cinyarta ina fadin “Inna albishirinki?” Ta ce, “Goro fari”
• Na ce, “Sai kin bani. Ta dauko dankwalelen goro daga cikin wata Kullin leda ta bani. Na ce mata,
“Wallahi Inna tare muke da Yaya Aminu jiya ya dawo”
Ta yi tsaki ta ture ni, tace, “Ke ni bace mini da gani wannan zancen ba nawa bane”
Ni kuwa sai ina ta kyalkyala dariya tare da su
Mama Inki da sauran jama’a, ita kuwa mahaifiyata don murna ji take kamar ta sheka kofar gida ta taryo shi.
Ana cikin wannan ruguntsumi murna sai ga shi ya shigo, wallahi mahaifiyata don tsananin murna sai ga ta durkushe gaban Aminu, muka hada ido da ni da Yaya Aminu muka yi murmushi.
Haka ya ci gaba da gaisawa da jama’ a tare da yin ta’aziyya. Bayan kura ta natsa ya nufi wani daki da yake a zaure, amma kafin ya tafi sai da ya waigo ya kira sunana ya yafito ni da ido, na bi shi zaure.
Ya ce, “Don Allah ki ce ma su Inna Aisha su rokar mani Inna Hafsatu tazo nan mu gaisa saboda mutanen sun yi yawa a cikin gida”.
Na ce, “To”. Na shaida ma Inna Aisha. A nan fa aka tarar ma Inna Hafsatu, da kyar aka shawo kanta Inna ta rakata, sai daga baya Inna Aisha ta dawo ta baro ta. Bayan an gama abincin rana na dauki na
Yaya Aminu zan kai masa, na yi masa sallama na aje
masa, sannan na dubi Inna Hafsatu wadda na lura hira ta yi dadi ita da dan fari, na zolaye ta na ce,
“Inna ko in kawo maki naki nan?”Ta ce,
“Ke Uwani bana son shegantaka”. Ta
mike ta shiga cikin gida. Sai Yaya Aminu ya ce
mani, “Asiya maza ki gama mu tafi kin san na gaya
maki Kano zan wuce”
Mun isa Zariya na yi ma Yaya kwatance
hanyar da zai bi inda na san zan ga Zahra’u, ai kuwa sai na hango ta a zaune ta kura ma hanya ido, ban
san lokacin da na kyalkyale da dariya ba, har na bai
wa Yayana mamaki.
Ya ce, “Asiya lafiya?”Na ce, “Zahra’un da nake baka labari ce na hango”
Shi ne na nuna masa da hannuna, ba ta san motar ba balle mai motar. Sai da na fito, ta kuma tabbatar ma idonta lalle nice, sai ta rugo da gudu ta
rungume ni. Ta ce, “Asiya kin cika mutuniyar wof kin
cuce ni a wannan kwanakin, sai kawai na shige daki
na cimma wata bakar wasika, kada ki so ki ga fushin
da na yi sai ka ce kumurcin maciji Sai na ce, “ke solobiyo ga fa Yaya Aminu na Rasha”
Shi kuwa Yaya Aminu yana jingine jikin mota yana mana murmushi, Zahra’u ta ji kunya Kwarai ainun har ta boye fuskarta a bayana saboda sokancin da ta yi, sannan ta daure suka fara gaisawa yana tambayar ta harkar karatu. Muka yi sallama ya ce sai ya zo kawo mani tsaraba, cikin satin nan idan kayansa sun iso, idan ba su iso ba sai wajen lahadi ko asabar zan gan shi.Mun isa daki ina kwancema Zahra’u irin tsarabar da na zo mana da ita, da ba ta labarin rasuwar da na iske. Ta yi mani ta’ aziyya, sai muka koma zancen Yaya Aminu.Ta ce, “Asiya Aminu ya fi Hadiza kyau, turkashi wai duk Aminu kyau gare shine ko?” Na ce, “Ke Zahra’u ke fa matar aure ce”Ta ce,
“Ai ba da wani abu ba har ga Allah, sai
dai an ce yabon gwani ya zama dole Asiya, duk da yadda idon mijina Aminu suke abin sha’awa ga kowa, amma: shi na Yaya Aminunku a kafe suke, kuma masu tsai da magana, amma ga wadda yake so, kuma a gaskiya idan kin tara maza dari da wuya ki sami masu cikar halitta irin tasa guda goma, ga kuma kyau. Gaskiya Hadiza ta more da wa Na yi dariya na ce, “Wacce Hadiza, ki ce dai matarsa ta more miji, ni kuwa abin da ya gaya mani jiya haushi yake bani
Ta ce, “Wani abu?”
Na bude jakata na nuna mata hoton da suka yi da wannan Baturiyar, na ce, “Wallahi daren jiya na tausaya mana Zahra’u mu mazanmu masu fita kasashen waje.
•Na rika kamanta wanna matar bisa Kirjin
Aliyu, hankalina ya yi mugun tashi, na ce,
“Yanzu angonki na can da tasa”. Muka Kyalkyale da dariya. Ta ce, “Ke Asiya ban da Aminuna, ki fidda shi a lissafi kin san Allah yadda kika tafi kwana biyun nan, da Aminu a Nijeriya yake da sai dai ya ganni gabansa. Haba Asiya kin ga irin so da jin dadin da ya nuna mani lokacin da muka je Yankari?
Abin ba a fada maku ku da baku san dadin aure ba”.
Muka kyalkyale da dariya, na ce,Aure insha
Allah gamu nan bisa hanya tunda dai yayanmu ya dawo, kuma daman dai shi ake jira balle na ga ya canza hali yanzu, duk fadan da yake mana da yanzu sai ji ake dani kamar zai lashe ni, saboda haka kin ga zai hanzarta ya ga an aurar damu
Ranar Juma’a bayan mun fito gwadawa, bamu sake fita ko ina ba saboda kada Yaya Aminu ya zo ya sha wahalar neman mu, amma har dare bai zo ba. Ranar asabar ya zamanto tilas mu fita zuwa wurin Kungiyarmu ta karatu saboda dai karatunmu na jami’a ya saba tilawar karatunmu na sakandire, sannan ni da Zahra’ u ba fanni daya muke karanta ba.
‘Yan Kungiyar su Zahra’u suka kebe wuri daya, dani da ‘yan Kungiyarmu kuma muka kebe waje guda. A ranar bamu bar tilawa ba sai da lokacin cin abincin rana yayi. Bayan mun koma daki mun yi wanka, sai muka bi lafiyar gado don mu huta. Da la’asar sakaliya muka tashi, na ce, “Kin ga Zahra’ u yau ma Yaya Aminu ba zai zo ba, abin da ya fi mu shirya mu leka cikin gari wajen bikin Attine kada ta ji haushi, kin san kwananta daya a wajen bikin ki”
Muka ci kwalliya yadda ya kamata, inda muka saka dogon wando cikin tsarabar Aliyu, kuma mun tsaru da kyau da kyau, wanda har mu da kanmu muka rika jin kunyar fita muna gudun kada a dauka barazanar ta yi yawa. Ko da yake ‘yan jami a babu ruwansu.
Mun yi shiga ta yadda wandon yake ja, ita kuma rigar fara ce da ratsin ja a jikinta, sai bakin takalmi da farin agogo, gashin kanmu kuwa mun hade shi a tsakiyar kanmu baki daya, muka matse shi da ribon ja da fari, muka fesa wasu bala’in turare
Hmmm