AMANAR MU CHAPTER 10
An d’aura auran barrister da amaryar sa Ikram,aka kai amarya abj dan daga nan zasu wuce lagos inji barrister dan baiso kowa yasan da zaman sa a kaduna,dan muddin Zee ta d’ago da zaman sa anan kd d’in toh zata je ko wani level dan ta wargaza shirinsa,yin koman sa a sirrince ya fiye mai komai.Bayan biki da 3days ya tattara matarsa bayan nasihohi da momy da dady suka masu da fatan zaman lfy da zuria d’aya ba suka kama hany’a,ba inda suka dira sai kaduna garin gwamna!.Dama already Ikram ta san da zuwan su Kd dan ya mata bayanin cewa akwai abubuwan da zaiyi a kadunan suna kammalawa zasu wuce lagos.Ikram macece mai mugun sany’in hali shuru shuru ce bata fiye magana ba,gajeruwa ce sosai amman ba wada ba,fara ce tas mai many’an idanuwa,kekkyawa san kowa k’in wanda ya rasa.!+
After one week
Sosai barrister ya maida hankalinsa kachokam akan k’anwar sa da duk wani shirgi nata,barrister sam bai cika samun lokacin kansaba dan so yake yasan ta yadda za’ayi ya 6ulloma lamarin Humy dan kwata-kwata Humy bata hayyacinta bata san kanta ba bata san wacece ita ba !,kaman rak’umi da akala haka Zee ta maidata ,sai yanda akayi da ita kawai.Zaune yake akan sallayansa yana jan
tasbaha yana zikiri,Ikram kuma na kwance akan makeken gadon d’akinsu tayi lamo tana jiran mijin mata ya kammala sallan nafilan da yake yi,wanda ta lura kusan babu ranar da baiyin wannan nafilan kuma sai yabari tsakar dare tayi sannan yake mik’ewa yayi,sosai take ganin yake dad’ewa akan sallaya wani zubin harda shesheqan kukansa take ji alamun yana mai tsananta rok’on ubangijinsa.Ita dai kullum cikin mamakin abinda ke damunsa take amman inta tambayesa sai yace mata kawai cases dake gaban sane suke damunsa yake tunanin yanda zai 6ullo masu.Sosai barrister yayi adu’oi kama daga adu’an kariya,Sharrin mutum da aljan da kuma adu’oin samun nasara akan abinda kasa a gaba kake sonyi,sosai ya duk’ufa yana rok’on jalla jalalu akan ya d’orasa kan Malamin Zee ya basa ikon cin nasara,ya karesa daga dukkanin sharrukan boka da aljan,sosai barrister ya ruk’a zubda kwalla yana rok’on ubangijinsa ya amsa mai dan babu wani wanda zai iya taimakon sa a wannan ga6an har yacinma nasara ba face ubangijinsa shine kawai zai iya taimakonsa,kuma in Sha Allah ubangijinsa zai dubesa ya kuma taimakesa!.
Bayan ya kammala yama Humy adu’an samun waraka ita da mahaifinsa sannan ya Idasa shafa adu’an ya mik’e ya linka dadduman ya ajiye,sannan ya wuce ya kwanta a bayan Ikram yayi lamo yana mai tunanin zuwansa gun malamin Zee a gobe duk ya k’osa gari ya waye dan sai yake ganin kaman zuwa wajen malamin na cikin babban samun Tufken zaran sharrukan Zee.
“Hayaty “!
Yaji Ikram ta kira sunansa a hankali,d’an bud’e idanuwansa yayi dan duk zatonsa tajima da bacci,mirginowa yayi wajenta ya rungumeta sannan ya sunbaci goshinta yace:
“Zawjati bakiyi bacci ba ashe?”
Murmushi tayi sannan ta k’ara gyara kwanciyanta akan k’irjinsa sannan tace:
“How can I sleep when kai bakayi ba?”
Ta ida maganar tana mai kwantarda hannunsa akan sajen fuskansa,murmushi yayi sannan yace:
“Hakane so let sleep now “
“Aa sai ka gayamun dalilin da yasa kullum inzaka yi sallan nafila inkana Adu’a sai kata sheshshek’an kuka “
Murmushi yayi sannan yace :”rigimau kawai yanzun dan kawai kinji ina sheshshek’an kuka shine sai kinsan dalili sweeetheart?”
Ya ida maganar yana mai sakan mata lausassan murmushi tace :
“Ay dole Na tambaya “
“Aduaa kawai nake yi bansan da cewa ina sheshshek’an kuka ba babynah “
Yaci gaba da cewa:”shi bawa a kullum ana son duk lokacinda yake da wata damuwa ko buk’ata ya yawaita rok’on Allah bawai boka ko malam bane zai rok’a biyan buk’ata ba,da Allah bai basu sanin abinyi ba da babu uwar abinda zasu iya tsinana ma mutane bare ma har mutane su shagala akan su,MALAM da boka suta ciny’ema kud’ad’e wanda wlh da ka natsu kakai kukanka ga rabbil izzati babu ko kabon ka with patience dakai zai amsa adu’anka ya kuma biya maka buk’atun ka fin yanda boka da malam zai ma,amman wasunmu sun shagala a tunaninsu malami ko boka sha yanzun biya yanzun ,ubangiji kuma sai kata rok’on sa sannan (kaji mutane da alkaba’ir Allah sa mu dace Mufi k’arfin zuk’atan mu Ameen ) wlh wani sa’in jinkirin da Allah zaima wurin biyama buk’atunka da ka rok’esa baiwace,zai kyaleka ne yayi testing patience d’inka inkai wanda ya iya jurewa ne har sanda ya biyama buk’atun naka babu wanda zai kaika jin dad’in jinkirin dakai,in kuma kak’i ka kauce hany’a shikenan daga nan kuma Allah ya rigada ya 6idda kai hany’a kenan sai dai wani ikon Allah ne kawai zai dawo dakai hanya madaidaiciya.
STORY CONTINUES BELOW
Yake matata Uwar ‘ya’yana a duk lokacinda kika tsinci kanki cikin matsanacin buk’ata ko kuma damuwa kikai kukanki ga ubangijinki wlh shi mai share maki hawayen ki ne ya kuma biya maki buk’atunki ya yaye maki damuwar ki inhar kika fallalawa Allah lamuranki,kark’i zak’u akan biyan buk’ata da wuri da yawan mutane abinda yake kaisu ga halaka kenan,Allah kad’ai shine wanda zai iya biya maki buk’atun ki”
Murmushi sosai Ikram tayi tana mai k’ara gode ma Allah daya mallaka mata barrister Bàshir a matsayin mijin auranta kuma uban ‘ya’yanta nan gaba in Sha Allah ,soyayyarsa sai k’ara linkuwa take a dukkanin sassan jikinta.
***********¥¥**¥+¥¥****^^*****
Washegari
Bayan barrister ya kammala shirinsa yayi breakfast d’insa matar sa ta rakosa har wajen motar sa sannan ya mata sallama ita kuma tamai fatan samun nasara da adu’an cin galaba a dukkanin lamuransa,sannan ta wuce tana d’aga mai hannu shima hakan ya mata kafin yaja motar tasa ya bar haraban gidan.Jefa motar tasa yayi kan titi yana mai adu’an Allah ya tsaresa yakaisa suleja lfy!
*******************************
“Wai har yanzun Rabin rai wannan tsohon kilakin (dadyn humy take nufi)bai baka dukiyoyin naka bane?”
Tsaki Umar yaja sannan yace:
“Last zaman da mukai a kotun ma kuma d’aga sauraren k’arar akai,ni wlh na rasa wannan irin abun,mtseeww wlh dolen sa dai koman jaan lokacinda yake sai an raba dukiya an bani “
Murmushin tak’aici Zee tayi dan wlh ita abinnan ya fara isarta gashi sai kashe uban dukiyoyinta take wajen malam,amman kullum sai dai yace mata ta hak’ura zuwa wani lokaci kud’i zai dawo hannayenta,ita wlh duk ta k’osa su dawo hannunta wlh ta wulak’anta Umar kamar yadda tayi alk’awari adaaa dan bazata barsa haka ba abinda ya ruk’a mata tana yarinya bazai wuce a banza ba!mtsewww
“Tsakin mai kike maman abul?”
“Babu komai “
Daga haka ta mik’e rai 6ace zata bar falan,Umar ya bita da kallan mamaki,yana son yayi tunanin wani abun amman ya kasa sam-sam,bai san dalili na tun last week in dai ya zauna sai yaji yana son yin wani tunani amman sai ya kasa wani zubin ma har kansa ya fara ciwo amman bazai iya tuno komai ba,gashi dai a kwakwalwansa yana son tuno abu amman sai ya kasa,yarasa wannan dalili!
Abul ne ya danno kansa cikin falan a guje
hannunsa rik’e da kofi da aka cika mai juice aciki ,yanzun kam yaron ya girma yayi wayau abinsa 6ul6ul dan zai kai shekera d’aya da satattaki akai,gijib Zee taji ya bige kansa akan ciny’oyinta ruwan juice ya zube mata a zaninta,dama gashi haushin ubansa take ji gashi shi kuma yazo ya zubar mata da juice akan zani,ai bata san lokacinda zuciya ya d’ebeta ba ta d’auki yaron chak ta wurgaza akan center Capet tana haki tace “dan Uwarka ni tsarar wasar kace zaka zubar mun ruwan juice a jiki aiko yau sai naci uwar ka acikin gidan nan Sha-sha “
Cikeda mamakinta Umar ya mik’e zai tare ta dan waya ta d’auka ta shiga rafta ma Abul shiko sai tsala kukan wahala yake,Amman kallan hadarin kajin data masa yaji ya kasa koda motsi balle matsowa inda take,haka dai yana ji yana kallo Tama Abul lilis sannan ta juya ta bankamai harara (umar)sannan ta tsallaka Abul tayi shigewan ta kitchen dan sama zaninta ruwa!
Da hanzarinsa Umar ya k’araso wajen Abul dake ta sauke lumfashi da kyar ,rungumansa Umar yayi yana hura masa iskan bakinsa akan fuskan abul har yasamu lumfashin sa ya daidaita sannan ya d’auke sa ya kai d’aki ya masa wanka ya chanza mai kaya,kafun wasu dak’ik’u bacci ya saci yaron.
Shi kuma ya koma gefe yayi lamo yana mai tunanin lamarin Zee ,yanzun duk ta sauya bata son Abul-islam samsam daga harara sai hantara take nuna masa tamkar ba ita bace ta haifesa,yanzun kuma ta zagesa da Uwarka nan ma bata san kanta take zaga ba kenan?”
STORY CONTINUES BELOW
Yadai rasa samun amsoshin tambayoyin sa da haka ya mik’e ya shiga ban d’aki ya sakan maa kansa shower kozai ji dad’i
************************************
Mama zaune tana matsama Baba k’afafusa da sukai yami tsaban rashin taka wansu dabai yi,Shiikam fa babu mara bansa da gawa face lumfashin da yake yi,wayan mama ne ya shiga ringing d’agowa tayi ta kalla wayan dan ganin mai kiran nata gashin malam Abubakar ke kiranta yasata saurin d’aukan wayan had’ida mik’ewa ta gyarama baba zaman k’afafunsa sannan ta fito waje tana mai amsa kiran:
“Hello malam barka da rana “
“Yauwa hajia barkan mu,kinga nakiraki rana tsaka ko?dama zan gaya maki cewa an kammala sauke ma Umar d’in qur’ani sannan kuma anmai sadaka da fatan Allah ya shiga lamuransa akan komai nasa,in Sha Allah sihirin jikinsa yana gab da warwarewa,Amman irin sihirin da aka masa na kwad’one (padlock)mafi sauk’i karayan sihirin ajikinsa da wuri shine sai dai wanda yamai wannan sihirin da hannunsa zai bud’e kwad’on ya warware sihirin inba haka ba da wuya sihirin ya karye putuk ajikinsa dan wanda yayi sihirin nan ba k’aramin sihiri yayi ba!Amman dai babu abinda yafi k’arfin Allah ,in Sha Allah munanan muna kai kukan mu garesa ,jikin mijinki kuma shima in Sha Allah munanan muna adu’a akai dan Aljanun dannau aka tura masaa “
Cikin jimamin wannan lamarin Mama tace:”Toh malam ubangiji Allah ya saka da alkairi nagode nagodesosai malam Allah k’ara tsawon rai,”
MALAM ya amsa da Ameen sannan sukai sallama ,mama ta kashe wayan ta furta afili:”lalle Zainab kaidinki yafi kaidin shed’an Allah ya isa tsakanin mu dake ,ranar girban abinda kika shuka nanan tafe in Sha Allah,kuma wlh bazan ta6a yafe maki ba zainab!koda ko ace nice k’arshen mutum dazai yafe maki ki shiga aljanna wlh bazan yafe ba,Uwa ai ba abin wasa bace munanan dake saidai ki chanza wata uwar in ana chanzawa dan nikam binta najima da yaye ki ciki ‘ya’yana gaki ga duniyan wanda bai zo bama tana jiransa balle ke da kika jima aciki kina ha’intan mutanen ciki ranar da duniyan taki zata juya maki baya na nan zuwa!”
Mama ta idaa maganar tana sharan kwalla,daga baya kuma ta koma cikin d’aki cikeda tausayin mijinta!.
-***************************
K’arfe biyu daidai na rana Barrister bashir ya isa garin suleja 3 da rabi ya gama shiga k’auyen da malamin yake,tun yana iya kutsawa da motarsa ciki wannan k’ololuwan dajin da wai mutum ne ke zaune a wajen hardai yayi parking ya fito dan kar tayarsa tayi faci ,fita yayi daga cikin motar ya soma kutsawa da k’afa har cikin dajin ,tun yana shawaran komawa ko wata k’ilan 6acewa yayi ba nan bane k’auyen amman dai mobile map d’insa na nunamai nan nedai inda malamin yake,cigaba yayi da takawa har ya iso kan wani k’atuwar dutse da hawanta ma aikine,tsayawa yayi chak yana sauke lumfashi yana kuma kallan yanayin tsawon duwatsun da kana gama hawansa zaka hango bukkar malamin Zee,shi har mamakin ma yanda Zee ke iya zuwa wannan wajen yake,da kyar dai da taimakon Allah Bàshir ya hau k’aton dutsen nan,duk k’aya sungama chakar-kasansa ,ga k’ishin ruwa dake damunsa ga kuma zafin rana da aketa kutsawa yasha wahala iya wahala amman yak’i yarda ya karaya dan dolensa sai ya cika alk’awarin da yad’aukan ma kansa sai ya dawo da martabar Humy ya kuma durk’usar da Zee,ganin ya isa bukkan malam har Murmushi yaruk’a sakin ma kansa yana mai godia ga Allah,tsananin cinkosan mutanen da bashir yagani zaune suna jiran layi yazo kansu ,su shiga wajen malam saida gabansa ya fad’i mutanene ba maza ba kuma ba mata ba many’an hajiyoyi Alhajai,samari,da budurwowi,kai abindai sai wanda ya gani,kallansu kawai Bashir ya tsayayi yana mai tunanin “wai shin mai mutanen duniya suka d’auki rayuwan nan ne shin wai basu san cewa shima boka ko malamin tsubbu halittan Allah ne d’an adam kaman su?wai kuma shi suke tunanin zai iya magance buk’atunsu?kaicho da mutanen da suka 6ata suka kauce hany’ar Allah suka bi hany’ar da bazasu ta6a cinmma burukansu ba,ko zasu ci baifi na d’an k’an k’anin lokaci ba,kai Allah ka k’aramana tsoronka karka ku6utar damu daga kauce ma hany’arka (ameen ya raab ).Da kyar Barrister yasama gurin zama ya zauna ba tareda yace ma kowa uffan ba,layi bai zo kansa ba sai kusan isha,abinda yafi basa mamaki shine rashin ganin ko wannen su dake zaman jiran layi tashi suyi salla kowa jiran layi yake ya iso wajensa suje su gayama malam buk’atunsu shikuma wai ya biya masu,wasu har danbe suke akan rige-rigen shiga ganin malam,shidai sai kallonsu yake rashin yin sallan dabai ba duk sunbi sun damesa!
************************************
Bayan shigansa wajen malam ya sama guri ya zauna yana kallan malamin da ya ajiye wani uban gemu har k’asa ,gashi tsoho dan zaikai shekaru 70 shida ya kamata yaje yata istigfari da hailala har mutuwa tazo masa amman wai yazauna yana bokanci shi adole yana biya ma mutane buk’atunsu hummm,malamin ya wani kafe uban malum-malum yana jan tasbaha,gaban shi kuma wani faranti ne cike da yashi aciki,gyad’a kai kurum Umar yayi cikeda tak’ai ci ya gyara zamansa ya gaida malamin da yawani kafesa da micimicin idanuwan sa,malam yace:
“Uhumm ina jinka yaro maike tafe dakai?fad’imun matsalanka ni kuma ayanzun in magance ma shi “
Murmushin tak’aici bashir yayi sannan yace:”ngde aiki (asiri)nake so kamun akan wata “
Barrister ya ida maganar yana mai ciro wani hoto a hannunsa ya mik’ama malam shi kuma ya amsa yana k’arema Zee kallo sannan ya tuntsure da daria yace:
“Yooo ai wannan tana yawan zuwa wajena,ko jia tazo “
Barrister ya jinjina kai sannan yace:
“Toh ni abinda nake so kamun,ba aiki nake so kayimin akanta ba,kawai abinda nake so shine kabani labarin abinda take zuwa yi wurinka!”
Kallansa sosai malam yayi ko mai ya hango a kwayar idanuwan Bashir Allahu a’alam nisawa yayi yna daria sannan yace:
“Toh Anawa?”
Ya ida maganar yana mai kuma kafe bashir da fici -ficin idanuwansa!
Barrister yace:”kama kanka cinikin da zanbiya kawai “
Jinjina kai MALAM yayi sannan yace:
“Shikenan aidama mu bamuda amana!mu zama mukeyi muna neman kud’i,indai zaka biyamu zamu maka abinda kakeso “
Gyad’a kai Bashir yayi sannan ya ciro dubu d’ari dama yayi hasashen sai bokan nan dan inma an kirasa da malam ancuta malamai magadan annabawa bokan dai shine daidai dashi!
Boka yace :yakuke da ita? Barrister yace :”k’anwata ce “
Ya ida maganar yana mai
Mik’amasa kud’in sannan bokan yaso ma zayyane wa bashir abubuwan da yayi ma Zee tindaga farko:
“Kaganni nan nine nan nayi asirin raba Humairah da iyayenta yanda bazasu ta6a ganin laifin Zee ba saidai na Humairah,sannan nine nan nayi asirin da mahaifinku ya kwanta jiny’a sanadiyan k’in amincewa da auran Zee da Umar,shine tace na kuma nak’asa mahaifin naku dama tunda a nak’asashensa ta taso ta gansa,kuma nine nayi asirinda Humairah tafita daga hayyacinta har izuwa yau Humairah bata san ko ita wacece ba!,sannan ninayi aikin asirin da Dangin Humairah suka k’ita a lokacinda take kawo masu k’arar Zaiyi aure suka kyare tama suka dinga jin haushinta ma,kuma kagnni nan nine nayi asirinda na raba Umar da Humairah,amman Umar har ila yau yana son Humairah,kuma nayi asirinda Umar ya aura Zee,dukda cewa bai ta6a k’aunarta ba! sai dana jefama Umar soyayyar Zee ta yaddaa bazai ta6a daina santa ba har saidai an karya asirin da aka mai,tun wannan musabahan (handshake)da Zee tama umar shine farkon silan kamuwan asirinsa akanta! Kaji kad’an daga cikin abubuwan dana ma zee kuma ni kad’ai keda ikon karya asirin danayi dan kaima karfin aduan ka ce ta shammaceni asirin danama na 6atar da tunaninka akan maganar bincike ya karye!”
Babu abinda umar ke nanatawa a zuciyansa sai innalillahi wainna ilahir rajiun shin wai mai Zee take naima acikin wannan duniyan?
Yace :”Toh yanzun malam nawa zan biyaka dan ka karya dukkanin asirin dakayi?”
Jinjina kai malam yayi dan indai zai biyasa tsaf zai karya nisawa yayi sannan yace:”naira miliyan biyu indai zakaban nikuma zan karya asirin ………………………✍🏻
Nisawa Barrister yayi sannan ya d’an murmusa yace ma bokan:
“Shikenan ba damuwa zan baka naira dubu d’ari biyar yanzun ,gbe in Allah ya kaimu zan kawo ma sauran cikon miliyan d’aya da rabi”!+
Jinjina kai kurum boka yayi sannan yace:”kar ka wuce gbe,inka wuce gbe baka kawo mun sauran kud’inba zan fasa aikin,gbe taal nabaka.Ni kuma nama alk’awarin karya dukkanin wani aikin asirin da Zee tasani nayi “
Jinjina kai Barrister yayi sannan ya masa gbe,ya fito ya soma kutsawa cikin dajin dan isa gurin daya ajiye motar sa,ya sha wahala kwarai kafun ya iso,ya tada motar ya soma fita daga cikin k’auyen.
Sosai barrister bashir ke gudu har saida yafito cikin gari sannan ya tsaya,ya siya ruwa mai sany’i dan wani kalan fitinanniyar k’ishin ruwa yake ji.Sai da ya shany’a goran faro d’aya sannan yayi alwala ya shiga masallaci ya biya sallolin dake kansa,bayan ya idar ya d’aga hannayensa sama yana mai godiya ga ubangijinsa da ya sauk’ak’a masa komai cikin ruwan sany’i.Sosai ya jima yana godia ga rabbil izzati kafun daga bisani ya shafa adu’oin da yayi,ya mik’e ya koma motarsa ya tada yabar unguwar da ya tsaya salla.
Sai wajajen misalin 11:30pm Na dare barrister ya iso garin kaduna,babu inda ya zarce sai gidansa.
Ikram zaune tana ta jiran dawowan bashir tun rana take kiran layinsa amman a kashe,hakan yasa duk tabi ta damu.Jin tsayuwan motarsa a harabar gidan ya sata saurin mik’ewa ta lek’a tagar falan.Wani kalan murmushi taketa sakin ma kanta,da saurinta taje ta tarbosa.Bayan ta taimaka masa yayi wanka ya shirya cikin k’ananun kaya ta gaba tomasa da abinci sosai yaci dan ya d’ebo yunwa rabansa da abinci tun breakfast.Koda ya kammala basu wani tsaya hira ba suka shiga d’aki kafin wasu lokutan bacci yayi awon gaba da barrister dan mugun gajiya yayi.
Washegari kuwa Barrister ya koma wurin malam ,bayan yaje banki ya ciro masa sauran cikon sa,har wani Murmushin jin dad’i kawai Barrister ya ruk’a sakan ma kansa,duk wanda yagansa yau sai yasan yana cikin farin ciki mara misaltuwa,yau kam yana ji ajikinsa k’arshen Zee yazo,dukkanin wasu abubuwan da take tak’ama dashi yazo k’arshe,kuma inda yake ta godema Allah shine har yau kotu bata raba kud’ad’en Umar a hannun dady ba,murmushi ya saki sannan ya gyara kwalan rigarsa yace:
“Taki tazo k’arshe yanzun kam Zainab,soranki girbe abunda kika shuka,wannan shi ake kira da qaik’ayi koma kan mashek’iya!.set and relax kiga yadda duniya zata juya maki baya Zee!”
Daidai nan barrister yayi parking motarsa ya bud’e ya fito,hannunsa rik’eda jakan kud’i.tafiya yasha kaman yanda yayi jiya har saida ya isa bukkar malam.Yauma haka yajira saida layi yazo kansa sannan yasama shiga gurin malam,MALAM Na hangosa da jakan kud’i yasoma murmushi har kod’add’un hak’oransa da sukai jajawur suka bayyana,k’arasowa barrister yayi sannan ya sama waje ya zauna ya gaida malam d’in sannan ya ajiye masa jakan kud’in a gabansa,MALAM yayi murmushi yana lashe gashin gemunsa da harshen bakinsa,bud’e jakan yayi ganin mak’udan kud’in cikin yawaani had’iye miyau sannan ya d’auko bandir d’aya yana wani liliya su,shidai barrister Bàshir nasa idanu dan ya k’osa kawai a karya wannan asirin,maganan malam ne yayi saurin katsesa daga zancen zucin da yake yi,yayi saurin maida hankalinsa wajen malam d’in:
“Ka cika alk’awari,nima bari na cika ma nawa alk’awarin “
Murmushin jin dad’i barrister yayi,had’ida cewa:
“Godia nake “
“Allah nagode ma “
Bashir ya fad’i hakan kuma acikin zuciyansa,bayan malam ya mik’e yaga ya shiga wani lungu,shidai barrister da kallo kawai ya bisa,chan baafi minti d’aya ba malam ya fito rik’eda wani kwarya wanda yake cike da jini aciki.k’arasowa yayi wajen zamansa ya zauna sannan ya ajiye wannan kwaryan jinin akan farantin dake cikeda k’asa,sannan ya kalla bashir dake ta faman kallansa kaman littafin karatu,murmushi bokan yayi sannan yama bashir alamun yak’araso wajensa,jiki ba kwari barrister ya iso ya zauna wajenda malam ya nuna masa,sannan yakai dubansa kan kwaryar da malam yamai nuni daya kalla,ganin jini acikin kwaryan jikin barrister ya gama mutuwa,dogon lumfashi boka yaaja sannan yad’anyi wasu rubutu akan yashin k’asan farantin gabansa sannan yace:
STORY CONTINUES BELOW
“Yanzun zamu fara da karya asirin mahaifinku.”
Barrister dai baice uffanba dan abin ya girmama lamarinsa bai ta6a experiencing irin wannan abun ba!
“Kalli cikin kwaryan jinin nan,fuskan wa kagani?”
Saurin kallan kwaryan barrister yayi sannan yace:”mahaifina!”
Jinjina kai bokan yayi sannan yace “yanzun zai warke,yanzun zai mik’e da k’afafunsa “
Daga haka kawai barrister yaga wannan bokan ya nannad’e rigar hannunsa sannan ya tsoma hannun hagunsa cikin kwaryan jinin,yasoma wasu surutai dashi kawai yasan mai yake fad’a,chan saiga iska tafara kad’a komai dake cikin bukkan tamkar zata tashi sama da komai aciki,tsananin tsoro,fargaba duk bayyane a fuskan barrister amman da yake jajirtaccen namijine sai kawai ya dake,yanata jero dukkanin wasu adu’oin da yazo bakinsa,chan kuma sai iskan ya tsaya yadaina kad’awa malam kuma ya daina surutan da yake yi sannan ya bud’e idanun sa ya ciro hannunsa cikin wannan kwaryan jinin,kallan hannun malamin barrister yayi bakinsa bud’e yana mamakin abinda yagani rik’e a hannun malamin!
“Mai kagani wannan?”
Bakin barrister na rawa yace:”kwad’o (frug)”
Gyad’a kai malam yayi alamun gasgata abinda ya fad’a sannan yace:”kana mamakin yadda akayi na tsamota cikin jinin nan amman babu koda d’igon jini a jikinta ko?”
Gyad’a kai kurum barrister yayi dan abin da mamaki ,murmushi bokan yayi sannan yace:”toh ba abin mamaki bane,wannan kwad’on (frug )bawai cikin kwaryan nan take ba!,tana cikin jikin mahaifinku ne!”
Zaro idanuwa barrister yayi cikeda mamakii bakinsa sai karkarwa yake,boka ya cigaba da cewa:”eh a jikinsa yake,kaga bakin nan nasa dake d’aure da zare ko?toh shiyasa mahaifinku baya iya magana ko kad’an dan rufe bakin kwad’on nan tamkar rufe bakinsa ne!mutuwan sassan jikinsa kuma Aljanun dannau muka aika mai,wanda iskan nan dakaga d’azun ya ruk’a kad’awa sune suka dawo gareni ma’ana sun bar jikin mahaifinku sun dawo wajena.Wannan kenan Na karya sihirin jikin babanku saur
a Na karya sihirin jikin Humairah!”
Barrister yama rasa abinda zaiyi ya kasa sanin tunanin da kwakwalwansa zata mai,kawai yaji hawaye sun wanke masa fuska,wai shin dan Allah dan annabi ana samun mutane masu irin halin Zee kuwa a doran duniyannan?bak’ar mace wacce batada imani ko kad’an cikin zuciyanta,akan son kanta koma waye zata iya kashewa ko nak’asawa?innalillahi wa’inna ilaihir rajiun wlh masu hali irin na Zee su kuji ranar da zasu tsaya a gaban Allah,shin wai sam-sam suna mantawa da cewa akwai k’iyamane?akwai ranar hisabi?ranar tonuwan asiri?inda kowa zaiga abinda ka aikata?wai shin mai ribar hakan?son zuciya ne kawai?irin su Zee fuskokin su baya ta6a had’uwa dana manzon rahma,kuma baza su ta6a jin k’amshin aljanna ba,fir’auna na saman kansu a jahannama “
***********************************
“Fatima binta!”
Baba ya tsinci kansa da fad’in sunan mama tangarau,mama dake zaune kan sallaya tana lazimi taji tamkar muryan baba ya kira sunanta,girgiza kai tayi dan tasan imagining kawai tayi!
“Maman Bashir “!
Baba ya kuma kiranta,saurin waiwayowa mamaa tayi,ware idanuwanta tayi tas akansa ganin baba zaune akan gado bawai a kwance ba,da kyar mama ta iya tattaro k’arfinta bakinta na rawa tace:
“Baban bashir kaine ka kira sunana?kaine zaune kan gado,?”
Gyad’a mata kai kurum baba ya shigayi yana murmushi hawaye na silalowa a fuskansa!
“Eh fatima nine,nina kiraki,kinga ikon Allah ko?yau bakina da sassan jikina suna aiki ko??bayan shekaru d’aya harda rabi yau bakina ya bud’eko?”
Saurin k’arasowa mama tayi wajen baba ta rik’esa gam-gam tana kuka sosai mai tsuma rai!
STORY CONTINUES BELOW
“Allah mungodema,yau uban ‘ya’yana ya mik’e bakinsa ya bud’e yana magaana shima tamkar kowa “
Runguma baba mama tayi tana kuka baba na kuka!
***************************************
(Wai ina Zee?🙄🌚munkusa waiwayan ta karku damu)
****************************************
“Kalli nan!”
MALAM boka ya katse bashir daga duniyan tunanin masu hali irin na Zee,saurin kallan inda bokan ya nuna masaa yayi,wani badubi ne rik’e a hannun malam in!
“Wa kagani aciki?l”
Kallan madubin barrister yayi sannan yaga sun bayyana acikin madubin,baba tsohuwa da Salamatu suna zaune a gefen titin da suka saba zama su kasa biredi,Salamatu na gefe tana aikin nata na zama jugum!
Da karkarwan baki barrister yace:”humairah ce “
“Hhhhh toh yanzun itama zata dawo hayyacinta “
Ajiye madubin malam boka yayi sannan ya d’an d’aga darduman da yake zaune akai ya ciro wani abu kamar laya da’aka zagayesa da bak’in zare!
A hankali malam ya shiga warware wannan bak’in zaren da aka liliyata akan laya,saida ya warware zaren tas sannan ya fiddo wani farin takarda,dake nannad’e warware takardan yayi sannan ya nunama barrister bashir yace;
“Mai aka rubuta ajikin takardan nan?sannan da mai aka rubuta?”
Kallan takardan Barrister yayi sannan yace:”Aisha Humairah maigoro,sannan kuma kaman da jini aka rubuta sunan “
Jinjina kai bokan yayi sannan yace:”gaskia kanada kwakwalwa ,kuma bawai kaman da jini bane,kanaji ko?da jinin nema aka rubuta sunan nata,wannan jinin kuma ba jinin kowa bane face jinin Humairan lokacinda sukai hatsarin nan,ai taji raunuka toh jinin dake fita a jikin nata,nasa Zee ta lakuto mun sannan na rubuta sunanta dashi na linke na maida shi laya! Sannan na bata wani ruwan magani ta baiwa Humairan ta ruk’a sha wanda in har tana shan maganin bazata ta6a dawowa cikin hayyacinta ba! Sannan na bata wani garin magani kamar hodo ta feshe fuskan Humairan dashi wanda zuk’an da hancinta yama garin maganin shine silan mance ko ita wacece!Amman yanzun zan k’ona takardan nan da zaren insuka kone k’urmus,zata dawo cikin hayyacinta kuma zata tuno dukkan wasu abubuwan da takeso ta tuno a kullum inta zauna tana tunani amman take kasawa sabida 6atarda tunaninta danayi,toh ayau zata tuno komai!”
Jinjina kai kurum barrister yayi dan kam yanzun abin yadaina basa mamaki saidai tsoro hummm Allah karka shagaltarda mu hanyar bokaye!
Ashana MALAM boka ya kyasta ya k’ona takardar da zaren,bayan sun k’one k’urmus ya d’au ashes d’in yasany’a acikin ruwa !sannan ya d’ago yace:”saura na Umar!”
Kuma gyara zama barrister yayi yana maia fatan duk inda Humairah take a yanzun ta dawo cikin hayyacinta (kai Allah ameen)
****************************************
Kawai ji tayi hankalinta yadawo gareta,zunbur ta mik’e da sauri tana k’arema inda take da wacce take zaune kusada ita da kallo,kallan sama kawai ta shigayi taji abinda take k’ok’arin tunowa tuni ta tuno shi,saurin dafa cikinta tayi taji wayam,had’a rai tayi tamau ta soma dunfano inda baba tsohuwa ke zaune tana k’arema Humairan kallan mamaki,kafin tsohuwa tayi wani yunk’uri ko tunani,tuni taji Humairah ta chakumota tana haki idanuwanta harsun chanza kala tace:
“Ina d’ana?!”
Yanayin yanda Humairah tayi maganar ba k’aramin firgita baba tsohuwa tayi ba ,tuni baabaa ta firgice tsoro ya dabai -bayeta hankalinta yayi k’ololuwan tashi! Jikinta babu inda baya rawa wallahi!
“Dan Uwarki bakiji ina tambayanki ina d’ana yake ba?ina kika kaimun d’ana?kin bama Zee d’ana ta kashe ne?wlh koki sanar dani inda d’ana yake ko wlh tallahi yanzun nan in maki jina jina “!
Tsananin firgici da tashin hankali kawai baabaa tsohuwa taji tana sakin fitsari a wando ita daii yau ta bani ta lalace kodai asirin daakama Salamatun ya karyene?ita yaya zatayi yanzun?mai zata cema Humairan?fad’a mata inda d’anta yake zatayi komai?inta sanarda ita kuma wlh Zee bazata barta baa cin ubanta zatayi ta maidata bara a k’ark’ashin gada toh mai zatyi?hawaye har sunrigada sun gama wanke fuskanta gashi Humairah tak’i sakanta sai huci take tana jiran amsar ta!
STORY CONTINUES BELOW
****************************************
Wani black leda malam boka ya d’auka sanan ya fiddo abubuwan dake ciki ya ajiyesu ajere one by one!
“Kaga wannan biyun padlocks ne ko ?babba da k’arami ko?wannan kuma allo daakai rubutu da jini ko?wannan kuma gashi daaka aske ko?toh duk zanma bayanin su ayanzun “
Gyara zama barrister yayi dan wannan yafi girmama zatonsa!
“Wannan babban padlock d’in dashi muka datse ko kuma nace na rufe soyayyar Humairah acikin Zuciyan Umar!kaga ayanzun ina bud’e wannan padlock d’in soyayyar Humairah zata dawo kaman yanda take abaya acikin zuciyan Umar fil!,kaga wannan k’aramin padlock d’in kuma dashi ne Zee take juya Umar kamar waina a tanda,take sashi yake ma ‘yan uwansa marik’ansa rashin mutunci da kuma k’in ganin laifin Zee a komai da kuma mance Humairah kwata-kwata a rayuwarsa!,kaga inna bud’e wannan padlock d’in a yanzun tsaf komai zai karye,zai tuno Humairah kaman ma bai ta6a mancewa da ita ba! Zai daina sauraran Zee zai koma yima marik’an sa biyayya.
Wannan allon k’arfen kuma da kake gani rubuce da jini ba jinin kowa bane face jnin hailan Zee wanda nasata kawomin dan dashi zaayi rubutun akan allon asa sunanta da sunan Umar a kunna wuta harsai sunan ya zauna rad’au akan allon k’arfen ta yadda Umar da Zee bazasu ta6a rabuwa ba kuma bazai daina sonta ba! Wannan sassak’en askekken gashin kuma na hammatar Umar ne wanda shi sai bayan auransu nasata kawomin dan yin laya dashi wanda zee zata sakaya a wuyanta a kullum in yaganta zata ruk’a mai kwarjini,amman a yanzun zan tawar watsa wannan k’ullin na aika aljanu su cire mata layyan dake wuyan nata!”
Saka hannunsa yayi cikin aljihun rigarsa sai kawai ga layar ta bayyana,barrister kam sai jinjina wannan makircin yake hawaye fal fuskansa! Malam ya shiga warware layyan tas,sannan yasa ruwa ya wanke wannan k’arfen nan da nan allon yadawo k’al boka ya nisa yace:”Zee taki tazo k’arshe yanzun saura mu karya na jikin iyayen Humairah da yayyinta “
^^^^^^^^^^^^^^^^^
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
Bud’e idanuwansa yaso mayi a hankali har ya bud’esu tangarau akan k’ofar d’akin nasa,ji yake kowani ga6o6in jikinsa a sake tamkar an sauke mai wani babban nauyi ajikinsa,murmushi ya bayyana a fuskansa,sannan ya d’an waiwayo dan ya tasheta tayi sallan asuba dan har alfijiri tafara fitowa sun makara salla!
Ganin wacce take kwance sha6e-sha6e akan gadon daga ita sai wani fitinanniyar sleeping dress tana baccinta cikin jin dad’i ,yasa ko ina ajikinsa shakku,mamaki,fushi,haushi duka cikeda mamaki Umar ya furta afili
“Zainab?!zainab kwance akan gadona?daga ita sai kayan bacci?any’a ba idanuwa na bane suke mun gizonta?toh uban maiyasa zasu mun gizon surarta da fuskarta uwar mai zasu mai?”
Goge idanuwansa da bayan hannayensa ya shigayi sannan ya kuma waro idanuwansa tangarau akanta still dai zee yake gani k’aremata kallo tsaf ya shigayi sannan ya matso daf da ita lalle wannan Zainab ce toh waii dan uwarta uwar mai take mai a d’aki eh?har tazo ta kwanta a gadonsa tare wai sukayi bacci ko mai?ina Humairah?da saurinsa kaman zautacce ya mik’e a fusace yayo kan Zee ba tareda yayi wani tunani ba kawai ya fisgota ta fad’o dum a k’asa da sauri Zee tashiga gurza idanuwanta dan tabbatarda badai mafarki take ba?ji kawai tayi Umar ya wanketa dawasu irin lafiyayun maruka ta rantse sai da jinta ya d’auke na wasu da k’ik’u!
“Kee Uban uwar mai kike mun a d’aki kwance shame _shame kamar matata?ke dabbar wace gari ce?a tahirin rayuwarki kaf kin ta6a cin karo da cewa Umar na wasa dake Zainab?kin ta6a koda ace da wasa Umar na dogon zance dake?dan nabarki kindawo gidana shine har kike da guts da zaki shugomun d’aki harki had’a shimfid’a dani!?eh answer my questions what the hell are you doing in my room?answer me bfr I shoot u down to death!”
Yanayin yanda Umar kawai ke magana ya isa Zee tsurewa bare kuma yanda taga launin jikinsa da idanunsa suka chanza yana dunfaro inda take itakuma tana matsawa dukkanin jikinta sai rawa yakeyi:
“Wai mai haka ?mai Umar ke nufi ?ha’a haukacewa yayi ne?”
Uwar ashar d’in da Umar ya mata ne yasata tsayawa da tunaninta chak!
“Zainab wlh inbaki gayamun Uwar abinda ya kawoki d’akina ba wlh tallahi saina kasheki,saina lahantaki!, za’a kasa ganeki wlh for the very last time Zainab u should answer my question “
Umar ya ida maganar cikeda masifa har jijiyoyin jikinsa na tashi,Zee tsananin tsoronsa,fargaba,firgici,rawan jiki duk ya hanata iya tunanin koda abu d’aya tak da kyar ta iya furtawa da k’arfi:
“MAIKE SHIRIN FARUWA WAI?!🤯”…………….✍🏻
Cikin hargagi da d’aga murya Umar yace:+
“Cin Mutuncinki da nannak’asa ki cikin d’akin nan ke shirin faruwa!,muddin baki bani amsar tambayata ba! Uwar mai kike mun a d’aki nace!”
Babu inda muryan Umar bai amsa maganan sa ba,tsaban bai masan halinda yake ciki ba da 6acin ran ganin wannan Zee d’in,had’iye miyau Zee tayi dake ‘yar duniya ce sai mik’ewa tayi dukda tsanin tsoratan Umar d’in da tayi amman ta dake,ta d’aure fuskanta tamau sannan ta kallo Umar d’in wanda in ransa yayi dubu toh ya gama 6aci,ji yakeyi wlh inhar bata basa amsar tambayar sa ba wlh zai iya nak’asata dan shi wlh bai k’aunar yariny’an nan!
Ta6e baki Zee tayi had’ida tafe hannayenta sannan tace:
“Aww tambayata kake mai nakeyi acikin d’akinka ko?”
Jin yayi banza da ita yana wurgo mata harara yasata cigaba da cewa:
“Yooo toh kai uwar mai kake tunanin nazo yi d’akinka?ko yaune farau kwanciyata a d’akin naka ?bansan sha-shanci da tashanci fa!harni zaka kalla kace mainakeyi a d’akinka?toh bari in tunama inka manta koni wacece awajenka,mainene matsayina wajenka in duk ka manta su let me remind u ! Bari na tunama ni Zainab ni matarka ce kuma uwar d’anka Abul-is…………..
Tas taji Umar ya wanketa da wani kalan gigitacciyar mari sannan ya nunata da yatsa:
“Ke! Ahir d’inki wlh in kika kuma danganta kanki a matsayin matata wlh saina zubar da hak’oranki balle kuma har in kikace ke Uwar ‘ya’yanane saina ci Ubanki wlh!”
Dafe kumatunta da har shedin hannayen Umar suka bayyana akansu Zee tayi sannan ta d’ago tana kallan Umar cikeda mamaki “kai any’a wannan Umar ne?any’a ba wani bane keson yin playing pranks akanta ba?yasany’a fuskan Umar?dole tasan abinyi dan wlh babu wanda ya isa ya shugo hany’anta,a yanzun daya rage mata k’iris ta mallaka dukiyoyin Umar mafarkinta nazama multy-billionaire yayi,sannan wai wani ya shiga gonarta koma dai bashir ne da wannan d’any’an aikin?toh ba malam ya 6atar masa da hankalin bincike akanta ba?toh wai waye?uban uwar waye keson dagula lissafinta da sassafen nan?dole yau sai taje Suleja dan wannan yafi k’arfin takira malam a waya saidai su gana face to face ta yanda zai binciko mata wani harsugumin d’an iskan ne keson fara wasa da kwakwalwanta!1
Kallan Umar d’in tayi sosai sannan tace:”Uban wa ya aikoka wajena?zaka fad’amun yanzun kosaina aikaka lahira?nasa an binciko mun uwar wanda kake ma aiki akaina?!”
Zee ta ida maganar tana zaroma Umar kwalakwalan idanuwanta!
Gaskia yariny’an nan tamugun raina masa wayau gyad’a kai umar yayi sannan yace a fili:
“Lallai Zee kin rainani amman I won’t blame u bari naje d’akin Humairan na tasheta tazo taga uwar iskancin da kika bijiro dashi a cikin gidanan,kuma wlh kisani bazan barki haka ba sai naci mutuncinki wawiya sokuwa doluwa “
Daga haka yasa kansa ya fice a d’akin ,Zee kuma ta tsaya sororo tana mamakin wannan lamari “kodai asirin dake jikinsa ya karyene???ha’an tayaya asirin zai karye bayan malam boka yace mata sam-sam sihirin dazai mata akan kowa bazai ta6a warware waba,har saidai in shini ya warware sihirin da hannunsa! Kuma duk uban kud’ad’an da take basa ai bazai ta6a warwarewa ba infact ai basu ta6a samun sa6ani da boka ba!toh tayaya hakan zai faru?tafi zaton gaskia wani ke wasa da kwakwalwanta bata yarda cewa wannan asalin Umar d’in Humy bane!1
Bud’e k’ofan d’akin Humy yayi ya shiga cikin fad’a fad’a yasoma cewa:
“Humy kifito kiga abinda aminiyar taki wacce kika dan k’ama AMANARKI ta aikata ayau,wai bakiji ina magana bane ki fito daga band’akin kiga ikon Allah nace ko!”
STORY CONTINUES BELOW
Nanma shuru yaji hakan ya kuma k’ular dashi da saurinsa ya banko k’ofan bayin amman to his surprise sai yaga wayam,waiwayowa yayi yashiga k’arema d’akin kallo ko zai ganta nanma wayam babu Humairah babu dalilinta! ,saurin fitowa d’akin yayi ya wuce kitchen kozai ganta achan nanma wayam babu inda bai shiga a cikin gidan ba amman bai ga Humairah ba,d’akin Abul-islam dake kusada nashi ya shiga turus ya tsaya ganin yaro kwance kan gado kuma d’akin anmai ado da kayan yara,saurin k’arasowa yayi wajen yaron gabansa yashiga dukan d’ari -d’ari ganin kamannin sa da yaron sak sak “kenan wnnan d’ansa ne?toh yaushene ya haihu haka da bai sani ba?”
_toh bari in tunama inka manta koni wacece awajenka,mainene matsayina wajenka in duk ka manta su let me remind u ! Bari na tunama ni Zainab ni matarka ce kuma uwar d’anka Abul-is_”
Maganar da Zee ta gayamai d’azun yayi ringing acikin kwakwalwansa saurin mik’ewa yayi da sauri ya dafe kansa yana ambaton sunayen Allah,yana son tuno taya wai Zee tadawo matarsa har suka haihu wai yake da d’a?sannan kuma ina Humairah?duk inda yake zaton zata shiga acikin gidanan ya duba bata ciki!toh da gaske kenan wai ya aura Zee?harsun haihu yaro ya girma?toh wai yaushe akayi hakan?yaya kuma akayi hakan ta faru,ya akayi bai tuno komai daya danganci Zee a matsayin matarsa ba?wai mai haka,maike shirinfaruwa dashi ,ina humairan sa?”
Kuma dafe kansa dake faman saramai tamkar zai rabe biyu yayi,yana jero inalillahi wa’inna ilaihir rajiun sau babu adadi hardai yasamu natsuwa ta ziyarce shi!
Babu maii basa amsoshin tambayansa sai Zee,saurin fitowa yayi daga d’akin Abul, yayi saurin shiga d’akinsa ya iske
Zee hartayi wanka ta sauya kaya tana kwalliya akan dressing mirror (ita anan tayi shirin zuwa wajen malam dan binciko mata uban dake son shigo hany’anta).Mamaki fal fuskan Umar aina tasamu kayan jikinta harta sauya ya kuma akayi kayan kwalliyan mata suke birjik jere akan dressing mirror d’insa wai what the hell is going on hear?”
Ya furta a fili da k’arfinsa wanda har yaso tsorata Zee amman saita dake ta ballomai harara tace:”duk d’an tashan ma daya aikoka wajena dan ruguza tanadina dakai da komawaye sai kun sha mamakina “
Daga haka ta waiga ta cigaba da fesa turaren dake hannunta rai kwance!
Umar kam daskarewa yayi a tsaye yana mamakin wannan al’amarin any’a kuwa ba mafarki yake yiba?mintsilin kansa ya shigayi sannan a lokaci d’aya kuma yana murza idanuwansa dan tabbatar da cewa badai a zahiranci wannan al’amarin ke faruwa ba.Ganin daifa tabbas lallai wannan al’amarin a zahirine ba mafarki ko tunaniba yasa Umar damk’o Zee ya had’a rai tamkar bai ta6a daria a rayuwarsa ba!
“Zee wallahi tallahi ni ba tsaran wasanki bane a tahirin rayuwarki kaf baki ta6a cin karo da Umar abokin wasanki bane,ki gaggauta sanar dani inda Humyna take sannan ya akayi kika zama matata ya kuma akayi wanchan d’an ya zama nawa answer my question Zainab if not I promise to make your miserable life at this moment pointless!answer me nace!”
Umar ya Ida maganar cikin d’aga murya lokaci d’aya kuma yana sakin huci da tsananta murd’e kunnen Zee!
Zee har saida ta saki fitsari a wando tsaban azaban murd’a kunnuwanta da Umar yayi,wlh fa wannan asalin Umar ne in bata saki jikinta tabasa labarin abinda ya faruba tasan wlh zai iya shek’ata lahira a irin wannan yanayin da yake ciki a yanzun! Tabbas kodama ace asirin jikin nasane ya karye toh zata sanar dashi komai da komai sannan a yau d’innan zata suleja dan malam ya kuma d’aure mata Umar kam-kam k’ila wani mushkilan aka samu asirin ya karye tunda tasama labrn mama kullum cikin sa malamai sauke ma Umar alqur’ani take,tsaf tacema MALAM bokanta ya nak’asa mahaifiyarta ma tunda tana son shiga gonarta amman boka yace mata jinin mama yafi k’arfin asirinsa ita tun kakannin kakaninta aka masu babban tsari wanda babu wani aljani ko boka ko malamin tsubbun dazai iya kaftawa dasu,hankalinta yayi masifan tashi amman malam yace mata babu fa yanda zai iya da mama! Kenan tashi tsayen da mama tayi ana saukema umar kur’ani shine yayi tasiri a kansa kenan?toh a yau ba gbema sai ankuma maidashi gidan jia ai shi Umar yake ba Fatima binta ba (mama )da wai sukeda tsarin sammu tun kakan kakanni!
STORY CONTINUES BELOW
“Waiyooo kasakeni zanma bayani “
Zee ta ida maganar tana fidda kwallan azaba!
Saketan yayi kuwa,ita kuma ta shiga share hawayenta sannan tace:
“Tabbas yanda na fad’ama a farkon cewa ni matarka ce babu ko shakku hakan take ni matarka ce kuma Abul-islam d’an kane nina haifama shi!”
Damk’e hannayensa Umar yayi sosai yana huci yana kuma lalla6an zuciyansa dan kalman nan da take cewa wai ita matarsa ce wlh jiyake kaman tana jefamai garwashin wuta a dukkanin sassan jikinsa,amman dole ya danne zuciyansa ya tsaya ya saurari abinda zata fad’a dan sanin inda humairah take da yadda akayi ya haifa yaro sak mai kama dashi,da baida masaniyar yin hakan!
“Eh ni matarkace…..:……………
Nan Zee ta shiga basa lbrn tas abinda yafaru tun lokacin fara soyyarsu har dukan humairah da koran kare da yamata,da kuma mutuwar Humairan,har raba kud’in gadonsa da yasa dady yayi!
Wlh shi dai umar kawai jin maganar yake tamkar tatsuniya dan inba tatsuniya take basa ba hankali bazai ta6a d’aukan wannan labarinba,dan duk wanda tafad’ima hakanma dukanta zaiyi dan kowa yasan halinsa bazai ta6a iya aikata hakan ba!
Tayaya Zai yi soyayya da Zee ?ta yaaah zai daka Humairah har yamata koran kare,wai duk akan Zee?yaushe humairah ta rasu dabai sani ba?how kuma why will he even say dady yabasa dukiyansa?yaushe akayi hakan?tayaaah akayi?”
Had’a girar sama data k’asa yayi sannan ya had’e ransa tamau ya kalla Zeen yace: “prove wat u just say or else wallahi tallahi ni kad’ai nasan abinda zan maki “!
Murmushin yak’e Tayi sannan ta mai nuni da wayansa dake gefen side drawer tace:”over there,ga duba wayanka zaka gani “
Saurin k’arasawa yayi wajen ya d’au wayansa ya kunna sai dai mai zai gani?hotonsa da Zee suna rungume da juna suna sakanma kawunan su murmushi,manne a screen d’in wayarsa,saurin unlocking wayar yayi,ya shiga gallery babu abinda yake cin karo dasu face hotunansa da Zee suna rungume da juna ko kuma suna cin abinci,wasu kuma a bich suka d’auka wasu kuma a k’asan waje wasu kuma da Abul-islam tun yana yaronsa har izuwa yanzun!
Inallilahi wa’inna ilaihir rajiun tabbas wannan shine acikin hotunan amman wlh shi yakasa tunanin lokacinda ya aikata hakan toh tabbas babu shakku Zee asiri tamai ta mantarmai dakomai ammanko wlh saiyaci uban Zee saina lahira yafita jin dad’i kenan da gaske Humairah tarasu wlh k’arya take Humynsa bata rasuba tananan da ranta karya kawai tamasa zaman dirshen Umar yayi akan tiles d’in d’akin ya d’ora hannun damansa kan fusakar sa hannun haganunsa kuma ya dafata akan gwiwan k’afarsa,kuka wiiwiii Umar ya fara dan yama rasa mai zaiyi dan yaji dad’i,wlh Zee ta gama dashi ta kashesa,Zee kuwa sai binsa da kallo kawai take ranta na matuk’ar 6aci ganin sihirin jikin Umar ya karye!muryansane ya katseta,cikin shashek’an kuka yace:
“Amman Wallahi Zee kin cuceni!,kin cuta rayuwata bazan ta6a yafe maki ba,koda ko ace nine k’arshen mutumin da zai yafe maki kafun abud’e maki k’ofar aljanna ki shiga!wallahi I will never ever forgive you,dama a kullum saina kwa6a Humy akan al’amarinki amman bataji dake ita da zuciya d’aya tal take zama dake kuma take k’aunarki,Amman wai kece yau kika karya AMANARKU kika aure mata mijinta ta hany’ar asiri wlh Zee Allah bazai barki haka ba,nima kuma dan busun rashin imaninki bazan barki ba wlh saina koya maki hankali,saina kafa tahiri a rayuwarki yanda ko en baya suka ci karo da yanayin yanda k’arshenki yak’are bazasu so su cigaba da rayuwa irin taki ba wlh Zee u must pay deathly wlh ,inda kika mun k’aryan cewa Humairah ta tafi kema wlh yau sai kin bak’unci wajen “!
Tal Umar ya wurgoma Zee wayansa akan fuskanta ihu Zee ta saki tana dafe wajen da wayan ya bigeta kafun tayi wani yunk’uri kawai sai ji tayi Umar na kwallo da ita yana kir6ar muguwa iyason ransa tun Zee na kukan wahala har muryanta ya dishe tashiga rok’on Umar amman ina baiji bai gani haka kawai ya rufe idanunsa yana cin ubanta!
STORY CONTINUES BELOW
Yatsan hannunta na dama tanaji tana kallo Umar ya mata targad’e da hannun.Jitayi ya daina bugun nata lokaci d’aya.Lumfashin wahala ta ruk’a jerowa lokaci d’aya muryan barrister Bàshir taji a dodon kunnuwanta.Shigowansa cikin gidan kenan ya ruk’a doka sallama amman ba wanda ya amsa mai hakan yasa shi shiga kai tsaye hargagin Kukan Abul -Islam ne yasa shi saurin k’arasowa d’akin dukda hargagin kuka da duka da yakeji na fitowa a d’akin Umar bai sashi fara lek’awa chan ba dan ya tabbata Zee UMAR ke duka tunda asirin jikinsa ya karye Murmushin jin dad’i barrister yayi sannan yashiga ya dauki Abul dake ta faman kuka harda haki,lallashin yaron ya shigayi saida ya tabbata yayi shuru sannan ya fito ya nufo d’akin UMAR din,ganin wani k’aramin wuk’a a hannun Umar d’in yana shirin sokama Zee a ciki Barriter bashir yayi saurin rik’esa yana girgiza mai kai,sai anan Umar ya kalla Bàshir din yaga duk ya rame!
Barrister Bàshir yace cikin d’aga murya:
“Barta Umar ,nace kabarta karka kasheta! Mutuwanta a yanzun wlh gatane a gareta,babban gata ka mata,karka kasheta kabarta tasoma girbe dukkanin wasu abubuwan data shuka,yanzun kam ai tataah kuma tazo k’arshe ,barinta a raye taga sakayyar da Allah zaima d’unbin mutanenda ta cuta kawai ya isheta ishara bare kuma in ta mutu ta koma gaban Allah
inda zata fuskanci babban hukuncin abinda ta aikata!Zee ta chanchanci kisa dan rage irinsu a doran k’asa amman mutuwarta a yanzun ba tareda tasha wahalan duniya kafun mutuwarta gata aka mata,saidai in Haka Allah ya rubuta lokacinda a daidai wannan ga6ar ne,amman If not Zee tsananin k’uncin duniyan da zaki soma fuskanta kawai ta isheki soma rok’ama kanki da kanki mutuwa!,barta Umar duniya zata koya mata hankali “!
Sakin wuk’an hannunsa tafad’a a tiles Umar yayi jikinsa duk amace dan maganganun wanta gaskiya ne barinta a rayen shine mafi alkairi dan ta kwashi kayan bak’incikin data sa kanta a ciki!”
Jan hannunsa barrister yayi sannan ya fito dashi waje yasa Umar d’in kulle d’akin dan karma Zeen tayi yunk’urin guduwa dan wani tarkon yakeson ya kuma d’ana mata (shi barrister Bàshir din kenan).Lallashin Umar Bareister ya shigayi sannan shima yace ma Umar d’in Humy bata raye wanda sanadiyan hakan saida aka kwantarda Umar a asibity!
*********************************
Zee kuwa a galabaice ta mik’e tasoma jan jikinta so take kawai ta k’arasa mirror ta d’au wayanta takira malam,k’arema kanta kallo tashigayi acikin mirror din,harsai data tsorata ganin yanayin yanda halittaan fuskarta ya sauya!
Sosai fuskanta ya kumbura suntum,sannan idon hagunta ya kumbura shima suntum harya tara jini saiwajen yayi bak’i bakinta kuma ya fashe sai fidda jini yake,bud’e bakinta da zatayi kawai taga Umar yamata ha6on hak’oran gabanta guda biyu suna lilon san 6allewa ko kuma nama ce fad’owa dan kyas kawai hak’oran ke jira su zube!
Wani kalan razananniyar ihu Zee ta sake tana kwala k’ara tana tashiga uku ta lalace Umar yanak’asata!kaman mahaukaciya haka tashiga naiman lanban MALAM boka tana kiransa amman wai layinsa a kashe dukkanin lanbobinsa da suke waya dashi babu wanda Zee bata kiraba amman duk a kashe Zee tasaki futsari har babu adadi a tsaye! Ihu kawai take kwalawa tana zagaye d’akin tana kuka harda majina tana “MALAM karkamun haka,dakai kawai Na dogara,karkamun haka ka kunna wayanka,Na shiga Uku nii Zainab ‘yar fatima mai ke shirin faruwa da rayuwata ne?”
Bubbuga kanta da hannayenta ta shigayi Waiko zata sama mafita,wajen k’ofa ta nufa tasa hannu zata bud’e dan wucewa suleja wajen malam taji k’ofa a gark’ame tayi-tayi k’ofa ta bud’e k’ofan tak’i bud’ewa k’arshe kawai Zee ta zame a k’asan tiles d’in bakin k’ofan tazauna dirshen ta cire d’an kwalin kanta gashin kanta ya barbaje a fuskanta,dukan kanta da fuskanta kawai ta shigayi ba tareda ta damu da irin yanayin datake ciki ba ihu ,kukan hauka,birgima,babu wanda Zee batayi ba idanuwanta duk sun kumbura sunyi jajawur kaman tattasai tsaban jaaa tun tana kiran lanban malam switched off hardai zuciya ya d’ebeta ta buga wayan tata a k’asa ta fad’a bugum ta tawarwatse a k’asan,amman hakan bataji ya issheta koya kwantar mata da hankalinta ba! Hakan yasata mik’ewa kaman mahaukaciya tasoma hargitsa kayan cikin d’akin da duk wani abu dazai iya fashewa tashiga faffasasu bata damu da taka kwalaben datayi a k’afafunta ba saii fiddo jini suke itadai burinta kawai ta hargitsa d’akin ko zata sama sassauci a zuciyanta!
STORY CONTINUES BELOW
Cikin dashashshiyar muryata tasoma fadin:”Ni Zee ni yau zan wulak’anta?wlh k’aryan koma waye wlh saina kuma dak’ule duk wani farincikinka Umar Yaah Bàshir kaikuma alamu sun nunamun kaine duk ummul haba’isin abinda ke faruwa dani a yanzun wlh sainasa aljanun malam sun shany’emun jininka!baka isa kashugo hany’ata ba! Wlh baka isa ba ,saina kasheka wlh saina kasheka,saika Mutu bashir saika mutu wlh!”
Zee ta ida maganar cikin d’aga murya da rufe kunnayenta da tafukan hannayenta ,tareda runtsa kumburarrun idanuwanta sosai ,ga gashin kanta daya barbazo mata har kafad’unta ,tashiga zagaye d’akin kaman zautacciya tana sunbatu iri iri!
Daga k’arshe sai tafad’a ragwaf akan gado tana sauke lumfashi tana magana k’asa-k’asa kaman bugaggiya “Wlh. Saina kasheka yaah bashir “
Haka ta ruk’a nanatawa har bacci 6arawo yayi awon gaba da ita,amman still bakinta na motsin kiran sunan bashir saina kasheka!
*************************************
Kitsaya wallahi ni bansan inda d’anki yake ba,kimun rai kizo mu koma gida zan maki bayanin komai kinga anan zaki tara mana jama’a ,dan Allah salamatu “
Kuma had’e rai Humairah tayi tamau sannan ta waiga ta kalla mutanen da suka masu tsaye suna kallansu,tsaki taja sannan tayi gaba baabaah tsohuwa kuma ta d’au farantin biredi ta d’aura akanta,sai mamakin Salamtun take kullum fa ita ke d’aura tiren biredin nan zuwa da dawo duka ,amman wai yau tayi biris tak’i d’auka.Ikon Allah wallahi babu mamaki yariny’an nan tadawo cikin hayyacinta,!
“Baza kiyi sauri kishiga gaba kinunamun gidan da d’an nawa yake ba ko saina zo na wanwankeki da mari?”
Saurin k’arasowa gaban baabaa tayi dan wallahi duk a kid’ime take,a haka dai tana gaba Humy Na biye da ita a baya har suka shiga cikin gidan!
K’arema gidan kallo tsaf Humairah ta tsayayi .Tana shirin yin magana taji ana doka sallama,ai da hanzarinta baabaa tsohuwa ta amsa sallaman had’i da cewa shugo dan k’ilan d’an Aiken Zee ne kuma k’ilan tareda Zeen suka zo ,shiyasa duk sai taji zuciyanta ya fara samun sukuni!
Amman ganin shine ya d’an sata sakin murmushin yak’e dan tabbas yanzun wannan mara mutuncin yariny’ar (humy) sai ta iya disgata gaban sulaimanu (barrister Bàshir ) takuma tona mata asiri.Ganin suna ma junansu kallon kallone yasata gyara tsayuwanta tana k’are masu kallo!
“Yaah bashir!”
Humy ta furta sunansa da d’an k’arfi fuskanta cikeda mamakin abinda ya kawosa nan,murmushi ya sakan mata yace: “na’am Humairah “
Zata jefo masa tambaya,yayi saurin dakatarda ita inda yake cewa:”Am Humairah rik’e tambayoyinki for now dan u deserve to ask many questions ,amman ba yanzun ba in lokacin yayi zan sanar dake okey?for now let me handle this old woman (bari nayi maganin wannan tsohuwar matar)”
Yanayin yanda ya ida maganar yana watsama baabaa tsohuwa uban harara,tsoro sosai ya diran ma baabaah dan wallahi babu ko shakku asirinta ne ya tonu.”Toh mainene had’in Sulaiman (bashir)da salame?”
Kafun takaiga bama kanta amsa kawai taji barrister Bàshir yana ma en sanda isowa,Aiko suna shiga ya nuna baabaah yace :”ita nakeson ku kama mun ku kulleta a cell sannan karku kuskura kubada belinta ga duk wani wanda yazo belinta “
“Ok sir “!
En sandan suka amsa ma barrister had’i da saluting d’insa!
Baabaa tsohuwa naji Na kallo wasu en sanda mata biyu suka kamata aka samata ankwa aka tasa k’eyanta zuwa motar en sanda,sai kuka takeyi tana :”wallahi sakani akayi nayi hakan , ku yimun rai wlh zan sanar daku komai “
Tanayi tana kuka da share majina wata er sanda tace:”Heys tsohuwa ki adana kalamanki har sai kinje station wa’allah achan in kina bada statement d’inki ya anfaneki “
Hakadai aka sa tsohuwa a motar en sada aka wuce da ita prison d’in Zaria aka kulleta achan,ita kuma ta sulale k’asa tana kuka tana tsine ma Zee :”Allah ya tsine maki Zee ,kema in Sha Allah k’arshenki anan zaki k’arasa shi ,dan wlh saina tona asirinki sai Na fad’a dukkanin abubuwan dana sani a kanki,waiyooooo en gadan bara kuzo ku ceceni,”
Tanayi tana kuka amman babu kowani mutum d’aya da ya mata kallon arziqi,en cikin cell d’in daaka gark’amesu ,suma aciki da suka harzuk’a da surutan da take masu kawai suka mik’e su kusan biyar suka shiga nannakad’ama Baabaah tsohuwa dukan tsiya tun tana kuka tana basu hakuri,har tazo ta daina motsi dan sun mata jina jina,k’arshe dai sai a clinic d’in police station ta kwana,bama tasan wanda yake kanta ba!
**********************************
“Calm down Humairah I will explain everything out (zan maki bayanin komai) “
Kuka sosai kawai Humairah keyi tana son sanin inda cikinta yake koda
i dama cikinta ya zubene?babu abinda take iya tunawa face zuwanta tasha da kuma tafiyansu abuja,daga nan bata san kuma abinda ya sake faruwa da itaba,sai yanzun data mik’e taganta wai a zaria ,toh ita mai ya kawota zaria,ita da zata abuja?Umar da Zee sun cuce rayuwarta wlh bazata ta6a yafe masu ba,sannan muddin in har wallahi tallahi cikinta zubewa yayi ko kuma kashe mata d’an cikinta Zee tayi kaman yanda ta fad’imata a baya d’an cikinta bazai rayuba!.Toh kuwa babu ko shakka Zee will left her with no option zata tabbata ta biya ran d’anta!
Wallahi tallahi tayi ma kanta alk’awarin ruguza rayuwar farin-ciki tsakanin Umar da Zee sai ta mayar masu da rayuwansu a living hell ! Zasuyi mamakinta wallahi ,basu santa bane ai hak’uri da kawaici ba hauka bane ,zata d’and’ana masu cewa rijiya ba wurin wasan makaho bane! They should sit and wait for her arrival dawowanta garesu daidai yake da chanza launin rayuwansu,tayi alk’awarin suma sai sun d’and’ani bak’in ciki kaman yanda suka d’and’ana mata!
Barrister Bàshir ne ya katseta daga zancen zuciyan da takeyi,yanayin yanda yaga tana huci kawai ya isa bada shaidan cewa ranta a matuk’ar 6ace yake,zai iya rantsewa cewa bai ta6a ganin Humy acikin wannan yanayin ba!
Kama hannunta yayi ya zaunar da ita sannan ya mik’a mata goran ruwa ta amsa ba musu ta shany’e tas dan zuciyanta Na barazanar fitowa!
Saida yaga ta samaa natsuwa sosai sannan ya soma cewa:”kiyi hak’uri ga dukkanin abubuwan da suka faru dake a baya Humairah shi mahak’urci mawa daci ne kibari Allah da kansa ya saka maki da abinda aka aikata a gareki,”
Tunda yake maaganan take k’aremasa kallo har saida taji yakai aya sannan tayi Murmushin gefen baki da yafi kuka ciwo sannan tace :”hak’uri?mainene kuma hak’uri yaah bashir?dan a yanzun Humairah batasan mainene kalman Hak’uri ke nufi ba!.Yanzun Humairah ba Ayeeshan daa bace dazaa takata yanda akeso,Humairan daa dana yanzun daban suke!wannan Humairan…!
Ta nuna kanta da yatsan hannunta sannan ta karkad’a k’afanta ,ta cigabada cewa:”batasan hak’uri ba kuma batasan yafiya ba!.Ita wannan humairan daidai take da k’ugun kowa,sannan mai d’aukar fansa ce!wallahi tallahi yadda aka tagayyara rayuwata aka rabani da farin ciki aka rabani da cikina,nima wlh saina rabasu da duk wani farin ciki a rayuwar nan “
Kallanta kawai barrister keyi cikeda mamakinta “wai dama Humairah nada baki har haka?koda yake wanda bai iya fushi ba inyayi fushi,fushinsa bazai ta6a kasan cewa mai kyauba,in Humairah ta chanza tadawo yanda ta ayyana masa ayanzun cewan zata dawo ,toh wallahi baiga laifinta ba dan ta6ata akayi ankaita mak’ura dole ta fashe itama ta nuna cewa ba kanwar lasa bace! Amman yanayin maganganunta nanu mai cewa kaman harda Umar take nufi ,tabbas dole ya zayyane mata dukkanin abubuwan da suka faru dan zuciyanta ta wanke Umar daga zargin da take masa dan shi bada masaniyar sa akai komai ba!Zee kawai itace wacce zata fuskanci hukunci ita kad’ai dan itace shed’aniyar bawai kowa ba! Dan kowa bayin kansa bane! Asirine,nisawa yayi sannan yace: “maganan ki hakan take humy saidai inaso bfr kiyi taking any action akan komai,inaso ki aramun kunnuwanki anan dan sanardake wasu muhimman abubuwa kafin ki yanke hukunci,nayarda bayan Na kammala gaya maki abubuwan da suka faru,ki yanke duk wani hukuncin da kikasan daidaine! Amman kifara saurarata da kunnayen basira…..,………✍🏻