ALMAJIRI KO ATTAJIRI COMPLETE

 ALMAJIRI KO ATTAJIRI COMPLETE

Wata doguwar motace mai k'irar hiace dake daukan passengers 14, an  rubuta kano line ajikinta tad'an ji jiki halamun ta jima akan hanya  misalin k'arfe 4:30 daidai suka shigo garin jos gari mai albarka mai dadin weather,a tashan da'ake kira bauchi pack suka dosa kai tsaye....

Suna shiga tunkafin ayi parking matasa kebin motar da masu wheelbarrow suna fadin hajiya za'a fitar miki dakayanne?


Motar natsayuwa matafiyannan suka soma sakkowa wanne  na hamdala ga Allah dayasa suka iso lfy da mulaman har cristoci dasuke ciki.....


Driver ne ya sakko yabud'e boot yafara sauke kaya nan yaran suka fara rububi wata yar matashiyace da bazata wuce shekara 27 ke tsaye dan duk wand yatab'a kayanta masifa take masa hkan yasa duk suka mayarda hankalinsu kan suran passengers din......

Ahka kowa yabarta tsaye tana faman latsa waya tana yamutsa fuska kaman zatayi kuka  ganin wayan bazata shigabane yasa tafara k'okarin jan akwatinta da wasu ledoji zata fita da gudu yazo yasa hannu zai karba ledan dake k'okarin zubewa a hannunta aiko bata ankaraba taji anajan ledan hannunta juyowan da tayi ko ta dauke shi damarin dayayi sanadiyar fad'uwan sa k'asa abinda yajawo hankalin wayanda ke gurun sukayo kansu knan.....

Shi aka fara d'agawa ko kukanma yakasa halamun tsabar yunwa ko mgna bayayi sai hawaye kawai dakebin idonsa baiwar Allah lfy meya miki zaki masa irin wannan marin hka cewar wani daga cikin matasan dake kansa......

Lafiyar kenan sata zaimun kayana nak'okarin zubewa yazo zai fusga ya gudu cikin hawaye yace naga zai zubene nayi k'okarin tayata shine tamareni kafin tayi mgna wata dattijuwa dake gurun takarba carab amma keko bakida imani meye abun duka ajikin wannan yaro kina ganin alamansa kaman wanda ko karin kumallo baiyi ba saboda rashin imani harzaki iya sa hannu kimare shi aiko kaman ana jira nankowa yatofa albarkacin bakinsa itakam har zuciyanta bai dameta ba dan ta tsani almajirai ko ganinsu ma batasonyi bare yakai da sutb'ata....

Tanajin kowa yagama fadin albarkacin bakinsa ko agyalenta saima k'okarin jan akwatinta da tayi tayi gaba nankowa yabita nasa bakin shikam dattijuwanan ce ta cire naira dari tabasa da murnnansa yakarb'a yana godiya baima sakebi takan mutanen dake gurunba yawuce ya gefensu yana murna yayi gun wata bayerabiya dakeda runfa agurun mazauniyar gunce anan take girki shekara da shekaru dan duk y'an tashan sunsanta da murnansa yamik'a mata naira d'arin ta karb'a da zuba masa abincin dayafi karfin kudinsa yakoma gefe yasamu wani dakali yazauna yafara ci kaman wani zai kwace dan sai lokacin yake tunawa rabonsa da abinci tin safe da daya taya wata mai koko wankin kofuna tabashi kunu kofi guda yasha........


Ma'araddeen knan kadan daga cikin sabon littafina knan.....
DOWNLOAD HERE👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *