ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 26 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
ce masa sai dai idan ta gama wannan makarantar ayi musu baiko, biki kuwa sai Allah ya dawo da yayanta lafiya Mahaifiyata ta bata labarin Kabir, ita kuma tace,
“To ai kin ji tsiyar ke nan, irin wadannan samarin masu nacin idan an nuna ba ayi dasu maimakon suyi hakuri, a a, sai su Kara tuso kansu, a gaba su nemi ruda maka ya”
Haka irin wannan hirar ta kasance har na yi
barci na barsu. Da safe bayan na gama *yan gyare-gyaren gida na so in shiga gidan su Hadiza, amma saboda maganar da na ji su Inna na yi jiya sai na ji duk raina ya baci, na ga ko ban sami Aliyu ba ya ya za a yi ma a ce in auri Aminu, ni ko a mafarki bana jin zan iya son Aminu duk da dai rabona da ganin sa tun ina firamare sai dai a hoto. Bayan Hadiza ta shirya ta biyo mini zuwa unguwa da muka yi alkawarin za mu gidan wasu kawayenmu.
A irin wannan zyara ce na lura da yadda wasu kawayen namu suke yi mini wani irin
kallo na bakin ciki, a cikinsu Zaliha ce ta Fito baro-baro ta gaya mini, tace,Asiya yan Kaduna, ai mu yanzu kinfi Karfinmu irin wannan shiga, da yadda launin jikinki ya canza sai kaCe yar Wani gwamna?” Na yi tsaki na ce, “Ba yar gwamna ba ce dai
“yar masinja ce, sai dai kada ki yi mamaki wata rana ki ga na zama matar gwamna in Allah ya yarda, ku wallahi ba ku san mutunci ba, ina laifin dama nazo gaida ku, amma tun da abin ya zama tsiya ba ku kara ganin Kafata a gidanku” Zaliha dai ta ce,Haba Asiya ki yi hakuri naga kin bata rai ban san abin zai yi zafi haka ba Muna nan tsaye sai ga malaminmu mai koya mana karatun Islamiyya, muka durkusa muka gai dashi
na bude jakata na dauko naira ashirin
*yan biyar-biyar sababbi fil na ce,Malam ga ta Annabi”. Ya yi murna kwarai, ya sa mini albarka. Ita ma Hadiza ta fiddo naira goma babu ko kari ta mika masa. Sai nan da nan Zaliha ta tabe baki ta nuna masa dai bakin ciki a fili. Sai Hadiza ta ce,Don Allah Asiya mu je kawance da irin ku Zaliha ai ba dole ne ba”
Muka rike hannu da ni da Hadiza muka yi
tafiyar mu. Na ce,Hadiza ko mun koma makaranta mu fita hanyar dukkan kawayenmu, mu maida hankalinmu wajen karatu, tsakaninmu dasu sai sannu-sannu kawai?? Hadiza taCe,wallahi
Qawancen ai ba dole ba ne, me za su bamu wanda Allah bai bamu ba Haka muka
kasance cikin yan sauran
kwanaki biyar mu koma makaranta, idan bamu
gidan su Hadiza to muna gidanmu.
Ranar Asabar da safe na dauko kayan gyara
gashina da Mama Inki ta saya mini, na je gidan su Hadiza ta gyara mini gashina, ni mana gyara mata nata gashin, kai idan ka gan mu a wannan rana ka dauka gidan miji za a kai mu.
Da misalin karfe biyu saura kwata sai ga
Mukhtar, muka je muka shirya masa abinci. Hadiza na zaune daf da shi yana ci tana Kara zuba masa muna taba ‘yar hira, ita kuma mahaifiyarsa na cikin gida wajen Inna Hafsatu da yake tare da ita sukazo.
‘Har zuwa karfe biyar amma Aliyu baizo ba,
Mukhtar ya ce,Kanwata na yi jiran Aliyu-amma
kin ga har yanzu bai iso ba, kuma kin ga na zo da Inna ba ni so mu yi dare a hanya”Na ce,
“Eh kam, tafiyar dare ba ta da dadi,
ina ganin sai wajen shida zai iso saboda ka san shi a nan zai kwana Daga nan sai na tashi tsam na shiga gidan su Hadiza saboda in basu wuri su ji dadin sallama.Bayan ya tafi tare da mahaifiyarsa muka fara duba irin kayan da ya kawowa Hadiza kwalaye biyu manya, kayan tafiya makaranta ne na masarufi wato
provision da kayan shafe-shafe su sabulai da turare masu Kamshi,sai kuma agogo da takalma rufaffu biyu ja da baki
Ita kuma mahaifiyarsa ta kawo mata atamfofi
turmi uku, yar Ingila daya,yar Holland biyu,
“Da muka gama gani Inna Hafsatu ta shiga bamu labarin ita mahaifiyarsa ta matsu da a ce an basu Hadiza, na ce su yi hakuri nan da wata biyar idan kun gama wanna makarantar za ayi baiko”Ta ci gaba da bamu labarin cewa,
“Mukhtar su uku ne ta haifa dukkansu maza ne, Mukhtar shi ne dan auta saboda haka ne take ji da shi kwarai ainun Kuma cikinsu shine mai kaifin hankali, shine ma ya tsaya ya nemi iliminsa sosai saboda a yanzu haka
digirinsa biyu, su kuwa yayyensa yan shiririta ne. Wannan labarin kuwa ta same shine ta
hanyar wata yar’uwarta
wadda ta ke zaune
a Katsina, ita ta binciko mata tarihin gidan su Mukhtar, shine dalilin da ya sa Inna ta amince da su Muna zaune Inna na mai da mana wannan labari sai ga Zainab ta shigo, ta ce,
“Yaya Asiya kiZo in ji Inna”Na ce,To, mu je”
Na sami Inna a kicin tana ta kokarin hada
abincin dare, ta ce mini,Wani yaro aka aiko ga
wasika nan da waccan jakar ledar
Na ce,Ina yaron?”Ta ce,Bisa keke yazo amma ya tafi” Na bude wasikar sai naga aiken daga Aliyu ne, ya iso amma ya je gidan yayansa sai yazo bayan sallar isha,i, amma ga danyen,,,,,nan in yi masa farfesu kafin yazo
Kafin a kira sallar magariba harna harhada
kayan miya da sauran kayan Kamshi na dora bisa wuta, bayan na gama sallar na ci gaba da girkin kafin a kira isha na gama. Sannan na yi wanka na kimtsa.Yusuf ya shigo ya ce,
“Aliyu ya zo”Na ce,Shi kadai ne ko da wani?”
Ya ce,Su biyu ne”Na yi sauri na harhada musu yan kananan farantai guda biyu na zuba kifin cikin wani tangaran daban, na kuma shirya musu cincin da gwandar daji na bai wa Zainab ta kai musu dakin Yaya Abubakar, ni kuma na dauki ruwan sha na bi ta a baya.Bayan mun yi sallama sun amsa na sami gefe guda na zauna, sannan na gai da su, na tambaye shi
ya ya hanya. Ya ce,Lafiya lau?.- Ba da bata lokaci ba ya shaida mini ga Umar karamin ango nan ya kawo mini. Na ce,
«Amma ka kware ni Aliyu, ai da ka gaya mini da ban gai da shi ba sai ya sayi baki”
Suka Kyalkyale da dariya, ya ce,Ai wata
rana kin rama Asiya
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe