake akan gadonsa yana amfani da wayarshi ta hannu. Kamshinta ya isar

masa da sakon zuwanta. Kyawawan idanunshi ya dora a cikin nata idanun. Da sauri ya wuntsilo daga kan gadon ya taso ya tare ta ta hanyar yi mata masauki a gefen kafadarsa. Ya hada kirjinsa da nata, yana fada wasu kalamai da suka sanya ta tsinci kanta cikin wani matsanancin nishadi.

Nan take Nur ya yi mata wani salo wanda suka Kara jefata cikin nishadi, ta rinka dariya har da kyalkyalawa. Ba su ne suka kwanta ba sai wajen karfe sha daya da rabi na dare. Naja ta maida dubanta sashen da Nur yake kwance yana baccinshi cikin kwanciyar hankali, ta dan janye bargon da suke rufe da shi ta nufi bandaki ta yo alwala ta fara jero sallolin nafila. Bayan ta gama ta yi salati ga Annabin Rahma sannan ta ci gaba da yin hailala dayin tasbihi ga Ubangiji tare da yi masa kirari ta kaskantar da kanta ta ci gaba da rokonSa Ya taimaka idan har tana da rabon samun haihuwa Ya bata “ya’ ya na gari, shiryayyu masu jin kan mahaifansu, masu amfani ga sauran “yan uwa musulmi, sai da dare ya yi sosai tukunna ta kwanta. Misalin karfe takwas na safiya ta nufi kicin domin shirya wa Nur karin kumallo, kunun gyada da kosai mai dauke da hadin hanta ta soya mishi. Sai Eng into egg, ta shirya tebur tsaf babu abin da za a nema a rasa.

Sai da ta tabbatar ta cika masa tumbinsa sannan ta dauko mishi brief case dinshi wadda zai tafi ofis da ita, har gurin da motarshi ta ke ajiye ta rako shi.

Da hanzari direbansa

Babangida Nashagamu ya taso ya bude masa mota. Naja ta mika masa ya hade da hannunta ya rike yana watsa mata wani murmushi. Ya sumbaci hannunta, real lobe you Didina

Ta sunkuya dai-dai kunnensa ta rada mishi,

“Me too”Ya ja karan hancinta ya ce,

«Sai na dawo”

Ba ta yi magana ba sai dai ta daga masa kanta ta dan ja baya tana yi mishi bye-bye har sai da ta ga motar ta bar cikin harabar gidan, sannan ta koma cikin gidan.

Dakin baccinta ta nufa don tana bukatar ta kwanta ta huta. Ta haye saman gado ta kwanta, ta lumshe idanunta cikin *yan dakiku bacci ya yi awon gaba da ita. Misalin Karfe uku dai-dai Nur ya shigo

cikin farfajiyar gidan, turare ta kuma daukowa

ta feshe jikinta da shi bayan ta gama tsantsara kwalliya, ta nufo kofa da sauri. Tana bude

kofar suka yi kicibus da juna ta ja gefe daya

tana murmushi cikin ‘yar siririyar muryarta mai taushi, ta ce, “Sannu da zuwa”. Ya langwa6e kansa

ya kwaikwayi muryarta, da yake matukar jin dadi. Ta yi masa kallonta na musamman wanda a duk lokacin da

ta yi mishi irin wannan kallon sai ‘yan hanjinsa

sun kada. Ya rasa dalilin faruwar hakan.

“Ka shigo mana ka yi tsaye a bakin kofa

sai wani kallona ka ke, ko ka ga na sauya maka

ne?” Tayi mishi wannan maganar ne cikin

yanayi na fari da idanuwa da ‘yar shagwabarta.

Ya kai hannu ya janyota zuwa jikinshi ya kai

bakinsaga lebenta da ke dauke da wetlips mai

kamshin strawberry.

Ganin zai wuce gona da iri ya sa ta riko

shi zuwa cikin falon gidan, inda ta ci gaba da

Hmmmm