zan ce maki ga takamaiman abin da ya dame ni ba sai Allah kawai ya sani Na sanya hannuna bisa goshinsa
Zuwa wuyansa naji sanyi Kalau, kuma idan ka dubi Aliyu da kyau ka san akwai magana, kuma na tabbatar akwai abin da ke damun zuciyarsa.
Sai na zagaya na bude kofar mota na shiga na zauna, na kamo hannunsa na hada da nawa, na harde yatsunmu Kai idan ka gansu yadda suka manne ka dauka haka Allah ya halittasu.
Da farko abin da na dauka kila ko a wajen aiki ya sami ‘yar matsala wadda ta daure masa kai, amma ni kam na san daga wajena babu komi wanda
*zai dagula masa lissafi, saboda haka ban sa ma raina wani abu ba. A haka dai cikin dabara ta mata na rika lallashinsa har ya kare ya ce mini, sal in na yi masa alkawarin abin da duk zai fadi raina ba zai baci ba, kuma ba zan yarda mu yi fadan da muka saba ba.
Na ce,Yanzu abin da ya fi damunka ke nan?”
Ya ce, “Eh”Na ce, “Na yi alkawari, fada mani”
Ya ce,Ina bisa hanya na doso hanyar
makarantarku, sai na sami zuciyata tana dakan uku-uku, wanda har gaban rigata ya rika dagawa sama hannuna ya rika rawa, babu abin da nake karantawa a zuciyata sai Lahaula wala Kuwwala illa billah aliyul aim. Bayan na aje ku dazun na tafi hote na yi odar abinci amma na kasa ci’
Daga nan ya yi shiru kadan, na kira sunansa a hankali, ya dago kai muka yi ido hudu da shi. Na ce,
“Har yanzu dai ba ka je inda nake son ji ba
Aliyu ya yi murmushi ya ce, “Kin amince in
fadi? Kwarai kuwa”
Ya ci gaba da cewa, “Gaskiya Asiya namiji ba ya iya yaudarar da namiji, mu maza mun san abin da ke zuciyar namiji dan’uwanmu a lokacin da muke a gaban mace da muke so kamar yadda ku mata kuna iya gane kishiyarku farat daya, idan kuna tare da saurayin da kuke so, ko kuma in ce mijinku” Sai na ce,
“Wai duk me ya kawo wannan kwana-kwanar Aliyu?”
Ya ce, “Zan gaya miki gaskiya idan ma bai riga ya sanar dake ba, wato abin da na gano yau lalle Yaya Aminu na matukar sonki, so kuma irin a aure
Asiya” gabana ya ba da ras! Haka labbana rawa suke yi na rasa yadda zanyi in yi magana domin tsananin rudewa, na ce, “Aliyu shi yasa aka ce zato zunubi ko da yo zama gaskiya, yadda ka gasgata da wai Aminu na sona, tuni kuma ina gasgata maka bana son sa, so irin wanda kake nufi. Ina tabbatar maka babu yadda za ayi ya ce haka domin ya dauke ni tamkar Hadiza, don Allah ka fidda wanna zargi a ranka, amma bai wa ranka auren mu ya zo, domin Yaya Aminu ya ce mani ya sanya ranar bikin su Hadiza, kuma yadda ka ce da namu za a hada”Ya yi sauri ya ce, “Insha Allah, idan kin sami dama sai mu hadu a Malumfashi kafin ayi muku hutu mu yi shirye-shiryen abin da ya dace, kin ga idan an yi hutu sai hidimar daurin aure da biki ke nan ya rage mana, ko ya ya kika gani?. Na yi sauri na bambare hannuna daga cikin nasa hannun duk sun yi zufa saboda mannewa, na dube shi na yi murmushi na matsa daf da shi na dora kaina bisa kirjinsa inda ya sanya hannu bibbiyu ya rungume ni yana mai shafa mani gashi tare da sumbatarsa.
Ni kuwa don tsananin jin dadi har bacci ya so
ya dauke ni bisa kirjin Aliyu, sai zuwa can ya duba agogo ya ce, “Asiya gara ki je ki kwanta domin kin ga gobe da safe za mu tafi Malumfashi”.
Na sami Zahra’u na karatu, ta dube ni ta girgiza kai ta yi dariya, sai na yi dukkan sallolina, na yi shirin bacci bisa gadona, sannan na warwarewa
Zahra’ u yadda muka yi da Aliyu. Ta yi sauri ta tashi zaune tare da yin ajiyar zuciya, ta daure fuska ta ce, “Asiya ture maganar wasa, amma maganar Aliyu bisa hanya take, domin ni tun ranar da ya fara kawo ki na lura da yadda yake kallon ki, babu maganar kanwa a wanna wurin sai dai maganar so. Kuma muna nan da ke ko bayan an aurar da ke wajen Aliyu ne, sai kin ji labarin ya ce shi ko ya so ki hanya ce bai samu ba
.Na ce,Ni kuwa kin san Allah daya. ne
Zahra’u bana sonsa ko kadan, in Allah ya yarda zarginku ke da Aliyu ba zai zama gaskiya ba
Zahra’u ta ce, “Bari in gaya maki wani abu daya, ba kawai ina son bata maki rai bane, a’a, ra’ayin da ke zuciyata ke nan. Wallahi! Wallahil! Asiya a zahiri dai ban taba ganin saurayi da budurwa ba wadanda suka dace da juna kamar ke da Yaya Aminu ba, ki ture ta wai kalar fatar jikinku, a’a, ki tsaya daf da shi sai in ga kamar irin greetin card din nan da Turawa ke yi, amma ba ina gaya miki wannan maganar ba ne don wani abu, ni kin san halina bana iya boye abin da ke zuciyata.
Sai.ki; yi hakuri, ki fahimci
maganganuna, kuma Allah ya sa mu dace, amin”.
Muka kwanta shiru yayin da na rika jin numfashin Zahra’ u na sauka a hankali, don ta sami bacci, ni kuwa ina kwance na zuba ma silin ido, abubuwan da suka faru tun dawowar Yaya Aminu suka rika dawo mani baya, ina Kokarin na gano abin da Aliyu da Zahra ‘u suka gani
Yadda Yaya Aminu ya rika mani magana a daren da ya dawo wato game da yarinyarsa, da irin kallon da ya’ rika mani lalle ne wannan kallo bai kunshi komi ba in ban da kallo na so da sha’awa.
Haka kuma lokacin da muke zuwa Zariya a bisa hanya irin tambayoyin’ da yake mani game da Aliyu, har yana fadin menene dalilin da ya hana ai mana baiko kamar yadda a kai ma su Miadiza?Na yi shiru sai ya kira sunana cikin wata irin murya wadda a yanzu na tuno akwai dalili mai karfi, ya ce, “Ki cira ido ki dubeni sai na sami kaina ban sami san amsar ba.
Sai ya ja dogon numfashi ya ‘ci gaba da dubansa yana Kara shigar da idanuwa, sai yayi mani wata magana a hankali wadda ban ji abin da ya fadi ba.
Ina kokarin tambayarsa sai naji ya ja birki da karfi Kuhhh! Na firgita na- kidime don rudewar naga”mutuwa kusa ban san lokacin da na bar mazaunina* ba na koma bisa kan cinyar Yaya Aminu na makaleshi sosai, shi kuma ya yi mani kyakkyawar runguma, mun dade a haka dömin ni a lokacin yadda nake jina na kubuta daga duk wata halaka, ko mene ne ya kubutar dani?
Hmmm