AMANAR MU CHAPTER 11 KARSHE

AMANAR MU CHAPTER 11 K’ARSHE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tsaf yaah Bàshir ya zayyanewa Humairah komai da komai babu abinda ya 6oye mata ko d’aya abu d’aya yasan cewa ya 6oye mata bai fad’aba shine adadin kud’ad’an daya kashe.Wannan ya barwa kansa da kuma Allan sa,dan beyi dan abiyasa ba!,hasalima da ace mahaifin Humy bai tsaya tsayin daka ya karantar dashi ba,da bazai ta6a kai wannan matakin da yake a yanzun ba,koda ace duka dukiyansa da ya mallaka zai kashe akan su Dady ya sani bazai ta6a koda biyan dady kotan mak’udan kud’ad’en daya kashe akansa bare kuma iyayensa da k’annansa!”+

Bilhakki da gaskia Humy keta rusa kuka,ta rasa wannan wani kalan rayuwa ce ta rasa dalilin da yasa mutane ke d’aukan duniyan nan da zafi har haka! ,yau wai makusan cinka shine mai cin duduniyarka,yaci Amanarka upon all the sacrifice u made for them ,babu wani wanda zai ta6a zaton cewa Xee zata iya aikata wannan d’any’an aikin data aikata,Allah sarki yaah Umar d’ina ashe bayin kanka bane asiri aka maka aka juyarmun da kwakwalwanka,d’an dana haifa maka aka danne mun aka nunama bani ce mahaifiyarsa ba,aka dannema soyayyata acikin zuciyanka lokacinda akasha Na mutu aka gogema tunanina acikin kwakwalwanka,Na yafema duk abinda ka aikata agareni dan bayin kanka bane!,Zee keda Allah shine kad’ai zai iya mana sakayyar abinda kika aikata garemu ,barin mahaifinki da kika fi muzgunawa kika maidasa tamkar gawa 😭Zee kaichonki Allah zai sakamun dukkanin abubuwan dakika aikata a gareni,kika gusar da kwakwalwata!,kikasa na manta koni wacece .Allah ya isana “

Humy ta ida maganar cikeda kuka jikinta sai rawa yakeyi da sauri ta kallo Yaah Bàshir wanda shima kukan yake tayata ,tamik’e da saurinta tazo daf dashi ta rik’e hannunsa sannan tana kuka tace :”yaah Bàshir dan Allah ka taimaka kakaini wajen Yaah UMAR yanzun plsss plsss “!

Ta ida maganar tana jan majina tana magiyan yakaita wajen Umar,kama hannunta barrister yayi sannan yajata sukaje harwajen motarsa ya shigar da ita sannan shima yashiga ya tada motar,sunyi tafiya mai d’an nisa sannan ya waigo ya kalla Humy da har idanuwanta sungama shid’ewa tsaban kuka,girgiza kai yayi dan he knows how she is feeling ryt now ,yace mata:”Humairah! Bazan kaiki wajen Umar ba a yanzun !”

Saurin kallan barrister tayi dan bata gane mai yake nufi da bazai kaita wajen Umar yanzun ba!toh sai yaushe zai kaita?bayan shekaru d’aya da Rabi basu tare an rabasu sannan kuma yanzun da kowannen su ke buk’atan junansu sai yace mata bazai kaita wajensa ba toh wajen wa zai kaita Zee ko wa? Katseta yayi da cewa:”zan kaiki gidana a kadunan kihuta sannan zan kirasu mama da dady duk abinda sukeyi su ajiye suzo kaduna a gbe dan akwai gagaruman nasara,anan ne zan gabatar masu dake sannan zamu tona asirin Zee kin fahimta?”

Sai anan Humy ta fuskancin abinda yake nufi dan haka ta girgiza masa kai cikeda gamsuwa,amman harga Allah taso ayau d’innan ba gbe ba tajita a kusada Yaah UMAR d’inta amman ba komai yau da gben duk d’ayane!

3:30Pm
Su Humairah suka iso kaduna,straight gidansa ya isa,bayan yayi parking ya fito ya bud’ema Humy murfin motar itama tasany’a k’afafunwanta ta fito tana k’arema gidan kallo.Sosai Amaryar yaah Bàshir ta tarbi Humairah ta shiga tattalin Humairah kaman zata maidata ciki,itadai Humairah saidai tayi murmushi kawai tace mata tagde dan ita yanzun wallahi tama kanta alk’awari ta daina yarda da mutane 100% inba iyayenta ba amman a part frm them tanaji koda en uwanta wanda suka fito ciki d’aya bazata iya basu 100% trust ba dan Zee ta koyamata hankali,yanzun ita da mutane saidai Hy hy babu wani wanda zai sake sanin sirrinta wlh koda ko ace abin zai iya kasheta ta gwammace ta rik’e kayanta! Dan ita wallahi ta tsorata sosai da kaidin mutanen duniya! Zee ta gama koyamata karatun,kuma ya isheta haka,tagane komai da komai!

*********************************

Umar kam Alluran baccin daaka masa maii k’arfi ce shiyasa har sai washegari alluran ta sakesa,yana bud’e idanuwansa yaga Bàshir zaune a gefensa da alamu jiransa yake ya farka,da sauri Umar ya zuge canula d’in hannunsa yafin cike ba tareda ya damu da d’inbin jinin dake anbaliyan fita a hannun nasa ba burinsa kawai yagansa a gidansa wlh yauyau dinnan saiya kafa tahiri a rayuwar Zainab!

STORY CONTINUES BELOW
Saurin rik’esa Yaah Bàshir yayi sannan yace :”haba Yaah UMAR bakaga yanda hannunka ke fidda jini bane “

Dafe kansa Umar yayi dan wani kalan jiri-jiri ke d’ibansa sannan ya kalla yaah bashir yace:”kace Humairah ta rasu?banga anfanin cigaba da rayuwata a duniya ba tareda itaba,abubuwa dayawa sun faru wanda banda masaniya akai kawai rana d’aya na bud’e idanuwana wai ni umar na aura Zee harda rabon d’a agaremu,tayaya hakan ya faru bashir?ya akayi banda masaniya?uhumm tell me?”

Umar ya ida maganar yana sheshshek’an kuka,babu wani mahaluki da zai ga umar a wannan yanayin bai tausaya masa ba,shima barrister bashir share hawayensa yayi yana mai tsananin tausayawa Umar,dan baa k’arya umar has undergo alot! .Da kyar Barrister bashir ya rik’e hannun Umar yakaisa wajen wata nurse ta gyaramai hannun nasa dake fidda jini,sannan barrister ya biya kud’i asibitin,suka fito suka shiga mota.Barrister bashir yaja motar suka bar haraban asibitin.

Tafiyan kuramai sukeyi bamai cema wani uffan,Umar yana chan duniyan tunanin in dagaske humairah ta rasu dan shi gangan jikinsa tak’i amince masa da cewa Humairah ta rasu,toh in ta rasun da gaske shi mai anfanin rayuwar tasa? Barrister Bàshir kuma yana chan duniyan tunanin irin tarkon daya had’ama Zee dan ayau zai fallasa asirinta,burinsa dai kawai su isa gidan Umar!

Sosai barrister ya k’ara gudun motarsa,har suka isa malali sukai horn a bakin gate d’in gidan Umar mai gadi ya bud’e masu,tun a haraban parking lots barrister Bàshir yaga motocinsu hakan ya tabbatar masa da cewa sun iso kenan,wani kalan shu’umin murmushi bashir ya saki sannan ya kashe motar ya fito ya bud’e ma Umar k’ofa,sannan ya taimaka masa yafito,yana rik’e da hannun Umar d’in wanda shi sam baima lura da motocin dake pake a haraban wajen ba,yana chan duniyan tunanin abubuwan wai daaka ce masa ya aikata ma Humy idanuwan sa sai zubda kwalla suke,any’a Humy zata iya yafe masa kuwa?”

Mutanen da yagani zazzaune a gujeran falansa ne ya sashi dawowa duniyan tunanin daya fad’a,hawaye taf fuskansa,da sauri momy ta mik’e tazo gaban sa tace :”Faruq ,UMAR mai ya sameka kuka kiramu kiran gaggawa jia?eh maisa kake kuka bakada lfy ne?ina matar taka Zee?”

Dum k’irjin Umar yashiga bugawa.Wai dagaske dama ya aura Zee?innalillahi wa’inna ilaihir rajiun ya ruk’a nanatawa har sau ba adadi,en falan ya shiga k’arema kallo,Momy dady,Yaah fareed,yaah khalil,mama,baba,da kuma yaah huzaifah.”babu Humynsa aciki hakan na nufin cewa dagaske Humairan sa ta rasu?”

Saurin dafe momy UMAR yayi dan k’afafuwansa suna barazanar k’in d’aukansa , “yi a hankali faruk muje ka zauna ” da kyar da taimakon momy da barrister bashir suka zaunarda Umar a kusada dady wanda duk hankalinsa a tashe ganin halinda Umar d’in yake ciki,mama kam ai tuni take zubda hawaye dan wlh ‘yarta ta cucesu ta gama dasu ,wl
h da zataga Zee anan gurin da saita karya mata k’afafu!

Barrister Bàshir ne yayi gyaran murya hakan yasa kowa ya maida hankalinsa wajensa dan dama shi ya masu kiran gaggawan:

“Nasan kowannenku dake zaune anan zuciyoyinku na tambayansa dalilin kiran danayi maku,kuma nace mu had’u a gidan Umar ko?murmushin tak’aici Barrister yayi sannan ya cigaba da cewa “a yanzun zan gaya maku dalilin ta ruwanmu anan d’in amman ku bani minti d’aya ina zuwa “!
Mik’ewa yaah Bàshir yayi idanuwan kowa akansa shidai Umar yakasa koda motsi bare yaga mai Bàshir d’in ke shirin aikatawa! Kowa da ido yabi bashir d’in har yagama hawa matakalen benen dazai sada shi da d’akunan gidan!

Atare kaman had’in baki suka sauke dogon lumfashi kowa da abinda yake sak’awa a zuciyansa.suka zauna jugum suna jiran fitowan bashir d’in.
Koda ya shugo cikin d’akin yaga ko ina a hargitse girgiza kai kurum yayi dan in hauka ma tayi toh k’aramin hauka ta fara babban hauka sai in asirinta ya gama tonuwa sannan zata fara haukan da hujja “
Barrister bashir ya raya hakan acikin zuciyansa!
Chan ya hangota k’udun dune waje d’aya a k’arshen bango,a kwana d’aya duk ta fige tayi duhu inka kalleta sau d’aya bazaka sake marmarin kallanta ba,girgiza kai kurum Barrister yayi dan shi wlh baya koda d’igon tausayinta!

STORY CONTINUES BELOW
Daf da ita ya matso yana k’aremata kallo ita kuwa Zee sai sheshshek’an kuka takeyi daka kalla idanuwanta zasu tabbatar maka da cewa ta kwana ta yini kuka,lumfashi barrister ya sauke sannan yace mata:”fito muje “

Sai da ya maimaita mata fito muje har sau uku sannan ta d’agoda raunannun idanuwanta ta kallesa ba tareda tace masa uffan ba ta cire idanuwanta akansa ta maida kallonta wajen k’ofan d’akin tagansa a bud’e mik’ewa tayi zumbur ta soma takawa a hankali dan fita a d’akin,shi kuma barrister ya girgiza kai yabita a baya,harsuka soma sauka daga stairs din,kowa idanuwansa ya mayar wajen Zee ,sanda mama taga yanda Zee d’in takoma saidata tsorata ainun (uwa dai uwace wlh) amman data tuno shaid’anci irin na ‘yar tata saita Ta6e baki tace “kad’an ma kika fara gani “

Sosai Zee tayi mamakin ganin iyayenta da iyayen humy a gidan wai mai ke shirin faruwa da itane? Shi ta ruk’a tambayan zuciyanta amman takasa samun amsan.kama hannunta taga yaah bashir yayi ya zaunar da ita a k’asan tiles d’in falan sannan shima ya koma yazauna a mazauninsa kusada k’ofan fita na falan,sannan ya fuskanci kowa dake falan ya soma gyara murya,kowa dai babu wanda yake kallo face Zee duk sunga tafita a hayyacinta tayi wani kala kaman ba Zainab d’inan maison kwalisa,ita dai Zee takasa koda d’agowa ta kalla kowa a falan dan tasoma ji ajikinta tamkar asirinta ne ya tonu .Umar kuwa ji yake kaman ya mik’e ya ba66alla ‘yar banza amman ganin idanun iyayenta yasa shi kyaleta amman zuciyansa sai tafarfasa yake,Baba kuwa kallan Zee yakeyi tamkar yau yafara ganinta yashiga tunanuka akanta har babu adadi!

Barrister bashir yace:”dalilin kiranku nan wajen yaku dangina ba’akan komai bane ba kuma akan kowa bane face kan Zee!”

Saurin kallansa Zee tayi taga bilhakki da gaskia yake kiran dominta yayi sa,”badai yaah bashir ya mata kamun kura bane?badai ta sanadiyar d’an uwanta asirinta zai tonuba?”

Wani kalan bak’in cikine ya turnuk’e wuyan Zee jikinta duk ya saki ta kafe yayanta da gunburarrun idanuwanta ,tana mai wani kalan kallo irin kagama dani d’innan.Zee tanaji tana kallo yayanta ya tona duk wani sauki burutsun data aikata babu wani abu tak da barrister ya 6oye masu har karya asirinda malam boka yayi a gabansa da komai da komai saida  yagaya saidai ya 6oye masu maganan Humy bai fad’i nata part d’inba,hakan ne yad’an sa Zee jin relieve dan ta san babu wanda zai raga mata anan kowa zaii fanshe haushinsa a kanta k’arshe su koreta ita kuma tad’au alwashin tana barin gidanan zaria zata wuce ayau d’inan zata Kashe Humy!

Shikuma malam boka saitasa an kullemata shi sai ya biya ta da ransa,wannan alk’awarine!
Babu abinda kakeji acikin d’akin nan inbanda sheshshek’an kuka yau harta dady saida ya koka yace:”shin Zee mai narageki dashi kekuwa a duniya mai muka aikata maki da kika d’au wannan matakin akanmu?ban ta6a nuna maki banbaci tsakaninki da ‘yata ba duk wani abu da uba kema ‘yarsa tare nake had’awa na muku keda Humy!shin da wannan kaidin dama zaki biyamu?”

Daga haka dady ya kasa k’arasa maganarsa kuka taci karfinsa,momy kuwa sai taji yau mutuwan Humy ta dawo mata fil amman sai take godema Allah daya d’auki ran ‘yar tata dan karta yi witnessing wannan abun,zee da ‘yarta tagama yarda da ita yau itace silan mutuwarta da rabata da farinciki ta datse soyayyan miji da mata,Momy ta shiga girgiza kaii tana fad’i a fili:”Zee bazan ta6a yafe maki ba wlh bazan ta6a yafe maki ba!Allah ya isa tsakaninmu dake Allah kuma zai sakama Umar da Humy irin abubuwan da kika aikata a garesu,bare kuma mahaifinki dakika nak’asashi nanma wlh Allah bazai barki haka ba zaki fara girban sakamakonki tun anan duniya!”

Momy ma kuka yaci k’arfinta takasa cigaba da maganarta!

Mama kuwa kasa cewa tak tayi dan wlh inta bud’e bakinta tayi magana toh alkairi bazai ta6a fitowa a bakin nata akan Zee ba shiyasa tayi shuru ta zubama Zeen idanu wacce notukan kanta sunrigada sun gama kwancewa jikinta ya gama saki hawaye kawai ke anba liya asamun kuncinta,bata ta6a zaton cewa asirinta na tonuwa har haka ba,kwasam suka mata kamun kura,ta sanadin d’an uwanta yau asirinta yagama tonuwa,Murmushin dayafi kuka ciwo Zee tayi sannan ta d’ago tana bin kowa a falan da kallo bayan tagama kallesu kaf kowa babu abinda take hangowa a kwayan idanuwansa face tsananin tsananta musamman mama,kuma sakin wani murmushin da yafi ciwo zafi Zeen tayi sannan cikin daskakkiyar muryanta ta soma cewa:”hummm dama ance rana dubu ta 6arawo rana d’aya tak ta maikaya “
Ta ida maganar tana mai nuni da d’an yatsanta alaman sign d’in one,ta kuma murmusawa sannan tace:”ban ta6a sanin cewa asirina yana tunuwa har hakaba danko kamun kura akamun,amman wlh dana san cewa asirina yana tonuwa kuma ta sanadiyyar d’an uwana! ,ta nuna bashir da yatsa sannan ta cigaba da cewa,”Toh dako tabbas saina kasheshi! Yes wlh dana san yana bin lamurana da wlh saina aikasa lahira!dan ni haka Allah ya halicceni tun ina yariny’ata banda imani kuma banda tausayi bansan mai imani da tausayi suke nufi baa! Nida kaina Na rantse maku ina tsoron kaina! Dan nasan banida imani lokacinda ake raba imani bana wajen! A rayuwata tunda nake banta6a koda ace na minti d’aya tak na k’aunaci Humy ba wallahi ban ta6a son humairah ba babu abinda nake ma humairah face hassada da tsananin k’iyayya I hate her with all my heart janta ajikin dana ruk’ayi kuma nake nunamata fake soyayya badan komai bane saidan insama sirrikanta hakan yasani danne zuciyata nake nuna ina tareda ita ina kuma sonta amman wlh a duk lokacinda Na bud’e idanuwata Na d’aurasu akan Humy ji nakeyi….1

STORY CONTINUES BELOW
Zee ta d’an tsaya da maganarta ta datse hak’oranta sannan ta furzarta huci mai zafi  tana demostrating hannayenta irin yanda kaji ke dunk’ula k’afafunsu in an yanka su alamun son shak’e mutum sanan ta cigaba da cewa:”kaman Na kasheta na huta natsani yanda kowa ke nuna tsananin soayyarsa akan Humy ni kuma kullum a tamun fad’a baga iyayena ba kuma baga iyayenta ba,baa kawayenmu ba kowa Humy komai Humy,shiyasa na d’au alwashin tawar watsa rayuwarta,bazan ta6a nadaman abinda Na aikata ba kuma bazan ta6a naiman yafiyan abinda Na aikata ba!”

Ta ida maganar tana mai gyara gashin kanta dayad’an ta6o bakinta!

Kowa salati kawai yake saki a falan inka cire Umar dako kallan inda Zeen take baiyi ba sai kuma Bashir dake tsananin mmakin kafiya da bak’in hali irin na Zee dukda asirinta daya tonu amman har take shaidawa kowa batayi ba kuma zatayi nadama ba,kuma bazata bid’a yafiya ba wannan wacce kalan yariny’a ce wai?is time for him to bring Humy cikin falan dan Zee ta gane cewa batayi nasara a komai ba!mik’ewa yayi har zai fita kunnuwansa ya jiyo mai abinda mama ta fa
d’a saurin waigowa yayi dan tabbatar da abinda kunnuwansa suka jiye mai:

“Allah ya tsine maki Zainab! ,Allah ya d’ebe duk wani albarka a rayuwarki!Allah nake rok’o yanda kika samu kuka da hawayenmu kema Allah ya hassasa damuwa da bak’in ciki a rayuwarki,bazan ta6a yafe maki ba Zee har abada “!

Daga haka mama ta kuma fashewa da kuka momy kam daskarewa tayi dan batyi zaton cewa mama zata iya tsinema Zee ba bakin uwa kaman rezane. Zee ta kuma sakin Murmushi sannan tace:”mama koke baki bud’e baki kin tsinemun ba!nida kaina zan rok’eki ki tsine mun dan ban buk’atan dawowa saliha nafison na cigaba da zama mara imani mara tausayi!”

Kowa ya mayarda hankalinsa kan Zee dan kam wannan zainab d’in ta wuce tunaninsu!
Sam barrister bashir baiji dad’in bakin da mamansu tama Zee ba amman Zee din ta chanchanci fin haka ma! Saurin fita yayi bai jima ba ya shugo cikin falan hannunsa rik’eda Humy!

A tare suka mik’e zumbur barinma yaaah umar,ganin yanda kowa ya zabura suna kallan gu d’aya yasa Zee saurin kallan inda suke ganin a take kaman had’in baki harda Zee din suka furta:”Humairah!”

Murmushi humairah tayi zatayi magana kawai sukaga Umar ya yanke jiki ya fad’i.Ai a 360 Humy ta k’araso wajen yaah Umar bama ta lura da bangaje Zee da tayi ba itadai burinta kawai taganta wajen yaah Umar!

Zee kuma kaman mutum mutumi ta dawo tsaban mamaki wannan kamai bashir ya gama wargaza mata komai amman kam bazata ta6a yafema bashir ba wlh ya mugun shammaceta!

Ruwa mama ta yayyafama Umar baifi 3mins ba ya farfad’o yana tari ganin tabbas Humynsa ce zaune kusada shi bawai imaginations bane kawai ya rungumeta a lokaci d’aya suka fashe da kuka “Humy dama baki rasuba?dama kina raye?”

Shine tambayoyin da kowa keyi acikin falan barrister ne yayi gyaran murya sannan ya kuma basu lbrn duk abinda yafaru akan Humy farkon ganinta dayayi da wata tsohuwa har sunanta daaka chanza infact komai dai da barrister yasani aakn Humyn saida ya fad’a!

Kai tsayawa fad’in maku tsananin tashin hankalinda wa’inan bayin Allan sukai 6ata lokacine sunma kasa sanin a wani mizanin marasa imani ya kamata su sa Zee d’in dan wannan tafi shaid’an ma!

Maganan Umar ne tadawo dasu duniyan da suka fad’a;

“Dady dan Allah karka bani wa’inan dukiyoyin kabarsu awajenka dan allah kadai ga bada hayyacina namaka wannan d’any’an rashin mutuncinba plss ku yafemun “

Dady ya nisasannan yace:

“Mun yafema Umar saidai gaskia bazan hak’ura akan k’in baka dukiyoyinka ba ,gwara a raba dukiya abaka naka,ita kuma Zee dukiyan da take tason araba ta kar6a tayi fachaka dashi ta maida Umar matsiyaci ki wulak’anta sa kaman yanda kikaci buri,toh hakan kuma baiyu ba saiki d’au dangana “!

Dady ya ida maganar yana mai watsama Zee harara dan jiyake kaman ya d’au bindiga ya harbe shaid’aniya!

Ita kuma Zee mamaki,tak’aici duk bayyane a fuskanta wai ace yau asirinta ya tonu kowa sai fad’an mata albarkatun bakisan yake ,uwar kuwa ta tsine mata,bata ta6a tsammanin cewa asirinta na tonuwa ba kawai kwasam suka mata kamun kura lokaci d’aya kawai yayanta ya shugo da Humairah tagani duk irin taka tsantsan data ruk’ayi dan ganin Bawanda ya gane cewa humairan Na raye ashe bashir ya rigada ya gane kawai kallan mahaukaciya da na kusa tona asirinki ya ruk’a mata kenan?kowa yanzun ya gane cewa humairah bata mutu ba?itace ta wargaza rayuwan humairan?gashi Umar kansa ya dawo hayyacinsa duk irin tanadin datayi nayin fachaka da dukiyansa yanzun ya tashi a banza kenan?muryan mamane ya katseta daga tunaninta!

“Allah nagodema Alhamdulillah Humairah ta tana raye Allah yayi maki albarkaHumairah Allah ya cigaba da kareki daga sharrin mahassada barka!barka my humairah Allah ya k’ara maki tsawon rai mahassada saidai su mutu kiga gawansu badai ke suga naki ba “!

Mama ta ida maganar tana watsama Zee data kafeta da idanuwanta hararan tsana!

Haka duniya zata juyamata baya yau?haka dama asirinta zai tonu?yaya zatayi yanzun?kowa yadawo cikin hayyacinsa boka yaci amanarta ita tamafi ganin laifin boka dan daace bai kwance asirin ba da duk hakan bazai faruba!
Haka Zeee ta ruk’a rayawa a zuciyanta duk jikinta yayi sany’i ainun!

Baba taji yana cewa:”humairah Allah yayi maki albarka nayi matuk’ar farin cikin ganinki a raye kuma nayi alkawarin yin azumi guda bakwai dan nuna godiayata wajen ubangiji,ke kuma Zee Allah wadai da halinki bazan maki baki ba dan kar gararin rayuwa su taru sumaki yawa mu mun gada imani dan haka bakin mahaifiyarki ya gama isanki basai na k’aramaki nawa ba,Zainab ni ban gama warkewa daga cutan dana tashi ba ashe wai harni zakima asiri ki kuma nak’asani?”

Baba ya ida maganar yana Kuka sosai mai tsuma zuciyan mai sauraro!

Awanan ga6an zuciyan zee da kwakwalwanta sungaza mata komai runtsa idanuwanta Zee tayi ta danne kunnuwanta da tafin hannayenta biyu babu abinda take nunanowa sai yanda d’an uwanta yaruk’a fayyace ma kowa abubuwan data aikata,girgiza kaii tashigayi tana ihu tana fad’in :”no !noo noo”

Kowa yamaida hankalinsa gareta ganin yanda Zee keyi maganganun iyayenta yarik’a kururuwa a kunnuwanta:”Zee Allah ya tsine maki,” sau bibbiyu duk wani maganganun da akamata yake ringingin a kwakwalwanta,durkushewa tayi a k’asa tana mai wani irin tari wanda babu inda sassan jikinta basu amsa wannan tarin tun tanayi tana sark’ewa hardai tafara tarin amai hancinta yafara zubda jini bakinta ma haka!

Tsananin firgici tsoro Humy ta tsinta kanta aciki tausayin Zee taji nason mamaya zuciyanta hawayene ya shiga anbaliyan fitowa a fuskan Humy ganin babu wani mahalukin dayayi yunk’urin taimakama Zeen!
“Zainab ni ban gama warkewa daga cutan dana tashi ba ashe wai harni zakima asiri ki kuma nak’asani?”
Maganan baba ya kuma kururuwa a kunnuwanta jin maganganun baban take yana amsakowa sau bibbiyu a kwakwalwanta “Allah tsine maki Zee”
Maganan mama ma ya kuma dakin kunnuwanta
“Zee Allah wadai da halinki bazan maki baki ba dan kar gararin rayuwa su taru sumaki yawa mu mun gada imani dan haka bakin mahaifiyarki ya gama isanki basai na k’aramaki nawa ba!”

Wannan maganan dayayi kururuwa acikin kwakwalwanta yayi daidai da tsayawan lumfashinta chak zuciyanta taji yana barazanar harbawa “Allah d’ibe dukkanin Albarka a rayuwarki Zee “
Wannan maganan na mama daya kuma gifto mata yayi daidai da buguwan zuciyanta (Zee) warwas Zee ta fad’a a k’asa a sittin Humairah tayo kanta tana kwala kiran sunan ta tana kuka “Zainab……………,😭😭✍🏻

Chak kuma Humairah taja ta tsaya tana mai sauraron gargad’in da zuciyanta ke mata,hakan yasa kowa zuba mata idanuwa suna jiran ganin abinda zata aikata,dan sam sam bai kamata ace Humy ta tausayama Zee balle harta taimaka mata,momy kam ji takeyi kaman ta kama Humy tamata tsinan niyar duka kozata huce dan kam inhar wallahi Humy ta taimaka ma Zee toh ko babu shakka akan Humyn zata sauke duk wani kayan tak’aicin da Zee tasata aciki.+

“Umm-umm Humairah akul d’inki karkiyi yunk’urin taimaka ma wanda ta tsaneki ,shin kin manta wai abubuwan da Zee ta aikata agrekine?bata chanchanci ki yafe mata ko kiji tausayinta ba,kar raunin zuciyanki ya karyaki abanza ki tausaya wanda ta zalunceki da zalunta mutane bila adadin,shin kin manta 6atar maki da hankali da tayi?ta dawo dake tamkar mahaukaciya amman ke ba haukaba?ta rabaki da d’anki?ta datse soyyarki keda mijinki?tasa mijinki ya ruk’a hantaranki,yayi maki koran wulak’anci,shin wai duk kin manta da hakan ne komai?har kike yunk’urin taimaka ma wacce da bakinta kunnuwanki suka jiyo maki cewa bata sonki bata ta6a k’aunatarki ba!toh ke mutum 6aro-6aro ya nuna shi mak’iyinkine ke mai naki na sansa da son taimakonsa da kuma tausayinsa?ke wai adole mai zuciyan kirki ko?ke nan wai mai mayarda sharri da alkairi ko?toh kul d’inki karki fara kuma karki kuma tunanin soma taimakon wannan azzaluman wanda ko Allah bazai barta haka ba!
Iyayenta ma sun mata baki saikece ta Allah kenan zaki taimaka mata ko? Upon all the evil deeds data maki?shin kinmanta a baya kind’au alk’awarin tawarwatsa farinciki a rayuwar Umar da Zee kodan kin yafema Umar a yanzun itama Zeen taci albarkacin Umar d’in Kin yafe mata?toh wlh ko kin yafe mata gangan jikinki bazata ta6a yafe ma Zee ba,kuma bazata ta6a barinki cikin sukuni ba muddin kika taimaketa ko kika tausaya mata ,kina tunanin wai mutuwa tayi ko?toh ai in harma mutuwan tayi ayanzun bak’in ciki ya kamata kiyi ba tausayi ba! dan mutuwarta ayanzun babban jin dad’ine a gareta ,dan kuwa bata rayu taga yanda duniya zata ci ubanta ba,yanda duniya zata maidata abar tausayi,kul kul humairah “

Zuciyoyinta duka suka shiga mata gargad’i.

Saurin maida hannayenta baya tayi daga yunk’urin taimakon Zeen wacce bata koda motsi ,kaman mai shirin fad’uwa k’asa humairah taja da baya,sai anan momy taja lumfashi ,mama kuwa wani dad’ine ya maimayeta dan Humyn bata taimaka ma Zeen ba!

Umar kuwa saurin zuwa yayi wajen Humairah ya rungumeta,dan al’amarin nason sata cikin Trauma!

Janta Umar yayi suka bar falan gaba d’aya,dady ma yafita nan dai kowa har yaah huzaifah suka tsallaka sukabar Zee kwance ak’asa kaman matatta!

Nisawa sosaii Barrter Bàshir yayi ganin kowa ya tsallaka Zeen batareda kowa yayi yunk’urin koda ta6ata ba dan ganin halinda take ciki amace ko araye!

Runtsa idanuwansa Barrister yayi koba komai k’anwarsa ce,kuma ai ita tajama kanta da bata aikata hakan ba da babu wani mai gudun ta!

D’aukanta chak barrister bashir yayi yanayin yanda yaji jikinta asake sai yake ganin kamar batada rai,sakata yayi bayan motarsa sannan ya shugo ya tada motar yakama hany’ar asibiti dan inhar mutuwarma tayi gwara yakaita asibitin ya biyasu akai Zeen mutuary (mutuware) dan ya tabbata babu wani danginsu dazai tsaya a sallaci gawan nata bare su rakata makwancinta,kuma babua wani wanda zasu kira su shaidama mutuwan nata bare har amasu ta’aziya ko azo a sallaci gawar nata! Mutuary d’inde shiyafi dacewa yakai gawan nata,shine kawai iya gatan dazai iya mata!

Koda suka isa asibitin saurin amsanta likitoci sukai suka kaita Emergency room dan sun shaida cewa ba mutuwa Zeen tayi ba,hakan yasa suka garzaya da ita Emergency dan ceton rayuwarta!.Barrister kuwa tunda akace tanada rai ya shiga tunanin kodai yatafi yabartane kawai?”

STORY CONTINUES BELOW

Fitowan likitocin ne bayan sun d’ebi awanni akan Zeen kafin suka iya ceto ranta da gano abinda ya sany’ata cikin halin nan,dr Nura ya kalla barrister bashir yace masa ya biyosa offishinsa,kaman rak’umi da akala haka Bashir yabi bayan dr har cikin office dinsa!

**************************************

Durk’usawa yayi a gabanta had’ida kamo hannunta ya had’e da nasa waje d’aya sannan ya kalleta ita kuma ta waiga tana kallan gefe d’aya tana shany’e hawayenta !

Cikin muryan tausayi yace ;

“Humynah nasan I don’t deserved to be forgiven ko?yau bazaki iya kallan yaah UMAR d’inki bako ?yaci amanarki ko?pls sweeetheart ki hukuntani da duk wani abu dakikaga ya kamaci yayi punishing d’ina,I don’t deserve ur forgiveness ki hukuntani ko zuciyata zata iya samun sukuni my Humy pls ki hukuntani nace punish me!”

Umar ya ida maganar yana mai tsananin kuka,had’ida kwantarda kansa akan ciny’ar Humairan!

Humairah kuwa wani kalan tausayin yayan nata kuma mijinta uban d’anta taji ya mamaye dukkanin ilahirin ga6o6in jikinta,a hankali tasoma mik’a hannunta harta sauke akan gashin kam Umar sannan ta had’iye kukan dake son fin k’arfinta sannan tace:

“Wlh na dad’e da yafe maka mijina,I have forgiven u since,nasan bayin kanka bane u were coerced (yin abu dole) ,Humairah ta yafe maka kuma bata rage sonka ba kodako da kwayar zarra,sai madai linkuwan soyayyarka acikin Zuciyata!i love u so very much Yaah umar “!

Daga haka itama humairah kuka yaci k’arfinta tare suka runguma juna itada yaah UMAR sun d’auki tsawon lokaci a haka kafun daga bisani suka saki juna Yaah umar ya kalleta sannan yace:”I hope wat Zee did to u zai saki shiga taitayinki,not everyone who laughs at u is ur friend okey? Ya k’arasa maganar yana d’agata mata girarsama cikin wasa daria sosai ya bata hakan yasata d’arawa sannan ta shiga girgiza kai takun tace:”okey abban Abul -islam “!

Murmushi sosai Umar yayi dan bayan Bàshir yamasu bayanin cewa yaron Zee ba d’anta bane ba ita ta haifesaba Humairah itane ta haifi d’an yasashi jin wani kalan relieves dan koba komai bai had’a zuri’a da makiraba! Gangan jikinsa kawai ta mora.kuma runguma Humairah yayi sannan ya rad’amata a kunne “I damn love u much more Umman Abul-islam “

Daga haka kuma suka mik’e cikeda soyayar juna suka shirya suka fito dan zuwa gidan bashir su dady na jiransu a chan dan Bàshir yace Abul -islam Na gidansa yasa abokinsa da yabaiwa ajiyan abul d’in kaisa gidansa.koda suka isa kowa cikin farin cikin ganin yaron suke dan yarone mai matuk’ar shiga rai barinma Humairah kaman tasa ruwa a k’asa tashanye haka takeji dan yau gata ga d’anta huhuuu waiyooo dadi,hakadai wannan family d’in suka ruk’a taya juna farin ciki da jajantawa juna abubuwan dasukai under going abaya.Ikram kuwa sai nannan take da dangin mijinta tanajin tsananin soyayyarsu na shiganta.

**************************************

Dr nura ya nisa sannan ya kalla Bàshir yace:”are u a family or guidance?”

“Yes fam “

Girgiza kai Dr yayi sannan yace:”am sorry to say this ,k’anwarka tasama mutuwan 6arin jiki she is paralyzed zuciyanta daya bugane ya hassasa mutuwan 6arin jikinta sannan kuma zuciyanta takamu Da ciwon zuciya (heart diseases ) wanda is hard for her to survive for a long period of time,dan zuciyanta ba k’aramin bugawa tayi ba kwananta nanan kusane kawai shiyasa bata mutu ba but if ace u haven’t rush her hear we couldn’t have saved her life ,sannan kuma sakamako yanuna cewa takamu da tarin sidaa (tuberculosis)but is a minor one,we can easily treat it,and jininta yayi mugun hawa,kai yariny’an dai wlh she is in a severe pain,yanzun dai mujira farkawanta kawai “

“Innalillahi wa’inna ilaihir rajiun “kawai barrister ke nanatawa duk zufa tagama wanke jikinsa,ace waiduk wannan cuta ajikin mutum d’aya,mutuwan 6arin jiki,ciwon zuciya,hawan jini,tuberculosis! Duka akan mutum d’aya anbarka da ordinary ciwo d’aya yaka k’arema bare 2,3,har 4zuwa biyar?wannan wani kalan musiba da bala’i ne ya tabbata wlh Allah ne yasaukar ma Zee wannan ciwon parat d’aya dan yanuna ihsani ga mutanen baya!

STORY CONTINUES BELOW

Kuka sosai barrister yayi daga karshe ya bar asibitin zuciyansa cikeda tausayin Zee !

*********************************

A Daren ranar Zee ta farka amman saitaji ta kasa yunk’urin koda d’aga hannunta tayi tayi amman takasa tanason juya wuyanta ma dan ganin inda takema hakan ya faskara kodai mutuwa tayi?shine tambayar data shiga yima zuciyanta!

“Hey kiyi a hankali kinji bakisan u are paralyzed bane?u can harm yourself by coercing hard faa “

Nurse d’in da shugowanta kenan duba Zeen ta ida maganar tata!

Kaman saukan aradu Zee taji wannan kalman “paralyzed “

Could this mean cewa she is paralyzed?inallilahi wa’inna ilaihir rajiun wannan wani kalan rayuwace ta kuma tsinci kanta aciki??mai yasa duniya keson juya mata bayaa?yau ace itace kwance wai da mutuwan 6arin jiki?wanda adaa take kyamatan mahaifinta sabida hakan har take kiransa nak’asaishe wai yau itace exact ciwon mahaifinta ya koma kanta shikenan itakam tata tak’are wallahi duniya tajuya mata bayaa!

Wani kalan tarine wanda har hanjin cikinta saida suka ruk’a kad’awa ya turnuk’e Zee a lokaci d’aya tamkar zata amayoda komai na cikinta sosai wannan tarin ya turnuk’eta harta shiga fiddo da jini both baki da hanci jin k’arnin jini a hancinta ya tabbatar mata da cewa tarin jini takeyi,nurse kuwa
rud’ewa tayi da gudu ta fita kirawo likita,Zee kuwa a wannan lokacin ta rigada tagama galabaita,hawaye kawai idanuwanta ke fitarwa dan ta sadak’ar nata kuma yazo k’arshe tafara girban abinda ta shuka soranta komawa ga mahaliccinta kuma dan d’and’ana nasa hisabin da zai mata kuma! Dan tasan tabbas sai Allah yasakama su Humairah!

Da sauri likita yashugo ya shiga bata taimakon gaggawa ita kuwa Zee tarigada tasan mutuwa zatayi dan batada saurin kwana!

**********************************

Koda barrister Bàshir yadawo gida ya sanarwa kowa abinda likita yace dangane da Zeen babu wanda ya tausaya mata Umar kamma rok’on Allah yayi kan Zeen ta mutu ko zaa rage mugun iri a duniya!

Humy kuwa shuru tayi tana ayyana zancen barrister acikin zuciyanta,batasan ko tausayin Zee takeyi baa ko akasin hakan,kawaidai ita tasan zuciyanta yak’i natsuwa da halinda akace Zee Na ciki,alk’awari tama kanta gbe in shaAllah zataje ta dubo Zeen.Dan ya kamata ace at least wani yana tsaye akanta a irin wannan yanayin datake ciki dukda she deserved to be ignored amman dai hausawa nacewa naka dai naka ne!

****************************

Satan jiki Humy tayi taje asibitin dan ankira Umar kiran gaggawa a office ,hakan yasata samun chance d’n zuwa dubo Zee itada d’anta sukaje.

Ganin Zee awannan yanayin ba k’aramin tsorata Humy yayi ba ta mugun ramewa tayi haske fayau tamkar wacce ake shany’ema jini Gawani wari dataji Zee nayi da alamu kashi tayi baa wankeba ,kuka wiiwiiwii Humy tashigayi Abul kuwa ihu ya ruk’a saki dayaci karo da fuskan Zee !

Zee kuwa kafe Humy da idanuwanta tayi tana tunanin abinda yakawota wajenta upon all abinda ta aikata mata kodai kasheta tazo yi?amman ganin Humy Na kuka yasa Zee karaya taji tasoma nadaman abinda ta aikatama Humyn,gashi yau kowa kyamatarta keyi daidai da nurse dake kulada ita yau saidata mata tatas ganin kashin datayi akwance hakan Nurse din ta tsallaketa tace bazata wanke mata ba aiba boyi boyinta bace ita!

Ashe haka mahaifinta keji shima lokacinda bai iya aikatama kansa komai?yau gashi itama kwance bata iya koda motsa yatsan hannayenta,kuka sosai zee keyi acikin zuciyanta sosai nadaman abinda ta aikata yashiga jikinta sai ayanzun take tambayan kanta dalilin dayasa ta aikata dukkanin abunuwan data aikata yanzun mainene ribar dataci aciki?wlh babu sam babu ribar dataci inbanda girbe ma kanta babban kaidi!

After a week a gurguje plsss

Tundaga wannan ranar Humy ke satan k’afa tazo asibiti ba tareda kowa yasan tanayin hakan ba!

Itace wanke kashin Zee intayi a gado chanzama Zee kaya wani zubin in warin da Zee keyi yayi yawa sai Humy ta gasa mata jikinta da tsunma ba tsana baa tsangwama Humy kema Zee komai,ta gyarata tabata magunguna ta bata abinci dukda Zeen bataci amman hakan take daurewa tabata wani zubin dakanta take girkawa takawo mata,sannan intana tarin jini da yazamemata jiki yanzun kullum sai tayi Humy ba kyama take goge mata jinin tayita lallashinta!

STORY CONTINUES BELOW

By this time kam Zee tarigada tazama abin tausayi kuma bilhakki da gaskia tayi nadaman abinda ta aikata kuma bata fatan su yafe mata dan bata chanchanci yafiyaba,yau Humyn data tsana a duk duniya wacce ta ha’inta takusan gur6ata rayuwarta,yau itace kawai tsaye akanta tana taimakonta ta wanke kashinta,fitsarinta ta goge jinin ta batareda kyamatarta ba,babu wani danginta dasuka zo wajenta iyayenta ma babu wanda ke tausayinta babu kuma wanda yazo ganin halinda take ciki,Humyn da wannan Humyn wacce ta tsana ta hantara itace tsaye akanta tana mata abunda iyayenta suka gagara yimata tasan basuda laifi dansun kyareta dan itama hakan ta aikata agaresu!

Wani kalan mugun son Humy Zee ta tsinta kanta damata,sosai tayi nadaman abinda ta aikatama Humairah Da kyar ta iya bud’e bakinta tace:

“Humairah “!

Tsayawa chak Humy tayi daga goge kashinda Zee tayi tana kallan Zee da duk tabi ta k’anjame kaman mai ciwon k’anjamau!

A hakali tace “naam “

Zee ta had’iye wani diddigin jini dake son fitowa daga bakinta,har batason bud’e bakinta dan wani kalan k’arnin warin jini da bakinta ke fiddawa,shiyasa kwata kwata bata magana sai yau data kira Humy hakan nema yasa Humy mamaki!

“Nasan bazaki ta6a yafe mun bako Humy?Humairah na zalunceki sosai a rayuwan banyi deserving yafiya a gareki ba ban dace ki yafe munba Humy,kobayan ba raina ban aminta,ki yafemun ba,nafison Allah ya hukuntani sosai akan abinda na aikata,kicema mama da baba da su dady har Yaah umar ma dan Allah kobayan ba raina karsu yafemun kinji!dan ban chanchanci yafiya ba gwara Allah ya hukuntani sosai dan nazama izina ga sauran mutanen baya,kinga yanda rayuwata tadawo a yanxunko Humy?yau babu wani riba da rashin imani na ya kawomin,yau gashi nazama nak’asashiya,nadawo kaman mahaifina ki……………..::.

Zee kasa k’arasa maganar tayi sakamakon wani kalan tari daya danno mata sosai yau tarin nata yafi sauran tarin datakeyi abaya dan wannan jini har kunne yake fitomata in hankalin Humy yayi dubu yagama tashi dan babu inda jikinta baya karkarwa tausayin Zee yagama mamayeta!

Tama rasa abinyi saurin k’arasowa wajen Zeen tayi tana kuka tana fad’in:

“Wallahi Zee nayafe maki su mama zasu yafe maki kinji bari Na kira likita “

Saurin girgiza kai Zee ta shigayi sannan cikin sark’ewan murya lumfashinta sai sama da k’asa yake tace cikin muryan wahala:”kaaaar ki kirasaaaa mutuwa zanyi Humy,mutuwa zanyi wlh sannan karki kuskura kiyafemun ban chanchanci yafiya ba,kibari Allah ya hukuntani,karki rok’amun yafiya wajen kowa “

Daga haka kuma Zee ta kasa k’arasa maganar da takema Humyn Humy kuwa a sittin tafita d’akin tana kwalama likita kira,Zee kuwa sai faman haki tana lumfashi sama da k’asa da sauri-sauri take bakinta hancinta duk suka shiga fidda jini!

A tare dr da Humy suka shugo d’akin kallo d’aya dr yama Zee yaga alamun mutuwa kawai zatayi amman sai yashiga bata taimakon gaggawa inda ya fad’ama nurse da k’arfi ta kawo masa oxygen dan ceto ran Zee ina Zee kam izuwa yanzun babu abinda takeyi saia ihu babu inda Zufa baya k’etowa ajikinta Zufa sosai take fitarwa wanda ya had’u da warin kashin datakeyi dana fitsari ya shiga bada wani kalan odor mai warin gaske daya gama karad’e d’akin,Humy kam babu abinda jikinta yakeyi inbanda karkarwa kuka sosai Humy keyi ta rungume Zee tanada nanatamata salatin annabi dan duk wanda ya ga Zee a wannan yanayin yasan lokacinta ne yayi kuma ranta ake cirewa dubada irin ihun azaban datake kwalawa,Humy sai faman nanata

“Lailaaa ha’illallah muhammadu rasulillah sallalahu alaihi wasalam “take da k’arfi kozata samu Zee ta amsa amman ina da zaran Zee tayi yunk’urin kama shahadan sai taji bakinta yakasa,wani kalan razananniyar k’arar da Zee tasaki wanda babu ko shakka har wajen asibitin saida yayi amsakowan ihunta,yayi daidai da gama zare ranta daakayi!

Lamo dukkanin sassan jikinta suka saki idanuwanta suka tsaya chak suna kallan silin a lokaci d’aya tayi wani irin tsayi wanda har k’afafuwan saida suka fito acikin hujin gadon datake kwance,Humy kuwa chak kwakwalwanta ya tsaya dan ganin Zee ta daina lumfashi hakan na nuna cewa Zee ta mutu!shikenan takoma wajen mahaliccinta,ihun da Zee ta saki a k’arshe yak’i barin kwakwalwan Humy tana ji likita yace:”innalillahi wa’inna ilaihir rajiun she is gone!”

STORY CONTINUES BELOW

Daga haka yasany’a kansa ya fita a d’akin daidai lokacinda nurse ta shugo da oxgen kallanta kawai yayi sannan ya girgiza kai ya fita!

Humy kam kwarai da gaske mutuwan Zee ya ta6ata ainun kawai rayuwansa Na baya sanda suke yara Humy ta shiga tunowa yanayin yandasuke fad’a da Zee yanayin yanda Zee ke dukanta,yanayin yanda Zee take tare mata fad’a a skul etc dai haka Humy tashiga tunowa tamkar ayanzun ne abin ke faruwa!

Hannunta takai kan fuskan Zee sannan ta rufe mata idanuwanta a hankaligood tace:”Allah j
ik’anki Zee “

Daga haka tamik’e chak tabar asibitin,gida ta koma tazauna shuru takasa aikata komai kaman wacce aka cirema lakka ajiki haka take zaune,dan kam she is traumatized da mutuwan zee!

“Heartbeat daga ina haka nadawo na iske bakinan?”

Ganin Humy shuru bata amsa masa ba sannan tana kallan gefe d’aya yasashi saurin dawowa gabanta ya kama hannunta yace:”wat wrong?”

Batason dogon zance a kunnuwanta hakan yasata saurin cemasa a gajarce “zee is death “

Saurin cire hannayensa yayi daga jikin Humyn sannan yace:”Toh sai yakayi dan ta mutu?wat will u gain frm her death?danaga duk kaman u are been traumatized by her death?ummm tell me y?”

Ganin zai hargitsamata lissafi yasata mik’ewa da sauri sannan tace “a hannuna ta rasu dole naji mutuwarta kuma after all tare muka taso and har yanzun tananan da matsayinta na yar uwata acikin zuciyata!”

Tas taji Umar ya wanketa da wani lafiyyan mari saurin dafe kuncinta tayi tana kallansa cike da mamaki sannan ya nunata da d’an yatsa:”bakida hankali ko tananan a matsayin ‘yar uwaki har yanzun fa kikace?”

Cikin dakewa Humy tace “eh haka nace “

Gyad’a kai Umar yayi sannan yace “fine and good “

Daga haka yatasa kan abul -islam suka fita gidan gaba d’aya itako Humy tananan tsaye kaman gunki tana tunanin abinyi,saurin daukan wayarta tayi tashiga kiran mama:bugu d’aya mama ta d’aga Humy kuwa cikin muryan kuka ta gaya mata mutuwan Zee dukda mama ta girgiza amman saita danne tace “Toh yayi ” Daga haka ta kashe wayan,tsananin mamakin abinda mama tayi humy ta tsaya yi,hakadai Humy ta shiga kiran kowa datasan ya kamata yasan da mutuwan Zeen amman fafur kowa ya nuna babu ruwansa da mutuwar nata cikiko harda yaah bashir shima yayi fafur yace bashi ba Zee!

Ganin bamai shirin taimakon Zee azo amata salla akaita gidanta na gaskia yasa Humy komawa asibitin nan ma suka ruk’a mitan azo a tafi da gawar Zee dan har sun fitarda ita a d’akin daaka kwantarda ita aka gungurata aka kaita wani lungu,Humy tayi kuka tayi kuka harta gode Allah dan kowa ta tara da su taimaka su naimo a sallaci gawan Zee fafur suke k’i.ganin Gawar Zeen na naiman kai awowi kuma gawa wari zai fara yasa Humy left with no option taje waje ta samo wasu almajirai su biyar ta biyasu akazo aka d’au gawan Zee dake ta tsungumo wari suma almajiran k’arfin hali kawai suka ruk’ayi Da danne zuciya dan kawai an biyasu,haka dai almajirannan suka kai gawan Zee masallaci aka mata wanka aka suturtata sannan aka fito da ita almajirai tsiraru zukazo suka sallaceta suka kaita gidanta Na gaskia akabarta daga ita sai halinta,.suka juya suka dawo Humy ta cika masu kud’insu sukai tafiyansu (😭kuga yanda k’arshen Zee ta kasance ace har sai anbita mutane sannan suka sallaceka mai yakai wannan jama’a!?Allah kamana kekkyawan cikawa ameen)

*************^********************

Koda labarin abinda humy ta aikata yadawo kunnuwan su momy ,dady,Yaah UMAR mama baba,yaah bashir etc duk saida suka jinjina k’arfin tausayi da jihadi irin na Humy lalle gaskiya da ana samun mutane irinsu Humy dayawa a duniyanan da ba k’aramin ihsani zaayiba,(Allah dai ya k’arama Humy lfy da tsawon kwana ya kareta daga dukkanin sharruka ya albarka ceta ita da dukkanin zuri’anta ameen)

STORY CONTINUES BELOW

After 7days

Babu yadda Humy batayi ba dan ganin kowa ya yafema Zee laifukan data aikata garesu dan ita tuni ta yafema Zee kuma ta rok’a Allah yamata sassauci,amman fafur kowa yak’i Umar kam fushima yayi da ita da kyar da kyar dai tasha kansa bayan nuna masa ribar yafiya a duniyannan!

Nisawa Umar yayi sannan yace :”kinada good heart Humy samun irinki a duniya sai an tona,inamai k’ara godia da Allah daya bani mata kamanki,Na godemasa daya dawo min dake gareni after rabamu daakai ,We were once on separate paths

     We knew nothing of each others existence

      I agonise by the thought of that

      Indeed they were my darkest time

      Fast forward to the present

      You have become part of me

      Like my very own DNA….

I love u sooo much my darling wife kece rayuwata “

Baijira Humy ta basa amsan maganarsa ba kawai ya had’e bakinsu waje d’aya yashiga sarrafasu dan ba k’aramin kewarsu yayi ba,itama humy sosai tasake tashiga maidama mijin nata martani dan rabuwa shekara d’aya da rabi ba rabuwan kwna d’aya bane ko sati d’aya ! Daga nan kuma suka luliya duniyan ma’aurata!

Humy da UMAR a kashe juna Da love dayawa a kuma kashe arna dayawa 😂😂🏃🏻‍♀️nidai bye bye 👋

*****************^***************

After 10yrs

Sosai abubuwa suka sauyawa wannan familyn tuni kowa ya shafe babin Zee Humy ce kawai mai tunata tana kuma mata adu’oin samun rahma wasu lokutan kuma har sadaka take ma Zeen ,sannan tasa aka hak’a rijiya da sunan Zee!

Sannan ta rarraba qur’anai izifi 60 gamasuyin hadda duk dasunan zee!

Sosai Umar ke bata goyon baya dan baison 6ata mata rai dan yagama yarda Humy mai matuk’ar tausayice zuciyanta bamai rik’o bane!

Humy kam yanzun anzama many’an hajiyoyi tayi 6ul6ul abinta ta goge tayi kyau yaranta uku yanzun’ ,Abul islam sai en biyu intisar da imtiman ,intisar takwarar momy (ramlah)imtinan kuma takorar mama (fatimah binta)

Sosai suke rayuwa gwanin ban sha’awa matar yaah Bàshir ma yanzun ‘ya’yanta biyu kuma duk maza junior  Takoran dadyn Humy (Abbaz)sai baabaa k’arami takoran baba (Ahmad )

Yaah Khalil  ma yayi aure da d’ansa d’aya sai yaah fareed shima da matarsa amman bata haihuba sai yaah huzaifa shima yanzun 2wks kenan dayin bikinsa!

Sosai yanzun babaa yake kasuwanci dan dady da Bàshir sun basa jari maitsoka ya tsunduma kasuwanci kuma Alhamdulillah Allah ya dafa masa dan yanzun har mama saida ya bud’ema shagunan kaya yakuma kaii momy da mama umrah sannan ya siya gidan kansa anan abujan kusada su momy,dady ma yanzun dukiyansa ta k’ara ha66aka dan ayanzun yana rik’e da kujeran senata,bashir ma yayi arzik’i sosai yadawo babban lauya daake ji dashi a nigeria dan yanzun suprem court Na abuja yake aiki shima chan ya koma da iyalansa!

Umar kuwa bayan raba dukiyansa daakai aka basa nasa kason yaransa da matarsa ya dank’ama kud’in Humy sosai tayi farinciki tayi kuka dan mijinta yanuna komai nasa da ya mallaka aduniya nasune ita da ‘ya’yanta,islamiya da boko da masallaci Humy tasa aka gina dan tace tawannan hany’ane kad’ai zata iya barin abinda zai ruk’a kawo ma dukkanin danginta lada ko bayan babu ransu!

Rayuwa gwanin sha’awa yake tafiya a tsakanin dukkanin family din maigoro da kuma Daleel!

Fatan Allah cigaba da kaii albarka acikin wannan zuri’an ameeen

*tammat bil hamdulillah *

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *