ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 32 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Dda karfe sha biyu daidai direban hmed yazo daükar Zahra°u, ni kuma sai da Aliyu ya sauko masallacin Jumma’a sannan yazo muka mika Malumfashi.

Mun isa Funtuwa mun dauke hanyar

Malumfashi, sai Aliyu yace, «Asiya bani aron hankalinki nan”A’a, ka fi karfin aro sai dai in mallaka maka shi duka” Ya dube ni ya yi dariya ya ce, “Allah?” Na ce, “Babu shakka” Sai ya ce, “To na gode”

Ya ci gaba da cewa, “Abin da nake so da ke, don Allah ki yi mani arziki daya, abin kuwa ba wani ba ne, so nake don Allah za mu je wajen Yayata Hajiya Rabi wadda na sha gaya miki a gidan masaukin bakin mijinta nake sauka. Ina son za ku shawarta wasu abubuwa ne dake don za ki fi fahimta tunda dai mace ce kamar ki”?.

Na cira kai na dube shi na ce, “Aliyu ba wai bana son zuwa wajen “yan ‘uwanka bane, a’a, sai dai duk tsawon lokacin nan da kake nema na babu wata

yar’uwarka mace da ta taba zuwa inda nake, ko sau

daya. To ka ga idan na cika shige masu sai a dauka

na cika zakewa” Ya sa hannu ya dakatar dani daga magana, ya shiga kawo mani misalai iri-iri har sai da na amince masa, amma na tabbatar masa ba zai sake matsa mani zuwa wani gida ba daga gidanta. Ya yi mani godiya mai tarin yawa, sannan ya dire ni kofar, gida ya ce, “Zan z0 bayan la asar mu je, wato misalin

biyar da rabi”. Na sami Inna ta yi wanka tare da kwalliyar Juma’a kamar yadda ta saba, ta zauna a tsakar gida tana murza taliya, na zauna muka gaisa irin ta da da mahai finsa, na je na sha ruwa.

Ta ce, “Akwai abinci a kicin idan za ki ci”

Na ce, “Cikina a cike yake

Sai na hango mangwaro cikin Kwarya na debo na wanke na zauna na sha kusa da Innata, ta

rika bani labarin cewa Yaya Abubakar wannan satin

Zai tafi Kano wajen kwas na wata uku.

Na yi murna da jin haka, na ce, “Shi Yusuf

Inna kun sanya masa ido ya Ki ci gaba da karo ilimi har sai Zainab ta zo ta same shi ko?”

Ta ce, “Don me za a matsa masa, ina laifin

aikin da yake yi, wata ran ba sai ki ga ya ta fi karo karatun ba, mene ne na sauri?” Muka barta a haka. Sai ta ce, “Shima Aminu ya sami aiki a Legos da kuma Katsina inda mijin Hadiza ke aiki’

Na ce, “Stcci Rolling” Ta ce, “Nan fa”

Na ce, “To yanzu wanne za shike nan?”

Inna ta ce, “Ya fi son zuwa Katsina Na ce, “Allah shi taimaka” Ta ce, “Amin

Na tashi na wanke hannuna, na ce, “Inna zan shiga nan wajen Inna Hafsatu” Ta ce, “To, idan zaki dawo ki amso mani yajin da muka samo a wajen barka jiya”

Na sami Inna hafsatu na alwala, nima na nemi buta na yi, sai da muka idar da sallar la’asar sannan muka fara hira. Bayan na yi mata murnar samun aikin Yaya

Aminu, sai na fara tambayar Shin Inna Yaya

Aminu ko ya fara maganar aure?”

Ta ce, “Uhm! Uwani kin dai san halinsa na miskilanci, har yanzu bai yi maganar ba, gara ma

‘yan’ uwansu na Danja da sukazo godiya a kan tsarabar da ya kai musu, to na ji sun fara masa maganar, ya ce su dan dakace shi yana da niyya, kwanan nan zai je ya same su a bisa maganar idan ya kammala harkokin gabansa” Na ce, “Wadanne irin harkoki ne?” Ta ce, “Na farko a kan maganar aikinsa, na biyu wai sun hada gwiwa da abokinsa El-Bashir zasu rika shigo da magani a nan Kasar’

Na ce, “To ni Inna ga wani hanzari ba gudu

ba Ta ce, “Kamar ya ya fa?”

Na kwashe yadda muka yi da Lauratu na gaya mata, ta ce, “To zan shawarce shi, idan ya amince ai kin ga faduwa tazo daidai da zama”

Daga nan ta kwada mana zogale muna ci tare da ita cikin akushi daya, muna kuma hirar bikin Hadiza.

Ta ce, “Yaya Aminu ya ce, ya dauke masu komi, abin da yake so ma sai ya gama gyaran wannan gidan, saboda ya ce zai canza fasalinsa” Na ce, “Kamar ya ya Inna”

Ta ce, “Zai gyara mini wanna dakin yadda rai zama ciki da falo, sai baranda da bandaki da kicin, sai daki daya a isakar gida saboda zaman baki, sauran tsakar gidan da sashen Babansu na aure da dakin zaure duk zai rushe su ya ja doguwar katanga tsakaninmu, ya zuba gini na zamani don amfanin shi, to kin ga tunda ya fara wannan shawarar da alamu aure yazo Sai muka ji sallama, na yi sauri na duba

Agogo ina zato ko Aliyu ne, to ashe Yaya Aminu ne. irin kallon da ya yi mini ganin muna cin zogale da Innarsa a akushi daya ya birge shi, na yi masa sannu da zuwa, sannan ya tambayi Inna ko akwai abinci?’ Ta ce, “A ‘a, sai dai akwai miya ana iya dora maka doya ko shinkafa” Ya ce, “Kai a barshi sauri nake yi, Kano za ni in hau jirgi zuwa Legos, saboda kadan daga. cikin magungunanmu sun iso” Ta ce, “To ya ya zai tafi da yunwa?” Na ce,Bari in je gida akwai abinci in kawo

masa”Ya dube ni ya ce, “Ke dai Asiya ba kya son daura dankwali me yasa?”

Sai Inna ta ce, “Kai dai da fitina kake, kullum sai ka sami abin da za kai masu korafi”

Na daura dankwali na fice. Na kawo masa abinci na aje masa a gabansa, sai da ya gama ci ya jawo wata jaka katuwa yana fiddo takardu masu ruwan Kwai da masu ruwan kore.

A nan ne ya kyalkyale da dariya, ya ce, “Ku ce ta yi hakuri ni na sami mata”

Na ce, “Yaya Aminu ai ta ce ita a shirye take ta zauna da kishiya