AL’KALAMINE SILA CHAPTER A

 AL’KALAMINE SILA CHAPTER A

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN-K’AI.+

Barkanmu da saduwa da ku a cikin wannan gajeren labarin namu mai taken AL-ƘALAMI NE SILA. Ba mu yi shi da nufin cin zarafin wani ko wata ba. Mun yi shi ne musamman domin tunatarwa, ko in ce tsoratar da marubuta har ma da makaranta bisa ga wasu abubuwa da akan samu wasu sun aikata.

Ƙirƙirarren labari ne, sai dai abin da ke faruwa kenan ga wasu mutanen. Kenan dai wa’azi ne ga masu aikata irin abubuwan da labarin ya ƙunsa. Wacce duk ta ga ya zo daidai da rayuwarta, to ta ɗauka cewa domin ta muka yi labarin. Allah ya sa ya isa inda muke son isar tashi.

***

Wasu irin abubuwa ta ji suna yawo a cikin idanuwanta, hakan ya sa ta yi amfani da yatsarta manuniya wurin murzar idon cike da tsoro. Abin da ta gani ne ya matuƙar tayar mata da hankali bayan ta ɗago yatsar tana kallo. Wasu irin tsutsotsi ne marassa kyawun gani. A kiɗime ta murza yatsar tata jikin kayanta, gabanta sai tsananta duka yake yi.

Motsin ta sake ji, na yanzu ma har ya fi wancan na farkon tsanani, ta yi yunƙurin murza idon amma sai ta fasa, sanadiyyar tunowa da ta yi da abin da ta gani a farko. Kasa jurewa ta yi, saboda yadda motsin ke tsananta, yana zarcewa har cikin kwanyarta, tamkar za ta zauce.

  Hannun ta sake kai wa ta murza sosai, a wannan karon sai jini ta gani a hannunta.

   Mamaki ya cika ta. Yatsar tata ma a hankali ta fara daddarewa tsutsotsin na shigewa a ciki, yayin da masifar idon nata yake daɗa yawaita.

Ihu ta fasa da ƙarfi, wanda ya yi daidai da farkawar ta daga barci.

   Ajiyar zuciya ta rinƙa saukewa. Ta ɗaga yatsun nata tana kallo, lafiyarsu lau ta gani. Ta kai su ga idonta nan ma ba ta ji motsin komai ba. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, hawaye na zirara daga ƙwayar idanuwanta.

Takurewa ta yi wuri guda, barcin da bai sake ɗaukarta ba kenan har asubah ta yi.

Tun daga nan gabanta ke faɗuwa. Hankalinta ya gaza kwanciya. Damuwa ta gama dabaibaye kaf ilahirin zuciyarta.

Bayan ta gama sallar asubah ta koma ta kwanta. A nan ne ta ci sa’a barci ɓarawo ya sace ta, ita ce ba ta farka ba sai kusan ƙarfe goma na safe.

Ƙarar wayarta ce ma ta tashe ta. Ta duba mai kiran nata sai ta ga sunan Hafsa ya bayyana a jiki. Ɗauka ta yi ta kara a kunnenta. Ji ta yi Hafsa ta ce,

“Surayya alƙawari muke jira ki cika mana. Kin ce yau da sassafe za ki yi mana posting zazzafan page, ga shi fans sai famar tambaya suke yi.”

Cikin firgita Surayya ta ce,

“Wallahi Hafsa akwai damuwa ne. Amma dai ina zuwa, bari in hau chart ɗin yanzu.”

Suka tsinke wayar.

Tana hawa ta fara cin karo da group chart ɗinta mai suna SURAYYA SURY FANS CLUB. Charts ne sun taru sosai, ta bi a hankali tana duddubawa.

Hira ce a ke yi a kan littafin da take musu posting mai suna MASOYA. Tana ganin ra’ayin readers game da fitsarar da take sakawa a cikin littafin, Kaf yabon batsar tata kawai suke yi. Daga cikinsu har da masu faɗin su sun matsu a kawo musu abin da ke faranta musu (Suna faɗin kalamai munana game da labarin.).

Ba za ta taɓa mantawa da mafarkin da ta yi a daren jiya ba. Sosai ya tashi hankalinta, ya kuma yi zaman dirshan a cikin zuciyarta.

Sai dai kuma kash! Kalaman da ta tarar wanda fans ɗinta suka yi, na ƙarfafa mata guiwa game da ci gaba da kawo musu labarin, sai ta samu nutsuwa, ta ji walwalarta ta dawo. Ba ta yi ƙasa a guiwa ba ta turo musu zungureren shafin da ta rubuta musu jiya, wanda tana yin sa ita kanta tana jin sauyin yanayi a tattare da ita, duk da cewa ita ɗin budurwa ce.

Kalaman jinjina suka rinƙa turo mata. Sosai suke daɗa koɗa ta. Ita kuwa sai jin kanta take yi ya yi girma, tana jin daɗi sosai, a ganinta ai babu tamkarta.

A take ta shagala, ta ji daɗi sosai, ta gaggauta sauka domin rubuto musu shafi na gaba, tunda ta ga sun ji daɗin wancan ɗin.Cikin takaici ya jawo wayarsa, yana jin zuciyarsa na tafarfasa sosai kamar za ta tsage tsabar takaici. Haushi ya gama rufe masa idanuwa, da ƙyar ya iya gano lambar da yake nema ɗin. Ringing biyu aka ɗauka, da ƙyar ya tattaro magana daga ƙarƙashin maƙogoronsa, ya yi sallama. A ɗaya ɓangaren aka amsa, haɗe da gaishe shi.+

“Yaya Shamsu ka yi haƙuri dai, amma tsakani da Allah na kawo ƙarshe a yau dai kam. Ina so ka zama shaida ne, wallahi idan har hakan ta sake faruwa to tabbas Zaliha za ta koma gida, kuma aurenmu zai zo ƙarshe kenan har abada!”

Cikin sassauta murya wanda ya kira da Yaya Shamsu ya ce,

“Haƙiƙa na san kai ɗin mutum ne mai haƙuri Kabiru. Na kuma san tabbas Zaliha ta kai ka ƙarshe tunda har ka kira ka sanar da ni a cikin daren nan. Wallahi ba zan taɓa ganin laifinka ba Kabiru. Ka ɗauki duk matakin da ka ga ya dace da Zaliha. Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Na san ka yi haƙuri sosai da ita.”

Kabiru ya sauke ajiyar zuciya. Har ga Allah yana ɗaga wa Zaliha ƙafa ne kawai saboda daga gidan da ta fito. Ta samu tarbiyya mai kyau, ƴar babban gida ce.

“Shi kenan Yaya. Ka yi haƙuri na kira ka a daren nan, wata ƙila ma har ka yi barci.”

“Babu komai Kabiru. Mu kwana lafiya.”

Suka yi bankwana. A daidai nan Zaliha ta shigo jiki saɓule, kallo guda za ka mata ka tabbatar da cewa ba ta da gaskiya. A kusa da shi ta dawo ta zauna, kansa sunkuye ƙasa. Kamar ba za ta yi magana ba, sai kuma ta daure ta ce,

“Yaya don Allah ka yi haƙuri. Ga shi can na ɗora maka indo…”

“Dakata Zaliha!”

Ya tsayar da ita cikin faɗa.

“Tun wuri ma ki je ki sauke ta don na gwammaci kwana da yunwa a kan na ci girkinki. Haba Zaliha! Wannan wace irin rayuwa ce? Kanki farau rubutun littafi? Na tabbata su kansu wanda kike rubuta wa ɗin ba su barin mazansu da yunwa. Suna ware lokutan da suke yin karatu, kamar yadda wasu marubutan ma suke ware lokutan rubutunsu. Me ya sa za ki min haka Zaliha? Tun safe na bar gidan nan na tafi nema mana halaliyarmu. Dama da safen ba wani kalacin kirki na samu ba, hankalinki na kan waya. Yanzu kusan sha ɗaya na dare na dawo amma Zaliha ba zan tayar kin girka min abinci ba? Mene ne babu a gidan nan? In ce ko na ajje komai Zaliha? Abin da kike koya wa mata kenan a rubutun da kike yi? Na tabbata soyayya kike koya musu. Kina nusar da su hanyoyin da za su kula da mazajensu. Amma ke ga ki nan kin kasa faranta wa naki mijin. Ba yau aka fara ba. Wannan shi ne kusan karo na biyar da muke samun irin haka, sai dai ki rinƙa ba ni haƙuri amma kina cutar da ni? To ki sani! Wallahi ba zan ƙara lamunta ba. Matuƙar hakan ta sake faruwa lallai ƙarshen aurenki ya zo!”

Ya fice ya bar mata ɗakin. Ba ta bi shi ba, sai ɗaga kafaɗarta da ta yi cikin halin ko’inkula. A tunaninta ai abin da ya faɗa ba zai iya aikatawa ba. Ta koma kitchen ta kaso gas ɗin. A nan ta ci karo da Kabiru yana dafa ruwan zafi. Ba ta bi ta kansa ba kawai ta fice ta koma ɗakinta. Wayarta da ke jone jikin caji ta jawo, dogon USB ɗin har inda take kwance kan gado yake isowa. Nan ta ci gaba da typing ɗinta babu damuwa ko kaɗan a tattare da ita. Kabiru kuwa yana can bayan ya dafa ruwan zafi ya haɗa tea, yana sha cikin takaici.

Washe gari Kabiru bai ko tsaya bin ta kan Zaliha ba, ya shiga kitchen ya haɗa wa kansa kalaci ya fice daga gidan. Ko da ta tashi har gari ya waye. Barci ta yi sosai, saboda barcin da ba ta kwanta da wuri ba tana ta aikin typing.

Ba ta wani damu ba da ta ga ba ya nan. Ta dafa wa kanta indomie ta ci, sannan ta ci gaba da sana’ar. Sai bayan ta yi sallar azahar sannan ta nufi ɗora girki. Saboda kiran da Yaya Shamsu ya mata ya ci mutuncinta sosai. Ya kuma tabbatar mata da cewa matuƙar ta yarda ta zama ƙaramar bazawara, to ba dai a gidanshi ba. Sai dai ta nufi wani wurin can, tunda dama a hannunsa ta tashi, tun tana ƙarama iyayensu suka rasu.

Jellof ɗin taliya ce ta yi. Ita kanta tana dafawar hankalinta na ga waya, har ruwanta ya tsane tsaf, ta yi ƙauri sosai amma hankalinta na kan wayarta. Ƙaurin da ta ji ne ya sa ta miƙe, rabin hankalinta na ga daidai wurin da take rubutawa, har ta bige kanta da bango ma ba ta sani ba. Saurin dafe goshin ta yi, nan ta ga jini na zirara sosai. Isar ta kitchen ɗin ta gaggauta kashe gas, ta duba ta ga fiye da rabin taliyar ta zama ƙanzo, ga wani irin mugun ƙauri da ya daki hancinta.

Saukewa ta yi ta kwashe ta saka a food flask, ta rufe sannan ita kuma ta fara cin ƙanzon a cikin tukunyar, hankalinta ya kasu kashi uku. Kashi na farko na ga azabtaccen ciwon da goshinta ke mata. Na biyu na ga cin abinci, na ukun kuwa na ga rubutunta da ta fara ba ta ƙarisa ba.3

Janye tukunyar ta yi daga gabanta, saboda rashin daɗin abincin. Ita kanta ta san cewa bai yi daɗi ba. Ga mugun ƙaurin da ya yi. Ta ɗauko wayarta ta buɗe, a nan ta tayar da abin da ya saka ta ɗora hannunta bisa kai haɗe da fasa kuka. Dogon shafin da take rubutawa ne ta ga baki ɗaya ya goge, ashe a lokacin da ta ƙume kanta, ta yi select all na rubutun, sannan ta yi cutting dukkansa ya goge ba tare da sanin ta ba.1

Sosai ta ji takaici, ta ma rasa abin da ke mata daɗi. Miƙewa ta yi bisa tafukan ƙafarta da take jin  tamkar ba za su iya ɗaukar gangar jikinta ba, ta isa wurin sink ta wanke hannunta, ba ta ko nufi gyaran kitchen ɗin ba kawai ta ɗauki wayarta ta koma falo.

A haka cikin ɓacin rai ta sako sabon rubutu, ta samu ta miyar da wasu abubuwan da ba ta manta su ba, wasu kuwa ta manta sai dai ta sake wasu.Dattijuwar mace ce zaune bisa kujera irin mai ɗaukar mutum biyu. Ta tsura idamuwanta bisa tv, tana kallon shirin Gari Ya Waye da ake gudanarwa a tashar Arewa 24. Ana cikin yi ne aka sako shirin Muna Kwarya, ɗaya daga cikin shirye-shiryen Gari Ya Waye ɗin.

 

Da ƙarfi matar ta ƙwala wa ƴarta kira,+

“Sameeha!”

Shiru ta ji ba ta amsa ba. Hakan ya sa ta sake maimaitawa har sau biyu, amma wacce ta kira ɗin ba ta amsa ba.

Wata dattijuwa ce ta iso da hanzari, ta sunkuya gaban matar cikin girmamawa, da alama mai aikin gidan ce. Ta ce,

“Hajiya, Sameeha sallah take yi. Na ji kina ta ƙwala mata kira shi ne na leƙa na tarar tana sallah.”

Cike da mamaki Hajiyar ta dafe haɓarta.

“Sallah? Sallar me Sameeha ke yi a dai-dai wannan lokacin? Biyar da rabi na yamma fa kenan.”

Kafin wata kalma ta ƙara gittawa a tsakaninsu sai ga Sameeha ta fito sanye da hijabi mai hannu. Hannunta na dama ta riƙe wayarta.

Bayan ta ƙariso gaban mahaifiyar tata ta rusuna.

“Ga ni Mama.”

Cikin fushi ta kamo kunnen Sameeha na dama.

“Sallar me kike yi da yammacin nan? Kar dai ki faɗa min cewa ta la’asar ce ba ki yi ba sai yanzu.”

Sameeha ta ji zafin riƙon kunnen sosai. Hakan ya sa ta saki ƴar ƙara.

“Mama azahar da la’asar…”

Sakin kunnen nata ta yi haɗe da bige mata baki da ƙarfi. Riƙe bakin nata ta yi a dai-dai sadda ruwan hawaye ke sauka bisa kumcinta. Ba ta iya furta komai ba gudun kar ta ji saukar wani dukan. Sai jin muryar mamar tata ta yi tana faɗin,

“Wai ke kam wace irin yarinya ce mai kunnen ƙashi Sameeha? Na kula da ke baki ɗayanki kin sauya. Kin tashi daga Sameehar da na sani, yarinya mai tsananin tsoron Allah da taƙawa. Yarinyar nan mai ibada da kiyayewa. Kin zama wata sakarya mara riƙo da addini. Haba Sameeha! Ki duba fa ki ga, dai-dai da islamiyya da kuke zuwa tare da ƙannenki kin daina zuwanta. Bokon ma ba ni da tabbas ko kina yin karatun kirki. Ke kenan kullum idanuwanki bisa waya, na tabbata cewa abin da kike yi a wayar bai ko kama rabi-rabin darajar ibadarki ba.”

Ta yi shiru daga nan tana bin Sameehar da kallo.

“Faɗa min in ji, wai mene ne kike yi da waya wanda yake hana ki tsayar da ibadarki?”

In-ina ta fara yi, tana son faɗa mata gaskiya sai dai tana tsoron abin da ka iya faruwa.

“Ke fa nake sauraro!”

Cikin rawar murya ta ce,

“Mama na fara rubutun Hausa novel ne, irin wanda ake yi a online yanzu.”

Cike da mamaki Mamar ta ce,

“Hausa novel? A yaushe? Da izinin wa?”

Hawaye sun gama wanke mata fuska. Sosai take tsoron mahaifiyarta, saboda in dai wurin bada tarbiyya ne to ba ta da wasa.

“Mama dama, ni ma ina son na faɗakar ne, ta dalilina a samu masu shiryuwa a kan wani abu da suka kasance suna aikatawa. Kin ga idan aka samu shiryayyu a dalilin rubutuna ɗaya ai zan samu lada.”

Kanta ta jinjina tana sauraron kalaman Sameeha.

“Don Allah kar ki hana ni Mama. Wallahi ina…”

Ta katse ta.

“Ni ban ce zan hana ki ba Sameeha. Saboda abin da kike yi ɗin abu ne mai matuƙar kyau, amma ga ɗaiɗaikun mutane ne yake da kyau. Domin kuwa a wurin wasu ne yake faɗakarwa, wurin wasu kam sai dai a kira shi da fanɗararwa. Idan har kika faɗakar, wani ya gyaru ta silar ki kina da lada. Amma matuƙar kika yi rubutin banza, to ki sani wallahi Allah ba zai taɓa ƙyale ki ba. Akwai ranar hisabi. Ranar da baki zai furta abin da ya faɗa. Ranar da hannu zai faɗi abin da ya taɓa, da kuma abin da ya rubuta. Ranar da ido zai furta abin da ya gani. Ranar da kunne zai bada labarin abin da ya saurara. Ranar da ƙafafuwa za su bada labarin inda aka taka aka je da su.

Sameeha za ki tsaya a gaban Allah ki kare rubutunki. Idan har kika rubuta abun banza, har wasu suka lalace ta dalilin rubutunki, to tabbas ke ce babbar mai zunubi.

Ki sani cewa rubutu wani abu ne, wanda mutum ɗaya zai yi shi, amma kuma ba a san adadin mutanen da za su karanta shi ba.

Rubutu wani abu ne, wanda ke ɗaukar tsayin shekaru ba tare da ya goge ba, ko in ce yake zama har gaban abada. Wanda ya yi rubutu zai mutu ya bar shi, amma shi yana nan yana ci gaba da yawo, ana ci gaba da karanta shi.

Idan kika rubuta abun alkhairi, to ko bayan babu rayuwarki abin da zai ci gaba da iskar ki shi ne wannan alkhairin da kika rubuta.

Idan kuwa kika rubuta akasin shi, to lallai ba za ki ga da kyau ba. Abin da zai iske ki kenan har cikin ƙabarinki.

Ki ji tsoron Allah Sameeha! Ki tsaftace alƙalaminki. Ki yi rubutu mai tsafta, ta yadda za ki kasance a cikin tsafta ranar gobe ƙiyama.”

Nannauyar ajiyar zuciya Sameeha ta sauke. Ta ji daɗi sosai da mahaifiyarta ba ta hana ta yin rubutun ba.

“Wato rubutu da kika fara ne ya saka miki raunin ibadarki ko Sameeha? Me ya sa za ki alaƙanta rubutu da lokacin mahaliccinki? Anya kuwa kina son ganin haske a rayuwarki? Komai na duniyar nan yana da lokacinsa. Kamata ya yi ki ware lokacin rubutun naki, ki san a irin lokutan da ya kamata ki yi shi.

A yanzu ba zan hana ki yinsa ba. amma ki sani, matuƙar ban ga sauyi ba, wallahi! kin ji na rantse? To sai na hana ki yin sa!”

Ta ɗago da kanta ta kalli Mamar cikin firgita.

“Kar ki ga kamar wasa nake yi miki. Matuƙar ba ki koma asalin Sameehar da na sani mai riƙo da addininta ba, lallai zan raba ki da wayar ma duka. Iyakar magana kenan. Tashi ki bani wuri!”

Sum-sum Sameeha ta tashi ta nufi ɗakinta. Tana jin yadda nasihar mahaifiyarta ta shiga ranta. Ita dama can ba ta da raayin yin rubutu mara tsafta. Haushin masu saka batsa a rubutunsu ma take yi. Babbar matsalar dai da rubutun nata ya shafi har lokutan ibadarta.

Gado ne irin mai ɗaukar mutum guda ɗaya ɗin nan, irin dai gadajen school hostels. Sai dai wannan ba mai up and down ba ne, single ne kawai.
   Ƴan mata ne jibge bisa ɗan ƙaramin gadon, su kusan bakwai sun takure junansu, sai mutum ɗaya daga can cikinsu riƙe da waya tana karanta musu littafi.+
Sosai suka shagala a cikin saurarar labarin. Wasu daga cikinsu duk sun canza yanayi, idanuwansu sun kaɗa sun yi jajur, sai famar lumshe su suke yi.
Ita kuwa gogar da ke karanta labarin, famar matse ƙafafuwa kawai take yi, tsabar fitina da masifa na cin ta, amma a haka ta dage karanto musu littafin.
A daidai sadda ta kai ƙarshen shafin, ta idar da sauke ajiyar zuciya, takaici lulluɓe da zuciyarta. Kafin ta ce komai ta ji wata ta ce,
“Kai! Amma fa ban ji daɗin tsayawar shafin nan a nan ba. Sai da aka zo inda harka take sosai sannan ya ƙare. Can’t wait for tomorrow’s post.”
Wata daga cikinsu ta ce,
“Ke ma ke faɗa ana ji Rumaisah. Ai ni nan kamar na fi kowa jin haushin tsayawarsa a nan. Keep it up our big writer, Surayya. Kina wuta muna bin ki da fetur.”
Su ɗin ne ke da bakin magana. Su kuwa mutum uku daga cikinsu shiru suka yi, saboda cikin yanayin da labarin ya jefa su. A yadda suke jin sha’awarsu ta tashi, ba su ƙi ko da ƙaramin yaro suka samu su biya buƙatarsu da shi ba. Barinma Lawisa mai ƙarfin sha’awa a cikinsu, tamkar ta shaƙo ɗaga daga cikin ƴan matan su yi lalata take ji.
“To ai an gama, duk ku tashi ku bar min gadona. Barci zan yi.”
Sakina ta ce,
“Ni dai kam Sarah ba zan iya tashi daga nan ba. Ki yi haƙuri pls ki koma gadona ki kwanta. Wallahi ba ki san me nake ji ba, ba zan iya misalta muku ba.”
Masu sauran kuzari a cikinsu ne suka saka shewa. Rumaisa ta ce,
“Yan mata fa an motso musu tsohuwar sha’awarsu. Kwa jure ma yara, tunda dai ba mazaje gare ku ba.”
Sarah ta taɓe baki.
“Please ni dai ku tashi zan kwanta. Uban wa ya ce dole sai kun saurari labarin bayan kun san ba dauriya ke gare ku ba?”
Rumaisa ta miƙe cikin sanyin jiki ta nufi gadonta. Mini skirt ne a jikinta wanda babu abin da ya ɓoye mata. Daidai da shatin pant ɗinta ana gani. Sai wata ƴar ficiciyar half best wacce da ita gwara babu.
Sakeenah ta ɗaga kanta ta ƙare ma siffar Rumaisa kallo, sai ta ji komai nata ya ƙarisa dagulewa. Tamkar ta je ta rungumo Rumaisar haka ta ji. Take munanan ƙudirirrika suka fara ɗarsuwa a cikin zuciyarta. Wanda ba ita kaɗai ba, yasu-yasu ɗin duk hakan ne.
Misalin ɗaya na dare suka kashe wutar ɗakin nasu. Sai dai dukkaninsu babu nutsuwa a tattare da su. Karatu ne ya zame musu tamkar ibada, littafin da babu batsa ma sam! Bai musu ba. A cewarsu ai babu harka a ciki. Su kuwa babban burinsu shi ne su karanta littafin da zai wanzar da rashin nutsuwa a zukatansu. Ba wani abu suke ƙaruwa da littafin ba ko kaɗan, sai ma wahaltar da kansu da suke yi.
Amma suna ji a zukatansu ba za su taɓa bibiyar wani littafi wanda ya ƙunshi faɗakarwa ko kuma ilimantawar a cikinsa ba. Da zarar ma sun fara suka ci karo da mai waazin, sai su fara tsinar marubuciyar, suna zaginta, suna ɗaukar alhakainta, kawai saboda ta ƙi ta yi musu yadda suke so.
Littafin da ba su fara bi ba kuwa da zarar sun ji ƙenƙyashen zance cewa akwai harka a ciki, to fa duk yadda za su yi su same shi sai sun yi, ba za su taɓa bari ya wuce su ba.
Har ma ta kai da sun san marubutansu musamman wanda suke yin irin abubuwan da suke so a labaransu. Suna kuma tare da su sosai, sun zama huge fans a gare su.
Yan matan nan bakwai da suke ɗaki ɗaya a hostel na jami’arsu, kansu haɗe yake sosai, suna kuma tare da manyan marubutan da suka yi suna wurin yaɗa alfahsha a tsakanin mutane, ta hanyar yin rubutu irin wanda ya take sharia.
‘Kina wuta muna bin ki da fetur. Kina ƙamshi muna bin ki da humra. Fire them…’
Da sauran wasu kalaman, su ne kawai aikinsu. Su kuwa marubutan abin da ke daɗa kawo ƙauna a tsakaninsu kenan. Kuma yake ƙara musu ƙaimi da azama wurin ci gaba da kawo ire-iren wancan labaran.
Labarin da ƴan matan suka karanta a yau ya sha bamban sosai da sauran labaran batsar da suke karantawa. Domin kuwa babu sakayawa sam a cikinsa. Komai a bayyane yake, tamkar kana kallo practically.
Wannan dalilin ne ya sa hankalinsu ya daɗa tashi, suka shiga yanayi mai wahalar controlling.
A hankali Sarah ta miƙe, lallaɓawa ta rinƙa yi ta yadda babu wanda zai ji ta. Hasken da ya gitto daga can wajen hostel na haska mata kaɗan, ta haka har ta gano inda gadon Rumaisa yake.
Bayan ta isa ta tsugunna a bakin gadon, ta jawo hannun Rumaisa ta rinƙa mata yawon tsutsa a hankali. Ko da Rumaisa ta ji ta ta gane manufarta sarai, to ita ɗin ma abin da take jira kenan. Sai ta langaɓe, cike da jin daɗi, har lokacin da susar ta iso bisa ƙirjinta.
A daidai wannan lokacin ne suka ci gaba da faranta rayukan junansu. Har sai da suka ji su daidai sannan suka rabu, cike da farin-ciki Sarah ta koma bisa gadonta ta kwanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *