AMININ MAHAIFINA CHAPTER 3

AMININ MAHAIFINA





CHAPTER 3







Wasu kyawawan idanu farare tas suka dago suka kalleni, ban sani ba ko tsananin hasken da falon yayi ne ta dalilin hasken chandeliers din falon ko kuwa idanunshi ne a haka? Brown eyelids suna ta wani sparkling da sheki, haka kawai na tsinci kaina da faduwar gaba. Ya sauke robar ruwan daga bakinshi ya jefa ta cikin waste bin tare da cewa, “lafiya qalau Nafeesah! Kin zo bana gari koh? Hope komi lafiya?” na gyada kaina da kyar, wani irin nauyin mutumin naji ya dabaibaye ni. Ya gyada kai, “OK!” ya wuce dakin Anty Mubeenah abin shi. Kafa na na masifar rawa na tashi na fada daki, hannuna dafe da kirjina kamar wadda take kokarin tsayar da racing din da zuciya na take yi wanda ya wuce misali. Idanu na zare sosai ina kallon reflection dina a jikin mirror, I couldn’t believe wai a haka na fita gaban Abbu. Kafar wando na daya a gwiwa, gashin kaina wani yayi baya, wani ya zubo a kafaduna, wani kuma ya tattare a gaban goshina saboda hular dana saka., idan ka ganni dai a lokacin babu bata lokaci zaka danganta ni da psychiatric patient dinnan irin stage one ma, kunya ta rufe ni sosai kamar in nutse a kasa haka naji. Tsalle nayi na dira akan gado na fara birgima, sai da nayi kaca-kaca da gadon sannan na saurara ina maida numfashi…
2

Karfe bakwai da mintuna biyar na safe na fito daga dakina a shirye na tsab, babu kowa a cikin falon. Kan dinning an shirya kuloli manya masu kyau, kila saboda dawowar maigidan ne aka fiddo sabbin kuloli don ban taba ganin irin su a gidan ba. Na bude kulolin, farfesun kan sa ne sai kamshin er daddawa da tafarnuwa yake yi, sai masa fara tas itama tana ta tururi a cikin wata kula, kunun gyada har da kosai. Kujera naja na zauna na zuba farfesun na fara ci kunnena har motsi yake yi, duk yadda aka yi abincin ba daga cikin gidan yake ba, idan ma daga gidan yake to ba Harira er aikin su bace ta dafa. A raina nace kila Anty Mubeenah ce ta dafa, Amma koda wasa ban ji kamshi yana tashi ba jiya ai. Na dai ture tunanin komi na ci gaba da dura abinci abu na, ina nan zaune na kusa gamawa Anti Mubeenah ta fito daga dakinta sanye da wando da riga na barci, ni kaina ina mace sai da shigar ta bani haushi. Gabadaya kirar ta marar fasali ta fita, tumbinta da zai sa kayi tunanin cikin en biyu ne ya fito yayi nashe-nashe a gaban ta, gashin kanta yayi buzu-buzu dan ma wai tana da yalwar gashi babu laifi, fuskarta sai naso take yi bana tunanin tunda ta tashi da safe ta wanke ta. Nayi kokarin kauda takaicin ta daya taso min na gaishe ta, ta amsa a kaikaice tana wani basarwa irin yadda take amsa min ta bude kofar dake fuskantar dakinta ta shiga, ina tunanin nan ne dakin maigidan don ban taba ganin ta shiga ciki ba tunda nazo gidan. Ni dai na gama cin abinci na na wuce abina. A farfajiyar gidan Malam Bala yana jira na, cike da girmamawa na gaida shi na bude bayan motar da kaina na shiga saboda na hana shi ya dinga bude min. Y’all ja motar muka tafi har cikin makaranta, ranar an kai wasu sabbin en IT lab din daga Leather Research Zaria don haka bamu samu cunkushewar ayyuka ba. Cikin dan lokaci muka saba dasu. Ranar tun karfe daya da rabi muka tashi, bayan mun fito daga lab din Zainab da Ikram suka mana sallama suka wuce gida, ni da Ramlah muka zauna a dan karamin garden din da muke zama muna tattaunawa akan saurayinta da yake so ya tura gidansu ita kuma tana ki wai bata so tayi aure yanzu ni kuma ina nuna mata rashin dacewar hakan, muna nan na hangi motar gida tana tunkaro mu duk da ba wadda aka saba kawo ni bace amma nasan duk motocin dake gidan, wannan shine karo na farko ma da aka zo daukar mu da motar, Anty Mubeenah naga tana jan motar. Na tashi muka yi sallama da Ramlah na tunkari motar, sai da nace tazo mu sauke ta tunda gidan su a hanyar mu yake amma tace zata jira Anti Haleemah don haka na kyaleta. Tun daga nesa Hafsatu ta fito daga cikin mota a guje tana min oyoyo, na tare ta da dan guduna muka fara juyi a wajen kamar wata yarinya, sai da muka gaji sannan na ja hannunta muka tunkari motar. Sai dana jira ta shiga sannan nima na shiga, na daga baki da niyar gaida Malam Bala kamar yadda na saba, “Malam Bala barka da war hak…..!” naji maganar ta kakare min sakamakon wanda na gani a gaban motar yana kokarin tada ta, da saurin na sadda kaina kasa tare da cewa “Abbu ina yini?” ya amsa idanunshi na kan titi. Ji nayi kamar wadda aka jefa ni cikin kankara, na kasa maida hirar dasu Qaseem suke min kamar yadda muka saba idan muka taho sai dai in gyada kai ko in bisu da uhm da ehh har muka isa gida. Cikin sauri na bude murfin motar na fita har ina hadawa da tuntube, ban tsaya a ko ina ba sai cikin dakina. Na zauna a gefen gado ina ajiye numfashi da kyar da kyar, ni kam me ke damuna ne haka? Ni dai nasan bani da wahalar sabo da mutane, amma me yasa a gaban mutumin nan nake ji na kamar wata haliita daban? Me yasa na kasa sakewa dashi? Me yasa nake jin kwarjinin mutumin har cikin tsakiyar kaina? Wata zuciyar tace min saboda ban jima da sanin shi bane, after all babban mutum ne kuma idan zan iya tunawa tun daga kan abokan daddy na har zuwa en uwanshi ni dai bude ido nayi na gansu tare, wannan kuwa daga sama kawai na san dashi, hakan da nake ji rashin sanayya ne kawai, idan na saba dashi komi zai daidaita. Da wannan tunanin naji na samu hope, na maida bayana na kwantar akan gadon tare da lumshe idanuna, a hankali barci ya sure ni, nasan biyan bashi ne tunda jiya ban samu nayi barcin kirki ba.Sai wajen karfe biyar da rabi na yamma na tashi daga barcin, toilet na shiga nayi wanka na fito na kimtsa jikina cikin wasu simple Pakistan riga da wando marasa nauyi, turare kadai na fesa a jikina da yake bana yin Sallah sai na koma kan gado na fara sana’ar chatting da kallace-kallacen film. Babu wanda ya leko dakina sai bayan isha’i Hafsat ta leko wai inje mu yi dinner, ina jin yunwa amma jin muryar Abbu a falon yasa nace mata a koshe nake, tayi tayi dani naki fita dole ta juya ta tafi tana gunaguni. Can kuma sai gata ta dawo dakin, “wai Abbu yace mai kika ci?” nace ban ci komi ba, Tun lunch ne amma ciki na a cike yake. Ta juya ta tafi, mintuna biyu ta sake dawowa, “Abbu yace ki fito ki ci abinci ko ran ki ya baci!” nayi shagaraaaa da baki ina kallonta cikin rashin abin cewa, ganin bani da niyar tashi yasa ta juya tana fadin “bari inje in gaya mishi kin ce ba zaki zo ba” da sauri na tsayar da ita tare da tashi tsaye na lalubi hijabi dogo har kasa na saka, Hafsatu ta saka ni a gaba kamar wadda zata gudu har gaban dinning table din Inda suke zazzaune bayan ta gama mitar wai gidan wa zan je dana saka hijabi, ban tanka mata ba, fargabar yadda zan zauna a teburi daya da Abbu ta cika min ciki, tsakani na da Allah ina jin kunyar shi. Naja kujera daya na zauna a hankali kamar wadda tayi laifi, daga Qaseem sai Abdul a wajen sai shi Abbu din Anty Mubeenah bata nan ban sani ba ko bata gidan ne? Tun kafin in gaida Abba ya tare ni, “wasa da cin abinci ko Nafeesah??” na sadda kaina a kunyace nace “Abbu na koshi ne” ya girgiza kai, “that’s not an excuse, dokar nan gidan ba a skipping meals uku ko da wasa, idan ma mutum bai jin yunwa sai ya tsakura, idan kuma ya ki dura muke mishi koh?” ya kalli su Qaseem kamar yana tambayar su, yaron ya gyada kai yana er dariya wadda ta fito mishi da goyen hakoran shi, ni kaina I couldn’t help it sai da nayi er dariya jin abinda yace, yace oya ci abinci. Babu musu na dauki spoon na jefa cikin jollop shinkafa da aka yi an kawata ta da nama, kifi, coleslaw da wainar kwai. Kamar dazu da safe abincin yayi dadi sosai kamar kunnen mutum zai tsinke, ga zobo mai sanyi a gefe ya sha kayan kamshi an yanka kankara, apple, cucumber da wasu nau’i’kan fruits dana kasa tantance ko menene. A nutse muke cin abincin, su Hafsat suna hirarsu da Abbu jefi-jefi su kan Sako ni a ciki ina amsawa da uhm ko a’ah, tun dai ina nodding har na dan sake na fara maida musu amsa sosai, Abbu yake tambayana game da karatu na ina bashi amsa a nutse. Muka gama cin abincin na kwashe kayan duka na kai kicin, sauran abincin da drink din na saka su a freezer su kuma kayan na wanke su tass. Falon na koma na zauna don Hafsat tayi kini-kini ta hana ni tafiya dakina dole na zauna a cikin su, su Abdullahi game suke yi a laptop din Abbu ita kuma Hafsatu na canza channels, bayan dogon lalube muka tsaya a mbc 3 suna hasko Despicable Me part 1. Muna cikin kallon muna kwasar dariya ni da Hafsat, gabadaya mun hade falon da hayaniya. Abbu ya fito daga dakin da yake fuskantar dakin Anti Mubeenah sanye da bakar jallabiya a jikinshi, take nayi tsit kamar bani ce nake ihun dariya ba. Ya zauna a kujera tare da daukar Hafsat ya dora ta akan cinyar shi tare da kallona, “are u a kindergarten kike kallon cartoon da girman ki??” kafin inyi magana Hafsat tayi caraf tace “Abbu tana dasu da yawa a cikin system dinta, har dasu na Disney princesses da fairy tales da…….” ta fara jero mishi sunayen films kala kala ni wasu ma ban rike su ba, Abbu sauraren ta kawai a yake yi yana gyada kai amma fa idanunshi suna kaina, hakan yasa naji gabadaya kamar wadda aka zare mata duk wani kuzarinta. Sai data gama lissafin sannan ya magantu, “wato dama saboda fina-finai kika sa aka sai miki laptop ba don karatu ba koh?” nayi saurin girgiza kaina, “a’ah Abbu! Ina yin karatu fa. Akwai text books a ciki da yawa da videos dinsu kuma Akwai docs da dama duk a ciki, da gaske ina yin karatu” ya kalli Hafsat, wai?? Ta gyada kai da sauri ehh Abbu, watarana ma tana koya min, kuma har Assignment take koya mana ni dasu Yaya Abdullahi. Ya daga gira daya, “Ohh really? A wani mataki kike a Islamiya?” kaina a kasa nace “nayi saukar Al-Qur’ani mai girma, na gama harda watanni biyar da suka wuce, na sauke littafin Umdatul-Ahkam, Riyadussaaliheen, Tafseerul-Jalalaini da Tafseerul-Ibn-Khatheer, da littafai da dama. Na fara Annissa’u war-rijaalu fil jannah amma ban gama ba har yanzu” yace “Mashaa Allah! I am impressed gaskiya” na sadda kaina kasa ina murmushi zuciyata cike da kaunar iyaye na da suka tsaye min na samu karatu mai inganci, tun ina primary six na sauke Al’Qur’ani mai girma, ban fara harda ba sai dana sake yin wata saukar sannan na fara tare da wasu manyan littafai na addini nasan ko a haka na tsaya Alhamdulillahi bani da matsala amma ban tsaya din ba, har yanzu ina cigaba da karatu na duk da cewa har gida Malamin yake zuwa yana koya min. Ganin ban yi magana ba yasa ya cigaba, “da alamu nima zan kawo nawa littafan ki dinga koya min don cikin wadanda kika ambata Akwai wadanda har yau ban gama su ba, zaki koya min?” mamaki ya matukar Kama ni, duk cikin saukin kan mutumin ne haka ko kuwa wani abu daban? Dana rasa abin cewa sai kawai nayi murmushi na maida kallona ga TV ba wai don ina fahimtar abinda ake yi ba anymore, sai don in janye yawan tambayoyin Abbu wanda nasan da kyar ne in samu amsoshin su. Ina ji yana tambayar Hafsat karatun ta tana gaya mishi abinda suka yi a Islamiya ranar, ta karanto mishi Hadisi da Qur’an ya saurara tare da gyara mata Inda ta kuskure. 1

Karfe tara da rabi suka gama film din da muke kallo, Abbu ya umarce mu da muje mu kwanta saboda makaranta. Sai da safe muka mishi kowa ya wuce dakin shi, anan muka bar shi yana danne-dannen laptop. Ina shiga daki su Mommy na kira don gabadaya ranar bamu yi waya dasu ba, muka gaisa dasu mun jima muna hirarraki kafin na musu sai da safe muka kashe wayar. Bayi na shiga na kimtsa jikina nazo na kwanta.

Washegari abincin mu marar taste da armashi ya dawo, Ashe wanda muka dinga ci daga gidan su Abbu aka kawo shi. Ni dai na tsakuri iya wanda zan iya ci na tashi, suma yaran haka nan dai suka tsattsakura muka tashi muka tafi makaranta. Ranar juma’a kamar satin daya wuce, ina dawowa naci karo da direba yana jira na, sallama nawa Anty da Hareera na tafi Kaduna wajen Mommy da Daddy na.


●●●●●●●●●●

Kimanin wata na daya da zuwa Kano, na riga nayi adopting da garin da yanayin gidan da nake zaune. Abbu bai cika zama a gida ba, it’s hardly yayi sati daya cur a gida, yawanci zuwa seminar ko kuma harkokin shi na kasashen turawa, na Ji Malam Bala ne ranar nan yace wai suna shirye-shiryen bude wani kamfanin kirar kayan sawa ne a China shi da abokan shi. Anti Mubeenah ma dai bata cika zama a gidan ba, yawanci ko tana gidan ma bata cika zama a falo ba shi yasa har zuwa lokacin bamu wani shaku da ita ba, tsakani na da ita gaisuwa ne kawai. Abin yana matukar daure min kai, ban taba ganin wani daga cikin dangin Abbu ba a gidan, amma nata da abokanta suna yawan zuwa har yini suna yi, daya daga cikin nasihun da Mommy ta min lokacin da zamu taho Kano shine kada in kuskura in shiga harkar da babu ruwa na, banda shisshigi da sa ido a rayuwar mutane, don haka na kauda kaina daga rayuwar su, koma meye ke faruwa dai rayuwar su ce ba tawa ba. 3

          Wannan satin ina gida ban je Kaduna ba saboda su Daddy sun tafi Malumfashi wajen bikin dan gidan Yayan Daddy din, ina zaune a daki ranar assabar da safe Hafsat ta shigo dakin, a shirye take tsaf cikin riga da siket na atamfa da dankwalin atamfar a saman kanta bata daura ba. Na kalleta da mamaki nace Hafsy ina makaranta ne yau baki je ba? Tace “hutu muke yi ai” na kalli kwalliyar da tayi nace “ina zaki je?” ta langwabar da kai, “Yaya Nafee ke da na gaya miki yau sunan Anti Raliya kanwar Daddy?” na dan dafa kaina, “na manta ne wallahi, har zaku wuce kenan?” ta gyada kai, “mu duka fa zamu tafi, idan kina so ki zo muje” cike da jin dadi na kalleta don dama gabadaya na takura da zaman hakanan da nake yi tun safe, nace “really? Can I??” tace why not? Bari in jira ki shirya. Dama ban dade da fitowa daga wanka ba, a gaggauce na shirya, na saka wata doguwar rigar material sky blue dinkin buba ne ta min tsaf a jikina, ban yi wata kwalliya ta azo a gani ba na shafa turare kawai na dauki gyale na yafa. Na kalli Hafsy nace “mu je?” dankwalin hannunta ta miko min tana turo baki yadda ta saba idan tana jin rigima, “dan Allah ki daura min irin yadda kika yi dinnan ranar nan?” ba musu na amsa na nada mata shi kamar gwaggwaro, ta kuwa yi kyau sosai wayata na dauka muka fara hotuna har sai da muka Ji karan horn sannan muka fita da sauri. Su duka suna cikin motar Abbu picnic yana zaune a seat din direba Anti Mubeenah a gefenshi su Abdullahi kuma a baya, ban san ko yaushe Abbu ya dawo daga tafiyar da yayi ba don tun ranar Laraba baya nan babu mamaki jiya da dare zai dawo. Gabadayan su suka bimu da kallo ni da Hafsy har muka shiga motar, a nutse na gaida Abbu. Thank goodness na daina jin wannan faduwar gaba da rikicewar idan ina kusa dashi, yaja motar a hankali muka bar farfajiyar gidan muka cilla kan titi. Muna baya ina nunawa su Abdullahi hotunan da muka yi ni dai Hafsy su Abbu kuma suna hirarsu shi da Anti Mubeenah kadan kadan Abbu ya kan juyo ya kallemu ko yaja Hafsy da hira har muka isa Gwamna Road inda anan ne ake sunan, ko shiga gidan Abbu bai yi ba yana ajiye mu ya juya tare da cewa bayan Magriba zai zo ya dauke mu.Muna shiga gidan sunan su Hafsat suka yi nasu wurin ko dakin mai jego basu karasa ba. Ni da Anty Mubeenah muka karasa har uwar dakan mai jegon lokacin babu mutane ma sosai, aka dan yi en gaishe-gaishe Anty ta hakimce a gefen gadon ta janyo wayar hannunta ta fara danne-danne da kiraye-kirayen waya. Gabadaya naji na takura don bansan kowa a wajen ba gashi su Hafsat sun bace a cikin gidan kwata-kwata, wata farar mata ta shigo itama kana ganinta Kasan er uwarsu Abbu ce don ga kama nan kamar an tsaga kara, da dan saurinta ta shigo tana mitar ina su Ni’ima suka shiga ne sun barta da aiki ita kadai? Ta kalli sauran matan dake dakin tace ku taso muje mu gama aikin samosa din can don Allah kafin rana tayi mana, duk suka mimmike yayin da Anty Mubeenah ta kara hakimcewa akan gado, ni kam ganin zan takura na tashi na bi bayan wadanda suka tashi. A can BQ suke yin aikin, na shiga na kama musu muka fara aikin suyar Samosa, Anti Amina kamar yadda naji ana kiranta ta Kalle ni tana murmushi tace “kece wadda take IT a gidan Ibrahim ko?” na gyada kaina, tace ai last week na sha labarin ki wajen Hafsat har sai da kunnuwana suka gaji. Nayi er dariya nace Ai Hafsat Akwai surutu, ta gyada kai. Kafin mu gama aikin mun saba da Anti Amina sosai, su Ni’ima suka dawo dauke da plastic robobi wadanda za a zuba soye-soyen da za ayi a ciki, kusan dukan su sa’annina ne Sa’adiya ce ta girme mu sosai don ta bamu kusan shekara uku zuwa hudu, dukansu suna jami’ar Bayero ita Ni’ima a level two tana mass comm yayin da Sa’adiya take shekararta ta biyan karshe a BS.  Kafin kace me mun saba dasu kamar wanda muka yi watanni da sanin juna, muna gama suyar samosa din muka fara shirya abubuwan a cikin robobi muna sawa a cikin Leda, abinci dama odar shi aka yo. Sai gab da la’asar muka koma cikin gidan, Anti Mubeenah bata nan wai ta tafi gidan wata er uwar su dake aure anan cikin unguwar, ina jin kananun maganganu na tashi game da halayen Anti Mubeenah din kun san taron mata ba a raba shi da kananun maganganu balle harka ta hado ku da dangin miji dama sai a hankali, ni dai nayi kunnen uwar shege dasu naki maida hankalina kansu don ba harkar shiga ta bace. Wanka muka sake yi Ni’ima ta bani wasu riga da siket na Swiss lace na saka saboda nawa na lalata su da abun fulawa sun yi fari tas. Bikin suna yaci gaba da gudana lafiya qalau, ina daga cikin masu kai da kawo na entertaining din baki, kawo abinci, dauke kaya, daukar gifts din maijego da wasu abubuwan. Duk Inda na motsa da sannun Anti Ameenah nake motsawa, naga alamu na shiga ran matar sosai. Anti Ameenah itace babbar Yayar su Abbu kuma babbar diya a wajen Alhaji Mad’udu Galadanchi, su shida ne wajen iyayensu kamar yadda Sa’adiya take bani labari, Anti Ameenah ce babba sai Abbu, sai Anti Rahina, Aminu Yayan Sa’adiya yana Bangladesh yana karatu sai Sa’adiya da Ni’ima auta. Family din sun burge ni sosai a gaskiya, na kula da hadin kansu kwarai da gaske abin ya burge ni ba kadan ba, ina son ganin yan uwa wadanda suke kula da zumuncin su sosai.

Bamu muka samu kanmu ba sai bayan isha’i, mutane duk an tattafi sai baki na nesa da dangin maijegon na kusa, muna wani daki dake kusa dana maijegon inda anan muke bidirin mu, hira muke dasu Ni’ima lokacin da Hafsat ta leko dakin tace in fito Abbu yazo zamu tafi, na dan hade fuska jin an katse min hira mai dadi da muke yi amma haka nan na tashi saboda bani da yadda zanyi na fito su Ni’ima suka biyo bayana, dakin Anti Rahina na shiga da niyar mata sallama. Abbu na zaune a cikin falonta kusa da Anti Ameenah yayinda maijegon take zaune a kujera daya rungume da babynta da alamun hirar en u want aka ce ake yi na durkusa na gaida Abbu tare da yiwa su Anti Ameenah sallama, Abbu ya mike nabi bayanshi. Su duka har maijegon suka fito mana rakiya, su Qaseem na jikin motar Abbu din suna jiran mu, duka muka shiga cikin motar. Su Ni’ima suka leko suna kara min sallama dama mun yi exchange din number waya dasu, Anti Ameenah ta miko min wata Leda mai dan girma tana kara min godiya tare da jaddada min in fa nemi maganin ciwon jiki in sha ina amsa mata da toh, Mai jegon MA ta leko tana min Allah huta gajiya da godiya sosai. Abbu kam baki a sake yake kallon en uwan nashi cike da mamaki, wannan shine karo na farko da suka fito wai da sunan mishi rakiya, sai daga baya ya kula ashe ma ba shi aka yiwa rakiyar ba, kulawar daya kamata ace matar shi ce suke wa sun kare da ba wata can, abinda yakamata ace matar shi ce tayi suke mata wannan yabawar wata can ce ta samu romon. Koda yake bai ga laifin su ba, Mubeenah ita tayi wasa da garinta har yayi ruwa, shi kanshi yaji haushin abinda tayi yau a wajen sunan nan, ance tunda taje ta gaida mai jegon bata kara yiwa kowa magana ba ko Anti Ameenah bata gaida ba, daga baya ma suka ce wai ta ajiye musu dubu goma ta tafi tun kafin ayi Azuhur abinda ya bata ran Anti Ameenah kenan, ya girgiza kai cike da takaicinta, duk iya kokarin shi na ganin Mubeenah ta ra6u da dangin shi don su saba abin yaci tura.  Shi har bai san me zai mata ba kuma. +

Sai da muka gama sallamar mu sannan suka koma gefe suka tsaya suna kallonmu tare da daga mana hannu har Abbu yaja mota muka tafi. Tunda muka fara tafiya babu wanda yayi magana, su Hafsy tuni tayi barci akan cinya ta. Muna isa gida na ciccibe ta muka wuce Abdullahi ya dauko min ledar da Anti Ameenah ta bani, dakin Hafsy na fara wucewa na kwantar da ita. Closet dinta na bude na ciro mata kayan barci na dawo na cire mata na jikinta na saka mata wadannan, addu’ar kwanciya barci na tofa mata tare da sauka daga kan gadon a hankali gudun kar in tashe ta daga barci, ina juyawa naci karo da Abbu a bakin kofa a jingine yana kallon mu. Na sadda kaina kasa na je zan wuce ta gefenshi, packet din magani ya miko min, nasa hannu na amsa ina kallon shi cikin alamun tambaya, yace maganin ciwon jiki ne Anti Ameenah tace in baki, ki sha kafin ki kwanta. Na gyada mishi kaina, “sai da safe koh?” ya fada yana kaucewa daga bakin kofar dakin, na bi ta gefenshi na wuce ya bini da kallo. Ina shiga dakina kayan barci kawai na saka na afa maganin a baki, sai dana bata mintuna kusan goma yadda maganin zai yi settling a jikina sannan na kwanta, babu dadewa barci ya kwashe ni, ni kaina nasan cewa a matukar gajiye nake saboda ba karamin aiki muka sha a gidan sunan nan ba.

Sai karfe goma na safe na tashi, nayi mika mai tsawo ina jin ga6o6ina kamar an bubbuge min su, kai tsaye toilet na fada nayi wanka da ruwa mai dumi, nayi brush kafin na fito. Wandon jeans na saka wanda bai kama jikina ba da shirt, na daure kitson kaina a cikin tafkeken hair band na dora hula a kaina. Falo na fito saboda wata 
mahaukaciyar yunwa da take nanikata, babu kowa a cikin falon haka babu hayaniyar yara nasan suna makaranta. Anti Mubeenah na hakimce a kan kujera a falon da takardu a gabanta tana buga lissafi, na durkusa a gefenta ina gaidata. Hankalinta yana kan takardun ta amsa min, baki na dan tabe na mike, har ga Allah halayen matar basa burge ni, wata na daya a cikin gidanta amma wani idan ya ga yadda take yazga ni sai yayi zaton bakuwar jiya ce a wajenta. Kan dinning table na wuce kaina tsaye sai dai kwalam!  Babu komi, cike da mamaki na tsaya ina kallon wajen a raina ina tambayar ko lafiya? A iya sani na ni dai a gidan nan ko an gama cin abinci ba a dauke kayan sai idan za a sake shirya wani meal din. Daga bayana naji Antin tana cewa “Yau bamu yi girki ba, Harira bata nan taje garinsu wajen biki. Yara ma sai oats na dama musu, kije kicin kema ki dama anjima kadan zan bada a yo take away” na jinjina kaina cike da mamaki, oats? Yaushe rabona da in sha Abinnan? Kicin din na wuce, kulolin da aka yi amfani dasu ba a wanke ba suna cikin sink har sun fara wari, nayi iya dube dube na a kicin din ban samu abu mai sauki da zan saka a bakina ba don bazan iya dama oats Inci ba, kawai ledar da Anti Ameenah ta bani jiya ta fado min a rai da sauri na koma daki na janyo ledar na bude, tarkacen su doughnuts, cake, cincin dasu biscuits ne a ciki har da naman suna, falo na koma na bude fridge na dauko lemun exotic na dawo nayi daidai a tsakiyar daki na fara ci, sai da naji nayi nak sannan na tattare sauran na ajiye a gefen gado. Waya na dauko na bude, missed calls na gani bila adadin nasu Ni’ima dana Daddy sai wata bakuwar number da ban sani ba, su Ni’ima na fara kira suka min ban gajiya sannan na kira bakuwar number nan ashe Anti Ameenah ce, itama dai ban gajiyar ta min har sai data saka ni jin kunya yadda take ta yaba min tana sa min albarka, muna yin sallama da ita na kira Daddy, nan muka kwashe lokaci mai tsaye ina bashi labarin abubuwan da suka faru cikin week din, bayan mun yi sallama kan gado na koma na kwanta ina sake-sake, ban san iya lokacin dana dauka ina tunanika ba sai dai na bude ido naga karfe sha biyu tayi, a raina nace su Hafsat karfe biyu suke dawowa daga makaranta, and I can’t stop imagining ya suke manejin oats a cikinsu fiye da awowi biyar. Cimak na tashi na fita falo, Anti ta gama lissafin nata tana zaune ne kawai tana kallon tashar CBN, na zauna a gefenta nace “Anti me za a girka ne na rana naga su Hafsat sun kusa dawowa?” dagowa tayi tana kallona cikin wani kallo dana kasa gane ma’anar shi, ta yamutse baki kafin tace “ke har kin iya girki ne dama?” nace sosai ma, ina taya mommy idan tana yi. A raina kuwa cewa nake “a yadda nake jina akan girki Allah na tuba ai gani nake zan iya karawa ko da wani irin chef ne!” saboda ba yabon kai ba, dishes dai tun daga kan na hausa, na Yoruba da abinda ya danganci na mai jajayen kunne na kware a yin su don mommy na gwana ce in dai akan girki ne. Sai daga kare min kallo kafin tace ki dafa shinkafa da miya to, zaki iya kuwa? Na danyi murmushi kawai, da alamu gani take girki wani katoton aiki ne bata san a wajena kamar shakar ruwa ne, nace “zan iya Anti” tace to shikenan, je ki fara” babu musu na tashi na fada kicin din ina tattare hannun riga ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *