ALLURA CIKIN RUWA BOOK1 CHAPTER 1 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Ni asiya yusuf mutumiyar malunfashi ce a
unguwar Kofar Fada. Malam Yusuf mahaifina
mutumin Katsina ne, haifaffen wata unguwa
wai ita Galadanci. Ya dawo Malumfashi ne da zama a
wurin Malam Bawa Kanin tsohonsa,
wanda a.
lokacin yana da shekara ashirin da daya a duniya. Mahaifina mahaddacin Alkur’ani ne, amma ba shida ilimin zamani.
Yana nan zaune a Malumfashi
rannan kwasam sai aka bude makarantar yaki da jahilci,
nan take sai mahaifina ya shiga. Da ya sami kimanin
shekara daya da rabi, lokacin ya iya karatu da rubutu da lissafi. Sai Kanin tsohonsa ya nemar masa aiki a Majalisar Yanki ta nan cikin Malumfashi a matsajin
Masinja. Kwanci tashi har Allah ya hada
shi da abokiyar rayuwa wato mahaifiyata
mai suna Aishatu, mutuniyar wani kauyen Kuka Sheka. Wata rana ta zo cin kasuwa ita da kawayenta, a daidai
lokacin mahaifina ya taso daga aiki yana bisa
kekensa, sai ya ci karo da ita, a nan take ya rinka binsu har Allah ya ba shi sa’a ya sami magana da ita. Ta shaida masa kauyensu, ta kuma gaya masa iyayenta
-fulani ne amma zaunannu.
Nan dai ta yi masa bayanin yadda in ya je za
su sadu ba tare da ya sha wahala ba, ya kawo sule biyar ya ba ta. Ta ce, a’a ya barsu. Ya dai nuna mata yar damuwarsa saboda ta ki karba, har ya kara dacewa,
“Kin ji Hausawa sun ce Sadakin soyayya kyauta Ta yi murmushi ta durkusa ta sa hannu biyu ta kara tare da godiya.
Bayan kwana uku da haduwarsu, mahaifina
ya ga ya dace ya kai mata ziyara ta tabhatar wa kansa yadda Aisha ta dauke shi a zuciyarta, ya yi kuwa sa’a Aisha ta amshe shi da kyau da kyau. Sai da ya yi kamar zuwa uku wajen ta, sai aka
neme shi da ya turo manya, saboda an ga mutane sun fara kawo hari a kanta, a nan mahaifina ya shaida
mata zai yi hanzarin yin hakan, domin kanin
tsohonsa ya fara tuntubarsa a kan maganar aurensa.Mahaifina ya sami Kanin tsohonsa Malam Bawa, ya shaida masa komai da komai tun farkon haduwarsa da Aisha har zuwa inda aka nemi ya kawo magabatansa.
A nan Malam Bawa ya shirya da kansa tare
da wasu mutane har zuwa kauyen Kuka Sheka. Sun fara isa wajen hakimin kauyen da yake amini ne ga Malam Bawa, ya shaida masa dalilin zuwan su da
bukatarsu.
Hakimi ya ce,
“Kun yi dace da samun gidan
mutunci, saboda ubanta dattijo ne ainun, kuma ga su
irin kyawu. Fulani ne amman zaunannu”
Daga nan suka isa gidan yayan mahaifinta,
bayan an gama gaisawa irin ta neman iri, ya ce masu babu komai idan an bincika an ji daga bakin Aisha ta
amincé da Yusuf, to za su ji aike daga Hakimi.
Suka yi sallama, suka kawo kudin neman
aure suka bayar. Bayan kamar sati biyu da zuwa su,Hakimi ya ba da kyakkyawar shaida a kan irin su Malam Bawa, aka aiko
an ba mahaifina auren
mahaifiyata. Aka yi biki dan lokaci kadan, Malam Bawa ya gyara musu wani sashe a cikin gidansa, suka yi zamansu tare da iyalansa.A wannan
lokaci ne na zaman amarci
mahaifina ya rinka nuna ma mahaifiyata karatun Mahammadiyya da na boko, inda har ta iya rubuta wasika ta kuma karanta da ajami da kuma boko.
Kwanci tashi da ta sami shekara biyu sai ciki
ya rinka bayyana a jikinta, wata rana ana hira
tsakanin mahaifina da mahaifiyata, sai gardama ta turnuke tsakanin wadannan
bayin Allah, inda mahaifina ya ce,
“Aisha Allah ya ba ki ‘ya mace mai
kyau kamar ki in sanya ta a makarantar Islamiyya,
sannan in sanya ta makarantar boko ta yi ilimi har sai ta ce ta gaji. Kin san wanna zamanin babu wani abu da za ka yiwa danka sai dai ka ba shi ilimin
neman lahira, daman abin da Allah ya ce kenan. Ko kuwa ya ya kika gani?”
-Ta dube shi tare da murmushi, sannan ta
sunkuyar da kai, ta ce,
“‘Ka ji wani irin zance wajen
Malam, abin da duk kake so da
ya?yanka wallahi
shi nake so. Ku maza ai kun fi mu kaifin hankali, har
abada iyaye abin da zai zama alheri ga ‘ya’yanmu shi suke nema musu Ta kara sunkuyar da kai ta sa yatsanta cikin
baki, ta-ci gaba da cewa cikin jin kuna, “Ni kuwa a nawa ra’ayin na fi son da namiji wanda zai rinka
taya ka aikin gona nan gaba, kuma kullum rokona Allah ya bani mai kama
da kai in sami da
kyakkyawa kamar ka, na sami fuska irin taka da hanci dan siriri har baka, ga manyan idanuwa farare, bakinsa dan karami mai dan fadi, labha sirara,
dogon mutum mai dan kauri kadan, ga shi mai yauki a bisa kumatunsa na hagu, a nan za a tsara masa fasali wanda zai yi masa kyau kwarai ainun”Ta ci gaba da cewa,
“Tun farkon gamuwa ta
da kai bahu abin da nake rokon Allah irin Allah yasa
kai ne mijina, in haifa maka ya’ya masu kama da kai, sannan in roke ka ayi masu dan fasali irin naka.
Haba! Ai kullum ba zan gaji da gyara musu ba, ina mai kallon su ina jin dadì tare da masoyanmu Sai Babana ya yi dariya ya ce,
“Aisha ai kin
fini kyau, ke mai jar fata kamar tsada, ga kyan fuska,ga gashi har gadon baya, ga ki girkakka abin so ga duk wani da namiji.murmushi na ga’
Aisha idan kinayi yar siririyar wushiryarki har bana kaunar in fita in barki don sha’awa.
Amma babu komai, Allah ya bamu
“ya yan da yawa suma su biyo ki, wasu kuma su biyo ni, zanji abin da mutane za su rinka fad, Allah Ubangiji yabamu masu albarka,
ya kuma bamu masu jin maganar iyayensu”
Mahaifiyata ta ce,Amin”
Rannan ciki ya bunkasa kwanakinsa sun cika,
ya kuma nuna alamar zai fito kowa ya ganshi, da misalin karfe tara na safe bayan mahaifina ya fita zuwa wajen aikinsa, sai ciwon nakuda ya turnike mahaifiyata.
Daga nan matar Malam Bawa ta shaida wa
Malam Bawa,a ka samo mata rubutu ta sha, aka shiga jira, aka shirya taren bako.
Can misalin karfe daya da rabi na azahar, sai
haihuwa ta kunno kai, kafin karfe uku an gama komai anguwarzoma ta wanke
da, ‘ta wanke wa mahaifiyata dakinta ta kunna mata turaren wuta.
Ita kuwa mai haihuwa aka yi mata wankan
jego kamar yadda ake yi a al’adar Hausawa. Wannan rana kuwa Laraba ce, kai da ganin wannan yaro kasan ya ci sunansa Balarabe ba ma sunan rana kadai ya ci ba.
Mahaifina yana isowa gida yana gunguro dan
kekensa, ba tare da ya san abin da ke nan ba. Sai Malam Bawa ya tare shi da yi masa barka mai dakinsa ta haihu, da namiji na nan kwance. Nan da nan ya kafe kekensa ya shiga cikin dakinsa, tsofaffin da ke dakin suna gasa wa jariri cibi, suka yi masa barka, sannan suka mika masa sabon zuwa.
Ya yiwa mahaifiyarmu sannu, sannan ya
amshi jariri ya dube shi da kyau, ya yi masa kiran sallah ya tofa masa a kunnensa na dama, sannan yayi ikama ya tofa masa a kunnensa na hagu tare da
addu’o°’in shiriya, ya bi duk jikinsa ya tattofa masa. À daidai wanna lokacì ya dubi mahaifiyata
fuskarta cike da fara’a, ya ce,
“Allah ya amshi
addu’ arki ya bamu da namiji, ni kuma ya amshi tawa ya bamu mai kama da ke”
Ta yi murmushi ta ce,
“Kai dai Malam baka
gajiya da tsokana Haka
dai aka yi ta hidimar haihuwa.
‘Yan’uwan Baba suka z0 daga Katsina, ita ma nata
‘yan’uwan suka z0 daga Kuka Sheka, aka yi suna bisa gwargwadón abin da Allah ya hore musu, aka
radawa jariri sunan Malam Bawa, wato Abubakar. Washe gari iyayen mahaifiyata suka nemi tafiya da
ita wankan bangwali a bisa al’adar
mutanenmu, aka amince masu. Bayan ta yada
wanka da wata hudu aka shiryo ta komo dakinta.
Haka rayuwa ta kasance tsakanin Inna da Baba.Mahaifina mutum ne mai kamun kai ba shi da wasa ko kadan, duk mutanen unguwarsu sun san shi
a kan irin wadannan halaye nasa, haka wajen aikinsa
duk da an san masinja ne karamin ma’aikaci, amma
ana mutunta shi saboda ya kama kansa kwarai da
gaske.
Bayan shekaru biyu da haihuwar Abubakar
suka dauke shi daga bakin shan nono, yana da shekaru uku cif ni kuma na bullo kai, kamar mu guda da mahaifina kamar ya yi kaki, na dauko kalar jikinsa wankan tarwada.
Ranar suna aka rada mini suna Asiya, wato
sunan mahaifiyarsa don tunawa da ita. Aka yi mini
dan fatali mai kyau daf da hancina. Nan ne ma
dangin mahaifina da suka fito daga Katsina suka ce
sai an sake wa Abuhakar nasa don bai fito sosai ba. Haka haihuwa ta bude musu, ina da shekara
uku aka haifi kanina aka sanya masa suna Yusuf
wato sunan mahaifinmu, Innarmu ce ta zaba. Shima
ya shekara uku sannan aka haifi Zainab, wato mu
hudu kenan, mata biyu maza biyu.
-Ni da Zainab kamar an tsaga kara, Yusuf da
Abubakar su ma kamar su daya. Ina da shekara
takwas na yi nisa kwarai wajen karatun Islamiyya, a
wannan lokaci har na shiga aji uku a firamare,
saboda na yi ido wajen karatun Islamiyya ban sami wata matsala ba a wajen na boko.
Abubakar shi kuma lokacin yana da shekara
sha daya, har ya dauki jarabawar makarantar shiga
sakandire. Shi kuma Yusuf ya shiga bana.
A wannan lokaci ne mahaifiyata ta yi Barin
ciki wata hudu, wanda ta sha wuya ainun. A wata rana na dawo daga makaranta, na gaji da yake
tsakaninmu da makarantar akwai ‘yar tazara, na kwanta bisa katifa a dakin mahaifiyata.
Zuwa can mahaifina ya dawo daga wajen
aiki, Abubakar ya gunguro masa kekensa, nace,Baba sannu da zuwa Ya ce,
“Yauwa Ummi, lafiya aka kwanta? Ko
da yake yau alhamis babu Islamiyya
Hmmm mu tara