AMANAR MU CHAPTER 7

AMANAR MU CHAPTER 7

Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Laaa Zee yaushe kika dawo?”

Humy ta ida maganar tana mamakin yaushe Zeen ta dawo!

Dariya Zee tayi sannan ta saci kallon Umar dake gefenta sai wani uban murmushi yakeyi kaman auduga fuskansa sai kyalli yake fiddowa!

Kallan Humyn tayi sannan tace:

“Ay fa nadawo zama dake aminiya ta ‘yar uwata,zama dani dake har abada”

Murmushi Aliyu yayi sannan yace:

“Aiko zama har abada “

Kallan mamaki Humy ta kafesu,Umar yace:

“Ay Zee itace kishiyar ki,itace wacce na aura “!

Kaman saukan aradu haka kalamansa suka ma Humy diran mik’iya,murmusawa tayi sannan tace:

“Haba dai wasa kakeyi ,ya za’ayi ka auri Zee?!”

Ta ida maganar tana kallan Zee dake ta faman rausaya!

“Wasa kuma? Kin ta6a ganin na maki irin wasan nan? Hhhhh toh tunda kin d’auka kaman wasane  ko?toh bari nacire maki shakku dan ki tabbatarda lallai Zee matata ce! Ba wasa nake maki ba,ita d’in Matata ce!”+

Fisgo Zee Umar yayi yakai bakinsa saman lips d’inta ya shiga tsotsansu kaman alawa!

Runtsa idanu Humy tayi sannan ta kuma bud’ewa dan tabbatarda ba mafarki takeba,ganin fa lallai tabbas Umar kissing d’in Zee yake kuma lalle Zee d’in itace wacce Umar ya aura!

bata san lokacinda ta kwala wani razanannen k’ara ba ta finciko Zee ta kaimata wani wawan duka,sannan ta fincikar   da ita a k’asa,sai haushi take bata ma kallan gabanta burinta kawai taci uban Zee ta mata lilis sai ta kusan nuna mata lahira!

Kururuwan data kuma yine zata afka ma Zeen again kawai taji Umar ya damqota ya wullar da ita a k’asa ,ta buge bum a bangon falan,nunata da yatsa Umar yayi sannan yace:

“Bakida hankaline nace maki matata ce ita ,ita na aura!”

Sunayen Allah kawai Humy ke bitar fad’a ko zata samu zuciyanta ya daina bugu kaman zai ratsa ya fito,Allahumma ajirni fi musibatihi ,tana kallo akan idonta Umar yayi hanzarin Zuwa wajen ,d’aukan wayan Humyn dake yashe a k’asa yayi sannan  ya durk’usa ya d’auketa chak kaman jaririya itako sai wani shagwa6ewa take tana matso kwalla dan dai duk Umar d’in ya rikice!(ZEE)

Ko kallan inda Humy ke yashe a k’asa baiba yayi wucewansa da Zee sama yashiga d’akinsa ya kulle dan lallashin Zeen!

Bata ta6a sanin cewa kuka ma rahma bane sai a wanan lokacin, dan a ganinta da kuka takeyi sha6e sha6e daya rage mata kaso 50 cikin d’ari nadaga cikin abinda ya turnuqe zuciyanta!

Wannan wani kalan cin Amana ne?wannan wani kalan yaudara ne?er uwarta aminiyarta itace ashe duk silan ta6ar6arewan farin cikinta?all this time ashe Zee na sane da duk wani abu dake faruwa?amman tayi shuru munafukar sai faman kissata da maganganu iri iri takeyi,ta ruk’a nunawa agabanta cewa tana bayanta tanuna sam abinda Umar keyi ba kyau 😭har kuka take tayata suyi tare! Ashe munafukan Allan kam kallonta kawai take! Ashe Zee kaman maciji take jikinta fari zuciyanta baqi kaman leda?ya akayi ma wai ta kasa fahimtar su,ya akayi takasa d’agosu?suna soyayyane dama?shin Ina Fatima Zarah ta Kt?dama duk zamanta da yaah Umar da Zee ashe duduniyanta sukeci?shi yasa yaah Umar ke nuna k’iyayyar Zee a fili itama zeen take nuna k’iyayyarsa?dan dai kawai karta d’ago su?innalillahi Yaah Allah kad’auke raina a dede wannan lokacin bazan iya cigaba da rayuwa da wa’inda suka karya AMANARMU ! Suka ruk’a cin duduniyan AMANARMU waiyooo Momy waioyoooo Dady dama kuna sane kuma cewa Zee Umar zai aura?shi yasa lokacin bikin babu wanda ya naimeni ?shi kenan nidai tawa ta k’are yau banda sauran kwana a duniya! ZEEE AHMAD DALEEL kinci Amanata duk irin soyayyar dana nuna maki?na za6a farin cikin ki sama da nawa! Tabbas kin nunamun ke d’in macijiyace,bazan yafe maki ba Zee bazan ta6a yafe maki ba keda yaah Umar!”

Bubbuga kanta kawai ta shiga yi tanakuka tama rasa abunda zatayi kai!wannan wani kalan abune ace wanda kayarda dasu kad’au amananka kabasu ashe suna chan sunacin duduniyan ka!

Wlh hausawa sunyi gaskiya da sukace mutum mugun icce ne ayau wlh tagasgata wannan maganan! Wlh baka ta6a shedan mutum Allah kasaka mun ka kawomin d’auki yaa allah kana ganin wacce na sakankance na damk’ama amanata yau itace ta yaudare ni,ta ha’inceni ta auremun miji,Allah kabinmun hakkina akansu!

STORY CONTINUES BELOW

Mik’ewa tayi da sauri kaman wacce aka mintsila ta wuce d’akinta da saurinta! Tanata risgan kuka kaman ranta zai fita kwana tayi tana kai kukanta wajen Allah dan shine kawai zai kawo mata d’auki kuma tasan yana sane da ita bazai jarrabota da abinda yasan bazat iya d’auka ba!

Washegari!

Closet d’inta ta bud’e tashiga kwaso kayanta ta d’au trolley bag d’inta taruk’a zuba kayayyakin nata aciki!

Saida ta iba rabin kayanta sannan ta kulle trolleyn tanayi tana share hawayen dasuka 6ata mata fuska,hijab ta d’auka ta saka sannan taja trolley d’inta da hanzarinta tabar falan!

*******************************

Gate ta nufa da hanzarinta ta shiga kiciniyan bud’e k’ofan saijin muryan mai gadi tayi:

“Hajia Hajia!”

Da sassarfa ya k’araso bakin gate d’in yayi saurin maida sakatan da Humyn tasoma cirewa!

Kallansa tayi da idanunta dasuka kumbura sukai jajawur cikin daskakkiyar muryanta tace:

“Mai haka kamatsamun na fita mana “

To her surprise sai ganin Isa maigadi ya fashe mata da kuka tay sororoo tabisa da kallo dan sanin mai tafad’a da zai sa shi kuka ji tayi yana cewa cikin muryan kuka;

“Hajia kiwa Allah da annabi karki fita acikin gidan nan wlh Oga yace muddin nabarki kika fita acikin gidan nan a bakacin aikina,kimun rai Hajia wlh inada ‘ya’ya inada mata duk a k’ark’ashin aikin nawa suka dogara kimjn rai Hajia kar OGA ya kureni”

Isa ya ida maganan yana kuma fashewa da kuka dan yanayin yanda yaga Humy yasan da gagarumin matsala amman barinta tafitan kuma zai jany’o masa rashin aikinsa!

Wani kalan k’ullutun bak’in ciki ne ya turnuk’e Humy bazata so adalilinta Isa wanda dagashi har iyalinsa sun dogara ne da aikin gadinsa tazo ta zama sanadiyan koransa,Amman inba haka ba wlh Umar yayi kad’an daga shi har munafukan Amaryar tasa wai susa a kulleta a hanata zuwa gidansu! Wannan ai shine a dukeka a hanaka kuka!

Juyowa tayi tana hawaye tabar wajen ta koma cikin gidan zuciyanta namata k’una!

******************************

Shiga falan tayi amman sai idanunta suka sauka akan Zee wacce daga ita sai k’aramun 3qauter da bra tana kwance a k’irjin yaah umar shiko sai faman kai mata sumba a ko’ina ajikinta yake ita kum sai faman narkewa takeyi ajikin nasa yanda zai kuma jin azaman yi mata komai!

Zuciyanta kaman yayi bindiga ya fashe.tayi nadaman fitowanta da kuma shugowanta falan sau babu adadi da saurinta ta shige d’akinta dan ko lura da ita basuyi ba!

Dannama k’ofan d’akinta key tayi sannan ta kife ruf da ciki akan gadonta ta rushe da kuka sosai !

  Sai datayi mai isanta sannan ta miqe daga kwancen da take ta zauna tana share hawayenta!

“In sha Allahu daga yau ni Humy bazan sake d’aga hankalina akansu ba! Akan
namiji bazata kashe kanta ba,bama zata sake fitowa falan ba ballan tana harsu k’untata mata zuciya,zuba masu ido kawai zatayi gasu ga duniyan wanda bai zoba ma tana jiransa!”

Saida tabari dare yayi sosai sannan ta bud’e d’akinta ta fito ba kowa a falan hakan yasata wucewa kitchen!

Kayan ciye ciye ta shiga d’iba kama daga madara,millo lipton snacks,fruits,cup,spoon ,dadai duk wani abu data san zata iya buk’ata har kettlo duk tasa a basket ta shugo dashi cikin d’akinta,ta jerasu a inda ya kamata!

Ahaka Humy ta kwashe kwana 2 a d’aki bata fitowa sai taji babu motsinsu acikin gidan sannan ne take fitowa ta

d’an girka abincin rana sannan ta dawo cikin d’akinta tarufe tundadai babu abunda zata naima a d’akinta tarasa kama daga kayan kallo wanda shikam ko kunna Tvn ma batayi sabida k’una da baqin ciki ,wayanta ma ranar Umar yayi mata gaba dashi barema tace zata ruk’a chat dan d’ebe mata kewa! Ita dai yanzun aikinta shine kuka sannan ta tashi tayi salla sai shiga bayi!

STORY CONTINUES BELOW

Ahaka dai Humy ta kwashe sati d’aya chur tana rayuwa cikin d’aki ita kad’ai bata ta6a jin koda wasa sun naimeta ba! Kullum saidai aci kwallliya a fita bazasu dawoba sai 11 na dare!

Yau sai kusan k’arfe 10:30Am na safe ta farka jikinta duk kasala ta rasa abinda yasa cikin kwanakin nan duk ta chanza sai yawan bacci da kasala gashi sai ta rik’a jin tashin zuciya tana son cin abi kaza bata son cin abi kaza!

Tadai rasa abinda ke damunta!

Yauma tunda tafarka take son cin taliyan manja da yaji kallan agogo tayi ta tabbata yanxun kam masu gidan sun fita hakan yasata rarrafowa cikin rashin kuzarin jiki ta wuce kitchen tareda mugun zak’uwa tajita tanacin taliyan manja da yaji!

Kunna gas tayi ta soma d’aura tukuny’a !

Kaman daga sama tasomajin wani kalan k’amshin turare yana dabai baye hancinta ji tayi zuciyanta ya soma tashi kan kace mai tafara yunk’urin Amai hakan yasata saurin fitowa daga kitchen d’in giftawan da zatayi sai ganin ashe Zee ce ke tahowa kitchen d’in kuma k’amshin turaren tane yasa mata tashin Zuciya!

Da saurinta ta k’arasa cikin wani lungu ta soma kwarara amai tamkar zata fidda hanjin cikinta!

Da mamaki Zee ta tsaya tana bin Humyn da kallo ,sannan ta k’araso inda Humyn ke d’urk’ushe cikin tausayawa Zeen tace:

“Sannu lafiya kike kuwa?bara’a kirawo likita yazo ya dubaki!”

Cikeda taqaici da haushi Humyn ta d’ago ta kalla Zeen sannan tace:

“Ki kira likita?akan wani dalili?maciyiya amana ,wacce bata san darajan abota ba!,ke yanzun har kinada idon dazaki kalleni dasu acikin gidannan Zainab?!”

Ta ida maganar tana bin Zee da kallan Allah wadai da halinki!

Daria Zee tashiga yi harda shewa da tafi sannan ta kallo Humyn ido cikin ido tace:

“Inadashi mana Humy! ,Humairah ‘yar gidan masu kud’i inada idon dazan kalleki mana! “

Ta6e baki Zeen tayi sannan tashiga zagaye Humy dake binta da kallo wanda suka k’unsa ma’anoni daban daban! Cigaba da cewa Zeen tayi:

“Shin Humairah ke a yanzun zuciyanki takasa jure ma k’iyayyan wanda kike so ne? Kinsan shekaru nawa na kwashe  ina jure k’iyayyan Umar akaina?shekara kusan goma na kwashe  ina jure  k’iyayyar Umar akaina mutumin da nake mutuwan so!

Ni ya tsana,k’awata da muke tare ita yake so,saboda ni ba kowa bace face ‘yar talakawa ‘yar nak’asaishen mutum! Kece fa kullum kike mun fad’a akan na ruk’a kula iyayena ke mai yasa ayanzun baza ki ruk’a kula naki iyayen ba?!

Kina mun hakan ne dan kinuna mun cewa ni ba kowa bace a cikin ku ,iyayena nak’asassune ko?,iyayena suna zaune ne acikin gidanku anbasu aran guri suna zaune !”

Ran Humairah ne yayi mugun b’aci ta d’ago cikeda tak’aici ta kalla Zee d’in sannan tace:

“Dama haka kike ?maciyiya amana,muguwa azaluma,mahaukaciya! Dama ance a duk lokacinda kaga mutum a rana kabarsa a cikin ranan dan tabbas idan kayi yunk’urin maidosa cikin inwa toh watarana kai zai mayar cikin ranar! Trrr da hali irin naki Zainab “!

Wannan maganan yayi mugun b’ata ma Zee rai had’ida tunzurata hakan ya sata cikin fad’a tace:

“Tabbas  magananki hakane amman saidai inaso kisani ni ranar da nasha banyi k’una ba saboda na kasance a inwan ku,ke kuwa bazaki kasance a inuwan kowa ba zaki sha k’unan daga ke har iyayenki sai kunyi dana sanin zuwanku duniya,dukiyan ma da iyayen naki ke tak’ama dashi ta wacece inba ta Umar ba?!toh dukiya sai tadawo hannuna ! Yanda babana ya had’u da mutuwan 6arin jiki kema sai naki uban ya had’u in yaso kema sai kije ki nuna ma duniya kice kema yau  ya ubanki  ya zama nak’asaishe”

Ran Humy yayi masifar tashi hakan yasata yunk’urawa zata damk’o Zee d’in amman sai taja baya tana fad’in:

“Aini bazan ta6aki ba saboda na fuskanci abinda yake tare dake,abinda ke tare dake ciki ko?toh nima cikin ne dani dan aranar danazo Umar gwarzo ne,aranar yayimin ciki,kema nasan kinada k’aramin ciki kuma  da alama cikina sa’an cikin kine,toh d’an cikin naki ma bazaki haifesa ba! Dan daga yau kin gama rayuwa acikin gidan nan ,idan yaso sai kije kiyi duk abinda kikeso “

Ta cigaba da cewa:

“Hmmmmm Humairah ‘yar so matar so,kowa Humairah kowa Humy saboda halinki yasa kikasa kowa ya tsaneni Na shiga k’unci dana zauna kowa fad’a wannan fad’a daidai da k’awayen mu ma saida kika tona mun asiri kika nuna masu cewa ni ‘yar matsiya tace,yaah Umar banida daman dazan sake inyi magana da mutum halinki ya jany’o yake ganina a matsayin azzaluma toh yau gani gake Humairah kowa tata ta fitasheshi,Humairah ‘yar so Humairah ‘yar dadynta Humaira ‘yar momyn ta,kowa Humy,Humy,Humy!”

Zee cikin hargagin d’aga murya tacigaba da cewa:

“Ni kuma Zee d’in babanta ko?Zee d’in mamanta, toh ke kika sani an maki kaza an maki kaza ke ‘yar masu kud’i ni  ‘yar talakawa,ke ‘yar masu k’afa ni ‘yar nak’asaishe ! Komai ke kowa ke toh mai yasa! Dan haka nima dole kishiga irin k’uncin dana shiga a lokacinda babu wanda ya fuskanci abinda nake ciki,yanzun kema ki d’and’ana abinda Na d’and’ana,kiyayyar mutane musamman ta yaah Umar dana jure mata  akanki dan duk akan waa Umar ya tsaneni saboda ke! Kin san shekara nawa na d’auka inajin k’iyayyarki a raina,Humaira kin san shekara nawa na d’auka inajin haushinki araina ,kin san adadin shekarun dana d’auka ina tsara irin wannan rana tazomun?nima naganni a matsayin irin matsayin da kike ciki adaa?cikin jin dad’i  da walwala da farin ciki kowa ke kowa ke?humy Humy! Humy my foot “

Zee ta ida maganar cikeda tak’aici da  baqin hassada!

Humy kam kasa cewa komai tayi kawai tana bin Zeen da kallon mamaki dan wlh Zee ta zarce duk wani zato nata Zeen ce ta kuma katseta tana fad’in:

“Nasan kina tunanin abubun dana ruk’a maki a baya ko?in kasance dake inyi kuka tareda ke har dukan daa Umar d’ina yake maki nake shigan maki a dake mu tare ko?toh bari na warware maki, duk act ne duk mu muka tsara hakan dan bama so kisani saboda zaki dagula mana lissafi,na fison kiganni a na rigada na shugo a matsayin matar UMAR ta yadda babu abinda kika isa kimun! Kinga Jabeer wlh ba saurayi na bane biyansa nayi kike ganin yake mun duk irin abubuwan nan! Fatima zarah kuma nice nan ba kowaba dani Umar ke waya dani kuma kikayi magana rannan na chanza maki murya,ni dakaina nasa Umar ke kirana Fatima zaraa ta yanda koda wasa bazaki ta6a d’agowa cewa nice wanda na sauya maki miji!all abubuwn dana ke maki is all for act! “

Guntun murmushin mugunta tasake sannan ta cigaba da cewa:

“Humm wlh Humy na zarce tunaninki wlh am very smart ko shaid’an tsorona yake idan na shuka wani kaidin! Mu zuba ni dake Humairah za’aga wacce wata wace zaraaa! Wlh na tsaneki I hate u Humy ban ta6a sonki a rayuwan nan ba!”

Daga haka Zee ta juya cikeda haushin Humyn da wutan k’iyayyanta ta shige ciki!

Ita kuma Humy tur
aren Zee ya kuma banko cikin hancinta hakan ya sata saurin juyowa tana kwarara amai tamkar zata shid’e ! Sai da tayi mai isan ta sannan ta d’an ja gefe tana mamaki!

“Dama ciki ne dani?……………….✍🏻Kwankwasa k’ofan d’akinta da’aka shiga yine ya sata mik’ewa daga zaunen da tayi akan gado ta wuce wajen k’ofan ta murd’a key ta bud’e likitan su tagani tsaye murmushi ya sakan mata sannan yace:

“Hajia dama Maigidanki ne ya kirani a waya yace nazo na dubaki ba kijin dad’i”+

Ba tareda tace mai komai ba ta saki murfin k’ofan ta k’arasa cikin d’akin dan yanda jikinta duk ke mata zafi!

Shugowa yayi ya zauna a d’aya daga cikin gujerun d’akin ya shiga mata wasu tambayoyi da aune aune tana basa amsa a tak’aice dan ba tada kuzarin magana wlh!

Bayan likitan ya gama mata gwaje-gwajen ya tabbatar mata da tana da cikin sati biyu daidai,daga nan ya rubuta mata magungunan da zata siya ta ruk’a sha dan rage mata yawan kasala da takeji a kullum,godia ta masa sannan yayi fitarsa,ya barta zaune akan soffa tana tunani!

“Tabbas yau sati biyu chur da Umar ya sadu da ita kenan sai a lokacin ta sama shigan ciki?duk zaman da tayi a baya bata sama ciki ba sai yanzun?”

Koda yake ba abun mamaki bane sai ayanzun rabonta ya k’uso kai rabon cikin ne ya jefo sa d’akinta a ranan kenan !

Shafa cikinta tayi “Toh d’an cikin naki ma bazaki haifesa ba!,dan daga yau kin gama rayuwa acikin gidan nan “

Maganan Zee data mata d’azun ne yayi ringing a kwakwalwanta!

Ita yanzun bama zata iya tunani ba dan in tace zatayi toh wlh zaucewa kawai zatayi dan Zee ta zarce tunaninta har yanzun ta kasa amincewa akan lalle Zee zata iya cin amanarta har haka!yariny’an da suka taso tare,sukai wasa tare,suke kwana tare,suke karatu tare,kai infact kusan komai tare suke,babu irin sirrikansu da basa fad’ama juna ashe duk a sololopiyo Zeen ke kallanta duk abubuwan da take gaya mata k’aryane duk bugan cikinta kawai take tana jin ruwan cikin ta dan ta k’ara samun daman cin duduniyan ta ko ? Ashe chan kwanaki da tazo abj ta iske Zee na fitowa daga d’akin Daddy abinda bata ta6ayi ba dan ba sa shiga d’akin Dady momy kawai ke shiga in ka gansu a d’akin Daddy toh wani abu muhimmine yakaisu! Koda ta tambaya Zeen sai ta wayince tace Mommy ne ta manta agogonta a d’akin shine tace tazo ta d’aukan mata! Sai yanzun tasan dalilin shigan Zee d’akin kenan bincike taje tayi ad’akin dadyn sosai har ta gano files d’in shedun cewa dukiyan mahaifinta (Humy) duk na Umar ne kenan anan ne ta bin ciko mahaifin Umar ne mai kud’in ba mahaifinta ba!kenan? “

Gaskia Zee k’arshe ce, Zee crook ce wlh kaidinta ko shaid’anu sai sun jinjina mata! She is very smart babu wanda zai iya sanin abinda take shiryawa a zuciyanta,wlh babu wanda zai yarda cewa Zee zata iya aikata hakan,ko ita wlh daba ace itace Zee ta mawa hakan da wlh babu abinda zai sata gasgata hakan! Kai Zee irinsune ake ma laqabi da gabansu fari bayan su baqi fat (green snacke under greengrass)

Amman Zee wlh ta cika butulu muddin in haka zata saka masu ita da iyayyenta toh Allah bazai barta ba saboda da zuciya d’aya suka rik’esu kuma basu nuna cewa su ba komai bane a wajensu,kowa a gidansu ya jasu ajiki tamkar ‘yan uwa anriga da an zama d’aya amman ashe ita tana chan tana qullamasu tuggu! Allah ka tsaremu da masu hali irin Zee dan bataga dalilinta na bijiro da wannan halin ba samsam inzatace saboda ana mata fad’a ne ita baa mata shiyasa zata d’au fansa ai wannan banzan daliline dan ai gaskia kowa ke fad’a mata dan ta gyara lahiranta!

Ke da Allah Zee in hakan shine kike ganin daidai gaki ga duniyanan Allah bazai baki nasara akan iyayena ba! Duk abinda zakiyi in Sha Allah akaina zai tsaya bazai shafa dangina ba!

STORY CONTINUES BELOW

Cikina kuma da kariyan Allah sai na haifesa ko nan gaba ya zama shine wanda zai d’aumin fansan abinda kuka mun keda Umar!

*************************************

Koda likitan yazo ya auna Humy yaga tana da ciki bai kira ya sanarwa Umar d’inba dan ya fiso matar tasa tamai albishir d’in cikin da kanta (Humy)!

Koda ya dawo gidan sai ya iske Zee zaune a falo tana ta disgan kuka kaman wacce aka aikoma labarin mutuwa har wani hucin kuka take tanayi tana sharewa da tissue data cika gabanta dashi,kallan tissue d’in dake gabanta duk ya jik’e da hawayenta ya tsayayi kafin yayi saurin k’arasowa wajenta!

“Subhanallahi sweeetheart lafiya?mai ya sameki kike kuka?kodai jikin baba ne?”

Saurin rungume sa tayi tana shasshek’a tace:

“Habibi ba wannan Humairan bace ina zaman zamana ta fito daga d’akinta ta shiga ya6amun maganganu tana mun gorin cewa iyayena talakawa ne ‘yar nak’asassuce ni,har cewa tayi wai wlh sai na barmata gidan mijinta kuma d’an uwanta!kaji faa dan kawai taga banda gata komai na taso ita kemun da iyayenta shine take mun gori yanzun,nidai wlh bazan iya d’aukan wannan wulaqancin ba da gori wlh saidai ka za6a kodaini ko ita a……………

Batakaiga k’arasa zan centa ba yayi saurin dafa mata yatsansa akan bakinta!

“Shhhh ya za’ayi kiruk’a irin wannan maganganun ita d’inma Uban nata da kud’in wa yake tak’ama?ai da kud’in ubana ne!toh wlh bazata sa6uba har cewa take zaki bar gidannan,Zee ai kece rayuwats wlh bazan iya rayuwa ba tareda keba ita d’in da tace zaki bar gidan itance zata barmun gida ayau shashancin banza “!

Fuuuuuu kaman wanda ake kad’awa yayi hany’an d’akin Humy ya banko mata k’ofa!

Itako Zee ta fashe da wani kalan munafukin dariya ta tafa hannayenta sannan tafurta a fili:

“Wlh Kad’anma kika soma gani daga cikin abinda na tanada maki Humy,kinyi kuskuren shiga gonan Zee,I will make sure I make ur life a living hell yanzun aka fara wasan “

Ta ida maganan tana share sauran kwallan k’aryan datayi sanda taga shugowan Umar gidan!

Jin anbanko mata k’ofan d’aki anshugo cikin hargagi ya sata saurin ajiye sallayan data d’auka dan yin salla ganinsa a haka kaman wani damisan daji ba k’aramin tsoratata yayi ba kafun tasamu tayi wani tunanin da yasa shi banko mata k’ofan d’aki ya shugo yana mata garaji taji yana cewa:

“Dan kaza-kazanki kifitan min agida ,yau zamanki yak’are acikin gidan nan,ki fita kibarmun gida “

Jikin Humy har kyarma ya shiga yi ganin yadda yake janta yana son fiddata daga d’akin cikin hawaye muryanta tace:

“Kabarni naje na kwaso kayana toh,sai in fitanma gida “

“Wallahi babu abinda zaki d’auka ay duk abinda kike tak’ama dashi nawa ne da dukiyata aka siyesu,har kinada bakin yima Zee gori kice ita ‘yar nak’asasshe ne ‘yar gidan talakawa ,kema ai in har babu kud’in ubana aikema uban naki talaka ne,abar kaza cikin gashinsa amman kafin na rufe ido na bud’esu ki fitanmu acikin gida nace “

Ya ida maganar cikin d’aga murya!

Hakanan Humy naji na kallo Umar ya tasa k’eyanta ko kud’in mota bai bari ta d’auka ba ya rakata har wajen gate ya bud’e gate d’in Zee na biye da shi a baya suka sa hannu a tare suka hankad’ata waje har da fad’uwanta a k’asa kafun ta yunk’ura ta mik’e harsun rufe Gate d’in sukai shigewansu ciki.Umar harda runguman Zee ita ko sai faman shige masa take zuciyanta fal farinciki yau babban first mission (burinta)ya cika Humy daga rana irin tayau tabar gidan Umar in Sha Allahu kuma ba ita ba dawowa ciki ta fita ta tafi har abada kenan no coming back!

Yanzun soranta cika burinta na gaba!ta rigada ta gama da Humy dan nan bada jimawa ba zatayi dukkanin kisisinanta tasa Umar ya saka Humyn shikenan zamansu is over! Umar zai dawo nata ita kad’ai har abada kaman yanda take mafarki a kullum kenan?ita kad’ai zata mallaka Umar da duk dukiyansa dan shima wlh sai ya dawo hannunta kota halin k’ak’a yanzun cikin Humy shi zai zaman mata cikas amman shima zata murk’ushesa ne da ita Humy ke zance!

STORY CONTINUES BELOW

Wani kalan murmushi ta sakan ma
kanta wanda ita kad’ai tasan ma’anan murmushin d’an juyo da kanta tayi tana kallan gate d’in gidan tana murmushin mugunta yau kam ta fidda Humy acikin gidannan acikin dak’ik’u da basufi 30 ba dogon lumfashi taja had’ida lumsa idanu tawaigo ta kuma shigewa jikin Umar shi kuma yasakalo kansa cikin fuskanta yana hura mata iskan bakinsa harsuka shiga cikin falan gidan!

Humy kuka kawai ta fashe dashi itakam wai maitama Zee haka da zafi ne a rayuwa? Nuna sonta da fifita farin cikinta akan nata shine aibun ta?shin laifi tayi da tad’au son duniya ta d’aurama Zeen?

“Gaki ga Zee watarana sai tasaki kukan bak’in ciki ,lokaci na nan zuwa dazakiyi nadaman sanin Zee a rayuwarki za kuma kiyi bak’in cikin damuwa da nuna soyayya akan Zee mark my words Zee saita zaman maki bak’in dare muddin baki bar yarinyan nan ba Humy”!

Maganan da Yaah Umar ya ta6a mata shekaru dasuka shud’e kwakwalwanta ta haskomata!

Munafukin ashe yasan Zee zata zame mata ciwon ido,ashe da saninsa shiyasa kullum yake kwa6arta akan tafita harkan Zee dan k’ilan tun alokacin suke soyayya kenan kuma watak’il Zeen na gaya masa k’udurinta akanta kenan shiyasa shi kuma amatsayinsa na yayanta yake kwa6arta amman ita tak’i ganin inda ya dosa ashe sun jima suna cin Amanarta amman kam ta jinjina masu dan ba k’aramin namijin k’ok’ari sukai ba amman tambayan anan shine ya aakayi mai kuma yasa Zeen tabari ita tafara auran Umar d’in?ko kuma shima duk yana cikin tsarin nasu ne?”

Kuka sosai Humy ta kuma fashewa dashi wlh bata ta6a zaton akwai ranarda Zee zata iyacin amanarta ba Allah kaine Allah!

Kuka mai tsuma rai Humy ta fashe dashi tama kasa sanin abinyi kuma ta k’i mik’ewa daga kwancen da take ak’asan!

************************

“Subhanallahi Humairah maikikeyi haka kwance a k’asa kina kuka sha6e sha6e mai faru lafiya kuwa?”

Da hanzarinta ta kamo Humyn ta mik’ar da ita Humy kam babu wani sauran k’arfi ajikinta yanda akay da ita kawai zata bi!

Kamata Raliya mak’ociyarsu tayi ta shigar da ita gidanta har falo ta zaunar da Humy sannan ta bud’e fridge ta ibo mata ruwan sany’i tabata abaki dan ganin Humyn tamkar bata hayyacinta!

Kad’an Humyn tasha ruwan,raliya ta ajiye cup d’in tana kallan Humy cikeda mamaki tadai san tabbas Umar ya k’ara aure dan ranar tarewan amaryan ma a gidanta Humy tazo ta wuni harta rik’a bata baki shin kodai Amaryarce ta hanata zama?”

Maganan Humyn ne ya katseta:

“Raliya pls ki aramun kud’in mota zan tafi abj innaje zan turamaki “

Da mamaki Raliyan ta kalla Humy sannantace:

“Kaman yaa humy ina zaki acikin wannan yanayin mai zakiyi a abj wanine ya rasu?”

Mik’ewa Humy tayi dan inta biye ma raliya ba barinta zatayi ta wuce abj ba danko ita bata kuma kwanan kd ba kuma ta tunanin zata kuma dawowa kd irin kora wulaqancin da aka mata kaman ba gidan d’an uwanta kuma mijinta ba!”

“Raliya kedai kiban pls innaje zan maki bayani kibani kawai “

Ganin dagaske Humyn keyi yasa raliya shiga d’akinta ta ciro 5k tabama Humyn sannan ta rakota bakin gate zuciyanta fal mamakin abinda ya sama Humyn haka aduaa ta mata akan Allah ya yaye mata koma mainene ke damunta!

Fita tayi da sauri daga cikin gidan tanufa bakin titi tana tafiya dasauri dan ta k’osa taganta a express dan tasama motar da zai kaita koda kawo ne tasama motan tafiya abj dan ayanzun kam banu station d’in jirgin dazai tashi sai kuma gbe and she cant wait har gobe!

Aiko batay nisaba tasama mai adaidaita ya kaita kasuwan bacci dan yace mata ba zata sama motar abj a kawo ba saidai a kasuwan bacci shima da kyar ne ta samu dan yamma yayi!

A kasuwan bacci mai napep ya ajiyeta ta basa kud’insa ko chanji bata tsaya ta amsa ba ta wuce inda ya nuna mata cewa anan zata sama motan Abj!

Koda ta Isa ance mata babu motan dazaije abuja Humy kaman ta kwala ihu tsaban tak’aici itadai ta rantse wlh babu abinda zai sata kwana a kd!

Magiya sosai da rok’ansu ta shiga yi amman kowa yace bazasu abj ba hany’an ba kyau musamman da yamma!

Tana kuka tajuya tasoma tafiya,kaman daga sama taji wani daga cikinsu yace:

“Hajia muje nakaiki amman kudinki dubu 10”

Dasauri tawaigo tana share hawayenta da bayan hannunta murya na rawa tace:

“Eh naji muje zan baka “

“Bismillah “

Jiki na rawa Humy tabi bayansa tana hamdala ga mahaliccinta data sama mai kaita alqawari ma tayi yana kaita abjn 20k zata shiga ta d’auko tabasa tunda shi kad’ai yayi tunanin taimakonta!

Shiga baya tayi shikuma yaja motar suka soma tafiya sosai direban ke gudu dan kar yamma tamusu lilis a hany’a !

****************************

Tana zaune kishingid’e a falo ta saka k’afa d’aya kan d’aya tana shan ruwa acikin glass cup gefe d’aya tana waya kaman batason maganan ma a hankali take maganan kaman mai rad’a koni dake kusa da ita banjin abinda take fad’i bare na rubutomaku 🤦🏻‍♀️ita kad’ai da wanda suke wayan sukasan abinda suke tattaunawa!

*********************

Dede dazasu shiga garin abuja wani k’atan tirela ya shige gabansu direban da ya d’au Humy yayi yayi ya tsaida birkinsa amman yaci tura gwalalo idanu Humy tayi shikuma direban yana furta “Innalillahi wa’inna ilaihir rajiun “

Gijib motan tirelan nan ta hau kansu!

Tankal tankal motarsu Humy tasomayi har tayi cikin daji itama tirelan tayi cikin daji ya bige a bishiya kance mai tirelan ya fad’i akan motarsu Humy dake wajen bishiyan tana tada hayak’i!

Motocin dake tafiya akan titine da jama’un dake tafiya a k’asa suna salati cikeda kid’imewa suka nufo inda hatsarin ya wakana!

Da kyar aka fito dasu Humy da direba duk sunyi rakokosa babu kyan gani mutanen tirelan kuma su biyu basu mutu baa amman sun kakkarye!

Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un shine abinda mutanen keta fad’a dan babu makawa tsinke Humy da direbanta sun rasu………………✍🏻Ambulance da polisawa a lokaci d’aya suka k’araso wajen aka tattara su Humy aka sany’asu aciki akaja aka tafi asibity dasu,police suka shiga investigating yanda zasu sama accesses da dangin victims d’in,mutanen dake cikin tirelan ne kawai sukai rai amman kam suma sunji jiki karaya har a k’afa!+

Humy da direba kam zan iya cewa tun dannesu da tirelan tayi lokacinda ta fad’o saman motan ‘yar kumbulan da suka zo aciki Allah ya Amshi rayukan su!

Da kyar da taimakon bincike aka samo lanban Dady wanda yake zaune shida momy suna tattaunawa ringing d’in wayansa ya katsesa hakan yasashi kallan mai kiran nasa d’agawa yayi ta reda yin sallama CP ya amsa masa sannan yace:

“Kana maganane da commissioner of police na nan headquarters na abj “

Da d’an mamaki Dady yace:

“Toh toh barka lafia dai ko inspecter?”

“Ina maganane da Abbaz lawal mai goro mahaifi Humairah Maigoro?”

“Eh ranka ya dad’e ni mahaifintane amman lfy dai ko?”

“Hatsari ‘yarka tayi daga hany’anta na shugowa Abuja yanzun haka Allah yayi mata rasuwa da ita da direban motan kuzo ku amsa gawanta anan mutuware na police qauters “

“Innalillahi wa’inna ilaihir rajiun “

Shine kawai abinda Dady ya shiga nanatawa zufa sai k’eto masa yake a ko ina ajikinsa Mommy da tunda ta fuskanci yanayin yanda mijin nata ya shiga kawai gabanta ya shiga fad’uwa,da sauri ta k’araso wajen Dady ganin k’afafunsa na shirin daina d’aukansa tarbosa tayi sannan cikin kid’ima ta soma fad’in Dadyn Humy lfy?mai faru “

Kuka sosai dady ya fashe dashi sannan ya duba momy yace “Ramla Allah yayiwa Humairah rasuwa,innalillahi wa’inna ilaihir rajiun “

Cikin zabura momy ta saki dadyn tana mai kallan mamaki bakinta yama
kasa furta komai dady ya kamo hannunta yace:

“Ramla kimin magana mana “

D’an murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace:”Haba Alhaji tayaya zakace Humy ta mutu?tafa rasu kace “?

Kasa cewa uffan dady yayi dan shi kansa wlh bai yarda Humynsa bace ta rasu maybe dai ba ita bace wrong details aka bama police station d’in Humyn sa dake kd taya zaayi ace tayi hatsari ta mutu?!

Mik’ewa da sauri momy tayi jikinta babu inda bai 6ari tabi bayan Daddy.ko kafun su iso bakin gate sai jin jiniyan ambulance sukai da sauri suka fito momy harda tuntu6e k’arasowa sukai aka bud’e masu ita yanda suka ganta raga-raga babu inda bai karye ajikin ta ba kai anan k’afa chan tayi raga-raga dai babu kyan gani!

Innalillahi wa’inna ilaihir rajiun fasalta irin musiba da tashin hankalinda momy da dady suka shiga 6ata lokacine dan tabbas wannan Humyn suce itace wlh ta rasu 😭innalillahi wa’inna ilaihir rajiun!

Momy kam saida aka shiga da ita ciki aka kulle tsaban kukan da takeyi shikenan Tilon ‘yarta ta mutu ta tafi tabarta shikenan Humairanta ba zata sake dawowa ba?bazata sake ganinta ba?ya akayi mai ya tasota daga kd?mai zata zoyi a abj?kenan ajalinta ke kiranta kenan!

Babu wanda zaiga gawan Humy bai zubarda hawayeba,ta mutu cikin bak’in ciki da k’unan zuciya ashe duk saurinda takeyi dan karta kwana kd ashe ajalinta ke kiranta hasbunallahu wal’ni’eemal wakil tabbas kullu nafsin za’ikatul maut dukkanin mai rai sai ya d’and’ani mutuwa!

STORY CONTINUES BELOW

Mutuwa zuwa take a lokaci d’aya ba tareda kowani bawa yayi shirin zuwanta ba,ko kashirya koba kashirya ba wlh in lokacinka yayi tafiya zakayi ko secns biyu bazaka k’araba!

Kuma kowa da yanda Allah ke rubuta masa lokacinsa da kuma irin yanayin lokacinda zai mutu,wani yana cikin shan giya zai mutu,wani kuma daga bacci yake tafiya,wani hatsari,wani cikin ruwa,wani ciwo,etc.Wlh kowa da yanda mutuwansa take zuwa masa kowa nasa a rubuce yake wlh in lokacinka yayi babu wanda ya isa yahanaka mutuwa,koda kana cikin bak’in ciki ko wahala,ko kuma farin ciki ko kuma ak’asin hakan mutuwa dai rigar kowace randa yazo turn d’inka dole ka tafi!

Hakan ne kuma ya kasance da Humy lokacinta ne yayi babu masaka tsinke Allah yasan dalilinsa na d’auke baiwar tasa adaidai wannan ga6a da take fuskantan wahalhalun rayuwa da gwagwar mayan rayuwar duniya,Allah yafi kowa sanin dalilinsa na d’auke Humy a daidai wannan ga6ar maybe hakan shine mafi alkairi ga rayuwanta,dan Allah bawai dan bai sonta bane ya d’auketa aa saidan k’ilan ta fiyanta a daidai wannan lokacin shine mafi alkairi ga duk wanda keson cutar da ita!

Humy Allah jik’anki Allah kuma ya gafarta maki Allah kuma yasa k’arshen wahalanki kenan!(Ameen yaaa raab)

Koda mutuwan Humy ya isa kunnan Zee har zuciyanta taji dad’in hakan dan koba komai mutuwanta ba k’aramin k’aramata armashin burinta zaiyiba babu Humy babu cikin jikinta kam ai komai na dukiya ya dawo hannunta sosai tayi farin cikin mutuwan Humyn!

*******************************

Dady ne ya kira Umar ya sanar masa mutuwan Humyn dan lokacin ya fita yaje siyoma Zee ice-cream!

Umar har cikin ransa saida yaji mutuwan Humy ya rasa dalilin da yasa bai k’aunan ganin Humy a gabansa amman a duk lokacinda ya mata wani abu in yaje office ko ya kad’aice shi kad’ai sai ya zauna yata kuka yana tambayan zuciyansa dalilin da yasa baisan ganin Humy agabnsa amman abayanta yata jin zafin abinda yake aikatawa a gareta!

Umar yayi kuka ya koka har ba’acewa komai kuma ko gida bai koma ba straight hany’an abj ya d’auka!

Koda ya iso ya iske gawan Humyn ba k’aramin rikicewa yayi ba,Humynsa ce amace?ta mutu tabarsa kenan?kuma da tsanansa ta mutu?innalilahi wa’inna ilaihir rajiun Nan umar yashiga rera kuka yana ta faman Humy ki yafeni Humy kiyafemun”

Babu inda mutuwan Humy bai karad’e ba en uwa da dangi abokan arziqi babu kuma wanda bai yima Humy kuka ba musamman wa’inda suka mata farin sani yariny’ace da babu ruwanta gata da ladabi ga sany’in rai kai Allah dai kajik’an wannan baiwar taka yasa Aljannah yazamto makoma a gareta (Ameen)gidansu Humy tip ya cika da mutane yayyunta duk gobe zasu zo sukam ay mutuwan yafi kowa bugunsu k’anwarsu wanda duk duniya babu wanda sukeso sama da ita yau mai rabawa ya rabasu!

Mutuwa mai yankan k’auna!

Washegari k’arfe 8:30 aka gama yima gawan Humyn wanka aka suturtata aka fiddo ta aka sallaceta daganan d’inbin jama’a da suka sallaceta suka d’unguma zuwa mak’abarta dan rakata makwancin ta!

Koda akaje anrigada an gama hak’a ramin Sata kawai zasuyi Dady da yaah umar dakansu suka sany’a Humy cikin kabarinta sunaji suna gani aka soma dumbuza k’asa akanta har aka rufeta ruf babu wani waje daaka bar mata a bud’e ,yanzun kam k’asa yarigada ya rufe mata ido .

Duniyan kenan fa wlh yanzun daga kai sai ayyukan dakai zasu zauna dakai!

Humy kam ai in sha Allahu tayi mutuwan shahada .Kuma kowa namata zaton alkairi acikin kabarinta!

Ta tafi tabarma Zeen duniyan wlh Zee itace keda sauran wahala dan inka aikata aikin alkairi lahira ya fiyema duniya sau dubu.ita dai Humy nata ya k’are tabarsu insuna so su had’iya duniyan gaba d’aya kuma sumata zaman dadiro,ita ko ta komaga wanda yafi son ta mahaliccinta kuma tabbas sai ya saka mata!

Zee itakeda sauran wahala a duniya

Umar kam mutum mutumi kawai yadawo ko gaisuwan daake masa ma bai amsawa saidai ya bika da ido kawai shi kad’ai yasan halinda yake ciki duk asanadiyansa Humy ta rasu tabar doran k’asa!

STORY CONTINUES BELOW

Dabai koreta a gidan ranar ba da k’ila wur haka tana nan araye!

So yake yayi dogon nazari akan abinda yakema Humyn amman sai ya kasa inyayi picturing d’inta a kwakwalwansa sai yaji kuma yanajin tsananta amman in sunanta yake bita a kwakwalwansa sai yaji yana hawaye yana nadaman abubuwan da ya aikata mata wanda shi sam ya kasa gane dalilinsa namata!

*********************************

Dawowansu daga jana’iza yayi daidai da isowan *Barrister Bashir Ahmad* (yayan Zee)haraban gidan parking yayi ya fito daga cikin tsadaddiyar motarsa daka gansa zaka ga tsananin kamanninsa da Zee kaman antsaga kara ankarya! Kallan K’ofan gidan nasu dake cike da mutane yayi,gidanda yayi rayuwa tun yana yaro har izuwa girman sa , bayan kammala makarantarsa daya sama aiki a fedral high court na lagos ya tattara ya koma chan da zama a kowani lokaci idan yayi yunk’urin zuwa gida sai yaji sam baison zuwa ya gwammace ya kira iyayensa da su dady a waya agaisa amman baiko marmarin zuwa ya ga gida amman abin na ransa kullum dan yana mugunson yazo yaga iyayensa!

Yanzun ma mutuwan Humyn ne yasashi yak’i da duk wani abu dake hanasa son Zuwa garin abj,dan Humy dabance acikin zuciyansa mutuwanta kuwa ba k’aramun ta6ashi yayiba!

K’arasa shugowa yayi wajen daake zaman amsan makokin yayi sallama sannan ya musu ta’aziya ya naima wuri wajen Da umar da yayyin Humy ke zaune shima ya zauna ya kuma masu ta’aziya sannan aka cigaba da amsan gaisuwa tareda shi!

Zee kuwa itama tun adaran ranar tayi diran mik’iya dan wajajen k’arfe 12 ma ta iso sai disgan kukan munafirci take kaman zata shid’e en uwa da abokai sai bata baki ake ana “dole mutuwan Humy yafi d’aga maki hankali Zee dan irin shak’uwan da kukai sai Mutuwan ce kawai mai iya rabashi kibita da aduaa kawai dan shi tafi buk’ata awajenki yanzun “

Itako sai ta kuma fashewa da kuka tana “Allah jik’anki Humy Allah gafartamaki mala’ikun rahma su amshi bak’uncinki”

Itako momy tak’aicin abubuwan data ruk’ama Humyn kafun auran Umar d’in sunk’i barinta tayi sukuni kukan zuciya kawai Momy keyi dan tasan ta juyama ‘yarta baya kafun ta mutu,Allah sarki Humy duk irin shasshareta da muke hakan bai hanata kiranmu ko a dagule zamu amsa bata zuciya Allah jik’anki ‘yata Allah ya rahmamiki ya sany’ay’a kabarinki,
Allah kuma yabani danganan rashinki ‘yata!

****************************

Da yamma bayan mutanen da suke shugowa gaisuwa suka lafa,bayan sallan Isha’i  Brrt bashir da yaah khalil wanda sa’annin junane tare ma suka kammala degree d’insu da masters a university d’aya saidai kowa different course dasuka gamane suka sama aiki shine suka rabu shi Bàshir yana Lagos shi kuma khaleel achan UK 🇬🇧 yasama aiki!

Tsayawa sukai a bakin gate d’in gidan dake ayau wangale Khalil ne ya murmusa yace:

“Barrister Bàshiru kana nigeria amman bakason lek’owa abj “

Murmushi kawai Brrt bashir yayii sannan yace “ba haka bane wlh aikine kasan yanayin aikin namu “

“Mutuwan Humy yamugun rikitani wlh shiyasa dolena nayi canceling duk wani ganawa da nake dashi da clients d’ina nama abj diran mik’iya ,Wlh ni Umar ma nafi tausayama mutuwan nan ya Mugun shigansa,ko yazai iya rayuwa ba tareda Humy ba nasan bazai sake aure a rayuwan nan ba indai Umar ne akan Humy zai iya aikata komai “

Kallan sa yaah khalil yayi sannan yace:

“Gaskia bayan daina zuwa gida dakai har daina bin lamuran dake gudana acikin gidan kai “

Cikin mamaki yaah bash yace “kaman yaah mutumina?”

“Atoh kaman yanda nake fad’a mana yanzun zaka ce mun bakasan Zee na auran Umar ba?”

Cikeda mamaki brrt bashir ya kalla yaah Khalil sannan yace ” Zee na auran Umar?Umar na gidanan wai kake nufi? Mijin Humy?!”

“Kwarai dagaske yau sati inaganin in ban manta ba biyu kenan da auran “

Ya cigaba da cewa:

“Allah sarki Humy lokacin auran nasa duk tabi ta d’aga hankalinta akan auran wlh dukda bani zaton tasan da cewa Zeen umar zai aura inaga dai daga bayane tasani ,da kyardai ta kwantarda hankalinta akai auran dan harni saida ta kirani achan Uk tana kuka ta sanarmun wai Umar zai k’ara aure niko namata fad’a sosai akan mai damuwanta akan auran,sam banson tuno fad’an danay matan nan wlh yanzun gashi ta tafi tabarmana gidan duniyan Allah jik’anki Humy”

Tsananin mamakine shimfid’e a fuskan barrister bashir yanzun ace wai k’anwansa tayi aure amman arasa wani wanda zai sanar masa kuma har waya sunayi da mama bata ta6a gaya masa cewa Zee zatayi aure ba saidai rashin lfyn Baba da koma wansu zamfara kawai ta sanar masa!”

Shuru kawai Barrister Bàshir yayi yana sauraran yaah khalil!

Daga bisani suka shiga cikin gida dan yima su Momy gaisuwa!

Koda yashugo cikin falan iske k’anwar tasa yayi a k’asa tana ta kuka duk idanuwanta sun kukkunbura sunyi jajazur tsaban kuka,k’aremata kallo tsaf tareda nazartanta sosai barrister yayi sannan daga k’arshe sukai ma su Momy sallama suka koma cikin gida!

*****************************

Bayan kwana 3

Yaune akay sadakan Uku na mutuwan margayiya Humy,Zee tun gama adu’oin ukun ta soma shirin komawa kd dan tace masu momy inta cigaba da zama a abj baza jura rashin Humy ba(kuji fa)

Wajajen k’arfe 2 tsaf tagama shirnta dan jirgin 2:30 zata bi!

Fitowanta kenan tana jan trolley taji maganan mutum a bayanta!

“Zee!”

Waiwayowa tayi ganinsa saida hantar cikinta ya kad’a amman dake ‘yar duniya ce sai ta dake tad’an naimo murmushi ta sakalama fuskanta shima murmusawan yamata ya kuma kallan fuskanta ya nazarta halinda tashiga a d’an mintunan nan lumfashi ya sauke sannan yace:

“Ashe kinyi aure shine baki sanar minba dan kinsan bazan amince ayi auranba?”

A tak’aice ta amsa masa da:”eh nayi “

“Baki sanar dani ba!sabida kinsan bazan bari ki aura mijin ‘yar uwarmu aminiyarmu,mutanenda sukai mana dare mukuma zamu masu rana Zee?mai yasa kika aureshi?”

Shuru tayi sannan tad’anyi dariya had’ida kallan yayan nata tace:

“Saboda yana sona ina son shi!”

Yace:”k’aryane! tinda nake a gidan nan  nasan cewa bakwa ga maciji tsakaninki daa Umar akwai dai abinda kika 6oye!”

Ya ida maganar yana kafe k’anwar tasa da idanu yana kuma mai nazartan ta!

D’agowa tayi ta kallesa sannan tayi banza dashi ganin yana 6ata mata lokaci tajuya ba tareda ta fuskance sa ba ta kallosa ta gefen idanu tace:

“Toh Allah yayi idan kuma kanada yadda zakayi toh sai ka raba!”

Daga haka tasa kanta tayi tafiyarta station !

Binta kawai da kallo Barrister bashir yayi ganin tayi tafiyanta sai yayi kwafa ya girgiza kansa ya kama gabansa ya tafi harkan gabansa shima!

**************************

A daran ranar bayan mutane sun lafa sai dai d’aid’ai ku dake shugowa gaisuwa sai kuma sauran en uwa da basu rigaya sun tafi ba!

Zaune suke ,yaah khalil,yaah fareed,yaah huzaifah ,Yaah Bàshir ! suna d’an hira sama sama!duk dai akan accident d’in da Humy tayi ne

Kaman wanda aka jefo haka suka gansa akansu Yaah khalil ne yace “ha’a lfy kuwa yaah faruq “

Banza Umar yamai sannan ba tareda ya damu da kallansa dasuke ba cikin d’aga murya yace:”Ina dady?yau yau d’in nan nake so ya fito ya bani dukiyata gaba d’aya,duk wani dukiya da akasan tawace a fito abani abuna “

Da sauri Dady ya k’araso cikin falan dan dama yayi rakiyane dawowan sa kenan yaji zancenda Umar d’in keyi cikin kid’ima da mamaki Dady ya k’araso cikin falan yana kallan mutanen ciki dasuka zubama Umar idanu suna masu tsananin mamakin kalamansa Umar naganin Dadyn cikin rashin mutunci ya kuma d’aga murya yace:

“Nidai a fiddomun da dukiyata,duk dukiya da akasan tawace a fito abani kayana ayanzun nan ba sai anjima ba!,an zalunceni ank’i bani hakkina tun ina k’arami harna mallaki hankalina an durk’ushemun dukiya ana fafata dashi abani dukiyata now!”

Umar ya ida maganar cikeda masifa da ruwan bala’i har kana iya hango jijiyoyin wuyansa!

Shuru Barrister bashir yayi tunda Umar ke hayaniyar ya kafesa da idanu yana mai nazartan Umar d’in anan ne yasoma ganewa akan lalle lalle akwai abinda k’anwarsa take k’unsawa amman yayi alwashi da zuciyansa cewa sai ya taimaki mutanenda suka taimakesu suka fito dasu daga cikin halin ha’ula’i ………………….. ✍🏻

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *