AMINIYATA CE CHAPTER A
👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
(Mrs nura kuriga)😘🌹
Dedicated this page to fatima zarah💃🏻
1⃣to5⃣
Da sunan Allah mai rahma mai jin qai, da ya sake bani dama na sake rubuta wani sabon littafi, Ina rokan Allah daya bani ikon kammalawa dan alfarman annabi Muhammad (s a w)
“Zeena ce zaune a class tayi uban tagumi, ta rasa maike mata dadi, mlmn maths nata musu bayani amma bata ma San yana yiba, kaman daka sama taji ana kiranta da sauri ta d’ago kai, ta saki murmushi da kara, suka rungume juna ita da Mysha, Zeena tace haba friend why are you late today,I though you are not coming today, Mysha tayi murmushi tace sorry Zeena na raka daddy airport ne daka nan driver ya Kawo ni, mlmn maths ne Ya katse su tare da fadin Zeena nd Mysha keep quick please, kasan cewan makarantan kudi ne, ba’a takura ma yaran sannan teachers din kaman tsoran student din suke, domin skul din sai dan wane da wane, kowa na tsoran ya bata ma student rai, kar allura ta janyo garma, Zeena tace sorry sir, yaji
gaba da gudanar dasu, har ya fita, wani ya shigo, har aka fita break, Zeena suka je, yin break suna tafiya suna fira har suka karasa restaurant din skul din, ga snacks nan kala2 sai wanda kaga daman ci, Zeena ta dauko musu ice cream Mysha kuma ta dauko, cookies suka nufi kan wani table suka ajiye kayan sannan suka zauna, suna ci suna fira, Mysha tace Zeena kin San wani Abu kuwa? Zeena tace a’a sai kin fada, Mysha taci gaba da cewa daddy dazu muna hanya zan raka shi airport yake cewa wai ina Gama secondary skul zai min aure, Zeena ta zaro ido tace what? Sai kace a zamanin da, may be he is joking, mysha tace no Zeena he is not joking, Ya dade yana yin wannan maganan, kuma daddy inya fada Abu toh he is serious, Zeena tayi shuru tare da tausayin kawar tata, can tace toh ke Mysha bakya kula kowa, yanzu wa zaki aura, Mysha tace nima abunda nake tunani kenan, yasa koda yaushe nake jin wani iri idan na tuna bani da saurayi wanda nake so, Zeena tace toh ke yanzu mai zaki fada ma daddy dinki inya tambayeki akan wanda zaki aura, Mysha tace nima ban San amsa din ba, ke gwara ke ko yanzu akace ki fito dashi zaki Kawo shi, duk da ban taba ganinshi ba, har yanzu, Zeena tayi murmushi taji an Kawo zan cen prince dinta, Mysha tace wannan murmushin fah, a dai2 lokacin wani yaro mai suna afraz yazo kusa dasu ya kafa ma Zeena ido kaman tsohon maye yace sannunku yan mata, Mysha ce ta amsa, yace ya naji kunyi shuru, yaci gaba da fadin Zeena wai mai yasa koda yaushe indai kika ganni saiki canza fuska, ki duba duk skul din nan ko wace yarinya so take yau ace ina kulata, amma ke na rasa dalili da yasa bakya so inzo inda kike, Ya kalli Mysha yace please Mysha am I not handsome, Mysha tace you are, infact ma babu macen da zata ganka bata kuma kallonka ba, yayi murmushin jin dadi yace thank, sannan ya kalli Zeena wanda ranta ya Gama baci da Mysha yanda take wasa shi, ta mike da nufin ta wuce, ganin haka yasha gabanta, Ya tare ta, tare da fadin Zeena you better stop this nonsense, how dare you ina magana kina wani tashi zaki wuce, duk wanda suke wajan hankalinsu ya dawo garesu, ta kalleshi ido cikin ido tace you have to know 1 thing I really hate you, I hate everything about you, infact ma bana son ganinka, tsayawa yayi yana kallonta da mamaki, dama zaiga irin wannan ranan har mace ta tsaya tana gaya mishi magana duk yanda yake da kyau ga kudi ga aji, yan mata suke rubi binshi, amma yau y’a mace take wulakanta shi, a gaban mutane, ihun da akeyi a wajan yasa ya dawo daka tunanin daya fada, a dai2 lokacin Zeena ta wuce Mysha ta rufa mata baya, yayin da afraz yaji kafanshi yayi mishi nauyi wani irin kunya ya rufe shi, amma haka ya fita, kai tsaye wajan motanshi yayi yashiga ya tada ta, Ya fita daka skul din,Sheraton hotel ya nufa ya kama d’aki, Ya kwanta idonshi yayi ja babu abunda yake tunani sai abunda Zeena ta mishi, Ya kasa komai Ya tashi dakyar yaje motanshi ya dauko kwalban codein ya kwankwade, sannan ya samu bacci ya dauke shi, a lokacin da Zeena da Mysha suka nufi class, Mysha tace Zeena kin San mai kikayi kuwa? Zeena cikin tsiwa tace mai nayi, tell me, Mysha tace Kin San afraz kuwa kin San waye shi kuwa, Zeena tace ban sani ba ban kuma fatan in sani, plz indai kin San maganan shi zaki min, plz leave me alone, jin haka Mysha tayi shuru, amma a cikin xuciyanta tana tsoran abunda afraz zai mata domin hatsabibi ne, gashi ta wulakanta shi gaban mutane, skul din duk an baza labarin, a lokacin da aka tashi Mysha tabi Zeena dan ta ajiye ta a gida, yau bada matan ta tazo ba, kasancewan ta raka daddy dinta airport, dukansu babu mai magana, can Zeena tace Mysha mai yasa kikayi shuru baki cewa komai, Mysha tayi Dan murmushin yake tace mai zance Zeena wlh ina tsoran afraz, ban San mai zaiyi ba, Zeena tayi dan murmushi tace plz Mysha kinga ni harna manta shidin banza wlh bai isa yamin komai ba, nafi karfinshi, ita dai Mysha jinta kawai take, domin afraz bama a skul dinsu ba, kaf garin Abuja dakyar ne kaji wajan da ba’a sanshi ba, baya ji gashi idan yana son abu, ko miye sai yasan yanda ya mallake shi, kota halin ‘ka’ ka wannan kenan da haka har suka karasa gidansu Mysha ta ajiye ta, ta wuce gida,+
Wacece Zeena?
Zeenat abubakar yan asalin garin katsina ne, su uku iyayensu suka mallaka, akwai yayanta adeel wanda yake karatu a kasar Japan sai ita dake aji hudu a famaks sai kanwarta mai suna aysha, suna kiranta da abda, sun taso cikin gata duk da irin gatan da suke ciki suna karatun islamiya kuma sun San addini dai2 gwargwado, mahaifinsu senator ne sau biyar yana ci saboda mutum ne mai rikon Amana kuma dadtijo ne, duk irin kudin da Allah ya mishi bai bar yayanshi sun lallace ba, yana tsaye akan iyalinshi, mutum ne mai son yaga yara sunyi ilimi sai yasa Zeena bata tunanin aure duk da, tana da saurayi wanda yake matukar sonta itama tana sonshi amma baya kasan nan yana China yana kula ma mahaifinshi da wasu aiyuka wajan shekara biyu, kullum suna makale a waya kaf gidansu babu wanda bai San zaheer ba, Zeena mutane da yawa suna mata kallon miskilanci don bata cika son yima mutane magana ba, in kaga ta kula ka toh babban dalili ne, sabanin kanwarta Mysha mai son magana, har wasu na mamakin kaman can nasu, sun hadu da Mysha a skul suka kulla kawance har suka hada iyayensu kawance.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
(Mrs nura kuriga)😘🌹
Dedicated this page to zee baby💃🏻
6⃣to🔟
“sai wajan shabiyu da wani abu afraz ya farka daka baccin daya dauke shi, Ya tashi tare da mika, komai daya faru duk ya manta, amma ganinshi a hotel yasa ya fara tuno abunda ya faru, lokaci daya yayi tsaki tare da fadin, Zeena you will regret it, toilet ya fada yayi wanka, Ya fito ya shirya ya nufi gida, kai tsaye dakin shi ya nufa, Ya fada kan gado yayi ruf da ciki, yana ta sake2 a ranshi, da haka bacci ya kuma dauke shi,
Zeena ce zaune akan dinning suna breakfast ita da abda, tana yi tana kallon agogo, har mahaifiyarsu wanda suke kira da ummi ta karaso, tace Zeena wannan saurin fah, tace ummi banso inyi late ne, muna da test yau ban samu nayi karatu ba jiya, so inna shiga skul da wuri zan Dan karanta wani abu, ummi tace yanzu na rasa dalilin da yasa bakya daukan karatunki da mahimmanci, kwata2 kinsa wasa inda dane aida kin San abunda kika taka, wai maike damunki ne Zeena? Tayi shuru ganin ummi din ta kafeta da ido yasa tace ummi nima kaina ban sani ba, ummi ta kuma kafeta da ido tana son ta fahimci wani abu daka yar tata, amma ganin babu abunda zata fahimta yasa ta canza maganan da fadin yau in kin dawo daka skul zaki rakani wani waje, ta amsa da toh ta Mike, abda tace ummi nima dani zaki koh? Tayi Dan murmushi tace yes my dear tasa dariya a dai2 lokacin skul boss din su abda yayi horn ta fita da sauri ta wuce.+
Mysha da Zeena suna zaune a study room suna ta karatu gefe kuma wasu student ne suma suke ta faman karatun, jin kaman tsayuwan mutum a kanta yasa ta d’aga kai, hada idon da sukayi saida gabanta ya fadi, amma ga mamakinta sai taga yana mata murmushi, ta tashi zata bar wajan, yace haba Zeena mai yayi zafi haka, tace afraz please ka fita daka harka na, bana son kana shiga cikin harkoki na, Ya kafeta da ido yace Zeena dan na miki magana nayi laifi ne? Tayi banza dashi ganin haka yasa ya kwace littafin dake hannunta, ta waigo cike da masifa amma ganin ya tamke fuska gashi sun hada ido, yasa tace plz kaban book dina, Ina karatu, kaman bazai bata ba, komai Ya tuna kuma oho, Ya mika mata littafin, tana amsa tabar wajan, Mysha ta tashi itama, amma jin ya kira sunanta yasa ta tsaya, yace ina son magana dake, tace ina jinka, yace wai mai zanma Zeena ta soni, ni inma samu ta dinga kulani, Mysha tayi shuru can tace afraz mai yasa baza ka barta ba tunda bata sonka, akwai wanda take so, tana fadin haka tabar wajan, Ya bita da kallo tare da wani murmushi wanda shi kanshi yasan dalilin yinshi.
Ummi ce cikin wani tsadaddan leshi mai kalan milk colour flower din jikin leshin kuma purple, yayi mata bala’in kyau, ta nufi dakin Zeena taga itama ta shirya cikin wani material red nd golden, dinki doguwan riga, yayi mata kyau sosai, ummi tace muje Dan Allah kin cika bata lokaci, Zeena tayi murmushi tace na gama ai, ta dauko wani karamin gyale ta yafa, suka fita, cikin wata mota suka shiga mai Kiran Prado, driver yaja su, Zeena tace ummi wai ina zamu haka ne, ummi tayi murmushi tace Mrs hakeem ce ta gaiyace ni dinner gidanta, tace owk, tun daka nan ta kama bakinta tayi shiru, Mrs hakeem wata kawar ummi ce mijinta minister ne na agricultural, sun karasa gidan, sunga motoci da yawa na mutane a gidan daka gani gidan cike yake da mutane, sun shiga falon makil da jama’a Ana ta ciye2, Mrs hakeem na ganin ummi tazo da sauri ta rungumeta sannan suka zauna, Zeena ta gaida ta, ta amsa cike da fara’a, ummi tace wai miye na hada wannan taron? Mrs hakeem tayi dariya tace yau 35yrs da auranmu, ummi tace wow har kun kai haka gskiya lokaci na gudu, anci ansha kowa ya watse daka gidan.
Wayan Zeena keta faman ringing, tayi dan gajeran tsaki ta dauka, ganin sunan mai Kiran yasa tayi sauri ta dauka, tare da fadin hello, ta dayan bangaran ya amsa da gimbiya ta, Ina kika shiga inata kira? Tace sorry dear bacci nake yi, karan Wayan nema ya tashe ni, yace kina bacci kin manta dani, tayi dan murmushi tace ni na isa, yace gest watch, tayi shuru can dai tace fada min, yayi dariya yace ina naija, dazu na sauka, tace what a surprise, amma baka kyauta min ba, shine baka gaya min ba, yayi dariya yace amin afuwa, cikin shagwaba tace anyi ma, yace gobe ina nan tafe, tace sai Kazo nayi missing dinka sosai, yayi murmushin jin dadi yana mamakin jin kalaman nan daka bakin Zeena, wanda ya tabbata baza ta iya gaya mishi tayi missing dinshi a gabanshi ba.
Washe gari Zeena anata shirye2 na taran adeel, Ana ta girke2 kala2 dasu drinks kala daban2, duk wanda yaganta yasan tana cikin farin ciki, bayan ta kammala komai taje tayi wanka ta shirya cikin wani leshi mai ruwan Zuma, da zanan baki a kai, yayi mata kyau sosai, tayi kwalliya na kece raini, duk wanda ya ganta saiya yaba da irin suranta da kyau da Allah yayi mata, ta zauna tana jiran zuwan gwarzon nata don tun dazu ya mata waya yace yana hanya, komai an jera a falon saukan baki, sai kamshin turaran wuta yake.
Wayanta ne yayi kara ta dauka, da sauri ji tayi yace gani a gidansu, tace gani nan, da sauri ta fita, ta iskeshi a mota, yana jiran zuwanta, ta karasa gareshi, Ya kafeta da idon nan nashi, wanda yake rud’a ta, itama kallon nashi ta tsaya yi, Ya kara kyau da wani haske, yace wow my princess kin kara kyau da girma 2yr rabon mu da ganin juna, tayi Dan murmushi tare dajin kunya, tace mai fito mu shiga ciki babu musu yabi bayanta, har falon baki, Ya zauna cikin daya daka kujerun falon, Ya kafe ta da ido, yana mamakin irin girman data kara, da kyau, wani irin sonta yaji yana kara shiganshi, tare da burin yaga ya mallaketa, ta matsa kusa da jerin kayan ciye2 da aka ajiye a falon ta zuba mishi coconut juice, ta mika mishi ya amsa tare da murmushi yasha, sannan ya kalketa yace Zeena har yanzu kina sona kuwa? Ko an kwace min ke, sai taji nauyin maganan daya mata, tayi kasa dakai, a dai2 lokacin Mysha ta shigo falon da sauri tare da fadin ina bakon namu, gabaki daya komai nata ya tsaya ta kasa ko motsi, sai dai a zuciyanta take ta nanata wa, tsarki ya tabbata ga Allah wanda yayi wannan hallita, adeel ne Ya katse mata tunani da fadin Mysha right?mai makon amsa sai tayi murmushi wanda ita kanta bata San tana dashi ba, ta karasa shigowa falon ta zauna, Zeena tace ya akai ka gane ta? Yayi dan murmushi yace nasan itace daka yanayin yanda ta shigo, Zeena ta kalli Mysha wanda ta kafe adeel da ido, tace sai yanzu koh, tace kiyi hakuri Zeena baki mukayi sai yasa banzo da wuri ba, haka suka zauna suna ta fira cikin nishadi, har adeel ya tafi yaba Zeena tsaraba da yawa, itama Mysha ya bata nata.
Mysha ta kasa tsaye ta kasa zaune sai kaiwa da kawowa take a dakinta, tabbas adeel ya hadu kalan namijin da take mafarkin samu kenan, ko wace mace zatayi burin yau ace ta mallake shi, a matsayin miji, wata zuciyan tace mata Mysha mai kikeyi haka, saurayin aminyar ki ce wanda take matukar so, kaman ranta, Ya kamata ki cire wannan tunanin a ranki, dan bai kamace ki ba.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
(Mrs nura kuriga)😘🌹
Dedicated this page to zee baby💃🏻
1⃣1⃣to1⃣5⃣
“Zeena kwance tana waya tana dariya koba a fada ba, da adeel take waya,tace adeel kaima kasan yanda nake sonka, bazan iya son kowa ba, kaman ka, zan iya hakuri da komai amma banda kai, Kaine komai nawa, daga ban garanshi yayi wani sayyanyan ajiyan zuciya tare dajin dadin kalaman nata, yace Zeena naji dadi dajin wannan maganan naki, dama inaso inyi miki magana mai mahimmanci, gabanta ya fadi, amma saita daure tace ina jinka, yace ba maganan waya bane gobe zanzo muyi magana, tace shikenan Allah ya kaimu, sukayi sallama.
Yau juma’a shot day kuma, a yau mahaifin Zeena zai dawo daka tafiyan da yayi na wajan wata daya, gidan Ana ta shirye2 kwata2 Zeena bata cikin kuzahari, dakyar ta shirya ta tafi skul,+
Suna zaune a class English teacher nata faman yin bayani amma Zeena bata ma San mai take fada ba, ba wani Abu ke damunta ba, sai fargaban mai adeel zai fada mata mai mahimmanci, english teacher ta kira sunanta Zeena what are you thinking? Idon kowa ya dawo kanta, mai makon ta bada amsa sai tayi shuru, ganin haka English teacher din taci gaba da bayani, har ta fita, daka class din.
Suna zaune ita da Mysha a class basu fita ba, saiga afraz ya shigo, da murmushi a fuskanshi suna hada ido ta kauda kai gefe tare da daure fuska, amma duk da hakan bai hanashi karasawa wajanta ba, Ya zauna gaf da ita yanda ba zata iya yin kurin tashi ba, tace afraz miye haka, ka matsa daka kusa dani, yayi murmushi yace haba Zeena miye dan na zauna a inda kike, wai miye laifina dan ina nuna kulawa na a kanki, tace laifinka shine kana min shi shigi a cikin al’amura na, na fada ma bana son kana kulani, Ya tamke fuska tare da matsawa kusa da ita sosai har suna iya shakan numfashin juna, yace Zeena tunda nake ban taba son abu na rasa ba, ko miye shi, balle mace, gwara ki daina bata ma kanki lokaci ki saurare ni, ganin irin yanda ya matseta yasa ta kasa magana, Mysha dake gefe itama kanta abun ya bata tsoro, ganin yanda ya mata, Dan kanshi ya tashi daka wajan tare da kallonta, Zeena saina nuna miki ban taba son abu ya kufce min ba, yana fadin haka yabar class din, ta fashe da kuka Mysha tazo kusa da ita tana rarrashinta tare da bata shawaran ta fada ma dad dinta, jin haka yasa ta tsagaita da kukan da takeyi tace Mysha wlh bazan fada ma dady ba, I know how to handle people like afraz, yana takama bai taba son abu ya rasa ba, I will teach him a lesson that he will regret to know me in his life, Mysha tace Zeena mai kike shirin yi? Ina baki shawara ki fita daka hanyan shi, bakya tsoran wani abu ya biyo baya? Tayi dan murmushin takaici tace karki damu Mysha babu abunda zai faru, a class suka zauna har aka tashi, suka fito da niyan tafiya gida, kai tsaye matan ta, ta nufa, ganin afraz akan matan yana zaune yasa ta daure fuska, taje ta bude motan da nufin ta ja motan, ganin ta kunna motan yasa ya sauka, ta fita da gudu kaman zata tashi sama, Ya bita da kallo tare da fadin saina cire miki wannan girman kan naki, this is a promise.
A lokacin da Zeena ta karasa gida ta tadda dady dinta ya dawo, da sauri ta karasa parking din motan ta, ta nufi cikin gida da gudu, tana shiga ta ganshi kan dinning yana cin lunch taje ta rungume shi, tare da fadin wlcm dady, we miss you alot yayi dariya yace my Zeena hope kina lafiya? Tace yes dady lafiya na qalau, ummi ta kalleta tace jiba yanda kike abu sai kace wata abda, ta turo baki tace kai ummi wajan 1 month rabo na da dady dan ya dawo nayi murna shine laifi, yanda tayi maganan ya basu dariya, dady yace bari in tafi masallaci, Ya fita ya barsu nan.
Wajan karfe takwas adeel ya dira gidansu Zeena, ta fito cikin Riga da skirt yan kanti ya mata kyau sosai, tace muje ciki mana, yace mata a’a ta shigo cikin motan kawai suyi magana, jin haka gabanta ya fadi, tare da tunanin mai zai fada mata, jiki babu kwari ta shiga cikin motan ta zauna, Ya kura mata ido wani irin sonta yake kara shigarshi, Ya rasa wani irin so yake mata, abun har mamaki yake bashi, kwata2 bata wuce 17yr ba amma ya mutu a kanta, ta katse mishi tunani da fadin adeel mai kake son ka fadamin haka, yayi dan murmushi yace Zeena wlh alhaji ya matsa min akan in fito da matar aure, jin haka yasa taji gabanta na dukan uku2 tare da na2 tawa cikin ranta aure, kwata2 babu tsarin aure a ranta tana burin ta kammala jami’a kafin tayi aure, gashi yanzu ko secondary skul bata Gama ba, yazo mata da maganan aure, Ya katseta da fadin Zeena kinyi shuru, tace adeel kai fa da kanka kasan yanda nake da burin inyi karatu kafin inyi aure, yanzu fa ss1 nake going to ss2 amma ka Kawo maganan aure, yayi shuru can yace Zeena alhaji ya matsa min banso yayi fushi dani plz ki yarda in turo,kin San indai karatu ne zan barki kiyi, a duk inda kike so, bani da matsala, duk wani abu da zai saki farin ciki shi nake so Zeena, tayi shuru tabbas tana son adeel irin son da bazata iya misaltawa ba, toh amma wannan batun nashi ba abu bane mai yiwuwa a gareta dan ita koda ta gama secondary skul ne Ya kawo mata wannan zancen baza aminta ba, balle bata gama ba,ta dai rabu dashi akan tayi shawara akan batun.
Kasan cewan yau sati ranan hutu, kuma a irin wannan ranan Zeena take samun zuwa yawo tayi duk abunda take so, kafin weekend ya kare, dan bata samun lokaci saboda skul, ta fito ita da abda, tasa doguwan Riga na atamfa da wani gyale ta yafa a kanta,ta tarar da ummi da dady dinsu a falo, tace dady zani gidansu Mysha daka nan za muyi shopping yayi murmushi yace ok amma karku dade, Ya zaro kudi yan 1k bandir daya ya bata yace sai kun dawo, abda tana yima ummi bye2 suka fita, kai tsaye gidansu Mysha suka fita, sun gaisa da mamanta sannan suka nufi dakin Mysha din, tana kwance tana tunanin adeel wanda sonshi ya shigeta lokaci daya, Zeena nata rafka sallama bata jiba, har saida ta taba ta, tayi firgit tare da fadin adeel, Zeena da mamaki take kallonta ta nanata sunan da taji ta fada da adeel, Mysha tayi saurin wayin cewa, tace ai sunanki kenan yanzu, adeel jin haka yasa Zeena tayi dariya tare da kawar da tunanin data fara, tace baki ma shirya ba, kin san zamu saloon kaina yayi datti, Mysha tace nayi wanka kaya kawai zansa, jirani minti biyu, ta nufi wadrop dinta daya cika da kaya makil ta dauko wata doguwan rigan kanti tasa, sannan tasa baby hijab suka fita, saloon suka nufa suka wanke kai daka nan suka nufa silver sand, suka dinga zaban kaya da takalmi, adeel ya kira Zeena ta fita suna waya, yace mata ya maganan su na jiya, tace bana gida muna silver sand inna koma zan kiraka muyi magana a nitse jin haka yaji dadi, Dan yana ganin kaman zata amince da zancen nashi, bayan ta kashe Wayan, ta koma ciki a wajan kofa sukayi karo da afraz yana tare da wasu mata biyu sunsha wando tree quarter, ansa top d’a mamma, Ya sakar mata murmushi yace Zeena dan zo in miki magana plz, tamai kallo na wulakanci tare da fadin bani da lokacin yin magana dakai, ganin zata wuce ya janyo mata hannu ta fado kan kirjinshi ya rungumeta, taja baya da karfi tare da shiga da sauri, duk ta rude, Mysha tace Zeena lafiya kuwa, ta kasa magana dakyar ta iya cewa zo mu wuce Mysha, bata musa ba suka biya kudin kayan, ta kama hannun abda wuka wuce sun ajiye Mysha gida sannan suka wuce gida, tunda ta koma dakinta ta nufa ta rufe kofan tana tuna abunda afraz ya mata.
Maryam obam ✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
(Mrs nura kuriga)😘🌹
Dedicated this page to hafsy (mamani) 😘
1⃣6⃣t2⃣0⃣
Adeel ne zaune cikin gidansu Zeena a falon baki yana jiran zuwanta, duk da baya kallon kofa, kanshin turaranta yaji yasa yasan ta karaso, da murmushi ya dago ya kalleta, amma ga mamakin shi, ba ita ya gani ba, Mysha ce, cikin wani Riga da wando yan kanti, tace barka da hutawa, Ya amsa da yauwa ya kike, cikin lallausar murya ta amsa da lafiya, kaifa? A dai2 lokacin Zeena ta shigo, ganin Mysha a wajan yasa ta tsaya tare da mata tambayan yaushe kika shigo? Tace yanzu ban dade ba, naga falon nan a bude na dauka kina ciki saina nufo nan, ashe baki riga kin iso ba, suka samu waje suka zauna, adeel ya kafe Zeena da ido, Mysha tana lura dashi duk sai taji wani iri, tunda take wannan ne rana na farko data fara kishi da Zeena sannan kuma rana na farko data yarda zata iya komai dan ta samu adeel, sai a yanzu ta kare mishi kallo, adeel namiji ne wanda ya hadu, Shiba dogo ba kuma ba zaka kirashi da gajere ba, sannan idonshi ma kanshi abun burgewa ne, dan inka kalla idonshi kaman mai jin bacci, (sexy eye) gashi yana da faffadan kirji, gashi yana da haske kaman balarabe, Zeena ce ta katse ta tare da fadin Mysha ya kikayi shuru, tayi firgit tace ina jinki, Zeena ta kafeta da ido tace wai mai kike tunani haka? Tace babu komai, adeel yace Zeena ya maganan mu? Taji gabanta ya fadi, tayi shuru, ganin haka yace Zeena plz kimin magana, tace adeel na fada Maka tun farko kudiri na akan karatu, bani da burin inyi aure yanzu, Ya kalli Mysha yace plz kisa baki, Mysha harga Allah taji dadin jin amsan Zeena, amma a fili sai tace haba Zeena aure ai shine darajan y’a mace, kuma babu abunda yafi ma mace mutunci face yau ace tana d’akin mijinta, kuma koda karatun zakiyi idan kina da aure za’afi mutunta ki, ada ina tunanin kaman mahaifina baimin adalci ba, nason inyi aure daka na kammala secondary school, amma da nayi nazari akan abun sai naga wannan shine babban gata daya nunamin, tunda Mysha ta fara magana adeel ya kafeta da ido tare da mamakin jin irin wannan kalaman a bakinta, yaji ta burgeshi, Zeena tace Mysha hakane, amma kawai bana ra’ayi ne, jin haka adeel ya tashi tare da fadin owk babu damuwa indai kin canza ra’ayi zaki iya nema na, yabar gidan ta bishi da kallo.+
Mysha nata jin dadin abunda ya faru yau, tabbas tasan halin Zeena indai tace abu da wuya kuma ta canza, lokaci daya wani haushin Zeena taji yana shiganta, tare da fadin Zeena ba kyau kika fini ba, sai dai ki nunamin hasken fata, hasalima da kadan kika fini haske, kowa yace ke yake so jiba afraz yanda ya mutu a kanta, yaro hadadde sai dai matsala daya bashi da hali, ga adeel shima kowa yace ke, why not me, dole sai na sami adeel at any cost.
Wasa2 yau satin adeel biyu baya zuwa wajan Zeena inta kirashi kuma sai yaga dama yake dauka, koda ya dauka dinma tambaya daya yake mata kin amince, tace adeel kamin hakuri, baya bari ta karasa saiya kashe Wayan, tayi bala’in shiga damuwa tabbas tana son adeel amma bazata iya yarda da kudirishi ba, tana burin tayi karatu mai zurfi kafin aure, domin tana ganin in tayi aure da wuya ta samu cikan burinta.
Yau Monday Zeena da abda suna dauke da kayan skul, abda ta kalli Zeena tace yau ke zaki Kaini skul plz, Zeena ta mata harara tace tunda nice driver koh, gwara ma ki nemi mai kaiki, jin muryan daddy dinsu sukayi yana fadin zo mamana ni dakai na zan kaiki, tayi dariya cike da jin dadi ta nufi mahaifin nata, tana yima Zeena gwalo, Zeena tace ina wasa dake koh, daddy yayi dariya yace haba Zeena mai mamana tayi miki da safen nan kike mata haka, ta dan turo baki irin na shagwaba tace daddy kana taking side dinta koh, babu komai, Ya karasa kusa da ita yace no Zeena dukan ku ina tare daku, jin haka yasa tama abda gwalo itama, ganin haka yasa abda tasa kuka Zeena ta fita da sauri tana dariya, daddy ya kalli abda yace lah kuka zaki sa tace ke raguwa ce, jin haka yasa tayi shuru, yace muje in kaiki, sai in wuce office,.
Alokacin da Zeena takai skul a tare sukayi parking ita da afraz, yayi sauri ya fito ya bude motarta yace fito mu shiga tare mana, ta sakar mai harara, yayi dariya yace in kika bata rai kinfi kyau, tayi tsaki tace wlh afraz kana da naci, wai mai zan Maka ka daina kulani, yace babu, dan komai zaki min bazan daina kulaki ba, tunda ina sonki kuma ke zan aura, ta saki dariya tare da tafa hannu, tace aiko maza sun kare wlh ban auranka, balle ma kai ba namiji bane, Ina maka kallon d’an daudu ne, tana fadin haka ta wuce, ranshi yayi mugun baci yace saina nuna miki ni a cikin mazan ma daban nake, Ya cije lebe u will regret it wallahi Zeena kota wani irin hali saina sameki, shima ya shiga cikin skul din.
Maryam obam ✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to waleeda luv😘
2⃣1⃣to2⃣5⃣
“wasa2 yau wajan wata daya adeel yana fushi da ita, ga Mysha ta rasa gane kanta, ta gefe daya kuma gashi zasu fara exam duk tunani ya mata yawa, ga afraz irin abubuwan da yake mata yayi yawa,
Zeena ta kalli Mysha tace muje study room muyi karatu, Mysha ta dan yamutsa fuska tace no kije kaina yana min ciwo, Zeena tayi dan sororo tana kallon ta, tace muje kisha magani mana, tace ki barni plz Zeena am ok, ganin haka Zeena ta fita, ta nufi study room din tare da tunanin maike damun Mysha kwana2, a lokacin data karasa taga afraz a kofan study room din, shida wasu abokan shi, ta daure fuska ta nufi ciki, shima bai kulata ba, hakan ya mata dadi, inta tuna ya kusa barin skul dinma sai taji wani farin ciki.
Mysha ce zaune a cikin Millennium Park, tana jiran adeel, tana shan drink, bata wani dade ba, yazo, bayan ya zauna ya kalleta babu yabo babu fallasa, yace Mysha lfya kika kirani nan, ko Zeena ta amince ne, ta dan yamutsa fuska jin an kira sunan Zeena, tace nop dama ina son magana dakai ne, yace ok ina sauraranki, ta dan saki murmushi tace adeel kai yanzu kana ganin zaka tsaya jiran Zeena har sai ta kammala karatun ta? Ya danyi shuru can yace bazan iya ba wlh Mysha alhaji na ya dameni yanzu ma yaban nanda wata daya in Kawo mata koya aura min duk wacce yaga dama, plz Mysha kima Zeena magana ko zata tausaya min wlh ina son Zeena kullum da tunaninta nake kwana nake tashi, Mysha tace indai Zeena ce ba zata amince dakai ba, tana da kafiya, babu yanda banyi da itaba amma taki yarda, sai yasa na kiraki in shawarceka, yace ina jinki, tace adeel nima mahaifina yace ina gama secondary school zaimin aure, yace gwd haka yana dakyau ai domin shine ya dace da y’a mace, gidan mijinta, tace haka ne, toh amma akwai matsala yace name kenan, tace bani da saurayi wanda nake so, yace aiya Allah ya baki, tayi dan murmushi tare da kara make murya tace adeel mai zai hana ka nemi aure na, yace what Kin San mai kike fada kuwa Mysha, tace eh na sani adeel, kaga kai an baka 1month ni kuma yanzu gobe zamu fara exam na zuwa ss2, anan kuma zanyi waec, nasan kana San Zeena ita kuma tana da burin karatu mai zurfi kafin aure, kaga nima ina da burin karatun amma dady na yace a d’aki na zanyi, kaga inka aure ni, zamu taimaki juna, zanyi karatu na, idan Zeena itama ta gama saika sakeni ka aureta, yayi shuru can yace sorry Mysha I can’t do it, Ya tashi yabar wajan, tayi tsaki tare da fadin wlh adeel kota wani hali saina zama matarka, taji wani tsanan Zeena a ranta.+
Su Zeena an fara exam yanzu ba kaman da ba Mysha an dan sake ma Zeena kadan, afraz an bar skul suma sun kusa fara waec,sai dai yakan dan zo jefi2,
Wayan Mysha kema ringing tayi tsaki ganin sunan adeel yasa tayi sauri ta dauka tare da fadin hello, bai jira ta gama fadin abunda zata ceba, yace ina kofar gidanku, tayi sauri ta tashi ta dauki gyale ta fita, ta sameshi cikin mota ta bude ta shiga, da murmushi a fuskanta, Ya kalleta yace Mysha na amince da kudirinki zan aureki amma zan sakeki bayan Zeena ta Gama karatu, don ita nake so, I tace zabi na, tayi dan murmushi tace babu komai, amma da sharadi yace name, tace karka fadama Zeena yanda mukayi, yace babu komai. Sukayi sallama ya wuce, ta shiga gida tana murna ta sami adeel, tace ai adeel kaida Zeena har abada tayi wani dariya wanda ita tasan mai take nufi.
Yau Zeena tayi mamakin canjin Mysha ganin haka yasa take fada mata adeel ya daina kulata, Mysha tace ki shareshi kema tunda ba’a dole, Zeena tace baki San yanda nake son adeel ba Mysha wlh ina son adeel fiye da komai, duk na rame ko abinci bana iya samun ci in koshi saboda tunanin shi, yaki yamin uzuri, wlh Mysha ban so inyi aure ban kammala karatu ba, domin bazan iya ba mijina kulawan daya dace ba, ga karatu ga hidiman mijina, kinga inna Gama karatun in mukayi aure zai samu kulawa sosai, Mysha tayi shuru amma ji takeyi kaman ta shake Zeena dan haushi, tace Zeena tunda kin dage karatu zakiyi sai kiyi ni bari inje inada abunyi.
Maryam obam ✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my kawata ta rai da rai nana fidaddusy😘💃🏻
2⃣6⃣to3⃣0⃣
“adeel ya aika gidansu Mysha an tsayar da komai na aure amma iyayenta sunce saita kammala secondary skul za’ayi bikin, mahaifin adeel ya yarda da hakan tunda ance bai kai shekara daya ba, zata kammala, kuma yaji dadin ganin gidan da d’an nashi ya nemo aure gidan mutunci,bayan an gama komai suka wuce tare da fatan Allah ya kaisu lokacin,+
Su Zeena an kammala jarabawa na zuwa ss2 sunyi hutu, yanzu babu skul, sai a yanzu take kewan adeel sosai kasan cewan suna hutu babu skul, kullum sai zaman gida, duk ta rame tayi dan duhu, gashi number din adeel din duk basa zuwa, tayi mugun shiga damuwa, har ummi ta fahimci hakan tayi tambayan duniya akan mai yake damunta, amsan dai kullum daya ce babu komai, ta dai zuba mata ido ta rabu da ita,
Yau an tashi garin Abuja da sanyi sosai yawanci mutane na dauke da rigan sanyi wasu harda hula, Zeena ta fito daka dakinta duk ta rame jikinta sanye take da Riga da wando ta daura suwaita akai, da hula kalan pink, hannunta dauke da key din mota, ta nufi falo ta tarar da ummi, tace ummi barka da Safiya, ganin yar tata kaman tana cikin ni shadi hakan ya mata dadi, tace yauwa Zeena ina zaki? Tace ummi wajan Mysha zani tace toh sai kin dawo, ta amsa da toh ta fita.
Lokacin da Zeena ta karasa gidansu Mysha tayi parking motar ta, ta nufi cikin gidan, ta tarar da mumy din Mysha a falo ta gaidata, ta amsa cikin fara’a har tana dan tsokanan ta, kin mana yaji dai Zeena kwana biyu bakya zuwa, tayi dan murmushi tace Amin hakuri mumy, tace Mysha tana dakinta, ta amsa da toh, ta nufi dakinta a kwance ta sameta cikin blanket, taja mata kafa, ta dan bude ido, Zeena ta sakar mata murmushi, ganin Zeena yasa ta tashi tare da dan yin gajeran tsaki, Zeena tace baki da matsala Mysha, ta dan ya mutsa fuska kaman bata son magana tace toh mai zai hanani bacci ai wannan sai ke, Zeena tace kaman kin sani wlh bana iya bacci wlh adeel kwata2 bana samun shi a waya, Mysha tace kai Zeena dan Allah kema ki rabu dashi nifa bazan dauka wulakanci ba, mutum ya shareki amma ke kullum kina nan cikin tunanin shi, Zeena tace Mysha wlh ba zaki gane ba, son adeel yamin yawa, yana da irin abubuwan da nake so mijin da zan aura ya kasance dashi, Mysha ta tabe baki tace toh yanzu miye abun yi? Zeena tace nazo muje gidansu ne ko Allah zai sa in ganshi, jin haka Mysha tace haba Zeena kin bada mata wlh akan mai zaki gidansu inya wulakantaki fa, tayi shuru, tabbas Mysha tayi gaskiya hala ma wata ya samu ya manta dani, lokaci daya taji wani bakin kishin adeel ya lullubeta, anya zan iya juran ganin adeel da wata mace kuwa, Mysha tace kinyi shuru, Zeena tace toh Mysha mai zance abun ne duk ya zama wani iri, Mysha tace Zeena ya kamata ki cireshi a ranki tun yanzu, kar nan gaba abun ya zaman miki matsala, Zeena tace Mysha kina ganin kaman Abu mai sauki ne in cire adeel a raina, kin San so kuwa Mysha? Bari kiji so ba wasa bane wani abu ne da yake shiga ran Dan Adam ba tare da notice ba, sai dai kaji ka fada wlh Mysha inda inada halin da zan cire son adeel toh zan cire saboda abu daya, a rayuwa ta banso in kira mutum ya kashe min waya, kinga adeel tunda haka ta faru ya daina daukan wayana kwata2, naso in shareshi inyi fushi dashi amma na kasa, Mysha dai kallonta take tana ganin duk sonda Zeena take ma adeel bata kaita ba, Mysha tace toh dazu da kikeso muje gidansu kin janye kudirin karatun ne, Zeena tace eh zan janye dan banso in rasa adeel dan naga idan nayi wasa zan rasa shi, Mysha tayi dariyan mugunta tare da fadin ai kin rasa adeel Zeena har abada, amma a fili sai tace kai kawata amma naji dadin hakan, yanzu tashi muje gidan nasu muga in yana nan, Zeena cikin murna tace suje, kai tsaye gidansu adeel suka nufa, da suka karasa sun tarar da mai gadi a zaune a wajan gidan suka mai sallama, Ya amsa sannan sukace dan Allah adeel muke nema, yace ai baya nan yana China wajan sati biyu kenan, gaban Zeena ya fadi, yace cikin ku wacece Zeena? Tace gani nan ya dauko takarda ya bata, yace ance in baki inji shi toh ban samu naje ba sai gaki, tace toh amma taya akai ka gane akwai Zeena a nan, Ya dan fara dan in ina, dama ya fada min kina da haske toh ganin haka nace hala cikin ku baza’a rasa Zeena din da yaban sako in bata ba, tace toh nagode suka wuce, saida suka karasa gidansu Mysha ta bude letter din rubutu ne kaman haka,. “Zeena ada naso ki naso in kasance dake a matsayin mata kuma uwar y’ay’ana kin nuna baki ra’ayina toh ina farin cikin shaida miki Zeena nima a yanzu babu sonki ko daya a raina, na samu wacce nake so Dan haka kiyi hakuri kar ki batama kanki lokaci, nagode. Sakin takardan tayi Mysha ta dauka ta karanta tace yanxu haka adeel zai miki lallai namiji badan goyo bane, ko jin abunda Mysha take fada batayi, ta shiga motar ta, ta wuce tuki take amma bata San maike gabanta ba idonta har rufewa yake bata gani sosai, ji tayi garab ta bugi wani mota, mai motan ya fito rai a bace amma ganin Zeena yasa yace Zeena what happen with you hope you are OK, kai kawai ta iya d’aga mishi tana ganin jiri2, mutane keta musu horn ganin ko daga hannu ta kasa yasa ya zagaya ya daukota dakyar ta iya fadin afraz ka daina taba ni, amma ko a jikin shi, yasa ta cikin motanshi sannan ya koma nata ya matsar gefe, Ya dauke nashi a hanya ma, ido ya kura mata tare da wani mugun sha’awanta, tabbas Zeena ta hadu, Ya tada motar ya figa, wani gidan gonanshi ya nufa da ita, bayan sun karasa ya dauketa cak ya kaita wani d’aki, Ya ajiye ta kan gado, yana wani murmushi, Ya fara kokarin cire mata riga..
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to huda baby💃🏻
3⃣1⃣to3⃣5⃣
“Ya cire cardigan din dake jikinta, sai yar riga karama ya rage mai gajeran hannu, Ya kurama kirjinta ido, har wani hadde miyau yake, Ya fara kokarin cire rigan itama, ta dan sa hannu ta rike tare da fadin ruwa2 ya tashi da sauri yaje ya dauko ruwa ya zuba mata maganin bacci a ciki sannan ya juya ya bata tasha duk idonta na rufe, bata san wake mata wannan aikin ba, bata dade dasha ba, bacci mai nauyi ya dauke ta, Ya cire mata rigan ganin kirjinta yasa ya kara rudewa, Ya fara wasa da kirjinta gaba daya ya fita hayyacinshi, afraz yayi nasaran raba Zeena da budurcinta, har ya gama komai bata farka ba, jini keta zuba a jikinta ganin haka yasa mata kayanta ya dauketa cak, Ya Sata a mota kai tsaye inda ya parka motan ta, Ya nufa, yako tarar da motan a wajan ya bude yasa ta a ciki yaja nashi motan ya wuce,+
Gaba daya hankalin iyayen Zeena ya tashi, tun dazu aketa nemanta amma ba’a ganta ba, ga wayanta yana ta ringing ba’a daga ba, ganin haka dady dinta ya fita ko za’a dace, amma babu labari, hankalinsu yayi mugun tashi, gashi Mysha tace tun dazu ta wuce, an sanar gidan radio da tv ko Allah zai sa a dace, police sunzo suma an bada report, ummi ganin wajan karfe goma shiru yasa tace bari dai taje gidansu Mysha taji ko wani abu ya faru kafin tabar gidan, jin haka dadyn Zeena shima yace suje tare, suna tafiya suna duba hanya ko Allah zaisa su ganta, driver ke tuka su, ummi tace tsaya2 kaman ga motan Zeena can, bayan driver ya tsaya da motan, da sauri ummi ta fita, ta bude motan sai ganin Zeena tayi cikin jini gabanta ya fadi ta fara salati, ta rike mijinta ta saki kuka mai karfi tare da fadin mai ya sami Zeena na shiga uku, dady yace ba kuka zakiyi ba, mu dauketa mu kaita asibiti, dady ya dauketa suka nufi asibiti da ita, likitoci sun an sheta anyi emergency room da ita, ummi ta kasa samun nutsuwa sai kaiwa da kawowa take yi, ita da dady an rasa mai bama wani baki, kowa yana cikin tashin hankali, likitoci sai wajan shadaya saura suka fito, ummi taje da sauri tace Dr maiya sameta? Dr yace muje office, suka nufi office dinshi bayan sun zauna, daddy yace Dr maiya sameta, dr yace anyi mata fyade ne sannan an bata maganin bacci wanda zai iya kaita nan da kwana biyu bata farka ba, dady yace what? Ummi babu abunda take iya fada sai innalillahi wa inna ilaihira jiun, wani hawaye mai zafi ke zuba daka idonta, dakyar daddy ya samu ta dan nutsu.
Police sun zo bincike akan abun amma ummi tace subar maganan dan bata son tonan asiri, domin bincike akan wannan abun kaman an tozarta yarta ne, ta dai ce koma waye shida Allah.
Kwanan Zeena uku ta farka daka baccin da take, a lokacin data bude idonta wani jiri2 take gani, ganin ta farka ummi ta kira Dr yazo ya kuma dubata yace ma ummi sai su godema Allah tunda ta farka, sannan a hankula komai nata zai koma normal domin kwayar da aka bata mai karfi ne.
Zeena anata samun sauki kwananta goma a asibiti aka sallameta, Mysha tazo sau biyu tana dubata, amma bata San mai aka mata ba, iyayen Zeena din ne kawai suka San mai ya faru da ita, ita kanta Zeena din ta kasa tuna komai, sai dai tana ganin kaman hatsari tayi lokacin da tabar gidansu Mysha.
BAYAN WATA BAKWAI
Alokacin su Zeena an fara waec tunda abun nan ya faru mahaifinta ya hanata zuwa ko ina ita daya saida masu bata kulawa harda skul, anata shirin bikin Mysha da adeel ba tare da sanin Zeena ba a kwana a tashi babu wuya su Zeena an kammala jarabawa, sai a ranan Mysha take fada mata maganan auran ta, Zeena tace haba Mysha aure zakiyi shine sai yanzu kike fad’a min kina ganin kin min adalci, Mysha tace kiyi hakuri Zeena abun ne yazo da haka, tace shikenan wa zaki aura, Mysha tace surprised nake son miki sai ran bikin zaki sani, tace Allah ya kaimu, kin ga da adeel na nan nema daya fito, Mysha tace Allah sarki ai adeel bai kyauta miki ba, Ya miki halin maza da haka dai suka wuce.
STORY CONTINUES BELOW

Anata shirin bikin Mysha kasan cewan angon baya farin ciki da bikin yasa bai dawo Nigeria ba yace sai Ana gobe bikin zai dawo andai yi komai daya dace, wani abokinshi mai suna ahmad shiya tsaya akan komai kuma shiya sallama yan matan amarya, a ranan da ango din zai dawo suka shirya kamu wanda ya hada manyan mutane, masu ji da Kansu anyi kamu lafiya kowa ya watse.
Yau sati aka daura auren Mysha da adeel, wajan karfe goma, mutane sun taru sosai, anyi kalanda dasu memo an raba ma mutane, a lokacin da Zeena ta gani ba karamin shock tayi ba na ganin adeel tare da Mysha, wani hawaye ya zubo mata wanda bata San yana zuba ba, waje tayi cikin motan ta, tana kara kallon Hoton tana ganin kaman idonta ke nuna mata adeel, amma bashi bane, ta dai tabbatar adeel din ne, tace driver ya kaita gida, yace toh suna tafiya tana ganin jiri2 dama Mysha haka take zata iya cin Amana na, wani hawaye mai zafi ya kara zubo mata, AMINIYA TA CE yau taci Amana ta, ta rabani da abun da nake so, ashe dama haka aminci yake yanzu na aminta da ita amma taci Amana ta dama shine surprised din da Mysha zata bani.
Maryam obam✍✍
👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to zee baby💃🏻
3⃣6⃣to4⃣0⃣
“wani azababban ciwon kai ne Ya kamata lokaci daya, inda ita take tuki toh da komai zai iya faruwa, shi kanshi driver din dake janta ganin yana yinta ta bashi tausayi duk da bai San maike damunta ba, Mysha why are you doing this to me, u are my best friend, why Mysha, I trust you but you break the trust that I have for you, inda kin fadamin kina son adeel zan iya hakura dashi in bar miki Mysha am not a selfish, you hurt me alot Mysha, ta saki kuka mai karfi, driver yace hajiya Zeena lafiya kuwa? Ta kasa ko motsa baki balle tayi tunanin bashi amsa, jin bata kulashi ba, yasa yaci gaba da tuki, har suka isa gida, da gudu ta shiga gidan kai tsaye dakinta ta shiga, iyayenta suka bita suma dan ganin yanda ta shigo da gudu, amma ta rufe kofan ta, suna ta buga kofan amma taki ta bude, haka suka barta.
Zeena komai Ya tsaya mata kwata2 ta tsani komai, ko fita batayi kullum tana gida, bata komai sai kuka, tare da bakin cikin abunda Mysha ta mata, ta rabata da farin cikin ranta, har yanzu tana mamakin abun, iyayenta na tausaya mata, sun dai yanke hukuncin su turata wajan yayanta zaheer kasar japan ko Allah zaisa ta manta komai, ummi ta shigo d’akin ta ganta tana ta faman hawaye kaman kullum, tace Zeena kiyi hakuri ki cire wannan abun a ranki dan Allah, ta kalli ummi tace haba ummi AMINIYA TA CE, fa Mysha taci Amana ta, ta rabani da masoyi na, ummi dama haka kawaye suke dacin Amana, yanzu babu mutane masu Amana, masu amana sun kare kwata2 ban taba tunanin Mysha zata min haka ba, ummi inda Mysha ta fadamin tana son adeel ni zan iya bar mata, amma ta yanda tamin is painful, ummi ni daya nasan abunda nake ji a raina yanzu babu mai fahimta na, ta saki kuka ummi ta janyo ta, ta rungumeta tana tausayin yar tata, tace Zeena ki daina fadin haka, akwai masu amana kar kiyi judging mutane ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai mutane masu aminci, tace ummi amma yanzu sunyi karanci, plz ummi ban San zama a kasar nan, Ina so in bar Nigeria gobe dan ina ganin kaman yanzu abun ya faru, ummi tace shikenan Zeena dama nida dady dinki mun yanke hukuncin ki tafi Japan wajan zaheer kiyi karatun ki a can, tace toh ummi I want to leave tomorrow, ummi tace shikenan amma kibar wannan kukan tace toh ummi ta fita daka d’akin.
Mysha ce zaune a falonta da yasha kayan ado na more rayuwa masu tsadan gaske, tana tunanin ta yanda zata bullo wa adeel, Ya dinga kulata, jin motsin shi tayi, yasa tayi saurin tashi ta nufeshi tare dayin hugging nashi, yayi sauri ya tureta, tare da daure fuska, yace Mysha karki manta nida ke fake marriage mukayi, lokaci kawai muke jira mu rabu, so plz ki daina shige min, domin bazan taba kallonki a matsayin wacce zan iya zama da ita ba, tace haba adeel nifa matarka ce kuma inada hakki a kanka, yace what, hakki matata, yayi wani murmushi tare da fadin dnt you ever think of this thing, you are not my wife, lalle Mysha har kina tunanin hakki, kina da hankali kuwa, kin manta yarjejeniyan mu nida ke, tace no adeel ban manta ba, naji na canza ra’ayi, bazan iya rabuwa dakai ba ina so ka daukeni a matsayin matarka wanda mukayi aure na soyayya, Ya kalleta a wulakance yace Mysha kinyi kuskure you are selfish kinci amanan kawance, but zan nuna miki kuskuranki, tace adeel baka isa kamin komai ba, sonka yasa nayi haka na rasa hanyan da zan sameka saida nabi ta wannan hanyan, yace Mysha sai kinyi dana sanin sani na, kin rabani da Zeena akan selfishness naki, zan zauna dake amma ki sani sai kin gwammace gwara mutuwa akan aurena, domin nan gidan daka yau zai koma miki gidan azaba, babu ke babu farin ciki,. Yana fadin haka ya fita, bai dade ba ya dawo, tare da masu aikin gidan duka, yace duk ya sallamesu, tace haba adeel wa zai dinga aikin? Yace ke, don shine abun daya dace dake, ta saki kuka haba adeel yanzu abunda zaka min kenan, yayi banza d ita ya haura sama, Ya barta a nan, cikin bakin ciki.
STORY CONTINUES BELOW

Zeena tabar Nigeria ta tafi Japan, da yake acan kasar daddy dinsu nada gida anan yayanta yake zama, toh itama a can zata zauna ummi ta had’a ta ita da wata yar dattijuwa dan ta dinga kula da ita, gashi kuma an kammala mata komai na skul, ta sami course din da take burin samu kuma, doctor, Zeena dan kwana biyu da tayi a kasar taji dadin kasar sosai, zaheer shi yake kaita skul ya dauko ta, kafin ta saba da kasar,.
Afraz zaune a d’akin hotel dake kasar nijar, shida wata mata, ta manne shi, amma ba komai yake tunani ba, sai Zeena tabbas mata suna suka tara, babu irin macen da bai nema ba, amma ya rasa dalilin da har yanzu bai sadu da wanda yaji ya gamsu da ita ba sai Zeena, duk da a lokacin shi daya yayi kadan shi yayi rawan shi, balle ace na sadu da ita cikin son ranta ya zan kasance, wani abu yaji yana to karan zuciyan shi tabbas Zeena ina sonki kuma zanyi farin cikin in mallake ki a matsayin matar aure na, ada ba sonki nake ba sha’awar ki nake amma yanzu, babu komai tare dani face soyayyan gaskiya, Ya lumshe ido, matar dake manne dashi tace Afraz inata magana kayi shiru, Ya dan tureta ya tashi, Ya fara sa kaya, tace ina zaka kuma yace zan koma skul, ban son in kara kwana a kasar nan.
Maryam obam✍✍
👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to yasmin darling 😘💃🏻
4⃣1⃣to4⃣5⃣
Zeena an fara sabawa da garin duk da ba fita takeyi ba, daka skul sai gida, koda tana son abu zaheer zai Kawo mata, kuma tana karatun ta cikin kwanciyan hankali, amma har yanzu ta kasa mantawa da adeel kullum dashi take kwana take tashi, duk yanda tayi kokarin ta cire shi a ranta amma abun yaki yi, ji take kaman kullum ana kara mata sonshi ne, ta dai barma Allah zabi akan ya zaba mata mafi alkairi.
Afraz ya dawo London amma kwata2 baya jin dadin kasar, ji yayi babu abunda yake son gani sai Zeena, har mamaki yake, kuma yakan tambayi kanshi wai mai yake damunshi, Ya lumshe ido tare da tuna surar Zeena, wani ni shadi yaji yana shigarshi, Zeena you are the best, kinfi ko wace mace, ke daban kike, burina in mallake ki.
Adeel yana zaune a cikin bedroom dinshi daka shi, sai singlet da shortener, yana danna laptop dinshi yana kallo yana murmushi, Hoton Zeena yake kallo, yana fadin Zeena ke tawa ce, saina mallake ki, you are my, bazan bari in rasa kiba, Mysha ta shigo d’akin harta zo kusa dashi bata sani ba, ganin Hoton Zeena a laptop din yana kallo yasa ranta ya baci, ta fisge laptop din tayi jifa dashi, Ya tashi rai a bace ya tsinka mata mari har sau biyu tare da fadin Mysha I hate you, you are evil, tace adeel ni ka mara? Ya daure fuska yace get out tare da nuna mata kofa, yace sai kin San kin fasa laptop din nan, ta fita da gudu tana kuka, toilet ya fada yayi wanka ya fito cikin kananan kaya ya mishi kyau sosai, Ya nufi d’akin ta, Ya ganta kwance kan gado tana rusa kuka, Ya tabe baki, Ya daka mata tsawa tare da fadin ke naki kukan najin dadi ne, sai na d’an d’ana miki irin radadin da kika sani a ciki, yana gama fadin haka ya fita.
Afraz yazo Nigeria, Ya samu labarin Zeena tana Japan karatu wajan mai gadin gidansu, Ya tambayi number dinta yace baida shi, Ya bashi kudi da yawa yace ga wannan plz ka samo min bayani akan inda take karatu a Japan din, mai gadi ya washe baki yace an Gama, Ya amsa number din Afraz din, akan zai kirashi idan ya samu information akan batun, Afraz ya wuce.
Zeena tana cikin class sun gama lecture, tana jiran zaheer yazo ya dauketa, sai ga wani bature yazo inda take, yace mata hello, Ya sakar mata murmushi ta amsa da hi,tana fadin haka ta tashi da nufin fita, yace mata please I want to talk to you, ta dan tsaya tare da fadin ok, Ya kalleta yace please sit down, batamusa mishi ba, ta zauna, Ya kalleta yace, na ganki a skul din nan, so ina lura dake kaman kina da damuwa, naga baki kula kowa, duk da harshen turanci yake mata maganan, ta kalleshi ta dan daure fuska, tayi shiru, ganin haka ya kuma tambayanta ya kikayi shuru, ganin ya matsa mata da tambaya yasa ta tashi tabar class din, tako ci sa’a ta hango zaheer da sauri ta nufeshi ta bude motar ta shiga, tace bros mai yasa kayi late din zuwa dauka na, Ya kalleta yace sorry little sis, naje amso abu ne, ta dan turo baki, irin na shagwaba, yayi dariya yaja motar suka wuce,
STORY CONTINUES BELOW

Mai gadin gidansu Zeena ya fad’a ma Afraz komai da komai na wajan da Zeena take karatu, yaji dadin labarin, Ya fara shiri na zuwa Japan,
Afraz an sauka a kasar Japan, bai bari ya huta ba, Ya nufi skul din, amma harya gama yawonshi baiga mai kama da Zeena ba, haka ya koma masaukin shi cikin takaici, haka kullum yake ta sintiri a skul din amma shuru kake ji, babu Zeena balle mai kama da ita, wajan sati daya kenan, yayi tsaki tare da fadin kodai mutumin nan wrong address ya bani, mai ma yasa na yarda dashi, Ya tada motarshi, da nufin ya wuce a dai2 lokacin Zeena ta fito daka class zata mota ya hango ta, da sauri ya fita, amma kafin ya karasa ta shige mota sun wuce, Ya koma da sauri yabi bayansu, har suka nufi gida, toh amma wani abu daya tsaya mishi a rai waye wannan namiji din daya dauko ta, miye halakan su, da yaga tana mishi dariya shima yana mata, wani bakin kishin Zeena din yaji yana shiganshi, wannan ne karo na farko daya taba jin kishin y’a mace.
Maryam obam ✍✍
👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to yasmin darling 😘💃🏻
4⃣6⃣to5⃣0⃣
Yayi tsaki tare da buga sitiyarin motarshi, yaja motar ya wuce, washe gari tun 7 ya fito, Ya nufi gidan da Zeena ta shiga, Ya zauna a mota har wajan 11 baiga kowa ya fito daka gidan ba, wajan 12 zaheer ya fito ya shiga mota ya wuce, abun ya kuma daure mishi kai, Ya dai yanke shawaran bari ya shiga gidan ya gani, Ya fito ya nufi kofan gidan, yayi nocking, a lokacin Zeena tana falo din, tana kallo, tasa wata top mai budaddan hannu ruwan yellow da skin tie, tace yes coming, jin kaman muryan Zeena yasa yaji dadi, Ya bude kofan ya shiga, bata waigo ba, balle taga wanda ya shigo, Ya kafeta da ido, tare da wani shaukin sonta da yake kuma shigarshi, jin kaman ana kallon ta, yasa ta waiga, da sauri ta tashi tare da fadin afraz, abun daya faru da ita lokacin da taje gidansu Mysha ta tuna, anya banga afraz ba lokacin ba kuwa, kodai shi ya kaini asibiti da nayi accident, kai anya bashi bane, domin in shine zai dawo duba ni, inma bai dawo ba ummi zata fad’a min, ya kafeta da ido, ganin irin kallon da yake mata yasa ta daure fuska, tare da fadin mai ya Kawo ka nan, mai kake so? Yace Zeena ke nake so, ta d’aga mai hannu alaman yayi shuru, tace afraz plz ka fita, yace haba Zeena wlh sonki yamin yawa, plz ki tausaya min, ta kuma daure fuska tace afraz na fada Maka tun tuni bana sonka, ban son ganinka, koh ana so dole ne, Ya matso kusa da ita yace Zeena plz ki soni, ta bude baki za tayi magana yayi hugging dinta, ta kasa ko magana, sai zuciyanta dake ta buga mata, Ya fara mata magana kaman mai rad’a, Zeena ina sonki ina so ki zama matata, jin haka ta tureshi tare da yin baya, tace afraz I hate you, wlh ko babu maza a duniya gwara in mutu banyi aure ba, tana fadin haka tabar wajan da gudu, ya bita da kallo, dama akwai macen da zata ‘kishi, duk kudin da yake dashi, ga kyau, tabbas sai a yanzu afraz yasan ba komai kudi zai iya samo maka ba, fita yayi yabar gidan cikin takaici.
Adeel yana zaune a falo yana kallo amma kwata2 hankalinshi baya wajan kallon, tunanin Zeena yake, Zeena kece komai nawa, bazan iya rayuwa ba tare dake ba, komai zai faru Zeena sai na mallake ki, yayi dan gajeran tsaki, tare da kara tsanan Mysha, jin maganan ta yayi tana fadin haba adeel tun dazu ina magana kayi banza dani, Ya kalleta yace inaji, tace ina so inje gidan mu, Ya sakar mata harara, tare da fadin ai babu ke babu fita, tace haba adeel wai mai yasa kake min haka, kwata2 baka kulani, kullum sai ka zauna kana bata lokacin ka akan tunanin waccen banzan Zeena mai take dashi wanda banda shi, Ya tashi tsaye rai a bace yace lallai Mysha sai yau na kara sanin ko ke wacece, bari kiji Zeena ta fiki kyau ta fiki tarbiya, ta fiki komai ki daina ma yaudaran kanki kina hada kanki da ita, ta fashe da kuka adeel ni fa matarka ce, kake yabon wata a kai na, kake nuna wata ta fini, ya kalleta yayi dan murmushi tare da fadin bazan taba kallonki a matsayin mata ta ba, Mysha yanda kika cuceni kika yaudare ni, kika barni cikin kunci haka zamu zauna ni dake, har Zeena ta kammala karatun ta in aureta, tace what adeel kasan mai kake fad’a kuwa? Yayi banza da ita ya haura sama ya barta a nan tana rusa kuka, tare da tausayama kanta.
Kullum afraz yana bin skul din su Zeena amma taki kulashi yayi naci yayi mitar amma duk a banza, gashi zasu fara exam a skul, dole ya koma London dan yayi exam, a na gobe zai koma yaje skul din su, a lokacin sun gama lecture ta fito zata koma gida, yau da kanta zata wuce don zaheer akwai inda zashi, ganinta yasa yayi sauri ya fito a mota ya nufeta, ganin yana nufota yasa ta daure fuska, bayan ya karaso ya kafeta da ido tare da fadin haba Zeena ke ko tausayi na, bakya yi, don Allah Zeena kiyi hakuri ki kulani, gobe zan koma nazo in miki sallama, ta kalleshi tace toh a sauka lafiya, taci gaba da tafiya, jin ta bashi amsa duk da cikin tsiwa tamai da gatsali, hakan yamai dadi, yaci gaba da binta Zeena ki taimaka kiban number dinki plz, ta daure fuska tace afraz dan Allah ka daina bina, bana so plz, yace shikenan amma ki bani number dinki, tace bazan iya ba, ganin haka yace toh muje in kaiki, shima tace bata so, daka karshe dai shiya bata tashi number din tare da rokonta ta kirashi, ta amsa da toh yana barin wajan ta yarda katin tare dayin tsaki.
Afraz ya koma London, sun fara exam amma kwata2 bai San abunda yake rubutawa ba, kullum da Zeena yake kwana yake tashi, yana mamakin irin azababban son da yake mata, amma yakan danganta abun da sakayya Allah ya mata akan abunda ya mata, yakan kara tausayin kanshi ya tabbata Zeena idan tasan shi ya mata fyade bazata taba kallonshi ba, yanzu Yama ya kare balle ace ta sani, ji yayi jikin shi yayi mishi sanyi, wayanshi dake gefe yaji yayi ringing da sauri ya dauka ganin sunan yasa ya dan canza fuska, domin yana tunani ko Zeena ce, Ya dauka tare da fadin hello mum, ta dayan bangaren ta amsa da hi, tare da fadin yakake, son kwana2 bana samin ka a waya ina ka shiga, yace mum naje Japan ne, tace Japan mai kaje yi? Yayi dan shuru can dai yace mum wlh ina sonta mum plz mum ki neman min auran ta, tace son wa kake so haka, yace mum Zeena, ta nanata sunan Zeena, a ina take yace a Abuja amma tana nan Japan tana karatu, tayi dariya tace toh kun dai daita ne, yace no mum bata sona, mum in ban sameta ba komai zai iya faruwa dani, jin irin yanda tilon d’anta wanda ta mallaka shi daya a duniya, yake magana hankalinta ya tashi, tace son karka damu koma yar gidan wanene ita zan nema Maka auranta, jin haka yace mum kin min alkawari, tace yes my son, kama fara Kiran kanka da mijin Zeena, yayi yar wata kara tare da fadin I love you mum, tayi dariya sannan sukayi sallama, ranan afraz ya kasance cikin nishad’i domin komai yake so iyayenshi suna bashi, gani yake kaman ma ya mallaki Zeena din.
Yau Sunday Zeena tana gida babu skul, tana kwance a d’akinta tana kallon sama, babu abunda take tunani sai adeel, ta rasa mai yasa kullum sonshi yake kara karuwa a ranta, duk kokarin da take don taga ta cireshi cikin ranta amma abun yaki, sai dai a kullum sonshi da yake karuwan mata, wani hawaye ne Ya zubo mata, adeel ina sonka, son da bazan iya musaltawa ba, duk da kunci amanata, ka barni da sonka a tare dani, kana tare da matarka ka manta dani, ta saki kuka mai karfi, taci kukanta babu mai rarrashinta don kanta tayi shuru, wayanta ta dauka ta kira daddy dinta, bugu daya ya dauka, yana jin muryanta yace Zeena kin yi kuka koh, jin tayi shuru ya tabbatar da hakan, yace Zeena har yanzu baki cire wannan abun a ranki ba koh, idan har kina son adeel kuma zaki aureshi ni dakai na zan nema miki auranshi, domin ban son abun da zai saki damuwa, jin haka tace dady a’a ka barshi, bai dace dani ba, inda yana so na da kanshi zai zo ya nemi aurena, mahaifin nata ya tausaya mata, yace Zeena ki dai yi tunani akai, tace toh dady su kayi sallama ta kashe wayan, tare da tunanin maganan da sukayi da daddy dinta, adeel ina sonka amma ka auri AMINIYA TA, wata zuciyan tace mata toh sai me, dan ya aureta, kawai in kina sonshi ki aureshi da wannan tunanin bacci ya dauketa.
Maryam obam ✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to zee baby💃🏻
3⃣6⃣to4⃣0⃣
“wani azababban ciwon kai ne Ya kamata lokaci daya, inda ita take tuki toh da komai zai iya faruwa, shi kanshi driver din dake janta ganin yana yinta ta bashi tausayi duk da bai San maike damunta ba, Mysha why are you doing this to me, u are my best friend, why Mysha, I trust you but you break the trust that I have for you, inda kin fadamin kina son adeel zan iya hakura dashi in bar miki Mysha am not a selfish, you hurt me alot Mysha, ta saki kuka mai karfi, driver yace hajiya Zeena lafiya kuwa? Ta kasa ko motsa baki balle tayi tunanin bashi amsa, jin bata kulashi ba, yasa yaci gaba da tuki, har suka isa gida, da gudu ta shiga gidan kai tsaye dakinta ta shiga, iyayenta suka bita suma dan ganin yanda ta shigo da gudu, amma ta rufe kofan ta, suna ta buga kofan amma taki ta bude, haka suka barta. +
Zeena komai Ya tsaya mata kwata2 ta tsani komai, ko fita batayi kullum tana gida, bata komai sai kuka, tare da bakin cikin abunda Mysha ta mata, ta rabata da farin cikin ranta, har yanzu tana mamakin abun, iyayenta na tausaya mata, sun dai yanke hukuncin su turata wajan yayanta zaheer kasar japan ko Allah zaisa ta manta komai, ummi ta shigo d’akin ta ganta tana ta faman hawaye kaman kullum, tace Zeena kiyi hakuri ki cire wannan abun a ranki dan Allah, ta kalli ummi tace haba ummi AMINIYA TA CE, fa Mysha taci Amana ta, ta rabani da masoyi na, ummi dama haka kawaye suke dacin Amana, yanzu babu mutane masu Amana, masu amana sun kare kwata2 ban taba tunanin Mysha zata min haka ba, ummi inda Mysha ta fadamin tana son adeel ni zan iya bar mata, amma ta yanda tamin is painful, ummi ni daya nasan abunda nake ji a raina yanzu babu mai fahimta na, ta saki kuka ummi ta janyo ta, ta rungumeta tana tausayin yar tata, tace Zeena ki daina fadin haka, akwai masu amana kar kiyi judging mutane ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai mutane masu aminci, tace ummi amma yanzu sunyi karanci, plz ummi ban San zama a kasar nan, Ina so in bar Nigeria gobe dan ina ganin kaman yanzu abun ya faru, ummi tace shikenan Zeena dama nida dady dinki mun yanke hukuncin ki tafi Japan wajan zaheer kiyi karatun ki a can, tace toh ummi I want to leave tomorrow, ummi tace shikenan amma kibar wannan kukan tace toh ummi ta fita daka d’akin.
Mysha ce zaune a falonta da yasha kayan ado na more rayuwa masu tsadan gaske, tana tunanin ta yanda zata bullo wa adeel, Ya dinga kulata, jin motsin shi tayi, yasa tayi saurin tashi ta nufeshi tare dayin hugging nashi, yayi sauri ya tureta, tare da daure fuska, yace Mysha karki manta nida ke fake marriage mukayi, lokaci kawai muke jira mu rabu, so plz ki daina shige min, domin bazan taba kallonki a matsayin wacce zan iya zama da ita ba, tace haba adeel nifa matarka ce kuma inada hakki a kanka, yace what, hakki matata, yayi wani murmushi tare da fadin dnt you ever think of this thing, you are not my wife, lalle Mysha har kina tunanin hakki, kina da hankali kuwa, kin manta yarjejeniyan mu nida ke, tace no adeel ban manta ba, naji na canza ra’ayi, bazan iya rabuwa dakai ba ina so ka daukeni a matsayin matarka wanda mukayi aure na soyayya, Ya kalleta a wulakance yace Mysha kinyi kuskure you are selfish kinci amanan kawance, but zan nuna miki kuskuranki, tace adeel baka isa kamin komai ba, sonka yasa nayi haka na rasa hanyan da zan sameka saida nabi ta wannan hanyan, yace Mysha sai kinyi dana sanin sani na, kin rabani da Zeena akan selfishness naki, zan zauna dake amma ki sani sai kin gwammace gwara mutuwa akan aurena, domin nan gidan daka yau zai koma miki gidan azaba, babu ke babu farin ciki,. Yana fadin haka ya fita, bai dade ba ya dawo, tare da masu aikin gidan duka, yace duk ya sallamesu, tace haba adeel wa zai dinga aikin? Yace ke, don shine abun daya dace dake, ta saki kuka haba adeel yanzu abunda zaka min kenan, yayi banza d ita ya haura sama, Ya barta a nan, cikin bakin ciki.
Zeena tabar Nigeria ta tafi Japan, da yake acan kasar daddy dinsu nada gida anan yayanta yake zama, toh itama a can zata zauna ummi ta had’a ta ita da wata yar dattijuwa dan ta dinga kula da ita, gashi kuma an kammala mata komai na skul, ta sami course din da take burin samu kuma, doctor, Zeena dan kwana biyu da tayi a kasar taji dadin kasar sosai, zaheer shi yake kaita skul ya dauko ta, kafin ta saba da kasar,.
Afraz zaune a d’akin hotel dake kasar nijar, shida wata mata, ta manne shi, amma ba komai yake tunani ba, sai Zeena tabbas mata suna suka tara, babu irin macen da bai nema ba, amma ya rasa dalilin da har yanzu bai sadu da wanda yaji ya gamsu da ita ba sai Zeena, duk da a lokacin shi daya yayi kadan shi yayi rawan shi, balle ace na sadu da ita cikin son ranta ya zan kasance, wani abu yaji yana to karan zuciyan shi tabbas Zeena ina sonki kuma zanyi farin cikin in mallake ki a matsayin matar aure na, ada ba sonki nake ba sha’awar ki nake amma yanzu, babu komai tare dani face soyayyan gaskiya, Ya lumshe ido, matar dake manne dashi tace Afraz inata magana kayi shiru, Ya dan tureta ya tashi, Ya fara sa kaya, tace ina zaka kuma yace zan koma skul, ban son in kara kwana a kasar nan.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to yasmin darling 😘💃🏻
4⃣1⃣to4⃣5⃣
Zeena an fara sabawa da garin duk da ba fita takeyi ba, daka skul sai gida, koda tana son abu zaheer zai Kawo mata, kuma tana karatun ta cikin kwanciyan hankali, amma har yanzu ta kasa mantawa da adeel kullum dashi take kwana take tashi, duk yanda tayi kokarin ta cire shi a ranta amma abun yaki yi, ji take kaman kullum ana kara mata sonshi ne, ta dai barma Allah zabi akan ya zaba mata mafi alkairi.+
Afraz ya dawo London amma kwata2 baya jin dadin kasar, ji yayi babu abunda yake son gani sai Zeena, har mamaki yake, kuma yakan tambayi kanshi wai mai yake damunshi, Ya lumshe ido tare da tuna surar Zeena, wani ni shadi yaji yana shigarshi, Zeena you are the best, kinfi ko wace mace, ke daban kike, burina in mallake ki.
Adeel yana zaune a cikin bedroom dinshi daka shi, sai singlet da shortener, yana danna laptop dinshi yana kallo yana murmushi, Hoton Zeena yake kallo, yana fadin Zeena ke tawa ce, saina mallake ki, you are my, bazan bari in rasa kiba, Mysha ta shigo d’akin harta zo kusa dashi bata sani ba, ganin Hoton Zeena a laptop din yana kallo yasa ranta ya baci, ta fisge laptop din tayi jifa dashi, Ya tashi rai a bace ya tsinka mata mari har sau biyu tare da fadin Mysha I hate you, you are evil, tace adeel ni ka mara? Ya daure fuska yace get out tare da nuna mata kofa, yace sai kin San kin fasa laptop din nan, ta fita da gudu tana kuka, toilet ya fada yayi wanka ya fito cikin kananan kaya ya mishi kyau sosai, Ya nufi d’akin ta, Ya ganta kwance kan gado tana rusa kuka, Ya tabe baki, Ya daka mata tsawa tare da fadin ke naki kukan najin dadi ne, sai na d’an d’ana miki irin radadin da kika sani a ciki, yana gama fadin haka ya fita.
Afraz yazo Nigeria, Ya samu labarin Zeena tana Japan karatu wajan mai gadin gidansu, Ya tambayi number dinta yace baida shi, Ya bashi kudi da yawa yace ga wannan plz ka samo min bayani akan inda take karatu a Japan din, mai gadi ya washe baki yace an Gama, Ya amsa number din Afraz din, akan zai kirashi idan ya samu information akan batun, Afraz ya wuce.
Zeena tana cikin class sun gama lecture, tana jiran zaheer yazo ya dauketa, sai ga wani bature yazo inda take, yace mata hello, Ya sakar mata murmushi ta amsa da hi,tana fadin haka ta tashi da nufin fita, yace mata please I want to talk to you, ta dan tsaya tare da fadin ok, Ya kalleta yace please sit down, batamusa mishi ba, ta zauna, Ya kalleta yace, na ganki a skul din nan, so ina lura dake kaman kina da damuwa, naga baki kula kowa, duk da harshen turanci yake mata maganan, ta kalleshi ta dan daure fuska, tayi shiru, ganin haka ya kuma tambayanta ya kikayi shuru, ganin ya matsa mata da tambaya yasa ta tashi tabar class din, tako ci sa’a ta hango zaheer da sauri ta nufeshi ta bude motar ta shiga, tace bros mai yasa kayi late din zuwa dauka na, Ya kalleta yace sorry little sis, naje amso abu ne, ta dan turo baki, irin na shagwaba, yayi dariya yaja motar suka wuce,
Mai gadin gidansu Zeena ya fad’a ma Afraz komai da komai na wajan da Zeena take karatu, yaji dadin labarin, Ya fara shiri na zuwa Japan,
Afraz an sauka a kasar Japan, bai bari ya huta ba, Ya nufi skul din, amma harya gama yawonshi baiga mai kama da Zeena ba, haka ya koma masaukin shi cikin takaici, haka kullum yake ta sintiri a skul din amma shuru kake ji, babu Zeena balle mai kama da ita, wajan sati daya kenan, yayi tsaki tare da fadin kodai mutumin nan wrong address ya bani, mai ma yasa na yarda dashi, Ya tada motarshi, da nufin ya wuce a dai2 lokacin Zeena ta fito daka class zata mota ya hango ta, da sauri ya fita, amma kafin ya karasa ta shige mota sun wuce, Ya koma da sauri yabi bayansu, har suka nufi gida, toh amma wani abu daya tsaya mishi a rai waye wannan namiji din daya dauko ta, miye halakan su, da yaga tana mishi dariya shima yana mata, wani bakin kishin Zeena din yaji yana shiganshi, wannan ne karo na farko daya taba jin kishin y’a mace.
Maryam obam ✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to yasmin darling 😘💃🏻
4⃣6⃣to5⃣0⃣
Yayi tsaki tare da buga sitiyarin motarshi, yaja motar ya wuce, washe gari tun 7 ya fito, Ya nufi gidan da Zeena ta shiga, Ya zauna a mota har wajan 11 baiga kowa ya fito daka gidan ba, wajan 12 zaheer ya fito ya shiga mota ya wuce, abun ya kuma daure mishi kai, Ya dai yanke shawaran bari ya shiga gidan ya gani, Ya fito ya nufi kofan gidan, yayi nocking, a lokacin Zeena tana falo din, tana kallo, tasa wata top mai budaddan hannu ruwan yellow da skin tie, tace yes coming, jin kaman muryan Zeena yasa yaji dadi, Ya bude kofan ya shiga, bata waigo ba, balle taga wanda ya shigo, Ya kafeta da ido, tare da wani shaukin sonta da yake kuma shigarshi, jin kaman ana kallon ta, yasa ta waiga, da sauri ta tashi tare da fadin afraz, abun daya faru da ita lokacin da taje gidansu Mysha ta tuna, anya banga afraz ba lokacin ba kuwa, kodai shi ya kaini asibiti da nayi accident, kai anya bashi bane, domin in shine zai dawo duba ni, inma bai dawo ba ummi zata fad’a min, ya kafeta da ido, ganin irin kallon da yake mata yasa ta daure fuska, tare da fadin mai ya Kawo ka nan, mai kake so? Yace Zeena ke nake so, ta d’aga mai hannu alaman yayi shuru, tace afraz plz ka fita, yace haba Zeena wlh sonki yamin yawa, plz ki tausaya min, ta kuma daure fuska tace afraz na fada Maka tun tuni bana sonka, ban son ganinka, koh ana so dole ne, Ya matso kusa da ita yace Zeena plz ki soni, ta bude baki za tayi magana yayi hugging dinta, ta kasa ko magana, sai zuciyanta dake ta buga mata, Ya fara mata magana kaman mai rad’a, Zeena ina sonki ina so ki zama matata, jin haka ta tureshi tare da yin baya, tace afraz I hate you, wlh ko babu maza a duniya gwara in mutu banyi aure ba, tana fadin haka tabar wajan da gudu, ya bita da kallo, dama akwai macen da zata ‘kishi, duk kudin da yake dashi, ga kyau, tabbas sai a yanzu afraz yasan ba komai kudi zai iya samo maka ba, fita yayi yabar gidan cikin takaici.+
Adeel yana zaune a falo yana kallo amma kwata2 hankalinshi baya wajan kallon, tunanin Zeena yake, Zeena kece komai nawa, bazan iya rayuwa ba tare dake ba, komai zai faru Zeena sai na mallake ki, yayi dan gajeran tsaki, tare da kara tsanan Mysha, jin maganan ta yayi tana fadin haba adeel tun dazu ina magana kayi banza dani, Ya kalleta yace inaji, tace ina so inje gidan mu, Ya sakar mata harara, tare da fadin ai babu ke babu fita, tace haba adeel wai mai yasa kake min haka, kwata2 baka kulani, kullum sai ka zauna kana bata lokacin ka akan tunanin waccen banzan Zeena mai take dashi wanda banda shi, Ya tashi tsaye rai a bace yace lallai Mysha sai yau na kara sanin ko ke wacece, bari kiji Zeena ta fiki kyau ta fiki tarbiya, ta fiki komai ki daina ma yaudaran kanki kina hada kanki da ita, ta fashe da kuka adeel ni fa matarka ce, kake yabon wata a kai na, kake nuna wata ta fini, ya kalleta yayi dan murmushi tare da fadin bazan taba kallonki a matsayin mata ta ba, Mysha yanda kika cuceni kika yaudare ni, kika barni cikin kunci haka zamu zauna ni dake, har Zeena ta kammala karatun ta in aureta, tace what adeel kasan mai kake fad’a kuwa? Yayi banza da ita ya haura sama ya barta a nan tana rusa kuka, tare da tausayama kanta.
Kullum afraz yana bin skul din su Zeena amma taki kulashi yayi naci yayi mitar amma duk a banza, gashi zasu fara exam a skul, dole ya koma London dan yayi exam, a na gobe zai koma yaje skul din su, a lokacin sun gama lecture ta fito zata koma gida, yau da kanta zata wuce don zaheer akwai inda zashi, ganinta yasa yayi sauri ya fito a mota ya nufeta, ganin yana nufota yasa ta daure fuska, bayan ya karaso ya kafeta da ido tare da fadin haba Zeena ke ko tausayi na, bakya yi, don Allah Zeena kiyi hakuri ki kulani, gobe zan koma nazo in miki sallama, ta kalleshi tace toh a sauka lafiya, taci gaba da tafiya, jin ta bashi amsa duk da cikin tsiwa tamai da gatsali, hakan yamai dadi, yaci gaba da binta Zeena ki taimaka kiban number dinki plz, ta daure fuska tace afraz dan Allah ka daina bina, bana so plz, yace shikenan amma ki bani number dinki, tace bazan iya ba, ganin haka yace toh muje in kaiki, shima tace bata so, daka karshe dai shiya bata tashi number din tare da rokonta ta kirashi, ta amsa da toh yana barin wajan ta yarda katin tare dayin tsaki.
Afraz ya koma London, sun fara exam amma kwata2 bai San abunda yake rubutawa ba, kullum da Zeena yake kwana yake tashi, yana mamakin irin azababban son da yake mata, amma yakan danganta abun da sakayya Allah ya mata akan abunda ya mata, yakan kara tausayin kanshi ya tabbata Zeena idan tasan shi ya mata fyade bazata taba kallonshi ba, yanzu Yama ya kare balle ace ta sani, ji yayi jikin shi yayi mishi sanyi, wayanshi dake gefe yaji yayi ringing da sauri ya dauka ganin sunan yasa ya dan canza fuska, domin yana tunani ko Zeena ce, Ya dauka tare da fadin hello mum, ta dayan bangaren ta amsa da hi, tare da fadin yakake, son kwana2 bana samin ka a waya ina ka shiga, yace mum naje Japan ne, tace Japan mai kaje yi? Yayi dan shuru can dai yace mum wlh ina sonta mum plz mum ki neman min auran ta, tace son wa kake so haka, yace mum Zeena, ta nanata sunan Zeena, a ina take yace a Abuja amma tana nan Japan tana karatu, tayi dariya tace toh kun dai daita ne, yace no mum bata sona, mum in ban sameta ba komai zai iya faruwa dani, jin irin yanda tilon d’anta wanda ta mallaka shi daya a duniya, yake magana hankalinta ya tashi, tace son karka damu koma yar gidan wanene ita zan nema Maka auranta, jin haka yace mum kin min alkawari, tace yes my son, kama fara Kiran kanka da mijin Zeena, yayi yar wata kara tare da fadin I love you mum, tayi dariya sannan sukayi sallama, ranan afraz ya kasance cikin nishad’i domin komai yake so iyayenshi suna bashi, gani yake kaman ma ya mallaki Zeena din.
Yau Sunday Zeena tana gida babu skul, tana kwance a d’akinta tana kallon sama, babu abunda take tunani sai adeel, ta rasa mai yasa kullum sonshi yake kara karuwa a ranta, duk kokarin da take don taga ta cireshi cikin ranta amma abun yaki, sai dai a kullum sonshi da yake karuwan mata, wani hawaye ne Ya zubo mata, adeel ina sonka, son da bazan iya musaltawa ba, duk da kunci amanata, ka barni da sonka a tare dani, kana tare da matarka ka manta dani, ta saki kuka mai karfi, taci kukanta babu mai rarrashinta don kanta tayi shuru, wayanta ta dauka ta kira daddy dinta, bugu daya ya dauka, yana jin muryanta yace Zeena kin yi kuka koh, jin tayi shuru ya tabbatar da hakan, yace Zeena har yanzu baki cire wannan abun a ranki ba koh, idan har kina son adeel kuma zaki aureshi ni dakai na zan nema miki auranshi, domin ban son abun da zai saki damuwa, jin haka tace dady a’a ka barshi, bai dace dani ba, inda yana so na da kanshi zai zo ya nemi aurena, mahaifin nata ya tausaya mata, yace Zeena ki dai yi tunani akai, tace toh dady su kayi sallama ta kashe wayan, tare da tunanin maganan da sukayi da daddy dinta, adeel ina sonka amma ka auri AMINIYA TA, wata zuciyan tace mata toh sai me, dan ya aureta, kawai in kina sonshi ki aureshi da wannan tunanin bacci ya dauketa.
Maryam obam ✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to yasmin darling 😘💃🏻
5⃣1⃣to5⃣5⃣
“tunda mum din afraz tayi mai magana akan zata neman mai auran Zeena ya cire duk wani fargaba da yake yi akan zai rasa ta, wannan ne Ya bashi da man yin karatu har suka kammala exam dinsu, kuma shine final year dinshi, zai zama cikakken engineer a quantity survey, a ranan daya gama exam din ji yayi kaman yayi tsalle ya gashi a Japan wajan Zeena domin yayi mugun kewanta, shi koda bata kulashi inya ganta ma dadi yake ji, amma dole yayi hakuri gobe tayi, yayi dan gajeran tsaki yaga dare ya mishi nisa ranan, washe gari da asuba ya tashi yayi sallah, sannan aka fara shiri, duk da wajan 10 zasu tashi yana Gama shiri ya nufi airport, Ya zauna kafin lokaci ya cika.+
Zeena tana gida yau bata je lecture ba, ta online take dubawa, wayanta dake gefe yayi kara, ta dauka taga abda, tace little sis yakike, abda ta amsa da lfya tare da fadin ya skul, ta amsa da lafiya, wai yaushe zaki zo Zeena, nayi missing dinki, Zeena tayi dariya tace kaman da gaske, abda tayi dariya tace dagaske nake, Zeena tace in mun gama exam zan zo, mun kusa farawa, jin haka abda tayi kara tare da fadin kizo keda bros zaheer, kice na mishi mata, Zeena tayi dariya tare da fadin wa innan kananan kawayen naki, a ciki kika zaban mai, ta dan turo baki kaman Zeena din tana gabanta, tace haba Zeena yanzu fa ina jss3 going to ss1 kinga ai ba za’a kirani da karama ba, Zeena tayi dariya sosai tace abda baki da dama, tace ina ummi abda tace tana kitchen Zeena tace takai mata Wayan, ta amsa da toh, ta nufi kitchen din taba ummi, bayan ta amsa suka gaisa tace ummi daddy ya fada miki wata magana, tace a’a maganan mai nene, tace akan adeel, ummi tace Zeena har yanzu baki cireshi a ranki ba, tayi shiru, ummi taci gaba da fadin ya kamata kima kanki fad’a, kara girma kikeyi Zeena ya kamata kisan abun da zai yiwu da wanda bazai yiwu ba, ki cireshi a ranki ki fara kema rayuwanki, tace toh ummi, tana fadin haka ta kashe Wayan, tabbas abunda ummi ta fad’a haka ne, Ya kamata ta cire adeel a ranta, amma ta yaya hakan zai faru taya zata cireshi, bayan kullum son shi kara karuwa yake a ranta, wani hawaye ya biyo kuncinta, adeel ka cuceni kaida Mysha kuna can kuna jin dadin rayuwanku kun barni cikin kunci da bakin ciki, sonka yamin yawa, mai zanyi sonka ya fita a raina, Allah sarki Zeena rashin masoyi babu dadi.
Afraz an sauka a kasar Japan, wani farin ciki yake ji tare da nishad’i yazo kasar da masoyiyarshi take, kai tsaye hotel ya nufa ya ajiye kayanshi, Ya fad’a toilet yayi wanka, bayan ya fito ya shirya cikin kananan kaya, yayi kyau sosai, kai tsaye gidansu Zeena ya nufa, yayi nocking, aka bashi izinin shiga, fatima ya gani wacce take kula da Zeena, Ya gaidata cikin harshen hausa da mamaki take amsa wa, don a zaton ta baya jin hausa don baiyi kama damai jin hausa ba, zata iya kiranshi da bature ko balarabe, Ya katse ta tare da fadin dan Allah Zeena nake nema, tace tana baya, ta nuna mai hanyan da zaibi, Ya shiga ya ganta cikin wani yar bukka, ta zabga uban tagumi, duk sai yaji wani kala kasancewan ya ganta a haka ya tabbata tana cikin damuwa, Ya matsa kusa da ita, Ya cire mata hannun, ganin afraz yasa tayi saurin tashi tare da fadin maiya Kawo ka nan, yace Zeena dan Allah ki tausayamin wlh Zeena ina sonki, tayi tsaki tare da fadin nace bana sonka wai afraz dole ne, ya kafeta da ido tare da fadin Zeena nasan abun daya faru da kike tunawa wlh Zeena na canza yanzu ba haka nake ba, tayi shuru bata kulashi ba, Ya matsa kusa da ita, tare da daura hannunshi kan kafadan ta, Zeena kece farin ciki na kece komai nawa, ganin bata kulashi ba ya janyota tare da rungumeta, babu abunda kake ji sai saukar numfashin su, sunyi wajan minti uku a haka, yace Zeena plz ki soni kaman yanda nake sonki, taja da baya tare da fadin afraz you will never change, who give you the right to touch me, let me tell you one thing, niba kalan yan iskan yan matanka din nan bane, so you better respect your self and leave, idonshi ya canza kala, Ya kuma matsawa yana fadin Zeena plz kiyi hakuri ki soni, tace nace bana sonka I hate you, yayi dan murmushi yace Zeena ko kina sona ko baki so na saina aureki kota wani haline, this is a promise, Ya fara tafiya tace afraz ya tsaya ba tare daya waigo ba, tace kace saika aureni koh, to bari kaji dana aureka gwara in mutu, ya waigo tare da matsowa kusa da ita, Ya janyo ta, ganin yanda ya daure fuska yasa ta kasa magana, Ya matsa da bakinshi kusa da nata kaman zaiyi kissing dinta, komai Ya tuna kuma ya fasa ya tureta ya fita, ta fashe da kuka tare da fadin wai mai yake shirin faruwa da ita ne, ta gefe daya ga adeel wanda take mutuwar so, tunanin shi ya hanata komai, ta dayan bangaran kuma afraz wanda yake takura mata, haka ta zauna taci kukanta, ta tashi ta shiga d’akinta.
Tunda wannan abun ya faru bata kara ganin afraz ba, hakan ya mata dadi, shima afraz din a washe garin ranan ya koma Nigeria, domin yaga inya biyema Zeena zai iya rasa ta, iyayenshi sunyi mamakin ganin yanda d’an nasu ya rame lokaci daya, sunyi mai tambayoyi afraz ya taso bai saba da karya ba, komai munin abu indai yayi in suka tambayeshi yana fada musu gaskiya, yace mum Zeena nake so ku nemo min auran ta, dady dinshi yace wannan wani irin sone afraz haka, wannan ne karo na farko daya ma iyayenshi karya tare da boye musu abu, Ya fada musu yanda suka hadu da Zeena amma bai fad’a musu ya mata fyade ba, daddy dinshi yace karka damu yar gidan waye, yace yar gidan senator abubakar daura ce, yace ok shikenan zanje gobe muyi magana dashi, yace thank daddy, Ya tashi yabar wajan cikin murna.
Zeena ta fito daka wanka taji karan wayanta da da sauri ta dauka, taga number ne, ta dannna tare da fadin hello, ta dayan bangaran aka amsa da Zeena, jin muryan tayi ya bugan mata dodon kunne, muryan da take burin ji take son ganin mai muryan, yace Zeena plz kiyi min magana, mai makon magana sai ta fashe da kuka, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, yace Zeena dan Allah ki daina wannan kukan, tace adeel mai yasa ka kirani, yace Zeena na kiraki in fad’a miki har yanzu ina sonki, son da nake miki bazan iya yima ko wace mace ba, plz Zeena ki yarda dani banci amanarki ba, jin haka tace adeel plz ban son wannan maganan, yace shikenan Zeena, amma ina so ki sani ina jiranki har ki gama karatun ki, Zeena ke daya ce macen da nake so kuma nake so in mallaka, kullum da sonki nake kwana nake tashi ta kashe Wayan da sauri, Zeena tayi shuru ta kasa furta ko kallama daya, wai mai yake shirin faruwa ne, Don son adeel tana yi amma mijin AMINIYA TA CE, hmmmm muje zuwa.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to sayyada darling 😘💃🏻
5⃣6⃣to6⃣0⃣
Mahaifin afraz bayan ya shiga d’aki ya dauki waya ya kira mahaifin Zeena, a lokacin mahaifin Zeena yana zaune a bedroom dinshi yana kallon news, yaji karan wayanshi, Ya dauko ganin sunan mai Kiran yasa ya dauka da sauri tare da fadin ranka ya dade barka da dare, mahaifin afraz ya amsa da yauwa, bayan sun gaisa mahaifin afraz yace mai gobe kana gida, Ya amsa da eh ranka ya dade, yace insha Allah gobe zanzo da yamma, mahaifin Zeena yace ranka ya dade lafiya dai koh, yace eh lafiya, mahaifin Zeena yace aida ka bari ni nazo da kaina, yace a’a karka damu zanzo da kaina, yace toh ranka ya dade sai na jika, sukayi sallama, bayan ya kashe Wayan yace lafiya kuwa alhaji umar na sidi yake son gani na, mahaifin afraz yana daya daka cikin manyan mutane a Nigeria, bama Nigeria ba kawai duk Africa, babu inda zaije yace yana son abu ba’ayi mishi ba, baya ga siyasa da yayi shi babban dan kasuwa ne, ranan mahaifin Zeena da tunanin zuwan alh umar na sidi yayi bacci.+
Zeena na kwance karar wayanta ne ya tashe ta, ta dauka tare da fadin hello cikin muryan bacci, jin muryan adeel yasa ta watsake, yace Zeena badai ni na tashe ki ba, tace a’a dama yanzu nake son in tashi, jin kaman ta dan sake, yasa yaji dadi, tare da fad’a mata yana so yazo Japan akwai maganan da yake so suyi, tace no adeel plz karka zo ka zauna kawai, yace Zeena kin San yanda nayi missing dinki kuwa? Tayi shuru yaci gaba da fadin da kin San yanda nayi missing dinki da baki cemin haka ba, Zeena na tabbata kema kina kewa na, tayi shuru dai bata kulashi ba, shi daya yake ta maganan shi, yace Zeena plz kimin magana, tace ina jinka, ta rasa mai yasa ta kasa fushi da adeel har take sauraranshi, ganin kaman bata son magana yasa yace gobe yana nan tafe, bai jira mai zata fad’a ba ya kashe wayan, wani farin ciki taji,tare da son ganin adeel, domin itama tana son ganinshi, lokaci daya kuma ta canza fuska, tare da tuna abun da ya faru, adeel kamin nisa yanzu ka auri AMINIYA TA, bazan iya auranka ba, tayi shuru na wajan minti biyar, can tayi tsaki tare da shirin zuwa skul.
Wajan karfe biyar mahaifin afraz yazo gidansu Zeena,tare da wani abokinshi aka saukesu a falon baki, sannan aka cika su da kayan ciye2, bayan sun gaisa cikin girmamawa, mahaifin afraz yace alh abubakar, nazo neman alfarma ne, Ina nema ma d’ana afraz auran yarka Zeena, mahaifin Zeena yace haba ranka ya dade ai kai ka wuce wannan, na bama danka auran Zeena, sukayi godiya sannan abokin mahaifin afraz yace a yanke musu sadaki su biya mahaifin Zeena yace Su bada dubu hamsin, nan da nan yaje mota ya dauko wani akwati da kudi cike a ciki, yace ga wannan 50million ne ni na kara akan sadakin, sukayi godiya sannan mahaifin afraz ya kuma neman alfarma akan yana son a daura auren nan da sati biyu, mahaifin Zeena yace babu matsala, sukayi sallama suka wuce.
A lokacin da dadyn Zeena ya shiga gida, Yama mahaifiyar Zeena din bayani kuma hakan ya mata dadi, domin tana ganin idan tayi aure hakan zai sa ta cire adeel a ranta, sannan tace kar’a fad’ama Zeena din maganan auran, domin karta sama kanta damuwa, tunda ta kusa zuwa in ta dawo sai mu mata bayani, daddyn Zeena ya yarda da shawaran matar tashi.
Adeel ya sauka a kasar Japan, kasancewan yana da address din gidansu Zeena din, Ya nufi gidan amma yayi rashin sa’a tana skul, yace bari yaje ya dawo, hotel ya nuna ya fada toilet yayi wanka, yasa kananan kaya, sannan ya fashe jikinshi da turare, Ya zauna tare da jiran anjima kadan yayi ya koma gidansu Zeena din, sai murmushi yake shi daya.
A lokacin da Zeena ta dawo fatima ta fad’a mata anzo nemanta bata nan, bata damu da ko waye ba, tace ok, ta nufi dakinta tayi wanka, tasa wata doguwan riga, ta dauki littafinta ta nufi bukka, don karatu gobe zasu fara exam, littafin dai yana hannunta kuma inka ganta zaka rantse shi take karantawa, amma tunani take, ganin adeel tayi ta gabanta yana murmushi sai taga kaman gizo, yake mata, tasa hannunta tare da taba fuskanshi, taga bai bace , ta tabbata dai shi dinne, tayi sauri ta cire hannunta, tare da fadin adeel yaushe Kazo? Yayi murmushi tare da fadin tun dazu, ya kura mata ido, yaga ta kara girma da kyau wani sonta ne yake kara shigarshi, itama ta nata ban garan, wani sonshi ne yake kuma shiganta, dukansu sunyi shuru suna kallon Juna, ya katse shurun tare da fadin Zeena kina sona kuwa kaman yanda nake sonki, jin haka yasa ta fashe mishi da kuka, hankalinshi yayi mugun tashi, yace Zeena plz kibar wannan kukan kar ki sani cikin damuwa, tace adeel mai yasa ka gujeni, a lokacin da nake bukatan ka, sannan kuma yanzu ka dawo zaka kara yaudara na, yayi sauri ya rufe mata baki da hannunshi yace Zeena ban yaudareki ba, Zeena kece macen dana fara so, kuma har yanzu banga wacce nake so ba sai ke, Zeena Mysha ce ta rabamu akan selfishness nata nan ya bata labarin yanda sukayi da Mysha, tayi shuru babu abunda take sai hawaye, ta kasa furta komai, ganin haka shima yayi shuru yana kallonta, ganin yanda take kuka bazai iya jure ganin kukan ba, Ya matsa kusa da ita, Ya fara share mata hawayen, tare da fadin plz kibar wannan kukan, jin haka tayi shuru, wani sonshi taji ya kuma karuwa a ranta tare da tausaya mishi, tabbas komai Ya faru laifina ne, inda ban Kawo maganan karatu ba da yanxu munyi aure, da hakan bai faru ba, a yanzu ta yarda bazata iya auran ko wani namiji ba inba adeel ba, domin shi daya take so, shima yana sonta, a ranan Zeena ta sake da adeel kuma tace mishi a shirye take data aureshi, hakan yamai dadi, sannan tace karya sake ya saki Mysha domin tana sonshi kuma komai tayi sonshi yasa tayi hakan, yace babu komai duk abunda tace shi zaiyi, daka karshe yayi mata sallama ya wuce masaukin shi, ranan su duka sun kwana cikin farin ciki.
Maryam obam✍✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to yasmin darling 😘💃🏻
6⃣1⃣to6⃣5⃣
Su Zeena an fara exam, cikin kwanciyan hankali, kullum suna tare da adeel, ji take kaman bata taba shiga wani matsala ba, haka shima ta ban garan adeel din, Ya manta da komai, jira yake ta gama exam su dawo Nigeria tare ayi maganan bikinsu, har zaheer yasan adeel kuma ya yaba da hankalinshi, Zeena ta fito daka lecture ta hango adeel ta wajan wata bishiya ya kura mata ido, harta karaso kusa dashi bai daina kallonta ba, tayi dan murmushi tare da fadin yaushe Kazo, yace tun dazu suka sami waje suka zauna, Ya kuma kafeta da ido, tace adeel lafiya kuwa, yace Zeena tun jiya nake jin wani kala a jikina, tace muje asibiti mana, yace no ba abun asibiti bane, tace toh miye adeel, yace inaji a jikina kaman za’a raba mu, tace adeel wannan wani irin magana ne haka, yace Zeena jikina yana bani haka, ta dan daure fuska tare da fadin sai dai in Kaine zaka gujeni, yace haba Zeena komai zai faru bazan taba gudun kiba, kece farin ciki na, tace toh adeel ka daina wannan tunanin ni taka ce, babu mai raba mu, yace Allah yasa, suka d’an taba fira sannan suka tashi suka wuce.+
Anata hidiman bikin Zeena da afraz, ba tare da sanin taba, harta zaheer bai San mai ake shiryawa ba, abda kuma daddy dinsu ya gargadeta akan karta fad’a ma Zeena din tace toh taja bakinta tayi shiru.
A lokacin da dadyn afraz ya fad’a mishi yanda sukayi wani farin ciki ne Ya kamashi tare da kara godema iyayenshi, kuma yana alfahari dasu akan komai yake so suna bashi, tunda yaji wannan labarin bai kara neman Zeena ba, yana ganin ya riga ya gama samun ta, ya rasa wani irin so yake mata, bai taba tunanin zai so mace tace bata sonshi ba sai Zeena, Ya lumshe ido tare da fadin Zeena you are special, zan iya yin komai a kanki Zeena.
Yau Thursday su Zeena an gama exam, ta fito tana murna don gobe zata Nigeria taba dady dinta surprise akan sun dai daita da adeel, kuma a shirye take data aureshi, tayi dan murmushi ta tabbata idan dady dinta yaji wannan labarin zaifi kowa murna, kai tsaye gida ta nufa, tana shiga ta fad’a toilet tayi wanka, ta fito falo ta tarar da zaheer yana kallo tace yaushe ka shigo bros, yace ban dade da shigowa ba, yace ya exam din tayi dan murmushi tare da fadin alhamdlh, yace gobe sai gida, tayi dariya tare da fadin ai wutun ma ba wani mai yawa bane, yace inye hutun wata nawa kikeso a baku, tace kaman 3month yayi dariya tare da fadin Zeena baki da dama, tace goben kaima zaka bimu yace eh tare zamu tafi, fatima itama ta fito kana ganinta kasan tana cikin murna domin ta kosa ta ganta a Nigeria itama, taga yan uwanta da abokan arziki, nan suka zauna suna ta fira gwanin sha’awa,
Adeel ya kira Zeena yace yana gidansu ta wajan bukka, tace tana xuwa, ta tashi da sauri ta dauki dan karamin gyale ta yafa a kanta kasancewan gown ne a jikinta na yan kanti, ta fito ta hango shi a zaune, wani dadi taji tare da kara sonshi ta aiyana a ranta adeel ka hadu, babu macen da zata ganka taji bata sonka, wani kishin shi taji data tuna yana da mata, ta karaso kusa dashi ta zauna ta gefe suna kallon Juna, Ya sakar mata murmushi tare da fadin gobe sai gida koh, ta daga mai kai alaman eh, yace ya exam din, ta amsa da alhamdlh, ya kuma kura mata ido yace Zeena bana gajiya da ganinki, kullum sonki kara karuwa yake a raina, tayi murmushin jin dadi, tace nima haka Kaine mai sani farin ciki, koda ina fushi inna tuna dakai sai inji farin ciki, ya sakar mata ido yana kallonta, tace wannan kallon fah, yace ina mamaki ne Zeena, tace name, yanda kike fad’amin wa innan kalaman da bakin ki, jin haka ta dan rufe fuska tana dariya, sunyi fira sosai daka karshe sukayi sallama akan sai gobe,
A yau juma’a aka daura auren Zeena abubakar da afraz umar na sidi, wajan karfe biyu na rana, daurin auren ya tara manyan mutane sosai, ranan afraz yayi kyautar naira kaman za suyi kuka, domin duk wanda ya gani a masallacin indai mai bukata ne saiya bashi kudi, ranan ji yake kaman an mai bushara da gidan aljanna, mahaifinshi duk yana kula dashi, hakan ba karamin dadi ya mishi ba, na ganin danshi cikin farin ciki, duk wanda suka zo daurin aure sun watse,
Su Zeena sai wajan karfe biyar suka sauka, kowa yaga driver dinshi yana jiranshi adeel ya shiga mota akan sai yazo, suma suka shiga nasu motar, kai tsaye gida suka nufa, Zeena taga gidansu makil da mutane, gabanta ya fadi tace mai yake faruwa, driver na parking ta shiga da sauri tana Kiran ummi abda dady, ga mamakin ta sai ta gansu dukansu, da gudu ta nufi ummi, tace ummi wannan taron fa, ganin bata, bata amsa ba ta nufi dady tace dady wannan taron fah, yayi dariya kije ki huta Zeena kafin muyi magana bata musa ba, ta nufi dakinta, tayi wanka ta fito taga an ajiye mata abinci kala2 a d’akin tayi murmushi ta zauna taci tayi nak, ta kwanta abinta,
A lokacin da adeel yaje gida, yaga Mysha shi harga Allah ya manta da tunda ya tafi bai kirata ba, ta rame tayi duhu, tana ganinshi ta taso da kuka, tana fadin adeel kamin adalci kenan, ka tafi wajan sati biyu amma babu waya, baka San ya nake ba, Ina matsayin matarka, duk sai yaji ta bashi tausayi, bai kuma dace ya mata haka ba, amma saiya dake yace ai bance dole ki zauna ba, yana fadin haka ya haura sama, ta zauna tana ta kuka, d’akinshi ya nufa, Ya fada toilet yayi wanka, ya fito cikin wata shadda dinkin kaftani yayi mishi kyau sosai, sai kamshi ke tashi, yaganta a inda ya barta tana ta aikin kuka, jikin shi yayi sanyi, a gaskiya baya mata adalci matarshi ce, kuma ko babu komai tana da hakki a kanshi, zama yayi ya kira sunanta ta amsa da na’am cikin muryan kuka, yace kinyi abinci ta amsa da eh, yace Kawo min, wannan ne karo na farko daya taba tambayanta abinci, jiki na bari ta nufa kitchen ta Kawo mishi, farfesun kayan ciki da fried couscous, da coconut juice, Ya zauna yaci sannan yace mata ya gode, hakan ya mata dadi sosai, Ya kuma Kiran sunanta ta amsa, yayi shuru can yace mata inaso inyi miki magana tace toh inaji, yace ina so in kara aure, gabanta ya fadi tare da tausayin kanta, ta daure dakyar tace wa zaka aura, yace Zeena ta Mike tsaye tare da fadin Zeena, yace yes ta fashe da kuka tare da rokan shi akan ya auro ko wacece, amma banda Zeena, yayi dan murmushi tare da fadin bazan iya kallon ko wace mace ba inba Zeena ba, ita nake so, itace farin ciki na, yana fadan haka ya fita, ta zauna tana tausayin kanta, tabbas idan adeel ya auri Zeena bazata iya zama a gidan ba, duk irin son da take mishi .
Zeena sai wajan 7 ta farka a lokacin dady dinta ya shigo d’akin, yace Zeena bacci kikayi bayan kin San babu kyau baccin bayan la’asar, tace daddy wlh gajiya ne yasa nayi, Ya nemi waje ya zauna akan wata kujera dake d’akin, tayi murmushi tace daddy wai taron miye akeyi haka, yace Zeena ta amsa da na’am ina so in fad’a miki wani magana, tace toh daddy nima zan fad’a Maka wani magana wanda zai saka farin ciki, yayi dariya tare da fadin mai nene Zeena, tace daddy ka fadamin kafin sai in gaya ma, yace toh Zeena, yayi shuru na wani lokaci can yace Zeena ina so ki zama mai biyayya, sannan ki zama y’a mai bin umarnin iyayenta, tayi dariya tace haba daddy baka taba sani abu naki yima ba, daddy wlh komai kake so indai bai sabama shari’a ba zan yima shi, yaji dadi tare da samun karfin giwa, yace Zeena wa innan mutanan da kike gani sun taru ba dan kowa suka taru ba sai dan ke, taji gabanta ya fad’i, tace daddy dan ni kuma, yace eh, a yau aka daura miki aure, inaso kimin biyayya duk da baki San da auren ba sai yanzu, ta Mike da sauri tare da dafa kirjinta tace aure, ta fara yin baya kaman zata fad’i.
Maryam obam ✍✍