ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 12 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Nayi masa kallon biyu babu na watsar, na ce,

“Ai ban saka ba, ko ka ga wasikata ta neman ka je dauka ta?”

Sai ya shigo cikin dakin ya ce, “ke Binta kanki daya kuwa yau?”Na ce, “A ‘a, daga turu aka kwanto ni karewar kai daya ke nan”

Ya zauna ya kwantar da murya ya ce, “Don Allah don son Annabinsa ki kwantar da hankalinki ki gaya mani laifin da na yi maki kada ki zartar da hukuncin da za ki dauki alhakina, ko mene ne da kike zaton na yi miki, to ai gara ki yi bincike kafin kici zarafina Binta

Da naji magiyar ta yi yawa, sai na ce,

“Aminu ka yi niyyar yaudarata, amma ta Allah ba taka ba, kai kuma Allah ya baku zaman lafiya da Asabe Labbo” Ya ce, “Wacce Asabe Labbo?” Na harare shi na ce, Ka fini saninta

Sai fada ya kaure a tsakaninmu har Gwaggo tasa baki, ta kira mu na fara kuka, sai shi Aminu ke mai da raddi.

Gwaggo ta ce,.Lalle kina da aiki in don

wannan, nina dauka wani abu ne daban? Sai ki shirya domin namiji mijin mace hudu ne”Na Kara ci gaba da kukana, na ce,Ni kam na yarda in auri wani ya yi mani kishiya da in auri Aminu ya hada ni da wata

Gwaggo ta ce, “Turkashi!” Shi Aminu jikinsa ya dau rawa yana ‘yan rantse-rantse. A wannan dare na aika ma Baba Sule da wasika a kan bani ba Aminu, aure dai ni na ce ina yi, amma yanzu na fasa.

Rigima ta tsananta a zuriyarmu, tun daga

Kaduna zuwa Funtuwa, har Yola rigima ce, wasu na goyon bayana, wasu kuma Aminu, yayin da sauran suka ce gara a fasa kada mu bata zumunci nan gaba.

Kakanmu kuwa Alhaji Amadu ya fi kowa bakin ciki, ni kuma ga kishi a zuciyata ga bala’in son Aminu, in kwana kuka amma da safe inyi mirsisi don kada a gane mani.Wata rana Aminu yazo gidanmu da daddare wajen mahaifina, sun dade suna magana daga bisani aka kira ni, Baba ya ce, “In fadi masa yadda abun ya «fara”. Na gaya masa komi.

Aminu ya rantse ya Kara a kan cewa, “Lalle ba shi ya ba ta wadannan hotuna ba, amma ya duba a kundin hotumansa bai gani ba”

Babana ya rika mani wa’azi da gargadi a kan yana tsorona da hakkin Aminu, kin san maganar iyaye da abin da rai ke so, sai na hakura na koma dakina.

Zuwa can Aminu ya biyo ni ina zaune bakin gado, shi kuma yana tsaye a tsakar daki yana kiran sunana cikin jan hankali.Na dago a hankali na dube shi, ya miko mani hannu ya ce, “Zo nan ‘yar kanwata?” Na tashi cikin mutsuwa ya tarbeni ya rungume ni, na ji ya koma dan siriri.Na ce, “Aminu ka rame da yawa”Ya ce,

• “Laifin wane ne?”Na boye fuskata a kirjinsa ina murmushi. A wannan dare bai bar gidanmu ba sai da karfe daya na dare.

Da gari ya waye muka shirya zuwa gidan kakanmu takwaran Aminu a Tudun Nufawa. Yana ganinmu ya fashe da dariya ya ce, “Oho dai kun ji kunya mun ganku a rana”. A ranar da aka yi mana tsiya bamu da bakin magana.

Amma daga wannan sai me zai wakana?

Tsiya ba ta kare ba wasa sabon girki. Wata rama ina kwance ina bitar littafina bayan na yi sallar la’asar, sai Abdullahi Kanin Aminu wanda yake aji uku a sakandire ya yi mani sallama ya shigo, ya ce mani,

“Gwaggo Badijo ta aiko shi lalle mu tafi tare yanzu zan mata kitso”

• Na ce, “To” Na shirya na shaida ma Gwaggo Karima.

Muna tafiya muna hira da Abdullahi har muka isa kofar gidan Baba Sule, na dubi motar yallabai Aminu na ce, “Su ranka ya dade ana nan ana barcin rana”. A zuciyata”Muna shiga harabar gidan sashen su Aminu za ka fara shiga kafin na Baba, sannan na Gwaggo.

Me zai faru? Sai na hango wasu bala’ in takalma na mace a bakin Kofar dakin Aminu, sai gabana ke dukan uka-uku, cikin hanzari na doshi dakin Aminu na daga labule.

Aminu na tsaye ita kuma Asabe Labo na tsaye gabansa, ga jam bakinta a kumatun Aminu, ya ture hannunta da ke bisa kafadarsa, tana hada ido dani sai ta yi murmushi ta ce, “Lah! Ashe ke ya gani?’

Na fara kallon sa na juya na nufi gidanmu.

Ina shiga dakina shima ya shiga, na daga kai na dube shi na ce, “Aminu ba ni kaunarka, ba ni kaunar ganinka, daga yau in ka kara zuwa gare ni ranka zai baci, ba na kaunar wata kalma daga gare ka, ka fita”.

Na san lalle ba shi da niyyar fita, sai ni na tashi zan fita ya rike ni, na yi masa wani irin kallon na shima ya san sauran.

Rigima tayi tsanani a danginmu, har iyayenmu mata suka yanke shawarar a bar wannan aure, mun same su suna zumunci, mu bamu isa mu hada su ba.

Baba Sule ya kori Aminu ya koma gidan

Yaya Ahmed, wanda shi kadai ya bai wa Aminu goyon baya, har ya sha alwashin sai ya gano makarkashiyar abin.

Zuwan Aminu na Karshe gidanmu shi ne randa ya je ina wanke-wanke, sai na saki kwano a kasa na rushe da kuka har Gwaggo ta firgita ta fito daga daki aguje, sai na ce, “Ni wallahi idan ba za ku hana shi zuwa gidan nan ba, to ni zan bar gidan”.

A ran nan na ga fushin Gwaggo, in da ta ce,

“Ke rufe mana baki mutuniyar banza wadda ba ta san ciwon kanta ba, ba barin gidan ba idan kin isa ki bar duniyar, amma ke din nan baki isa ki hana Magaji zuwa nan gidan ba, sha-sha-sha za ki rufe mana baki ka da ki tara mana makwabta a gida don neman tonon asiri irin naki na mahauka”

Aminu ya rika ba ta hakuri yana fidda

Kwalla, ya ce, “Insha Allah ba zai zama sanadiyyar barina gida ba’. Ya dube ni duba na nadama da kaico yasa kai ya fita.

Asiya kada ki tambayan maganar kuka, wannan babu dadin fadi a wannan zamanin, na tsani kaina na kuma tsani Aminu, domin shine uwa uban. saka ni cikin wannan kunci na rayuwa, domin shi ya

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *