ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2  CHAPTER 24 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Zuwa can ya nisa ya fara zazzaga fada Ni dai kaina na sunkuye ina sauraro can na.JI masifar ta isa sai nace

*Dakata haka, yanzu me kake so in yi? Zaman, matarka nake ko kuwa. a.zaman wa nake?”Sai ya Kara fusata, yace Ke karki gaya mani maganar banza, idan za kiyi samari ban hana. kiba, amma ai bai kamata suna daukar ki a mota ba

Na ce,eh, ai ka san shi dan iska ba ya lura;

idan iskancinsa ya motsa, da kowa ma yi yake, tunda ina bin mutane iskanci dole ne ka zarge ni da yin. hakan Ya ce, Me kike so ki gaya mini ko kuma,

rashin kunya za ki yi mini?”

Na ce masa, “Mene ne sabo a wajen ka, ka san bani da ita kunyar, sanda ake rabata  bani wajen”

Ya ce, “Yanzu ke ba kyajin kunya a  dinga ganin ki da irin su Alhaji Ibrahim? A kayan miya. bakin me yake, amma fa ga mai tunani”Na ce, A hayye-nanaye, ai baka san a ko me yakeba? To attaruhu ne mai ya yi zafi Wannan magana ba karamin Kara daga ma

Aliyu rai ta’ yi ba, ya harzuka tare da fadace-fadace naci gaba da cewa,Wannan fa shi ne harara cikin duhu, idan ba ka san wani abu ba yau zan gaya maka, tun tsawon shekarun da muke tare da kai muke tare da Ibrahim, kuma ba don. bata mana lokacin da kake ba da tuni na tsufa a gidansa.

Aliyu zan gaya maka abu guda, duk ta zargi da kishi ya Kare, idan da gaske kake sona, to a yau ka aiko gobe kamar yanzu an dade da daura mana aure, idan kuma yaudara kake yi to ka bar masu aure na su aure ni, amma ni na gaji kura ta kai bango, na gaji da

Jiranka” Na fashe da kuka, hankalinsa ya tashi, na shiga gida na barshi tsaye a zaure. Mun sami lokaci mai tsawo muna rigima da Aliyu daga bisani muka shirya. 

Abin mamaki ba shi karewa a duniya, dana

ban haushi da na murna, kuma Hausawa sun ce komi nisan jifa kasa za ta kamar yadda aka ce komi da lokacinsa ban da ikon Allah.

Abin da yasa na ce haka, wata rana muna

Daki ni da Zahra°u da la’asar sakaliya mun yi

•kwalliyarmu daidai mu za mu tafi lambun shakatawa mu dauki hoto da kyamarar Aminu, sai ga wata kawarmu tare da wata wadda ban taba gani ba, Kawarmu ta ce, “Asiye ke ake nema kin yi bakuwa dega Kano”

Na yi masu sannu da zuwa, da duk abin da ya dace a girmama bako da shi. It wannan bakuwa babu abin da take illa aikin kallonmu.

Na kawo mata hotuna tana kallo, na lura da. idonta ya cika da kwalla, amma ban san dalili ba.

Zuwa can ta dube ni, duba na hakika, ta ce,

“Sannu Asiya’Na ce, “Yauwa”

Sai jikina ya bani lalle da magana a zuciyarta, ta rika raya mani kome ne ne zai faru ban ga abin da zai daga mani hankali a kanta ba, sai • ma ni in firgitata.

Bayan ta gama mana kallon kut da kut sai ta

Tashi za ta tafi, har ta kai bakin kofa nace mata,

“Don Allah kada ki ce reni ne, amma ban gane ki

ba. Sai ta ci gaba da ta fiya mu kuma muna binta a haya, har muka kai gindin mota ba tare da ta ce komi ba, baya ga uhum!

Da Zahra’u ta lura lalle ba za ta bamu sani ba sai ta kara ce mata,

“Baiwar Allah kin nemi inda

muke kin zo mun gaisa, amma kin ki yarda mu san ko ke wace ce, don Allah ki daure ki ba mu sani”

Sai ta bude mota ta nuna alamun shiga, < sannan tace, “Na zo ganin Asiya ne saboda an bani labarin wai za ta auri wani dan uwana, shi ne nazo in ganta kurum”

Zahra’u ta yi sauri tace Wane ne dan’ uWan

naki ke nan fa?”

Sai ta yi ‘yar dariyar yake hakora ta shiga motarta ta tayar. Ta dube ni ta ce, “Idan Aliyu ya zo ki ce masa Doctor Mairo na gaida shi”

Na dube ta da kyau, na ce, “Zan gaya masa, amma kanwarsa zan ce ko yayarsa”

Ta ce, “Duk yadda kika ga ya dace shi za ki ce”. Ta ja mota muka daga mata hannu har ta bace. Na dubi Zahra’u ita ma ta dube ni, sannan muka yi murmushi, na dora hannuna bisa kafadarta muka juya muka tafi.

Na ce, “Zahra’u kin san wani abu??” Ta ce, “A’a”

Na ce, “Ni kuwa matar nan bata kwanta mini a rai ba, duk yadda za ayi wani abu zai biyo baya, kuma za ki ce na gaya miki”Zahra’ u tace, “Nima ina zaton hakan, amma kuma kin yarda suna da dangantaka tsakaninsu da Aliyu?” Na ce, “Ban jin hakan, amma na sha alwashin in Allah ya yarda zan gano komi ke tsakaninsu da Aliyu” ilai kuwa washegari muka tafi Kaduna gidan Baba Suraj inda suke zaune a unguwar rimi. Bayan mun gaisa da Jamila matarsa nace Ina Baba Suraj?” Ta ce, “Ya ta fi Legas”

Da muka nutsa cikin kogon labarai sai kamar yadda mata suka saba idan an hadu, sai na sake tambayarta, “Shin wai kuwa Jamila ina son don Allah don Annabinsa ki Kara mani haske game da wata mata idan kina da masaniya, ni dai na tabbata ba jininsu daya ba da Aliyu”.Jamila ta ce, “Wace ce wannan Asiya?”

Hmmmm