AMININ MAHAIFINA CHAPTER 2

AMININ MAHAIFINA







CHAPTER 2



Sai dana kwashe lokaci mai tsawo a cikin farfajiyar gidan a tsaye kafin na samu kwarin gwiwar jan kafafuna da kyar na koma falon. Ina shiga na ci karo da er aikin gidan wadda saboda tsabar wata irin shiga mara fasali da tayi yasa na kasa gane ko wace irin yare ce, cewa tayi in zo muje ta nuna min dakin da zan kwanta inji madam dinta, babu musu na dauki jakar hannuna na janyo daya daga cikin jakunkunan dana taho dasu nabi bayanta bayan itama ta dauko wasu. Abinda na kula duka dakunan gidan a falon kasa suke, ni tunda nazo ban ga kowa ya hau saman ba. Wani dan madaidaicin daki cikin jerin dakunan dake cikin falon ta bude muka shiga ciki. Dakin yana da fadi ba laifi, Akwai toilet a ciki ga wani medium size gado ruwan golden, mirror da closet sai er karamar sofa da study table. A tsakiyar dakin an malala wani tattausan circle carpet baki, sauran dakin kuwa malale yake da wasu en ubansun marbles fari da gold, well, ba laifi ya burge ni sai dai yadda aka tsara dakin ne sam bai min ba. A raina nace sai na canza shi. Ina ta karewa dakin kallo har ta gama shigo min da kaya na duka, ta tambayeni idan Akwai abinda nake bukata? Kai kawai na girgiza mata tare da mata godiya, ta min sai da safe ta wuce abinta. Jakar hannuna na jefa akan gado na samu gefen gadon na zauna Ina kara karewa dakin kallo, tashi nayi na leka toilet, Shima babu laifi ya hadu, na dawo na bude closet din babu komi a ciki sai er guntuwar kura data yi, tsumma na lalubo na goge ta tas na lalubo turaren kaya a cikin kayana na watsa a gefen closet din kafin na fara shirya kayana a ciki, sai dana cika ta tsil da kaya wasu ma da kyar suka shiga, na makare kan mirror na da tarkacen kayan shafa dana kwalliya da nau’in perfumes kamar a wani dan karamin super store. Sallar isha’i nayi na hada da shafa’i da wutiri, ina gamawa naji wayana tana kara, ringing din dana sakawa daddy ne. Da sauri na tashi na daga kiran, gaisawa muka yi ya fada mun sun isa gida lafiya, mun danyi hira kadan yaba mommy wayar itama muka dan yi hira, sai data kara min da en nasihu akan wadanda ta min sannan muka yi sallama na ajiye wayar. Ruwa na watsa a jikina na nemi kayan barci marasa nauyi na saka na kwanta, amma kwata-kwata barci yace bai san idanuna ba, tunanika iri-iri suka dinga min yawo a kwakwalwa, daga karshe waya ta na dauko na fada duniyar gizo.


Washegari kamar yadda na saba da asubahi na tashi nayi sallah, shiru Ina kan abin sallah a zaune ina debating akan in fita in taya matar gidan aiki ko kuwa in zauna a daki? Daga karshe dai kawai na tashi na fada wanka, usual ways din harkokin rayuwata na bi, kwalliya data kwashe ni kyawawan mintuna talatin, minti ashirin na fiddo kayan sawa da shiryawa, zuwa lokacin dana tsaya a gaban dogon yaro ina sake duba kaina, karfe bakwai da mintuna ashirin. Cike da tunanin yadda zan karasa cikin makarantar BUK na fito falo, babu kowa a cikin falon amma na jiyo motsi a can wata kofa dake gefen dakin matar gidan. A hankali na karasa tare da lekawa, hangame baki nayi kamar zai rabe biyu. Wani dankareren kicin dana gani wanda zan iya cewa ya lunka dakina sau biyu, kayan
kayan electronics na kicin babu kalan wanda babu. A gaban gas cooker na hangi er aikin gidan tana soya plaintain, karasawa wajenta nayi muka gaisa cikin girmamawa, na tambayeta matar gidan tace min wai bata tashi daga barci ba, Kai na gyada cike da mamaki. Wace matar aure ce ke kai karfe takwas na safe saura tana barci?? Tambayarta nayi yadda zan isa wajen IT dina, tace ai Direban da zai kaini yana waje yana jirana, tun dazu yayi magana. Juyawa nayi na fita, daga kicin din tace min breakfast fa? Nace mata zanyi acan. A farfajiyar gidan na hangi direban, a mutunce na gaida shi ya bude min gidan baya na shiga yaja motar muka wuce. Mintuna talatin mun shiga cikin BUK, har gaban microbiology lab muka je yayi parking, tare dashi muka shiga lab din ya samu lab attendants suka yi maganganun da zasu yi, ya tafi ya barni bayan ya fada mun lokacin da zai dawo ya dauke ni. Ina zama sai ga Ramla sun shigo ita da Antin ta, nan muka rungume juna cike da murna, itama Anty Halima tafiya tayi ta barmu anan. Da yake ranar farkonmu ce a wurin babu wasu ayyuka da muka yi, wajen karfe goma sha daya muka fito ni da ita zuwa Cafeteria din dake cikin department din. Tafiya muke yi a hankali, tsarin makarantar ya burgeni kwarai, er hira muke yi da ita game da wajen har muka shiga cikin cafeteria din, babu students sosai zama kawai muka yi muka yi order din abinda zamu ci. 2

Muna gama cin abincin lab muka koma, lab attendants din were very friendly don haka cikin dan kankanin lokaci muka saba dasu. Wadanda suke yin aikin project dinsu sun kawo ayyuka, nan ne fa muka tashi muka fara aiki. Sai wajen karfe biyu muka tashi, wani dan karamin garden muka zauna muna ta hirarmu ni da ita ina jiran Direba yazo tunda ita sai ta jira Anti Halima ta gama ayyukanta, sai wajen karfe biyu da rabi sannan Bala Direba ya iso. Ina hango motar na gane ta saboda a cikinta muka zo. Da sauri nawa Ramla sallama na tashi nayi wajen da yayi parking, a mutunce na gaida shi na bude bayan motar na shiga.
Wata kyakkyawar yarinya cikin kayan makaranta dogon wando navy blue da shirt fara ta dago kyawawan idanunta tana kallona, ban san lokacin dana sakar mata murmushi ba saboda tsananin burge ni din da tayi, a gaban motar kuma maza biyu ne suma cikin shigar kayan makaranta irin na yarinyar, duk suka juyo suna kallona. Zama nayi sosai a gefenta ina ta watsa musu Murmushi yayin da direba yaja motar, yarinyar da nake tunanin shekarunta zasu kai bakwai zuwa takwas tace min ke ce bakuwar da daddy yace zata zo mana gida? Na gyada kai ina kallonta, nice beauty, ya sunanki? Murmushi tayi, sunana Hafsah amma daddy yana ce min pretty Hafsey, su yaya Abdallah kuma suna ce min Hafsatu… Ta karasa tana pouting cike da shagwaba. Er dariya nayi tare da jan kumatunta, “kai amma Yaya Abdallah bai kyauta ba! Hafsatu ai sunan tsofi ne” ta gyada kai tana turo baki tare da kallon wanda yake kama da shine babban yayansu, “ai kullum sai na gaya mishi amma sai yace wae ai nima tsohuwar ce” na kalli yaron Ina Murmushi, “Yaya Abdallah baka kyauta ba gaskiya, tana yarinyarta ka dinga ce mata tsohuwa?” yaron yayi dariya, “sunan maman Daddy gareta pa, don Allah ba tsohuwar kenan ba?” daya yaron na gefenta ya kwashe da dariya, “tsohuwa ce mana, baka ga har ta fara furfura Akanta ba?” Hafsat ta kai mishi duka a kafadar shi, ya kauce yana mata dariya. Tsokanarta suka ci gaba dayi suna dariya har sai data fara kwalla sannan na tsaida su, “here, enough with the teasing, a kyale pretty haka nan ko?” ta gyada kai tana min murmushi, kanta na shafa ina jinta har cikin raina. Yarinyar tana da wani irin kyau duk da suma sauran yaran suna dashi amma ai kun san kyan mace ya banbanta dana namiji, ina mamakin inda ta gado shi a raina nace kila sai dai wajen mahaifinsu don babu mai kama da mahaifiyar su, dama dama dai Qaseem mai bin Abdallah, naga suna dan yanayi da Anti Mubeenah. Kafin kace me mun saba da yaran, dama ni bani da wahalan sabo suma naga hakan a tattare dasu. Muna isowa gida na dauki school bag din Hafsat ita kuma ta rike lunch box dinta, hannunta cikin nawa muka shiga falo ina taya ta miming din wakar twinkle little star. A daya daga cikin kujerun falon, Anti Mubeenah ce zaune ya harde tana duba jarida, yaran suka zube a gabanta suna bata labarin makaranta, sai dana bari suka gama hayaniyar su sannan na duka na gaida ta. Fuskarta dauke da dan murmushi ta amsa tare da ce min Akwai abinci a kicin, godiya na mata tare da cewa sai nayi sallah, dakina na wuce nayi sallah, na janyo wayata na kira mom don nasan daddy yana office ni kuma ban cika son kiranshi a wajen aiki ba, mun jima muna hira da ita kafin muka yi sallama, ana kiran sallar asr nayi na janyo system dina na kunna kallo tunda babu abinda zanyi, da a gida ne kila na shiga kicin ina taya mommy na girkin dare.
.

Ina zaune anan ina kallo Hafsat ta shigo cikin kayan makarantar islamiya, na daga Kaina na kalleta ina dan murmushi, “pretty Hafsat an dawo ne?” ta zauna a gefena tana turo baki, “malam ya bamu aiki a makaranta kuma ban iya ba, gashi Abbu da yake koya min karatun baya nan” zama nayi sosai akan gadona nace bani littafin in gani, ta bude jakar ta ta miko min na duba, Tawheed ne, tambayoyi akan imani. Murmushi nayi na kalleta nace “yanzu dai je ki kiyi sallahr magriba tunda an kira, bayan isha’i sai ki dawo mu yi” da murnarta ta tashi ta tafi, har ta kai bakin kofa ta dawo da gudu ta rungume ni, “Aunty thank u” dariya nayi na bita da kallo har ta bar dakin, kai na girgiza na tashi na fada bandaki. +

Bayan sallar isha’i ina kan sallaya a zaune Qaseem yayi sallama ya shigo dakin, yace Aunty Nafeesah wae Mami tace kizo mu ci abinci, ba musu na tashi nabi bayanshi don dama yunwa nake ji. A kan dinning na samesu su duka suna cin abinci, gefen Hafsat naja kujera na zauna. Ganin kowa serving din kanshi yake yi yasa na dauki plate na bude flask din abincin, tuwo ne kaman na semovita miyar danyen kubewa, tunda naga miyar tsululu kamar ba danyen kubewa ba nasan cewa tuwon sai a hankali, Illa kuwa ina kai loma daya bakina da kyar na hadiye, tuwon gashi nan latab kamar danyen gari alamun bai gama dahuwa ba, miyar sai dan banzan yaji kamar da taruhu kadai aka yi ta, babu taste ko na anini sai shegen karnin kifi. Da kyar na iya hadiye lomar farko, ban yi kuskuren kai wata bakina ba don na tabbata idan na kuskure ta sake shiga bakina sai na amayar da dan guntun abincin daya rage a cikina. Su kansu na ga tsakura kawai suke yi, kallonsu kawai nake yi cike da mamaki. Ta ya za ayi mutane su rayu da irin wannan abincin a duniya? Koda yake yau ne karo na farko dana ci abincin gidan, ban sani ba kila rana ce ta bacewa mai girkin kawai, da wannan tunanin na gyada kaina na tashi daga kan table din bayan na wa Anty Mubeenah sai da safe. Dakina na koma naje nayi brush na wanke bakin da mouth wash, cikina wani irin hautsinawa yake yi saboda yunwa, jikar dana fita da ita dazu na bude, wata irin ajiyar zuciya na sake ganin Pack din cookies din New Yorkers, na manta dashi ma ni shaf dazu muka saye shi a cikin makaranta. Zama nayi akan gado na bude shi na fara ci, wayata na hannuna ina chatting, Hafsat ta shigo dakin. Tare da ita muka cinye cookies din, daga nan na koya mata aikin da aka basu, kallon film dina da nake kallo muka ci gaba dayi sai wajen karfe goma da rabi ta min sai da safe, na shafa kanta nace ki tashi lafiya pretty., kar ki manta pa kiyi addu’ar kwanciya barci kinji? Ta gyada kai, “thank u Aunty, sai da safe” na dan hade fuskata, “ohh pretty, sau nawa zan gaya miki bana son Aunty dinnan? Call me Yaya Nafee, bai fi dadi ba?” ta girgiza kai cikin tsokana, “babu dadi gaskiya” kofar dakin na nuna mata “oya, bi can sai da safe” ba musu ta tashi ta fita tana er dariya kasa-kasa. Tana fita na janyo wayata ina kallon screen din, a cikin messages nake ina shawara da zuciya ta akan abinda nake shirin aikatawa, daga karshe dai nayi typing, *”you sleep?”* na turawa Muneer, tsawon mintuna sha biyar babu amsa, na sake tura *”seems like you are, good night!”* na kashe wayar na dorata akan bedside table na kashe wuta tare da yin addu’ar kwanciya barci na kwanta.
Nayi tunanin idan na tashi zan ga reply daga Muneer ko kuma missed call dinshi, sai dai har na gama shirina tsab babu shi babu alamun shi. Sai zuwa lokacin ne na fahimci imma dai yana sane yaki min reply jiya ko kuma yayi barci wulakanci ne ya hana ya biyo sahuna da safe, kwafa nayi ina jijjiga kai. 2

Ranar ma dai abincin safen sai godiyar Allah, plaintain ne aka soya da shayi da soyayyen kwai, tsakani na da Allah nasan ba zan iya cin abincin nan ba, haka nan dai na dan tsakura har zuwa lokacin da Bala yazo muka dunguma gaba daya har su Hafsat muka fita. A mota daya muka tafi dasu, sai da muka biya ta makarantar su muka ajiye su sannan muka wuce. Da rana koda muka dawo bamu samu Anti Mubeenah a gidan ba, har dare bata dawo ba sai bayan isha’i likis sannan. A zaman sati dayan da nayi a gidan zan iya cewa zama ne na takura, if not for Hafsat dasu Abdul I didn’t think I would’ve survived. ita dai matar gidan yadda na kula da ita, bata cika jan mutane a jikinta ba, ni dai tunda nazo gidan ban ga bare ya leko ba, makota ne, abokai ko dangi. Tsakanina da ita gaisawa ne kawai, idan mun hadu a dinning mu danyi hira sama-sama, ga yawo, idan ta saka Kafa ta fita daga gidan tun safe sai dare take dawowa duk da Hindatu mai aikinsu naji tace tana da saloon da take kula dashi. GA er aikinsu kuwa ban ma san me zan ce ba, ni ban ga dalilin da zai sa in dauko er aiki ba kuma ba zata min gamsasshen aiki ba in kyaleta duk da cewa ni har ga Allah I dont have any plan na daukar er aiki Ina nayi aure, ga Hindatu dai kam abin babu bayani, ita ba ga girki ba, ita ba ga gyare-gyare ba. Aikin data iya daya; ta sha kona sanwa idan ta dora ta fara kallo. 3

A takaice dai kafin zagayowar ranar juma’a sai da naji Kano ta fita daga raina, ni ban saba irin rayuwar kadaici dinnan ba. Ranar juma’ar kuwa Ina dawowa daga wajen IT dama dan karamin kit dina a Shirye yake tsab, Anty ta fita yawon data saba sai sako na bari a wajen Hindatu nace tace mata na tafi weekend gida, dama Daddy ya turo wanda zai dauke ni, a farfajiyar gidan ma na dawo na tarar dashi yana jirana don haka babu bata lokaci muka wuce Kaduna. Sai wajen karfe biyar da rabi muka isa gida saboda yanayin go slow da muka samu a hanya kafin mu fita daga cikin Kano, da ihu na da komi na shiga gidan, kit dinma sai driver ne ya shigo min dashi. Mommy tana kicin tana girki ita kadai, na rungumota ta baya ina tsallen murna, juyowa tayi tana kallona cikin murmushi, “oh ni wannan yarinya tawa ban san yaushe zata girma ba” na buga kafa cike da shagwaba nace “mommy!!” dariya tayi ta rungumo ni jikinta cikin nuna kewa. Dakina na shiga an share min shi tass sai tashin kamshi yake yi, na cire kayan jikina na fita zuwa kicin na kamawa Mommy girkin, muna yi muna hira, yawancinta tambaya ce akan wajen da nake zaune, babu matsala dai ko? Kina cin abinci? Tambayoyi dai iri-iri. Muna nan Daddy ya dawo, har cikin kicin din ya shigo ya daga ni sama Cak yana juyi dani, dariya na saki na rirrike shi har ya dire ni kasa. Sannu da zuwa na mishi ya amsa yana shafa kaina, na amsa brief case din hannunshi na raka shi har dakin shi kafin na fito na barshi ya shirya.
Bayan isha’i muna falo zaune akan babbar tabarmar cin abinci, hira nake musu, duk abinda nake yi a Kano babu wanda ban tsallake ba, su kuma suna sauraro cikin nuna rashin gajiyawa na dariya su yi, na mamaki kuma su jinjina kai. Ranar kam sai wajen karfe sha daya muka yi barci muna ta hirar yaushe gamo. Kwana na biyu a gida na koma Kano cike da kewar iyayena, ji nake kamar inyi zama na acan. 1

Hindatu kadai na samu a gidan, tace yaran dama a gidan kakannin su suke yin weekend, ita kuma Anty Mubeenah tace wajen bikin kanwarta mawuyaci ne ma idan ba kwana zata yi a can ba, na jinjina kai tare da kwaso tsarabar fruits dana musu a hanya na shirya su a cikin fridge. Wajen karfe takwas na dare ina zaune gidan shiru babu motsin kowa, nasan da su Hafsat suna nan da yanzu suna dakin ko dai muna hira ko kallo ko kuma ina koya musu assignment. Horn din mota naji a bakin gate kafin naji karar bude gate, a raina nace Anty Mubeenah ta dawo kenan. Hasken motar ya ratso ta cikin windown dakina zuwa cikin labulaye na da yake window din dakin a kusa da garejin gidan take. Minti kamar biyar na bata na tashi na fita da niyar inje in mata sannu da zuwa. Tsaye a jikin fridge hannunshi dauke da gorar ruwan Sanah yana sha directly daga cikin gorar, hannunshi daya rataye da suit dinshi yana kuma rike da brief case. Dogo ne ba can ba, idan da ba don na sanshi a hoto ba to da zan iya rantsewa da Allah ince bashi bane, saboda ko a cikin hoton ban hangi yarintar dana gani a tattare dashi ba a lokacin, da nace yarinta ba wai ina nufin yaro bane, aah Ina nufin wanda bai kai girman daddy na ba; Abban su Hafsat ne. Wata irin gigicewa naji nayi, haka kawai naji kafafuna sun yi wani irin sanyi wanda ban iya daurewa ba sai dana dangana gwiwoyina da marble din dake malale a tsakiyar falon, ban sani ba tsabar kwarjinin da yayi min ne yasa gabana ya tsananta faduwa ko kuwa wani abu daban?? Cikin rawar murya nace “sannnnnu da….. Zuwa…… Abbbbuh!!”………

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *