ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 29 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

har kala uku, inda muka dinga kamshi na

• musamman. Mun fito ina kulle mana daki sai ga Raulatu tana nishi, na ce, “Raula ya ya lafiya?” Ta ce, “Haba Asiya kin wahalar dani yau, kusan minti ashirin ke nan ina neman ku, idan na je can a ce kuna nan, har dai na hadu da wata ‘yar arziki tace mani taga shigar Zahra’u wanka, ga alama kuma kuna nan daki”

Na yi murmushi na ce, “Ayya Laura sannu fa,lafiya?’

Ta ce, “A’a, lafiya lau, kun yi bako ne ya ce yayanki ne Aminu Na ce, “Kai amma na ji dadi wallahi, Allah *

ya sa bamu riga mun fita ba”.Muka nufi inda yake zaune bisa kan motarsa

-yana kada ‘yan makullai, yana hango mu ya fara murmushi, muka isa fuskarmu cike da fara’ a tare da yi masa kyakkyawar maraba.Ya ce, “Baiwar Allah kin sha wahala dani na gode”. Ya mika mata naira hamsin. Raula ta daga mana hannu ta tafi.

Na dubi Yaya Aminu ya yi murmushi, na ce,

“Yaya Aminu ya ya hidimomin ke tafiya?”

Ya ce, “Lafiya lau, amma sai da na je Legos,

kin ga wannan motar na daya daga cikin kayana da

suka fara isowa” Ni da Zahra’u muka ce, “Muna murna”, Amma cikin harshen Turanci, wato

“‘Congratulation: Ya ce, “Na gode”Lalle ya more da mota mai suna Honda

Prelude mai launin kara ruwan toka, sai na neme shi

da mu karasa babban shagon da ake sai da kayan

ciye-ciye na cikin makarantarmu.

A nan na ga abin mamaki, lokacin da muka

bude gidan baya za mu shiga sai nan da nan ga Yaya

Aminu ya tsare ni da idanuwa, ba tare da na gane

manufarsa ba, sai kamannina suka canza don jin

tsoronsa, sannan ya dan saki fuska ya ce, “Asiya don

kun yi shigar Turawa za a mai da babban Yaya

direba, ai gara ki zauna gaba ki karrama Yayanki

ko?”Sai na yi murmushi na zaga gaba na shiga,

Zahra’ u ta shiga baya. Muka isa shagon, bayan mun

zauna bisa kujera sai na shiga cikin shagon sayen

kaya na sawo masa kek da coca-cola ta gwangwani

da kwai wanda aka nade cikin nama, na fiddo kudi

cikin jakata na biya na zo na sami Zahra’ u suna hirar

mijinta, kai ka ce sun dade da sabawa. Ya miko mani wasiku guda biyu tawa data

Zahr a°u, ya ce, “In ji Hadiza, saboda ya je Katsina ya gano ta”. Sannan ya ce, “Ya shaida mani, ya sanya ranar bikin Hadiza da Mukhtar da mun je hutu za ayi”

Sai gabana ya ba da ras! Na tuno maganar

Aliyu ya ce lalle da namu za a hada. Yaya Aminu ya fiddo mani wani dan Karamin akwati mai rawul ya miko mani, ya ce, “Ga tsarabata nan”. Ita kuma Zahra’ u ya ba ta wani kyakkyawan karamin agogon hannu, mukayi godiya. Sai Yaya Aminu ya ce,

“A’a, ban son godiya domin yiwa kai ne kin tuna?”

•Muka Kyalkyale da dariya ni da shi. Daga nan ne ya ci gaba da bamu labarin neman aikinsa.

Zahra’u ta ce,Ai ku Yaya ‘yan gata ne,

domin yanzu Nijeriya irinku take fafutukar nema”

Ya yi murmushi ya ce, “Eh, haka ne domin yanzu duk inda na aika da takarduna ina ganin akwai nasara?

Sai na ce, “Da ina da ina ka aika?”

Ya ce, “Na aika jihar Kaduna da jihar Kano, sai kuma gwamnatin tarayya kamar a Katsina Steel Rolling.

Muna hirar yana kurbar coca-colarsa sannu a hankali, sai na hango motar gwarzona. Aliyu, ina dariya nace”Lah! Zahra’u ga Aliyu” Muka mike tsaye, ya nufo mu a hankali. Yaya Aminu ya ce, “Wanda ake labarin ne ya zo?*

Ya iso inda muke suka yi hannu da Aliyu da Aminu, sannan Zahra”u ta je ta yowa Aliyu sayayyar abin motsa baki. Ya dube ni ya ce, Na ce, “Eh, wurin bikin Attine za mu nan cikin Tudun Wada Zariya, shima Yaya Aminu sa’a ya yi ya same mu”.

•Aliyu ya dubi Yaya Aminu da kyau, ya ce mani, “Kina nufin Yayanmu ne ya dawo daga

Rasha?” Na ce, “Kwarai kuwa”.

Sai suka sake sabuwar gaisuwa, tare da tambayar juna wasu al’amura da suka shafe su.

Aliyu ya yi mani gaisuwar kakana, ya ce ya je har

Kuka-Sheka ranar laraba.

Mun yi hira kamar ta tsawon minti ashirin da biyar, sannan Yaya Aminu ya ce,Zai wuce

Malumfashi, idan za shi Kaduna zai biyo ya sake

•tambayarmu ya ya ko akwai abin da muke so?” Na ce, “A’a, babu komi”

Muka yi sallaha ya tafi. Shi kuma Aliyu ya ce, “Sai ku shiga ku fito in rage maku hanya zuwa cikin gari ko, ko kun fasa?’ na ce, “A’a, bamu fasa

Bayan ya aje mu kofar gidan su Attine ya ce, zai je Zariya Hotel ya dan yi bacci, zai dawo karfe takwas na dare ya dauke mu. A haka muka rabu.

Muna tsakiyar cashe rawa wanda har na fara gajiya, amma abokai basu yadda su bar mutum ya huta ba, sai can aka ce ga* Aliyu yazo Na ji dadin hakan.

• Mun isa makaranta Aliyu ya nuna mani yana son. magana dani, a fuskarshi na gane hakan, sai na tsaya, yayin da Zahra’u ta ce, “Dama ina son zuwa Malumfashi in ma Inna gaisuwa, amma kuma bana son mu kwana saboda karatu”.

Ya ce, “To abin. da za a yi shine, ku shirya gobe da wuri inzo in kai ku mu dawo in wuce

Kano Ta-ce, “To na gode Allah ya kai mu, sai da safe”. Ta nufi dakinmu ta barni tsaye a gaban motar Aliyu, yayin da shi kuma yake zaune ya dora hannayensa bisa sitiyarin mota.

Na ce, “Aliyu yau kuwa na ga kamar baka da

“kuzari kamar yanda na sanka, ko ka yi ciwo ne?”

Ya dube ni da fararen idanunsa wadanda suka kada suka yi ja, sai ya ce,Wallabi nima kaina ba

Hmmm