AMININ MAHAIFINA
CHAPTER 4
Tsaye nayi a tsakiyar kitchen din ina tunanin ta Inda zan fara, sai dana danyi sighing kafin na tunkari freezer na bude, kayan vegetables da nama ne da dangin kifi a shirye kala-kala a ciki saboda tsabar ajiya duk da cewa a cikin freezer suke amma sun fara sauya kama musamman vegetables din. Kashe freezer din nayi yadda zan samu in ciro kaya ta sauqi, na shiga store nan ma kayan abinci ne dankare kamar a super market babu nau’in da babu daga na gida har na waje. Maimakon shinkafa da miya sai nayi fried rice wadda na wadata ta da dangin veggies, na yanka hanta kanana a ciki. Na dauko fresh sardines na wanke na yanyanka shi na soya wanda zan yi decorating din shinkafar dashi. Ina tsaye ina slicing din albasa wadda zanyi onion sauce da ita, ban ji shigowar mutum kicin din ba sai magana naji a baya na, “what are you doing here?” na juya a firgice na kalli wajen da sautin maganar ya fito. Abbu ne tsaye a kofar kicin din ya rungume hannuwa a kirjin shi yana kallona, naji na diririce da kyar na iya cewa “ammmm…. Girki?!” na fada kamar ina tambayar shi, ya shaki numfashi yana lumshe idanu, yace “woah! What a delicious smell!! meye kike dafawa haka ya cika mana hanci da kamshi?” dan murmushi na saki kadan, “fried rice ne” yace I hope kin kusa saukewa? I can’t wait to taste it. Na gyada kai nan ma, nan da en mintuna zan sauke. Ya juya zai bar kicin din, “OK! I’ll go and take a shower then sai in dawo” ya karasa fita daga kicin din yana uttering “thank Goodness!” a kasan zuciyar shi, dama dawowa yayi yayi wanka ya fita ya samo musu abincin da zasu ci sai kuma yana shigowa yaji wani mahaukaciyar kamshin abinci yana fitowa daga kicin wanda ya taso mishi da yunwar shi ta kwana da kwanaki da yake dannewa da lemuka, yana shiga kicin din yaci karo da “beautiful sight’ a cewar shi, tana yanka albasa a cutting board cikin kwarewa kamar irin chief cook dinnan a 5 stars hotel, da kyar ya iya suppressing din urge din daya taso mishi na aikata wani abu da yasan will never ever be appropriate, wanda yasan mawuyaci ne idan bai zubar mishi da kimar shi ba a idon yarinyar na har Abadan. Sai kawai ya buge da jingina da bango. 1
Ina gama yin sauce din na juye shi cikin wani kwanon tangaran, itama fried rice din sauke ta nayi don ta gama, ta min yadda nake so kuwa, wara-wara, yellow shar sai tashin kamshi take yi, na fito da babban food flask na zuba ta a ciki. Oranges na dauko manya da apple da water melon, na bare lemun na saka a juicer ta markada min shi na tace ruwan, na yanka kankanar itama na cire yayan tas, na yanka ta kanana a cikin lemun tare da tuffa, na kawo syrup sugar na zuba a ciki na watsa kankara na fara ciccibar kayan zuwa dinning table. Ina gama shiryawa su Hafsy suka fado falon a guje da alamun gajiya a tare dasu, lokacin dana tare su sai na dinga jina kamar wata Mummy dinnan mai jiran ‘ya’yanta su dawo daga makaranta, nayi kokari na kauda weird tunanin daya lullube min zuciya na karbi jakar hannun Hafsy na kai mata daki, ai ko kayan makaranta basu cire ba kowa yayi settling akan kujera na fara serving dinsu kafin na zauna a gefen Hafsy nima na fara ci. Zo kaji santi kuwa, Qaseem har da cewa wai shekarata nawa a makarantar koyon girki? Dariya kawai nake musu acan kasan zuciyana kuwa jin kaina nake a sama, me yafi yabo dadi a duniya?? Abbu ya fito daga dakinshi sanye da wandon jeans da shirt na shan iska, Shima kan dinning din yazo ya zauna. Na mike na fara serving din shi abincin yayin da yake gaisawa da iyalan shi, na zuba mishi komi na ajiye a gaban shi na koma mazaunina na zauna muka ci gaba da cin abincin mu. Wajen cin abincin ya koma shiru, Abbu bai yi magana ba sai kai kawai da yake girgizawa, rashin magana ma yabawa ce. Sai da kowa ya cinye abincin plate din shi duka, suna gamawa kowa ya wuce dakinshi saboda ranar ba zasu koma makaranta ba. Na fara tattare plates din da muka yi amfani dasu na kai kicin, Abbu yana zaune a har a lokacin yana cin dura abinci a cikinshi cikin alamun rashin saurarawa, na fahimci matsananciyar yunwa a tattare dashi. Na kai hannu da niyar dauke jug din juice din da nayi, cikin rashin sa’a shima ya kai nashi hannun don haka nayi saurin janye nawa hannun amma duk da haka sai da hannunshi ya dan gogi hannuna, Ya Allah!! Wani irin current naji ya taba ni kamar na taba budaddiyar wayar wuta. Naja baya da sauri ina shivering, shi kam hannunshi ya kurawa idanu yana kallo kamar wani bakon abu kafin ya dago idanunshi yana kallona mai cike da ma’anoni wadanda na kasa pathorming abinda suke nufi. A hankali ya maida kanshi ga plate dinshi ya cigaba da cin abincin amma fa cikin rashin kuzari, ganin haka yasa sumi-sumi na wuce dakina kafafuna na shaking. Ina bada baya ya maida kanshi ya jinginar da kujera yana ajiyar numfashi da sauri-sauri, what the hell did he just felt??! Yake tambayar kanshi embarrassingly.
1
Ina shiga dakina na zube a bakin kofa rawar da jikina yake yi ta karu, Innalillahi!! Kadai naji bakina yana furtawa da karfi, da kyar na iya daidaita natsuwa ta. Wannan wani irin abu ne haka? It’s not as if ban taba gogar hannun namiji bane, God Forgive me amma ni har hugging dinsu nayi amma ban taba jin rabi rabin abinda naji ba yau da Abbu ya taba ni, ban taba jin hakan a tattare da ko wane namiji ba sai shi, ko me yasa hakan?? Ban zurfafa tunani na ba na mike na fara gyara daki na ba wai don yayi wani abu ba sai don bani da aikin yi kawai. Har bayan la’asar ina gyara, dana gama wayata na dauka na shiga dakin Hafsy, tana zaune a kasan carpet tana kokarin warware kitson kanta, na zauna a gefen gado ina kallonta, “ya ne pretty?” as usual sai data yi pouting kafin ta kalleni da dara-daran idanunta, “na manta ban fadawa daddy a kaini saloon ba har ya fita, kuma idan Anty Kate taga kaina a haka gobe sai ta dake ni!” na shafo kitson kaina nima ina kallonta, yakamata ma in tsefe shi don ya fara tsufa. Nace “to taho in taya ki” ta waro hakora, “yauwa, kin iya kitso ai koh?” na girgiza mata kai, ta 6ata fuska, nace “noo, kar ki damu, zamu san dabarar da zaa yiwa kan yadda Anti Kate ba zata taba min ke ba koh?” ta gyada kai tare da zuwa ta zauna a kusa dani. Haka kuwa aka yi, muna gama tsifar ta dauko kayan kitso dasu ribbons na fara gyara mata kai, kalba na mata manya wadanda na kayata da ribbons din da dutsunan kitso kuma ga mamaki na yayi kyau sosai, ita kanta data kalli kanta a madubi tsalle-tsalle ta hau yi. Ni kam dariya na mata na tashi na fada kicin don yamma tayi sosai, sakwara nayi da miyar ganye, na wadata miyar da nama da busasshen kifi, na hada fruit salad na kai komi kan dinning na ajiye. Da wuri na tattaro kan yaran muka ci abincin mu kowa ya koma daki ya kwanta duk a dabara ta na kaucewa haduwa da Abbu, sai Allah ya taimake ni har na koma daki bai dawo gidan ba. Sai da na gama shirin kwanciya barci sannan na jiyo tashin muryar su shi da Anti a falo da alamun tare suka dawo gidan. 1
Washegari tun da safe na fada kicin, potato chips nayi da egg sauce sai ruwan shayi wanda yasha kayan kamshi, na soyawa su Qaseem doya da kwai wanda zasu tafi makaranta dashi na zuba musu a lunch boxes dinsu, yin komi nake yi cike da kuzari da walwalata. Aikin daya jima yana burge ni kenan, kullum naje gidan Aunty Uwani ina ganin tana hadawa yaranta abincin tafiya makaranta irin haka, abin yana burge ni ba kadan ba, at last yau gashi dai nima na hadawa nawa. A gurguje na shirya na fito saboda lokaci daya fara wucewa, yanzu ma mu hudu kadai muka ka
kadai muka karya don daga Abbu din har ita Aunty din babu wanda ya fito, muka gama karin mu muka wuce makaranta.
1
Gabadaya kwanakin girkin gida da kula da gidan ya koma hannuna yayin da ita uwar gida mai gayya mai aiki kullum sai dai tayi rashe-rashe sai dai a dafa ta zauna taci ta tashi ta kara gaba abun ta babu godi bare na gode, dama dama ma Abbu. Yana nuna jin dadin shi kwarai game da hakan, ina kuma shan godiya a wajen shi sosai wanda ina ga hakan ne yasa nake dagewa tun karfi na ina musu dadadan girki wadanda zasu sa zuciyar shi a farin ciki yayi ta mun addu’ar daya saba, halin Aunty kam tun ina damuwa dashi har na daina. Matar is really complicated, gane halinta da Inda ta saka gaba abu ne mai wahala kam, to mai wahala mana. Ban ka kula da cin abincin miji, baka san shan miji ba, Baka san gyara muhallin mijinka ba, ba ido na saka musu ba, amma nasan bata kwanan dakin miji, ko ina suke ko a gaban wa suke she is always making it obvious that bata damu da mijinta, rayuwar Aunty Mubeenah fa tana bukatar gyara sosai da sosai. Allah Allah nake juma’a tazo in wuce Kaduna, va wai don na gaji da hidimar da nake yi dasu ba in fact, kwanaki biyar zuwa shidan da nayi ina yiwa Abbu da iyalan shi girki has been the best and happiest moment na rayuwata, sun kara min kusanci da iyalan, sun kara min so da qaunar su kamar yadda suka kara musu sona da qaunata. Kawai dai nayi kewan su Mommy da Daddy ne don haka ranar juma’a da wuri na dawo na hada kayan da nasan zan bukata, Abbu baya gari yayi tafiya ranar Thursday. Direba yana zuwa na fito tare da kulle gidan don babu kowa, Hajiya Aunty Mubeenah an tafi neman kudi bayan babu abinda ta nema ta rasa a gidan auren ta.Abinda na karanta kenan daga wayana bayan na shiga dakina, Kimanin awowi biyu da dawowa na kenan. Na duba kasan message din inda nake zaton zan ga sunan wanda ya turo text din saboda babu suna a jiki sai number kawai. *’_Galadanchi!’* shine sunan dana gani. Crap! Abbu ne!! Zuciyata ta hau fadi ina jin tana wani tsalle-tsalle, wayar na zurawa idanu ina lalubo abinda zan tunana amma komi ya tafi blank, na lalubo su da kyar na shiga jefawa kaina su kamar ni ce Abbu din, “Friday message kuma? Why would he?” zuciya ta tace stupid! Kuma ba zai miki message ba kike nufi ko me? You know this is a normal thing tsakanin mutane yanzu, ke da Daddy da sauran uncles dinki ba kuna exchanging irin wannan messages din a tsakanin ku ba?? Na gyada kai a hankali kamar wawiya, sai a lokacin kuma na gano shirmen da nayi, God! I can be silly sometimes, saboda Allah addu’a ya min mai dadi amma ban amsa mishi ba na hau tuhumar dalilin da yasa ya turo min sakon. Da kwarin gwiwa ta na tura mishi amsa, *’Ameen Abbu, and same to you. How’s your presentation? Allah ya dawo daku lafiya Ameen!’*. Shiru har aka dauki lokaci babu reply, na daga kafada ta, watakila I’ve gone too far ne, meye nawa na wani tambayar yadda harkokin shi suke tafiya kamar wata shakikiyar shi? Na tabe baki na tashi daga kan kujerar dana zauna don wai da zama nayi ina jiran amsar shi kamar wata sakara. Kayan jikina na shiga cirewa ina jifa dasu cikin laundry bin, na daura towel a jikina nazo fada bathroom. 1
☆☆☆☆☆☆☆☆
Idanunshi kur akan wayar yana kallo cikin wani irin yanayi, kalmomi ne da rabon daya jisu daga bakin matar auren shi har ya manta su, anya ma ya taba jin su kuwa? Ta yaya ma aka yi tasan cewa presentation yaje? He can’t recall telling her, wani sashe na zuciyar shi yace ba mamaki wajen su Pretty taji don ya kula tana son yarinyar sosai, yana mamakin yadda idan suna hira da Hafsy take maida kanta kamar yarinyar har ka kasa tantance yaro da babba a cikinsu. Ya lumshe idanu a hankali…… Bai san cewa ya zurfafa a tunani ba sai daya ji muryar Chairman dinsu ta microphone, “Dr. Galadanchi?? Anything from you??” yayi firgigit ya dawo daga duniyar imagination daya tafi, “yeah of course Mr. Collins…” ya jefa wayar shi a aljihu ya dauki wasu takardu ya tafi kan step fara bayani a nutse….
●●●●●●●●●●
Wannan weekend din ziyara nayi, naje gidan Anti Uwani na musu yini a can, daga nan ni da AbdulJalal muka shiga gari sai bayan isha’i ya sauke ni a gida bayan mun tsaya a Mcbae mun sayi tarkacen chocolates da ice cream. Washegari lahdi sai wajen karfe biyar na bar gida cike da kewar Mom da Dad, amma fa can kasan zuciyana wani farin ciki da doki ne dankare a cikinta, dokin in koma inci gaba da yiwa Abbu dadadan girki na yana ci yana yaba min har da santi. Sai dai koda na isa sai na tarar Hareera ta dawo daga biki, Abbu kuma baya gari, gwiwa na yayi sanyi sosai, jiki a sanyaye na shige daki na.
Washegari a tsaitsaye muka ci abinci muka wuce makaranta, ranar mun sha ayyuka a lab kamar me! A matukar gajiye muka zauna akan dakalin da muka saba zama ni da Ramlah cikin dan garden din da muke hutawa, na kalle ta ina dan murmushi, “ke jiya fa muka hadu da Muneer” bata nuna alamun abun ya dadata da kasa ba kamar yadda nayi zato, tayi fuskar shanu tace a ina? Nace “McBae, mun shiga siyayya ni da AbdulJalal. God! Baki ga yanda gayen nan ya kara kyau ba, yayi fari yayi kiba sosai, I think he misses me so much, kin kuwa ga irin fara’ar daya dinga min? Rabona da in…..” tayi saurin katse ni, “ai fa kin kika fara bada labarin Muneer kamar wata radio mai jini ba kya ko son kiyi shiru, to sai ki tashi an zo daukar ki” na kalli inda suka saba tsayawa idan suka zo, gabana ya fadi sosai, Abbu ne yazo daukar mu! Ganin Qaseem ya fito yana tunkarar wajen da nake yasa na mike ina lalubar jakata nawa Ramlah sallama. A hankali kuma a sanyaye na bude bayan motar na shiga, “Abbu ina yini?” na furta cikin siririyar murya ta, ya amsa “lafiya qalau Nafeesah, ya kika baro Kaduna?” na amsa da lafiya lau. Yaja motar muka tafi babu mai furta uffan. Hafsat ce ta ciro drawing book dinta daga cikin school bag dinta tana nuna min Assignment din dana taya ta jiya akan zanen gidaje da motoci, tace “Kuma Uncle Jamilu yace ni na cinye 20 over 20 duk cikin class din” na shafa kanta ina murmushi, “Ohh that’s very good princess, am proud of you” tayi dariya tana kwantowa a jikina na rungume ta. Muna isa gida sallah muka yi, na bude fridge na ciro fura da nono dana kawo daga gida, musamman Mommy ta bada aka yi, na zauna na dama ta da dan kaurinta na saka kankara da dan sugar, cups na dauko na zuzzubawa su Abdullahi. Muna zaune a falo muna sha kafin lokacin zuwa Islamiyar su yayi. Abbu ya fito daga daki hannunshi dauke da jakar laptop dinshi, dan karamin coffee table din dake gefen mu ya janyo ya dora laptop din nashi akai, kasa kasa yake kallon mu har ya zauna. Ya kalli kofin dake hannuna yace meye wannan kuke sha haka babu tayi? A kunyace nace fura ce! Idanunshi suka dan ware cikin mamaki, “wow, daga ina muka samu fura?” Hafsat tayi caraf tace “daga gidansu tazo da ita jiya!” ya jima sosai idanunshi suna kaina ban san ko tunanin me yake yi ba, ya kauda kanshi ya maida shi ga laptop dinshi, “tunda ba a mana tayi ba ni zan yiwa kaina, a bani idan da akwai” da sauri na tashi naje na dama mishi na kawo na ajiye mai a gefenshi. Su Hafsy suna wucewa makaranta na koma dakina na zauna ina kallo. +
Tara da rabi ta nuna lokacin dana kalli agogo, nayi mika ina hamma ina jin kasusuwan jikina na amsawa saboda gajiya, ban kai ga kwanciyar da nayi niyar yi ba na jiyo kamar muryar Abbu a falo yana kwala min kira. Na saurara sosai har zuwa lokacin dana sake jin wani kiran kafin na warci hijabi na zura na fita, yana kan dinning a zaune yana kokarin rufe daya daga cikin food flasks din da aka ajiye akai, ya kalleni fuskar shi dauke da
wani irin expression dana rasa ko wani iri ne; na jin haushi ne, embarrassment ne ko fusata? Shi dai ya bar wa kanshi sani. Na dan duka a gefenshi nace Abbu gani a sanyaye. Sai da yayi gyaran murya sannan yace “Please samo min noodles ko simple abu da zan ci, am quite hungry” na danyi jim kamar ba zan tashi ba suna da er aiki, yana da matar shi, ba za a ga laifi na ba idan na tashi na fada kicin na dafa mishi abinci? Koda yake ban ga laifin shi ba, abincin da Hareera tayi yau yadda kasan faten shinkafa saboda yadda shinkafar ta cafke, ita kanta Anty Mubeenah sai data mata fada yau dai har da ce mata idan ba zata gyara ba to lallai tana gab da barin gidan don ita ta gaji haka nan…. Abbu ya dan sake gyara murya ya kalle ni, “well??” nayi saurin dawowa cikin hankali na, “umh…. Dama zan ce ne noodles din kadai ta isa?” ya gyada kai, da sauri na tashi na wuce kicin cikin hardewar kafafu, zuciyana na gaya min cewa idanunshi shi a kaina suke. Tukunya na dora akan gas na hada duk abubuwan da nake bukata, ruwan yana tafasa na zuba indomie a ciki na kara da sardines, na dora ruwa a cikin kettle na zuba danyar citta da kanumfari er garlic don naga alamun kamar mura tana dan damun shi. Ina sauke indomie din na soya kwai na dora a sama, na juye shayin a cikin flask na dora duka kayan akan tray mai fadi na fita. Yanzu ya dawo tsakiyar falon ya zauna hannunshi rike da waya yana karatun labarai, na ajiye su a gefenshi na tura indomie din gaban shi da fork a ciki, na dauki kofi na tsiyaya shayin na mika mishi, shayin ya fara kaiwa bakin shi, ya dan yamutse fuska yana kallon shayin jin kamshin tafarnuwa na tashi, da sauri nace “umh… Naga kamar kana mura ne shine…..” na kasa karasawa saboda kalmomin sun kare min kuma sai ya girgiza kai kawai ya fara kurbar shayin a hankali. Naje na dauko mishi ruwa da lemu irin wanda naga yana sha masu rangwamen sanyi a cikin fridge na kai na ajiye a gefenshi, “Abbu kana bukatar wani abu kuma?” ya girgiza kanshi, “babu Nafeesah, nagode. Sai da safe koh?” na tashi da sauri na bace a wajen. Duk zaman da nayi jina na dinga yi kamar akan kaya, zuciyana wani irin duka take kamar zata tsaga kirjina ta fito, ban san me yasa Abbu yake da wani irin effect a kaina na saka ni cikin rashin natsuwa ba. 3
Washegari ba laifi anyi abinci mai sense don mun zauna mun ci sosai, Abbu ya kalle ni yana ajiye spoon din hannunshi, “Nafeesah ko zaki iya dora min shayi irin na jiya?” a hankali na saci kallon Inda Anty take zaune, abincin ta take ci Hankalinta kwance kamar bata san Allah yayi ruwan tsirar mu a wajen ba. Na dan jijjiga kai na tashi, cikin mintunan da basu gaza bakwai ba na gama na juye a cikin flask, na hada da cup na fito falon. A gaban shi na ajiye su, ya kalle ni yana furta thanks! Kafin ya kalli su Hafsy, “oya a tashi a tafi koh? Malam Bala yazo” duk suka mike kowa yana daukar school bag din shi, muka musu sallama muka tafi.
Muna zaune da Ramlah a lab muna hira na kalleta, “babe ya za ayi ne? Ina bukatar wankin kai da kitso fa kaina yayi datti wallahi” tace ba damuwa, idan mun tashi sai mu biya ta saloon din Anty Haleemah, nima ranar Saturday naje aka wanke min” nace “to shikenan”. Muna tashi kuwa Allah yasa su Malam Bala sun zo kenan, nace su wuce gida kawai ni Akwai inda zani. Muka je saloon aka wanke min kaina aka min kitso, da yake ba laifi Masha Allah ina da gashi sosai, Mommy irin bakaken fulanin nan ne, na gado zubi da kira irin tasu da kuma yalwar gashi, kalar fatar jikina kuma ta daddy ce, haka dangin shi suke wankan tarwada duk da cewa Akwai farare, kyawawan dara-daran idanu farare tas da bakaken eyelids, dogon dan siririn hanci kamar an zana da biro, dan karamin zagayayyen baki da jerarrun hakora kanana kuma farare tas da er siririyar wushirya a tsakiyar su. Muna gamawa da saloon gidan Anty Haleemah muka wuce, gidan flat ne dan madaidaici mai kyau dakalin ganshi kaga gidan mutum daya. Mijinta navy ne don haka bai cika zama a gidan ba, tare suke zaune da kanwar mijinta Khaleesat,mun dan saba da ita saboda a cikin BUK take karatu, tana yawan zuwa wajen Anti Haleemah din. Danta daya Mahmoud, nan muka wuni a gidan sai bayan Magriba ta hada ni da direba ya maida ni gida, kafin mu isa tuni an kira sallar isha’i. A bakin gate ya ajiye ni, na gaida maigadin gidan na wuce ciki. A hankali na tura kofar falon na shiga baki na dauke sallama, babu kowa a cikin falon. Na maida kofar na rufe na fara tafiya zuwa dakina, kamar daga sama naji maganar, “Where the heck have you been???”. A gigice na juya, Abbu ne zaune akan kujera yana kallona kamar a fusace? Cikina ya bada sautin kululu…. It seems like m in trouble.