- AL’KALAMINE SILA CHAPTER B KARSHE
A daddafe ta samu ta gama typing ɗin, tana jin wani irin yanayi, wanda ya zame mata jiki, a duk sadda take rubutun labarin haka take kasancewa a cikinsa.
Wayar tata ta jona jikin chaji sannan ta dawo ta kwanta. Ta runtse idanuwanta, tana ayyano yadda wasu abubuwa suka wanzu a cikin labarin da ta gama rubutawa.
Ta rasa abin da za ta yi, sai ta jawo pillow ɗinta ta rungume, tana yin wasu irin abubuwa masu wuyar fassarawa.
A take kuma gabanta ya hau faɗuwa, tunowa da mafarkin jiya da ta yi. Ta gaggauta sakin pillow ɗin nata, ta dafe gabanta da ke tsananta faɗuwa, fargaba ta wanzu a cikin zuciyarta.
A cikin wannan halin ne barci ya ɗauke ta, ba tare da ta yi addua ba, kodayake dai dama ba saba yin ta ta yi ba..
Ilau kuwa, ta sake yin wani mafarkin, sai dai na yau ya sha bamban da na jiya. Wasu irin ruwa ne ta ji suna tsiyaya daga cikin idanuwanta, ta tara hannunta da nufin murje ruwan. Daidai sadda ta ɗora hannun a fuskarta, sai ta ji wasu irin abubuwa sun caki fuskar tata, tamkar allurai ne a jiki.
Hankalinta ya tashi sosai, ta yi saurin janye hannun nata, tana jin yadda raɗaɗi ke addabar fuska da idanuwanta. Wannan ruwan bai daina fita ba sai ma tsananta fitar da ya yi.
Tana cikin neman mafita ne ta ji wata irin murya ta karaɗe kaf ilahirin ɗakin nata. Muryar garjejiya ce da alama namiji ne, tun tana jin shi daga nesa har ya matso daf da ita.
Ta saka hannuwan nata a kunne da nufin ta kare ƙarar, sai ta sake cakar kunnuwan kamar yadda ta caki fuskar tata ɗazu. Ta gaggauta janye su cikin fasa ƙara mai tsanani.
“Mun gina tarbiyyar ƴarmu amma kin lalata mana ita ta hanyar wulaƙantaccen al-ƙalaminki. Ina ta ba ki alama a tunanina ko za ki hankalta ki daina lalata mana tarbiyyar yara, amma sai na ga abin naki ƙara yin gaba yake yi ma.
Idan har halinki shi ne ruguza ginin tarbiyyar da iyaye suka jima suna yi wa yaransu, to ki sani abun ya ƙare! Daga yau ba za ki sake samun damar yin rubutun ba ma bare har ki ci gaba da lalata wasu.
Ni aljani ne, aljanin da ke jikin mahaifin ɗaya daga cikin yaran da kika yi silar lalacewarsu. Na jima a jikinsa, sai dai ba na tasar masa. Babban abin da yake ɓata min rai shi ne in ga ranshi ya ɓaci.
An kama ƴarsa kwance da namiji, kuma a cikin gidansu, wanda hakan ya yi silar zubewarsa, yana can kwance da mutuwar ɓaren jiki. Mahaifiyar yarinyar ta shiga ƙunci da damuwa, ita kanta ba wadatacciyar lafiyar ce da ita ba.
Kin san cewa kuwa ba a nan abun ya tsaya ba?
Rubututtukanki sun ƙeƙasar mata da zuciya, ta zaɓi tafiya ta bar iyayenta, ta bi namiji.
A halin da ake ciki kenan yanzu. Wannan dalilin ya sa na ƙudirci aniyar ɗaukar fansa, ke ma na guma miki tamkar yadda kika guma wa wasu. Ke ma ki naƙasa kamar yadda kika yi silar naƙasar wani.
Sannan kuma na tabbatar cewa ba a kansu kawai abun ya tsaya ba, wanda kika yi silar lalacewarsu suna da yawa. To an gama!”
Yana kai wa nan ya furzar da iska daga bakinsa. Iskan ya isa har cikin idamuwanta, a take ruwan da ke fita daga cikinsu suka tsaya.
Abubuwan da suka fito daga cikin hannuwanta duk suka koma, sannan ya ɓace ɓat! Daga ɗakin.
A razane cikin kiɗima ta tashi zaune. Zufa ta gama wanke mata kaf ilahirin jikinta.
Wani irin zugi haɗi da raɗaɗi take jin idanuwanta na mata. Haka hannuwanta ma, tamkar ta cire su ta yar haka take ji.
Da ƙyar ta samu ta lalubo wurin kunna haske ta kunna. Sai kuma ta yi ƙoƙarin buɗe idanuwan nata, amma sam! Suka ƙi buɗuwa. Duk yadda za ta yi ta buɗe su ta yi amma gam suka manne suka ƙi buɗuwa. Azabar da take ji a cikinsu ba ta misaltuwa, tsananta kawai abun yake yi.
Ƙara ta saki da ƙarfin gaske, wacce ta rakaɗe kaf cikin gidan, har sai da iyayenta suka farka.
A guje suka yo ɗakinta, da kuma ƙannenta maza guda biyu, sai yayanta namiji ɗaya. Suka yo kanta a kiɗime suna tambayar ta abin da ya faru.
“Abba na kasa buɗe idanuwana, ku taimake ni Abbana. Wallahi duhu kawai nake gani.”
Kanta suka yi suna jinjina lamarin, yadda take kuka sosai duk sai suka tausaya mata.
“Abba hannuwana ma kamar za su cire tsabar azaba. Ku taimake ni Abba, na shiga uku ni Surayya!”
A haka wannan daren ya ƙare musu, a wahalce sosai, amma idanuwan nata sun gaza buɗuwa.
A tsawon wayewar garin nan, sosai hannuwan Surayya suka kumbura suntum, tamkar za su fashe. Ga wani irin rurewa da suka yi, wani irin ruwa mai yauƙi na ɗiga daga ƴan yatsun.
A haka rayuwar Surayya ta ci gaba da tafiya. Ta makance, hannuwanta sun lalace, a ƙarshe ma aka yanke shawarar yanke mata hannuwan saboda abun ƙara ta’azzara kawai yake yi.
Duka hannuwan nata aka yanke iya guiwar hannu, kuka iya kuka Surayya ta yi shi. Sai a yanzu take nadamar abin da ta aikata. Ga shi readers tun suna kiranta su ji ci gaban zazzafan labari, har sun gaji sun daina. A nan ta tabbatar cewa ba saboda Allah suke son ta ba, dama saboda labarin da take yi musu ne kawai. Ga shi yanzu da duniya ta juya mata baya, su kansu sun guje ta, sun daina neman ta.
Mahaifiyarta ce ta shigo duba ta da hannu, a nan ne Surayya ta cire son zuciya, ta bata labarin kaf abubuwan da suka faru, har kalar rubutun da take aikatawa sai da ta ba ta.
Sosai uwar ta jinjina lamarin. A ƙarshe aka kai ta wurin wani malami, ya mata addua sosai sannan ya bata magunguna. Tsawon watanni biyu ana mata maganin, aka samu nasarar idanuwan nata suka yi sauƙi sosai, tana gani biji-bini.
Wannan shi ne ƙarshen rayuwar Surayya. Ta biye wa zuga-zugin fans ɗinta, ta biye wa koɗa tan da suke yi, ta afka ga halaka. Ta zama musakar ƙarfi da yaji. *AL-ƘALAMI YA YI SILAR NAƘASAR SURAYYA.*
Muna roƙon Allah Ya kare mu da kariyarSa, ya tsarkake mana zukatanmu mu yi tsarkakken rubutu. Allah ya sa wannan labarin ya zama ishara ga marubuta masu irin wannan halin. Wallahi kaɗan kenan daga al’amarin Allah. Idan Surayya ta naƙasa ne, to ke kina iya mutuwa har lahira ta silar alƙalamin nan da muka miyar ba a bakin komai ba, muka ɓata shi.
Mu tuba zuwa ga Allah, mu rubuta abin da za mu iya kare kawunanmu a kansa ranar gobe ƙiyama.
Mutuwar nan da muke ji fa ba ta alerting, zo wa mutum kawai take yi a duk sadda ta ga dama.
Yau a ce kina kan rubuta wani labari sai Allah ya ɗauki rayuwarki, ta yaya kike tunanin za a kwatanta ki cewa ke ce kika mutu? Wallahi cewa za a yi wannan mai rubuta littafi kaza, wanda ya ƙunshi abu kaza, ai ita ce ta mutu.
Wa iyadhu billah! Kowa da kuke gani shaidar kirki yake so.
Mu wa kawunanmu faɗa, mu gyara alƙalaminmu, mu yi rubutu ba tare da son zuciya ba.2
Ku ci gaba da bibiyarmu, shafi na gaba insha Allahu za ku ga yadda rayuwar Zaliha za ta ƙare.