AMANAR MU CHAPTER 5
K’arfe 6 daidai Zee ta isa garin abj already driver na jiranta a tasha hakan yasa tana zuwa ta zarce mota!+
Gidan koda tashugo babu kowa da alamu dukkanin baqi sun koma, fitowa tayi daga cikin motan sannan driver ya jaa mata trolley d’inta zuwa cikin gida.
Harta gifta zata shiga cikin gida sai ta tuno da zancen Humy data sameta in private (cikin sirri) ana gobe d’aurin auranta!
_Zee dan Allah inaso kimin wani alqawari_
Kallonta Zee tayi sannan tace “ok inaji “
_Zee dan Allah ina rok’anki bayan tafiyana kiruqa shiga kina duba su baba koda sau d’ayane a rana kimin alk’awari zaki ruk’a kula dasu saboda sunada tsananin Buk’atan wani a kusa dasu,kinga yanzun zan tafi zuwana abuja zai ruqa d’aukan lokaci!_
_Kinga babu kowa yanzun a cikin gidan sai ke da momy da masu aiki su kuma kinsan ba kwana sukeyi ba momy kuma sai yamma take dawowa aiki,Na rok’eki Zee kiruqa shiga kina d’ebema su mama kad’aici daga ita sai baba kawai suke wuni acikin gidan nan fa! Mama ita kad’ai kema Baba duk wani hidima nasa tayi na baba tazo tayi nata baki ganin k’arfinta yafara k’asa masu aikin nan ko ance suyi ba yi suke sosai ba! Zee awannan lokacin iyayenki nada matuk’ar buk’atanki wlh Zee kinada Zuciya mai kyau wanda bai maki farin sani bane kawai zai d’auka zuciyanki ba fari bane amman ni Humy nice nasan Wacece Zee kuma nasan zaki kula da mama da Baba a wannan lokacin dan kece kawai zaki zama mafi kusa dasu a yanzun! _
Dogon lumfshi Humy tasake dan taga alama tamkar Maganganunta sun fara ratsa Zee d’in dan haka ta kuma sassauta kalamanta had’ida dafa Zee d’in sannan ta cigaba da cewa;
_Dan Allah karki bari shaid’an ya ruk’a ingizaki har yasa kina banzatar da iyayenki ,shaid’an yayi alk’awari kauda halittun ubangiji daga duk wani rahmar Allah.Karki bari yaci galaba akanki ked’in mutum ce mai Sauk’in kai da Sha’ani saidai wanda bai maki farin sani bane zai d’auka kinada zafi plss Zeeta kimun wannan alqawarin dan_”
Tabbas maganganun Humy gaskiane ita kanta wasu lokutan inta zauna ta tuna yadda take hantaran iyayenta da kyamatar su abin na susa ranta saidai ya ta iya haka Allah yayita bata k’aunan talaka kuma bata mafarkin had’a wuri wajen talaka da ace mahaifinta arziqinsa bai karyeba kuma ba nak’asaishe bane ai da babu wanda zai kaita son iyayenta itafa da ace iyayenta kaman iyayen Humy ne ai babu abinda zai hanata yimusu ladabi da biyayya tamkar yadda take ma iyayen Humy!
Kallon Humyn tayi sannan tace
_Shikenan in Sha Allah zan k’ok’arta_
Murmushi Humy ta sakar mata had’ida rungumanta!
Dogon lumfashi Zee tasauke sannan takalla side d’in iyayen nata wani qullutun bak’in ciki ya turnuk’eta dukda side d’imsuma akwai kyau da tsaruwa amman ai in an had’a da side dinsu Humy side nasu bakomai bane face boys qauters!
K’udurtawa tayi a zuciyanta ko ana ha maza ha mata itama sai nata iyayen sunyi kud’i sannan ita kanta sai tayi arziqi tayadda baza ta ta6a sake zama a k’ark’ashin wasu ba bare ata hantaranta ana mata fad’a dan ita aganinta saboda iyayenta ba masu shi bane yasanya Umar tsananta sannan ita Humy dan taga iyayenta da en uwanta da ita kanta duk ak’ark’ashin Dadynta suke shine shansu,Cinsu,suturansu ,kudin makaranta da Islamiya su! Kai har iyau dinnan iyayen Humy ke masu komai shiyasa Humyn ke tunkaranta tana gaya mata maganganu iya son ranta akan iyayenta!
Amman bakomai in sha Allahu daga rana irin tayau zata chanza halinta zata koma ta runguma iyayenta,watarana suma arziqinsu zai dawo su tashi a k’ark’ashin wasu!
STORY CONTINUES BELOW
Suma su shiga duniya asan dasu,amman tawacce hany’a zata bi dan samun wannan ‘yancin?babanta kudinsa bawai kwacewa akai ba arziqin ne dakansa ya karaya ya gudu tamkar baiyi dukiya ba! Dama kwacewa akai zata iya cewa zata shiga tafita dan kwacema mahaifinta hakkkinsa
Ta wacce hany’a ya kamata tabi itako? Dan she is desperate (k’aguwa) tabar k’ark’ashin wasu suma sudawo masu kudi masu yima kansu komai da komai ba tareda taimakon kowa ba!
Dole tanada buk’atan taimakon wani amman wa zai taimaketa? Karatunta?
“Aa sam karatuna bazai taimakeni ba dan kona sama aikin kafun abiyani sai wata ya qare sannan kudin daza a ruqa batan bawai mai yawa bane!
Toh wazai taimaketa?
Yaah bash?
Kai no yaah bash zaii 6atamun shiri ne nasan sa dabin kwakwafin bala’i zai iya bincikowa yasan dalilinta dakuma sirrinta! Wanda sam bazata ta6a barin wani yasan wannan sirrin nata ba!
Dole kenan ita kad’ai zata yi abinta bata buk’atan taimakon kowa kenan!
Dole indai tana son wannan mission (buri)d’in nata ya cika tana buk’atan ta aiwatarda abinda tajima dashi a ranta takeson aiwatar wa kenan? Shi kad’aine zaisa iyayenta su azurta itama ta azurta kenan?”
Tabbas wannan itace kawai hany’a mafi sauqi dazai iya 6ullar da ita ga cin nasara dolenta ta chanza takun ta dole kuma tayi bincike mai zurfi akan wannan k’udiri nata!
Murmushi tayi kawai sannan afili tace
“Nagode Humy sosai da shawarwarinki ked’in Amintacciyar k’awa kuma er uwa ce! If badan nasihohinki da shawarwarinki ba dabaki gajia dayimunsu da bazan ta6a natsuwa Na rungumi iyaye na nafiddo su cikin k’angin nan ba!thank u in Sha Allah iyayena kuma kuna gab da zama masu enci masu kuma dogaro dakansu ni Zee namaku alqawarin hakan!dukda zuciyata nasan da kyar zata aminta akan kusanci daku ayanzun ba! Amman zanyi iya yina kafun lokacinda zaku azurta nasoku kaman raina kuma mahaifina yawarke “
Murmushi takuma sakewa wanda ita kad’ai tabarma kanta sanin fassaran ma’anoninsa!
Juyawa tayi tawuce side d’in iyayenta!
********************************
10:30pm
Zaune take akan kujeran falan nata hannunta riqeda remote tana kallan Televista!
K’aremata kallo nayi sany’e take cikin riga da Wando wanda yayi matuqar kama jikinta da fidda surarta tayi kyau sosai sai fidda k’amshi take mai dad’i!
Tun d’azun zaman jiran yaah Umar take dan tunda Zee ta tafi suna shugowa falo akayi kiransa wajen aiki badan yasoba yaje dan anshaidamai zuwansa dolene hakan yasa ya lalla6a Humyn yatafi tun tafiyansa har yanzun bai dawoba “
Knocking kawai taji anayi hakan yasata kallan agogon dake manne abangon falanta 10:50pm mik’ewa tayi tanufa bakin k’ofan a hankali ta sany’a idanunta wajen kallan mutum dake waje yaah umar ne hakan yasata saurin bud’ewa k’uramata ido yayi saiyaga yau tachnza mai dan babu wani surarta dabata fito acikin kayan ba sosai yaji wani kalan bak’on yanayi na shigansa a hankali taje ta rungumesa tamai peck a kumatu sannan cikin sexy muryanta mai rikita duk wanda yaji tace “I missed u so much Sweetheart “
Kuma rungumota yayi sannan ya k’arasa shugowa falan dake ta tashin k’amshin turare mai sany’ay’a rai da zuk’ata!
“Missed u more Humynah “
D’agota yayi yana k’aremata kallo daga sama harqasa shikam inbai godema ubangijinsa da azurtashi da mace kaman Humy ba baisan maizai yiba kuma! Godia ya shiga yima ubangiji Na mallakamasa Humy amatsayin abokiyar rayuwarsa (life partner) matsowa yayi daf da ita harsuna iya jiyo bugun da zuciyoyinsu keyi a hankali yasa hannunsa ya talla6o ha6arta sannan ya matso da fusknsa daidai saitin wuyanta!
STORY CONTINUES BELOW
Wani kalan yaaar Humy takeji daga saman kanta har k’asa ,kwantarda fusknsa yayi a wuyantayana sunsunan k’amshin turarenda yazama jikinta a hankali yacire fuskansa akan wuyanta yamaido dashi saitin fusknta itakam Humy runtsa idanunta kawai tayi dan jima tayi k’afafunta suna gagara daukanta!
Bakinta yasoma laluma a hankali itama ta shiga bud’esu sany’a bakinsa yayi cikin nata yasoma mata wasu kalan hot kisses masu rikitarda kwakwalwa!
Tsayuwan ma gagaransu yasomayi a hankali yazaunarda ita kan kujera ya shiga sarrafa bakinta!
Waiyooo itakam Humy tunda take tana ganin bata ta6a tsintan kanta cikin yanayi mai wuyan fassarawaba irin yanzun kai aure ma rahmane Allah ya k’arama annabi daraja (Amin)
Ganin zata jikata gashi yaah umar yasoma fita hayyacinsa yasata saurin janyewa had’ida wucewa d’aki da gudu!
Shiko yaah umar binta da kallo kawai yayi dan gudun ma kyau yamata yanda mazaunanta keta karkad’awa 🙊
Da sauri ya shugo d’akin isketa abakin gado yayi tana maida lumfashi jin kaman mutum a tsaye akanta yasata d’agoda kai sukai ido hudu saurin rufe fuskanta da tafukan hannayenta tayi dan kunyarsa takeji!
Murmushi yayi ya qaraso inda take zaune shima yazauna har jikinsu na gugan na juna!
Rungumeta yayi sannan a hankali ya rad’a mata a kunne
“Zan cire wannan kunyan nawa da kikeyine ma ai ayau dinnan “
Ya ida maganar yana murmushi da ya bayyarda fararen haqoransa itama Humy murmushi tayi tad’an bugi k’irjinsa a hankali tana fadin “kai yaah umar!”
Daria yayi sannan yace miqe muje muyi alwala muyi salla mugudema ubangiji daya mallakamana junan mu ayau Humynah!”
Kuma sunnar dakanta qasa tayi tana murmushi k’asa k’asa chak taji ya d’auketa kaman baby yayi hany’an toilet da ita bai direta a ko inaba sai sink nan sukai alolan tare sanan suka fito sukayi nafila raka’a biyu bayan sun sallame Umar yajima yana masu rok’on Allah da basu Zuria d’ayaba da d’aurewan auransu har a aljannah!
Bayan ya kammala yamata tambayoyi kuma tsaf ta amsa masa su daidai harda k’arin sharhi ma sosai Umar yaji dadi dan yasan baima ‘yay’ansa za6en tumun dare ba kobai tura ‘ya’yansa naiman karatuba mahaifiyarsu mai basu ingantacciyar ilimine!
Miqewa yayi yaje ya bud’e fridge din d’akin ya fiddo fresh milk da nama yazo ya diresu agaban Humy wacce duk jinta take kaman a mafarki yau gata ga masoyinta wanda tun bata san mainene so ba tafara sonsa shine first love dinta kuma tana fata yazama last ma! Yau sune zaune a d’aki d’aya a matsayin ma’aurata ba masoyaba ?!
“Heys are u lost?”
Yayi maganar yana huremata fuska da iskan bakinsa
Murmushi tayi sannan ta gyad’a mai kai!
Ajiye komai yayi sanan ya kamo hanna yenta ya kalleta yace:
“Humynah mai yakai yau dad’i a rayuwannan yau gani gaki a matsayin ma aurata Humy ayau in Allah ya amsa raina zan mutu cikin farin ciki dan koba komai ban rasa raina ba harsaida na mallaka abar qaunata wlh Humynah Ina sonki ,inasonki so na haqiqa banta6a son wata mace a doran duniyannan bayan keba nasoki tun bansan zakizo duniya ba nasoki tun kina cikin Momy wlh Humy bazan iya qiyasta rayuwa babu keba”
Dogon lumfashi yasauke yana kallan Humyn da itama shi take kallo tanajin wani adda6a66iyar soyayyarsa har cikin ranta!
Dafe kanta da hannunsa yayi sannan yace “Ayau ni Umar Khalil maigoro namaki alk’awarin zama dake har abada Na maki alqawarin baki dukkanin wani kulawa da dukkanin farin ciki a rayuwan nan , namaki alk’awari bazan ta6a bari wani abu ya sameki bare har yasaki cikin damuwa ba. I promise i will always be there!”
“Bazan ta6a daina sonki ba Humynah har abada ko a aljannah kece shugaban matayena a duniya kuma kece kad’ai Matar Faruq! Kuma ke kad’ai zai qauna,zai So, har abada bazai hadaki da kowaba wannan alk’awarine ni Umar Faruq Na daukan maki in Sha Allah rabbi zai dafamun dan cika wannan alqawarin “!
Itakam Humy tuni hawayen dad’i suka gama wanke fuskanta rungume Yaah umar din tayi tana kuka !
D’agota yayi suna kallan juna gyad’a mata kai yayi alaman maganansa hakan yake kuma in Sha Allah ta6batacciya ce!
Nan yashiga bata naman abaki itama tana basa abin gwanin ban shaawa!
Allah kak’arama aure daraja
Allah kabama sauran al’umman annabi mazaje da mataye na gari!
Bayan sungama ya umar yadauketa chak saikan gado ya rungume abarsa ya kashemasu wuta sannan ya tofesu da aduaa sannan a hankula ya shiga naiman hakkinsa……………🚶🏼♀️🚶🏼♀️
Sumsum nafita a d’akin na jany’o masu k’ofan d’akin dan annabi da kansa yace fayyacha sirrin ma’aurata ba kyau!
Tohm Yaah UMAR da Humy asuba tagari a kumaci amarci lafiya!
Bari mu waiwayi Zee kuma!……..✍🏻