AMINIYATA CE CHAPTER B KARSHE
👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to yasmin darling 😘💃🏻
6⃣5⃣to7⃣0⃣
Daddy yayi sauri ya riko ta, tare da zaunar da ita akan gado, yace Zeena baki son auren? Tayi shiru babu abunda take sai hawaye, tabbas bana son wannan auren amma taya zan iya kallon daddy ince mai bana so, daddy ya katse ta tare da fadin Zeena kiyi magana nasan ba zaki bani kunya ba, tace daddy Kaine mahaifina baza ka, zaba min abunda zai cutar dani ba, jin haka yace Allah ya miki albarka, yana ta mata godiya, tare da fadin yana alfahari da ita, yace ta tashi ta shirya yanzu za’azo daukanta, ta amsa da toh, sannan ya fita, kuka ta saki mai karfi yanzu na rasa adeel a karo na biyu, a lokacin da muka dai daita, mai yasa haka ya faru dani, jin kaman karar bude kofan d’akin yasa ta goge hawayen fuskanta, ummi ce ta shigo ita da abda, ummi ta zauna ta gefenta tare da fadin Zeena naji dadi da kika yarda da wannan auren kika mana biyayya, yanda kika mana biyayya kema Allah ya baki masu yi miki, ta amsa da ameen, sannan tace abda ta taya ta shiryawa don anzo daukanta, jin haka hawayen da take boyewa suka zubo mata, yanzu wa aka aura mawa ni, Ya zanyi da son adeel, abda tace muje ki shirya, bata musa ba, ta shiga toilet tayi alwala tazo tayi sallah bayan ta idar abda ta taimaka mata ta
shirya, ummi da daddy suka kuma shigowa suka mata nasiha akan tabi mijinta tayi mishi biyayya, domin aljannarta yana karkashin kafan mijinta, komai naki yanzu ya koma kan mijinki a yanzu Muda muke iyayenki bamu da iko dake, sai mijinki dan haka kimai biyayya yi nayi bari na bari, babu abunda take sai kuka, ummi ta kama hannunta suka fita falo, a nan yan daukan amarya suka amsheta da yan uwan ummi din akai mota da ita, motocin daukan amarya sun kai hamsin, Zeena kuka take kaman ranta zai fita, abda nata faman rarrashi, hankalinta bai tashi ba sai da taga an kunna mota an fara tafiya, har suka karasa gidan da za’a kaita tana Manne jikin abda, maitama aka kaita wani katoton gida ne suka shiga, gidan ya hadu fadan haduwan gidan ma bata lokaci ne, wata kanwar ummi ta zagayo tace ta sauka da kafar dama tare da bismillah, hakan ko tayi suka shiga cikin gidan, akai sama da ita, cikin wani d’aki aka kaita wanda yaji kayan alatu, wanda suka Kawo amarya suka duba gidan tare da San barka, aka fara shirin tafiya anan hankalin Zeena ya kuma tashi ganin harda abda za’a wuce dakyar ta saki abda suka wuce, aka barta ita daya, tana ta aikin kuka, kanta ya fara ciwo dan taci kuka ta kwanta bata dade ba bacci ya dauke ta.+
Wajan karfe goma afraz ya shigo gidan shida wasu abokanshi, yace Su zauna a falo yana zuwa kai tsaye sama ya haura, Ya nufi dakinta ya bude yaga tana bacci, Ya matsa kusa da ita yaga fuskanta ya kumbura da alaman taci kuka, duk sai yaji ta bashi tausayi, ya fita ya kashe mata wutan d’akin, yace ma abokanshi tana bacci bazai kuma iya tashin ta ba, sukace ai dole ma ka tashe ta, yace haba ai tunda ta kwanta sai dai wata rana kun hadu, daya daka cikin abokan mai suna jabir yace inma mu anki taso mana ita ai kai dole ka tashe ta, suka saka dariya sannan ya rakasu suka wuce, bayan ya dawo dakinshi ya nufa ya kwanta amma kwata2 ya kasa bacci, sai tunanin Zeena yake,
Zeena ta farka wajan karfe dayan dare jikinta ya rufeta da zazzabi, ta tashi ta nufi toilet, tayi wanka amma jikin dai sai zafi yake mata, ta kwanta akan carpet din d’akin ta dauko blanket ta rufe kanta tana rawan sanyi,ga yunwa da take ji.
Afraz dai shima ya kasa bacci ya tashi ya nufi d’akin Zeena din ya kunna wutan d’akin ya hangota a kasa tana rawan sanyi, da sauri ya nufeta yace Zeena maike damun ki, jin kaman muryan afraz yasa ta dago da kanta tace afraz, Kaine wanda ka aure ni, bai bata amsa ba, ya dauketa cak ya daura ta kan gadon d’akin sannan yaje ya kashe a.c din d’akin, fita yayi a d’akin Jim kadan ya dawo da cup a hannunshi tea ne a ciki da paracetamol, ya bata taki amsa, ganin haka yasa ya kafa mata kofin a baki, ta fara sha, duka ta shanye sannan ya bata paracetamol tasha, sannan ta kwanta, bata dade ba bacci ya dauke ta, shima a gefenta ya kwanta yana kallonta tare da kara godema Allah daya mallaka mishi Zeena a matsayin mata, ranan afraz kasa bacci yayi, bini2 ya duba Zeena yaga ya take ciki, can yaga jikinta ya fara zufa ya cire mata blanket din, sai wajan karfe biyar ta farka a lokacin afraz ya nufi masallaci, itama toilet ta fada tayi alwala tazo tayi sallah, bayan ta idar ta zauna akan dadduma din, tana tunani yanzu afraz shine mijin da daddy ya zaba min, zan iya kallon afraz a matsayin miji kuwa, wani haushin afraz din taji ya kamata, a lokacin afraz ya bude kofan ya shigo ya ganta kan dadduma yaje kusa da ita ya kira sunanta Zeena bata amsa ba kuma bata d’ago ba, hakan bai dameshi ba yaci gaba da magana ya jikin naki, tace ina ruwanka da jiki na, Malam ka fita ka barni dan Allah, jin haka ya fita dakin shi ya nufa, Ya kwanta, dan jiya baiyi bacci ba.
Tunda adeel ya fita jiya da daddare yaje gidansu wajan alhaji amma yayi rashin sa’a baya nan, sai mahaifiyar shi ya tarar da kannan shi, suka d’an taba fira, mamanshi ta tambayeshi Mysha yace tana gida, tace in gaidaku tace muna amsawa rannan tazo ta wuni a nan ai, yace eyya ya tashi sukayi sallama,
A lokacin daya koma gida yaga Mysha a falo tana gyangyadi, ya matsa kusa da ita wato da bana nan kullum fita kike koh, tayi shuru ya daka mata tsawa bada ke nake ba, tace babu inda naje gidanku kawai naje da gidanmu, yace uban wa yace ki fita, tace kayi hakuri, yace daka yau in kika kuma fita ban sani ba saina bata miki rai, Ya haura sama,.
Wayan shi ya dauka ya kira Zeena amma a kashe hankalinshi duk ya tashi, ya tuna yana da number din zaheer ya kira bugu daya yayi ya dauka, bayan sun gaisa yace mai yakira Zeena number dinta yaki shiga, zaheer yace eh Zeena tana gidanta, yace ban gane ba, zaheer ya fadama adeel abunda ya faru, sakin Wayan yayi tare da zama a kasa, yanzu Zeena tayi aure, kai wasa zaheer yake min, hakan bazai faru ba, Zeena tawa ce, he is joking daukan key din motanshi yayi ya nufi gidansu Zeena din, amma abunda idonshi ya gani ya tabbatar mishi da haka din, ganin motoci yayi da mutane birjik a kofar gidan, Ya tambayi wani a kofar gidan yace mai yar sanata ce take aure yace wacce a ciki, mutumin yace Zeena, hankalin adeel ba karamin tashi yayi ba, ya shiga motarshi yana tuki kwata2 baya ganin gabanshi, bai ma San mai yake yiba, shidai ya farka ya ganshi a asibiti jikin shi duk ansa flasta a jikinshi, yaga alhaji da mamanshi, ga Mysha dake gefe tana ta kuka, alhaji yace sannu adeel ya jikin ya amsa da sauki, kwanan shi biyar aka sallame shi, a asibitin, Allah ya taimake shi babu karaya, sai dai bugawa da yayi a bayan shi.
Zeena tana dakinta a kwance afraz ya shigo d’akin ta daure fuska ya matso kusa da ita ta tashi da sauri ya janyo ta, ta fada kanshi, yace ina zaki, tace ka sake min hannu, yayi dan murmushi tare da kuma janyo ta, suka had’a ido tayi sauri tasa kanta a kasa, yasa hannunshi kan kirjinta ya fara wasa da wajan, ganin haka yasa ta fara kuka, Ya cire hannun shi tare da fadin Zeena plz ki bar wannan kukan, ganin haka yasa ta tashi da sauri tayi wajan toilet, tace afraz I hate you bazan taba sonka ba tana fadin haka tayi sauri ta shige toilet, yayi murmushi ya fita tare da fadin zanyi maganin ki.
Maryam obam ✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to basma darling 😘💃🏻
7⃣0⃣to7⃣5⃣
Jin karan kofan d’akin yasa ta fito, tare da rufe kofan ta da key, tayi tsaki yanzu wannan ne miji na, ai wlh ba zaka taba samun abunda kake soba a waje na.
Afraz tunda ya fita daga d’akin ta, gidan ya bari gaba daya, bai dawo ba sai wajan karfe tara, a lokacin tana falon kasa tana kallo har ya shigo bata sani ba, ji tayi an rukota ta baya, ta saki ihu, duk ta tsorata, ta bashi dariya amma saiya dake, ta fara kokarin kwace kanta daka rikon daya mata, ya sake ta, ganin haka yasa ta tashi zata gudu ya kuma kamo ta, tace ka sake ni, yai kaman bai jita ba, ya kuma janyo ta, Ya zaunar da ita kan kafanshi, ta daure fuska, ganin shima ya tamke fuska yasa ta kasa cewa komai, yace kinci abinci, ta daga mai kai alaman eh, ya janyo wani leda, ya bata, bata musa ba ta amsa, ta tashi daga jikinshi tayi sauri tayi sama, ya bita da kallo harta bace sannan ya kauda kanshi, yayi murmushi ya rasa wani irin so yake ma Zeena.+
Bayan taje d’aki ta bude ledan taga kaza ne da ice cream da abinci, ta bude kazan taci da ice cream, tayi nak, ta fad’a toilet tayi wanka ta fito tana shafa mai, a lokacin ya shigo d’akin ya kura mata ido, ta waiga ta ganshi ta tashi da sauri tare da fadin miye na shigo min d’aki babu neman izini, yayi dan murmushi tare da fadin nida d’akin matata saina nemi izini, ganin yana matsowa yasa tayi shuru, tana matsawa baya, har ta hade da bango, shima ya karasa ya manneta, suna shakan numfashin juna ganin yanda yake kallonta yasa tayi kasa dakai, wani nugun sha’awanta yake ji, wanda bazai iya hakuri ba a wannan lokacin, daukanta yayi cak, ganin haka ta fara wintsil2 amma ko a jikinshi dakinshi yayi da ita, ya ajiyeta a kan gadon d’akin sannan ya rufe kofan, ganin haka ta fara kuka tare da fadin dan Allah afraz karka min komai kayi hakuri, yace Zeena nifa mijinki ne, kuma ina bukatanki, tace bana so bana sonka dan Allah karka min komai, yace bakya sona koh, tace eh, yace owk shikenan bari in kira daddy dinki saiki fad’a mishi ni kuma saina sauwake miki, jin haka tace karka had’a ni da iyayena bana so, yace toh ki bani hakki na, tun daka lokacin bata kuma magana ba, nima ganin haka na fita daka d’akin, na koma da asuba naga Zeena tana ta kuka shi kuma afraz yana ta rarrashi yana bata hakuri, dakyar ya shawo kanta tayi shuru ya kaita toilet yace ta shiga tayi wanka, ganin kaman bata da niyan shiga ya dauketa yasa ta cikin ruwan zafi, ya kura mata ido wani sonta yake kara shiganshi, ganin kallon da yake mata yasa ta kuma sakin kuka, duk ya rud’e yana tambayanta mai nene, tace ka fita, yayi dariya ya tashi ya fita.
Adeel ya yanke hukuncin komawa China da zama domin bazai iya zama a nja ba, yaga Zeena tare da wani mijin, tunda ya tabbatar tayi aure komai nashi ya canza abu kadan, yaita fad’a akai, ga saurin fushi da yake yi yanzu wanda duk bayayi da, itama Mysha ta samu labarin Zeena tayi aure hakan ya mata dadi domin tana ganin yanzu zata samu mijinta, tayi alkawarin ko zuciyan dutse gareshi saiya sota, wannan kenan.
Zeena inta tuna abun daya faru tsakaninta da afraz sai tai ta kuka, yanzu ya rabata da adeel kenan, yayi nasara akan ta, ta tuna lokacin daya mata alkawari saiya mallake ta, gashi yanzu ya sameta, wani takaici taji tare da bakin ciki, tace afraz zaka iya samu na, amma ba zuciya na ba, bazan taba sonka ba,
Afraz tunda ya sami Zeena duk ya daina harkan mata, domin duk yawon barikin da yayi bai hadu da wacce takai Zeena ba, tunda ya sami Zeena yanzu bashi da wani buri illa ace Zeena ta fara sonshi, shine abunda yake fata.
Yau watan Zeena uku da aure, tana zaune a falo, afraz ya fito, ta kalleshi tace ina son magana dakai, yace inaji, tace inaso inje gida yau yace ba yanzu zaki fara fita ba, ta dan marairaice tace plz, yace in kina so kije gida sai kin min kiss a baki, jin haka yasa ta daure fuska tare da kau dakai gefe, yace ok ni na fita ganin zai fita yasa ta tashi da sauri ta shiga gabanshi, yaso yayi dariya yanda yaga tazo da gudu amma saiya dake, ta rufe idon ta, yace ai bani zan miki ba, ke zaki min, ta dan turo baki, ganin yana kallonta tace toh ka daina kallo na, Yayi dariya yace in ban kalleki ba taya zaki min, tayi shuru tana kallon kasa yace ni zan fita in ba zakiyi ba, da sauri tayi mishi kiss din sannan ta ruga da gudu, Ya bita da kallo yana dariya, ya koma ya zauna a falo din, Jim kadan ta fito cikin wani material mai kalan c green ya mata kyau sosai, yace Zeena yanzu haka zaki fita babu mayafi, tace toh ba’a mota bane, yace koma a miye ban yadda da hakan ba, ki koma kije kisa hijab muje, kaman za tayi kuka ta koma ta dauko hijab din, yace kinga yanda kikayi kyau kuwa, ta turo baki, suka fita, wani super market suka je, yace suje tayi musu tsaraba suka shiga ta dauka abubuwan d zata dauka ya biya suka wuce, bayan ya sauketa yace wajan 5 zaizo daukanta tace toh, ta shige, masu gadin gidan yasa suka shigar da kayan tsaraban,Ya wuce.
STORY CONTINUES BELOW

Da gudu ta shiga cikin gidan ta fada jikin ummi dake zaune akan kujera tana kallo, ummi tace miye haka karki karyani, tayi dariya tace kai ummi bakiyi missing dina ba, tace banyi ba, ta turo baki tare da fadin bari daddy yazo dama shine yake sona, jin haka ummi tayi dariya abda ta fito da gudu sukayi hugging juna, tace wow zee zee dina kinga yanda kika kara kyau da haske, Zeena tayi dariya tare da fadin haba, abda tace dagaske, tun shigowan Zeena ummi ta lura da hakan, tana zargin kaman ciki take dashi, nan suka zauna suna ta fira, har daddy ya dawo shida zaheer, shima daddy yaji dadin yanda yaga yar tashi cikin kwanciyan hankali, wanda ada yake farga akan idan Zeena tayi aure, babu wanda yasan fyade aka mata, amma a yau ya cire ganin yar tashi cikin jin dadi, zaheer yace ya maganan skul dinki tace ina yi ta online, yace ok sai a kara bada himma, tace toh bros,sai bayan magrib afraz yazo daukan Zeena, a lokacin ya shigo suka gaisa da mahaifin Zeena din da ummi, mahaifin Zeena nata sa mishi albarka, ummi tace ma Zeena tazo zata mata magana kafin su wuce, tace toh ta tashi suka nufi d’akin ummi din, ummi tace Zeena ciki kike dashi, tace a’a ummi banda komai, jin haka ummi tabar maganan, tace gaskiya kinyi dacen miji, ji yanda yake kula dake sosai ki rike mijinki dakyau, ada ina fargaban idan kikayi aure duk mijin da kika aura bazai ga darajarki ba, tace ummi kaman ya, nan ummi ta fad’a mata abun daya faru, ta tashi da sauri tace fyade tare da fadin afraz.
Maryam obam✍✍
👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fancy habiba 😘💃🏻
7⃣5⃣to8⃣0⃣
Ummi tace ki zauna Zeena amma ina tayi hanyan waje, ganin haka itama ummin ta rufa mata baya, falo ta nufa taga daddy shi daya, yace Zeena kije mijinki yana jiranki tun dazu, dan Allah Zeena ki zauna da mijinki lafiya, yaron yana da kirki, wani hawaye ne Ya zubo mata na takaici yanxu idan daddy yasan afraz shine wanda ya mata fyade ya zai dauka abun, tace toh daddy nagode, tayi waje ta sameshi a mota yana jiran ta, da murmushi yace sai yanzu kika fito, ganin tayi banza dashi yasa ya lura da hawayen da takeyi, hankalinshi ya tashi a duniya babu abun daya tsana kaman yaga Zeena tana kuka, yace Zeena mai nene, mai akayi miki, waya taba ki, ganin bata da niyan yi mishi magana yasa yaja motar, tuki yake amma zuciyan shi yana tafarfasa, gani yake kaman an mata wani Abu ne, har suka karasa gida, suna shiga ta fita da sauri ganin haka shima ya bita, yana fadin Zeena Zeena amma ko ta waigo ta kalleshi harta shiga d’akinta, Ya bita shima ya kamo mata hannu yana fadin haba Zeena mai ya faru kike ta kuka, plz ki fad’a min, ta waigo cikin kuka tace afraz wlh ka cuceni ka cuci iyayena sun daukeka mutumin kirki amma basu San ko kai waye ba, na tsaneka bana son ganinka, jin haka duk ya rude yace Zeena maiya faru wai don Allah, tace afraz ka rabani da budurcina kayi min fyade, jin haka yasa gaba daya ya dauke wuta, har d’aci yaji bakinshi yana mishi, ganin yana yinshi yasa ta tabbatar dashi dinne, dakyar ya iya cewa Zeena kiyi hakuri, wlh nayi nadama akan abunda nayi miki, tace afraz wlh ba zaka taba canzawa ba, ka cuceni duk da abun daka aikata sai da kaje ka nemi aurena domin wani manufa naka, yace Zeena wlh na aureki ne tsakani da Allah, Zeena nayi miki fyade ne dan in rama wulakancin da kika min a gaban mutane, amma bayan haka sai Allah ya jarabceni da sonki, Zeena wlh son da nake miki na gaskiya ne bazan iya rayuwa ba tare dake ba, tace afraz ban taba sonka ba bazan kuma taba sonka ba, kana da son kanka ka, kai da kanka kasan ban dace dakai ba, rayuwa na ba kalan naka bane, na tsare kaina amma saida ka tozartani, bazan taba yafe Maka ba, yace Zeena kiyi hakuri nima nasan ban kyauta ba, koda son da nake miki aka barni, nasan wannan babban sakayya ne, ta toshe kunnenta, tace dan Allah ka fita ka barni, yace zan fita Zeena amma dan Allah kibar wannan kukan tace ina ruwanka dani, jin haka ya kama hanyar fita har yazo bakin kofa ta kira sunan shi afraz, Ya waigo tace bazan iya zama dakai ba zan fad’ama daddyna abun da kamin na tabbata bazai barni in zauna dakai ba, jin haka ya matso yana fadin Zeena ki tausayamin ina sonki inna rasa ki, banga amfanin rayuwa na ba, wani jiri takeji yake dibanta tace afraz wlh ka…. Ta fad’i kan gadon d’akin da sauri ya nufeta yana fadin Zeena Zeena duk ya rude ya rasa abun yi, Ya dauketa cak ya nufi waje da ita, cikin mota yasa ta, kai tsaye asibiti ya nufa da ita, aka shigar da ita cikin emergency room,
STORY CONTINUES BELOW

nan da nan likitoci suka tsaya a kanta Ana ta aune2, afraz ya kasa tsaye ya kasa zaune kanshi keta sara mai, duk wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali, Jim kadan Dr din ya fito yace afraz ya sameshi a office, bayan yaje office din Dr din yace mai congratulations your wife is pregnant, afraz cikin murna yace what ciki, you mean Zeena tana da ciki, dr yace yes harna wata biyu, yace zan iya ganinta Dr yace ka barta ta huta, kuma sannan ku daina tasar mata da hankali yanzu jininta ya hau, kasan mace mai ciki bata son damuwa, afraz yace insha Allah, Ya fito sai a sannan ya samu nutsuwa, abda ya kira ya fad’a mata Zeena tana asibiti an kwantar da ita, ta rude tare da fadin maiya sameta, yace karta damu ciki take dashi da murna ta kashe Wayan ta nufi d’akin ummi ta fada mata, ummi tayi dariya tare da fadin ai dama na sani, taje ta fad’a ma daddy yace toh su shirya sai suje, ummi tace in sunje ita zata kwana da ita, daddy yace babu damuwa, hakan ko akayi suka nufi asibitin sun tarar da afraz a reception, ya nuna musu d’akin da aka kaita, suka shiga, kwata2 shi ya kasa shiga d’akin domin a yanzu kunya had’a ido yake da Zeena, koda suka shiga tana bacci bata farka ba, dady da abda suka fito zasu wuce afraz ya raka su, sannan ya dawo dakyar ya daure ya shiga, ganin bata farka ba yayi ajiyan zuciya, ummi tace afraz kaje gida ka huta, ya amsa da toh sannan ya fita,.
Sai wajan karfe biyun dare ta farka taganta a gadon asibiti, ga ummi kuma a gefe tana sallah, abubuwan daya faru suka fara dawo mata, jin muryan ummi tayi tana fadin kin farka Zeena sannu, ta amsa da yauwa, ummi ta had’a mata tea amma tace bata sha, ummi tace ai kodan abunda ke cikin ki kyasha tace ummi ciki na kuma, tace eh tunda yanzu bake daya bace, a nan ne ta gane inda ummi ta dosa, tace ciki nake dashi yanzu cikin afraz a jikina, ummi ta mika mata kofin ta amsa tasha.
Afraz shima daya je gida kasa baccin yayi yana fargaban kar Zeena ta fad’a ma iyayenta, ta gefe daya kuma yana farin cikin zai samu d’a, Ya janyo wayanshi ya kira mum dinshi har sau biyu ba’a dauka ba, Ana ukun ne ta dauka tace afraz lafiya kuwa, yace mum Zeena nada ciki, cikin murna tace wow tana ina, yace tana asibiti, tace gobe zata ita da daddy dinshi, mum din afraz taji dadin wannan labarin zata samu jika, tana son yara sai kuma Allah ya bata kwaya d’aya,
Washe gari afraz tun wajan karfe 7 ya nufi asibiti amma duk sammakon shi, daya je ya tarar da mum dinshi, tana kusa da Zeena tana bata abinci, suka hada ido da Zeena din ta sakar mai Harara, sannan tayi kasa da kanta, yace ya jikin ta amsa da sauki, sannan ya gaida ummi ta amsa cikin fara’a, yace mum ina daddy tace anjima zai zo, mum din afraz tace ma ummi taje gida ta huta zata zauna da Zeena din, babu yanda ummi ta iya dole ta wuce driver din mum din afraz ya kaita gida,..
Kwanan Zeena uku aka sallameta, mum din afraz tace gidanta zata tafi da Zeena afraz bai so hakan ba, amma dole ya hakura, aka wuce da Zeena din, Kwanan ta biyu gidan mum dinshi shima yace ya dawo gidan, yana tsoran kwana shi daya, mum ta Harare shi, tace toh da bakai daya kake kwana ba, yayi dariya tare da Sosa kai, afraz shima ya tare a d’akinshi na gidan, Zeena ta lura da yanda afraz yake zumudi akan cikin, hakan ya mata dadi don tana ganin ta sami hanyan da zata Rama abun daya mata, idan suna zaune mum ta Kawo abinci sai taki ci, tace ta koshi ta lura da hakan yana bata mishi rai, amma idan baya wajan tana ci,
Satin Zeena biyu gidansu afraz, Ya matsa ma mum dinshi akan zasu koma gidansu, dakyar ta yarda aka samar ma Zeena wata yar dattijuwa,mai suna jamila don ta dinga kula da ita.
Tunda suka dawo bata sakar ma afraz, hakan bai dameshi ba, shi abun daya dameshi yanda bata son cin abinci, yana zaune a falo jameela ta haura sama da abinci, sai gata ta sauko dashi, yace wannan ba abincin Zeena bane tace eh tace bata ci, ranshi ya baci yace mai taci, jameela tace babu abunda taci, Ya amsa abincin ya haura sama rai a bace, tana zaune akan gado tana game a wayanta, Ya shigo cikin fushi ya fisge Wayan tare da mika mata abincin, yace Zeena wannan wani irin abune ni na miki laifi a kaina zaki rama ba akan yaro na ba, wanda bai San komai ba, zan iya juran komai amma bazan jura wannan ba, ko kallo bai isheta ba, yace Zeena ki amsa wannan abincin kici, taki amsa babu yanda baiyi da ita ba, amma taki amsa, ganin haka ya fita rai a bace Jim kadan sai gashi da ummi, ummi tama Zeena ta tas, tace da badan kina da ciki ba wlh dazai nayi mugun bata miki, babu shiri ta dauki abincin taci, ummi tace ma afraz ai duk shine yake mata wasa sai yasa take iskanci, ummi ta wuce, afraz ya dawo tana ganin shi ta saki kuka, nan ya zauna yana ta rarrashi.
STORY CONTINUES BELOW

Maryam obam✍✍
👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fancy habiba 😘💃🏻
8⃣0⃣to8⃣5⃣
Adeel yana kwance a bedroom dinshi, Mysha ta shigo da plate dauke da kayan fruit a ciki, ta ajiye mai a gefe, tace adeel ka tashi kaci, ya amsa da toh, ya tashi ya faraci ita kuma ta koma gefe tana kallonshi tana murmushi, ci kawai yake amma yana tunanin Zeena ya rasa mai yasa kullum son Zeena yake kara karuwa a ranshi, duk yanda yayi kokarin ya cireta a ranshi amma abun yaki, wani zubin har tausayin Mysha yake yanda take bashi kulawa sosai amma bai taba jin sonta ba, tunda suka zo China ya dan sakar mata, domin yana tsoran kar Allah ya kamashi da hakkin ta, itama kanta tasan ba sonta yake ba, tasan Zeena yake so, sai yasa har gobe take jin haushin Zeena, kuma take kishi da ita.
Afraz tunda Zeena ta sami ciki kullum Ana gida Ana kula da ita, baya zuwa ko ina, daka tayi motsi kadan yace miye, ganin haka yasa da gangan ma sai tayi abu, shi kuma sai ya rude yaita tambayanta mai nene, mai kike so, tace wannan tace wancan sai ya Kawo tace bashi ba, ga abunda take so, haka zai koma ya nemo mata, inya Kawo kuma tace ta koshi, haka kullum suke,
Zeena tana kwance a d’aki, tana tunanin yanda zata Japan, tana tunanin dakyar afraz ya barta, jin karan bude kofan da yayi ne yasa ta rufe ido kaman mai bacci, ya zauna akan gadon kusa da ita, yasa hannunshi a bakinta yana wasa dashi, ta dan bude ido daya, suka had’a ido yayi dariya tare da fadin har kin tashi, ta dan turo baki tare da fadin mutum yana baccin shi, Kazo kana damu na, yayi dariya tare da fadin ai ba zaki iya bacci ba in ina kusa, ta daure fuska tare da turo baki, yayi dariya yace idan kina fushi kinfi kyau, ya Mike bari inje in dawo, tace afraz ya amsa da na’am tace exam din mu a Japan kasan dole inje, yayi shuru can yace bari in dawo sai muyi maganan, tace toh har ya kusa fita tace ina zaka, da mamaki yake kallonta wannan ne karo na farko data taba tambayan shi ina zashi, hakan ya mishi dadi yace zani wajan budurwana ne, abun ya bata mata rai amma sai ta dan dake, duk yanda ta dake saida fushin ya fito, yayi dariya yace ashe Ana sona, ta sakar mishi Harara, ya fita yana dariya,
Tunda afraz ya fita ta kasa zaune ta kasa tsaye yanzu afraz dagaske tad’i zaije, wani bakin ciki taji ya taso mata, tayi tsaki inma yaje tadin ni ina ruwana, wata zuciyar tace da ruwanki mana mijinki nefa, ta dauki wayanta ta kira shi, bai dauka ba, ranta ya baci ta kuma kira bai dauka ba, ta zauna tana huci, ya bude kofan d’akin ya shigo ta sakar mai harara, yace bakiyi bacci ba, wani haushi ya kamata ya zauna a kusa da ita tare da fadin ance in gaidaki, ta daure fuska tace ka fitar min a d’aki, yace haba Zeena daka fadan sako ki bari in baki labarin abunda ya faru jin haka yasa ta fara mishi kuka, yace Zeena kin San ban San wannan kukan naki plz kiyi shuru, ya janyo ta ya kwantar da ita kan kirjinshi, yace Zeena ke bakya sona dan nace naje tadi shine kike kuka, ta kuma sakin kukan ai dole kaje tadi tunda ni ka cuceni kamin ciki shi yasa kake min haka, yaso yayi dariya amma saiya dake, yace haba Zeena ba haka bane so nake in Kawo miki wacce zata dinga taya ki aiki, tace bana so ai inada jamila, inma mutum daya yayi kadan ko masu aiki nawa ne ummi zata iya Kawo min, yayi dan murmushi najin dadi ya tabbata yanzu Zeena ta fara sonshi tunda har ta fara kishin shi, yace ni ban cika son masu aiki ba kinga idan ko matata ce zata fi kula dake, a matsayinki na yayarta, tace Allah ya kiyaye in zama yayarta taje ta nemi yayarta bani ba, ta tashi daka kan kirjin nashi cikin fushi, yace come on Zeena ina zaki kin San ban San fushin ki, tayi banza dashi, ganin haka yace kin San banso inga kina damuwa kar kisa babyna shima cikin damuwa, tace wato wannan bata ni yake ba, ta baby dinshi yake ba, ta kwanta ta baya tare da juya mishi baya, abun ya bashi dariya shima ya kwanta ta gefenta,.
Zeena yanzu indai taga afraz ya fita toh haka zata zauna cikin fushi da kunci, taita tunanin ya fita tad’i ne, shi kuma afraz din yana mata hakan ne don yaga ko tana sonshi, ya fito cikin kananan kaya ya mishi kyau yana ta kamshi, ya kalleta yace Zeena nayi kyau kuwa, ta kauda kai gefe, yayi dariya tare da fadin plz ki fad’amin in banyi kyau ba, in canza kaya kar inje tad’i taki fitowa, tayi tsaki tare da tashi ta haura sama ya bita da kallo yana dariya, Jim kadan sai gata ta fito dauke da key din mota a hannunta, yace ina zaki tayi banza dashi, ya tare ta, ta saki kuka tace ni ka matsa min in wuce gidan mu, yace haba Zeena akan wani dalili zaki gida, jin haka tayi shuru ya kuma tambayanta tayi shuru, ya kamo mata hannu yace zo muje na fasa fitan, jin haka yasa taji dadi harta yarda suka koma ciki.
STORY CONTINUES BELOW

Adeel yana office amma duk ya kasa komai, yana tunanin Zeena wanda ya zaman mishi aiki kullum, ya lumshe ido tare da fadin Zeena Allah ya jarabce ni da sonki, na rasa yanda zanyi in cireki a raina, na kasa yarda da na rasa ki, kullum zuciya na tana yaudara na, akan ban rasa ki ba, karan wayanshi ne ya katse shi, ya dauka yaga Mysha ce, yayi dan tsaki sannan ya dauka, tace adeel yaushe zaka dawo ina so muje hospital inga Dr, yace anjima tace toh sai Kazo bai bata amsa ba ya kashe Wayan,.
Afraz yace ma Zeena ta shirya suje Japan din,ta hada kayanta sukaje suka ma kowa sallama, washe gari suka cala harda jameela, wani gida suka sauka, gidan duk da bashi da girma sosai amma ya hadu, afraz yana ba Zeena kulawa sosai, ita da kanta yanzu ta yarda tana son afraz, amma ta kasa nuna mishi, bata san ya Riga ya ganota ba, satinsu biyu suka dawo Nigeria, afraz yayi siyayyan kayan yara sosai na mata da maza, d’aki daya aka ware aka shirya komai yasa ansa na mace dana miji, yace duk wanda aka haifa ga kayanshi nan.
Cikin Zeena yakai wata takwas, amma inka ganta zaka ce haiyuwa yau ko gobe ne, don cikin yayi girma sosai, afraz yace in kika haifi mace sunanki zan sa Zeena, tayi dariya tace saboda me, yace Zeena saboda ina sonki, kullum sonki kara karuwa yake a raina, tayi dan murmushin jin dadi, yace amma ni har yanzu ba’a sona, ta dan turo baki suka hada ido tayi sauri ta kawar da kanta gefe, yayi dariya yace idan namiji kika haifa sunan wa zaki sa, tace ka bari saina haiyu sai in fad’ama, yace shikenan Allah ya kaimu wannan ranan Zeena, ji nake kaman yanzu inga kin haiyu, ki haifar min mace mai kama dake, tayi dariya tace in namiji ne kuma yayi kama dakai, ya kalleta yace Zeena kina son ki haifa mai kama dani tace eh, a ranta tace afraz kana da kyau, inna haifa mai kama dakai ba karamin kyau zaiyi ba, nan suka zauna suna ta fira cikin so da kauna, aka kira afraz a waya ya dauka tare da fadin gani nan zuwa, bayan ya kashe yace Zeena bari inje in dawo, tace ina zaka yace wasu kaya dana bada oder dinsu aka Kawo, tace daka bari gobe mana afraz yace bazan dade ba ta dan turo baki, yayi dariya tare da fadin Zeena say you love me, ta turo baki yayi dariya sannan ya fita, ita dai bata so wannan fitar ba, dan yanzu bata son afraz yana nisa da ita.
Tunda afraz ya fita har wajan karfe goma bai dawo ba, duk ta rud’e, ta kirashi baya shiga, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ta fito falo ta zauna, taji ana buga kofan falo din da sauri ta nufi falo din tare da fadin sai yanzu ka dawo koh, amma abunda ta gani yasa ta tsorata police ta gani guda biyu, suka ce kece matar afraz koh, ta amsa da eh, sukace yayi accident a halin yanzu yana asibiti, tace innalillahi wa inna’ilaihira jiun, da sauri ta koma ta dauko hijab tabi su, kai tsaye asibitin suka nufa, a lokacin suma su mum din afraz din suka zo da daddy dinshi, Zeena ganin yana yin afraz yayi mugun bata tsoro, duk jikinshi ansa flasta kuka take kaman ranta zai fita, tana fadin afraz saida nace karka fita amma kaki, mai yasa ka fita afraz, yayi mata dan murmushi yana son yin magana amma ya kasa, tace afraz ina sonka, yayi murmushi a dai2 lokacin oxygen din da aka samai ya tsaya.
Maryam obam✍✍
👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
8⃣5⃣to9⃣0⃣
Shima komai nashi ya tsaya, ganin haka ta fara girgiza shi, tana fadin afraz, dr ya shigo da sauri yace Su bashi waje, nan ya fara yan dube2 amma ina rai yayi halinshi, Zeena ta bude kofan ta shigo da sauri itama mum ta biyo ta, tace Dr ya tashi, dr yace sai dai kuyi hakuri Allah ya mishi rasuwa, Zeena ta saki dariya tare da fadin no afraz bazai mutu ba, ta matsa kusa dashi tana fadin afraz ka tashi ka karyata wannan Dr din, nasan ba zaka mutu ka barni ba, get up afraz, taja hannunshi taga yayi nauyi, ta saki ya fadi sharaf, ta saki kuka afraz why mai yasa ka tafi a lokacin da nake bukatan ka, afraz saida sonka yamin yawa sannan zaka tafi ka barni, ka tashi your unborn child is waiting for you, ba haka mukai dakai ba afraz ka tashi ta fara girgiza shi, mum dinshi ita Suman tsaye tayi ta kasa ko motsi, a dai2 lokacin dad dinshi shima ya shigo cikin rudewa ganin afraz din yasa ya tabbatar ya rasu, hawaye ke zuba a idonshi, ya matsa kusa da matarshi wanda ko digon hawaye yaki ya zubo mata a ido, gaba daya ta shiga cikin d’imuwa, Zeena ta taso da sauri tace dad kace ya tashi, yace Zeena kiyi hakuri afraz bazai tashi ba, addu’a kawai zamu mai, tace dad afraz ya mutu dagaske, yace eh Zeena ta fara baya2 tana fadin no no he will not die and leave me lokaci daya jiri ya dauketa ta fadi kasa, da sauri dad din afraz ya fita ya kira Dr, nan da nan aka fara dubata, shi kuma afraz aka daukeshi akai gida dashi da safe za’a kaishi gidanshi na gaskiya, labarin mutuwan ya baza ko ina, su abda suma sun zo asibitin, ita zauna da Zeena ummi kuma tana gidansu afraz din, kwata2 hawaye yaki zuba a idon mum sai zuciyanta dake faman buga mata, ummi tana ta mata maganan da zata danji sanyi, kiyi hakuri duk mai rai mamaci ne, kar ki zama mai butulci a lokacin da Allah zai baki shi bai fad’a miki ba, har kika sameshi kika nuna farin cikin ki, yanzu Allah ya dauki kayanshi sai ki zama mai hakuri duk son da kike mai Allah yafi sonshi, sai a sannan kukan yazo mata tace shine daya dan dana haifa yau na rasa shi, don me bazan damu ba, afraz shine komai nawa shine kwai na dana mallaka yau na rasa shi, mutuwa mai yasa baki daukeni ba, ummi ta to she mata baki, tare da fadin kar kima Allah butulci karki manta rayuwa akwai mutuwa kuma koda afraz bai mutu yanzu ba zai mutu wata rana, ki zama mai hakuri da dan gana, a yanzu babu abun da afraz yake so sai addu’a wannan kukan bashi da amfani, tayi shuru tare da fadin haka ne, ta tashi da sauri ta nufi dakinta sai gata da alkur’ani ta matsa kusa da inda aka ajiye afraz din ta fara karatu tana kuka,
Zeena wajan karfe hudu ta farka, ta bude idonta tare da fadin afraz ta tashi zaune, taga ansa mata drive, ta tsige abun ta tashi da sauri, jin kaman motsi yasa abda ta farka taga Zeena na kokarin bud’e kofa da sauri ta tashi tace Zeena ina zaki, tace abda ina afraz, tayi shuru, tace abda dagaske afraz ya rasu, abda tace Zeena kizo ki zauna, tace no ta bude kofa ta fita abda ta rufa mata baya tana kiranta ganin bata da niyan tsayawa yasa ta koma da sauri ta dauki jakanta ta fito bata ga Zeena din ba, da sauri ta shiga motarta, tayi waje ta hangota tace ta shigo suje, babu musu ta shiga, gidan su afraz din suma suka nufa, sun shiga falon gidan sunga ummi da mum suna ta karatu gefe kuma afraz ne kwance an rufe shi, da sauri ta karasa wajanshi ta bude shi, taga fuskanshi kaman mai yin bacci, tace afraz mai yasa kamin haka ka tashi in fad’ama abun da kake so kaji, afraz ina sonka ina sonka afraz, baby dinka yana son ya rayu dakai plz ka tashi kar ka maida baby dinka maraya, ummi ta matso kusa da ita, tace Zeena ta rungume ta, tana kuka ummi afraz ya tafi ya barni, saida nace karya fita ummi amma yaki, inda bai fita ba da hakan bai faruba, ummi tace Zeena kiyi shuru ki daina fadin haka koda bai fita ba indai kwananshi ya kare bazai kara koda kwana daya ba, tace ummi bazan iya rayuwa ba tare da afraz ba ummi ina sonshi ummi mai yasa haka yake faruwa a kaina, ta kuma sakin kuka, ummi tace ta daina kuka tamai addu’a ne, ta matsa kusa dashi tana tamai addu’a tana kuka, duk wanda yake wajan saida ya tausaya mata.
Mutane sun taru a kofar gidansu afraz din sosai daka gari2 mutane keta zuwa, anyi mishi wanka an mai sutura dama an barshi sai wajan 8:30 za’a kaishi gidanshi na gaskiya hakan ko akayi, a lokacin da aka dauko shi Zeena kuka take kaman ranta zai fita, ta kankame gawan, dakyar aka banbare ta, aka wuce dashi, rayuwa kenan, afraz yayi mutane sosai, Allah yasa mu cika da imani,
Ana ta zuwa musu gaisuwa kota ina, Zeena kwata2 taki cin komai, anyi2 taki ci, saida mum din afraz tazo da kanta sannan ta yarda taci, shima ita take bata a baki, ci kawai take amma bata jin dadin komai, inta kalla cikin ta saita fashe da kuka, tana fadin afraz ka tafi baka ga baby dinmu ba.
A yau akayi addu’an uku, mutane kowa ya watse, an barsu su kadai, ciki harda ummi wanda tun da akayi rasuwan itama tana gidan ita da abda, yanzu daka Zeena sai mum din marigayi afraz da dad dinshi, suka rage a gidan sai masu yi musu hidima, Zeena duk ta rame tayi baki kullum tana cikin hawaye, mum taita bata baki akan tayi hakuri ta rage damuwa ba ita daya bace, inta kiyin shuru saita ce mata da afraz yana nan ba zaiji dadin wannan kukan ba, inta ji hakan sai tayi shuru.
Wata ranan juma’a da yamma Zeena tana zaune tana karatun alkur’ani mum ta shigo d’akin ta zauna a gefe, Zeena ta saki kara tare da fadin ciki na, mum tace Zeena sannu tashi muje asibiti, ta kira daya daka cikin masu aikin gidan suka kama Zeena din aka sata a mota sukai asibiti da ita, tana ta faman fadin ciki na, nan da nan akai labour room da ita, mum ta kira ummi ta fada mata bata dade ba tazo, tare da abda, sun dauki wajan awa uku amma shiru babu labari sai azaba da Zeena din kesha, akace dole sai an mata operation domin ba zata iya haiyuwa da kanta ba, suka ce sun yarda ayi, nan da nan likitoci sukayi kanta aka fara aiki, su ummi babu abun da ake sai addu’a, wajan karfe goma da wani abu Dr ya fito yana murmushi tare da fadin congratulations an sami twins, baby girl nd baby boy, mum ta d’aga hannu tana ma Allah godiya, suka cewa Dr din zasu iya shiga yace eh, da sauri suka nufi dakin, Zeena tana kwance yaran na gefe, babu abun da take sai hawaye, mum ta dauki yaran duka yaran kaman afraz kaman an tsaga kara, kaman yayi yawa sosai, mum itama ta fara hawayen tace Allah sarki afraz, Allah yaji qanka, ummi tace Zeena ki daina wannan kukan, tace ummi naso afraz yaga wannan ranan inga wani irin murna zaiyi, ya dade yana burin zuwan wannan ranan, ta kuma zubo da wani hawayen wani son yaran taji yana shiganta tare da tausaya musu.
NOTE: masu cewa afraz bai kamata ya mutu ba, inya mutu novel din ya baci, kufa tuna Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, kuma karku manta duk mai rai mamaci ne. Rayuwa akwai mutuwa akwai tsufa kar ko da yaushe mu dinga mantawa da mutuwa, duk da novel ne wannan ya kamata mu dinga sawa akwai mutuwa a ciki ba kullum ace sun kasance tare cikin jin dadi da kwanciyan hankali ba, indai akace kullum haka ne Ya zama babu amfani rubuta littafi tunda ana mantawa da mutuwa ya zama shirme, sau da yawa ina rubuta akan abun da yake faruwa ne, Allah yasa mu dace
Maryam obam✍✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fancy habiba 😘💃🏻
7⃣5⃣to8⃣0⃣
Ummi tace ki zauna Zeena amma ina tayi hanyan waje, ganin haka itama ummin ta rufa mata baya, falo ta nufa taga daddy shi daya, yace Zeena kije mijinki yana jiranki tun dazu, dan Allah Zeena ki zauna da mijinki lafiya, yaron yana da kirki, wani hawaye ne Ya zubo mata na takaici yanxu idan daddy yasan afraz shine wanda ya mata fyade ya zai dauka abun, tace toh daddy nagode, tayi waje ta sameshi a mota yana jiran ta, da murmushi yace sai yanzu kika fito, ganin tayi banza dashi yasa ya lura da hawayen da takeyi, hankalinshi ya tashi a duniya babu abun daya tsana kaman yaga Zeena tana kuka, yace Zeena mai nene, mai akayi miki, waya taba ki, ganin bata da niyan yi mishi magana yasa yaja motar, tuki yake amma zuciyan shi yana tafarfasa, gani yake kaman an mata wani Abu ne, har suka karasa gida, suna shiga ta fita da sauri ganin haka shima ya bita, yana fadin Zeena Zeena amma ko ta waigo ta kalleshi harta shiga d’akinta, Ya bita shima ya kamo mata hannu yana fadin haba Zeena mai ya faru kike ta kuka, plz ki fad’a min, ta waigo cikin kuka tace afraz wlh ka cuceni ka cuci iyayena sun daukeka mutumin kirki amma basu San ko kai waye ba, na tsaneka bana son ganinka, jin haka duk ya rude yace Zeena maiya faru wai don Allah, tace afraz ka rabani da budurcina kayi min fyade, jin haka yasa gaba daya ya dauke wuta, har d’aci yaji bakinshi yana mishi, ganin yana yinshi yasa ta tabbatar dashi dinne, dakyar ya iya cewa Zeena kiyi hakuri, wlh nayi nadama akan abunda nayi miki, tace afraz wlh ba zaka taba canzawa ba, ka cuceni duk da abun daka aikata sai da kaje ka nemi aurena domin wani manufa naka, yace Zeena wlh na aureki ne tsakani da Allah, Zeena nayi miki fyade ne dan in rama wulakancin da kika min a gaban mutane, amma bayan haka sai Allah ya jarabceni da sonki, Zeena wlh son da nake miki na gaskiya ne bazan iya rayuwa ba tare dake ba, tace afraz ban taba sonka ba bazan kuma taba sonka ba, kana da son kanka ka, kai da kanka kasan ban dace dakai ba, rayuwa na ba kalan naka bane, na tsare kaina amma saida ka tozartani, bazan taba yafe Maka ba, yace Zeena kiyi hakuri nima nasan ban kyauta ba, koda son da nake miki aka barni, nasan wannan babban sakayya ne, ta toshe kunnenta, tace dan Allah ka fita ka barni, yace zan fita Zeena amma dan Allah kibar wannan kukan tace ina ruwanka dani, jin haka ya kama hanyar fita har yazo bakin kofa ta kira sunan shi afraz, Ya waigo tace bazan iya zama dakai ba zan fad’ama daddyna abun da kamin na tabbata bazai barni in zauna dakai ba, jin haka ya matso yana fadin Zeena ki tausayamin ina sonki inna rasa ki, banga amfanin rayuwa na ba, wani jiri takeji yake dibanta tace afraz wlh ka…. Ta fad’i kan gadon d’akin da sauri ya nufeta yana fadin Zeena Zeena duk ya rude ya rasa abun yi, Ya dauketa cak ya nufi waje da ita, cikin mota yasa ta, kai tsaye asibiti ya nufa da ita, aka shigar da ita cikin emergency room,+
nan da nan likitoci suka tsaya a kanta Ana ta aune2, afraz ya kasa tsaye ya kasa zaune kanshi keta sara mai, duk wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali, Jim kadan Dr din ya fito yace afraz ya sameshi a office, bayan yaje office din Dr din yace mai congratulations your wife is pregnant, afraz cikin murna yace what ciki, you mean Zeena tana da ciki, dr yace yes harna wata biyu, yace zan iya ganinta Dr yace ka barta ta huta, kuma sannan ku daina tasar mata da hankali yanzu jininta ya hau, kasan mace mai ciki bata son damuwa, afraz yace insha Allah, Ya fito sai a sannan ya samu nutsuwa, abda ya kira ya fad’a mata Zeena tana asibiti an kwantar da ita, ta rude tare da fadin maiya sameta, yace karta damu ciki take dashi da murna ta kashe Wayan ta nufi d’akin ummi ta fada mata, ummi tayi dariya tare da fadin ai dama na sani, taje ta fad’a ma daddy yace toh su shirya sai suje, ummi tace in sunje ita zata kwana da ita, daddy yace babu damuwa, hakan ko akayi suka nufi asibitin sun tarar da afraz a reception, ya nuna musu d’akin da aka kaita, suka shiga, kwata2 shi ya kasa shiga d’akin domin a yanzu kunya had’a ido yake da Zeena, koda suka shiga tana bacci bata farka ba, dady da abda suka fito zasu wuce afraz ya raka su, sannan ya dawo dakyar ya daure ya shiga, ganin bata farka ba yayi ajiyan zuciya, ummi tace afraz kaje gida ka huta, ya amsa da toh sannan ya fita,.
Sai wajan karfe biyun dare ta farka taganta a gadon asibiti, ga ummi kuma a gefe tana sallah, abubuwan daya faru suka fara dawo mata, jin muryan ummi tayi tana fadin kin farka Zeena sannu, ta amsa da yauwa, ummi ta had’a mata tea amma tace bata sha, ummi tace ai kodan abunda ke cikin ki kyasha tace ummi ciki na kuma, tace eh tunda yanzu bake daya bace, a nan ne ta gane inda ummi ta dosa, tace ciki nake dashi yanzu cikin afraz a jikina, ummi ta mika mata kofin ta amsa tasha.
Afraz shima daya je gida kasa baccin yayi yana fargaban kar Zeena ta fad’a ma iyayenta, ta gefe daya kuma yana farin cikin zai samu d’a, Ya janyo wayanshi ya kira mum dinshi har sau biyu ba’a dauka ba, Ana ukun ne ta dauka tace afraz lafiya kuwa, yace mum Zeena nada ciki, cikin murna tace wow tana ina, yace tana asibiti, tace gobe zata ita da daddy dinshi, mum din afraz taji dadin wannan labarin zata samu jika, tana son yara sai kuma Allah ya bata kwaya d’aya,
Washe gari afraz tun wajan karfe 7 ya nufi asibiti amma duk sammakon shi, daya je ya tarar da mum dinshi, tana kusa da Zeena tana bata abinci, suka hada ido da Zeena din ta sakar mai Harara, sannan tayi kasa da kanta, yace ya jikin ta amsa da sauki, sannan ya gaida ummi ta amsa cikin fara’a, yace mum ina daddy tace anjima zai zo, mum din afraz tace ma ummi taje gida ta huta zata zauna da Zeena din, babu yanda ummi ta iya dole ta wuce driver din mum din afraz ya kaita gida,..
Kwanan Zeena uku aka sallameta, mum din afraz tace gidanta zata tafi da Zeena afraz bai so hakan ba, amma dole ya hakura, aka wuce da Zeena din, Kwanan ta biyu gidan mum dinshi shima yace ya dawo gidan, yana tsoran kwana shi daya, mum ta Harare shi, tace toh da bakai daya kake kwana ba, yayi dariya tare da Sosa kai, afraz shima ya tare a d’akinshi na gidan, Zeena ta lura da yanda afraz yake zumudi akan cikin, hakan ya mata dadi don tana ganin ta sami hanyan da zata Rama abun daya mata, idan suna zaune mum ta Kawo abinci sai taki ci, tace ta koshi ta lura da hakan yana bata mishi rai, amma idan baya wajan tana ci,
Satin Zeena biyu gidansu afraz, Ya matsa ma mum dinshi akan zasu koma gidansu, dakyar ta yarda aka samar ma Zeena wata yar dattijuwa,mai suna jamila don ta dinga kula da ita.
Tunda suka dawo bata sakar ma afraz, hakan bai dameshi ba, shi abun daya dameshi yanda bata son cin abinci, yana zaune a falo jameela ta haura sama da abinci, sai gata ta sauko dashi, yace wannan ba abincin Zeena bane tace eh tace bata ci, ranshi ya baci yace mai taci, jameela tace babu abunda taci, Ya amsa abincin ya haura sama rai a bace, tana zaune akan gado tana game a wayanta, Ya shigo cikin fushi ya fisge Wayan tare da mika mata abincin, yace Zeena wannan wani irin abune ni na miki laifi a kaina zaki rama ba akan yaro na ba, wanda bai San komai ba, zan iya juran komai amma bazan jura wannan ba, ko kallo bai isheta ba, yace Zeena ki amsa wannan abincin kici, taki amsa babu yanda baiyi da ita ba, amma taki amsa, ganin haka ya fita rai a bace Jim kadan sai gashi da ummi, ummi tama Zeena ta tas, tace da badan kina da ciki ba wlh dazai nayi mugun bata miki, babu shiri ta dauki abincin taci, ummi tace ma afraz ai duk shine yake mata wasa sai yasa take iskanci, ummi ta wuce, afraz ya dawo tana ganin shi ta saki kuka, nan ya zauna yana ta rarrashi.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fancy habiba 😘💃🏻
8⃣0⃣to8⃣5⃣
Adeel yana kwance a bedroom dinshi, Mysha ta shigo da plate dauke da kayan fruit a ciki, ta ajiye mai a gefe, tace adeel ka tashi kaci, ya amsa da toh, ya tashi ya faraci ita kuma ta koma gefe tana kallonshi tana murmushi, ci kawai yake amma yana tunanin Zeena ya rasa mai yasa kullum son Zeena yake kara karuwa a ranshi, duk yanda yayi kokarin ya cireta a ranshi amma abun yaki, wani zubin har tausayin Mysha yake yanda take bashi kulawa sosai amma bai taba jin sonta ba, tunda suka zo China ya dan sakar mata, domin yana tsoran kar Allah ya kamashi da hakkin ta, itama kanta tasan ba sonta yake ba, tasan Zeena yake so, sai yasa har gobe take jin haushin Zeena, kuma take kishi da ita.+
Afraz tunda Zeena ta sami ciki kullum Ana gida Ana kula da ita, baya zuwa ko ina, daka tayi motsi kadan yace miye, ganin haka yasa da gangan ma sai tayi abu, shi kuma sai ya rude yaita tambayanta mai nene, mai kike so, tace wannan tace wancan sai ya Kawo tace bashi ba, ga abunda take so, haka zai koma ya nemo mata, inya Kawo kuma tace ta koshi, haka kullum suke,
Zeena tana kwance a d’aki, tana tunanin yanda zata Japan, tana tunanin dakyar afraz ya barta, jin karan bude kofan da yayi ne yasa ta rufe ido kaman mai bacci, ya zauna akan gadon kusa da ita, yasa hannunshi a bakinta yana wasa dashi, ta dan bude ido daya, suka had’a ido yayi dariya tare da fadin har kin tashi, ta dan turo baki tare da fadin mutum yana baccin shi, Kazo kana damu na, yayi dariya tare da fadin ai ba zaki iya bacci ba in ina kusa, ta daure fuska tare da turo baki, yayi dariya yace idan kina fushi kinfi kyau, ya Mike bari inje in dawo, tace afraz ya amsa da na’am tace exam din mu a Japan kasan dole inje, yayi shuru can yace bari in dawo sai muyi maganan, tace toh har ya kusa fita tace ina zaka, da mamaki yake kallonta wannan ne karo na farko data taba tambayan shi ina zashi, hakan ya mishi dadi yace zani wajan budurwana ne, abun ya bata mata rai amma sai ta dan dake, duk yanda ta dake saida fushin ya fito, yayi dariya yace ashe Ana sona, ta sakar mishi Harara, ya fita yana dariya,
Tunda afraz ya fita ta kasa zaune ta kasa tsaye yanzu afraz dagaske tad’i zaije, wani bakin ciki taji ya taso mata, tayi tsaki inma yaje tadin ni ina ruwana, wata zuciyar tace da ruwanki mana mijinki nefa, ta dauki wayanta ta kira shi, bai dauka ba, ranta ya baci ta kuma kira bai dauka ba, ta zauna tana huci, ya bude kofan d’akin ya shigo ta sakar mai harara, yace bakiyi bacci ba, wani haushi ya kamata ya zauna a kusa da ita tare da fadin ance in gaidaki, ta daure fuska tace ka fitar min a d’aki, yace haba Zeena daka fadan sako ki bari in baki labarin abunda ya faru jin haka yasa ta fara mishi kuka, yace Zeena kin San ban San wannan kukan naki plz kiyi shuru, ya janyo ta ya kwantar da ita kan kirjinshi, yace Zeena ke bakya sona dan nace naje tadi shine kike kuka, ta kuma sakin kukan ai dole kaje tadi tunda ni ka cuceni kamin ciki shi yasa kake min haka, yaso yayi dariya amma saiya dake, yace haba Zeena ba haka bane so nake in Kawo miki wacce zata dinga taya ki aiki, tace bana so ai inada jamila, inma mutum daya yayi kadan ko masu aiki nawa ne ummi zata iya Kawo min, yayi dan murmushi najin dadi ya tabbata yanzu Zeena ta fara sonshi tunda har ta fara kishin shi, yace ni ban cika son masu aiki ba kinga idan ko matata ce zata fi kula dake, a matsayinki na yayarta, tace Allah ya kiyaye in zama yayarta taje ta nemi yayarta bani ba, ta tashi daka kan kirjin nashi cikin fushi, yace come on Zeena ina zaki kin San ban San fushin ki, tayi banza dashi, ganin haka yace kin San banso inga kina damuwa kar kisa babyna shima cikin damuwa, tace wato wannan bata ni yake ba, ta baby dinshi yake ba, ta kwanta ta baya tare da juya mishi baya, abun ya bashi dariya shima ya kwanta ta gefenta,.
Zeena yanzu indai taga afraz ya fita toh haka zata zauna cikin fushi da kunci, taita tunanin ya fita tad’i ne, shi kuma afraz din yana mata hakan ne don yaga ko tana sonshi, ya fito cikin kananan kaya ya mishi kyau yana ta kamshi, ya kalleta yace Zeena nayi kyau kuwa, ta kauda kai gefe, yayi dariya tare da fadin plz ki fad’amin in banyi kyau ba, in canza kaya kar inje tad’i taki fitowa, tayi tsaki tare da tashi ta haura sama ya bita da kallo yana dariya, Jim kadan sai gata ta fito dauke da key din mota a hannunta, yace ina zaki tayi banza dashi, ya tare ta, ta saki kuka tace ni ka matsa min in wuce gidan mu, yace haba Zeena akan wani dalili zaki gida, jin haka tayi shuru ya kuma tambayanta tayi shuru, ya kamo mata hannu yace zo muje na fasa fitan, jin haka yasa taji dadi harta yarda suka koma ciki.
Adeel yana office amma duk ya kasa komai, yana tunanin Zeena wanda ya zaman mishi aiki kullum, ya lumshe ido tare da fadin Zeena Allah ya jarabce ni da sonki, na rasa yanda zanyi in cireki a raina, na kasa yarda da na rasa ki, kullum zuciya na tana yaudara na, akan ban rasa ki ba, karan wayanshi ne ya katse shi, ya dauka yaga Mysha ce, yayi dan tsaki sannan ya dauka, tace adeel yaushe zaka dawo ina so muje hospital inga Dr, yace anjima tace toh sai Kazo bai bata amsa ba ya kashe Wayan,.
Afraz yace ma Zeena ta shirya suje Japan din,ta hada kayanta sukaje suka ma kowa sallama, washe gari suka cala harda jameela, wani gida suka sauka, gidan duk da bashi da girma sosai amma ya hadu, afraz yana ba Zeena kulawa sosai, ita da kanta yanzu ta yarda tana son afraz, amma ta kasa nuna mishi, bata san ya Riga ya ganota ba, satinsu biyu suka dawo Nigeria, afraz yayi siyayyan kayan yara sosai na mata da maza, d’aki daya aka ware aka shirya komai yasa ansa na mace dana miji, yace duk wanda aka haifa ga kayanshi nan.
Cikin Zeena yakai wata takwas, amma inka ganta zaka ce haiyuwa yau ko gobe ne, don cikin yayi girma sosai, afraz yace in kika haifi mace sunanki zan sa Zeena, tayi dariya tace saboda me, yace Zeena saboda ina sonki, kullum sonki kara karuwa yake a raina, tayi dan murmushin jin dadi, yace amma ni har yanzu ba’a sona, ta dan turo baki suka hada ido tayi sauri ta kawar da kanta gefe, yayi dariya yace idan namiji kika haifa sunan wa zaki sa, tace ka bari saina haiyu sai in fad’ama, yace shikenan Allah ya kaimu wannan ranan Zeena, ji nake kaman yanzu inga kin haiyu, ki haifar min mace mai kama dake, tayi dariya tace in namiji ne kuma yayi kama dakai, ya kalleta yace Zeena kina son ki haifa mai kama dani tace eh, a ranta tace afraz kana da kyau, inna haifa mai kama dakai ba karamin kyau zaiyi ba, nan suka zauna suna ta fira cikin so da kauna, aka kira afraz a waya ya dauka tare da fadin gani nan zuwa, bayan ya kashe yace Zeena bari inje in dawo, tace ina zaka yace wasu kaya dana bada oder dinsu aka Kawo, tace daka bari gobe mana afraz yace bazan dade ba ta dan turo baki, yayi dariya tare da fadin Zeena say you love me, ta turo baki yayi dariya sannan ya fita, ita dai bata so wannan fitar ba, dan yanzu bata son afraz yana nisa da ita.
Tunda afraz ya fita har wajan karfe goma bai dawo ba, duk ta rud’e, ta kirashi baya shiga, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ta fito falo ta zauna, taji ana buga kofan falo din da sauri ta nufi falo din tare da fadin sai yanzu ka dawo koh, amma abunda ta gani yasa ta tsorata police ta gani guda biyu, suka ce kece matar afraz koh, ta amsa da eh, sukace yayi accident a halin yanzu yana asibiti, tace innalillahi wa inna’ilaihira jiun, da sauri ta koma ta dauko hijab tabi su, kai tsaye asibitin suka nufa, a lokacin suma su mum din afraz din suka zo da daddy dinshi, Zeena ganin yana yin afraz yayi mugun bata tsoro, duk jikinshi ansa flasta kuka take kaman ranta zai fita, tana fadin afraz saida nace karka fita amma kaki, mai yasa ka fita afraz, yayi mata dan murmushi yana son yin magana amma ya kasa, tace afraz ina sonka, yayi murmushi a dai2 lokacin oxygen din da aka samai ya tsaya.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
8⃣5⃣to9⃣0⃣
Shima komai nashi ya tsaya, ganin haka ta fara girgiza shi, tana fadin afraz, dr ya shigo da sauri yace Su bashi waje, nan ya fara yan dube2 amma ina rai yayi halinshi, Zeena ta bude kofan ta shigo da sauri itama mum ta biyo ta, tace Dr ya tashi, dr yace sai dai kuyi hakuri Allah ya mishi rasuwa, Zeena ta saki dariya tare da fadin no afraz bazai mutu ba, ta matsa kusa dashi tana fadin afraz ka tashi ka karyata wannan Dr din, nasan ba zaka mutu ka barni ba, get up afraz, taja hannunshi taga yayi nauyi, ta saki ya fadi sharaf, ta saki kuka afraz why mai yasa ka tafi a lokacin da nake bukatan ka, afraz saida sonka yamin yawa sannan zaka tafi ka barni, ka tashi your unborn child is waiting for you, ba haka mukai dakai ba afraz ka tashi ta fara girgiza shi, mum dinshi ita Suman tsaye tayi ta kasa ko motsi, a dai2 lokacin dad dinshi shima ya shigo cikin rudewa ganin afraz din yasa ya tabbatar ya rasu, hawaye ke zuba a idonshi, ya matsa kusa da matarshi wanda ko digon hawaye yaki ya zubo mata a ido, gaba daya ta shiga cikin d’imuwa, Zeena ta taso da sauri tace dad kace ya tashi, yace Zeena kiyi hakuri afraz bazai tashi ba, addu’a kawai zamu mai, tace dad afraz ya mutu dagaske, yace eh Zeena ta fara baya2 tana fadin no no he will not die and leave me lokaci daya jiri ya dauketa ta fadi kasa, da sauri dad din afraz ya fita ya kira Dr, nan da nan aka fara dubata, shi kuma afraz aka daukeshi akai gida dashi da safe za’a kaishi gidanshi na gaskiya, labarin mutuwan ya baza ko ina, su abda suma sun zo asibitin, ita zauna da Zeena ummi kuma tana gidansu afraz din, kwata2 hawaye yaki zuba a idon mum sai zuciyanta dake faman buga mata, ummi tana ta mata maganan da zata danji sanyi, kiyi hakuri duk mai rai mamaci ne, kar ki zama mai butulci a lokacin da Allah zai baki shi bai fad’a miki ba, har kika sameshi kika nuna farin cikin ki, yanzu Allah ya dauki kayanshi sai ki zama mai hakuri duk son da kike mai Allah yafi sonshi, sai a sannan kukan yazo mata tace shine daya dan dana haifa yau na rasa shi, don me bazan damu ba, afraz shine komai nawa shine kwai na dana mallaka yau na rasa shi, mutuwa mai yasa baki daukeni ba, ummi ta to she mata baki, tare da fadin kar kima Allah butulci karki manta rayuwa akwai mutuwa kuma koda afraz bai mutu yanzu ba zai mutu wata rana, ki zama mai hakuri da dan gana, a yanzu babu abun da afraz yake so sai addu’a wannan kukan bashi da amfani, tayi shuru tare da fadin haka ne, ta tashi da sauri ta nufi dakinta sai gata da alkur’ani ta matsa kusa da inda aka ajiye afraz din ta fara karatu tana kuka,+
Zeena wajan karfe hudu ta farka, ta bude idonta tare da fadin afraz ta tashi zaune, taga ansa mata drive, ta tsige abun ta tashi da sauri, jin kaman motsi yasa abda ta farka taga Zeena na kokarin bud’e kofa da sauri ta tashi tace Zeena ina zaki, tace abda ina afraz, tayi shuru, tace abda dagaske afraz ya rasu, abda tace Zeena kizo ki zauna, tace no ta bude kofa ta fita abda ta rufa mata baya tana kiranta ganin bata da niyan tsayawa yasa ta koma da sauri ta dauki jakanta ta fito bata ga Zeena din ba, da sauri ta shiga motarta, tayi waje ta hangota tace ta shigo suje, babu musu ta shiga, gidan su afraz din suma suka nufa, sun shiga falon gidan sunga ummi da mum suna ta karatu gefe kuma afraz ne kwance an rufe shi, da sauri ta karasa wajanshi ta bude shi, taga fuskanshi kaman mai yin bacci, tace afraz mai yasa kamin haka ka tashi in fad’ama abun da kake so kaji, afraz ina sonka ina sonka afraz, baby dinka yana son ya rayu dakai plz ka tashi kar ka maida baby dinka maraya, ummi ta matso kusa da ita, tace Zeena ta rungume ta, tana kuka ummi afraz ya tafi ya barni, saida nace karya fita ummi amma yaki, inda bai fita ba da hakan bai faruba, ummi tace Zeena kiyi shuru ki daina fadin haka koda bai fita ba indai kwananshi ya kare bazai kara koda kwana daya ba, tace ummi bazan iya rayuwa ba tare da afraz ba ummi ina sonshi ummi mai yasa haka yake faruwa a kaina, ta kuma sakin kuka, ummi tace ta daina kuka tamai addu’a ne, ta matsa kusa dashi tana tamai addu’a tana kuka, duk wanda yake wajan saida ya tausaya mata.
Mutane sun taru a kofar gidansu afraz din sosai daka gari2 mutane keta zuwa, anyi mishi wanka an mai sutura dama an barshi sai wajan 8:30 za’a kaishi gidanshi na gaskiya hakan ko akayi, a lokacin da aka dauko shi Zeena kuka take kaman ranta zai fita, ta kankame gawan, dakyar aka banbare ta, aka wuce dashi, rayuwa kenan, afraz yayi mutane sosai, Allah yasa mu cika da imani,
Ana ta zuwa musu gaisuwa kota ina, Zeena kwata2 taki cin komai, anyi2 taki ci, saida mum din afraz tazo da kanta sannan ta yarda taci, shima ita take bata a baki, ci kawai take amma bata jin dadin komai, inta kalla cikin ta saita fashe da kuka, tana fadin afraz ka tafi baka ga baby dinmu ba.
A yau akayi addu’an uku, mutane kowa ya watse, an barsu su kadai, ciki harda ummi wanda tun da akayi rasuwan itama tana gidan ita da abda, yanzu daka Zeena sai mum din marigayi afraz da dad dinshi, suka rage a gidan sai masu yi musu hidima, Zeena duk ta rame tayi baki kullum tana cikin hawaye, mum taita bata baki akan tayi hakuri ta rage damuwa ba ita daya bace, inta kiyin shuru saita ce mata da afraz yana nan ba zaiji dadin wannan kukan ba, inta ji hakan sai tayi shuru.
Wata ranan juma’a da yamma Zeena tana zaune tana karatun alkur’ani mum ta shigo d’akin ta zauna a gefe, Zeena ta saki kara tare da fadin ciki na, mum tace Zeena sannu tashi muje asibiti, ta kira daya daka cikin masu aikin gidan suka kama Zeena din aka sata a mota sukai asibiti da ita, tana ta faman fadin ciki na, nan da nan akai labour room da ita, mum ta kira ummi ta fada mata bata dade ba tazo, tare da abda, sun dauki wajan awa uku amma shiru babu labari sai azaba da Zeena din kesha, akace dole sai an mata operation domin ba zata iya haiyuwa da kanta ba, suka ce sun yarda ayi, nan da nan likitoci sukayi kanta aka fara aiki, su ummi babu abun da ake sai addu’a, wajan karfe goma da wani abu Dr ya fito yana murmushi tare da fadin congratulations an sami twins, baby girl nd baby boy, mum ta d’aga hannu tana ma Allah godiya, suka cewa Dr din zasu iya shiga yace eh, da sauri suka nufi dakin, Zeena tana kwance yaran na gefe, babu abun da take sai hawaye, mum ta dauki yaran duka yaran kaman afraz kaman an tsaga kara, kaman yayi yawa sosai, mum itama ta fara hawayen tace Allah sarki afraz, Allah yaji qanka, ummi tace Zeena ki daina wannan kukan, tace ummi naso afraz yaga wannan ranan inga wani irin murna zaiyi, ya dade yana burin zuwan wannan ranan, ta kuma zubo da wani hawayen wani son yaran taji yana shiganta tare da tausaya musu.
NOTE: masu cewa afraz bai kamata ya mutu ba, inya mutu novel din ya baci, kufa tuna Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, kuma karku manta duk mai rai mamaci ne. Rayuwa akwai mutuwa akwai tsufa kar ko da yaushe mu dinga mantawa da mutuwa, duk da novel ne wannan ya kamata mu dinga sawa akwai mutuwa a ciki ba kullum ace sun kasance tare cikin jin dadi da kwanciyan hankali ba, indai akace kullum haka ne Ya zama babu amfani rubuta littafi tunda ana mantawa da mutuwa ya zama shirme, sau da yawa ina rubuta akan abun da yake faruwa ne, Allah yasa mu dace
Maryam obam✍✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fancy habiba 😘💃🏻
9⃣0⃣to9⃣5⃣
A lokacin da dady din afraz yazo asibitin yaga yaran, yace namijin Sak afraz a lokacin yana yaro, ya tambayi Zeena akan wani suna take so a musu huduba dashi tace asa ma namijin afraz, mumy sai da tayi hawaye don jin dadin sunan, macen kuma tace asa sunan mumy din afraz, jin haka mum din tace a’a marigayi ya taba fad’a mata indai ya haifi mace sunan matarshi zai sa, jin haka yasa Zeena ta saki kuka mum ta rarrashe ta tayi shuru, anyi ma macen huduba da Zeena, tana ta samin sauki kwananta biyar aka sallameta daka asibitin suka koma gida, tana ta samun kulawa wajan mumy din afraz, idan ta zauna taita kallon yaran tana jin sonsu na shiganta, tana fadin ina ma afraz yana nan yaga yaranshi, wani hawaye mai zafi yake fita daka idonta, idan mumy ta sameta cikin wannan halin taita mata nasiha akan ta daina sa damuwa karta jama kanta matsala.+
Yau juma’a kuma ranan sunan Zeena da afraz, mutane sun taru sosai an hada gagarimin biki, mum ba karamin kudi ta kashe ba wajan siyayyan kayan yara, itama ummi din Zeena tayi siyayya sosai, Zeena babu abun da take sai kuka, har ummi tayi fushi da ita, tana ta fad’a yau ranan suna amma kin zauna kina ta kuka, sai kiyi tayi, mum tace haba ummi aiba fad’a zakiyi mata ba, ai ba’ama yaro haka, tace yi shuru Zeena kinji ki daina wannan kukan, ganin yanda mum take rarrashin Zeena yasa abun ya bata haushi tace aiki ya ganku, ita kuma Zeena tana kuka ne tare da aiyana wa dama mijinta yau yana raye yaga wannan ranan, da wani irin taro zai had’a inta tuna hakan sai taita kuka, anyi suna kowa ya watse duk wanda yazo sunan yaga yaran sai yaji kaman ya wuce dasu dan kyau.
Mysha tana zaune da dan cikinta na wata Bakwai, adeel yana ta mata hidima, duk abunda tace shi yake mata, don adeel Allah ya yishi da son yara, duk ya tare gida wajan kula da Mysha don yana burin shima yaga danshi na cikin shi, itama ganin yana son cikin yasa take amfani da daman take kara tusa mishi kanta, kuma babu laifi yana biye mata, ba kaman daba,
Zeena tana zaune tana karatu ta cikin system dinta afraz da small Zeena suna ta wasa, yaran yanzu watan su goma sai wayau, gashi basu da kiriniya, harta nono bai dame suba, ganin haka yasa aka fara basu abinci, a lokacin da suka cika shekara daya da wata biyu ta yaye su, a lokacin suka shirya tafiya umra ita da yaranta da abda, sunje umra sun gama aikin su, suna ta yawo suna siyayya yawanci siyayyan duk kayan yaran ne, sun fito daka wani shagon kayan yara a lokacin Mysha da adeel suka zo shiga shagon suma, tare da yaransu wanda adeel ya rike a hannunshi, ganin Zeena yasa ya tsaya ita kuma Mysha ta daure fuska ta shiga cikin wajan tare da fadin sai dai ka kalleta amma tama nisa tunda tayi aure, Zeena ta bita da ido da mamaki, ya matsa da murmushi yace Zeena kece a nan tace eh, abda ta gaida shi, ya amsa da fara’a, yace yaranki ne wa innan abda ce ta bashi amsa da eh, ya kamo hannun small Zeena yace wow so cute, ganin haka shima afraz ya matsa kusa dashi yana dariya, yaji yaran sun birgeshi, ya aiyana dama ace yaran shine, yace ina dad dinsu fa, dukansu sukai shuru Zeena tayi gaba, yace ma abda ya naga kinyi shuru tace dad dinsu ya rasu, yace INNALILLAHI’WA INNA’ILAIHIRA JIUN, nan yama abda gaisuwa sannan yace ta bashi number dinta zai kirata yama Zeena gaisuwa ta amsa da to ta bashi number dinta na nigeria don gobe zasu wuce,ta kama hannun yaran suka wuce suna ta mishi bye2 shima yana musu, harga Allah yaji mutuwan mijin Zeena ya kuma tausaya mata tare da yaranta,
A lokacin daya shiga cikin shop din yaga Mysha tana cika tana batsewa, tace kai abun da kayi kana ganin ka kyauta kenan, dan wulakanci kaje ka tsaya kana musu magana, ni ka shareni ina jiranka a nan, ya daure fuska tare da fadin na tsaya kiyi abun da zakiyi, ya juya tare da fadin in kin gama abun da kikeyi ki sameni waje, wani bakin ciki ne Ya kamata tare da tsanan Zeena,.
Ranan adeel kasa bacci yayi daka ya rufe ido Zeena yake gani,tare da yaranta wanda yaji yana matukar so, yaran abun burgewa, toh amma mai yasa Zeena ta kasa tsayawa su gaisa ma dakyau, take ta daure fuska, Mysha tace inafa ta magana kayi banza dani, ya d’aga kai yace inaji, tace daka nan zamu dubai dinko, yace no Nigeria zamu wuce, tace Nigeria, da mamaki take mai tambayan, yace eh, jin haka yasa ta zauna tare da tunanin mai zai kai adeel Nigeria, bayan babu zuwa nja a tsarinshi yanzu, kai akwai wani abu, haka ranan dukansu suka kwana tare da tunani ita da adeel din,.
Su Zeena sun koma gida, ita Zeena tunda mijinta ya rasu take zaune wajan mum din afraz din, yanzu haka ma gidansu afraz din suka sauka, abda ita ta wuce gida, kwanansu biyar da dawowa adeel suma suka dira a Nigeria, an gyara musu gidansu, a nan suka sauka, a ranan ya kira abda ta dauka bayan sun gaisa yace ina Zeena, tace tana gidan iyayen mijinta, anan take yanzu, yace a ina kenan, ba tare da wani abuba abda ta fada mai gidan yayi godiya tare dayi mata sallama,
Washe gari adeel ya nufi gidan, ya samu masu gadin gidan yace yazo wajan Zeena, suka cemai injiwa zamu ce, yace adeel kace mata nazo yi mata gaisuwa, jin haka suka bude mai gate din ya shiga gidan, a lokacin Zeena da mum suna falo suna fira, mai gadin yayi sallama bayan sun amsa yace Ana sallama da Zeena taji gabanta ya fadi tace waye yake nema na, yace wai adeel yazo miki gaisuwa, tace kaje kace bana nan, Jin haka mum tace mai gadin yace tana zuwa ya amsa da toh ya fita, mum tace waye shi, tayi shuru can tace wani friend dina ne, mum tace haba Zeena shine ba zaki fita ba, ai babu kyau wulakanci, maza ki tashi kije, ta amsa da toh badan ranta yaso ba, ta dauki dogon hijab tasa sannan ta fita, ta sameshi cikin mota ta zagaya ta inda yake ta tsaya yayi dan murmushi shima ya fito daka motan, yace Zeena ya gida ta amsa da lafiya, sannan ya mata gaisuwa ta amsa data gode, ta fara tafiya yace haba Zeena ina zaki muna magana, tace gida zan shiga, tunda kamin gaisuwa din, yace Zeena wai mai yasa kike haka ai ya kamata ki Kawo min yaran mu gaisa dasu, ta daure fuska tare da fadin toh, ta shiga cikin gidan ya bita da kallo, Jim kadan sai gata ta fito tare da yaran, ta tsaya ta gefe yana ma yaran wasa suna ta dariya gasu da baki suna ta mai surutu yana dariya ya dauko leda guda biyu ya basu suka amsa suna murna, ya kalli Zeena da tasha mur yace to ni zan wuce sai wani lokacin, ta amsa da toh an gode, ta kama hannun yaran suka fara kuka ganin adeel zai wuce.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to aysher likymo 😘💃🏻
9⃣5⃣to1⃣0⃣0⃣
Ganin haka yasa yace kar suyi kuka zai dawo, yaja motarshi ya fita, ganin ya fita din suka saka kuka, ta fara rarrashin su, har Suka shiga ciki, mum tace mai aka musu, tace kawai daka sunga zai tafi suke wannan kukan, tace aiya yaro kenan ta tashi ta janyo jikokin nata ta fara rarrashinsu, sukayi shuru suka mika mata ledan daya basu, su chocolate ne dasu biscuit, kalan na waje dinnan sune kala2 a ciki, mum tace harda tsaraba dole kuyi kuka dan zai tafi, Zeena ta danyi murmushi,.+
Bayan Zeena ta shiga d’aki ta kwanta yanzu twins wajan kakarsu suke kwana, ita a yanzu adeel baya cikin tsarin rayuwanta tunda ta rasa mijinta ta cire komai a ranta, take ganin ba zata iya kara kallon wani namiji ba da sunan so ko aure ba, yayanta ma sun isheta rayuwa, wannan abun Zeena tasa a ranta.
Adeel tuki yake amma yana ganin Zeena, ya rasa wani irin azababban so yake mata, ga yaranta wanda suka shiga ranshi jinsu yake kaman yaranshi, har yakai gida yana wannan tunanin, a lokacin daya shiga cikin falon gidan yaga Mysha tana cika tana batsewa, yace ina ahmad, tayi banza dashi, ganin haka yace ba dake nake magana ba, tace na kaishi gidan mu, ya daure fuska tare da fadin bana hanaki fita ba, ba tare da izini na ba, ta yamutsa baki tare da fadin duk ka gama abunka fita ne dai sai nayi, dama tunda naji kace mu dawo nja nasan akwai dalili, dama mijin waccen yar iskan ne Ya mutu wato shine ka dawo ka jajubota, toh wlh….. Saukan mari taji, ta rike wajan tana hawaye, yace ki dinga sanin abunda zaki fad’a akan Zeena, domin Zeena ta fiki itace macen da nake so kuma har gobe nake burin aure, darajan Zeena din kikeci shi yasa nake jure duk wani abu naki nake zama dake, inda badan ita ba, dana dade da rabuwa dake, tace adeel akan wata mace kake fadamin haka, ta shige dakinta da gudu tana rusa kuka, yayi tsaki ya kuma barin gidan.
Tunda Mysha tasan Zeena bata da aure, ta shiga cikin damuwa, ta takura ma adeel akan su koma China amma yaki, yace mata ya dawo kenan, haka suke zama kullum ita bata jin dadinshi shima baya jin dadinta, duk abubuwan da takeyi mai da dan yaji dadi duk ta daina, kullum sai mita, inya gaji ya bata waje, shi yanzu babu abunda yake damunshi illa ace yau ya sami Zeena.
Zeena tana falo suna wasa da twins saiga mai gadi nan yayi sallama ta amsa sannan ya shigo, yace gashi wai inji adeel yace abama twins, leda ne manya2 guda uku, ta amsa tare da fadin kace angode, yace aiya wuce, ta amsa da toh, mum ta fito tace a’a wa innan kayan fah, tace adeel ne yace a Kawo masu afraz, mum tayi dariya tare da fadin Allah sarki baya gajiya da hidima, tunda yazo mata gaisuwa bai kara zuwa ba, sai dai yaba mai gadi kaya ya Kawo ma yaran, mum ta bude ledan taga kaya ne masu tsadan gaske ya siyo da takalmi masu kyau, mum ta kalli Zeena tace ya kamata dai nima in mishi godiya, Zeena tayi shuru bata ce komai ba, mum tana son duk wanda yake son jikokinta bata iya boye son su ako ina, ko ‘kuda bata so ya taba mata su, sai yasa bata cika son suna fita sosai ba.
Adeel ya yanke hukuncin turawa wajan iyayen Zeena, don wannan karan dagaske yake, bazai bari ya kuma rasa taba, hakan ko akayi iyayenshi sunje sun sami dadyn Zeena sun mai magana, yace Su bashi dan lokaci kadan zai kirasu sukayi godiya tare da sallama, a lokacin daya je, gida ya sanar da ummi, a lokacin zaheer yana wajan, yace ma dady ai Zeena tana son adeel domin kuwa a ranan da suka dawo da maganan zai turo ta dawo, sai kuma ta tarar da ana bikinta, dady yayi shuru tare da tuna lokacin tabbas Zeena tace tana son fada mai magana, duk sai yaji tausayinta ya kamashi, yace Zeena kin min biyayya kin auri mijin dana baki, ya aiyana a ranshi akan wannan karan zai cika mata burinta ya aura mata adeel.
Dadyn Zeena Yama mahaifin afraz bayani yayi na’am da abun yace dama ya kamata tayi aure, a lokacin da Dady afraz ya fada mum din afraz yanda sukayi da mahaifin Zeena ba karamin dadi taji ba, nan ta fadama dady irin hidiman da adeel yake ma twins, shima yaji dadin hakan, dady yace yasan baban Yaron sosai dan gidan mutunci ne,.
Dadyn Zeena ya kira magabatan adeel ya fad’a musu akan su turo ayi komai, sunyi godiya sosai, cikin kwana uku suka Kawo komai da komai da ake bukata, duk wannan abun da akeyi Zeena bata San wainar da ake toyawa ba,
Adeel yasa anci gaba da gina mai gidanshi, wanda da ya tsaya, ya tafi China, yanzu anci gaba da gina gidan a ciki yake son saka matanshi dan yace wanda suke ciki yayi karami, ummi ta kira mum tace Zeena tasan da batun auren kuwa mum tace a’a bata sani ba, ummi tace mum ta fada mata, tace shikenan, hakan ko akayi Zeena tana zaune a d’aki tana karanta wani littafi mum ta shigo tace Zeena ina son magana dake, tace to mum, tace Zeena ansa bikinki keda adeel nan da wata biyu, tace what mum aure, mum tace eh, tace dan Allah mum kar kumin haka babu aure a tsari na ta saki kuka, mum tana ta rarrashi tace kiyi hakuri Zeena ba zaiyu mu barki haka ba, dole kiyi aure Zeena, tace no mum bazan iya auren kowa ba mum, bana son yin aure mum, jin haka taba mum din tausayi tasan duk macen da mijinta ya rasu yawanci ana samun irin wannan matsalan kafin su sake aure, tace kiyi shuru Zeena in bakya so babu mai miki dole, jin haka yasa tayi shurun,
Mum ta kira ummi washe gari ta fada mata Zeena bata son auren, ummi tace zata zo ta sameta suyi magana, ko awa daya basuyi ba ummi tazo, ta sami Zeena din tace miye dalilin ta nakin auren tace ummi kawai banso inyi aure ne, jin haka ummi tace toh bari kiji ko kina so ko bakya so sai kinyi wannan auren, so kike mu ajiye ki kita zama a gida babu aure to gwara ma ki canza tunani, babu abun da take sai kuka, har ummi ta gama ta fita, mum tana ta bata baki har tayi shuru, ta dai yanke wannan karan ba zata bari a mata dole ba, domin yanzu ta cire shi a tsarinta.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣0⃣0⃣to1⃣0⃣5⃣
A lokacin da ummi ta koma gida tama dady magana akan a daura auren nan da sati biyu, in yaso saita tare daka baya, dady yace akan wani dalili kuma, bayan an tsaida rana kuma yanzu a canza, ummi tayi shuru bata kuma cewa komai ba, jin haka dady yace akwai wani matsala ne, tace a’a babu, naga kaman ansa lokacin ne yayi yawa, dady yayi shuru can yace ai kaman yanzu ne, zaki ga yayi, abda ta shigo falon da fara’a a fuskanta, ummi tace anyi nasara kenan, tayi dariya tare da fadin eh ummi, ta mika ma ummi takardan tace lallai abu yayi kyau, dady tace mai nene, ummi tace waec din tane, yace har ya fito, yanzu sai shirin zuwa high instuition kenan, tace eh dady, tana dariya, nan suka zauna suna ta fira cikin sha’awa,.+
Tunda ummi tazo gidan tama Zeena magana, babu wanda ya kuma mata maganan auren, hakan ya mata dadi dan tana ganin kaman an fasa ne, ita kwata2 yanzu adeel baya cikin tsarinta, domin kuwa ba zata iya kishi da Mysha ba, domin yanda taga Mysha a saudiya ta musu, Ina ga in sun hada miji, wani hawaye ya zubo mata tare da fadin afraz ka tafi ka barni gashi yanzu ina cikin kunci, babu mai rarrashi na, Ina ma kana nan da duk haka bai faru ba, mutuwa ta rabani dakai masoyi na, a lokacin da nake son kasancewa dakai, lokacin da nake bukatanka, ta kuma zubo da wani hawayen afraz ka tafi ka barni da sonka, a raina, naso ace tare muka mutu, duk wannan maganan da takeyi a fili take, mum ta shigo d’akin taji duk abunda take fad’a, taji tausayin Zeena din sosai, ta matsa kusa da ita, tace Zeena ki daina fadin haka, afraz ya tafi yabar miki yaranshi Zeena ki daina sa wannan abun a ranki, afraz addu’a yake bukata, sannan kuma yaranshi duk da basu sanshi ba, ki fad’a musu waye babansu su taso suna mai addu’a indai kikayi haka kin mai babban gata, kuma kin nuna mishi dagaske kina sonshi, ta kuma fashewa da kuka ta rungumi mum din,.
Yau an tashi garin Abuja ana zafi, Zeena tama twins wanka tasa musu kaya mara nauyi, tana zaune taji zafin itama ya isheta duk da a.c a kunne yake, ta tashi ta sami mum tace zata wajan ummi, mum da fara’a tace kai yau wani rana, tunda afraz ya rasu sau biyu taje gidansu, itama tayi murmushi, mum tace ai kin kyauta Zeena amma zama waje daya babu dadi, shi yake sama mutum yaita tunani, tace hakane, tace ma mum ta wuce ganin zata fita twins suka bita da gudu, suka makale ta, abun ya bata dariya tace ku koma ku taya mum fira, suka ki sakinta, mum tace haba ya zaku min haka, dawa zaku barni a gida, kuzo muje muma anjima zamu fita, ganin mum zata zo inda suke suka sa kuka, mum tace kuyi shuru tare zaku, jin haka sukayi shuru suna dariya, suka fita suna ma mum bye2, tace zaku dawo ai ku sameni,
Kai tsaye gidansu Zeena ta nufa, bayan tayi parking ta shiga, taga motar dady a gidan alaman yana gida kenan, sun shiga falon gidan da gudu abda tazo ta kamo hannun twins, tana fadin what a surprise yanzu nake son kiranki ince zanzo sai gaku, Zeena tace kedai abda kin iya tsara zance, tayi dariya tare da fadin ki tambayi dady kiji, a gabanshi na fada, jin haka dady yace to ai tunda tazo shikenan, nan ta gaida dady ya amsa cikin fara’a ya kira jikokin shi, suka zo wajan shi yana musu wasa, ummi tace ma afraz yazo ya noke alaman a’a, tace au niko to yau babu auren na sallameka, dady yayi dariya yace kishin ne ya motsa kinga amarya tazo ko, sukayi dariya, Zeena da abda suka shige ciki,
Bayan sun shiga Zeena take tambayan abda akan maganan bikin da ake shirin yi, yana nan ko an fasa, abda da mamaki tace a fasa kuma, aike zaki fi kowa sani ai, tunda kuna waya da adeel din, ni nasha mako kinzo mu tattauna akan bikin ne, Zeena ta sakar mata harara tare da fadin sai ki tattauna dashi ai, abda tace mai yayi zafi kuma, Zeena tace abda Kin San wani abu, kin dai San yanda abubuwa suka faru a baya toh ina so kiban shawara, ada naso adeel Mysha ta aure shi, daka baya na gano, abunda yasa ya aureta, a lokacin Allah yasa bani zai aura ba, nima na auri afraz bana sonshi amma daka baya Allah ya dauramin sonshi, har ya rasu ya barni da mugun sonshi a raina, wanda a yanzu nake kallon bazan iya kallon wani namiji da sunan so ba, ko aure ba, gashi su ummi sun tsaida ranan aurena da adeel, abda bazan iya kishi da Mysha ba, taya zan rusa wannan auren, abda tace haba Zeena ban taba tunanin haka daka gareki ba, dady yasan ba zaki bashi kunya ba shiyasa ya amsa musu, kuma bros zaheer ya fada mishi kina son adeel, shi yasa ma harya amsa maganan auren kuma dady yayi hakan ne dan ya faranta miki, bama haka ba idan kince baki son auren haka zaki bar yaranki babu uba, ai ya kamata yau ace sun taso da wanda zasu dinga kira da mahaifinsu,kuma na tabbata yanda adeel yake sonki zai rike miki yaranki, tace abda banki taki ba adeel fah mijin Mysha ne AMINIYA TA, abda tace to sai me dan mijin tane, idan ita bata ji kunyan aurenshi ba, taci amana toh kece zaki ji kunyan aurenshi, aiba zamanta zaki yiba, Zeena tayi shuru tabbas maganan abda hakane kuma gaskiya ta fad’a, toh amma yanzu taya zata kalli adeel a matsayin mijinta, harta iya zaman aure dashi, wata zuciyan tace don yaranki zakiyi, sai wajan 5 Zeena suka koma gida, da gudu twins suka shiga suka fad’a kan mum dake zaune a falo tace oyoyo, suka saki dariya da murna na ganin mum, nan suka nuna mata kudin da dady ya basu,tace to su bama mamansu ta ajiye musu, suka nufi Zeena suka bata, nan suka zauna suna ta fira da mum,
Bikin yana ta gabatowa, ita Zeena harga Allah bata murna da auren, dan tana ganin kaman taci amanan afraz idan ta sake wani auren, gashi a yanzu babu daman tace ta fasa domin bikin baifi sati daya ba, ga adeel tunda yazo mata gaisuwa bai kara zuwa wajanta ba, sai dai twins da yake aiko ma da kaya, kala2 hakan yana mata dadi sosai, tana zaune a waje kan kujera ta gaban swimming pool dan zafin yau yayi yawa, aka bude gate din gidan aka shigo, motar tayi packing ta bayanta, ya fito yazo inda take yace barka da hutawa, ta waiga taga adeel, ta amsa babu yabo babu fallasa, ganin hakan yasa ya sami karfin giwa, yace Zeena nazo muyi magana ne, bata amsa Shiba, shima hakan bai dameshi ba, yaci gaba da magana, Ina so inji mai kike bukata, ta dan tabe baki tare da fadin bana bukatar komai, yace ok babu damuwa ya ciro kudi yan dubu daya2 ya bata bandir biyar yace ga wannan ki saima su twins sweet, tace no ka barshi an gode, ya danji wani iri, amma sai yace ai bake naba ba, so baki da right din da zaki ce a barshi, tace amma ai…… Ya katse ta tare da fadin na wuce………
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣0⃣5⃣to1⃣1⃣0⃣
Ganin haka yasa ta diba kudin, ta shiga ciki itama, tare da fadin ni wannan auren ba sonshi nake ba, kawai dai so ake amin dole, tayi tsaki, tare da tausayin kanta,..
Anata hidiman biki, ango shi daya yake hidimar shi, amma Zeena ko a jikinta, itama Mysha bata San da batun ba, yadai ce mata zasu koma sabon gidansu ta shirya kayanta hakan ko akayi, tana ta shiri suka koma, a lokacin da suka koma taga yanda yayi tsarin gidan abun sha’awa, gidan babba ne, falon gidan ya hadu sosai, ya nuna mata wani kofa yace nan ne dakinta, ta bude taga falo sannan taga kofofi guda uku taga bedroom ne ko wanne akwai toiled a ciki, kuma duk dakunan ansa kayan gado a ciki, sannan falon ma data gani shima an hada shi, tace wancan shine babban falo kenan,ta fito ta nufi wata kofar taganta a rufe, ta matsa wanda yake kusa dashi shima a rufe, tayi dan tsaki to miye na rufe kofofin ma toh, ta koma babban falon ta ganshi yana tama ahmad wasa, yana dariya tace sauran kofofin can fa, mai yasa aka rufe, ya tamke fuska tare da fadin ainan ba hurumin ki bane, tace kaman ya, yayi banza da ita, ganin haka ta fara surutu ta inda take fita ba tanan take shiga ba, jin haka ya tashi yabar wajan.+
Yau ranan laraba kuma a ranan aka kai akwatin auren Zeena, gidan su ummi aka kai, mum ta tafi can aka bar Zeena da twins, akwati 24 aka kai mata ko wanne cike da kaya masu tsada, abun dai ba’a magana, sai San barka, a ranan itama yakai ma Mysha nata akwatin, tace adeel wannan akwatinan fah, yace nama nama amarya tane, kema na miki, komai kala daya nasa muku, sai dai colour din na ban banta, tunda ya fara magana tasa mai ido tana kallonshi, wani hawaye yake zuba a fuskanta dama tasan za’ayi haka, tun zuwan su gidan Nan take zargin hakan, tace adeel wa zaka aura ba tare da fargaba ba ko tsoro yace Zeena, tace what Zeena kake nufi zaka auro ka Kawo ta cikin gidan Nan, yace yes, tace wlh baka isaba ba adeel dan rashin adalci ka rasa wacce zaka auro sai Zeena, ta saki kuka, yace Mysha ke har kina tunanin banyi miki adalci ba, ai bai kamata kima cemin hakaba, kanki ya kamata ki kira da hakan, tace adeel ka auro koma wace ce, bazan damu ba, amma dan Allah karka auro Zeena, yace Mysha kiyi hakuri Allah yasamin son Zeena, bazan iya fasa aurenta ba, tace adeel ka tausaya min nima ina sonka adeel, nasan kayi hakan ne dan ka rama abinda nama, duk sai yaji ta bashi tausayi yace Mysha badan in rama abunda kikamin ba yasa zan auri Zeena, keda kanki kin San yanda nake son Zeena, Mysha bazan wulakantaki ba dan na auri Zeena ba, taci gaba da kuka yana ta bata baki ganin bata da niyan yin shuru yasa ya bata waje, ganin ya tashi taci gaba da kukan ta, tasan idan Zeena ta shigo gidan nan zata koma bora, yanzu ma yata kare balle Zeena tana gidan, tace Zeena sai nasa adeel ya tsaneki.
Yau juma’a aka daura auren Zeena da adeel, ranan Zeena kuka take tayi tana fadin ita bata son wannan auren, amma ina babu mai sauraronta, tun Ana saura kwana biyu bikin ta koma gidan ummi, abda cema mai bata baki, ummi ta shigo d’akin taga tana ta kuka, nan ummi ta mata ta tas, tare da fadin in batayi shuru ba saita saba mata, ganin ran ummi din ya baci yasa tayi shuru, mum ta shigo d’akin ta tarar da ummi tana huci tare da fada, nan tace ma ummi ta daina mata fad’a haka ai rarrashinta za’ayi ba fad’a ba, ummi tace wani rarrashi ne ba’a mata ba, amma dan iskanci tazo tana ta kuka da yake ta raina mutane, ki duba ko wanka taki tashi tayi, jin yanda ummi take ta fad’a yasa ta tashi da sauri tayi toilet nan taci gaba da kukan ta, tayi mai isarta sannan tayi wanka ta fito, abda ta mata makeup tare da taya ta sa kaya, tayi kyau sosai, ta fito falo suna ta gaisawa da mutane, ummi ganin haka yasa ta saki ranta,.
Mysha tun safe itama take aikin kuka a d’aki tana fargaban a Kawo mata Zeena gida, amma babu yanda ta iya domin aikin gama ya Riga daya gama, son adeel dinne yasa ta kin barin gidan, dan har mahaifiyarta tace ta dawo gida, amma taki,
Wajan karfe 8 a Kazo daukan Zeena, tana ta rusa kuka, iyayenta sunyi mata nasiha sosai akan ta zauna lafiya ita da mijinta da abokiyar zamanta, aka fito da ita aka kama hanya, har aka karasa gidan tana kuka, abda dake gefe tace Zeena fito kiga gidan da aka Kawo ki, ya hadu sosai, tama abda harara sai kace tana ganinta, a cikin masu Kawo ta harda mum, tace ta fito da bismillah, hakan ko tayi suka shiga ciki, babu kowa da yake sun san dakin Zeena din suka bude suka shiga, tsarin dakinta yayi kyau sosai, itama da falo da 3bedroom ne a ciki, sun dan zauna kadan kafin suka wuce tana ta kuka, bayan sun tafi ta kifa kanta a giwa tana ta kuka,
Adeel wajan karfe goma ya shigo gidan, kai tsaye dakin Mysha ya nufa, yaga tana ta rafsa kuka, duk sai yaji ta bashi tausayi, ya zauna yana ta rarrashinta, yace taci abinci, ta girgiza mai kai alaman a’a, ya dauko daya daka ledan daya shigo dashi ya bude kaza ne a ciki, ya bata yace gashi taci, ta amsa, ya tashi tare da fadin saida safe, nan ta kuma sakin kukan haka ya fita ya barta, cikin kunci da bakin ciki, yanzu adeel zai kwana da Zeena a matsayin matarshi, wani bakin kishi taji yana dibanta,.
A lokacin daya shiga d’akin Zeena da sallama, yaga tana ta kuka, ya zauna kusa da ita, yace haba Zeena wannan kukan fa, na tabbata tun dazu kikeyi, ya kamata kiyi shuru kibar wannan kukan, jin bata kulashi ba, kuma bata daina kukan ba, yasa ya d’aga mata kai tayi sauri ta matsa baya, ganin haka yace ga abinci kici karki zauna da yunwa, ya fara bude mata, kaza ne da yogurt, ya mika mata ta amsa, ya fita daka d’akin ganin haka yasa tayi sauri ta rufe kofan ta da key, shima falo ya nufa ya kwanta kan kujera, ya daura hannunshi akan kanshi, babu abunda yake sai tunani, wai yau shida Zeena suna matsayin mata da miji, ranan da suke ta buri, amma ranan tazo Zeena kwata2 bata murna, yanzu Zeena bata sona kenan mijinta take so, wani irin kishi yaji ya rufe shi.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣1⃣0⃣to1⃣1⃣5⃣
Ga kanshi dake ta sara mishi, a falon ya kwanta har bacci ya dauke shi, ita kuma Zeena bayan fitanshi itama kwanciyan tayi abunta, sai wajan asuba ta farka taje toilet tayi alwala tazo tayi sallah, bayan ta idar taji kaman ana mata nocking, taso ta share komai ta tuna kuma ta tashi ta bude kofan, taga adeel ne Ya shigo tare da fadin kinyi sallah, ta d’aga mai kai alaman eh, ya bude daya daka cikin d’akin ya shiga wanda ya ware nashi, bayan ya shiga tayi dan tsaki ta nufi d’akin ta itama,+
Mysha tun jiya ta kasa bacci sai aikin kuka, babu abunda take gani sai adeel da Zeena, tana ganinsu a tare a matsayin ma’aurata, tace ni nayi sake ya kamata in dau mataki, tayi dariya tare da fadin Zeena nasan ko ke wacece, nasan yanda zan miki keda kanki zaki bar gidan nan, wannan tunanin da tayi shi yasa bacci ya dauketa
Zeena tunda ta koma bacci sai wajan 10 ta farka, ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin wani doguwar rigan material, duk da batayi makeup ba tayi kyau, ta zauna ta zabga tagumi tace koya twins suke yanzu oho, duk kewarsu ya kamata, ta dauki wayanta ta kira mum, bugu daya ta dauka, Zeena ta gaidata mum ta amsa cikin fara’a, bayan sun gama gaisawa tace ina twins mum tace sun fita da dady yanzu, tace to a gaidasu, mum tasan Zeena kewarsu take domin bata taba tafiya koda na wuni daya bane ba tare dasu ba, tace in sun dawo zata kirata, ta amsa da toh sukayi sallama, a dai2 lokacin adeel ya shigo cikin kananan kaya ya mishi kyau sosai sai kamshi yake tashi, ya kalleta yace an tashi lafiya, ta amsa da lafiya, yace muje muyi breakfast, taji gabanta ya fad’i, don bata san wani irin tarba Mysha zata mata ba, yace let go, tace no bana jin yunwa, ya kafeta da ido ganin irin kallon da yake mata yasa ta daure fuska tare da tashi tasa hijab, yayi dan murmushi yace mai kika ci, ki tashi muje ban San musu, ta mike suka fita tare sun sami Mysha a falo tasa wani top mai hannu daya da 3quater jeans, ta daure fuska kaman bata taba dariya ba, adeel yace Mysha ina breakfast ban gani a dining ba, tace breakfast banyi ba, yace saboda me, tace bashi aka Kawo ni in dinga yiba, ita wanda kaje ka kwana a wajanta ta baka mana, ranshi ya baci sosai amma saiya dake, ya kalli Zeena yace bari in Kawo miki abunda zaki ci, tace no kabarshi kawai, yace akan me kinci wani abu ne, Mysha ta kwashe da dariya tare da fadin yau ina ganin ikon Allah, ganin haka yasa Zeena ta juya tayi dakinta, shima ya bita, bayan sun shiga d’akin ya rasa mai zaice mata, can dai yace kiyi hakuri Zeena bari inje in dawo, ta amsa da toh sannan ya fita, Mysha na falon har yanzu tana ganin shi ta fara bala’i tana fadin an dai zama mijin tace, kana wani binta kana kaudi ko kunya baka ji, yayi banza da ita ya fita, har yaje ya dawo ya sameta a zaune a falon tana kad’a kafa tace Malam nima fa yunwa nake ji, ya mika mata leda daya sannan ya wuce ta bishi da harara, a lokacin daya shiga d’akin Zeena ya ganta a kwance amma idonta biyu, yace ki tashi kici abinci, bata amsa ba amma ta tashi, ya mika mata, ta amsa sannan ya fita, dakinshi ya shiga ya kwanta, ranshi ya baci akan abunda Mysha ta mishi, ina kyaleta ne kawai saboda Zeena, amma duk da hakan zanyi maganin ta, yayi dan tsaki wayanshi dake gefe ya fara kara ya dauka yaga Mysha ce, yayi rejecting Kiran, ta kara kira, da yaga hakan saiya kashe Wayan gaba daya,.
Sai wajan karfe biyu ya fito ya shiga d’akin Zeena, ya ganta tana ta aikin kuka, nan ya zauna yana tambayanta akan mai nene, mai aka mata take kuka ko Mysha ce, ta girgiza mai kai alaman a’a, ya matsa kusa da ita tare da janyota kirjinshi, nan gabanta ya hau bugu, yace kiyi shuru Zeena bana son wannan kukan, ta dan tsagaita da kukan da takeyi, yace ta tashi su shirya suje suyi lunch, tace a’a taci sauran abincin safe, yace ok, ya fara wasa da gashin kanta, wani irin sonta yake shiganshi tare da wani sha’awarta, jin bugun kofa sukayi anayi kaman za’a balla, da sauri ya tashi ya bude kofan yaga Mysha ce tana huci, tace toh Malam saika fito ka nemo min abincin da zanci, yace kina da hankali kuwa Mysha, tace ban sani ba, in banda wulakanci Kazo ka ajiye mutum babu abinci, yace wani kalan abinci ne babu miye babu a gidan Nan, tace ni dafaffe nake so, dan bazan iya girki ba, yace ok ya rufe kofan ya barta a nan waje tana ta bala’i, Zeena tana ta kuka dama abunda take tsoro kenan irin wannan abun, gashi kuma an fara, yace dan Allah Zeena kibar wannan kukan, bata kulashi ba taci gaba da kukan, dakyar ya rarrasheta tayi shuru, tace ya tashi yaje ya siyo mata abincin, yace babu inda zashi tunda akwai abinci a gidan, ganin ta bata rai yasa yace bari yaje, bai sami Mysha a falo ba ya fita,
STORY CONTINUES BELOW

Yau Zeena zata bar girki, Mysha zata amsa, ya kirasu dukansu falo akan su tsara yanda zasu dinga kwana, ranan Mysha ta sake kaman ba ita ba, itace ma ta yanke tace kwana biyu2 ya kalli Zeena yace kinji hakan yayi, jin haka yasa tace inma bai mata ba ni haka na tsara, yace Mysha ki dawo cikin hankalinki bake nake tambaya ba, jin haka yasa tayi shuru tana hararan Zeena, Zeena tace duk yanda kuka tsara yayi, Mysha ta tabe baki, sannan yace ya maganan abinci ya zakuyi, Mysha tayi caraf tace duk mai girki zata dinga yi, ita dai Zeena bata ce komai ba, sai bugun da zuciyanta yake mata, ita kwata2 bata son wannan zaman jinta take kaman akan wuta take, domin irin kallon da Mysha take mata abun ya isheta, adeel yace shikenan hakan yayi, jin haka Zeena ta tashi tayi ciki, ya tashi da nufin ya bita, Mysha ta shiga gabanshi tace ka manta yau nice dakai, Ina kake kokarin zuwa, yace kaman ya dan yau girkin kine banda iko inga matata, tace hakane, yace ok hakan ko akayi, ya fasa shiga, Zeena ko tana shiga d’aki ta dau wayanta taga misscall din mum da sauri ta kirata, ta dauka suka gaisa sannan take tambayanta komai lafiya tace eh, ta bata afraz yana ta mata surutu wani ta gane wani kuma tayi dariya, mum taba small Zeena itama suna ta surutu tana dariya, tayi kewan yaran ta sosai, sun dauki lokaci suna ta surutu, sannan sukayi sallama.
Bayan Mysha ta gama dinner, ta jera a dining adeel yace taje ta kira Zeena, tace toh, ta nufi d’akin Zeena din ko nocking batayi ba ta bude kofan ta shiga taga bata falo dinta, taje wata kofa ta buga jin kaman ana buga kofa yasa ta fito, taga Mysha ce,ganin kayan dake jikin Zeena din yasa ta daure fuska tare da wani bakin kishi, wani top ne mai gajeren hannu da skin tie tasa ribbon ta kama kanta, ganin kallon da take mata yasa tace lafiya kuwa, tace ke ko kunya bakya ji, kin auri mijin kawarki, tir da halinki, Zeena tayi dariya tace ni ko ke, jin haka Mysha ta kuma tamkewa tace karki fad’amin magana dai, Zeena tace ni banda ma lokacin ki ta bude kofa ta shige, tabar Mysha da bakin ciki, ta fita ta sami adeel akan dining yace ina Zeena din, tace tana d’akin ta, tace ta koshi, yace kaman ya mai taci, tace oho aiba gadinta nake ba, ya tashi ya nufi d’akin Zeena din ya ganta a kwance yace Zeena ki tashi kizo kici abinci, ta amsa da toh, ganin bata tashi ba yace ina jiranki, ta tashi ta dauki hijab, tasa suka fita tare, Mysha tayi tsaki, ta zuba ma adeel abinci ta zuba nata, Zeena itama tasa kadan, bata wani ci da yawa ba, ta ajiye tare da mikewa, adeel yace ina zaki baki gama cin abinci ba, tace na koshi, tayi gaba abunta, Mysha tace ikon Allah yau ina ganin abunda yafi karfina, yayi banza da ita, dan duk abunda take yana tara tane, yau yake so yayi maganin ta.
Maryam obam✍✍
👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣1⃣5⃣to1⃣2⃣0⃣
Bayan adeel ya kammala ya tashi daka kan dining din, ya nufi gefen Mysha, itama ganin haka yasa ta bishi, don ta zauna ne taga ko zaije d’akin Zeena, bayan ya shiga ya bude dakin shi ya shiga, toiled ya fad’a yayi wanka ya fito yaga Mysha daka ita sai night gown, kallo daya ya mata ya kauda kai gefe, bayan ya gama shiri ya kwanta ta gefen gado, ganin bai kulata ba yasa tayi tsaki tare da fad’in ikon Allah, ya tashi fuska a daure yace ta tashi tabar d’akin, tace kaman ya, wlh babu inda zani in tashi in fita kaje d’akin wancan munafukar koh, ranshi ya kuma baci yace bari kiji Mysha duk abunda kikeyi na gaji dashi bazan dauka ba dan haka kije gidanku na gaji, tace toh, ta juya baya tare da fadin Allah ya kaimu gobe zan wuce,
Ranan Mysha kasa bacci tayi domin ba zata iya komawa gida ba, koda lokacin da adeel yake bata wuya bata koma ba, balle yanzu da take ganin ya kara aure, wato ta basu waje suyi abunda suke so, tace no way, lokaci daya tayi dan murmushin takaici, ta tashi da sauri ta fara hawaye tana rokan adeel akan yayi hakuri bazata kara ba, yayi banza da ita don har ya fara bacci ta tashe shi, ganin bai kulata ba, yasa tace duk abunda take mai zata daina sannan zasu zauna lfya ita da Zeena, jin haka yasa yace shikenan, tace mai ta gode ta koma ta kwanta tana goge hawayen tare da dan murmushi.
STORY CONTINUES BELOW

Washe gari Mysha tun wajan 7 ta shiga kitchen ta had’a breakfast, ta jera akan dining, ta koma d’aki tayi wanka sannan ta tashi adeel, shima ya shirya, bayan sunje kan dining, ta tashi bari inje in kira Zeena hakan yamai dadi, ya amsa da toh, kai tsaye d’akin Zeena din ta nufa ta bude kofan, taje kusa da kofar da taga ta fito jiya tayi nocking Zeena ta bude kofan, Mysha taya mutsa fuska, tare da fadin ki fito muyi breakfast, kina wani kasa2 dakai kaman wata munafuka, Zeena tayi shuru, Mysha tayi tsaki ta fita, Zeena ta koma ta dauki dankwalin atamfan ta, ta daura, sannan ta fito, bayan Zeena ta zauna ta gaida adeel ya amsa tare da fadin kin tashi lfya, ta amsa da eh, Mysha ta zuba ma adeel breakfast sannan tasa ma Zeena tace ga naki in yayi kadan sai in kara miki, Zeena da mamaki take kallon ta,tace yayi haka, suna ci Mysha tana dan Jan Zeena da fira, wani Zeena ta amsa wani kuma tayi murmushi, adeel shiko yau yana cikin nishad’i, bayan sun kammala Zeena tayi d’akin ta, adeel da Mysha suka zauna suna dan taba fira jefi2 yin firan kawai yake amma kwata2 hankalin shi da tunanin shi, yana wajan Zeena yana son zuwa wajanta, ya tashi yace bari inje mu gaisa da Zeena ta amsa da toh, yaji mamaki dan baiyi zaton haka daka gareta ba, amma saita amsa, yace ya kamata ma ki dauko ahmad, tace toh anjima zan dauko shi, ya nufi d’akin Zeena, bayan ya shiga ya ganta tana waya da mum, bayan sun gama ta kalleshi tace nagode mum tace ka kaima su twins kaya, yace dan na kai musu kaya shine kike min godiya dan nama yarana hidima, taji dadin abunda yace, tayi dan murmushi, ya kafeta da ido wani irin shaukin sonta ke shiganshi, ganin yanda yake kallon ta yasa taji wani iri, yayi murmushi yace mai kike bukata, ta amsa da babu komai yace ok, ya fita daka d’akin, har lokacin Mysha tana falo, tana ganin shi tace dama kai nake jira ka fito in wuce, yace ok ki gaida mum nd dad ta amsa da toh sannan ta wuce tare da fadin yace ma Zeena ta fita, d’akin Zeena ya koma a lokacin tana toilet, bai dade da shigaba yaga ta fito da alama wanka ta karayi dan towel ne a daure a jikinta, ya kafeta da ido, ta dauko hijab dinta da nufin tasa, yazo yayi hugging dinta ta baya, tare da amsan hijab din, ya fara wasa da gashin kanta wanda ta jika da ruwa, yayi dan murmushi tare da fadin very soon zaki bani cute baby kaman ki, jin haka yasa ta matsa da sauri tare da daure fuska, ya kuma janyota, ta fad’o jikinshi, ya fara kokarin cire mata towel din jikinta gaba daya ta sandare ta kasa ko motsi haka ya dinga wasa da ita, yasa jikinta yayi sanyi, ta saki kuka, ya fara magana kaman yana rad’a yace Zeena mai nene, tace ka kyakeni bana so, jin haka yasa ya sake ta, tare da barin d’akin, tana ganin ya fita ta tashi dakyar tasa ma d’akin ta, key, ta dawo ta kwanta,
Mysha tunda ta fita ta kasa sakewa dan gani take kaman Zeena da adeel suna tare yanzu tayi dan tsaki, ta dauki ahmad tace ma mamanta zasu wuce, tace tun yanzu tace mum zanyi dinner a gida inna koma, Ina so ki samo min mai aiki wacce ta iya girki nan da kwana2 na gaji da wannan girkin, maman tayi dariya tace toh shikenan zan sa a samo miki, ta amsa da to suka wuce, a lokacin da suka shiga gida taga babu motar adeel, tayi ajiyan zuciya cikin jin dadi, tace yauwa basa tare, lokaci daya kuma ta gimtse kodai tare ma suka fita, da sauri ta dauki ahmad sukai ciki, d’akin Zeena din tayi, tana ta nocking kaman zata balla kofan, Zeena ta fito tace lafiya kuwa, Mysha ta mata kallon sama da kasa, tace lafiyan ya Kawo haka, Zeena tayi dan murmushi tace toh Allah ya karo lafiyan, nan Mysha ta kumbura tare da fadin mai kike nufi kina nufin banda lafiya, ko mai, Zeena tace ni bance haka ba, keda kike da lafiya dan nace Allah ya karo ai ba laifi bane, Mysha ta matso kusa da Zeena kaman zata daketa, nan Zeena tayi sauri tayi baya tace badai fad’a zaki dani ba, rufamin asiri, kiyi hakuri, Mysha tace aikin banza ai wlh idan kika fad’a abun da yafi karfin bakin ki saina zane ki a gidan Nan, suna cikin haka saiga adeel Mysha tana ganinshi tace Zeena muje kitchen ki tayani muyi dinner yau a gajiye nake wlh, Zeena da mamaki take kallon ta, ta kasa furta komai, ganin haka yasa Mysha ta kuma cewa kiyi hakuri inna takura miki ki barshi zanyi, adeel yace zama ta taya ki ko Zeena, sai a sannan tasan adeel yana wajan, tace lallai Mysha makira ce, amma a fili sai tace kanta na ciwo, Mysha tace Allah sarki ban sani ba, Allah ya sawake bari inje inyi in barki ki huta, adeel yanda yaga Zeena tayi mata baiji dadi ba, amma saiya basar ya mata uziri, Zeena ta koma d’aki, shi kuma ya dauki ahmad yana mai wasa, ya shiga d’akin Zeena din yaga tana danna waya, yace kinsha magani ta amsa da eh fuska a daure ganin haka yasa ya fita, ita kuma tayi dan tsaki ta kwanta abunta,
STORY CONTINUES BELOW

Yau Zeena ita zata karbi girki dan haka, tun wajan 4 tayi kitchen taga duk yayi ‘kura ta zauna ta goge ko ina, ta maida komai wajan shi, sannan ta daura girki, tayi tuwo miyan danyan kubewa, da yaji nama da kayan ciki, tayi Mango juice ta jera akan dining sannan ta fad’a toilet tayi wanka tasa wata doguwar riga na yan kanti, ta kama gashinta da ribbon, sannan tasa wani karamin gyale ta daure kanta dashi tayi kyau sosai, ta fito falo din taga Mysha da adeel, Mysha tace yanzu nake kokarin tashi in kiraki, yunwa nake ji, Zeena tace aida kinci basai kin jirani ba, adeel tunda ta fito ya kafeta da ido, ji yake kaman yaje yayi hugging dinta, amma babu dama, tazo ta zuba musu, ita kuma ta koma kan kujera tana kallo, adeel yace kizo kici abinci mana, tace no na koshi, yace mai kikaci tace babu komai, ya tashi tare da plate din abincin yazo inda take, ya zauna ya fara bata tana ci,tana kallon Mysha wanda ta kumbura kaman zata fashe, dama tayi hakan ne dan ta nuna mata itama ta iya makircin,shi kuma adeel din kwata2 ya manta da Mysha tana wajan.
Maryam obam✍✍
👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣2⃣0⃣to1⃣2⃣5⃣
Mysha ta tashi da sauri tabar wajan, ganin haka Zeena yasa itama tace ma adeel ta koshi, yace ki kara ci kad’an, tace no, ka barshi jin ihun Mysha sukayi, da sauri adeel yayi d’akin, yana fadin lafiya Mysha mai nene, tace ciki na, yace mai ya sameki tace murd’a min yake, yace tashi muje asibiti, tace bazan iya ba ka taimaka min, yace ina zuwa yana fita tayi dariya tare da fadin yau kwanan kine Zeena amma ni zan amshe, Jim kadan sai gashi da Zeena din sun shigo, ta kuma langwabe wa, adeel yace Zeena ta dauki ahmad ta kaishi d’akinta ta amsa da toh, ta daukeshi ta kaishi, shi kuma adeel ya dauki Mysha yayi mota da ita, kai tsaye asibiti suka nufa, an duba ta, aka bata magani suka dawo gida wajan karfe goma da wani abu, a lokacin Zeena harta fara bacci, taji kaman ana taba ta, da sauri ta tashi taga adeel tace har kun dawo ya jikin nata, ya amsa da sauki sannan ya dauki ahmad, ya fita, tunda ya fita bai dawo ba, daka yazo zai fita Mysha taita nishi, ganin haka saiya dawo ya zauna da ita, ita kuma Zeena baccin ta tayi abunta, sai wajan asuba tayi bacci sannan ya fita masallaci, yayi sallah, bayan ya dawo ya duba ta yaga tana ta bacci, kai tsaye d’akin Zeena ya nufa, yaga tana sallah,ya zauna akan gado, harta idar bata tashi ba taci gaba da zama akan dadduman, ganin bata da niyan tashi yasa yazo inda take ya zauna a ‘kasa ya kamo hannunta da take wasa dashi, yace Zeena kiyi hakuri kin jini shuru sai yanzu ta samu tayi bacci, tace babu komai ta tashi ta haye gado, ganin haka shima ya haye gadon ya janyota jikin shi,ya manneta kaman zata gudu, da haka bacci ya dauke shi, ganin yayi bacci yasa ta zame jikinta cikin nashi ta nufi kitchen don ta had’a breakfast, ta had’a farfesun fresh fish, tayi sandwich da tea ta jera kan dinning ta koma dakinta taga har yanzu yana bacci, ta fad’a toilet tayi wanka ta shirya cikin wasu kananan kaya Riga da wando tayi kyau sosai duk da batayi makeup ba,ta fashe jikinta da turare sai kamshi ke tashi, ta koma falo dinta ta zauna tana kallo, sai wajan 10 ya farka yaga bata kusa ya shiga toilet shima ya fito ya shirya, ya ganta a falo tana kallo wani sonta yake shigar shi, musamman shigan da tayi wanda ya rud’a shi, tabbas Zeena ta hadu, jin kaman ana kallon ta yasa ta waigo, suka had’a ido ya sakar mata murmushi tayi sauri tayi kasa dakai, ya matso kusa da ita tare da janyota jikin shi, suna shakan numfashin juna, ta kasa ko motsi, yasa hannunshi ya d’ago mata kai, ya kafeta da ido itama ta kasa, ‘kasa da kanta jin bakinshi tayi cikin nata sun dauki lokaci cikin haka kafin ya sake ta, ta fara mayar da numfashi ta kasa ko tashi dan gaba daya ya kashe mata jiki, jin hannunshi tayi cikin kirjinta tare da kara rungumota, ganin dagaske yake yasa tace breakfast is ready, yayi dan murmushi ya matsa kusa da kunne ta, yace kece abinci na, ta dan tureshi ya kuma yin dariya ganin yanda take daure fuska, yace Zeena ina sonki, nan taji gabanta yana bugu da sauri ta tashi tayi bedroom dinta nan ta saki kuka, jin ta dade bata fito ba, yasa ya bita yaga tana kuka yace lafiya kuwa Zeena tayi shiru babu amsa, ya matsa kusa da ita tare da fad’in ban San kukan ki Zeena plz, nan ta kuma jin wani hawayen sau da yawa adeel yana mata abubuwa shigen na afraz, dakyar ya samu tayi shuru, suka fita falo don yin breakfast,baiga Mysha ba yasan tana bacci har yanzu dan haka baiko leka d’akinta ba suka fara yin breakfast.
STORY CONTINUES BELOW

Mysha itama tuntuni ta farka taga adeel baya wajan tayi dan tsaki yanzu saida yaje d’akin waccen mayyar, wani bakin ciki taji yana damun ta, yanzu duk abunda na shirya a banza tayi tsaki ta tashi, ta fito falo taga Zeena da adeel suna cin abinci suna fira cikin Jin dadi, nan ranta ya kuma baci ji take kaman ta shage Zeena dan takaici, adeel yace Mysha har kin tashi ta amsa da eh, nan Zeena tace ya jikin, tace da sauki kiyi hakuri naso in taso in taya ki aiki, bacci yaci karfina, adeel yace keda baki da lafiya Mysha ina ke ina tayata aiki, Zeena tace lallai Mysha ke daban kike, nan Zeena ta dan fahimci wani abu, anya ciwon Mysha ba karya bane kuwa, inma karya tayi tama kanta, amma zan nuna mata tayi kuskure, Mysha ce ta katse ta tare da fad’in ahmad jiya baiyi miki kuka ba, Zeena tace a’a aini yara suna sona, Mysha ta turo baki tare da fadin Allah sarki, Zeena ta kalli adeel wanda bini2 idonshi na kanta, tace ya kamata inje inga su twins, nayi missing dinsu, adeel yaji dadin wannan maganan dan dama yana neman dama ne da zasu fita shida Zeena, yace ok dama zan fita yanzu ki shirya sai in kaiki, jin haka Mysha tayi caraf tace nima bari in shirya muje tare, yace no keda baki da lafiya ina ke ina fita, tace na warke ai, yace kiyi hakuri ki zauna kar kije abun ya kuma tashi, haka ta hakura dan babu yanda ta iya, don idan ta matsa zai gane karya takeyi, Zeena ta tashi taje ta shirya cikin wani atamfa dinkin riga da skirt ya mata kyau sosai, tasa gyale kalan kayan, ta fito falo, adeel ya kalleta yace ta koma tasa hijab indai tana so ta fita, nan taji wani hawaye na shirin zuba daka idonta, da sauri ta koma tasa hijab, suka fita, Mysha kaman zata fashe dan bakin ciki, tace kuje Ku dawo zan nuna miki naki kadan ne Zeena.
Hotel ya nufa da ita, bayan sun shiga yace ta fito su shiga, bata musa ba ta fito, yaje yayi komai da komai ita bata san mai yake yiba, dan tana zaune nesa da inda yake, yazo yace suje ta bishi, wani d’aki suka shiga taga ya zauna akan gadon d’akin sai a sannan tace mishi mai suka zoyi nan, ya tashi yazo kusa da ita ya fara cire mata hijab din jikinta,ganin haka gabanta ya fara fad’i, harya cire hijab din, ya cire mata rigan jikinta, tace adeel M….. Kafin ta karasa abunda take son cewa yasa bakinshi cikin nata, nima ganin haka na fita na basu waje,
Mysha tunda suka fita take ta zarya ta kira adeel bai dauka ba, tayi tsaki yanzu hala suna can tare suna cin Amana na, wani haushin Zeena take ji, gashi plan dina na jiya bai yiba, tunda ya koma d’akinta ya kwanta, tayi dan dariya tare da fadin Zeena sai nasa adeel ya wulakanta ki, da kanshi zai koreki,.
Zeena tana toilet tana wanka tare da hawaye, shi kuma adeel yana kwance kan gado cikin nishad’i, tabbas mata suna suka tara kuma ko wace mace tana da nata baiwar da Allah ya mata, har Zeena ta fito ta ganshi a kan gado suka had’a ido tayi sauri tayi kasa dakai wani irin kun yanshi, take ji, yayi murmushi ya matso kusa da ita, yayi hugging dinta, tare da fad’a mata I luv u Zeena, you are my happiness, jin tayi shuru yace bari insa miki kaya ta saki kuka yace mai nene, tace bana so zansa dakai na, yayi dariya ta diba kayanta tayi toilet, ya bita da kallo yana dariya harta fito fuskanta a daure yace mai nene kuma, tace kayana duk ya yamutse, taya zani gidan mum a haka, yace ai yau babu zuwa gidan mum gida zamu koma, tace plz ka kaini, yace a haka, tayi shuru can tace toh ka kaini gida in canza kaya sai muje, yayi dariya tare da fadin zan dauko miki twins in Kawo miki su, ba karamin dadi taji ba, suka koma gida, sunga Mysha a falo tama Zeena kallon sama da kasa, tare da aiyana wa a ranta, anya ba wani waje sukaje ba, dubi yanda adeel yake ta wani zumudi sannan bada wannan kayan ya fita ba, ita kuma Zeena kayanta ya yamutse ta kasa, nan taji kirjinta yana buga mata, ta daure tace har kun dawo nasha aiko dasu twins din zaku dawo, Zeena ta fahimci tana so tasan daka inda suke ne, tace eyya ai bamu samu munje ba, munje wani waje ne, nan Mysha ta kumbura, adeel yabar wajan yayi gefen Zeena ganin haka Mysha ta taso taje gaban Zeena tace ina kukaje, Zeena ba tare da tsoro ba tace hotel muka je, dan bama son takura, wani kululun abu ne ya tsaya mata a wuya, ta cakumi wuyan Zeena.
Maryam obam✍✍
👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
STORY CONTINUES BELOW

Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣2⃣5⃣to1⃣3⃣0⃣
SALAM MY FANS PLZ KUYI HAKURI NAJIN BAN MUKU POSTING KULLUM KWANA2 BAN ZAMA GA DAD DINA BASHI DA LAFIYA PLZ KUSA SHI A ADDU’A, SANNAN KU KARA HAKURI NA KUSA KAMMALA MUKU NOVEL DIN NGD
Zeena ta fara kokarin cire hannun Mysha daka wuyanta, ta kasa domin ba rukon wasa tayi mata ba, sai da tayi dagaske kafin ta samu ta tureta da kafa tayi ‘kasa, ta tashi ta wanke Mysha da mari a dai2 lokacin adeel ya fito ya tsaya yana kallonta rai a bace, yace miye haka Zeena kina da hankali kuwa, ganin adeel din itama Mysha tasa kuka tana fadin daka tambayan yara sai ki mareni, ran adeel ya kuma baci, yace ma Zeena kin kyauta ki bata hakuri, Zeena tayi shuru taki bata hakurin ganin haka ranshi ya kuma baci ya dinga fad’a ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, ganin haka yasa Zeena tayi d’akinta da gudu tana kuka, ita kuma Mysha sai rusa kuka take, ranshi ya baci sosai ya fita yabar gidan, ganin ya fita Mysha ta tashi tana dariya tare da fad’in yanzu kika fara ganin haka Zeena, tunda kika auran min miji,.1
Zeena tunda ta shiga d’aki bata fito ba, har wajan 7 gashi itace da girki, kanta keta sara mata ga zazzabi daya rufeta lokaci daya, dan taci kuka sosai, tana ganin adeel bai mata adalci ba, ya kamata ya tambaye ta, yaji ta bakinta, amma ya rufeta da fad’a ya daura mata laifi.
Adeel shima sai wajan 9 ya dawo tare dasu twins, yaga Mysha a falo tana ganin shi, ta tashi da sauri tana fad’in yauwa gwara da ka dawo yanzu, yace lafiya, tace ni yunwa nake ji sosai, yace yunwa kaman ya babu abinci ne, tace toh mai girki batayi ba, ga ahmad harya gaji yayi bacci da yunwa, ranshi ya baci yaja hannun su twins yayi d’akin Zeena din yaga tana kwance tana rawan sanyi da sauri ya karasa wajanta tare da taba jikinta yaji zafi, duk yabi ya rude yace Zeena maike damun ki, tayi shuru ba tare data kulashi ba, ganin haka yasa ya d’agata duk sai yaji ta bashi tausayi, yace fever kikeyi, ta d’aga mai kai alaman eh, ya fita falon ta ya shigo dasu twins tana ganinsu ta tashi da sauri tayi hugging dinsu tana hawaye, shi kuma ya fita kitchen ya fita ya had’a mata tea ya Kawo mata tasha sannan tasha magani, ya kuma fita d’akin Mysha yayi wanda take ta murna ta had’a su, yau adeel zaiyi maganin Zeena, tana ganin ya shigo ta zabga tagumi tace adeel wlh yunwa nake ji, yace Mysha Zeena bata jin dadi, ki taimaka ki daura abinci, ranta ya baci tace wlh bazai yiwu ba, akan mai zan daura aiba girki na bane, ya tsaya yana kallonta da mamaki yace idan kin daura kinma kanki, tace bazan daura ba kuma a Kawo min abinci dan yunwa nake ji, in banda ni an raina ni har zaka zo kace in daura abinci tunda gani baiwa ita yar hutu, toh bata isa ba, in makircinta yana aiki a kanka to ni bazai yi a kaina ba, tana ta surfa bala’i ganin haka ya fita ya barta, wajan saida abinci yaje ya siyo musu, yakai ma Zeena nata da yaran ta, sannan yakai ma Mysha itama ta amsa tare da fadin wlh aiki ya ganka, bai kulata ba ya fita.
Ya shiga d’akin shi ya kwanta, can ya dauki waya ya kira Zeena kaman ba zata dauka ba, ta dai daure ta dauka, yace Su twins sunyi bacci ne, ta amsa da eh, yace ok kizo d’aki na, Ina son ganinki yanzu, yana fad’in haka ya kashe Wayan, tayi dan gajeran tsaki sannan ta tashi, tasa hijab ta nufi d’akin ta shiga ta ganshi a zaune yana kallo, ta tsaya a tsaye tana sauraranshi, yace kizo ki zauna, kaman karta zauna ta dai daure ta zauna, yace ya jikin tace da sauki, tana fadin haka ta tashi zata fita ya tashi ya janyota ta baya, ta fado kan jikin shi, ta fara hawaye yasa hannu yana goge mata, yace kiyi hakuri Zeena kibar wannan kukan shima da kanshi yasan bai mata adalci ba, ya kamata ya tanbayeta mai yasa tayi hakan, dan yasan haka kawai ba zata mari Mysha ba, ta katse shi tare da fad’in bacci nake ji, yace a nan zaki kwanta tare dani, jin haka yasa tayi shuru bata kara magana ba, yace kiyi hakuri Zeena, daka yau ko mai ya had’aki da Mysha karki kara cewa zaki taba ta, kinji, ta d’aga kai alaman eh, yaci gaba da cewa idan ta miki wani abu ki fad’a min ni da kaina zan dauki mataki, ta amsa da toh, ta tashi ta kwanta ta gefen gadon, shima ya kwanta tare da daura hannunshi a kanta, da haka bacci ya dauke su, ita kuma Mysha cikin takaici ta kwanta dan taga duk abun data had’a bata samun yanda take so.
Tunda Zeena ta tashi tayi sallah, taje taga su twins suna ta bacci abun su, ta nufi kitchen dan daura breakfast, ta soya doya da kwai sannan ta had’a kunun gyad’a, tayi farfesun kaza, ta jera akan dining, ta gyara ko ina, a dai2 lokacin Mysha ta fito ta sakar ma Zeena harara, Zeena ganin haka yasa ta wuce tabar wajan dan yanzu bata da lokacin ta, d’aki ta shiga tayi wanka ta tashi su twins ta musu wanka suma ta shirya su, afraz yace mum nan ina ne, Zeena tayi dariya tace gidanku ne nan, adeel ya shigo d’akin da gudu suka tashi suna dady yayi dariya tare da d’aga small Zeena sama, shima afraz yace sai an d’aga shi, yayi dariya shima ya d’aga shi, nan suka fita falo yin breakfast, sun tadda Mysha akan dinning din tana cin abinci, ko kallo basu isheta ba, taci gaba dacin abincin ta, adeel yace an tashi lfya, ta amsa a dakile lafiya, ganin haka shima ya shareta, suka fara cin abinci su twins suna ta surutu su Zeena suna ta dariya, Mysha tace dalla ku mana shuru kunzo kun dame mu da surutu, small Zeena ta tashi ta make Zeena, ran adeel ya baci yace miye haka Mysha yara nefa, tace toni ina ruwana, an Kawo mana yara suna mana hayaniya, yace sai yau nasan baki da hankali Zeena ta kama hannun yaran tayi ciki dasu, Mysha tace aiba karya nayi ba, ya tashi ya bata waje ya shiga wajan Zeena yaga tana hada kayan yaran, yace lafiya kike hada musu kaya, tace yau zasu koma, yace akan wani dalili, tace hakanan yace toh babu inda zasu, tace kayi hakuri bazan iya bari su kara kwana a nan ba, yace indai ban isa dake ba toh kiyi abunda kika ga dama, ya fita ya bata waje, tayi shuru tare da bakin cikin abunda akama yaran ta, tabbas zan iya jure komai amma bazan bari a wulakanta yara naba, domin sune rayuwa na, tun daka ranan bata bari suna zuwa babban falo komai sunayi a gefenta, hakan na damun adeel, yanda yaga tana janye yaran bata bari suna fita suna sake wa, satinsu daya mum tace su dawo, Zeena bata soba, amma haka suka koma shima adeel yaso mum tabar musu yaran, taki tace su take gani taji dadi sannan ba zata iya barin jikokinta suyi rayuwan agolanci ba,.
BAYAN SHEKARA DAYA
Zeena tana d’aki ita da adeel suna fira cikin so da kauna, ta tashi da gudu tayi bayi tana ta amai, ya bita da sauri duk ya rude yana mata sannu, bayan ta gama sukayi asibiti, nan aka dubata akace tana da cikin wata daya da sati biyu waiyo zo kuga murna wajan adeel,nan suka dawo lokacin sun tarar da Mysha a falo tana ganinsu, tace an daiji kunya kuma sai Allah ya saka min yau girki na amma ka fita da ita, yace Mysha kiyi hakuri lalura ne yasa hakan, tace babu wani lalura ita bata da mota ne da ba zata ita kadai ba, nan Zeena tayi ciki da gudu tana kokarin amai, shima yabi ta, toh fa nan Mysha kanta ya kulle tare da tambaya kardai ace ciki gareta, kai anya bata da komai taya hakan ma zai faru, tace inko cikin ne dana bani ni tunda na haifi daya har yanzu shuru amma ace ita ta samu aiko dana yarda namiji munafiki ne, nan ta zauna tana ta tunani kala2
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣1⃣5⃣to1⃣2⃣0⃣
Bayan adeel ya kammala ya tashi daka kan dining din, ya nufi gefen Mysha, itama ganin haka yasa ta bishi, don ta zauna ne taga ko zaije d’akin Zeena, bayan ya shiga ya bude dakin shi ya shiga, toiled ya fad’a yayi wanka ya fito yaga Mysha daka ita sai night gown, kallo daya ya mata ya kauda kai gefe, bayan ya gama shiri ya kwanta ta gefen gado, ganin bai kulata ba yasa tayi tsaki tare da fad’in ikon Allah, ya tashi fuska a daure yace ta tashi tabar d’akin, tace kaman ya, wlh babu inda zani in tashi in fita kaje d’akin wancan munafukar koh, ranshi ya kuma baci yace bari kiji Mysha duk abunda kikeyi na gaji dashi bazan dauka ba dan haka kije gidanku na gaji, tace toh, ta juya baya tare da fadin Allah ya kaimu gobe zan wuce,+
Ranan Mysha kasa bacci tayi domin ba zata iya komawa gida ba, koda lokacin da adeel yake bata wuya bata koma ba, balle yanzu da take ganin ya kara aure, wato ta basu waje suyi abunda suke so, tace no way, lokaci daya tayi dan murmushin takaici, ta tashi da sauri ta fara hawaye tana rokan adeel akan yayi hakuri bazata kara ba, yayi banza da ita don har ya fara bacci ta tashe shi, ganin bai kulata ba, yasa tace duk abunda take mai zata daina sannan zasu zauna lfya ita da Zeena, jin haka yasa yace shikenan, tace mai ta gode ta koma ta kwanta tana goge hawayen tare da dan murmushi.
Washe gari Mysha tun wajan 7 ta shiga kitchen ta had’a breakfast, ta jera akan dining, ta koma d’aki tayi wanka sannan ta tashi adeel, shima ya shirya, bayan sunje kan dining, ta tashi bari inje in kira Zeena hakan yamai dadi, ya amsa da toh, kai tsaye d’akin Zeena din ta nufa ta bude kofan, taje kusa da kofar da taga ta fito jiya tayi nocking Zeena ta bude kofan, Mysha taya mutsa fuska, tare da fadin ki fito muyi breakfast, kina wani kasa2 dakai kaman wata munafuka, Zeena tayi shuru, Mysha tayi tsaki ta fita, Zeena ta koma ta dauki dankwalin atamfan ta, ta daura, sannan ta fito, bayan Zeena ta zauna ta gaida adeel ya amsa tare da fadin kin tashi lfya, ta amsa da eh, Mysha ta zuba ma adeel breakfast sannan tasa ma Zeena tace ga naki in yayi kadan sai in kara miki, Zeena da mamaki take kallon ta,tace yayi haka, suna ci Mysha tana dan Jan Zeena da fira, wani Zeena ta amsa wani kuma tayi murmushi, adeel shiko yau yana cikin nishad’i, bayan sun kammala Zeena tayi d’akin ta, adeel da Mysha suka zauna suna dan taba fira jefi2 yin firan kawai yake amma kwata2 hankalin shi da tunanin shi, yana wajan Zeena yana son zuwa wajanta, ya tashi yace bari inje mu gaisa da Zeena ta amsa da toh, yaji mamaki dan baiyi zaton haka daka gareta ba, amma saita amsa, yace ya kamata ma ki dauko ahmad, tace toh anjima zan dauko shi, ya nufi d’akin Zeena, bayan ya shiga ya ganta tana waya da mum, bayan sun gama ta kalleshi tace nagode mum tace ka kaima su twins kaya, yace dan na kai musu kaya shine kike min godiya dan nama yarana hidima, taji dadin abunda yace, tayi dan murmushi, ya kafeta da ido wani irin shaukin sonta ke shiganshi, ganin yanda yake kallon ta yasa taji wani iri, yayi murmushi yace mai kike bukata, ta amsa da babu komai yace ok, ya fita daka d’akin, har lokacin Mysha tana falo, tana ganin shi tace dama kai nake jira ka fito in wuce, yace ok ki gaida mum nd dad ta amsa da toh sannan ta wuce tare da fadin yace ma Zeena ta fita, d’akin Zeena ya koma a lokacin tana toilet, bai dade da shigaba yaga ta fito da alama wanka ta karayi dan towel ne a daure a jikinta, ya kafeta da ido, ta dauko hijab dinta da nufin tasa, yazo yayi hugging dinta ta baya, tare da amsan hijab din, ya fara wasa da gashin kanta wanda ta jika da ruwa, yayi dan murmushi tare da fadin very soon zaki bani cute baby kaman ki, jin haka yasa ta matsa da sauri tare da daure fuska, ya kuma janyota, ta fad’o jikinshi, ya fara kokarin cire mata towel din jikinta gaba daya ta sandare ta kasa ko motsi haka ya dinga wasa da ita, yasa jikinta yayi sanyi, ta saki kuka, ya fara magana kaman yana rad’a yace Zeena mai nene, tace ka kyakeni bana so, jin haka yasa ya sake ta, tare da barin d’akin, tana ganin ya fita ta tashi dakyar tasa ma d’akin ta, key, ta dawo ta kwanta,
Mysha tunda ta fita ta kasa sakewa dan gani take kaman Zeena da adeel suna tare yanzu tayi dan tsaki, ta dauki ahmad tace ma mamanta zasu wuce, tace tun yanzu tace mum zanyi dinner a gida inna koma, Ina so ki samo min mai aiki wacce ta iya girki nan da kwana2 na gaji da wannan girkin, maman tayi dariya tace toh shikenan zan sa a samo miki, ta amsa da to suka wuce, a lokacin da suka shiga gida taga babu motar adeel, tayi ajiyan zuciya cikin jin dadi, tace yauwa basa tare, lokaci daya kuma ta gimtse kodai tare ma suka fita, da sauri ta dauki ahmad sukai ciki, d’akin Zeena din tayi, tana ta nocking kaman zata balla kofan, Zeena ta fito tace lafiya kuwa, Mysha ta mata kallon sama da kasa, tace lafiyan ya Kawo haka, Zeena tayi dan murmushi tace toh Allah ya karo lafiyan, nan Mysha ta kumbura tare da fadin mai kike nufi kina nufin banda lafiya, ko mai, Zeena tace ni bance haka ba, keda kike da lafiya dan nace Allah ya karo ai ba laifi bane, Mysha ta matso kusa da Zeena kaman zata daketa, nan Zeena tayi sauri tayi baya tace badai fad’a zaki dani ba, rufamin asiri, kiyi hakuri, Mysha tace aikin banza ai wlh idan kika fad’a abun da yafi karfin bakin ki saina zane ki a gidan Nan, suna cikin haka saiga adeel Mysha tana ganinshi tace Zeena muje kitchen ki tayani muyi dinner yau a gajiye nake wlh, Zeena da mamaki take kallon ta, ta kasa furta komai, ganin haka yasa Mysha ta kuma cewa kiyi hakuri inna takura miki ki barshi zanyi, adeel yace zama ta taya ki ko Zeena, sai a sannan tasan adeel yana wajan, tace lallai Mysha makira ce, amma a fili sai tace kanta na ciwo, Mysha tace Allah sarki ban sani ba, Allah ya sawake bari inje inyi in barki ki huta, adeel yanda yaga Zeena tayi mata baiji dadi ba, amma saiya basar ya mata uziri, Zeena ta koma d’aki, shi kuma ya dauki ahmad yana mai wasa, ya shiga d’akin Zeena din yaga tana danna waya, yace kinsha magani ta amsa da eh fuska a daure ganin haka yasa ya fita, ita kuma tayi dan tsaki ta kwanta abunta,
Yau Zeena ita zata karbi girki dan haka, tun wajan 4 tayi kitchen taga duk yayi ‘kura ta zauna ta goge ko ina, ta maida komai wajan shi, sannan ta daura girki, tayi tuwo miyan danyan kubewa, da yaji nama da kayan ciki, tayi Mango juice ta jera akan dining sannan ta fad’a toilet tayi wanka tasa wata doguwar riga na yan kanti, ta kama gashinta da ribbon, sannan tasa wani karamin gyale ta daure kanta dashi tayi kyau sosai, ta fito falo din taga Mysha da adeel, Mysha tace yanzu nake kokarin tashi in kiraki, yunwa nake ji, Zeena tace aida kinci basai kin jirani ba, adeel tunda ta fito ya kafeta da ido, ji yake kaman yaje yayi hugging dinta, amma babu dama, tazo ta zuba musu, ita kuma ta koma kan kujera tana kallo, adeel yace kizo kici abinci mana, tace no na koshi, yace mai kikaci tace babu komai, ya tashi tare da plate din abincin yazo inda take, ya zauna ya fara bata tana ci,tana kallon Mysha wanda ta kumbura kaman zata fashe, dama tayi hakan ne dan ta nuna mata itama ta iya makircin,shi kuma adeel din kwata2 ya manta da Mysha tana wajan.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣2⃣0⃣to1⃣2⃣5⃣
Mysha ta tashi da sauri tabar wajan, ganin haka Zeena yasa itama tace ma adeel ta koshi, yace ki kara ci kad’an, tace no, ka barshi jin ihun Mysha sukayi, da sauri adeel yayi d’akin, yana fadin lafiya Mysha mai nene, tace ciki na, yace mai ya sameki tace murd’a min yake, yace tashi muje asibiti, tace bazan iya ba ka taimaka min, yace ina zuwa yana fita tayi dariya tare da fadin yau kwanan kine Zeena amma ni zan amshe, Jim kadan sai gashi da Zeena din sun shigo, ta kuma langwabe wa, adeel yace Zeena ta dauki ahmad ta kaishi d’akinta ta amsa da toh, ta daukeshi ta kaishi, shi kuma adeel ya dauki Mysha yayi mota da ita, kai tsaye asibiti suka nufa, an duba ta, aka bata magani suka dawo gida wajan karfe goma da wani abu, a lokacin Zeena harta fara bacci, taji kaman ana taba ta, da sauri ta tashi taga adeel tace har kun dawo ya jikin nata, ya amsa da sauki sannan ya dauki ahmad, ya fita, tunda ya fita bai dawo ba, daka yazo zai fita Mysha taita nishi, ganin haka saiya dawo ya zauna da ita, ita kuma Zeena baccin ta tayi abunta, sai wajan asuba tayi bacci sannan ya fita masallaci, yayi sallah, bayan ya dawo ya duba ta yaga tana ta bacci, kai tsaye d’akin Zeena ya nufa, yaga tana sallah,ya zauna akan gado, harta idar bata tashi ba taci gaba da zama akan dadduman, ganin bata da niyan tashi yasa yazo inda take ya zauna a ‘kasa ya kamo hannunta da take wasa dashi, yace Zeena kiyi hakuri kin jini shuru sai yanzu ta samu tayi bacci, tace babu komai ta tashi ta haye gado, ganin haka shima ya haye gadon ya janyota jikin shi,ya manneta kaman zata gudu, da haka bacci ya dauke shi, ganin yayi bacci yasa ta zame jikinta cikin nashi ta nufi kitchen don ta had’a breakfast, ta had’a farfesun fresh fish, tayi sandwich da tea ta jera kan dinning ta koma dakinta taga har yanzu yana bacci, ta fad’a toilet tayi wanka ta shirya cikin wasu kananan kaya Riga da wando tayi kyau sosai duk da batayi makeup ba,ta fashe jikinta da turare sai kamshi ke tashi, ta koma falo dinta ta zauna tana kallo, sai wajan 10 ya farka yaga bata kusa ya shiga toilet shima ya fito ya shirya, ya ganta a falo tana kallo wani sonta yake shigar shi, musamman shigan da tayi wanda ya rud’a shi, tabbas Zeena ta hadu, jin kaman ana kallon ta yasa ta waigo, suka had’a ido ya sakar mata murmushi tayi sauri tayi kasa dakai, ya matso kusa da ita tare da janyota jikin shi, suna shakan numfashin juna, ta kasa ko motsi, yasa hannunshi ya d’ago mata kai, ya kafeta da ido itama ta kasa, ‘kasa da kanta jin bakinshi tayi cikin nata sun dauki lokaci cikin haka kafin ya sake ta, ta fara mayar da numfashi ta kasa ko tashi dan gaba daya ya kashe mata jiki, jin hannunshi tayi cikin kirjinta tare da kara rungumota, ganin dagaske yake yasa tace breakfast is ready, yayi dan murmushi ya matsa kusa da kunne ta, yace kece abinci na, ta dan tureshi ya kuma yin dariya ganin yanda take daure fuska, yace Zeena ina sonki, nan taji gabanta yana bugu da sauri ta tashi tayi bedroom dinta nan ta saki kuka, jin ta dade bata fito ba, yasa ya bita yaga tana kuka yace lafiya kuwa Zeena tayi shiru babu amsa, ya matsa kusa da ita tare da fad’in ban San kukan ki Zeena plz, nan ta kuma jin wani hawayen sau da yawa adeel yana mata abubuwa shigen na afraz, dakyar ya samu tayi shuru, suka fita falo don yin breakfast,baiga Mysha ba yasan tana bacci har yanzu dan haka baiko leka d’akinta ba suka fara yin breakfast.+
Mysha itama tuntuni ta farka taga adeel baya wajan tayi dan tsaki yanzu saida yaje d’akin waccen mayyar, wani bakin ciki taji yana damun ta, yanzu duk abunda na shirya a banza tayi tsaki ta tashi, ta fito falo taga Zeena da adeel suna cin abinci suna fira cikin Jin dadi, nan ranta ya kuma baci ji take kaman ta shage Zeena dan takaici, adeel yace Mysha har kin tashi ta amsa da eh, nan Zeena tace ya jikin, tace da sauki kiyi hakuri naso in taso in taya ki aiki, bacci yaci karfina, adeel yace keda baki da lafiya Mysha ina ke ina tayata aiki, Zeena tace lallai Mysha ke daban kike, nan Zeena ta dan fahimci wani abu, anya ciwon Mysha ba karya bane kuwa, inma karya tayi tama kanta, amma zan nuna mata tayi kuskure, Mysha ce ta katse ta tare da fad’in ahmad jiya baiyi miki kuka ba, Zeena tace a’a aini yara suna sona, Mysha ta turo baki tare da fadin Allah sarki, Zeena ta kalli adeel wanda bini2 idonshi na kanta, tace ya kamata inje inga su twins, nayi missing dinsu, adeel yaji dadin wannan maganan dan dama yana neman dama ne da zasu fita shida Zeena, yace ok dama zan fita yanzu ki shirya sai in kaiki, jin haka Mysha tayi caraf tace nima bari in shirya muje tare, yace no keda baki da lafiya ina ke ina fita, tace na warke ai, yace kiyi hakuri ki zauna kar kije abun ya kuma tashi, haka ta hakura dan babu yanda ta iya, don idan ta matsa zai gane karya takeyi, Zeena ta tashi taje ta shirya cikin wani atamfa dinkin riga da skirt ya mata kyau sosai, tasa gyale kalan kayan, ta fito falo, adeel ya kalleta yace ta koma tasa hijab indai tana so ta fita, nan taji wani hawaye na shirin zuba daka idonta, da sauri ta koma tasa hijab, suka fita, Mysha kaman zata fashe dan bakin ciki, tace kuje Ku dawo zan nuna miki naki kadan ne Zeena.
Hotel ya nufa da ita, bayan sun shiga yace ta fito su shiga, bata musa ba ta fito, yaje yayi komai da komai ita bata san mai yake yiba, dan tana zaune nesa da inda yake, yazo yace suje ta bishi, wani d’aki suka shiga taga ya zauna akan gadon d’akin sai a sannan tace mishi mai suka zoyi nan, ya tashi yazo kusa da ita ya fara cire mata hijab din jikinta,ganin haka gabanta ya fara fad’i, harya cire hijab din, ya cire mata rigan jikinta, tace adeel M….. Kafin ta karasa abunda take son cewa yasa bakinshi cikin nata, nima ganin haka na fita na basu waje,
Mysha tunda suka fita take ta zarya ta kira adeel bai dauka ba, tayi tsaki yanzu hala suna can tare suna cin Amana na, wani haushin Zeena take ji, gashi plan dina na jiya bai yiba, tunda ya koma d’akinta ya kwanta, tayi dan dariya tare da fadin Zeena sai nasa adeel ya wulakanta ki, da kanshi zai koreki,.
Zeena tana toilet tana wanka tare da hawaye, shi kuma adeel yana kwance kan gado cikin nishad’i, tabbas mata suna suka tara kuma ko wace mace tana da nata baiwar da Allah ya mata, har Zeena ta fito ta ganshi a kan gado suka had’a ido tayi sauri tayi kasa dakai wani irin kun yanshi, take ji, yayi murmushi ya matso kusa da ita, yayi hugging dinta, tare da fad’a mata I luv u Zeena, you are my happiness, jin tayi shuru yace bari insa miki kaya ta saki kuka yace mai nene, tace bana so zansa dakai na, yayi dariya ta diba kayanta tayi toilet, ya bita da kallo yana dariya harta fito fuskanta a daure yace mai nene kuma, tace kayana duk ya yamutse, taya zani gidan mum a haka, yace ai yau babu zuwa gidan mum gida zamu koma, tace plz ka kaini, yace a haka, tayi shuru can tace toh ka kaini gida in canza kaya sai muje, yayi dariya tare da fadin zan dauko miki twins in Kawo miki su, ba karamin dadi taji ba, suka koma gida, sunga Mysha a falo tama Zeena kallon sama da kasa, tare da aiyana wa a ranta, anya ba wani waje sukaje ba, dubi yanda adeel yake ta wani zumudi sannan bada wannan kayan ya fita ba, ita kuma Zeena kayanta ya yamutse ta kasa, nan taji kirjinta yana buga mata, ta daure tace har kun dawo nasha aiko dasu twins din zaku dawo, Zeena ta fahimci tana so tasan daka inda suke ne, tace eyya ai bamu samu munje ba, munje wani waje ne, nan Mysha ta kumbura, adeel yabar wajan yayi gefen Zeena ganin haka Mysha ta taso taje gaban Zeena tace ina kukaje, Zeena ba tare da tsoro ba tace hotel muka je, dan bama son takura, wani kululun abu ne ya tsaya mata a wuya, ta cakumi wuyan Zeena.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣2⃣5⃣to1⃣3⃣0⃣
SALAM MY FANS PLZ KUYI HAKURI NAJIN BAN MUKU POSTING KULLUM KWANA2 BAN ZAMA GA DAD DINA BASHI DA LAFIYA PLZ KUSA SHI A ADDU’A, SANNAN KU KARA HAKURI NA KUSA KAMMALA MUKU NOVEL DIN NGD
Zeena ta fara kokarin cire hannun Mysha daka wuyanta, ta kasa domin ba rukon wasa tayi mata ba, sai da tayi dagaske kafin ta samu ta tureta da kafa tayi ‘kasa, ta tashi ta wanke Mysha da mari a dai2 lokacin adeel ya fito ya tsaya yana kallonta rai a bace, yace miye haka Zeena kina da hankali kuwa, ganin adeel din itama Mysha tasa kuka tana fadin daka tambayan yara sai ki mareni, ran adeel ya kuma baci, yace ma Zeena kin kyauta ki bata hakuri, Zeena tayi shuru taki bata hakurin ganin haka ranshi ya kuma baci ya dinga fad’a ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, ganin haka yasa Zeena tayi d’akinta da gudu tana kuka, ita kuma Mysha sai rusa kuka take, ranshi ya baci sosai ya fita yabar gidan, ganin ya fita Mysha ta tashi tana dariya tare da fad’in yanzu kika fara ganin haka Zeena, tunda kika auran min miji,.+
Zeena tunda ta shiga d’aki bata fito ba, har wajan 7 gashi itace da girki, kanta keta sara mata ga zazzabi daya rufeta lokaci daya, dan taci kuka sosai, tana ganin adeel bai mata adalci ba, ya kamata ya tambaye ta, yaji ta bakinta, amma ya rufeta da fad’a ya daura mata laifi.
Adeel shima sai wajan 9 ya dawo tare dasu twins, yaga Mysha a falo tana ganin shi, ta tashi da sauri tana fad’in yauwa gwara da ka dawo yanzu, yace lafiya, tace ni yunwa nake ji sosai, yace yunwa kaman ya babu abinci ne, tace toh mai girki batayi ba, ga ahmad harya gaji yayi bacci da yunwa, ranshi ya baci yaja hannun su twins yayi d’akin Zeena din yaga tana kwance tana rawan sanyi da sauri ya karasa wajanta tare da taba jikinta yaji zafi, duk yabi ya rude yace Zeena maike damun ki, tayi shuru ba tare data kulashi ba, ganin haka yasa ya d’agata duk sai yaji ta bashi tausayi, yace fever kikeyi, ta d’aga mai kai alaman eh, ya fita falon ta ya shigo dasu twins tana ganinsu ta tashi da sauri tayi hugging dinsu tana hawaye, shi kuma ya fita kitchen ya fita ya had’a mata tea ya Kawo mata tasha sannan tasha magani, ya kuma fita d’akin Mysha yayi wanda take ta murna ta had’a su, yau adeel zaiyi maganin Zeena, tana ganin ya shigo ta zabga tagumi tace adeel wlh yunwa nake ji, yace Mysha Zeena bata jin dadi, ki taimaka ki daura abinci, ranta ya baci tace wlh bazai yiwu ba, akan mai zan daura aiba girki na bane, ya tsaya yana kallonta da mamaki yace idan kin daura kinma kanki, tace bazan daura ba kuma a Kawo min abinci dan yunwa nake ji, in banda ni an raina ni har zaka zo kace in daura abinci tunda gani baiwa ita yar hutu, toh bata isa ba, in makircinta yana aiki a kanka to ni bazai yi a kaina ba, tana ta surfa bala’i ganin haka ya fita ya barta, wajan saida abinci yaje ya siyo musu, yakai ma Zeena nata da yaran ta, sannan yakai ma Mysha itama ta amsa tare da fadin wlh aiki ya ganka, bai kulata ba ya fita.
Ya shiga d’akin shi ya kwanta, can ya dauki waya ya kira Zeena kaman ba zata dauka ba, ta dai daure ta dauka, yace Su twins sunyi bacci ne, ta amsa da eh, yace ok kizo d’aki na, Ina son ganinki yanzu, yana fad’in haka ya kashe Wayan, tayi dan gajeran tsaki sannan ta tashi, tasa hijab ta nufi d’akin ta shiga ta ganshi a zaune yana kallo, ta tsaya a tsaye tana sauraranshi, yace kizo ki zauna, kaman karta zauna ta dai daure ta zauna, yace ya jikin tace da sauki, tana fadin haka ta tashi zata fita ya tashi ya janyota ta baya, ta fado kan jikin shi, ta fara hawaye yasa hannu yana goge mata, yace kiyi hakuri Zeena kibar wannan kukan shima da kanshi yasan bai mata adalci ba, ya kamata ya tanbayeta mai yasa tayi hakan, dan yasan haka kawai ba zata mari Mysha ba, ta katse shi tare da fad’in bacci nake ji, yace a nan zaki kwanta tare dani, jin haka yasa tayi shuru bata kara magana ba, yace kiyi hakuri Zeena, daka yau ko mai ya had’aki da Mysha karki kara cewa zaki taba ta, kinji, ta d’aga kai alaman eh, yaci gaba da cewa idan ta miki wani abu ki fad’a min ni da kaina zan dauki mataki, ta amsa da toh, ta tashi ta kwanta ta gefen gadon, shima ya kwanta tare da daura hannunshi a kanta, da haka bacci ya dauke su, ita kuma Mysha cikin takaici ta kwanta dan taga duk abun data had’a bata samun yanda take so.
Tunda Zeena ta tashi tayi sallah, taje taga su twins suna ta bacci abun su, ta nufi kitchen dan daura breakfast, ta soya doya da kwai sannan ta had’a kunun gyad’a, tayi farfesun kaza, ta jera akan dining, ta gyara ko ina, a dai2 lokacin Mysha ta fito ta sakar ma Zeena harara, Zeena ganin haka yasa ta wuce tabar wajan dan yanzu bata da lokacin ta, d’aki ta shiga tayi wanka ta tashi su twins ta musu wanka suma ta shirya su, afraz yace mum nan ina ne, Zeena tayi dariya tace gidanku ne nan, adeel ya shigo d’akin da gudu suka tashi suna dady yayi dariya tare da d’aga small Zeena sama, shima afraz yace sai an d’aga shi, yayi dariya shima ya d’aga shi, nan suka fita falo yin breakfast, sun tadda Mysha akan dinning din tana cin abinci, ko kallo basu isheta ba, taci gaba dacin abincin ta, adeel yace an tashi lfya, ta amsa a dakile lafiya, ganin haka shima ya shareta, suka fara cin abinci su twins suna ta surutu su Zeena suna ta dariya, Mysha tace dalla ku mana shuru kunzo kun dame mu da surutu, small Zeena ta tashi ta make Zeena, ran adeel ya baci yace miye haka Mysha yara nefa, tace toni ina ruwana, an Kawo mana yara suna mana hayaniya, yace sai yau nasan baki da hankali Zeena ta kama hannun yaran tayi ciki dasu, Mysha tace aiba karya nayi ba, ya tashi ya bata waje ya shiga wajan Zeena yaga tana hada kayan yaran, yace lafiya kike hada musu kaya, tace yau zasu koma, yace akan wani dalili, tace hakanan yace toh babu inda zasu, tace kayi hakuri bazan iya bari su kara kwana a nan ba, yace indai ban isa dake ba toh kiyi abunda kika ga dama, ya fita ya bata waje, tayi shuru tare da bakin cikin abunda akama yaran ta, tabbas zan iya jure komai amma bazan bari a wulakanta yara naba, domin sune rayuwa na, tun daka ranan bata bari suna zuwa babban falo komai sunayi a gefenta, hakan na damun adeel, yanda yaga tana janye yaran bata bari suna fita suna sake wa, satinsu daya mum tace su dawo, Zeena bata soba, amma haka suka koma shima adeel yaso mum tabar musu yaran, taki tace su take gani taji dadi sannan ba zata iya barin jikokinta suyi rayuwan agolanci ba,.
BAYAN SHEKARA DAYA
Zeena tana d’aki ita da adeel suna fira cikin so da kauna, ta tashi da gudu tayi bayi tana ta amai, ya bita da sauri duk ya rude yana mata sannu, bayan ta gama sukayi asibiti, nan aka dubata akace tana da cikin wata daya da sati biyu waiyo zo kuga murna wajan adeel,nan suka dawo lokacin sun tarar da Mysha a falo tana ganinsu, tace an daiji kunya kuma sai Allah ya saka min yau girki na amma ka fita da ita, yace Mysha kiyi hakuri lalura ne yasa hakan, tace babu wani lalura ita bata da mota ne da ba zata ita kadai ba, nan Zeena tayi ciki da gudu tana kokarin amai, shima yabi ta, toh fa nan Mysha kanta ya kulle tare da tambaya kardai ace ciki gareta, kai anya bata da komai taya hakan ma zai faru, tace inko cikin ne dana bani ni tunda na haifi daya har yanzu shuru amma ace ita ta samu aiko dana yarda namiji munafiki ne, nan ta zauna tana ta tunani kala2
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣3⃣0⃣to1⃣3⃣5⃣
Jin adeel ya dade bai fito ba yasa tabi bayanshi, ta shiga falon taje kofan d’akin Zeena din tana ta nocking, adeel ya fito Zeena na biye dashi, tace toh Malam sai muje haka, cin amanan ya isa, ya kalleta yace haba Mysha wannan wani irin magana ne, tace ai dole kace haka, inka manta yau girki nane dan mai zaisa ka fita da ita, sannan kuma yanzu ka biyota d’aki, yace bata jin dadi ne na kaita asibiti shine laifi, ko kece ran girkinta baki da lafiya bata isa ta hanani kaiki asibiti ba, ai dole kace haka, tunda ka zama mara adalci, ganin tana ta surfo magana ga Zeena a wajan yaja hannunta suka fita, d’akinta yayi da ita sannan ya sake ta, yace kina da hankali kuwa Mysha anya baki fara tabuwa ba kuwa, wlh da hankali na, dan mai zaka cuceni sannan inki magana, dan nayi magana shine kake cemin banda hankali, wlh da hankali na sarai, yace toh wannan bala’in da kikeyi mai zai amfana miki, miye riban shi, tayi tsaki tare da fadin ai wlh bala’i yanzu na fara indai akace cuta na za’a dinga yi, ahmad dake kwance ya tashi yana kuka ganin yanda mamanshi ke ihu, adeel yayi sauri ya dauke shi, yana rarrashin shi, tayi tsaki ta amshi danta tayi falo dashi, adeel yace Allah ya shiryaki yasa ki gane.+
Zeena wannan cikin yana bata wahala, harta dan rame, ga yawan amai da takeyi, adeel yana tausaya mata sosai, yau itace da girki duk ta rasa mai zatayi mai dan sauki dan yanda take jin jikinta kaman ba zata iya komai ba, Jin sallama tayi da sauri ta tashi tare da fadin muryan wa nake ji, abda tazo da sauri tayi hugging din Zeena tare da fadin I miss you, sis,Zeena tayi dariya tace saukan yaushe, abda tace jiya na dawo muna hutu, Zeena tace kaga mutanan dubai yanda aka kara kyau, abda tayi dariya sannan tace naga kin rame kin kara haske kodai an samu abun ne, Zeena ta harare ta da wasa tace sa ido, daka zuwa har kin fara, abda tayi dariya tace aiko makaho ya ganki yasan akwai magana, Zeena tace iye yarinya an iya hausa, abda tace sai kace ba yar hausawa ba, dan nayi wannan karamin hausan, Zeena tayi dariya tace abda nayi kewanki wlh,, amma dai a nan zaki kwana koh, ta zaro ido tare da fadin rufamin asiri in kwana gidan siriki na, Zeena takai mata dukan wasa tace toh anty babba, suna cikin haka saiga Mysha ta kallesu tayi tsaki tare da fadin an dai bani, abda ta kwashe da dariya Mysha tace ke dawa kike wannan dariyan badai dani kike ba, abda tace da wanda ya tsargu dashi nake, nan Mysha ta hasala tace ke bari kiji in kina tashen rashin kunyanki toh wlh kasan da wanda kike don bake bace sa’a ta, abda ta tashi Zeena tace abda kiyi shuru, abda tace wlh Zeena ba zanyi shuru ba, ta kalli Mysha sama da kasa tace ke yanzu ko kunya bakya ji, duk cin amanan da kikayi amma kinzo kina wani kumfan baki, nan Mysha ta d’aga hannu zata mareta abda ta rike hannun tace idan Zeena kina mata ita tana kyaleki toh ni ba ita bace dan bazan dauki raini ba, kinci daraja daya duk da irin mugun halin ki, ke abokiyar zaman yar uwata ce, amma dasai na miki dukan tsiya wlh, Mysha ta tsaya tana kallon ta da mamaki, tace lallai yarinya kinyi baki sai kin San ni kika ma rashin kunya, abda tace ke din banza mai zakiyi, kiyi duk abunda za kiyi ina dai2 dake, ganin abda dagaske take kuma inta biye mata komai zai iya faruwa tayi saurin barin wajan, abda ta kalli Zeena tace dama irin wannan zaman kukeyi, Zeena tace mai yasa zaki mata haka, karki manta AMINIYA TA CE, kuma abokiyar zama na, abda tace wannan ba aminiyar ki bace domin inda aminiyarki ce baza ta miki abunda tayi ba, wlh sis Mysha bata da kunya kuma bata san abunda takeyi ba, in banda raini muna zaman mu tazo ta tsokane mu, Zeena tace aida baki kulata ba dakin barta da halinta, ni yanzu mubar wannan zancen, ummi tace auren bros zaheer nan da wata biyu, kina nan har sai anyi bikin ko zaki koma, abda tace babu inda zani sai an gama bikin, Zeena tace zaki missing abubuwa fah, tace hutun yana da tsawo, tace au yanzu naji magana,nan suka tashi sukayi kitchen suka daura girki, cikin kan kanin lokaci suka gama, abda tayi shirin tafiya gida Zeena tace ta kwana amma taki tace gida zata, adeel yayi sallama ya shigo yace yau wa nake gani, abda tayi dariya tace inlow sai yanzu ka dawo, saida kaga zan tafi, yace amin hakuri ban san kinzo ba da nabar komai na dawo, yace amma laifin Zeena ne da bata kirani ba, abda tace toh ni zan gudu, adeel yace ki mana kwana biyu mana, tace wai ni gidan mu zan wuce ko ku barni in wuce ko in muku kuka, Zeena tace toh bismillah, tayi dariya tare da fadin na tafi, Zeena tace tazo gobe ta taya ta aiki, tace shikenan, ta wuce, adeel ya shiga d’akin Zeena yayi wanka sannan ya shirya ya kalli Zeena yace kullum kina kara kyau ta dan turo mai baki tace a haka din, yayi dariya yace kinfi kyau ai a hakan, tace muje kayi dinner suka fita tare, yace ina Mysha tace tana d’akinta, yace ina zuwa ya nufi gefen Mysha din, ya ganta a kwance yace ta tashi suje suyi dinner, tace toh ta tashi suka fita tare, ganin Zeena a dinning din yasa ta daure fuska, Zeena ta bude abincin nan warin abincin ya hau mata kai tayi d’akinta da gudu, adeel ya bita nan Mysha tace wlh da sake ni za’a mayar yar iska, wato ciki ya mata ni kuma ko oho kenan, toh wlh adeel baka isa ba, itama tabi bayansu taga adeel din yana rike da Zeena yana wani lallaba ta, tace toh munafiki yanzu ciki ka mata toh wlh baka isa ba, yau sai anyi ta, da mamaki yake kallon ta, yace Mysha ki kama bakin ki, tace ai dole kace haka tunda kaci Amana ta, yace amanarki name naci, tace dan mai zaisa ka mata ciki wlh baka isa ba sai anyi ta, ta kare yau din nan, ta dinga magana ta inda take shiga bata nan take fita ba, ranshi yayi mugun baci nan ya matsa kusa da ita ya wanke ta da mari, ta saki ihu ta matsa kusa da Zeena tana kokarin dukanta.
Maryam obam✍✍👩❤💋👩AMINIYA TA CE👩❤💋👩
💅💅 NA✍✍
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA 💁💁
Dedicated this page to my fans 😘💃🏻
1⃣3⃣5⃣to1⃣4⃣0⃣
Adeel yayi sauri ya janyo ta, Zeena wanda tayi Suman tsaye dan tsoro, tace ka sake ni, yau sai anyi ta, ta kare, ta kuma zabura zata nufi Zeena, ganin haka Zeena ta matsa da sauri tayi baya, shi kuma ya kuma janyo ta, tare da marinta har sau biyu yace kije na sakeki saki daya,nan komai nata ya tsaya, da mamaki ta kalle shi, tace adeel saki, nika saka takan wannan banzan, ya kalleta yace wannan ya rage naki ya kama hannun Zeena sukai ciki, suka barta a nan, bayan sun shiga Zeena harda sama d’akin key tayi adeel yayi murmushi, dan tana ganin Mysha Zata iya shigowa ciki, adeel ya zauna akan gadon d’akin ya daura hannu akan kanshi, duk sai yaba Zeena tausayi, ta matsa kusa dashi tace adeel gaskiya banji dadin abun da kayi ba, yasa mata hannu a baki alaman tayi shuru,yace Zeena wani kalan adalci ne banma Mysha amma duk bata gani, ban taba cin amanarta ba ran girkin ta, amma ita bata da wani Abu kullum sai zargi, na rasa wannan irin halin nata, Ina zama da ita ne saboda ke da kuma yarona, amma yanzu na gaji gwara ta wuce, dan wata rana zata iyayi miki komai karta je ta kashe min baby, Zeena tayi shuru bata ce komai ba, ganin haka yasa yace ki daina tunani kar kisa baby dina cikin damuwa shima, tayi dan murmushin yake,ita harga Allah bata ji dadin sakin daya ma Mysha ba.+
Mysha ta nufa d’akin ta, tana ta rusa kuka, tare dajin haushin Zeena, tace Zeena saboda ke adeel ya sake ni, yanda ya sake ni kema haka saiya sake ki, dan bazan barki ba, ta diba wasu daka kayanta tasa a akwati tayi gidansu ita da ahmad, tana shiga taga mamanta da gudu ta fad’a kanta tana kuka, mahaifiyar ta duk ta rude tana tambaya lafiya, mai ya faru, tace mum adeel ya sake ni, maman tace what saki, tace eh mum, tace kiyi shuru ki daina kuka bari in kira dady dinki, maman ta tashi ta nufi d’akin dad din Mysha din, Jim kadan sai gasu tare sun fito, mahaifin ta, yace maiya faru, nan ta fad’a mishi karya da gaskiya ranshi ya baci yace tayi shuru taje d’aki zai nemi adeel din, maman tace neman shi akan me mai za’a mai kawai ka barshi, yace ai ba’a haka dole shima inji ta bakinshi wannan shine adalci, tace wani adalci bayan ya wulakanta mana y’a harda saki kuma, ni na yarda da y’ata ba zata min karya ba, yace hakane amma koma dai miye dole inji ta bakin shi, yana fad’in haka ya koma d’aki, ranan Mysha kasa bacci tayi sai aikin kuka, tabbas tana son adeel irin son da ba zata iya musultawa ba, Zeena kece silan komai saboda ke ya sake ni, tayi murmushi tare da fad’in adeel dole in koma gidanka ko dan darajan dana,.
Zeena tana falo tayi uban tagumi kaman wacce aka ma mutuwa, adeel ya fito daga d’aki yaga yanda ta zabga tagumi, ya karasa gareta tare da cire mata hannun, yace tunanin mai kikeyi haka Zeena, tayi dan nishi sannan tace adeel dan Allah kayi hakuri ka dawo da Mysha, jin haka yasa ya daure fuska tare da fadin indai kika ci gaba da fad’a min wannan maganan zaki ga fushi na, tace adeel nasan bata kyauta ba am…. Ya d’aga mata hannu tare da fadin ni na fita, ta bishi da kallo cikin takaici, ita dai tana so ya dawo da Mysha dan tasan Mysha tana son adeel sosai kuma sonshi yasa take duk abunda take yi, haka ranan Zeena ta zauna cikin tunani.
Mysha duk irin gatan da mum dinta take mata, bata jin dadin zaman gidan, ita burinta yau ace ta koma gidan adeel, domin inta tuna yana tare da Zeena wani bakin ciki take ji, tare da tsananta, Zeena na rasa dame kika fini da yasa komai nake so sai kin raba ni dashi, kowa ke yake so, miye banda shi wanda ke kike dashi, kukan ahmad ne yasa tayi sauri ta dauke shi, tana jijjiga shi,
Mahaifin Mysha ya kira adeel, akan maiya had’a shi da Mysha nan ya fada mishi irin abubuwan da take mai, ran mahaifin nata ya baci sosai, yace ma adeel ya gode saiya neme shi sukayi sallama, yana zuwa gida ya kira Mysha ita ma mamanta ta fito, nan ya zayyane mata abun da Mysha tayi, itama taji mamaki tace Mysha ce take hakan, gaban Mysha sai fad’i yake dan tasan yau ta bani, mahaifin nata yace kin kyauta tunda zaman gida kika zaba saiki zauna, kin samu yaro mai hakuri kinje kina mai abunda kika ga dama, inda wani ne daya dade da koranki ko kuma ya miki dukan tsiya, tunda baki da kirki daka yau zan kafa miki doka bake ba fita, ki zauna a gida tunda shi kike so mutuniyar banza, mamanta tace Mysha ina kika koyo wannan bakin halin wanda ban sanki dashi ba, ke kin taba ganin inama babanki haka, babu abunda Mysha take sai kuka, domin tasan tunda dad dinta yayi fushi da ita, tasan yanzu bata ba wani jin dadi, dad dinta yace ta tashi ta basu waje, ta tashi da gudu tayi d’aki tana aikin kuka,
Bikin zaheer ya matso anata shirye2, dakyar adeel ya bar Zeena taje gida tayi sati daya, anata shagalin biki gidansu Zeena ya cika da mutane sosai, an daura auren zaheer da amaryan shi Zaynab yar garin adamawa, washe garin daurin dauren zasu koma Japan domin ya samu aiki a can haka ko akayi ango da amarya suka wuce yan biki kowa ya watse, adeel ya kira Zeena yace yaushe zaki dawo, tace nan da 2week dan na gaji da hidiman biki, Ina so in dan huta, ya kashe Wayan Jim kadan ya kuma kira yace fito ina kofar gidanku, yana gama fadin haka ya kashe Wayan,sai gata ta fito ta zagaya ta shiga cikin motan tana shiga yaja suka wuce, tace ya zaka wuce dani banyi ma ummi sallama ba, yace ki kirata a waya, tun daka lokacin bata kuma cewa komai ba har suka isa gida, ranan Zeena tasan mijinta yayi kewanta kaman itama yanda tayi,
Mysha ce zaune ahmad nata wasa ta rame da danyi duhu, kullum tana cikin tunani ga iyayenta sun daina sakan mata sosai, mu samman ma dady dinta, gashi bata fita ko ina, inta kira adeel baya dauka, sai dai ta mai text tana bashi hakuri akan ya maidata, shima babu reply, sai a yanzu take nadaman abunda tayi, wani hawaye ya xubo mata, adeel sanka da kuma kishinka yasa nayi duk wa innan abubuwan, gashi yanzu ya tashi a banza tunda ka sakeni, lokaci daya taji tana nadaman abunda tayi, domin tasan nata kishin ya wuce musali,cikin wannan halin mum dinta ta sameta a ciki, ta tausaya ma yar tata, tace Mysha ki daina wannan kukan domin bashi da amfani, kuma komai Ya faru ke kika jama kanki, tace mum wlh ina son adeel dan Allah mum kisa dady ya mishi magana ya mayar dani, mamanta tayi shuru, tace Mysha dad dinki yayi fushi sosai dakyar in zaima adeel magana amma zan jaraba bashi hakuri.
Cikin Zeena yakai wata7 tana samun kulawa wajan adeel, kullum yana nuna mata so da kauna, itama tana iya kokarin ta wajan nuna mishi kulawa, suna zaune a falo wayanta yayi ringing ta dauka taga number ne, ta kara a kunne jin muryan Mysha tayi tana kuka, tace Zeena dan Allah kiyi hakuri akan abunda na miki, Zeena tace babu komai, sannan tace dan Allah kisa adeel ya dawo dani, wlh Zeena Allah ya jarabce ni da sonshi, Zeena tayi dan murmushi wanda bai kai ciki ba, tace zan mai magana duk yanda mukai zaki jini, ta kashe Wayan sannan ta kalli adeel wanda ya bata rai, tace lafiya kuwa naga ka daure fuska, yace banso kimin maganan Mysha plz, tace haba adeel karfa ka manta akwai yaro a tsakaninku ko danshi ya kamata kayi hakuri ka dawo da ita, yace Zeena bazan iya dawowa da Mysha ba, domin Mysha ba macen aure bace, Zeena tayi kaman za tayi kuka tace adeel ka dawo da ita saboda Allah, badan halinta ba, kuma na tabbata tayi nadama tunda harta kirani tana kuka akan inyi hakuri akan abunda tamin, nan yayi shuru dakyar Zeena ta samu ta shawo kanshi ya yarda,..
Adeel da Mysha sun dawo matsayin mata da miji Mysha ta canza kaman ba ita ba, komai ita take ma Zeena tace bata so tana komai tunda ba ita kadai bace, adeel har dan kiba yayi saboda yanzu ya sami kwanciyan hankali a gidanshi,
Adeel shi ya dauke biya masu twins karatu yana musu hidima kaman yaran daya haifa, Zeena kullum tana kara godewa Allah akan baiwar da yayi mata, ita da Mysha sun fara business Ana Kawo musu kaya daka waje suna sai dawa, Mysha da Zeena Ana zaune Ana fira, Zeena taji kaman ana tsungulinta a mara, tun tana ji kadan harta fara ji sosai, nan ta saki kara Mysha tayi sauri ta riketa tana fadin Zeena lafiya maike damun ki, tace Marana, dakyar Mysha tasa ta a mota sukai asibiti suna zuwa akace haiyuwa ne, akai labour room da ita ko minti talatin ba ayi ba ta haifa yarta mace, sai a sannan Mysha ta kira adeel take fad’a mai, zo kuga murna nan da nan yazo asibitin, yaga yar kaman Zeena sai dai ta dauko kalan hancin shi, yarinyan kyakyawa,
Zeena da baby dinta suna samun kula wajan Mysha sosai, ranan suna yar taci sunan ummi habiba, suke kiranta da ma-ma, mum tasai ma yarinyan kaya da yawa, haka itama ummi, ga wanda Mysha itama tayi, abda itama tayi aure ta auri wani saurayinta wanda suke san juna sosai, a dubai zata zauna saboda karatun ta.
BAYAN SHEKARA BIYAR
Zeena zaune da yaranta su uku, ma-ma da sadeeq sai anan, suna ta wasa, Mysha ta shigo ita da yaranta da gudu yaran suka tashi suna tsalle na ganin yan uwansu, Zeena tace har kun dawo kunyi sauri, Mysha tace wlh kuwa duk na gaji, itama yaran Mysha biyu, ahmad da saudat, nan yaran sukai waje suna wasa, ita kuma da Mysha suna ta hira, har adeel ya dawo, shima ya zauna anayi dashi, yace yanzu dai kun daina bani kulawa aure zan kara, jin haka Zeena ta tamke fuska, Mysha tace ai babu wacce ta isa ta shigo wannan gidan, yace haka kika ce, zaku gani ai jin haka Zeena tabar wajan, Mysha ta saki dariya tare da fadin sai kaje kaba aminiyata hakuri, yayi dariya shima sannan ya tashi ya nufi d’akin Zeena din, tana ganin shi ta kawar dakai gefe, yayi dariya yace haba amarya ta, jin haka ta saki kuka tana fadin ni ka daina cemin amarya wanda zaka aura ita zaka kira da haka, yayi dariya tare da fadin kece amarya ta, tunda na sameki na cire ko wace mace a raina, taji dadin abun da yace, yace ashe dai ana kishi na, ta rufe fuskanta da hannu, yayi dariya nan suka fada faranta ma juna nima dai a nan zan tsaya.
ALHAMDULILLAH