To kai ka kafe shima ya kafe, mu mene ne namu. Sanin kanka ne yadda ‘yan uwanka suka auri wadanda Baba ke so, kai ma dole ka bi hanya, kuma ya sha gaya maka ba zai taba yarda ka auro masa
‘yar masinja a cikin zuriyarsa ba, ka dai san halin ra’ayin Baba, ba daya ba ne da namu”
Da dai na ji maganganun sun yi yawa sai na tashi da sauri na fice abina. Duk da nisan da ke tsakani, amma wannan bai sa na damu ha, ban yi tafiyar minti uku ba sai ruwa ya goce, sai tsawa da walkiya. Ni dai tafiya kawai nake yi ba ni ko ganin hanyar da nake bi, idan na ga motar Aliyu sai in rabe wata hanyar, ruwa ya yi mani duka na tsawon minti arba’ in da biyar amma ban kula ba.
Da na isa unguwarmu na hango motar Aliyu tsaye a kofar gidanmu, sai na shiga zauren su Larai
•na labe, na tsuguna ina ta hadiyar zuciya, har ya gaji da jiran ya tafi. Sannan na shige gida, na wuce mahaifiyata a kicin.
Ta dube ni a dakile ta kawar da kanta, na shige dakina na tube kayana. Da kyar na yi sallolina, daga nan kuma sai zazzadi ya lullude ni, na leka na kwalla ma Larai kira ta amso mani rob da panadol a wajen Innata.
Idan, har ance yi bacci an san karya nakeyi ga zazzabi, ciwon kai da ciwon ido, ga kuma zafin zuciya, yadda na ga rana haka naga Dare
ruwan sama kuwa bai dauke ba sai misalin
Karfe biyar na asuba Da misalin Karfe shida na safe ina tashar Malumfashi ba tare da na sanar da mahaifina abin da ya faru ba na koma makaranta. Na shiga daki na Kulle na yi kuka kamar raina zai fita, ga ciwo ya dame ni, ga uwa uba bacin zuciya.
Da la’asar na daure na fita zuwa asibitin
makarantar har na hadu da wata yarinya, ta ce,
“Yanzu Aliyu ya tafi, ina na shiga?” Na yi mata
Karya na ce, “Dawowa ta ke nan
Na sha maganin da aka bani amma sai na
dinga amai, wanda ban yi mamaki ba, saboda ba ta
yiwuwa a sha magani babu abinci a cikin mutum.
Sai na daure na sha shayi, bayan minti biyar na kara shan maganin, na yi sa’a an hada mani da maganin mura, nan da nan bacci ya dauke ni.
Ban farka ba sai asubar fari, na rama sallolina na sha shayi tare da magani, maimakon in ji sauki sai ma jikin ya kara rude mani, da na sami bacci ban
farka ba sai misalin karfe daya na rana shima a
dalilin Zahra’u da ta dawo.
Yadda Zahra’u ta dube ni ta ga na canza mata
sai jikinta ya dau rawa, ta tabbatar babu lafiya. Na fashe da kuka ina fadin “Zahra’u na shiga uku na lalace, na rasa Aliyu har abadan-abada”
Zahra’u ta rike ni a rude tana bani magana, don in gaya mata abin da ake ciki, a cikin rawar murya na zayyana mata komi tun bayan rabuwarmu, ita ma ta barke da kaka. Na ce, “Haba Zahra’u wai ba a so na domin ubana na talaka ne, talakan ma masinja akwai bakin ciki da ya fi wannan?”
Ta fashe da kuka, sannan ta ji jikina ya Kara rudewa, sai ta fara bani magana, ta bude kayan da ta zo dasu ta bani fura na sha, sannan na Kara shan magani.
A bisa dole Zahra°u ta matsa mani sai da na ci abinci, sannan ta rika Kokarin kare Aliyu wai ba shi da laifi in daina zarginsa, kuma shima abin da za a tausaya masa ne, domin ya fi kallafa rai a kaina fiye da ita.
Na ce, “haba Zahra’u laifin Aliyu ya fi na kowa yawa, me zai hana tun farko ya sanar dani, sai ya barni ina ja ma mutane rai”
Haka muka samu kanmu a kullum muna tattauna wannan maganar, sai dai kuma na samu na warke zazzabin da ruwan sama ya saukar mani.
Wata rana mun bi Anti Wasila cikin gari a gidanta na Kuyambana, ita dai Anti Wasila wata babbar aminiyarmu ce tazo jami’a ne don neman digirinta na biyu, tana da miji da ‘ya’ ya shida.
wanna rañar laraba da muka bi ta gida, bayan mun tashi aji muna kwance a dakinta ta rika matsa mani’ a kan tana son sanin ainahin abin da ke sanya ni rama, muka yi shiru daga ni har Zahra’u muna tunanin ta inda za mu bullo mata,, domin abin yana da nauyin fadi. Da ta matsa mana sai na daure na gaya mata tun farkon haduwarmu da Aliyu zuwa halin da muke ciki a yanzu. Ta yi shiru can sai ta ce, “Asiya kada ki kara damun kanki a bisa wanna lamari, ai sara da. sassaka ba ya hana gini tofo, ba a san irin daukakar da Allah zai yi miki ba a nan gaba. Idan kuma Aliyu shi ne mijinki, to wallahi ko ana ruwa da iska sai kin aure shi, ki kwantar da hankalinki kada ma ki bari iyayenki su ji wannan magana tunda dai ba da uban
Aliyu za ki zauna ba da Aliyu za ki zauna.
.. Ni shawarar da zan baki a nan kada ki Kara zafafa ma kanki a bisa harkar aure, babu mahalukin da ya isa ya yi jayayya da yin Allah. Kuma ke ma Asiya kina da laifi, yanzu duniya ai ba a zama haka, me ya sa tuntuni ba ayi maki istahara ba? Kuma ya dace ki sa ana maki addu’a, yanzu ku tashi muje
Kusfa gidan kawuna Na ji dadin hakan, amma da muka je gidan
Malam din sai aka ce ya je Kano, sai in ya dawo an aiko ma Anti Wasila.
Muna isowa gidan su Anti Wasila ta kashe motarta ke nan za mu fito sai ga motar Aliyu ya tsaya.
Na ce, “Ni kam zan tafi makaranta bana son ganinsa”. Su Anti suka tasa mani da fada, a kan har shekara nawa zan rika gudunsa?
Muna cikin dakin Anti, mijinta Baban su
Bashir ya zo yana lallashina in yi hakuri in saurari Aliyu. Da kyar suka shawo kaina muka je falon gaba daya mu dasu, na zauna na hade kai da gwiwa duk surutun da akeyi ban tanka ba.
Baban Bashir ya ce, “Asiya saurin fushi ba naki bane, idan iyayenki ne suka ki yadda da Aliyu ya aure ki shi ne mai ciwo, ki sani ko ni nan kaina ina iya wakiltar Aliyu ya aure ki”.
To a wannan lokaci ne na fara magana. Na cira kai na dube su na ce,
. “Wallahi ba zan kai kaina inda za a wulakanta mani iyaye ba, na san mahaifin su Aliyu ya nuna masu gatanci kudi ne, to ni nawa iyayen basu da kudi da za su nuna mana, amma sun nuna mana so da kauna wanda na san su Aliyu basu sami wannan gatanci ba”.
Hmmm