ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 36 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

wanda za ki aura Allah kadai ya sani sai dai a bar mu da luguden labba mu ‘yan adam.

Yanzu ni kam’ abin da zan taimaka miki da shi addu’a, ke ma zan baki wasu ki je ki rika yi, mu ga abin da Allah zaiyi kafin ku dawo hutu”

A cikin kuka na ce, “Ni dai Malam wallahi wannan Aminu shine bana so”

Shi kuwa ya ce, “To idan mijinki ne Asiya ya ya za mu yi, ai mu bamu da abin yi sai wanda Allah ya ya yi”

Ita kuma Zahra°u don iskanci sai cewa ta yi,

“Amma Asiya a da cewa ki kai za ki sa a roka miki

Allah ya fidda Aliyu a rank?

Na harare ta cikin kuka na ce, “Ai na fasa” Sai Malam ya fashe da dariya, gaba daya da su Anti Wasila. Malam ya ce, “Ina zanyi haka Asiya, idan ya zama mijin kuma fa? Ku z0 ku yi zama baran-baran”

Ya sanya Anti Wasila ta rubuta mani

addu’o’i, sannan ya yi mani nasiha hade da wa’azi har naji zucivata ta saki ta kuma karkata a bisa abin da ya gaya mani. Na hakura na sa ma zuciyata dangana, na bar ma Allah ikonsa. A ranar hutu mun rabu da Zahra’u a kan kwana biyu zanyi in taho Kaduna, saboda haka idan ta isa sai tayi Kokarin sanar da Mama Inki don ta aiko direbansu ya dauke Na isa gida da azuhur, na sami Inna tana alwala, irin kallon da ta yi mani na san akwai magana. Shima mahaifina haka abin yake, saboda haka ina kwance a daki ina tunanin mene ne na yi ma wadannan bayin Allah haka mai zafi har suka fita harkata? Ban san dalili ba, sai da na kwana biyu direban su Mama Inki yazo dauka ta, ina shaida ma Inna zan tafi Kaduna, ai kamar za ta nemi wuta ta jefani. Na koma daki ina sauraron shigowar Babana in tambaya idan ya barni in tafi.

Amma me zai faru? Yusuf kanina shi ne ya shigo dakina ya ce, “Wai ke Yaya Asia baki san abin da ke faruwa da ke bane?”

Na dube shi na ce, “Kamar me fa?”

Ya ce, “Na ji Baba ya sallami direban su

Mama Inki har ya tafi, yace ya shaida masu ana shirin daura miki aure ne” Nan da nan na dafe kirji na ce, “Yusuf da wa kaji ana shirin daura mini auren?”

Ban sani ba Ya ce, “Kina nufin duk rigimar da ake ba ki jiba Jikina ya dau kyarma, cikin murya mai rikitarwa na ce masa, “Don Allah ka gaya mini abin da ka sani”.

Ya gyara zama ya fara kamar haka.

A wata Juma°a da ta shige Yaya Aminu ya zo misalin tara na safe, a ranar ban tafi aiki ba, saboda

•. na tashi da bacin ciki. Bayan sun gama gaisawa sun yi hira bisa auren Hadiza, da kuma kan maganar kayan gininsa da zai fara, sai na ji shi Yaya Aminu ya ce, “Baba ni fa ban gane ba, ya ya ina ganin mutane na zuwa wajen Asiya amma har yanzu babu wata maganar kamawa? Ina ganin ya dace wannan biki na Hadiza a ce tare da Asiya za a hada, yadda ku iyayenmu kanku yake hade, to komi gara ya tafi baki daya”.Wannan yasa Baba ya tashi zaune domin da yana kishingide ne. ya ce, “A gaisheka dan albarka, tuni daman nima abin na yi mini kuna a zuciya, amma na rasa ta inda zan bullo ma al’amarin, ka riga ka sani na shaida maka masu sonta, to sai ta nuna ta amince da wannan yaro Aliyu, kuma ka san ni mutum ne wanda bai son wulakanci a rayuwata. To sai na lura Aliyu ya dauki son duniya ya dora a kan Uwani, ni kuma a nawa tunanin sai na ga kamar bai dace ba, ace daga wajenmu za a fara aika musu tunda a bisa al’ adarmu daga gidan maza ake zuwa neman aure, ba domin zamani da ke canzawa ba.

To ita ma Uwanin kusan in ce halinmu daya da ita, saboda duk son da take wa Aliyu ba ta taba buda baki ta ce ya aiko gidansu ba. Kuma ni ina gudun abu daya, sanin kanka ne wanna mahaifi na Aliyu mutum ne mai arziki kuma ya rike mukaman azo a gani a wannan Kasa tamu.

Yanzu yana kuma daga cikin masu fada a ji a kasar nan baki daya, har yanzu ba su ce komi ba to kai ka ga ya dace kamar ni in tunkare su a kan maganar auren “yata?” Akayi shiru a cikin zauren, yayin da shi Yaya Aminu ya sunkuyar da kai kasa, zuwa can ya dago ya dubi Baba ya ce, “Baba ita gaskiya guda daya ce har abada, saboda haka ayi shiru ba daidai ba ne, domin karatun ita Asiya ya zo Karshe gara a basu hakkinsu a aika musu, idan har suna so to, idan kuma basu so wannan ya rage ma dansu, ga shi kuma Asiya tana da masu jiranta”

Sai Baba ya ce, “To yanzu kai ne za ka ko?”

Yaya Aminu ya ce,A’a, Baba wannan

maganar ta manya ce, Malam Bawa ya dace ya je a matsayinsa na kakan yarinya. Kuma Baba kada ka damu a kan mutane su dinga surutai marasa dalili a ce an sai da ma Asiya mutunci, babu komi durkusawa wada ba gajiyawa ba ne, sai ka tashi da tsawonka”

A nan take dai ni da Baba da shi Yaya Aminu muka fada mota sai gidan Malam Bawa. Muka same shi tare da wannan aminin nasa wato Liman, suna zaune a zaure. Bayan an gama gaisawa sai Liman ya shuri takalmi zai tafi Baba ya dakatar da shi, ya ce, “Gara ka tsaya domin ko ka tafi za a sake nemo ka, tunda abin da ya kawo mu ya shafe ka”.

Liman ya koma ya zauna. Sai Baba ya gaya masu abin da ake ciki. Liman ya yabawa Yaya Aminu a bisa wannan shawara da ya ba da, shima

Malam Bawa ya ce,

“Gaskiya wannan yaro ka kyauta”

A nan dai aka shirya idan an sauko daga

masallacin Juma’a Yaya Aminu zai turo direba ya kai su. Da la’asar sakaliya na yi ma Baba shimfida

•bisa baranda, na koma dakina na zaure ina gyaran wani kaset nawa na rikoda, sai na ji su Malam Bawa sun iso, na fito da sauri-sauri don in ji wace amsa suka zo da ita.

Hmmmm