AMJAD CHAPTER B KARSHE
Lokaci guda cikinta ya d’uru ruwa,ba shiri ta fito daga d’akinta ta sakko laundry room anan ta d’akko broom stick tare da mop.Tunanin yanda zatai masa bayani ta shiga yi kafin tayi knocking tafi 4min,jin shiru yasa ta murd’a handle d’in ‘kofar ta shiga.Gani tayi baya ciki kuma ba alamar yana bathroom ,hakan ba ‘karamin dad’i yayi mata ba.Cikin sauri ta fara gyaran d’akin tana yi tana masif-masife.”K’azami kawai ,dubi kan katifa mtchww!”ba dan Allah ba haka ta gyara d’akin tass bathroom d’in ma haka ta gyaresa.Tana goge kan mirror ne taga wani d’an ‘karamin doki da aka sassa’ka da katako,d’auka tayi tana ta kallansa ta juya can ta juya nan garin haka ya su’buce ya fad’i,aiko tana dubawa taga kansa ya gutsire,salallami ta hau yi tana tarkatoshi.+
D’akinta ta koma ta d’akko wani super glue ta shiga mannawa a wuyan, daya jonu seya ‘bintire har ta ‘karar da glue d’in gashi duk ta ‘bata dokin yayi fari-fari a brown colour d’in
Amjad kuwa jin zaman d’akin ya isheshi yasa ya fice waje garden yayi zamansa,seda ya shafe ‘yan mintina ya komo.
“What is she doing?” Ya fad’a a ransa ganinta bakin mirror ta juya baya.
“What are you doing in my room?”
Nan da nan ta soma mutsu-mustsu ,da sauri ta ‘boye dokin a bayanta,gashi yau ba gyale a jikinta doguwar rigar atamfa ce da d’ankwali.
“You’re hiding something” Ya ‘karaso inda take a fusace ya mi’ka mata hannu ta fito da abunda take ‘boyewa.
“Let me see”
“Ni babu abinda na d’auka” Ta turo baki.
Ganin zata ‘bata masa lokaci ya mi’ka
hannu bayanta ze kar’be abinda take ‘boyewa,da sauri ta juya bayanta gam ta ri’ke dokin kamar nata.Kici-kici suka shigayi yana murd’e mata hannu tana ihu amma ta’ki saki,jin nauyinsa gabaki d’aya a bayanta yasa tayi saurin saki da ‘karfi ya wafce body d’in dokin. Ba shiri taja jiki ta matsa gefe du se taji wani irin dama bata ri’ke ba.
Ganin tsurar doki ba kai yasa Amjad ya waigo ya dubeta.”You broke it “
Shiru tayi bata ce komai ba kan dokin na hannunta na hagu ta dam’ke.
“Give me the other part” Ya mi’ka mata hannu.
Tana so ta bashi kuma tana tsoro kar yayi mata wani abun dan ta kula ta irin expression d’in fuskarsa d’auke da guntun murmushi mey manufofin.
A sanyaye ta bud’e ta mi’ka masa daga nesa -nesa,ganin hannunta be kai ba ta d’an matsa aiko abinda take tunanin shiya faru.Hannunta ya janyo har kan dokin ya fad’i ‘kas ita kuma ta fad’o jikinsa.
“Can’t you apologize?”
“Ka cika ni,kai kayi min godiya?”
Ta kasa ku’bucewa sam se raba idanuwa take.”Shut up!”
“Toh ka cikani”
“Keep your mouth shut”
Ya sake matso da fuskarsa har numfashinsu na had’uwa.Tsoro ne ya fara kamata dan haka tayi shiru mutsunma ta dena idanunta a rufe.
Door bell rang qlin! Jin haka yasa ya cika mata hannu har tana shirin fad’uwa da’kyar ta iya balancing kanta,a kunyace tayi sauri ta fita daga d’akin.
“Aunty” Ta furta lokacin data bud’e ‘kofar.
“Sannunku da zuwa” Ta fad’a tana bud’e musu ‘kofar widely.
Waje suka samu suka zauna su hud’un ,bayan data gaishesu ta kawo musu drinks.”D’ayan d’an kunnen fad’uwa yayi?”Wata daga Cikin ‘kannan Mami ta tambayeta.
STORY CONTINUES BELOW

Se lokacin ta shafa kunnenta taji ba d’an kunne d’aya,zuciyarta ce ta bata a d’akin Amjad ta yar.
Amjad bayan fitarta ya lura da d’an kunnen ma’kale a jikin shirt d’inshi,kallo d’aya yayi mishi ya bud’e drawer ya cillar a ciki coz yana expecting zata zo kar’ba.
Hira suka shiga yi irin ta ‘yan uwa har wajen maghrib tukun suka tafi.Suna tafiya ta koma d’aki ta d’akko mayafi ta yafa ,d’akkunen kuwa ta cire ta sauya wani dan bata jin zata iya komawa ta d’akko kayanta.
★★★
Tun abinda ya faru Laila bata sake yarda ta shiga d’akinsa ba ,Amjad ya samu sau’ki har ya koma aikinsa.Aliya a makaranta daga tayi mata maganar aurenta seta share zancen gashi lecture tayi nisa yanzu har sun fara test,tana dad’ewa ma bata sakko ‘kasa ba rabon data had’u dashi tun da safe yanzu har 10:23pm gashi an shigo watan azumi gajiya take sata kwanciya da wuri.
Amjad ma yanzu da wuri yake barin wajen aiki kuma yaci abincin ta ya’ki ko tayi dayawa sede ta bawa mey gadi da yazo kwanannan,wani lokacin fita yake restaurant ko ya siyo ya taho dashi kullum a wahale.
Aliya haka tayi ta ‘ko’karin turo mata video girke-girke iri-iri idan taga dama tayi wani kuma ta share musamman idan taga mey wuya ne.
Yau ba school,tunda ta tashi take jin alamar ciwon mara kad’an-kad’an aikuwa wajen 11:30am azuminta ya karye,dan haka ta shiga kitchen dan had’a abinda zata ci indomie kawai ta dafa bayan taci tasha magani ta komo d’aki tayi kwanciyarta.
Amjad shaf ya mance be tafi da key ba,2:30pm ya dawo a gajiye.Qlin!Qlin ya danna door bell shiru, har ya soma gajiya da tsaiwa.Laila kuwa baccinta take ta shara bata san yana yi ba.Gwada kiranta yayi a waya amma switchoff tana charge.
Ransa ba ‘karamin ‘baci yayi ba gashi ko mey gadi baida key d’insu na ciki,cikin mota ya koma ya kunna Ac.Se wajen 3:45pm ya koma ya sake ringing,dede lokacin ta sakko ‘kasa ita a tunaninta ma ko ba’ki tayi.Yana tsaye fuskarsa ba annuri kamar ya sha’keta haka yaji, gefe ta matsa ya shigo tukun ta rufe ‘kofar.
“I spent more than 1hr waiting for you to open this fucking door”
“Ni na hanaka fita da key”
“You…” Ya nuna ta da yatsa.
Matsawa tayi daga pointing d’inta da yayi ta waiga gefe.”You’re disrespecting me”
“Nasan matsalarka ,yunwa” Ta fad’a a ranta.
Ring! Ring! Wayarsa tayi ‘kara, Dad ya gani jikin screen.Be sake wata maganar ba ya bar gun.Gwalo ta bishi dashi ba tare da yasan tana yi ba.
Da lokacin shan ruwa doya da ‘kwai kawai tayi ta d’ibawa mey gadi saura data ci ta ajje,Amjad yau ko fita ya siyo abincin beba koda aka sha ruwa iya fruits yasha da. dabino.Seda ya dawo daga masjid ya lura da flask d’in da ta ajje doya da ‘kwan,d’aya ya d’auka yasa a baki yana feeling taste d’in.
“Not bad” Ya fad’a kafin ya sake d’aukan wata ya lun’kume a wasa awasa har ya kusan cinyewa.
Washegari da safe bayan ta gama shirinta tayi toasting bread da d’an yawa saboda zata je school dashi.Tana cikin yin breakfast Amjad ya shigo,jitai kunya ta kama ta lomar dake bakinta ta had’iye da ‘kyar ,saboda gudun karya ganta yasa bata ci a dinning ba amma duk da haka seda ya ganta.
“Are you suppose to eat? You don’t even feel guilty of what you’re doing”Ya ‘karaso yana janye plate d’in gefe ,kuma ya gane amma jan magana yasa shi yin haka.
” Meya shafe ka?”
“Repeat what you said, I can understand little of it”
Jin ya fad’i haka tayi shiru bata kuma wata maganar ba.
STORY CONTINUES BELOW

“Yarinya I’m soon living you here alone”
D’agowa tayi ta kalleshi jin ya anbaci yarinya”Toh a ina ya fara koyan wannan?”
“Surprised koh?”Murmushi kawai yayi ya fita daga kitchen d’in, abincinta ta cigaba da ci tana tunanin yadda ya fara iya Hausa.
Tunda aka fara azumi sau d’aya ta sake zuwa gida yanzu har za’a ‘kar’kare.Tana d’aki bayan ansha ruwa yazo yace mata ta shirya su fita,seda suka tsaya a mall tasan inda zasu.Siyayyar kayan sallah suka yi,daga nan suka komo gida ,su Maryam da suka zo ta basu suka kai mata d’inki,ranar sallah ji take kamar ba sallah ba ita kad’ai sede idan kunna chat tayi,jitai tayi missing tuwon Mami na sallah ,kira tayi a ways race su kawo mata ko abincinta ‘kinci tayi tana jira anjima su Nusaiba su kawo mata tuwo.
Basu suka zo ba se 4pm,ganin ‘kunshinsu datai taji ya birgeta jitai dama itama taje anyi mata ,Aliya seda tayi ta fad’a mata amma ta’ki.
Biyu ga sallah ta shirya zata gida,Amjad ne ya d’auketa badan yaga dama ba saboda Mom tace yaje.Suna tafiya a hanya ta ciro mirror d’in powdernta tana kallan fuskarta.” You better stop it ,you’re not even beautiful “Taji ya fad’a.
Har cikin ranta taji haushi” Banyi dan kace nayi kyau ba”Tayi maganar a fili.
“I can understand all you’re saying better watch your tongue”
Baki ta zun’buro ta mayar da mirror d’in, sam bata lura dashi ba yana ta satar kallonta,kayan jikinta ya amsheta sosai.Lace tasa maroon da torches golden se sar’karta ma golden data kwanta a wuyanta,fuskarta ma tayi makeup dede ,lipstick maroon tasa da eye liner kwalli ya fito tar a idonta.Mayafinta ma golden ne tayi d’aurin….(guess).
Zaman kurame sukayi har suka isa gidan Mami,ta bud’e ‘kofar zata fita ya tsayar da ita.”Don’t expect me to take you back home “.
” Better “Ta fita.
Se bayan ta shiga ya shiga gidan ,yana gaisawa da Mami ya fita daya had’u da Fauzan a ‘kofar gida ya bashi 10k ‘yan 500 sabbi.
” Ashe de da sauran mutunci”Laila ta fad’a sanda Fauzan ya shigo yana nunawa su Mami.
“D’azu nayi waya da Maman shi take fad’a min Amjad d’in zeje can Canada d’in” Mami ta fad’a.
“Uhm..eh” Ta fad’a a ranta kuwa tunani ta shiga yi,da gaske yake ashe.
“Mami yaya gida zata dawo ko?Nusaiba ta tambaya.
“Eh toh..”
“Ehmana nan zan komo” Laila tayi saurin fad’a.
Dad’i taji sosai dama exam zasu fara ba dad’ewa ,a ranta tana fad’in”Na huta yaje can ya ‘karata da ba’kin halinsa”.
Laila bayan ta ‘kare wuninta a gida wajen 5 :30pm ta tashi tafiya dan tasan ba zuwa ze d’aukanta ba.Lokacin da ta koma gida ta tarar yana gida,d’akinta tayi wucewarta.
Haka ta ‘kare sallah ba inda ta sake zuwa,bayan 1week suka koma school,yanzu shirye-shiryen exam suke ba dad’ewa suke ba 12pm wani sa’in ta komo gida,ita jira take taji yayi mata maganar tafiyarsa amma shiru beyi ba.
8:05am ta sakko ‘kasa,’karamar trolley dake girke a living room ta tsaya kallo bata gama sa’ke-sa’ke ba sega Amjad yana sakkowa daga steps. Yau ana ganinsa za’a san yana cikin farinciki,specs dake idansa ya zare.
“Home alone” Taji ya fad’a.
“Ni nace maka anan zan zauna?”
“You can speak the way you like to but you can’t change it ,I’m leaving now”.Yaja trolley ze fita Laila tace.” I’m not staying here alone “
STORY CONTINUES BELOW

“That is none of my business, the decision is yours” Yayi mata waving bye cikin rainin hankali.
Tana gani driver ya amshi trolleyn yasa a bayan mota ,Amjad ya shige baya abinsa driver ya jasu suka fice. Bata ‘kara ko minti d’aya ba tayi sauri-sauri ta haye sama.Nan take ta soma had’a nata kayan duk wani school things ta d’auka tazo duba phone d’inta kan drawer ta lura da kud’ad’e kan drawer d’in 50k ta gani.Handbag d’inta kuwa ta d’auka ta zira a ciki tasa wayarta key d’in gidan ta d’auka ta sakko bayan data kulle d’akinta,sauran doors na ‘kasa ma ta rife tukun exit door taja akwatinta ,mey gadi ne ya samar mata Napep ta tafi.
Tun a hanya ta kira Mami take fad’a mata tana hanya.Tana shiga gida ta ajje akwatinta a d’aki ,se murna take.”Se yaushe ze dawo?”Mami ta tambaya.
“Uhnmm.uh..3weeks” Ta kintata ta fad’a.
“Allah ya kaimu”
“Ameen” Ta amsa.
“Mami wainar gero nake son ci” Laila ta fad’a.
“Toh ta rashin ta idon zaki min” Cewar Mami.
Ita kwata-kwata Laila bata zaci za’a d’auki hakan da wani manufa ba da bata fad’a ba,kawai de ta dad’e bata ci bane shiyasa taji sha’awa.
“Kai mami nifa..”
“A’a kina sani kawai de tareraya irin ta yaran zamani”
Tashi tayi ta koma d’aki ta d’auko handout d’inta ta soma duba kayanta tunda su Maryam basa nan gidan shiru,wainar ma fasa siyowa tayi.
★★★
Amjad kuwa koda ya isa be damu da kiranta ba ,shi sam hankalinsa ba anan yake ba baida buri irin ya had’u da Rosie.
Mom ,Zakia da Shaheed ne suka taro shi a airport,Dad yayi tafiya,Mom ce first d’in ganinsa cikin sauri ta ‘karasa tayi hugging d’insa tightly.”My baby ,missed you so much”
“Missed you too”
Jitai kamar karta cika shi,su Zakia ma sukai hug lastly Shaheed, brother’s hug
Tunda suka taho a mota zuwa gida Mom hirar Nigeria take masa tana tambayarsa amma yana amsa mata kad’an -kad’an wani abun ma ‘karya yake mata idan yaga ta isheshi.
“Laila told me she’s staying there with her Mom” Yaji Mom ta fad’a.
“Uhmm” Ya kawar da maganar amma a ransa yayi ‘kwafa dan shi bece mata ta tafi ba.
Dinner na musamman aka shirya masa, se ji dashi Mom take zakia har tana tsokanarsa momy’s bae amma wannan karan be taya ta ba.Sam ranar be samu chance ba balle yaje wajen Rosie, se washegari da safe 10am bayan sunyi breakfast yace zeje wajen Sam abokinsa duk da kuwa Mom jikinta ya bata wajen Rosie zeje.Be tashi zuwa ba seda ya siya mata flowers da bracelet mey tsadan gaske,har wani rawar jiki yake.
“Angel I’m on my way to your house”Ya tura mata text.
Few minutes later ya isa gidan,3missed call yayi mata bata d’aga ba,yasan wani lokacin tana yin haka idan tana so tayi surprising d’inshi sometimes seya shiga gidan.’Karasawa yayi hannunsa ri’ke da flowers d’in se bracelet d’in a aljihunsa ,knock! knock! Yai knocking ba’a bud’e ba.Handle d’in ya murd’a ya Shiga.
” Hello”
“Hello”Ya ‘karasa living room.” Hel….”
‘Karashen lo d’inne ya ma’kale a ma’kogoro dan tsananin tashin hankali ,jiyai kunnensa ya dena jin sound tsaiwar ma da’kyar yake.Irin yanayin da ya tsinceta yasa ya kasa magana,a zuciyarsa yana ‘kokonto anya Rosie d’insa ce.Tana zaune a cinyar wani guy da besan waye ba suna kissing passionately ,tana sanye da wani fitinannun sleeping dress wanda dashi da babu duk d’aya.Guy d’inne ya fara lura da Amjad dake tsaye kamar gunki,ganin guy d’in ya dakata yasa ta d’ago tana kallon direction da yake kalla.”Amjad “Ta fad’a a hankali cikeda mamaki….
A inde yake tsaye ya yasar da flowers d’in ba tare da ya san yayi hakan ba ,kamar ‘kiftawar ido ya fita daga gidan. Da fitarsa da shiga mota be wuci ‘yan sakanni ba,tu’ki yake amma besan inda zashi ba,seda ya tabbata yayi nisa da area d’in ya samu yayi parking can bayan gari.”No!”Ya daki steering d’in motar ya zira yatsansa cikin sumarshi se mutstsukawa yake kamar ze cire gashin kansa.”It can’t be,No! Rose why? why?”be ankara ba yaji idanuwansa na tsiyayar hawaye,feeling his heart broken into pieces.
Tunanin rayuwarsu da suka shafe tare ya shiga yi,ko a mafarki idan aka ce Rosie zata ci amanarsa baze yarda ba amman yau ya gani da idansa.
Yafi 20 min yana abu d’aya wayarsa da tayi ringing yasa ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.
“Mom” Ya gani a jikin screen.
Ta kira har sau uku amma ya’ki d’agawa,lokaci guda yaji ciwon kai ya kamashi.Da ‘kyar ya samu ya iya komawa gida, image d’inta ya’ki gushewa daga idansa.
Mom ganinsa ya shigo gida tayi sauri ta ‘karasa inda yake.”Son, where have you been? are you ok?”
Kai kawai ya kad’a yana ‘ko’karin cire jacket d’inshi.
“Amjad, you’re looking sick” Ta fad’a tana dafa kafad’arsa fuskarta d’auke da damuwa.
“Mom ,I just need to rest”Yayi ‘ko’karin fad’a.
“Ok ,go to your room I will prepare your a meal immediately you woke up”
Yana shiga d’akinsa ya rufo ‘kofar,yana ciro wayarsa daga aljihu sega kiran Rosie.
“Baby boo” Ya bayyana a screen.
Gabaki d’aya wayar yayi switching off ya cilla gefe,ya fad’a kan gadon ya rufe idansa trying to force him self to sleep.
An hours later,2:30pm ya farka har lokacin kanshi be dena ciwon ba,tashi yayi ya shiga bathroom ya watsa ruwa yayo alwala ya tada sallah.
Knock! Knock! Mom tayi knocking ,ganin be bud’e ba ta murd’a handle ta shiga,sallah ta tarar yana yi haka yasa ta koma.Chicken Spaghetti ta dafa mashi tayi arranging,tana gamawa ta koma sama ta kirashi.
Ga abincin yasa a gaba amma ya kasa ci ,Mom data san Chicken spaghetti ne favorite d’insa tayi mamaki ganin ko fork d’in be d’aga ba.
“Amjad, don’t you wanna eat?”
“I lost my appetite”Yana fad’ar haka ya mi’ke ya bar wajen.
” Am..”Bata ‘kare ba taga har ya ‘bace mata daga gani.
★★★
Laila
7:12pm suna d’aki ita dasu Maryam se hirarsu suke ta mance da wani Amjad,idan Mami ta tambayeta suna waya da Amjad setace eh,wani lokacin har alarm take sawa idan yayi ringing setai pretending kamar kiran waya ne.
Amjad kuwa cikin dare 11:00pm sam ya kasa bacci kawai juye-juye yake akan gado daga ya rufe ido Rosie yake gani da wannan guy d’in,tashi yayi ya d’auko wani box a ‘kar’kashin gado.Hotuna ne ciki na Rosie harda wanda sukai tare dashi tun suna teens daga gefe kuwa teddy ne ‘karami mey heart a cikinsa wanda Rosie ce ta bashi wani lokaci da yayi birthday. D’aukansu yayi ya tarkata duka ya fita can backyard ya cinna musu wuta yana kallo har suka ‘kone ya watsa tokar a dustbin.Hatta phone d’insa babu wani abu na Rosie daya bari pictures nata na musamman daya tanada musu folder seda yayi deleting,seda ya tabbata ba abinda ya ragu nata a wayarsa ya iya samun yin bacci.Amjad sam be iya so ba haka be iya tsana ba,ya tsani yaudara mutum ne mey zafin kishi ko Zakia idan ya ganta da wani classmate bama boyfriend ba seya ji haushi.
STORY CONTINUES BELOW

“I hate you like hell”
“I hate you forever,I never wanna see your face again”
Idansa a rufe yake fad’ar haka ,firgit! Ya farka ,se lokacin ya lura 5:54am yayi,nan ya tashi yayi sallah.Yana idarwa ya sauka ‘kasa “Morning”
“Morning” Mom ta amsa.
Da ‘kyar ya samu ya iya yin breakfast d’in, data tambayeshi meyake damunsa ya’ki fad’a.
★★★
Amjad ko kwana uku beyi ba ya koma Nigeria dan ji yake kamar a kan ‘kaya yake a Canada,sede ba wanda yasan Nigeria ya koma ‘karya yayi musu yace Ethiopia yaje daga can ze wuce Nigeria.
Yana komawa Nigeria ya cigaba da zuwa aikinsa dan so yake ya mance da komai har ‘karawa kansa lokaci yake kafin ya tashi se wajen 5:30pm,daya koma gida ma baya hutawa wani aikin ze tsiri yi yaita dube-dube a system, a ‘yan kwanakin da akai har ya rame da an ganshi za’a san yana da damuwa.
Laila kuwa cikin kwanciyar hankali take exam d’inta,ji take kamar ta komo gida kenan dan ko maganar komawa bata yi.Seda suka kwashe 2weeks da ‘yan kwanaki suna exam,yanzu anyi hutu na ‘yan weeks kad’an.Yanzu ta komo hawa online sosai ba kamar sanda suna exam ba idan ba abu daya shafi karatu ba bata bud’e data.
Yau bayan sun gama cin abincin dare,su Maryam suna parlor suna kallo ita kuwa tana d’aki se chat d’inta take hankali kwance.
9:45pm,yana d’aki be jima da dawowa ba daga restaurant kullum seya je yaci abinci acan,yana watsa ruwa ya d’auka waya ya hau whatapp chat ,abinda ya dad’e beyi ba.Contact ya shiga yana ta duba numbers ,yazo N letter idansa ya sauka kan Nigeria,daya duba kuwa yaga tana online. Profile d’inta ya shiga viewing inda yaga profile picture d’inta dake d’auke da photo d’inta tayi rolling da red mayafi kuma fuskarta tasha make-up sede ba duka ta d’ago fuskar ba ta d’an sunkuya inba wanda yasanta ba baze gane itace ba.
“Hi” Yayi sending da ‘kyar dan ya dad’e kafin ya iya turawa.
Tana cikin chat taga “hi” data dubi number d’in taga na Amjad ne ,tafi 10min kafin tayi reply da .
“Hello” Tayi reply.
“Why are you chatting at this time, aren’t you suppose to be reading ?”
“Exam is over ,hutawa zanyi”
“What did you mean by those last words?”
“You don’t need to know”
“Ok,can you please change that profile pic with something better? coz you’re looking ugly”
“I choosed it myself and I like how I’m looking”
Murmurshi abinda ta fad’a yasa shi.”But I don’t like it”
“I don’t care”
“Ok,where are you now?”
“Home”
“You’re Lying, Mom told me everything”
“Your house is not my home, I’m referring to Mami’s house”
“Good for you,you’re soon coming back”
“No”
“You must”
Laila: “When are you coming back?”
Amjad:” Do you care?”
Laila: “No”
STORY CONTINUES BELOW

Amjad: “Then why did you ask?”
Laila: “Just wannan know”
Amjad: “I knew you missed me”
“Wallahi a’a”
Amjad:”Lier”
Laila:”I’m not”
Amjad:”You are!”
Daga haka bata sake tura wani abu ba tayi banza dashi ta cigaba da sauran chat d’inta. Amjad kuwa da tun tini dama da ita yake chat in banda it a ba kowa,ganin shiru ya sake yi mata magana.
Amjad:”Laila”
Laila:”Mene?”
Amjad:What is your problem?
Amjad: What is the meaning of “mene” ?
Laila :”It means “what”
Amjad: What of “why” Ya sake tambaya dukda kuwa ya san ma’anar kawai jan magana be.
Laila: “Meyasa”
Amjad:I gerrit,what of “Ni nace” You often say the words.
Laila:I’m not a teacher, I’m going to bed”
Amjad:😎 who care to learn your language? disgusting!
Laila:Eh d’in chat d’in ma baza a sake yi dakai ba”
Amjad:Rubbish!
Sauka tayi daga chat d’in ta zira charger a wayarta tayi shirin kwanciya,tana kwance chat d’in da sukai yana ta dawo mata wani abun ya bata dariya wani ya bata haushi.Se to 11:30pm tayi bacci.
Ta ‘bangaren Amjad kuwa ganin ta sauka ya koma Instagram,”Lai-mus” sunan da take amfani dashi a insta.526 followers,jiyai ya damu da yaga followers d’in kad’an-kad’an yana scrolling jama’a iri-iri maza sunfi ma yawa ,post d’inta ya koma dubawa yaga har 27 sede photo d’inta a ciki 3 ne sauran duk qoutes pic ne,+200 yaga like da + 62 comment kan wani pic nata da niqab nema a fuskarta idanuwanta ne kawai suka fito wanda sunsha kwalli rad’au.
Nan take yaji wani Abu ya tokare mashi a ma’kogoro,musamman wani comment dayaga wani guy yayi.”Baby I love your sparkling eyes🔥🔥”
Instagram d’in ma fita yayi ya ha’kura da chat d’in,se jin haushi yake ,chat d’in da sukai ya shiga ya soma dubawa a haka har bacci ya d’aukeshi.
Washegari
Laila bayan tayi breakfast su Maryam dake gida kasancewar yau Saturday basu je makaranata ba suna parlor suna kallo tare.
“Laila” Mami ta kirata daga d’aki.
“Na’am” Ta amsa tare da mi’kewa.
“Mami gani” Ta fad’a bayan ta shiga d’akin.
“Ke ashe Amjad d’in ya dawo baki fad’a min ba” Cewar Mami.
“Uhmm?” Ta waro ido tana kallon Mami.
“Ehyi,yanzunnan muka gama waya da mamansa take fad’a min jiya ya dawo”
“Uuhm”
“Toh yau zaki koma kenan?”
“A’a Mami ba yau ba” Ta diririce harda kad’a hannu tana maganar.
“Se yaushe kuma?”
“Uhnmm wani satin”
“Kin manta wata shekarar,ke mijin naki ya dawo ma ba ko d’an ‘kunshi single kamar namiji”
“Ni bana so”
“Aiko anjima ki shirya Maryam ta raka ki ,hannu kamar muciya”
Ring!Ring tajiyo ‘karar wayarta daga d’aki,haka yasa ta dakata da maganar da suke da Mami ta tafi d’aukan wayar.
Numbern Amjad ta gani jikin screen aiko ta’ki picking bayan kiran ya ‘kare ta saka wayar a silent.Seda ya kira sau uku ganin batai picking ba dole ya ha’kura.
Wajen 3:30pm Mami tasa Laila zuwa gidan ‘kunshi,haka bata so akai mata ja.Ba ‘karamin kyau yayi mata ba yayi maroon a farar ‘kafarta ,a hanya zira hannayenta tayi a hijab tana karewa dan jitake wani iri.
“Toh baga shi ba ,amma da sekace namiji” Mami ta fad’a sanda suka shiga gidan.
Ita de bata ce komai ba ta wuce d’aki,ita kanta se kallon hannun take yana birgeta.Idan ta tuna da batun komawa gidan Amjad kuwa setaji ‘bacin rai.
“Ko bazan ‘kara sati ba sena yi kwana hud’u kafin na koma” Ta fad’a a ranta.
Amjad ganin bata d’aga kiran nashi ba seya hau WhatsApp ko ze ganta online amma shiru ba alama, tashi yayi ya fita daga gidan ,dan yanzu idan yana zaune shi kad’ai tunanin Rosie ne yake addabarsa.
Har ya dawo gida ya sake dubawa ko ta hau online amma shiru se ha’kura yayi ya kwanta.
Itama ta ‘bangarenta tana so ta hau chat amma kuma tana gudun kar yau ma yayi mata magana ,shiyasa ta ha’kura da chat d’in ta ajje wayar.
★★★
Yau tun 4:30am ya farka bacci amma ya kasa komawa sakamakon mafarkai marasa dad’i da yayi tayi wanda duk akan Rosie ne.Asuba nayi ya tashi ya fita masjid,koda ya dawo be koma bacci ba ,wayar tashi ya sake duba last seen d’inta ko zega ta hau jiyan amma still bata hau ba.
Laila kuwa yau se 9:53am ta tashi daga bacci tun bayan sallahr subh,hakan ma seda Mami ta tashe ta da kanta.
“Yini zaki a haka? sekace kasa”
“Mami goma ma fa batai ba” Ta fad’a tana murza ido.
“Kin ajje waya tun d’azu ana ta kira”
Tana jin haka ta ayyana Amjad ne,bataso ba ta mi’ke ta shiga bathroom tayi wanka bayan ta shirya tayi breakfast.Data duba wayarta kuwa 6missed call ta gani na kiran Amjad,ganin ta gaji da ganin numbernshi ba suna ta shiga yi saving, sunan da zata saka mashi tayi ta tunanowa.Ta san idan tasa Amjad gatsau da matsala dan su Mami zasu iya gani.
‘Hus…’ Ta fara seta goge.”Hauka ma kenan”.
‘Na dole…’
“A’a”Ta goge.
Finally de tayi saving da ” Canada “.
12:34pm suna kitchen da Mami suka ji knock,Fauzan yana d’aki ,Laila ganin ta fi kusa da ‘kofar yasa ta tafi bud’ewa.
Tsegege ta tsaya tana kallonsa shima kallon nata yake cikin ido hakan yasa tayi sauri ta kawar da idonta.
Tana tsaye ita bata ce ya shigo ba kuma bata rife ‘kofar ba.
“Can I come in?” Ya tambaya.
“No” Ta girgiza kai.
“OK,then I will wait for you outside”
“Me..? “
“Yes ,you’re following me home”
“I will not”
“Stop wasting your time,just hurry up and park your things”
“Laila!” Tajiyo Mami ta kirata.
Sauri tayi ta bar gun ta tafi.”Naji shiru,waye?
“Uh..Amjad ne”
“D’aukan ki yazo yi kenan?”
“Mami nifa..”
“Ke mey?,kinga ki shiga ki shirya kayanki”
A kasalance ta shige d’aki,cikin sanyin jiki ta soma shirya kayanta kamar mara laka a jiki.Hijab d’inta ta d’akko ta zirma ta ri’ke niqab d’in a hannu ta fito d’ayan hannun ta ri’ko akwatin.+
“Kin fito?”
“Uhmm” Ta amsa.
Su Maryam suna daga d’agi suka fito,ganin Fauzan yasa ta fad’in.”Mami dan Allah Fauzan ya bini”.
“A’a ba yanzu ba,se anyi hutun makaranta”
Ita tama manta yau Sunday,tana jin haushi ta fita su Maryam suka rakota har bakin mota,Amjad yana ciki yana jiranta.Da kanshi ya fita ya taimaka mata tasa kayan a baya,kafin ya koma motar ta rigashi shiga.Niqab dake ri’ke a hannunta ta d’aura a fuska ko idanuwanta ba’a gani,jin alamar ya shigo motar ta kawar da kanta window.Har suka hau titi ba wanda yayi magana ,sede lokaci-lokaci yana kallonta.Suna isa gida tayi tafiyarta ko kayan bata bi ta kansu ba,key dake jakarta ta ciro ta bud’e ‘kofar.
Sama ta haye direct d’akinta ta shiga ta rufo ‘kofarta.
“An dawo Prison”Ta fad’a a fili.
Knock!knock! Tajiyo bugu,handbag d’in ta ajje sannan taje bud’ewa.Amjad ta gani ri’ke da akwatinta,jira take taga ya mi’ko mata amma shiru.
“Remove this from your face” Yayi nuni da hannunsa.
“I wanted it this way”
“And I don’t like it”
“But you don’t wanna see ugly face”
Se yanzu ya tuna ,dariya abin ya bashi dan shi ya mance ya fad’a.Seda ya d’an murmusa tukun yace”So now you believed you’re ugly?”
Komawa tayi cikin d’akin ta barshi a tsaye gun, gefen gado ta samu ta zauna tare da ciro wayarta cikin jakarta. Akwatin ya ri’ko ya shigo da ita d’akin daga gefen gado ya ajjeta.”Answer my question “
“Did you believed?”
An d’au mintina a haka ita bata amsa ba shi be fita ba yana tsaye a kanta.Laila data gaji da zaman hakan tashi tayi ta wuce bathroom kafin ya farga ta rufo ‘kofar.
“Laila!” Ya kira sunanta.
“I’m not going anywhere until you answer my question?”
“Shiru tayi kamar ba jinsa take ba,niqab d’in kuwa ta yaye shi tana tsaye jikin ‘kofar tana jira ya fita.
” Laila,can’t you hear me? talk to me”
STORY CONTINUES BELOW

Ya gama surutansa ko ‘kala batace ba,can jin shiru yasa ta kasa kunne taji ko ya fita,alwala ta d’auro ta cire hijab d’in ta had’a da niqab d’in ta ri’ke a hannunta.
“Am..Amjad” Ta kira a hankali kamar mey rad’a.
Amjad dake zaune kan gadon dariya ya soma yi yana rife bakinsa.
“Amjad” Ta sake kira.
Jin shiru zuciyarta ta raya mata ya fita dan haka ta murd’a handle d’in a hankali,cikin sand’a ta fara takowa.Data duba ko ina taga ba kowa ta saki hamdala,kamar ance juya ta ganshi tsaye a bayan ‘kofa .
Da sauri ta kwasa da sauri zata koma bathroom d’in carpet dake wajen ya zamar da ita “Aghh!” Ta ‘kwala ihu tana jira ta jita a ‘kasa.
A hankali ta bud’e ido,taganshi ri’ke da ita ‘kiris ya rage bata kai ‘kasa ba ,kallo suke ido cikin ido ,d’ankwalinta da be gama zama a kanta ba ya zame ‘kasa,kitson gaba ya yarfo a goshinta har yana rufe mata ido d’aya.Hannunsa ya d’ora kan gashin a hankali yana matsar dashi daga fuskarta.
“Let me go”Ta fara kici-kici.
Mi’kewa yayi completely tare da d’ago da ita,hannunta tasa ta ture nasa daga ‘kugunta ta matsa gefe.
Ring! Ring! Wayarsa tayi ‘kara,daya duba yaga daga office ne.Bece komai ba ya fita daga d’akin,yana fita ta rufo ‘kofarta tare da murd’a key d’in.
★★★
Laila tunda ta rufo ‘kofarta bata sake budewa ba ,har 4pm tayi gashi yunwa take ji biscuit dake jakarta ma ta cinye shi.
Hijab ta zumbula har ‘kasa tana ta ‘boye hannayenta ciki,sekace mara gaskiya tana sakkowa daga benen she waige-waige take.Kitchen ta shiga ta bud’e fridge tana dube-dube,fruit salad ta had’a tasha abinta ,data fito daga kitchen ta bud’e ‘kofar waje ta fito.Gani tayi ba motarsa ” Ashe ma ya fita”Ta fad’a.
Komowa tayi sitting room ta kunna TV,Bollywood ta kai tayi zamanta kan sofa.Tunawa tayi da aya mey gishirinta data taho da ita daga gida dan haka ta koma d’aki ta d’akko sannan ta dawo ta cigaba da kallonta tana yi tana cin abarta.
Maghrib nayi ta tafi d’aki seda tayi sallah ta sakko kitchen, jollof d’in taliya tayi dede bakinta tana gama ci ta dawo sitting room ta iske an fara film d’in data ke so.Zamanta tayi harda dad’o volume.
9:45pm,ya shigo gida ganin TV a kunne kuma bega alamar mutum a parloun ba ya ‘karasa ze kashe.Se lokacin ya lura da ita tana kwance se bacci take hankali kwance ta d’ora tafin hannunta a fuskarta ,yawanci haka take baccinta inde zatai bacci seta d’ora tafin hannunta ta kare fuskarta shiyasa ya zame mata jiki ko bata san tayi bacci ba se tayi haka.
Ba abinda yake kalla se ‘kunshin hannunta daya sake maroon barin ma ga’bo’bin yastsunta data rufe fuska.Ba sosai ya fiya ganin ‘kunshi ba ,dan ko su Mom da Zakia ba yi suke ba inba a TV ba.
Idansa ne ya sauka kan ‘kafafunta da zanen ‘kunshi ya bayyana sosai,’karasawa yayi inda take ya zauna kan gwiwoyinsa ,zanen ‘kunshin ne yaja hankalinsa har da ri’ko hannunta yana kalla.
Kamar a mafarki taji ana motsa mata hannu, kad’an-kad’an tana bud’e idonta har ta bud’e tar tayi ido hud’u dashi ,a razane ta mi’ke daga kwanciyar ,shi dake zaune seda ya mi’ke tsaye.
“Is ok”Ya fad’a a sanyaye.
” Is ok a ina ana shafan hannu”ta fad’a a ranta.
Tashi tayi daga zaunen ta matsa can gefe,10:05pm taga agogon parlorn ya nuna TVn ma ta kula har an gama film d’in datake kallan ma.
STORY CONTINUES BELOW

D’an ‘karamin bowl d’in data zuba ti’kar ayar data ci ta d’auka kan center table d’in ta wuce kitchen se wuri wuri take.A kitchen d’in ta dad’e ba abinda take tana tsaye se murza yatsunta take tana kallon hannun.Du da batai ‘kunshin ba da ba haka ba.
“Laila” Taji ya kira sunanta.
A rud’e ta d’ago ta kalleshi yana daga bakin ‘kofa.”Are you alright?”
“Yes” Ta amsa a hankali.
“Aren’t you watching movie?”
“No I’m not…I will not..” Ta shiga stammering.
“What are you waiting for?”
“I’m going to bed”
“Ok,let’s go”
“Uhn..aa’ai ba ..uh..” Du ta diririce.
Kamar yayi dariya ganin yadda ta rikice dama yana sane ya fad’i haka,takawa ciki ya soma yi.Laila ganin yana doso inda take ta fara baya ,gefen locker tayi tabi tana zagayewa the more yana tahowa the more tana kewaye drawer d’in kitchen d’in.Ganin ya tsaya tayi sauri tabi gefe ta fice daga kitchen d’in, binta kawai yai da kallo yana dariya.
Tana shiga d’akinta ta shige bathroom dan gani take kamar d’akin ma she is not safe.Se yanzu taji gumin daya tsatstsafo mata a jiki alhali ba zafi.
“Mey ya sami kansa a Canadan?” Ta tambayi kanta.
“Wayyo!”
Washegari
7:30am ya gama shirinsa cikin blue T-shirt mey long sleeves,se black jeans.Abubuwan da suka faru jiya ne sukai ta fad’o masa,shikad’ai ya hau murmushi agogon hannunsa yake sawa amma ya tsaya seda wayarsa yayi ringing ya dawo daga duniyar tunani.
Laila data farka tun 7:14am amma ta kasa fitowa se le’ken window take tana jira taga ya fita,aiko cikin le’ken ta hangoshi ta sakankance tana kallonsa yazo bud’e mota kamar ance kalli ya d’ago kansa.Laila tsabar rikicewa ta kasa barin window d’in kunya ce ta rifeta seda tayi da tasanin le’kawa,shikuwa be fasa kallonta ba seda ta bar wajen.Murmushi yayi yana zira specs a idonsa ya shiga motar.
Tana jin ya fita ta sakko ‘kasa ta shiga kitchen domin had’a breakfast.Bayan ta gama breakfast ne ta koma d’aki tayi wanka ta shirya,jitai shirun ya isheta ta d’auka waya ta shiga chat.
Amjad:”Mrs Amjad” Yai mata sending ganinta online.
Laila:”I’m not”
Amjad:”What were you doing at the window ?”
Laila: Nothing
Amjad:You missed your husband.
Laila:No you’re not my husband “
Amjad: Stop pretending.
Amjad: Who was your ex bf ? “
Laila:Someone
Amjad: Name?
Laila:You don’t have to know “
Amjad:”Ok,What are you doing now?
Ganin tambayoyinshi sun’ki ‘karewa yasa ta sauka ,aiko ba jimawa sega kira ya shigo.’Canada’Ta gani jikin screen.Ajje wayar tayi ta’ki picking har ya gaji da kira,daga baya ma tashi tayi ta sauka parlor ta kunna kallo.
★★★
4:30pm yau ya tashi daga aiki, Laila tana parlour jin shigowarshi yasa tayi saurin mi’kewa ta koma d’akinta.Tana shigowa yaga ba kowa a parlour sede ga TV a kunne ,hakan yasa ya gane da tana zaune kallon wata’kila ko taji dawowarsa ne.
STORY CONTINUES BELOW

Tana jin sanda ya shiga d’akinsa ,dan haka ta zauna kan gado aikin zama.
1hr later,Knock! Knock! Taji bugu,tana daga shingid’e tayi saurin mi’kewa zaune zuciyarta na dukan uku-uku.
“Laila” Ya kira sunanta.
‘Kin amsawa tayi se wararo idanuwa take wata zuciyar tana ce mata ta bud’e ‘kofar bathroom immediately ta bud’e masa ‘kofar seta shige bathroom,haka tayi ta sa’ke-sa’kenta.
“Laila open this door”
Hijab d’inta ta d’auka ta zurma ta ma’kale shi a jikinta, a hankali ta bud’e ‘kofar ta ra’be daga baya-baya.Tsayawa yayi daga bakin ‘kofar bema shigo ba,wani card dake hannunsa ya mi’ke mata,a tsorace tasa hannu ta ‘kar’ba ba tare da ta d’ago sun had’a ido ba.
Anniversary Invitation ne wanda taga yau ne ranar zuwan 8:00pm aka rubuta a jiki,bata gane nasu waye ba ita de ta karanta.Tana d’ago da kai taga har yana komawa d’aki dan haka ta shigo ta rufo ‘kofarta.
“Ni naje nayi mey acan? wa na sani a wajen? Tare zamu?” Ta jero wa kanta tambayoyi.
Har bayan maghrib bata soma shiryawa ba seda taga ya turo mata text.”Are you ready?”
“No” Tayi reply.
“What are you waiting for?”
Bata sake wani reply d’in ba ta tashi ,wardrobe ta bud’e ta soma duba kayan da zata saka,ganin zata ‘bata lokaci ta ciro wani ba’kin abaya me golden duwatsu,nan da nan ta saka.Powder ,lipstick da kwalli kawai ta sa ta fesa turare mey taushin ‘kamshi,red mayafi tayi rolling dashi.
Wayarta kawai ta d’auka ta zira takalmi mey matsakaicin tudu golden ta samu waje ta zauna.7:41 knock! Knock!
Tsaye ta ganshi yayi shigarsa cikin dark blue suit ciki white shirt da ba’kin jeans ,gashin kanshi yasha gyara se shining yake,turarensa mey ‘kamshin gaske se dukan hancinta ake.
“Ready?”
“Uhm” Ta amsa ciki-ciki.
“Let’s go” Yayi nuni da hannu.
‘Kofar d’akin ta rufo tabi bayansa dan ta’ki bari su jera ,a haka har suka sauka ‘kasa.A mota shiru ba mey magana,laila ita tama kau da kai can tana kallon waje.Suna isa gurin mutane an hallara ,ita de kallo take binsu dashi dan ba wanda ta sani,se gaisawa yake da mutane wanda yawanci duk abokanan business ne.Wani table suka zauna kafin daga bisani ya tashi amsa kira,bayan ‘kan’kanin lokaci sega iyayen taro sun shigo wajen tare da baby d’insu wanda bata wuce 3yrs ba sunsha ‘kwalliya gwanin sha’awa,ana ta gaggaisawa dasu tana gani Amjad yaje suka gaisa bata ankara ba taga sun nufo inda take.
“Wayyo ni Laila” Ta fad’a a fili.
Matar cikin fara’a ta soma mata magana Laila ma ‘karfin hali tayi suka gaisa tayi musu fatan alkairi,sede taga Nigerians ne kuma hausawa “how come’s Amjad ya sansu?” Abinda ta tambayi kanta kenan dan a iya saninta dashi baida wani abokai.
“Laila ko?” Macen ta fad’a.
“Eh” Ta amsa.
“Ni kuma Aisha,yau Allah yasa min had’u de”
“Gaskiya kam” Cewar Laila.
Sauran ba’ki da suka zo gaisawa da Aishan yasa suka katse hirar da suke,Amjad d’in ma se hangoshi tayi daga nesa yana gaisawa da mutane.
Farouq d’an abokin Dad ne yawanci inde suka zo Nigeria suna zuwa gidansu,shekararsu hud’u kenan da yin aure ,duk a Nigeria shikad’ai ne wanda Amjad zece suna abota ,bayan shi baida wasu abokai.
Laila Tana zaune Aisha tazo “Nan hayaniya,taso mije ciki” Ta taso laila dan ta lura kamar laila bata son hayaniya.
Cikin gidan nasu ta shiga da laila ta kaita wani parlour.”Bari gani zuwa”.Ta fad’a tare da barin parlourn.
Kitchen ta shiga d’aya daga cikin masu aikinta tasa ta kawowa Laila abinci,kiran waya da akai mata yasa ta fita zuwa wajen ba’kin .Ita kuwa mey aikin ganin aiki ya mata yawa yasa tasa wata ‘yar uwarta da tazo daga ‘kauye ta zibawa Laila.
Kai tsaye ta bud’e wani plate dake kan drawer ganin friedrice tasha chicken akai ga kayan had’i burjik ,dama ma’kuiyaciyace yasa kawai tasa spoon ta d’ora plate d’in a tray tare da d’ora robar ruwa da orange juice ta kaiwa Laila.
Laila dama tun yamma take jin yunwa,ba ‘bata lokaci ta bud’e plate ta soma ci,sede taji abincin taste d’in ba dad’i cabbage d’in yayi wani iri gashi ba zafi ita a tunaninta ko hucewa yayi.Haka ta lalla’ba taci, naman ma ba sosai ta iya ci ba,rabi taci ta rife plate d’in.Leman ne ma tasha da yawa ta kora da ruwa.
Wayarta ta kunna Tana d’an duddubawa a haka lokaci naja har taci fin 30min.Sede kuma tun bayan cin abincin ta fara jin suka a cikinta kad’an-kda’an yana murd’awa.
Wani irin murd’awa cikinta ya hau yi,nan take gumi ya soma keto mata ta rasa abinda ke mata dad’i wayar ma ajje ta tayi gefe.Tashi tayi a rud’e ta nufi inda taga mey aikin ta shiga,a kitchen ta tarar da ita tana wanke-wanke.Laila tambayarta tayi toilet tana ta zufa.D’aki ta rakata wanda yake d’auke da toilet a ciki,da sauri-sauri laila ta fad’a ciki.+
Minutes later ta dawo parlour gwiwoyinta sun fara sanyi gashi cikin har yanzu be dena hautsinawa ba,wayarta ta duba taga 3missed na Amjad. Bata ko zauna ba ta fita,a chan farfajiyar gidan ta hangeshi yana zaune a table shi kad’ai jama’ar wajen ma sun fara raguwa.A hankali ta taka zuwa inda yake,sede ta ‘karaso ya kula da ita.
“Where have you been?”
“Gani na fito ai”Ta fad’a.
Mi’kewa yayi tsaye ya fara tafiya tana biye a bayansa Farouq da Aisha suka ‘karaso inda suke.
” Tafiya?”Ta tambayi Laila.
Laila cikin ya’ke ta amsa da “Eh”
“Toh bari na kar’bi numbernki”.
Numbernta ta fad’a mata a take tayi flashing itama Laila tayi saving, har waje suka rakosu ita de Laila kawai basarwa take cikinta ba abinda yake se hautsunawa ta ‘kagu su koma gida.
Tunda ta shiga mota bata ce ‘kala ba,gani take kamar ba tu’ki yake ba har wani le’kawa take tana ganin speed d’in.”Mtchww” Tayi tsaki ba tare da ta sani ba.
“Are you alright?” Ya tambaya.
Kai ta kad’a alamar “eh” se kad’a ‘kafa take tana tapping cinyarta.”Innalilahi wainna ilaihirraji’un”Ta fad’a a ranta ganin traffic light ya tsayar dasu.
Da ‘kyar ta samu ta iya jurewa har suka koma gida,cikin sauri ta fad’a toilet ko ‘kofar d’akin yau bata rufe ba.Daga dawowarsu zuwa yanzu Laila ta shiga toilet yafi sau uku,gwiwoyinta gabad’aya sunyi sanyi da’kyar take takawa.Gashi batasan inda zata sami magani ba,lokaci guda tayi zuru-zuru jinta take kamar kara dan tsabar rashin ‘kwarin jiki.
11:29pm Ring!Ring! wayar ta tayi ‘kara lokacin tana toilet har 3 missed call batai picking ba.
Amjad yana d’akinsa dede lokacin yake shirin kwanciya wayarsa tayi ‘kara,koda ya duba yaga Farouq.
Knock! Knock! Ya ‘kwan’kwasa ‘kofar d’akinta shiru,handle d’in ya murd’a ya shiga beganta ba.
“Laila” Ya kira sunanta.
Tana shirin fitowa taji ya kira sunanta ,zaro ido tayi ido tana mamakin jinsa a d’akinta a irin wannan lokacin.
“Laila ,come on open the door”
Tsit kake ji ko motsi ta’ki yi gashi tsaiwar ta isheta,kan bathtub ta samu ta zauna ta dafe cikinta.
“Laila,can’t you hear me? open the door now stop pretending I know everything”
“Mey? Waya fad’a masa? Yasan…” Ta dafe kai shikenan tonon silili.
“Laila don’t let me open it myself, you know I have a spare key right?”
“Innalillah” Jiki ba ‘kwari ta mi’ke tsaya a daddafe ta ‘karasa jikin ‘kofar gashi jikinta kayan bacci ne riga da wando kusan ¾,inda Allah ya taimaka ma rigar ta hauro kusan cinya,d’an’kwalin kanta ta ware yadda ze sakko ‘kasa , a sanyaye ta bud’e ‘kofar kanta a ‘kasa.
“Laila” Ya kira sunanta.
A hankali ta d’ago da kanta kallo d’aya tayi masa ta maida kanta ‘kasa,se jan mayafin take tana kare ‘kirjinta.
STORY CONTINUES BELOW

“Uh…you need to see a doctor”
“I’m fine” Ta fad’a murya ‘kasa-‘kasa.
“You’re not,you better stop pretending I know you’re not ok they explained everything to me, you ate a spoiled food”
Shiru tayi bata musa masa ba,ta kasa d’ago da kai dan tsabar kunya a ranta tana da tasanin cin abincin.
“We need to go now”.
Tana jin kunya ta wuce zuwa wardrobe ta ciro hijab d’inta ta zira, wata doguwar riga ta d’auka tana so tasa gashi yana tsaya a d’akin se so take ya fita amma yayi burus sema folding arms da yayi yana kallonta.’Karfin hali tayi ta ri’ko doguwar rigar a hannu ta wuce bathroom yana kallonta.
Tana fitowa ya tafi d’akinsa ya d’auka key ya fito,a sitting room ya taradda ita zaune kan sofa dan ko tsaiwa ta kasa.
Ganin ya sakko ta mi’ke a kasalance ,suna fita kafin ta shiga mota kawai amai ya tunkaro ta kafin ta koma ciki ta she’kashi a cikin flowers.Kafin aje asibiti ta sake galabaita ,suna zuwa aka sa mata drip,tana kwance se kallon carnula d’in dake hannunta take,hijab d’in ta cire se mayafin kanta ta yafa.Amjad yana daga zaune kan kujera daga gefenta.Gashi ta manta wayarta ba dama ta kira Mami,ga abinci daya siyo mata ta kasa ci maganin ma da’kyar tasha.
“You need to eat”
“Na ‘koshi” Ta fad’a a ciki.
Be sake ce mata komai ba ya cigaba da tapping wayarsa.
★★★
5:06am ,ta bud’e idonta hannunta ta d’aga ganin carnula ta mayar,a kan kujera ta kalleshi ya jingina se baccinsa yake.Data kalli ledar ruwan taga ya kusa ‘karewa,tunanin yadda za’ai ta tashesa ta fad’a masa ta shiga yi.Pillow ta d’auka ta d’an buga ‘karshen gadon amma kamar bayi take ba,haka tayi -tayi harta gaji,daga baya kawai ta cilla masa pillow d’in aiko ya sauka kan fuskarsa.Yana bud’e ido ta sunkui da kai kamar ba ita tayi ba.
Pillow d’in ya kalla kan cinyarsa ya dawo da kallonsa kanta,ganin ba pillow kan gadon yasa ya gano abinda tayi.”What do you want?” Ya tambaya.
Drip d’in ta kalla tayi masa nuni dashi yanda tayi da bakinta ne yaso bashi dariya har ma da birgeshi,cikeda shagwa’ba ta ta’be bakinta.
Da kanshi ya cire mata ,bayan ya kira nurse kuma ta cire carnula d’in.Cikin sanyin jiki ta tashi ta shiga toilet ta d’auro alwala,shima masjid ya fita sallah.Bayan ya dawo daga masjid ya siya mata abinci,dama yunwa take ji tana ci tasha magani.Wajajen 8:30am akai discharging d’insu suka koma gida,se bayan sun dawo ta tuna da office d’insa,tana so ta tambayesa zeje amma ta kasa.”Toh zaman mey kake ai na warke”Ta fad’a a ranta.
“How are you feeling now?” Ya tambayeta.
“I’m fine” Ta amsa kamar bata so.
Daga yadda ta amsa ya gano bata son maganar.”Any story? tell me about it how does it started? “
Tasan dama za’a rina,bade yaga taji sau’ki ba.Sake murtuke fuska tayi ta kauda kai.
“Come on,it started with stomach ache followed by….” Be ‘kare ba yayi shiru yana murmushi.
Ring!Ring! Wayarta tayi ‘kara ‘Aisha’Ta gani a screen.
“Hello”
“Hello Laila,ya jikinki?”
“Da sau’ki”
“Ayya ,kiyi ha’kuri shirmen mey aiki ne bata duba ba ta baki lalataccen abinci”
STORY CONTINUES BELOW

“Karki damu ba komai na samu sau’ki”
“Aha,Allah ya ‘kara sau’ki se munzo”
“Nagode” Daga haka sukai sallama.
Suna gama wayar tayi dialing number Mami har lokacin Amjad be fita ba,ita kuwa tayi hakane dan karya dameta.Bayan ta gaisa da Mami ta shiga labarta mata abinda ya faru harda ‘kara langa’be murya.”Mami ruwa leda 2 fa aka ‘kara min”
“Toh Allah ya sawwa’ke”
“Mami su Maryam suzo”
“Har sai kin ro’ka? sarkin raki anjima sazo amma karki zaunar dasu”.
” Toh Mami ,mami dan Allah kiyi min tuwo”
“Tuwo? toh shikenan se sunzo” Daga haka sukai sallama.
Tana had’a ido dashi taga ya ta’be baki kamar yadda tayi.Dariya da kunya taji ta kawar da kanta.
“Mami,Mami ruwa..bla..bla” Ya kasa ‘karasa ‘karshen dan sunyi skipping daga kansa.
“Bade zaka fahimta ba” Ta fad’a a fili.
“Bade mey ba?” Taji ya fad’a.
Yadda ya iya had’a sentence d’inne yasa tayi mamaki ta d’ago tana kallonsa.
“Surprised?”
“I saved each an every word you’re saying”
“Toh ina ruwana”
“Zaki ga” Wani mamakinne ya sake kamata tana kallonsa sa’kalo.
Daga haka bata sake magana ba dan yanzu kuma ta soma shakkar fad’ar abinda ranta yaso.
Pillow ta janyo ta gyara kwanciyarta ta rufe idonta,so take taga ya fita.
“Sleep tight” Yana fad’ar haka ya fita yaja mata ‘kofar.
Yana fita ta bud’e idonta,wayarta ta d’akko ta shiga chat.
Su Maryam se wajen 2:30 pm suka zo,tana ganinsu ta mi’ke kamar ba itace mey shamo-shamo ba.Tuwon da suka kawo ta zuba a plate taci kayanta sauran ta ajje na dare.
Yau ‘yan mutucine akan Amjad ,dasu Maryam zasi tafi da kansa ya kaisu harda tsayawa a mall yayi musu ‘yan siyayyar biscuits da chocolates.
★★★
A kwana a tashi Laila har sun koma school, yau zata koma , 7:25am ta gama shirinta breakfast zatai ta tafi. Ta gama had’a sandwich d’inta da tea ga pancake d’inta tayi dede bakinta ,a tray ta jero ta kawo kan table ta ajje,tuna bata d’akko bag d’in ta ba ta hau sama.
Few minutes later ta dawo dinning d’in ganin mutum ya hakimce yana sambad’ar abinci yasa ta tsaya kallo.Ko a jikinsa hankali kwance yana ta enjoying breakfast d’insa,tana kallonsa yana kallonta bako kunya.
“What?” Ya tambayeta bayan ya dire cup d’in shayin.
Kallan abincin tayi sanna ta komo kansa.”My meal”
“Yours? Where is mine?”
“I didn’t cook for you”
“Why?”
“Because I always prepare a Nasty food”
“Exactly,you gerrit,that’s why I wanna show you how to make your food yummy”Yana maganar ya goge bakinsa da tissue ya tashi.
” Oh I remembered, I will drive you to school you need to hurry up I’m almost late”
“Ni bazaka kaini ba,sena ma yi abinci”
STORY CONTINUES BELOW

“Who will eat the rest of this?” Yayi nuni da pan cake a plate.
“Left over d’in zanci?”
“What wrong with that?”
“Bazan iya ci ba”
“Bazan ..iya …ci ba” Ya maimaita abinda ta fad’a.
Tana kallo ya ciro wani d’an ‘karamin note book a pocket d’insa tare da pen,gani tayi yana rubutu amma bata ga meya rubuta ba.
” Read”Ya nuna mata note d’in.”Bazan iya ci ba”Taga an rubuta a jiki.”I’m gonna search it’s translation in English”
“Ka wahala”
Wani rubutun taga ya sake yi,exactly abinda ta gama fad’a ya rubuta.
“I think this wiil work” Ya fad’a tare da mayar dashi aljihun suit d’in.
“Let’s go”
“I’m not ready”
“Then I will wait for you”
Tana jin haushi ta koma kitchen ta soya egg ta had’a da slide bread,a kitchen ma tayi breakfast d’in yana dinning yana jiranta har ta fita.Se bayan sun shiga mota ya tambayeta.”Where is your niqab?”
Shaf ta mance ta baroshi kan kujera dinning aiko ta fita ta d’akko abinta,tana shigowa ta d’aura kayanta.
“You’re pretty enough to cover your face right?”
“Yes” Ta amsa.
“I see”
“Mrs beautiful, pretty, cutiee, flower,diamond, gold, silver…and rest”
“Who was your first love? I asked again”
Da kamar bazatai magana ba kuma setayi.”Safwan”Ta kama suna .
Be ta’ba tunanin zeji haushi ba amma jin ta fad’i suna yaji ransa ya ‘bace,daurewa yayi ya cigaba da magana.
“Nice name,tell me about him,show me his picture?”
D’age niqab d’in fuskarta tayi dan ta tanadi abinda zata fad’a kuma so take yaga yanayin expression d’in fuskarta.
“He is handsome,very kind person he is so sweet, shining like a diamond”. Yanda take maganar har fuskarta tana nuna farinciki.
” The first time I set my eyes on him I felt like I’m in Paradise,the first time I heard his voice …ohh he’s the beat of my heart I so much eternally love h…”Ai bebar ‘karshen ‘im’ d’in ya fito ba yaci burki.
“Ya Allah” Ya daki steering.
“Are you alright?” Ta tambaya cikeda tsokana har tana le’ka fuskarsa.
“Yes,I’m fine ,fine!” Yayi ‘ko’karin fad’a yana ‘ka’kalo murmushi.
“Ok,so I should continue?”
“Laila is ok,time to stay quite, phem!” Ya had’e lips d’inshi da yatsa alamar shiru.
Kai ta kad’a tare da yin murmushi.”Gobe ka sake tambayata”
Har yakaita school be sake magana ba,ita kuwa dad’i taji ta huta da tambayoyinsa.
Tana sauka ta had’u da Aliya da itama yanzun mijinta ya sauketa.
“Babyn mijinta irin wannan fresh haka” Aliya ta fad’a lokacin da Laila ta d’age niqab d’in.
“Mtchww! daga dawowa har kin fara”
“Gani nayi kinyi fresh ko kema?”
“Sede ke d’in”
“Gashi kuwa ni ina ruwana” Aliya ta fad’a.
“Tohhh sekice kece mey abu”Laila ta fad’a tana kallon cikin Aliya daya tasa.
Haka suka cigaba da hirarsu kafin a shiga lecture,a class malami yana explanation amma gaba d’aya hankalinta baya gurin.Tuna d’azu tayi -tayi tana tambayar zuciyarta koh da gasken yaji haushi har cikin ransa?
Seda Aliya ta ta’bota tukun ta dawo daga tunanin data tafi.Malamin taga yayi pointing d’in ta ,tana mi’kewa yayi mata tambaya akan abinda ake tayi tsilli-tsilli da ido se Aliya ce ta rad’a mata ta fad’a.
Da aka fito Aliya tayi ta mata tsiya wai tunanin Babynta take,lecture d’aya suka ‘kara wajen 3:30pm suka tafi gida.Bata yi zaton ganin motarsa a yanzu ba dan a tunaninta se anjima ze komo gida.D’akinta ta wuce seda ta watsa ruwa ta fita ‘kasa, kitchen ta shiga ta dafa couscous da miyan cabbage.Tana dinning Sega Amjad ya sakko,da beyi niyyan zuwa table d’in ba amma ganin tana wajen yaje.
” Where is mine?”Yayi nuni da abincin.
“You don’t like a Nasty food”
Kamar be jita ba ya bud’e food warmer d’in ya rife tare da ta’be baki.
“It smells bad”
Dama ta ‘koshi ta tattare plate d’in ta wuce kitchen.
“I heard about him but you didn’t show me his picture” Tajiyo muryarsa.
Shiru tayi masa ta cigaba da d’auraye plate d’in hannunta.
“I’m talking to you”
Nan ma batace komai ba,wani takaici ne ya lilli’besa dan zuciyarsa tana fad’a masa gaskene abinda ta fad’a d’azu.’karasawa yayi har inda take bata zata ba taji d’imin mutum a bayanta.A firgice ta juya amma ko tsaiwar arzi’ki bazata iya ba dan distance d’insu kad’an ne.Zuciyarta tuni bugunta ya ‘karu ,ta manne da jikin drawer d’in kamar zata shige ciki.
“Is’t true what you said earlier?”
“Move back first” Tayi ‘ko’karin fad’a.
“I wanna see it through your eyes” Ya sake matsawa kusa ,kallon nashi ma yanzu ta dena ta rife idanuwanta gam zuciyarta kamar zata fito,gashi ko mayafi bata yafa ba riga da skirt ne na atamfa tayi d’auri mey steps.
A hankali ya rage tsahonsa fuskarsa ba alamar wasa ya d’ora hannunsa all side na drawer d’in har yatsansa na ta’ba hannunta data dafe drawer.
***
Tap d’in sink dake zuba ya mi’ka hannu ya kashe sannan yaja baya.Laila har lokacin idanuwanta a rufe suke zuciyarta bata fasa bugawa ba,a hankali ta rage jin d’umin mutum a jikinta,da ‘kyar ta soma bud’e idanuwanta gani tayi ba kowa a kitchen d’in.Tunani ta shiga yi ko dama ba gaske bane,data dubi sink d’in taga tap d’in ya dena zuba.Da sauri-sauri ta ‘karasa d’auraye plates d’in ta koma d’aki,har lokacin bata dena jin tsoro ba gani take kamar zata sake ganinsa.+
Shi kuwa daya koma d’aki murmushi ya shiga yi ,be zacci tsoronta yakai haka ba shikam yanzu ya samu damar hanata fad’ar abinda ranta yaso.Phone d’insa ya d’auko yayi plugging earphone tare da turning on song(Can I have this dance:high school musical).
🎵Take my hand, take a breath
Pull me close and take one step🎵
Keep your eyes locked to mine 🎵
And let the music be your guide Won’t you promise me? (Now won’t you promise me?)🎵
That you’ll never forget (We’ll keep dancing) 🎵
To keep dancing wherever we go next🎵
It’s like catching lightning The chances of finding someone like you It’s one in a million,🎵
the chances to feeling The way we do…..🎵
Ba’ai nisa ba ya katse wa’kar dan ta soma tuna masa da Rosie,dan itama bata da wa’ka kamarta asali ma ita tasa masa son wa’kar dan wasu lokutan tare suke jin wa’kar suna bi.
★★★
Laila har 9pm bata fito ba ‘kishir ruwa take ji amma ta kasa fitowa gudun kar wani abun ya sake faruwa.Wayarta ta d’auka ta hau Instagram taga Amjad mu’az started following you,profile d’inshi ta bud’e taga post kala-kala.Wani photo data gani seda tayi tsaki ganin ko riga besa ba showing his six packs ,daga shi se ¾.
“Se kace d’an arna”Ta fad’a tana scrolling taga wani photo nashi ta gani yana yaro sosai befi 9yrs ba dariya photon ya bata yanayin yadda yayi wani kalar soko ya cakumi teddy bear.Haka tayi ta bin sauran pics d’in wasu tare da su Mom wani friends, a haka har ta soma jin bacci daga baya ta ajje wayar tayi kwanciyarta.
Washegari da wuri tayi shirin makaranta ko breakfast bata yi ba ta fice se sauri take karya fito yace ze kaita.Seda taga ta hau d’an sahu hankalinta ya kwanta,lecture biyu kad’ai sukai amma Laila ta’ki tahowa gida,2pm lokacin masjid kawai taje bayan datai sallah ta kwanta bacci ya kwasheta.
4:09pm ta farka ,mamakine ya kamata ganin har tayi bacci me tsaho haka.Tashi tayi ta d’auro alwala tayi sallah,bata ankara ba taga garin yayi duhu sakamakon hadari daya had’u.Ba shiri ta tarkata handout d’inta ta zira a jaka ta fito,sanda ta hau napep har an fara iska mey ‘karfin gaske kafin ta isa gida ruwa ya sakko.Kafin ace mey nan da nan danan titi ya d’inke da abin hawa a hankali ake tu’kin ruwan se shigowa yake cikin napep d’in rabinta ta jike,ganin ta kusa ‘karasawa gida kawai ta sauka ta kama tafiya sauri-sauri ,tun daga nesa ta hango wani mota a ranta ta ayyana na Amjad ne aiko tana ‘karasowa ta ga shine yana ciki ya’ki fitowa gashi motar ta gagara tashi ya dad’e yana ta fama ganin ruwa ya sakko yasa ya shige ciki ya zuge glass rabi.Ta mirro d’in gaba ya hangota ,a tunaninsa ko zata tsaya amma yaga ta wuce kamar bata gane shi bane.Da kanshi ya fito daga motar dukda tsananin ruwan da ake.”Laila” Ya kira sunanta.
STORY CONTINUES BELOW

Tana jinsa yana kiranta amma tayi burus,sema ‘kara saurin tafiyarta da tayi.Da sauri yasha gabanta ya ri’ko hannunta.
“Laila I’m talking to you”
“What?”
Shiru yayi dan baida abin cewa.”Get inside the car,it’s raining heavily”
“No”
Tayi saurin matsar da hannunsa kan kafad’arta,sauri-sauri ta cigaba da tafiyarta.Ganin ba tsayawa zatai ba ya koma motar ya ciro umbrella ya biyota ,matsawa yayi kusa da ita ya bud’e umbrellan yayi musu rumfa.Ganin jikinta na gogar nashi ta matsa, kusan rabinta ruwa na shafa,kamar ‘kiftawar ido taji ya dafa kafad’arta har tana fad’owa jikinsa.”Stop misbehaving”
Ita ba abinda yake damunta kamar yadda hijab d’in ya manne a jikinta gashi rigar material ne a jikinta curve ya bayanna ,se jajjan hijab d’in take amma a banza.Suna shiga gida ta matsa daga jikinsa da sauri ta ‘karasa jikin ‘kofar ta ciro key ta bud’e, kafin ya shigo har ta haye sama.Tana ajje jakar ta fad’a bathroom,ruwa mey zafi tayi wanka dashi ta d’aura towel zata fito ta tuna bata shigo da wani hijab d’in ba gashi kayan data cire duk a ji’ke.Hakannan ta murd’a handle ta fito ta rufo ‘kofar toilet d’in,ganin mutum a tsaye yasa ta razana.Juyawa tayi da sauri tana kici-kicin bud’e ‘kofar bathroom ,kamar rufewa take sake yi ‘kofa ta’ki bud’uwa,haka ta gaji ta ‘kyale ‘kofar amma ta’ki waigawa ta kalli inda yake.
“Mey zeyi a d’akinnan inba neman masifa ba?”Ta fad’a a ranta.
” What are you waiting for?”
Ta’kowa yayi ya ‘karaso har inda take ya mi’ka mata Biro”You left it in my car?”
Ko waigowar arzi’ki ta kasa illa mi’ka hannunta da tayi ta kar’ba sede kuma bawai ya cika biro d’in bane duka, yana ri’ke da farko tana ri’ke da ‘kasan biron. Tunda ga sama har ‘kasa yake ta binta da kallo tana jin idonsa a kanta ta rasa inda zata saka kanta ji take kamar ta nutse a zuciyarta se zagin towel d’in take dan iya cinya yake ,biron ta sake masa ganin ya’ki cikawa shima sakinsa yayi ya fad’i ‘kasa.
“Pick it up”Taji ya fad’a cikin tattausan harshe.
” Innalilahi”Ta fad’a a ranta.
“I ca..” Bata ‘kare ba ta tsaya da maganar dan kar ayi irin ta jiya batasan ya za’a ‘kare ba.
A sanyaye ta waiwayo tana dafe da towel d’in ta dur’kusa ta d’auka jelar gashinta dake ta kwanta gadan bayanta.Tana d’aukan biron bata ko tsaya a ko ina ba se wajen wardrobe cikin sauri ta ciro hijab ta zira,yana kallonta ta gama zire-zirenta be sake cewa komai ba ya fita daga d’akin.
“Yanzu akan biro shine za’a biyoni har d’aki mtcww!”
Tun bayan komawarsa d’akin ba abinda ke yawo a kansa irin image d’in Laila a yanayin daya ganta d’azu,da yayi ‘ko’karin kauda tunaninta seya kasa ,laptop d’insa ya d’akko ya soma dann-danne amma sam hankalinsa ba anan yake ba faga baya ya d’auki waya ya soma game a thinking of Laila,pillow ya d’ora kansa ya kwanta ko zeyi bacci.Ko Rosie da take sak English wears matsastsu dasu mini skirt be ta’ba jin abu a kanta ba kamar irin Laila.”She is pretty”Yaji zuciyarsa ta fad’a.
Laila kuwa bayan ta gama shirinta cikin atamfa riga da skirt ta d’aura d’ankwalinta,lokacin ruwan ma ya tsaya yamma tayi li’kis maghrib ya kusa.Windown d’akin ta bud’e tana kallon yadda flower plants sukai kore shar ga furannnin sunyi fresh sosai view d’in ya birgeta jitake kamar ta sakko sede kuma tana gudun had’uwarsu.Seda taji anyi kiran sallah ta zuge windown d’in tayo alwala itama.Bayan ta idar da sallah kuwa a jakarta ta d’akko meatpie data siya a school gida biyu ta soma ci dan yunwa ta isheta,taci abu kuma ba ruwa.
STORY CONTINUES BELOW

Shawara tayi-tayi daga ‘karshe de ta sakko ‘kasa,cikin sand’a ta shiga kitchen da sauri ta d’akko bottle d’in ruwan ta fito zata hau sama taji ‘karar tsawa ,harda dur’kusawa kamar wacce za’a kama.”Terrified”
Bata kalli inda take tsammanin daga nan yake ba tayi sauri ta hau sama,tana shiga d’akinta ta rufo ,ba ita ta sake fitowa ba se washegari.
Yau d’inma da sauri ta yi shirinta sede tana sakkowa ‘kasa ta ganshi a dinning yana shan tea se biscuit a da’n plate.Da kamar ta koma kuma ta daure ta wuce kitchen.”Morning “Taji ya fad’a.
Ko amsawa kasa yi tayi na d’aya tasan ita bata ta’ba gaisheshi ba na biyu bata sani ba ko d’aya daga cikin abunsa ne na tsokana.A kitchen d’in ma ta rasa mey zata dafa,dankali ta soya tayi ‘yar chicken sauce.Sauri tayi taci gudun kar ayi ta d’ayan ranar yasa koh wanke plates d’in bata tsaya yi ba.
Tana fitowa ya bar wajen,direct ta koma d’aki ta d’akko jakarta,cikin ‘kan’kanin lokaci ta fito daga gidan.Yana komawa d’aki ya d’akko key d’in motarsa,ganin bata kitchen yasan har ta fice.Ba ‘bata lokaci ya fita,a hanya ya tarar da ita tana tafiya,horn yayi tayi mata amma ta’ki juyowa,sede ya fito yayi mata magana tukun ta shiga.
” Ko yaushe aka gyara motar?”Ta tambayi kanta.
“Oho” Ta fad’a.
Shiru bame cewa komai har suka isa makarantar,tana fita ta rufo ‘kofar ta kama hanya ta wuce,be ja motarsa ba har seda tayi nisa yana kallonta kan daga bisani ya tafi.
Tunda ya shiga office ko aikin kiriki ya kasa banda tunanin Laila ,tun farkon aurensu zuwa wannan lokacin yayita tunawa.Shi kad’ai yana murmushi,ana knock a ‘kofar office d’insa amma hankalinsa baya gun.
“Sir,sir!” Yajiyo ana kiransa.
Se lokacin ya farga ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.
2:30pm nayi ya tashi daga aiki be tsaya ko ina ba se school d’insu Laila. Da farko yayi niyyar kiranta daga baya kuma ya fasa dan yasan zata iya ‘kin fitowa.Haka ya zauna a mota zaman jira kad’an-kad’an yana ganin students na fitowa amma be hangota ba ya kwashe kusan 1hr 20min kafin ya hangota tana tahowa bakin titi.Motarsa ya ‘kara yin gaba da ita dede inda take a tsaye ya sauke glass d’in motar.Ta kalleshi sarai amma seta matsa gefe,tana jin wasu cikin ‘yan mata a gurin suna gulmarsa.
“Yana shigowa school d’innan,ko d’azu naga motarsa”.
“Wannan za’a ga kyawawan ‘ya’ya”
” Kamar balarabe ne naga” D’ayar tace”A’a bature ne.
“Ke india ne bakiga irin gashinsa ba ai turawa farin gashi garesu”
Ita dariya ma suka so bata dan yadda taga hankalinsu yana kanshi se kallon motar suke kamar saje su shiga.
Basu suka rud’e ba seda suka ga ya fito,basu kad’ai ba hatta wasu mata dake gefe seda suka kalleshi.Tana ganin tahowarsa ta gefen ido ta’ki juyo wa.”Laila come on get into the car”Taji ya fad’a cikin tattausan harshe.
Gefen fuskarta ta waigo tayi masa wani kallon banza,ita bata so taga yana shishshige mata”Nina ce kazo d’aukana”Ta fad’a ‘kasa-‘kasa dan beji mey tace ba.
Badan kar ta yarfa shi cikin mutane ba da bazata bishi ba,a hankali ta taka wajen motar.Kallo suka bita dashi suna mamaki.”Wace wannan d’in?”
“Matarsa…”
“A’ina d’in”
“Matar aure ce ai” Wata daga cikinsu ta fad’a.
Da ido suka bi motar da kallo har suka bar gun suna mamaki.
“How was the lectures?”
Banza tayi dashi bata amsa ba kamar bata ji ba tama kawar dakai tana kallon window.
“Are you hungry?” Ya sake mata wata tambayar.
“A’a” Ta bashi amsa a ciki ciki.
Ganin ba son magana take ba shima yai shiru a tunaninsa ko stress ne.Suna komawa gida ya sake fita cikin ‘yan mintina se gashi ya dawo da leda a hannunsa.
“Knock! Knock! Taji an bugo ‘kofar d’akinta ko wankan ma bata shiga ba,hijab d’inta ta zira tukun ta bud’e.Ledar ya mi’ka mata fuskarsa a sake ita kuwa ko d’an sakin fuskar ta’ki yi,hannu tasa ta kar’ba batace komai ba ta koma ciki ta ajje kan drawer, da ya tsaya kamar zeyi wata maganar se kuma yayi shiru ya tafi d’akinsa.
” Better “Ta fad’a.
Se bayan ta fito daga bathroom ta duba ledar,burger ne da baguettes se sauce da tana bud’ewa ta ta’be baki “‘Karni ma take Allah kad’ai yasan wacce ta dafa,Allah yasa ba miyar ‘kwad’o bace dan shima baze rasa ci ba ko kuma ma tsutsa”
Koda ta gama shirinta bata kalli abincin ba dan a ‘koshe take ,haka ta ‘karachi zamanta har se bayan isha’i ta janyo ledar ,burger d’in kawai taci ta ajje saura baguettes d’in kuma ta sauka ‘kasa a kitchen ta ajje, miyar kuma ta ajje a fridge.Cock da bottle of water ta d’auka ta komo ,tana hawa bene shikuma yana sakkowa daga d’aki sukai karo har kayan hannunta suna fad’uwa,kusan shine sila tunda shine da sauri-sauri yake sakkowa.
Nan take ta dur’kusa tana dafe ‘kafarta,ha’kuri ya shiga bata “I’m sorry ,I’m so sorry Laila”.
” Ba wani sorry kana sani”Ta fad’a tana ri’ke da ‘kafar.
Cock d’in ta kalla daya gangara ‘kasa dan shi take tunanin ya fad’o mata a ‘kafar.Mi‘kewa tayi tsaye ta fara tafiya amma ta ‘kasa take ‘kafar se d’ingisawa take.”Let me help you”Ya taho da shirin ri’ke hannunta ya d’ora a kafad’a aiko tayi saurin matsawa garin haka ta take ‘kafar.”Aghh!”Ta tsala ‘kara.
Bata ankare ba taji an raba ta da ‘kasa anyi mata d’aukan amarya, tuni ta shiga wutsul -wutsul tana d’uma masa duka a kafad’a.”Mami!”Ta hau kiran sunan Mami.
Har seda ya kaita d’akinta sannan ya direta kan gadon.”Stubborn “.Ya fad’a.
“Nan da nan idanuwanta sun cika da ‘kwalla seda taga ya sauketa a d’akinta ta d’an nutsu.” You can leave now”
“You’re sending me away,what did you think I’m doing? Sometimes you’re crazy”
Fita yayi daga d’akin bayan ‘yan minti kad’an ya dawo da man zafi a hannunsa.Jira take taga abinda yake ‘ko’karin yi,tana gani ya zauna gefen gadon tare da ri’ke ‘kafar ta matsar da ‘kafar.”Na iya shafawa”
Duk da be fahimci abinda ta fad’a ba ganin ta matsar da ‘kafarta ya mi’ka mata man “Rub it”.
Kar’ba tayi cikin sanyin jiki ta bud’e man ta soma shafawa a ‘kafar a hankali sekace mey tallan mai.Ta sakankance taga ya wafce man ya soma shafa mata yana matsa ‘kafar,hannunsa tasa tana ‘ko’karin janye nasa hannu amma ta kasa sema ri’ke hannayenta biyu da yayi waje guda ta kasa ku’bucewa ,haka tayi ta raki har seda ya gama.
” Toh sake min hannun tunda ka gama”
“Mey kika fad’a?” Taji yayi magana.
“Tunda ka iya yaran ai zaka sani”
“I can speak hausa for the whole entire day”Yadda yayi pronouncing d’in hausar kamar like ” Hosa”
“Ok,start”
“Ok,yanzu” Ya fad’a yana murmushi.
Itama murmushin tayi tana kallon arm d’insa data buga d’azu har wajen yayi ja kasancewar singlet ce a jikinsa.Shikuwa murmushin datai ne yasa ya kasa dena kallonta dan ba ‘karamin kyau tayi ba.Saurin kawar da ido tayi ganin ita yake kallo,wayarta dake gefe ta d’auka ta hau dubawa dukda ba abinda take da ita.
“Na fita?”Taji ya tambaya.
“Eh”Ta amsa kanta a sunkuye.
” Ok,I’m going but you have to answer my questions “
“Questions”.
“Yes”.
Kai kawai ta girgiza tana tunanin irin tambayar da zeyi mata.”Do you have feelings on me ? don’t lie”
Sam batayi tunanin wannan tambayar zeyi mata ba duk da bata rasa amsar fad’a masa ba sede kuma tana mamakin dalilinsa na tambayar.Ya tsireta da ido kawai jiran amsarta yake.
“No” Ta amsa ba tare da ta bari sun had’a ido ba.
“No” Ya maimaita abinda ta fad’a.
“Ok,let’s assume I love you? Will you love me back?”
“No”
“Why?”
“Because I don’t love you”
“Your heart is for only one person?”
“I want to sleep” Ta fad’a tana janyo blanket d’in.
STORY CONTINUES BELOW

“Are yo sleeping like this?”Ganin ba sleeping dress bane a jikinta.
” Uhm”Ta rufe kanta.
Tashi yayi yazo fita ya kashe wutar d’akin sannan yaja ‘kofar,tana jin fitarsa ta bud’e kanta, tambayoyin da yayi mata ta shiga yi ,seda ta jima kafin bacci ya d’auketa.
12:13am ya farka daga bacci ,da tunanin Laila a ransa ya farka.Drawer side lamp ya kunna ya tashi zaune agogon d’akin ya kalla yaga 12am,mi’kewa yayi tsaye ya bud’e ‘kofarsa ya fita zuwa d’akinta,yana murd’a handle d’in yaga a bud’e ‘kofar ma take.Tana ta baccinta yau ma tafin hannunta na kan fuskarta kamar rannan hakan yasa shi yin murmushi yanzu ya fahimci d’abi’arta ce haka.A hankali ya d’akko stool d’in mirrorn d’akin ya ajje opposite da ita ya zauna se ‘kare mata kallo yake,tuna ko pic d’inta bashida yasa ya koma d’akinsa ya d’akko wayarsa ya komo ,hannun data kare fuskarta dashi ya matsar yadda fuskarta zata fito,pictures kala-kala yayi ta d’auka har kusan 12:40am tukun ya koma d’akinsa.
★★★
Kwanaki suna sake yin nisa ,Laila lecture d’insu yayi nisa kullum Amjad ne yake kaita school baya ta’ba bari ta tafi da kanta,hatta dawowa gida wasu lokutan shi yake d’akkota hatta saba ma yanzu ta dena gudun.Haka ta ‘bangaren abinci ma inde tayi girki zeci inba wai yaga besan irin abincin ba.A kullum Laila sake shiga ransa take duk wani abu da tayi birgeshi take haka idan yana office yata kallon photos nata kenan ,tunanin ta ba ‘karamin d’auke masa hankula yake ba daga al’amuransa na yau da kullum ana meeting seya tsinci kanshi yana tunaninta wanin sa’in harse P.A d’insa ya masa magana.
Yau ma bayan ya tashi daga aiki ya biya mall ‘yan siyayya,wani henna ya gani wanda ya tuna masa da ‘kunshin da Laila tayi kwanakin baya,jiyai yanaso yaga ta sake yi dan haka ya siya mata.
Yana zuwa school d’insu tana fitowa,suna tafiya yana mata tambayoyi da suka shafi school d’inta rabi maganar da yaran hausa yake dan yanzu ya fara iya hausa sosai sede wajen pronouncing ne ake samun kura-kurai , kad’an -kad’an take bashi amsa dan ita har yanzu ta’ki sakin jiki dashi.Seda suka isa gida tazo fita ya kira sunanta.”Laila”
Tana juyowa taga ya mi’ko mata package na henna d’in.Seda ta ‘karewa lallen kallo sannan ta dawo da kallonta kansa daga bisani kuma ta kar’ba ba ko godiya tayi ficewarta.
Tana shiga d’aki ta bud’e drawer ta ajje ciki ta rufe ta wuce bathroom tana fitowa bayan ta shirya tayi sallahr asr.
Knock!Knock! Taji bugun ‘kofarta.Dama hijab d’in ta na jikinta ta tashi ta bud’e,yana tsaye bakin ‘kofar fuskarsa d’auke da murmushi.
“I just wanna inform you that I will take a trip tomorrow morning”
Kai kawai ta kad’a a ranta dad’i kamar ta ziba ruwa a ‘kasa tasha.
“Alhamdulillah ” Ta fad’a a ranta.
Dama gobe Saturday bikin Bahijja ‘kawarta,tasan idan yana nan ba yadda za’ai ta kwana a gida yanzu kuwa setai amfani da wannan damar.
Yayi tunanin zega ta damu amma yaga sa’banin hakan ,du seyaji jikinsa yayi sanyi,gwiwa ba ‘kwari ya koma d’akinsa.
Laila da farinciki ta kwana a ranta da sassafe ta soma had’a kayanta,dan tsabar farinciki kota kan breakfast bata biba,se wajen 9:30am ta sakko ‘kasa a kan dinning ta hangi wata takarda dake ninke.Har zata shige ta ta dawo, tana bud’ewa taga short note.
I’m sorry for leaving without saying goodbye, I don’t wanna wake you up.
Amjad
Duk da ba wani damuwa tayi ba amma seda taji wani iri dan tayi tunanin yana d’aki,ninke ta tayi ta ajje kan table d’in sannan ta shiga kitchen had’a breakfast.
STORY CONTINUES BELOW

Cikin azar’ba’bi tayi sauri tayi breakfast tana kammalawa ta koma d’aki ta shirya,kit d’in data sa kayanta ta d’auka ta fito daga gidan ,a hanya ta kira Maryam ta fad’a mata tana tahowa.Laila tana isa gida ta tafi gidan ‘kunshi aka tsantsara mata ta dawo gida.
“Gan d’oki” Mami ta fad’a.
“Nice fa babbar ‘kawa Mami”
“Da haka nan aka ce kiyi ‘kunshi da tuni kina nan kina zun’buro baki amma dayake kin sa kanki har rawar jiki kike”
“Kwana nawa zeyi?”
“Sati d’aya” Tayi ‘karya.
“Abin nema ya samu”
Kallon Mami kawai tayi a ranta ta san ‘karya take.Wajajen 4:30pm ta tsantsara kwalliyarta ta rangad’a d’auri ta yafa gyale d’an ‘karami ta fito.
“Inde a haka zakije kuwa sede bazaki fita ba,haka kike fita mijin naki ya barki?”
“Mami biki ne fa?”
“Koh meye zaki wani d’ora mayafi a wuya ke bakisan babbancinki da ‘yan mata ba?”
Bata fita ba seda ta koma ta sauya mayafin ,ita kad’ai ko ‘yan rakiya ma bata d’auka ba.
7:30pm ta komo gida Mami kam tayi ta mata fad’a tana kallo Amjad yana kiranta a waya amma ta’ki d’auka,daga baya taga text nashi.
Hi,how was the day? Hope you’re doing good.
“Ina ruwanka?” Ta fad’a a fili tayi cilli da wayar.
“Komai ace aure..aure “
Tunda ta cillar da wayar bata sake dubata ba tayi baccinta,Amjad kuwa baida tunanin daya wuce nata ya matsu yaji muryarta yana ta jiran reply amma shiru.Ko washegari ma beyi zuciya ba da safe seda ya kirawo ganin bata d’aga ba yayi mata message.
Morning hope you’re doing good?
Laila ba ita taga message d’in ba se to 10am shima ‘kin reply tayi ta maida wayar ta ajje.Dan saboda Mami ta barta taje yinin bikin seta d’auki Fauzan suka je tare da ita aka kai amarya sannan ta komo gida.
Messages da missed call ba adadi ta tarar a wayarta banyan ta komo gida.
“D’azu kuwa Amjad ya kirani ” Taji Mami ta fad’a.
“D’azu” Ta maimata tana zare ido a ranta tana fad’in Allah yasa Mami bata gani ‘karya nayi ba.
“Mami se kuka gaisa?” Ta tambaya tana neman ‘karin bayani.
“Ehyi naji yanzu ma ai Hausa ta shiga bakinsa ba kamar da ba”
“Uhm” Ta fad’a zuciyarta na raya nata Mami batasan komai akai ba.
“Ashe ma gobe ze dawo” Taji Mami ta fad’a.
Ita a tunaninta ze iya yin sati d’aya ,nan take murnarta ta koma ciki.
“Uhm” Ta fad’a a ciki.
“Toh gobe seki koma da safe aiko”
STORY CONTINUES BELOW

Nan ma ta amsa da “Uhm”.
Haka ta kwanta tana jin haushi plan d’inta ya rushe kwana biyun datai d’in ma bata gode ba.Washegari da safe tayi ta la’kai-la’kai ta gaji da baccin safen ma amma ta’ki tashi seda taga dama kafin tayi wankan ma tayi ta la’kai-la’kai haka breakfast ma, ba ita ta tafi ba se wajen 1pm,tan d’an sahu taji shigowar text.
I’m on my way back home
” Naji”Ta fad’a.
Tana shiga gida tayi zamanta a d’aki ko kitchen bata kalla ba balle tayi tunanin wani abu shi girki.Tana yin sallah ta kwanta bacci, bama baccin take ji ba ta dole kawai tayi forcing kanta tayi baccin.
3:30pm ‘karar doorbell ya tasheta daga bacci,seda ta d’auka mayafi ta yafa dan ta ayyana shine ya dawo.Fuakarsa d’auke da murmushi yake kallonta amma ita kuwa…
Bata tsaya ya shigo ba ta komo ciki.”Laila, you don’t like me here?”Ya fad’a bayan ya shigo.
Shiru tayi bata amsa ba kuma bata cigaba da tafiyar ba haka bata juyo ba.
“Are you mad at me?”
“No I’m not” Ta amsa sannan ta hau sama.
Shide ya rasa gane kanta the more yana showing mata kindness the more tana gudun sa besan dalili ba.Hakannan ya wuce d’akinsa ya watsa ruwa ,daga shi se singlet ya sakko ‘kasa neman abinda zeci dan yunwa yake ji.
Babu wani alamar girki daya gani,’karshe se ‘bigewa yayi da shan cornflakes,ya fito daga kitchen d’in ya had’u da Laila.Yanzu ba mayafin daga ita se doguwar riga na material red colour,’kunshin hannunta ya yi rad’au a fatarta,idanunsa basu sauka a ko ina ba se hannunta.Ba ‘karamin dad’i yaji ba ganin tayi ‘kunshi,a hankali ya taka zuwa inda take.
“Beautiful, I like it” Ya fad’a lokacin ya dawo da kallonsa kan Laila.
Hannayen nata ta ‘boye a bayanta tana sunkui da kai.Batayi aune ba taji ya ri’ko hannayenta biyu kamar yarinya,duka biyun ya d’ago dasu kusa da face d’inshi ta rasa ma abinda zatai illa tsayawa kallan ikon Allah.
“Your hands always look good” Kamar ‘kiftawar ido taga yayi kissing hannayen ta tsaya uwa gunki,seda hankalinta ya dawo jikinta tayi saurin ‘kwatar hannun ta koma d’aki da sauri ta barshi a tsaye ya rasa ma mey zeyi sam ya kasa controlling kansa shikansa besan yadda akai haka ta faru ba.
Tana shiga d’aki tasa key ta rufe,hannayen nata tayi ta kallo tana tinawa.
Da’kyar ta iya tashi yin sallahr asr dan tsabar hankalinta ya kasa kwanciya se recalling take.Yunwa take ji amma ta kasa sakkowa kitchen, har bayan maghrib se shawara take daga ‘karshe de ha’kura tayi ta kwanta a haka yunwa na addabarta.
Washegari 8:12am ya gama shirin office saboda makarar da yayi ko tunanin breakfast ma beba ,koda ya sakko ‘kasa yaga be ganta ba.Haka ya hau bene yayi knocking d’akinta,tana zaune dama ba zuwa zatai ba yau.
“Laila” Ya kirata.
Da farko ‘kin amsawa tayi se a karo na biyu ta amsa .
“Are you not going to school today?”
“Yes” Ta amsa daga ciki ta’ki tasowa ma daga kan gadon balle ta bud’e ‘kofa.
Jin haka yasa ya kama hanya ya sauka,yau duk seya ji ba dad’i fitar kasancewar ba ita.Yana driving kusan rabin hankalinsa baya gurin,ya hau gadar sama yana driving be lura ba da wuri sega mey d’an sahu ya biyo one way garin kaucewa mey napep d’in motarsa ta daki gefen gadar ta fad’a ‘kasa,upside down ta sauka ,tayi mugun chanja kamanni,mey d’an sahu ya daki gini, lokaci guda jama’a aka hau salati a take waje ya d’inke da mutane.
Thank you for your warm support sister,Amjad fans kuma ina godiya ,ana tare✌
Mey d’an sahun da aka yi ‘ko’karin ciro shi daga d’an sahun aka ga ko numfashi bayayi ,kwance aka ajje shi gefe,daga ‘kasan gada kuwa mutane uku ne suka shiga kici kicin bud’e ‘kofar motar amma abu ya gagara ,seda ambulance suka ‘karaso suka ciro Amjad da ‘kyar sakamakon belt dake ma’kale a jikinsa, jini ya wanke fuskarsa haka aka sanya shi a mota a sheme.
★★★
2hrs later,tana d’aki tana duba handout wayarta tayi ringing,ganin Canada jikin screen ta’ki picking.Sau biyu ana kira bata d’aga ba se ana uku.”Hello”.Cikeda ‘kosawa.
Jin murya daban bana Amjad ba yasa ta gyara zama.Tana jin abinda aka fad’a ta d’ayan ‘bangaren ta saki wayar kan gado.
Ta rasa abinda zatai,wayar ta d’auka ta sake kallan call d’in.”Amjad “Ta furta a tsorace.Tafi 10min kafin daga baya ta d’au waya ta kira Mami.
” Innalilahi wa innailaihirraji’un”Mami ta fad’a.
“Kina asibitin?” Mami ta tambaya cikin rud’ani.
“A’a”Ta amsa feeling guilty.
” Mey kika zauna yi da baza ki tafi ba?”
“Zan tafi yanzu” Ta fad’a.
“Toh nima ina tahowa”.
Mami kafin ta tafi seda taje gidan Kawu Yunus ta fad’a masa halin da ake ciki,tare suka tafi asibitin kusan tare suka isa da Laila, Kawu Yunus ne ya kira Dad ya sanar masa.A gabansu aka shiga dashi theater room hankalinsu yayi mugun tashi dan yanayin da suka tsince shi.8:15pm aka fito dashi daga nan aka kaishi d’akin kwanciya,suna kan bench ko d’akin basu samu shiga se bayan doctor ya fita daga d’akin,Mami da Kawu suka shiga abin tausayi hannunsa yasha plaster sakamakon karaya se kanshi an zagaye masa da bandage, ga ‘karin jini da ake masa.
” Allah ya baka lafiya”
“Ameen” Mami ta amsa cikin nuna jimami.
Kawu Yunus se can dare ya tafi ya bar Mami da Laila data kasa shigowa tana waje kan bench itama daga baya Mami fitowa tayi ta zauna kan bench d’in.
Mom kuwa basu san mey ake ciki ba se ji sukai Dad yasa su shirin tahowa Nigeria da suka tambayesa dalili ya’ki fad’a musu.Koda ta kira Amjad d’in ma ta fad’a masa suna zuwa taji wayar a kashe.
Washegari 9pm suna Nigeria, Mom tunda taga an shigo asibiti jikinta yayi sanyi.”Tell me what’s going on?”
“It’s Amjad…”
“Mey ya sameshi ? What happened to my son?”
“He had an accident”
Dukansu ba wanda be firgita ba,cikin rashin ha’kuri driver na parking ta fita a motar Dad yana kiranta amma ta’ki tsayawa,da ‘kyar ya samu ta tsaya ganin ba sanin d’akin tai ba.Seda suka kira Mami ta fad’a musu numbern room d’in.Cikin rud’ani suka ‘karasa ,Laila tana zaune kan bench tagansu tsidik cikin hanzari suka shiga ita de ta bisu da kallo dan har lokacin ta’ki shiga d’akin.
Har yanzu yana kwance same position ko motsi beyi ba,Mami da Zakia tuni suka fara tsiyayar hawaye.
“Amjad” Ta ‘karasa gefen gadon.
Hannunta ta d’ora kan gashin kansa tana shafawa.
“My child”
Suna tsaye a kansa Mami ta shigo d’akin,bayan sun gaisa suka jajantawa juna Mami se bawa Mom ha’kuri take amma ta’ki dena sharar hawaye.
STORY CONTINUES BELOW

“Ina Laila” Mom tayi ‘ko’karin tambaya.
“Ta’ki shigowa tana waje” Mami ta amsa.
Mom da kanta ta fita wajenta ta tararda ita ta jingina da alama tayi nisa cikin tunani.”Laila”Ta kira sunanta.
Da sauri ta dawo daga tunanin data tsillima.”Mom,Ina yini”Ta gaisheta tana sunkui dakai.
Hannu tasa ta d’ora a kafad’arta.”Kiyi ha’kuri kinji,pray for him ze zamu sau’ki”
Kai kawai ta kad’a ba tare da ta d’ago ba,bata ankara ba taji Mom ta jawota jikinta kamar ‘yar baby tana shafa bayanta se bata ha’kuri take.Itade Laila tayi lif ita kad’ai tasan abinda take ji a ranta.
Sun dad’e a asibitin kamar baza su tafi ba Dad ya tashesu suka tafi,aka bar Mom se Laila Mami ma gida ta koma. Mom bata da buri irin taga ya farka,tafi 1hr tana zaune gefen gadon tana kallonsa.Laila data shigo d’akin ma daga can baya ta ta tsaya kamar bodyguard ta’ki zama.
Seda dare ya nisa ta zauna kan d’aya daga cikin kujerun d’akin,a hankali gyangyad’i ya fara d’aukanta daga bisani tayi bacci.Mom data kalleta du setaji tausayinta ya kamata.
★★★
Kullum se su Dad sunzo asibitin ,yawanci su suke kawo musu abinci sometimes Mami ,har anyi kwana shida amma Amjad be farka ba abin har ya soma damin Mom ko tashi ta shiga bathroom ba son yi take ba dan gani take kamar idan ta dawo bazata ganshi ba.Laila dan ma Allah yasa yawancin coaurses d’in duk anyi covering ba zuwa school take ba.
Yau ne ma da Aliya ta kirata take fad’a mata za’ai test shine taje school d’in tana yi ta komo asibitin.Ganin Dad ,Shaheed Zakia da Kawu duk suna d’akin yasa ta fito ta samu bench tayi zamanta,sun jima kafin su fito tayi bacci kan bench d’in lokacin 10pm yayi.
★★★
Gidansu Amjad taf yake da mutane,tana shigowa taga su Mami suna zaune kan carpet da sauran mutanen da ba sanin fuskokinsu tayi ba,Mom ta hanga daga kan step d’in bene gefenta Zakia se kuka take tana wata magana da baji take ba.Gwiwa a sanyaye ta ‘karasa inda suke bata yi musu magana ba ta haye saman ,’kofa ta gani daga gefen side d’inta a bud’e tana shiga taga gawa a kan makara cikin likafani ba kowa d’akin a tsorace ta ‘karasa tana zuwa taga fuskar a bud’e ganin Amjad ta saka ihu.
“Amjad!”Ta mi’ke firgit se zufa take ,asibitin yayi shiru se yanzu ta gane mafarki take,zuciyarta se dukan uku-uku take da sauri ta tashi ta bud’e ‘kofar d’akin ta shiga.
Mom ta gani tana bacci a zaune kan kujera,1:28pm agogon d’akin ya nuna.A hankali ta ‘karasa gadon tana kallonsa ko ‘kifta ido ta’kiyi,gefen gadon ta zauna tana ‘kare masa kallo mafarkin datai yana dawo mata ,zuciyarta ce ta raya mata what if da gaske mutuwa yayi.Tsoro ne ya hauta lokaci guda, hannunsa ta d’ago ta d’ora a tafin hannunta ‘kwallar dake ma’kale a idanuwanta ta zubo kuka sosai ta shiga yi mara sauti.Mom dede lokacin ta bud’e idanuwanta ta d’ora su kan Laila dake zaune gefen gadon ri’ke da hannunsa, ganin haka setayi murmurshi ta maida idanuwanta ta rife a zuciyarta tana mey jin dad’i ta wani ‘bangaren tana jin tausayin halin da Laila ta shiga.Tafi 20min a haka har lolacin bata sake masa hannunsa ba sede yanzu ta dena kukan,kamar gangan taji motsin yatsansa d’aya a hannunta.Tana kalla taga ba gangan bane ,a sanyaye ta mayar da hannunsa ta ajje ta mi’ke daga kan gadon zuciyarta kuwa wani irin farinciki mara misaltuwa ne ya ziyarce ta.Gefe ta samu wani kujerar ta zauna cikin ‘kan’kanin lokaci bacci ya saceta.
Yau ma da safe akai mata waya ake fad’a mata za’ai test dan haka ta shirya ta tafi school,har se to 12pm akai musu test d’in bayan nan kuma aka shiga lecture,hakannan ta samu ta zauna se 4pm tukun ta komo asibitin.Tana shiga ta tsaya daga ‘kofa ganin mutum ido biyu tayi yana magana da Mom amma bata san mey yake cewa ba.Ba wanda ya lura da shigowarta se Zakia ta kira sunanta,se lokacin kallo ya komo kanta Amjad yana daga kwance ya kallota a wahale idanunsa sun ‘kan’kance fuskarsa ta nuna alamar ramewa.
“Laila,I’m glad you’re back” Mom ta fad’a tana kallonta sannan ta komar da kallonta kan Amjad irin alamar ya farka d’innan take nuna mata.Kallo d’aya ta sake yi masa ta kawar da kanta,duk wani move datake yana kallonta gashi ko magana yaga ta’ki yi ,su Mom kuwa basu ma lura da hakan ba.Mami da sukai waya da Mom take sanar mata ya farfad’o tare da kawu suka zo suka duba shi daga nan ta sake tahowa da Laila wasu kayan nata.Se 9:30pm suka bar asibitin aka bar Mom da Laila,gabaki d’aya ta kasa sake wa fiye da da.
“Amjad you need to eat” Mom ta fad’a dan tun d’azu da rana dayaci chicken spaghetti be kuma cin wani abu ba.
“No I’m ok”
Fruit salad d’in ta samu ya sha kad’an,ita de Laila kallonsu kawai take duk abinda suke,jinta take a takure dama ta koma gida da yafi mata take fad’a a zuciyarta.Bayan yasha magani ya kwanta bacci daga baya Mom itama tayi,Laila ‘karshe se tunanin yadda zata ‘kare wannan zaman take.
Washegari 5:40am Mom ta tashi bayan tayi sallah Amjad ya farka ta taimaka masa yayi taimama yayi sallah,Laila dama bayin sallah zatai ba amma dukda haka takan tashi sede kuma yau baccinta tayi har se wajen 7:30am ta farka.Tana bud’e ido taga Mom tana gefen d’anta tasa abinci a gaba tana bashi yana ci da ‘kyar,duk kunya taji ta isheta tashar’bi bacci surukarta na kallo abin kunya tayi tunani a ranta.Kamar ko yaushe cikin rissinawa ta gaisheda Mom ganin ido yasa shima ta gaishehi harda tambayarsa ya jiki, shikuwa ya’ki amsawa yayi kamar beji ba.
Bayan awanni kad’an sega su Zakia sunzo asibitin,dama haka take so tana ganinsu tayi fitowarta ta fita can waje ta samu bench ta zauna tana kallon shuke-shuke.
“Mom are you staying here until…” Shaheed be ‘kare magana ba Mom tace.”No..no I’m not going to stay here beside I’ m going back home today”
“What? Are you leaving me like this?”
“Amjad ,Laila is here and I think is ok like that”
“Yes!” Zakia da ba da ita ake ba ta tsomo baki.
Kallonta kawai yayi ya kawar da kai ba tare da yace komai ba dan yanzu ba lokacin wannan bane.
“Your wife is here,I’m sure she will take good care of you I knew it”
“But..”
“Do you want me to tell you something you don’t know?”Ta tambaya bayan data ga yaran hankalinsu baya gun.
“What?”Ya tambaya.
” The time when you were unconscious I saw Laila holding your hands crying, tears flowing down her cheeks,you know why? Because she cares about you she don’t wanna lose you “
Kallanta ha tsaya yi saroro yana tunanin anya kuwa Laila ce zatai haka.
“Didn’t you believed me?”
“I do 100% remember I trust you Mom” Ya fad’a yana murmushi har cikin ransa ,farinciki ya mamayeshi.
“Laila cried for me ,does this means she loved me?” Abinda ya shiga tambayar zuciyarsa kenan yana mamaki.Ya ‘kosa yaganta a halin yanzu amma ya neme ta a d’akin ya rasa ko ina tayi?
Laila seda ta gaji da zaman wajen ta komo ciki,abinda take gudun shi ta sake tararwa watoh kallon da yake mata,ko abinci ta’ki sakewa taci Zakia tana mata hira kad’an-kad’an tana amsawa,suna zaune har Dad yazo bayan ‘yan awanni suka tashi tafiya jin Mom tace tafiya zatai itama Laila hankalinta ya d’aga.Kamar ta tsuguna ta ro’keta ta zauna haka taji,tana kallo ta tattara inata-inata suka tafi tare aiko Laila harda biyo bayansu irin rakiyarnan zatai suna tafiya ta zauna kan bench ta’ki komawa d’akin,ta gwammace ta zauna a waje data shiga.Ko wayarta bata fito da ita ba ,zaman wajen kuma yanzu taji ya gundireta 7:40pm ta tashi ta komo d’akin kamar wacca “kwai ga fashe mata a ciki.Ta shiga ta rufo ‘kofar ko kallonsa ta’ki shikuwa tana shigowa ya sauke idanunsa a kanta kallo bama na wasa ba…
Kan kujera ta samu ta zauna tana sake gyara zaman mayafinta data yafa kanta.
“I thought you run away” Taji ya fad’a.
Shiru tayi bata ce komai ba tana hangen handbag d’inta dake kan drawer,mi’kewa tayi daga zaune ta taka inda jakar take ta ciro wayarta ta dawo ta zauna.
“Where is my phone?” Ya tambaya ganin ta ciro tata wayar a jaka.
Tuna inda ta jefa wayar ta shiga yi dan tun sanda aka dam’kamata a hannunta sanda tazo asibitin.Mi‘kewa tayi daga zaune ta shiga duba akwatin kayansu ta bud’e can ta bud’e nan can ta gano ta ‘kasan akwatin.Tana ri’ke da wayar ta ‘karasa gadon ta mi’ka masa.”Thank you”.Ya furta.
Suna zaune d’akin shiru bame magana nurse ta shigo,kai tsaye ta wuce inda yake ba tare da ta lura da Laila ba.
“Amjad Mu’az,sannu koh”
Alluransa da ake masa ta had’a ta bud’e carnula ta tsiyaya,se magani data mi’ka masa bottle of water data gani kan drawer side na gadon ta d’auka ta tsiyaya a cup a mi’ka masa se wani ‘kwar’kwasa take.”
Se lokacin ta waiwayo ta kalli Laila dake latsa wayarta.”Ke ki biyo ni ki kar’bi wasu magunguna nashi”Ta wani kalleta a wula’kance.
Laila tajita sarai amma jin tace ‘ke’ yasa ko d’ago kanta batayi ba balle ta kalleta.
“Baki ji bane” Ta matso inda take.
“Ke naji kin anbata kuma a nan d’akin ba mey suna ke” Laila ta fad’a bayan ta komo da kallonta kanta.
“Ba irinku ya dace kuke jinyan mutum ba dan baku san darajar wanda kuke jiyyar ba,” Tana gama fad’ar haka ta fita ta bar Laila.
Ranta in yayi dubu ya ‘baci ,duk wannan uban zaman da take sha a asibitin nan shine zata fad’a mata ‘bakar magana.
“What did she said?” Ya tambayi Laila.
“Nothing” Ta amsa bata ko kalleshi ba.
Gida’a kai yayi dukda be aminta da abinda ta fad’a ba dan yaga sauyin yanayin fuskarta fiye da da.Wayar ma ajjeta tayi dan tsabar takaici ta kasa yin abinda zatai.
“Laila I’m hungry” Taji yayi magana.
D’agowa tayi ta kallesa nan Mom tace yaci abinci amma ya’ki shine yanzu zece mata wani zeci abinci.A hankali ta tako zuwa inda warmer d’in yake ta samu plate ta ziba masa pasta had’e da sweet creamy potato sauce ta samu spoon ta d’ora ta mi’ka masa, ganin be kar’ba ba ta ajje masa kan gefen gadon ta koma ta zauna.
“Laila can’t you see ? I can’t use my hand to eat”
Se lokacin ta d’ago ta kalli hannunsa na dama dake nad’e a plaster.”Kaci da hannun hagun”.
“Laila it’s not good to eat with left hand”
Sekace ba shine mey cin abinci da hannun hagun ba wata rana.”Laila I’m starving “
Cikin sanyin jiki irin nata ta ‘karasa,a gaskiya bazata iya zama gefensa ba kamar yadda taga Mom nayi, tsayawa tayi ta d’auki plate d’in a tsayen ta d’ibo a spoon ta mi’ka masa.
“I can’t take this while you’re standing”
“It’s ok for me”
“But it’s not ok for me,sit”Ya fad’a.
A raku’be ta zauna daga gefensa dan wajen ba wani space ne dashi ba duk yadda takai ga no’kewa seda ta ra’bi jikinsa abinda bataso kenan.Bata bari sun had’a ido ba ta mi’ka masa, yana sane ya ‘bata lokaci kafin ya kar’ba har hannunta ya gaji.Dayaga ya kusa ‘koshi inde ta d’ibi abincin seyace lomar tayi masa girma har seta rage zeci.Tana gama bashi ta mi’ke da sauri.
STORY CONTINUES BELOW

“Water” Ya tuna mata.
Shima ruwan seda ta tsiyaya a cup ta bashi ,yana sha yana kallonta.Laila a yadda ta kula ruwan ya isheshi amma da gayya take sake d’ura masa seda yayi mata alama da hannu ta maida cup ta ajje.
Tana komawa kan kujerarta ta gado ta jingina ta rufe idanunta.”Are you comfortable there?”
“Uhm” Ta amsa.
Yana kallonta se motsi take dan ba bacci take ba.”Laila come over here”
“Wa ? Cinyarka kake so na kwanta? you’re sick” Ta fad’a a ranta.
Haka yayi tayi mata magana har ya gaji bata ko bud’e ido ba.
★★★
Tun 5:00am ya tashi daga bacci,kwanciyar du ta isheshi ya juya nan ya juya can,Laila kuwa se sharar bacci take.
6:30am ta farka daga bacci, tana maida kallonta kan gadon nashi ta lura da nurse dake tsaye a bakin gadon sede kuma bata jiya bace.
“Your sister?” Ta tambayi Amjad lokacin data ga Laila ta tashi daga zaune.
“No,my wife” Ya amsata yana kallon Laila fuskarsa d’auke da murmushi.
“Married at young age”Nurse ta fad’a tana kallon Laila.
” Your wife is pretty but she don’t smile”Nurse d’in tayi dariya,Amjad ma dariya yayi yana kallon Laila data sunkui dakai tana guntse dariyarta dan ita kanta Nurse d’in ta bata dariya musamman yadda tayi maganar dan ba bahaushiya bace.
“Ehnn…amma ita ba Nigerian bane?,yayi kamanni irin na bature mijinka” Ta tambayi Laila cikin gur’batacciyar Hausa.
“Nigerian ne mana” Laila ta amsa.
“Ehenn ban yarda ba,baka so nace mijinka yafika kyo”
Itade Laila dariya tayi ta rabu da ita da surutunta har ta fita.
“Morning” Taji ya fad’a.
Shiru tayi batace komai ba ,akwatin ta zuge ta ciro kayanta ta shiga bathroom.10min later ta fito cikin shirinta na atamfa doguwar riga ta yafa mayafi.
“Can you please help me sit up?”
Basarwa tayi kamar bata ji ba.”Laila I’m talking to you,why are you shunning me as if you’re not the one crying for me…”Ya ‘kare maganar a hankali.
‘Kiri tayi da ido tana mamakin yanda akai ya sani.”Taya ya sani,ko dama yana jina lokacin? “
“I’m gonna call Mami to tell her how you’re treating me,you don’t show any respect to your husband”Ya mi’ka hannu ya d’auki wayarsa.
Ganin haka tayi sauri ta ‘karaso inda yake,pillow daya d’ora kansa tasa hannunta zata zame.” Laila ,do you wanna break my neck?”Ya ‘kwantar da murya.
D’an d’ago da kanshi yayi yana jiran nata taimakon ,rufe ido kawai tayi ta zagaye hannunta a bayansa da taimakon ta ya mi’ke zaune ta sanya masa pillown a baya yanda zeji comfortable.
“Thanks dear” Ya fad’a yana murmushi.
Suna zaune aka kawo musu breakfast,Laila tana kallon abincin amma ta’ki ko ci balle ta bashi shima,shiru yayi beyi mata magana ba.
“Laila” Ya kirata .
“Why are you always mad at me ,is’t because of…” Se kuma yayi shiru.
“Because I’m not suppose to be with you here but your girlfriend.”Ita kanta bata zaci haka ba daga bakinta.
Ya dad’e kafin ya sake wata maganar.” Laila I know I was wrong to treated you like that,I’m sorry for hurting you…”Be ‘kare maganar ba aka turo ‘kofar d’akin.
STORY CONTINUES BELOW

“Assalamu Alaykum”Mom ta tayi sallama.
” Waalaikissalam”Suka amsa.
Cikin rissinawa ta gaisheda Mom.”Laila, how you? “
“I’m fine” Ta amsa.
“Mom I’m the patient not Laila?”Ya fad’a.
” You’re jealous “Cewar Mom tana dariya.
“Have you eating?”
“No” Ya amsa yana kallon Laila tare da yin makirin murmushi.
“Why?”
“He refused to eat” Laila tayi saurin fad’a.
Waro ido yayi yana kallonta ashe itama ta iya sharri.”Mom I …”
“You what? You have nothing to say,now that i’m here I will force you to eat”
Abincin data taho musu dashi ta d’akko.Baguette da liver sauce se sandwich.A plate ta jera komai ta zauna ta soma bashi.Laila haka kawai taji ‘bacin rai ganin Mom ke bashi,ita kanta batasan dalilin fushin ba(Jealous).
Komawa tayi gefe ta zauna dan ta huce takaici seta d’auki wayarta tana dubawa.
“Laila,are you not gonna eat?”Mom ta tambayeta
“Ita ai taci d’azu” Amjad ya fad’a.
Shima ya rama,suna had’a ido yayi murmurshi ita kuwa ta murgud’a masa baki tare da watsa masa harara.Kamar wani dolo haka ya saki baki ya bita da kallon dan be ta’ba gani tayi masa irin abinda tayi yau ba,ba ‘karamin birgeshi tayi ba yaji dama tana kusa dashi.
Mom duk wannan dramar da ake bata kula ba ,haka Laila ta zauna bata ci abinci ba wajen 12pm Mom ta tafi ta barsu da halinsu.
“Why did you lied?”
“Toh ai kaima ka rama”
“Wannan is a little thing,when the time you will see”
“Allah ya nuna mana”
“I know you will cry”
“Cry? Tabb god forbid”
“Hmm” Yayi murmushin mugunta.
Ganin haka kuma seta ji jikinta yayi sanyi lokaci guda ‘kwa’kwalwarta ta fara ganar da ita mey hakan yake nufi.
“I’m hungry”Ya fad’a.
” D’azu kaci abinci fa”
“Yes I want more”
Tana jin haushi ta mi’ke ta ajje wayar dake hannunta,yau ma ra’ku’bawa tayi a gefensa lomar farko data mi’ka masa yasa hannunsa na hagu kan nata hannun ya mayar da spoon d’in saitin bakinta.”Eat,I know you’re hungry”.
“No I’m not”
“You’re”
Tana bud’e baki zatai magana ya saka mata,ba yadda ta iya ta had’iye.Plate d’in ta maida kan drawer ta mi’ke zata bar wajen yasa hannu ya ri’ko hannunta bata ankara ba ta fad’o jikinsa.
“Auch!” Yayi ‘yar ‘kara.
“Sannu ,I’m sorry” Ta rikice se duban hannun take ta d’auka ko bigeshi tayi.
“Relax” Ya fad’a hankali kwance.
Ganin fuskarsa ta gane ba abinda tayi masa ma yana sane,tayi ‘ko’karin tashi daga kanshi ya sake janyota ta zauna kan cinyarsa.
“Ka sake ni”Ta shiga mutsu-mutsu amma ko jinta ya’ki yi.
” You care,you care about me Laila I knew it”
“No” Ta harareshi.
“I like the way you glared at me,you look beautiful doing it”
Jin haka yasa bata sake hararar ba balla murgud’a baki.Muryarsa a raunane ya soma fad’in;
“Laila I gave up ,I have no choice my heart choosed you,I fall for you Laila why can’t you understand?I’m thinking of no one but you it’s always you Laila I mean it”
“I don’t care,you love her not me”Ta fad’a zata tashi ya sake ri’keta gam.Hannunsa mey plaster ta kalla.” You’re hurting your self”
“Anything that happen to me is you, it’s because of you Laila, I no more love her again I was wronged to love her when I have someone like you ,I have regretted everything I have done,I was so stupid to turned my back on you,Laila I’m begging you to forgive me I’m very sorry”
Alamun murya taji a waje wanda yake tabbatarwa d’akin za’a shigo.”Dan Allah ka sakeni,please let me go”+
“You have to repeat what I will say before I let You go”
“My husband, please let me go” Ya fad’a.
Ganin ba mafita ta maimata”My husband please let me go “.Tana fad’a ya saketa yana murmushi.
Da sauri ta mi’ke ta bar gurin tayi chan nesa dashi ” Mugu”Tayi maganar a ciki.
“Assalamu Alaykum” Akai sallama bayan an turo ‘kofar d’akin.Laila tana d’agowa ta had’a ido da Aisha ri’ke da ‘yarsu se Farouq a bayansu.
“Waalaikumussalam” Ta amsa fuskarta a sake.
Da yake Aisha irin mutanennance masu saurin sabo kamar ta dad’e da sanin Laila haka suka gaisa ,dukda yarinyarsu mey ‘kwiyace da Laila ta kirata bata ‘ki zuwa ba.
“Fad’a min sunanki?”Ta tambaya tana d’orata kan cinyarta.
“Minal” Ta amsata tana wasa da takalmin ‘kafarta.
Amjad dake hira da abokinsa Farouq rabin hankalinsa na kanta ,seyaga tayi ‘kyau da kid a hannunta.Zuwan Aisha ya d’ebe mata kewa taji dama karta tafi,lokacin da zasu tafi har rakasu waje tayi bayan sun tafi maimakon ta dawo setai zamanta a waje kan bench.
Amjad jin shiru bata dawo ba ya kirata a waya sejin ringing d’in wayarta yayi a d’akin,yasan dama so take ta samu damar da zata fita shiyasa tayi rakiyar.
Seda taji zaman wajen ya gundireta tukun ta komo ciki.
“Meyasa baki zauna chan ba?” Taji ya fad’a.
“Ai yanzu zan koma” Ta fad’a stubbornly.
“Zan gani taya zaki fita”
“Taya za’a iya ,mutum a kwance”Tayi maganar a hankali.
“Haka kika fad’a koh?”Ya kad’a kai.
Jin haka yasa bata ‘kara fad’ar ‘kala ba se wayarta data d’akko ta soma dubawa.
★★★
Haka suka cigaba da zaman asibiti koyaushe rikici na yau daban na gobe daban ,wani sa’in ko ze iya yin abu da kansa seyace baze iya be setayi masa ,seda suka kwashe sati biyu cir aka yi discharging d’insu daga asibitin lokacin ya samu sau’ki sosai dan a yanzu an cire masa plastern hannunsa an sauya masa da arm sling,bandage dake zagaye a kansa shima an cire iya patch d’an ‘karami be ya rage gefen eyebrow d’insa na hagu.Mom kuwa kwanansu biyu da komawa Canada,Laila jefi-jefi tana shiga school yanzu ma exam zasu fara result nasu na wancen semester ya fito ta samu sakamako mey kyau.
First day da suka komo gida,tunda ta shiga d’akinta kuma shikenan ko le’kowa ta’ki yi 7:30pm se addu’a take karya kirata dan tana expecting hakan.
Ring! Ring! Wayarta tayi ‘kara ,har cikin zuciyarta taji kiran.”Canada”
“Mutum sekace tsoho”Ta d’aga kiran.
” Laila where are you?”
Bata amsa ba ta katse kiran ,mayafinta ta sura ta yafa ta fita zuwa d’akinsa.Tana shiga ta tsaya daga bakin ‘kofa tana kallan gefe.Yana zaune yayi d’are- d’are kan mirror drawer.
“Laila you left me alone,I’m hungry”
Juya tayi zata fita ya tsayar da ita”You didn’t ask me what I wanna eat”
“What is your favorite?” Ya tambayeta.
“D’an wake” Ta amsa dukda kuwa ba shine fav d’inta ba.
Kasa repeating d’in abinda ta fad’a yayi dan haka ya gid’a kai kawai.
“OK,make me your favorite”.
” Uhum”Ta fita.
“Zaka ga favorite sekayi regretting cin d’an wake,bade kai d’an takura ba” Ta fad’a tana d’akko bowl zata had’a d’anwaken.Cikin ‘kan’kanin lokaci ta gama kwa’bawa ruwan data d’ora ya tafasa nan ta soma sakin d’anwakenta kai kace d’an ‘karamin ball ne dan girma,tana gamawa after few minutes ta sauke.Plate ta cika taf ta ziba manja ko soyawa batai ba danma ba’a daskare yake ba,Maggie ta ‘bare ta barbad’a ta d’ibi yaji tea spoon hud’u ta ziba akai ta ko ina,ta d’akko fork ta d’ora.
Dayake tasan mey ta shirya se gimtse dariyarta take ta shiga d’akin,daga drawer side na bango ta ajje plate d’in dake a rufe. Ganin haka Amjad ya sakko daga kan mirror drawern ya ‘karaso inda take.
“Sit” Ya fad’a yana d’aukan plate d’in.
Tana tsaye kawai jira take taga ya bud’e taga irin reaction d’insa,d’an basarwa yayi ya kalli kalar d’an waken ya d’anyi guntun murmushi. “Feed me” Ya mi’ka mata plate d’in. Daga gefen gadon ta zauna opposite dashi,’kwaya d’aya ta soka wanda yaji yake mamaye a kai ta mi’ka masa saitin bakinsa.Amjad yana kallonta ya mi’ka baki ya kar’ba ,tashin farko yaji uban yaji gashi ya shika masa bakinsa ko taunawa da’kyar yake,kamar ma’kogoronsa ze fashe haka ya had’iye.Kafin ya dawo cikin nutsuwa tasake sokar wani ta mi’ka masa, kamar wanda aka dannewa baki ya kasa maganar,haka ya bud’e bakinsa ta sake zirawa.Ma‘kwat! kuke ji take bakinsa ya d’ad’e shhh! Ya fara.
Tana sake mi’ko wata lomar ya kauda kai murmushin fuskarsa ya d’auke.Wata muguwar dariyace ta ku’bucewa Laila har tana rufe bakinta.
“What did you do?” Ya kalleta cikeda tuhuma
Tashi tayi da sauri ta dire plate d’in tayi hanyar ‘kofa tana dariya harda dafe ciki,kamar kiftawar ido taga yasha gabanta”You’re not going anywhere”Ya kulle ‘kofar dakin.
I’m sorry for the short chappy am busy sosai.Love ur❤
Dijensy❤
Tana gani ya rifo ‘kofar hanjin cikinta ya kad’a ta soma had’iye dariyarta.A hankali ya soma takowa inda take ta fara ja da baya ganin ta kusa ‘kure bango ta fara zagaye a d’akin “What did you do?”Ya fad’a yana nufar inda take.Ganin ya’ki tsayawa gashi tazo daf da gadon aiko take ta haye kan gadon tana so ta zauka gefe.” Laila you better stop you can’t run away from me because I have the key with me”
Dukda abinda ya fad’a bata sauraresa ba seda ta ‘karasa ‘kofar tayi ta girgizawa amma ta kasa bud’ewa,ganin ya zagayo inda take ta sake guduwa yayi can tayi nan haka sukai ta zagaye a d’akin ,daga ‘karshe yayi nasarar ri’kota.”Please I’m sorry”Ta fara bashi ha’kuri take idonta ya raina fata.
“Why? did you want me dead?”
Girgiza kai tayi alamar a’a.”Then why did you do it?”
“I said I’m sorry”
“I don’t need your sorry, this is pay back time now is my turn” Ya fad’a yana ri’ke da hannunta ya janyo plate d’in d’an waken ya mi’ka mata.
“Eat”
Ita kanta data saba ganin d’anwake seda taji tsantsamin ci gashi yaji burjik ya ratsa ko ina.”Please sorry “
“Don’t sorry me ,you didn’t offended me ai I just want you to taste it isn’t it your fav?”
Da sauri ta girgiza kai “No” Ta amsa.
“Then why did you lied?”
“I’m sorry”
“You lied because you wanted to purnish me ,now eat”
Ya sake mi’ka mata,fafur taki kar’ba aiko ganin haka ya zaunar da ita daga can jikin gadon ya zauna daf da ita yadda bazata iya gudu ba.Hannunta ya sake ya d’auka fork d’in ya soka d’aya kamar yadda yaga tayi ya mi’ka mata “Arhh”
‘Kin bud’e baki tayi ta marairaice ,yana sake matso da fork d’in tasa hannunta ta rife bakin, yin duniya ta’ki yarda ta bud’e bakinta garin zillewa ta kwanta kan gadon a rigingine kafin ta yun’kura ta d’ago yayi mata runfa.
“Sorry” Ta fad’a kamar zatai kuka.
“Don’t mention” Yayi maganar cikin sanyi murya wadda bata ta’ba jin yayi irinta ba.
“Please let me go”
The more tana magana the more yana sake matsowa kusa,ganin baida niyyar dakatawa tasa bayan hannunta ta rufe bakinta ta rufe idanunta.Tafin hannunta taji yayi kissing wani irin shock taji take ta soma mutsu-mutsu,garin haka ta bigi hannunsa mey karaya.”Auchh!”
D’agowa tayi da sauri tana kallonsa cikeda rud’ewa ta dafa kafad’arsa “Sannu ,sannu”.
D’ago da kansa yayi yana kallonta ya soma murmushi,ganin faking ne ta d’auke hannunta ta d’aure fuska da sauri ta mi’ke harta kai bakin ‘kofa be mata magana ba.
“Please ka bud’e min”
Shiru yayi bece mata komai ba se blanket d’inshi daya janyo ya gyara kwanciyarsa bayan ya cire Shirt d’in jikinsa.
Ganin ya juya baya ta dafe kai “innalillah kwana anan d’akin?” Ta fad’a a ranta.
Tsaiwa ta cigaba dayi tana ri’ke da handle d’in ‘kofar,tafi 30min a tsaye harta gaji gashi couch d’in d’akin bata nan balle ta zauna.Drawer mirror ta soma dubawa ko zata ga key amma babu alamarsa,drawer side na bed ta dudduba nan ma babu a cikin sand’a ta ‘karasa drawer side d’in dayake kwance taga ya rife idanunsa yana bacci.A hankali ta duba itama babu ,wani tunani ne ya fad’o mata aiko ta zagaye baya tana tunanin ta ina zata soma lalubar aljihunsa,cikin sand’a ta d’an d’age blanket d’in a hankali ta zira hannunta a cikin pocket d’in sede ba komai ciki ganin alamar yana motsi tayi sauri ta d’auke hannunta taja baya.
STORY CONTINUES BELOW

Haka ta cigaba da tsaiwa tun tana jurewa ga bacci data keji haka ta zauna kan tiles ta d’ora kanta kan gadon.
6:03am,ta bud’e ido a firgice ta tashi ganinta tai d’are-d’are kan gado mayafinta ma ta nema ta rasa,gefe kuwa Amjad ta ganin yana baccinsa hankali kwance,cikin sauri ta yaye blanket d’in ta sauka daga kai.Ganin har 6am yayi ta shiga bathroom d’in d’akin ganin be bud’e ‘kofar ba,tana yo alwala ta fito ta d’auko mayafinta daya fad’i ‘kasan gado ta yafa ta tada sallah.
Har ta idar da sallah be farka ba,ganin lokaci na sake ja yasa ta mi’ke daga zaune ta ‘karasa inda yake.Pillow daya d’ora tasa hannu ta bubbuga ,tayi haka yafi sau uku amma ya’ki tashi.Komawa tayi gefe tana jira ko ze farka da kansa amma shiru,haka ta sake komawa tayi ta magana”Wake up,is time for prayer”
Kamar bakinta zeyi tsini amma be tashi ba har 7:15am yayi,gashi ta tsani ta tashi mutum ya’ki farkawa.D’aya pillown ta d’auko ta fara buga masa a ‘kafa nan ma shiru,bata ankara ba taji hawaye sun fara tsiyaya kuka ta fara sosai harma ana jin sauti.
Jin ta fara rera kuka yasa ya tashi dan duk wannan abin da take yana jinta.Gani yayi ta dasa tagumi ta juya baya “Laila” Ya kira.
Ganin ta’ki amsawa kuma ta’ki dena kukan yasa ya ‘karasa inda take ya zauna kamar yadda tayi ta tan’kwashe ‘kafarta.
“Laila why?”
Se lokacin ta d’ago ta kalleshi idanunta yayi ja.”Open the door and let me out”Ta fad’a cikin rawar murya.
“I will,but tell me why are you crying are you so worried about me like this?”
Wata uwar harara ta watsa masa tare da mi’kewa ta koma jikin ‘kofar ta juya masa baya.
“Laila I’m still alive don’t worry”
“I don’t care”Ta fad’a bayan ta juyo.
“Lie,now tell me did you pray?”
“Do you have to ask? I’m not like you ,you know”
“What do I do laila” Yayi maganar yana ‘karasowa inda take.
“You always pray late”Tana fad’a ta juya.
“So this is the reason why you’re crying?”
“Laila you suppose to wake me up”
“How many times? it’s your habit ai ” Ta ‘kare maganar a hankali.
“Ok, now help me perform ablution will you?”
Shiru tayi kafin daga bisani ta gid’a kai,se bayan yayi sallah tukun ya bata key ta bud’e ‘kofar ta fita.Seda ta shiga d’akin bayan tayi wanka ta shiryo tukun ta fita kitchen tayi preparing breakfast.Tana kammalawa ta jera a tray tana shirin hawa sama da abincin taga yana sakkowa,ya sauya cikin shirt red da ba’kin wando.
Kallo d’aya tayi mishi ta juya kan dinning ta jere kayan ,ba ‘karya yayi mata kyau sosai ga ‘kamshin turarensa dake dukan hancinta.
“Morning” Tajiyo muryarsa.
“Morning” Ta amsa masa kanta a sunkuye tana ziba abincin a plate.
“May I sit?”
“Juyowa tayi da gefen ido tana kallonsa ta amsa da ” Yes”.
“You look pretty” Ya fad’a bayan ya zauna.
For the first time an yaba ‘kyanta dukda ba wani heavy makeup tayi ba ,blue atamfa tasa mey adon ba’ki se lipstick da kwalli tayi d’aurin step-step.
STORY CONTINUES BELOW

Kujerar dake kusa dashi taja gefe ta zauna ,d’aya daga cikin plate da tasa abincin kuma ta matso dashi kusa.A zuciyarta kuwa addu’a take Allah ya kawo ranar da ze warke ta dena bashi a baki.
Lomar farko data mi’ka masa be kar’ba ba.”You need to eat first”.Ya fad’a fuskarsa d’auke da murmushi.
Bata ce komai ba taci se a na biyu data d’akko ya kar’ba.”Laila look into my eyes”Ya fad’a dan bata iya kallon cikin idanunsa.Yitai kamar bata jiba.”Laila I’m talking to you”.
Tana d’ago da idanta kallo d’aya tayi masa ta mayar gefe.Har suka gama breakfast bata iya had’a ido dashi ba,tana gamawa ta tashi ta kwashe komai na dinning ta wuce dasu kitchen.
★★★
2 weeks later
Cikin sati biyunnan Amjad ya warke yanzu hannunsa an cire arm sling d’in yana iya amfani dashi har ya koma office, Laila sunyi nisa da fara exam ,a kullum sake sabawa suke sede tun rannan bata sake bari ta shiga d’akinsa ba ko gyara d’akin zatai seta tabbata baya nan.
8:12am suna dinning breakfast sun d’au minutes shiru ba wanda yayi magana,tsam ya ajje chokalin hannunsa bayan ya kalli wrisk watch d’insa,kur’ba d’aya yayiwa coffee d’in gabansa ya mi’ke.”Laila I’m done”
Tana daga zaune kawai gid’a kai tayi batace komai ba.”Laila no good bye?”
Tana jinsa tayi shiru dan kullum haka yake fama da ita ko bye baya samu wani lokacin ma se taga ya kusa tafiya ta shige d’akinta.
Tana sunkeye da kanta ba zato ba tsammani taji kiss a cheeks d’inta ,a take tsigar jikinta ta mi’ke kafin tayi wani ‘kwa’k’kwaran motsi ta sake jin wani a d’ayan side d’in.”Good bye my heartbeat”.
Daskarewa tayi a zaune ta kasa sake wani motsin har ya fice bata lura bama,hannunta tasa ta shafa kumatun dama sannan na hagun ta dafe ,murmushi ta tsinci kanta tana yi wanda bata shirya masa ba.”Heartbeat”Ta maimaita a fili cikin sanyaryar murya.
Ta dad’e a haka ko cikakken breakfast batai ba banda tunaninsa.Ganin 9am na shirin yi ta tashi ta wuce da plates d’in kitchen bayan ta d’auraye ta koma d’aki ta ciro handout ta soma karatu dan tana da exam gobe.Tiryan-tiryan ta fara karatunta bata ankare ba taji ta dilmaya cikin tunani,tunaninma na Amjad. Duk yadda takai ga kawar dashi bata iya ta dena ba,abin har ya soma isarta dan tana so tayi karatu amma ta kasa.
2pm ,ta samu da ‘kyar ta karanta iya abinda zata iya ta rufe,tunanin girkin da zatai ta shigayi.Lokaci guda taji tana so tasan favorite d’insa sede kuma batajin zata iya tambayarsa,har ta yanke shawarar abincin da zatai wani tunani ya fad’o mata nan ta tuna sanda suna asibiti Mom ta kawo masa abinci tabbas idan bata manta ba kamar Chicken spaghetti ne,ganin haka kawai ta fara had’a pineapple juice tasa a fridge, daga baya ta soma had’a chicken spaghetti d’in ba jimawa ta kammala ,tsaf ta gyare kitchen d’in ya dawo normal yadda yake.
Tana komawa d’aki text ya shigo wayarta,data duba taga “Canada”
“Hi my heartbeat how is the day,hope you’re doing good. I love you”
“I’m doing good” Tayi replying cikin ‘kan’kanin lokaci.
Yana daga office ya murmusa ganin tayi replying, gwada kira yayi ga mamakinsa taga tayi picking a kira na biyu.
Shiru tayi bata yi magana ba bayan ta d’aga.”Hello”Yayi magana.
“Laila are you there?” Ya fad’a jin tayi shiru.
“Laila talk to me”
“Uh.. Yes” Tayi ‘ko’karin fad’a.
“Are you ok?”
“Yes”
“Have you eaten?”
“No” Ta amsa.
“Why? Are you waiting for me ?”
A zahirin gaskiya amsar itace “yes”,amma kuma seta ce “No”
“Sure?”
“Yes”
“Don’t lie,did you missed me”
Shiru tayi ta’ki amsa masa,se magana yake mata amma ta’ki magana.
“Laila you missed me I knew it”
“No” Tana fad’ar haka ta kashe wayar ta kasa dena murmushi.
Data d’inta ta bud’e taga yayi posting status, bud’ewa tayi karantawa taga yayi note data karanta taga akanta ne heartbeat. Profile status ma it’s about her,ajje wayar tai chat d’inma ta kasa yi se tunani data shigayi tana blushing.Shima ta ‘bangaren Amjad wayar tashi yabi da kallo yana murmushi yana ayyanawa the answer is yes kawai kunyar fad’a take,jiyake kamar yafi kowa farinciki a duniyar “She love me”.
15min later tana cikin wannan tunanin taji ringing d’in door bell,mi’kewa tayi ta bud’e window ta le’ka ta hanging motarsa,mamakin yadda akai har ya dawo da wuri ta shigayi ganin zata ‘bata lokaci ta d’auki mayafinta ta yafa ,har zata wuce ta dawo ta kalli mirror ,powder ta sake dusting a fuskarta tare da sake shafa humranta. Mayafin ma taga beyi mata ba ta cire ta fita a haka cikin riga da skirt na red atamfa,ta ri’ke handle zata bud’e ta kalli jikinta tana jin kunya hakanannan ta bud’e.
Tana had’a ido dashi ta sauke duk kunya ta isheta,fuskarsa d’auke da murmushi ya ‘karaso ciki tare da rufo ‘kofar.Hannayenta biyu ya ri’ko cikin hannayensa yana murzawa softly.”Laila what are you hiding on your face? let me see your pretty face”.
“Laila” Ya sake kiranta ganin ta’ki d’agowa.
A hankali ta d’ago da kanta sede ta’ki bari su had’a ido,hannayen nata duka biyun ya had’a yayi kissing.”Did you know how pretty good your hands look like? I really love them”.
“Amjad’Ta kira sunansa.
” uhm?”
Be ankara ba cikin sauri ta zare hannunta kafin yayi wata maganar tayi sauri ta haye sama ta barshi tsaye a gun,tana shiga d’akinta ta rufe ‘kofar se numfarfashi take hannayenta tasa a gaba tayi ta kalla.
Amjad kuwa hanyar kitchen yayi kan dinning yaga warmer daya bud’e kuwa yaga fav d’inshi”Wow!”Ya furta ,ba ‘bata lokaci ya d’auka serving spoon ya ziba a plate
har rawar jiki yake yakai loma d’aya waje ya samu ya zauna dan santi harda cire suit,seda yayi dam tukun ya tashi ya shiga kitchen daya bud’e fridge yaga pineapple juice nan ya tsiyaya a glass cup ya kora dashi.
★★★
20 minutes later, taji knocking ‘kofar d’akinta,a d’ari-d’ari ta ‘karaso ta bud’e. Tsaye ta ganshi ri’ke da tray a hannunsa.”May I come in?”
Kai ta kad’a alamar “eh” tana sunkui da kai.Daga kan drawer side na gadon ya ajje sannan ya dawo inda take. “Laila you haven’t eat and you’re here alone it’s boring”
Hannunta ya ri’ke ya zaunar kan gadon,daga gefenta ya zauna ya d’auko plate d’in abincin.Open up”Ya mi’ka mata spoon d’in cikeda abincin.
“I…” Bata fad’i abinda take son cewa ba yasa mata a baki,itade tana ganin ikon Allah ‘kiri-‘kiri ta kasa hanashi bata abincin kuma ta kasa hana kanta ci,tana so ta tambayeshi ko yaci abincin amma ta kasa.”Is ok”Ta fad’a bayan ta ‘koshi.
“Sure?”
“Yes” Ta amsa tana gid’a kai.
Juice d’in ya tsisaya a cup ya bata shima ta kur’be.”Laila did you know my favorite food? “Ya tambayeta bayan ya maida cup d’in.
” Yes”Ta amsa still ta’ki kallonsa.
“How?” Ya tsireta da ido.
Shiru tayi ta’ki fad’a yin duniya ta’ki fad’a masa se murmushi kawai da take. “Come with me” Ya ri’ko hannunta bayan ya mi’ke daga zaune, ba musu ta tashi daga zaunen itama.
Hannunta a cikin nasa suka fita daga d’akinta,a tsorace take tafiyar ganin suna yin hanyar d’akinsa.Suna shiga be tsaya da ita a ko ina ba se gaban mirror.Drawer taga ya bud’e daga gefe taga ya d’akko d’an ‘karamin box blue colour.Hannu yasa ya bud’e nan had’ad’d’en necklace ya bayyana mey silver chain pendant d’in blue stone se walwali yake,bayan ya d’akko sar’kar ya ajje box d’in gefe stool d’in mirrorn ya gyarawa zama sannan ya juyo gareta.”Laila ,sit”Ya fad’a cikin tattausan murya.
Ba musu ta ‘karasa ta zauna tana facing mirror d’in,a tsanake ya bud’e sar’kan tare da saka mata a wuyanta ,sosai ta zauna a wuyanta ita kanta sar’kan ta burgeta matu’ka,ta sakakance tana ta kalla taji ya d’ora ha’barsa kan kafad’arta fuskarsa d’auke da murmushi yake kallonta ta mirror tana gani sun had’a ido tayi saurin sauke idonta
“For you only my heartbeat”
“Now i don’t care about anything , i am not afraid of anything”
STORY CONTINUES BELOW

“I want to split myself in you dear”
“You’ve captured my mind, my heart, my soul on earth”
“My heart need your heart dear”
Laila tunda ya fara maganganunnan ta wulla wata duniyar se bayan da tunaninta ya dawo ta lura da hannanyensa daya zagaye cikinta yayi hugging d’inta tightly ta baya,data lura da fuskarsa taga idanuwansa a rufe suke ,motsi tayi tana so ta mi’ke amma ta kasa dan jitai ya sake ‘kan’kameta.
“Laila stay with me, never leave me alone”Taji muryarsa almost like rad’a-rad’a.
An d’au tsahon lokaci a haka shiru kowa a ransa da irin feelings d’insa.”Amjad ,please go off me” Tayi maganar cikin siririyar muryarta.
“Please be with me,I so much love you I always want you by my side”Ya ‘kare maganar yana bud’e idanunsa.
Tayi tunanin ze barta ta tafi kamar yarda ta ro’ka amma setaga ba hakan ba,a hankali ya fara kissing wuyanta yana sha’kar ‘kamshin turarenta.Ai tuni hankalinta yai mugun tashi fiye da koyaushe,kamar zatai kuka ta soma magana.” Amjad please let me go”Tasa hannu tana matsar da hannunsa dake zagaye a cikinta.
Ring! Ring wayarsa tayi ‘kara cikin pocket.Kamar baze d’aga ba seda ta katse a na biyu yasa hannu a aljihu ya zaro wayar,ai bata bari ta ‘kara koda 2 second ba tayi sauri ta mi’ke bata tsaya ko ina ba se d’akinta a d’akin nata ma bathroom ta shige ta rufo ‘kofar se tsuma take.Zuciyarta se harbawa take kamar ta fito,tunanin abinda ya faru tayi tayi tana raba idanuwa.Sar‘kar ta shiga kalla taga ta jujjuyata sosai tayi mata kyau,se yanzu ta tuna ko thanks bata fad’a ba.
Amjad kuwa bayan ya gama wayar ya kalli stool d’in only to found empty space ya sani ta gudu kuma a yanzu ko meh zeyi ba bud’e ‘kofarta zatai ba,murmushi kawai ya saki ya komo gefen gado ya zauna yana tunaninta.
Har maghrib,isha’i bata ko kalli ‘kofar d’akinta ba ,handout d’inta ta d’auka ta shiga karantawa se 11:16pm ta kwanta.Washegari bayan ta gama shirinta ta zauna ta kasa fita, ganin zata makara ta samu hakannan ta sakko sede ta zira hijab d’inta yau har niqab d’in ma ta saka.
Tana zuwa dinning ta tarar dashi kamar dama jiranta yake.”Morning “Ya fad’a fuskarsa d’auke da murmushi mey manufofi iri-iri.
“Breakfast is ready” Yayi mata nuni da jerin plate dake kan dinning d’in,tayi mamaki ganin yawan kayayyakin wajen shikam yaushe ya girka wannan ? Tayi maganar a zuciyarta.
“For you heartbeat, I made all this for you”
“Come on sit” Yayi maganar yana jan kujerar gefensa.
‘Karasawa tayi a hankali ta zauna kan kujera amma bata kusa dashi ba,murmushi yayi ganin ta’ki zama kusa dashi,niqab d’in ta d’age tukun ta soma duban abincin.
Slide bread d’in ta d’auka data dubi soyayayyan ‘kwan taga half done ,nashi plate d’in ta kalla taga ya kusan cinye nashi kuma irin suyar ne,ita kam bazata iya cin d’anyen abu ba dan haka ta matso da butter ta shafa a bread d’in, plate d’in ‘kwan ta matsar dashi.
“Don’t you like it?”
“Yes” Ta amsa.
“Why?”
“It’s undone”
“Who told you so,it’s yummy this way”
“No,I need it solid”Ta kalli kwan tana ta’be baki.
Dariya ta bashi dan yadda tayi ina irin ‘kyan’kyami d’innan.”Sorry Heartbeat next time I will make it solid”
“What of the fruit salad do you like to taste it?” Ya tambayeta.
“Uhmm” Ta kad’a kai.
Da kanshi yayi serving a bowl ‘karami ya mi’ka mata. “Ba laifi” Ta fad’a bayan tayi cokali d’aya.
“What did you mean by that?”
“Uh…uh..I like it ,it taste good”
Suna hira kad’an-kad’an har suka kammala,tare suka fita daga gidan driver ya jasu dan tun bayan accident be sake driving da kansa ba.Har cikin school aka kaita da tazo fita ya ri’ko hannunta. “I love you” Ya fad’a a hankali.
Itade kallansa tayi ta juya ta fita bayan ya saki hannunta.
★★★
Tana fitowa daga exam 12pm ta komo gida,tana cire hijaba ta dire bag d’inta ta sakko kitchen domin had’a girkin rana.
Ring! Ring! Wayarta dake parlour tayi ‘kara,da sauri-sauri ta fito daga kitchen d’in ta d’auko wayar.’Canada’Ta gani a take ta saki murmushi,ta kai hannu zata danna answer se kuma wata zuciyar tata tace’Kija aji mana”
Bari tayi kiran ya katse kamar yadda tayi expecting yana katsewa ya sake kira.
“Hello” Tayi maganar cikin siririyar murya mey tafiya da imanin mey saurara.
“Lai..La” Ya kira sunan a rarrabe dan ta kashe masa jiki da yana tsaya a jikin window amma daga baya ya koma ya zauna.”Where are you now?”
“At home” Ta amsa.
“I’m on my way” Ya fad’a.
Shiru tayi bata ce komai ba tana sauraronsa.”Heartbeat? are you there?”
“Ah..uh.yes..yes”Tayi stammering.
Daga haka sukai sallama ta koma kitchen, nan da nan abinci ya kammala couscous da miyan cabbage tayi.Bayan like 30min tana d’aki taji shigowar motarsa,mi’kewa tayi daga zaune ta ‘karasa wajen window ,labulen ta yaye kad’an tana le’kawa ,nan ta sakankance tayi ta kallonsa har ya ‘bace mata daga gani.Se lokacin ta dawo cikin wannan duniyar,mirror ta sake kallon fuskarta ta d’auki sponge ta sake gyara fuskarta ta fesa turare.
Don’t just added my story to your reading list,I want you guys to support by comment, vote and share. Thanks alot for the love, ana tare✌
★★★
Knock! Knock!
Tajiyo a ‘kofar d’akinta,dudum! zuciyarta ta buga,tana so ta bud’e ta wani ‘bangaren kuma tana tsoro.Da‘kyar ta daure taje ta bud’e,gani tayi fayau ba kowa bakin ‘kofar fitowa tayi ta dubi hanyar d’akinsa a zuciyarta tana fad’in “koya koma d’akinsa?”
Har zuciyarta taji ba dad’i fuskarta ba walwala ta komo d’akin ta rife juyowar da zatai taga mutum tsaya yayi folding arms yana kallonta.Cikeda mamaki ta saki baki tana kallonsa.”Yaushe ya shigo? sekace aljani?”
“Surprised huh” Ya fad’a yana murmushi ya ‘karaso wajenta,kafin ta sunkui da kanta yadda ta saba ya tallafo ha’barta kallo d’aya tayi masa ta sauke idanuwanta da suka sha adon eye liner.Ba zato ba tsammani taji saukan kiss a idanta take ta sake rife idan gam tsigar jikinta na tashi.+
“Your eyes are great” Ya furta.
“Uh..lunch is ready” Tayi ‘ko’karin fad’a gudun wani abin ya sake biyowa baya.
“Laila stop pretending”
Wani kunya taji kamar ta nitse “I’m not pretending”
“Ok,let’s go” Ya ri’ko hannunta.
A haka suka ‘karasa har dining table yaja mata kujera ta zauna shima ya zauna a nashi kujerar.Yau ma shiya bata abinci da kansa se kunya take ji.
Bayan sun kammala cin abincin ta koma d’aki,dayace ta zauna siyi kallo tace karatu zatai.Koda ta koma kasa duba handout d’in tayi illa kwantawa da tayi badan bacci ba kawai tunani ta shiga yi ta rintse idanunta.Se wajen asr ta iya samu tayi karatu ,har bayan maghrib bata fito ba.
9pm ta sakko kitchen ganin baya ‘kasa ta saki hamdala,cookies kawai tasha da hollandia ta koma d’aki,bathroom ta fad’a tayi wanka sede handle d’in shower d’in ya birge sam ta kasa kashewa data gaji ta fito ta zira sleeping gown d’inta bayan ta yafa d’an guntun gyale ta fita zuwa d’akinsa ta sanar masa bata ko shiga d’akin ba tana daga bakin ‘kofa kafin ya fito tayi tahowarta.
Koda ya shigo d’akin tana tsaye daga gefe,a hankali ya ‘karasa bathroom d’in ya kalli shower dake zubar ruwa ,yayi iya nashi ‘ko’karin amma ya kasa.”Laila come over and help me with thi..s” Ya ‘kare maganar a rarrabe.
“Uhmm?” Kamar bata jiba.
Alama da hannu yayi mata alamar ta ‘karaso,a hankali ta taka zuwa bathroom d’in.”Something on your face”Ya ta’ba saman eyebrow d’insa.
Hannu tasa ta ta’ba gurin amma taji ba komai,girgiza kai tayi alamar babu wani abu.”Very close to your hand…you’re almost there…”.
Haka yayi ta mata wasa da hankali daga baya yace “Come over”.Cikin sanyin jiki irin nata ta ‘karasa inda yake.”Close your eyes”
“My eyes?” Ta had’e gira.
“Yes” Ya amsata.
Rife idanunta tayi kamar yadda ya fad’a d’in,ruwan shower d’in dake zuba ya tara hannu yayi sprinkling a fuskarta.Da sauri ta bud’e idonta ta d’ora a kansa ta tamke fuska bata tsaya wata-wata ba itama ta bud’e tap d’in sink ta cika tafin hannu ta rama tana watsa masa ta juya zata gudu yaja hannunta ta baya ta fad’o jikinsa,se fisge-fisge take amma ta kasa.Dede saitin shower d’in ya tsaya yadda duka su biyun yana ta’basu ruwan,d’an gyalen dake kanta ya zame gashinta yayi jagaf duk ya kwanta ga ba’kinsa daya sake bayyana.An d’auka kusan 5min sannan daga baya ya sunkuceta kamar ‘yar baby ,be direta a ko ina ba se kan gado,jikinta jagaf ya ji’ke, saboda sanyin ac ta fara d’an rawar jiki towel ya d’auko ya d’ora mata akai ya shiga tsane mata gashi ita de ta kasa making any move.Yana goge mata kan idonsa yayi focusing lips d’inta sam ya kasa controlling mind d’insa bata ankare ba taji saukan lips d’insa a nata……
STORY CONTINUES BELOW

***
6:03am
“Laila I said I’m sorry ,please let me help..”
“Banaso!” Tayi maganar fuskarta a cikin pillow.
“Laila please” Ya kai hannunsa kafad’adarta ta tsala ihu.
“What do you want now?” Yayi maganar cikin sanyin murya.
“Leave”.
” Ok,but you need to get up I can’t leave you like this you know “.
Anfi 30min se fama yake da ita kamar zeyi ciwon baki still ta’ki d’agowa balle ta mi’ke zaune gashi da yayi ‘ko’karin ta’ba ta tasa ihu.Daga baya de haka ya mi’ke ya zagaya gefenta tana bigeshi a haka ya d’auketa zuwa bathroom ya taimaka mata tayi wanka, idanunta sunyi mata nauyi ko had’a ido dashi ta’ki bari siyi,yana yafa mata towel ta saiti hanya da yana dafe da shoulder d’inta amma ta bangaje ta fito d’akin a daddafe da ‘kyar take tafiya.” Mugu kayi abinda ranka keso”Tayi maganar a zuciyarta harda sheshshe’kar kuka.Wani doguwar riga ta d’akko a wardrobe ta zira hijab zimbilele,sallar ma da ‘kyar ta yarda sukai tare.
Ganin ko magana idan yayi ma ba amsawa take ba ya fita daga d’akin ya bata space,yana fita ta sakko daga kan gadon ta rufo ‘kofar d’akin ta ta komo ta kwanta cikin ‘kan’kanin lokaci bacci ya d’auketa.
11:34am ta tashi daga bacci ga uwar yunwa dake damunta,a sanyaye ta mi’ke tsaye har takai bakin ‘kofa ta tsaya ,last night ta shiga recalling tana tuna abinda ya faru ba yadda batai ba tana ro’konsa amma be ‘kyaleta ba seda ya aiwatar da abinda ransa keso”Mugu”Ta fad’a a fili ‘kwalla na cika a idanunta.
Wayarta ta koma ta d’auko ta shiga contact zata kira Mami wata zuciyar tace “Toh mey zatai miki?” Kamar tasa kuka ta mayar da wayar ta ajje.
2min later sega text ya shigo wayarta ,data duba taga shine”Heartbeats please come down and eat something, I love you my wife”
“An’ki a sakko d’in”
Haka ta cigaba da zama yunwa se cinta take,ganin idan bata rufawa kanta asiri ta sauka taci wani abun ba zata ‘kwari kanta yasa ta tashi tsaye,hijab d’in ta zira sannan ta fita.Gani tayi ma baya ‘kasan ,dinning ta gani cikeda abinci iri daban se wanda ta za’ba ,kujera ta gyara ta zauna nan ta d’ibi abinda zata iya ci taci ta ‘koshi sannan ta komo d’aki ko takan plates data ‘bata bata biba.Amjad bayan ta komo ya sakko ya tarar taci abinci,da kanshi ya kwashe kayan dishes da suka ‘baci ya wanke.
Laila se wannan karon data komo d’akin ta lura da bedsheet d’in ba wanda yake kai bane,wani sabon kuka ta shiga yi tana sheshshe’ka dan kanta ta dena ta zauna tayi tagumi.
Ranar haka ta wuni ‘buya bata sake bari sun had’u ba ,washegari ma ‘kin fitowa tayi har d’aki ya kawo mata breakfast daga bakin ‘kofa ta kar’ba dan bata ko bari ya shigo ba haka bata bari sun had’a ido ba.
Amjad har ya soma gajiya da abun nata, ita a lalle bazata sake kulashi ba ko waya yayi mata bazata d’aga ba hatta school da kanta taje.Yau 10:12pm tana karatu taji an turo ‘kofar d’akin,data d’ago taganshi tsaye tana shirin mi’kewa taga har ya shigo ya maida ‘kofa ya rife.
“Mey kuma zakai Anan”
Tayi maganar cikin Hausa dan yanzu English d’in ma ta dena yi masa.
“Do I have to explain myself?” Yayi maganar yana ‘karasowa.
“This is my room” Ta fad’a a ta’kaice.
“And this is also my room” Ya zagaya ta gefe ya yaye blanket d’in tare da zama”
Bata ce komai ba ta tattare handout d’inta dake kan gadon tayi hanyar fita bata kaiga ‘kofa ba ya isketa.”You’re not going anywhere”
Bata ko sauraresa ba ta shigeshi ta hau murd’a handle,hannunta ya matsar ya rufe ‘kofar ya zare key d’in “You’re going to sleep here tonight, now!”Yana gama fad’in haka ya koma ya zauna.
” Dama mana ka yimin gadara tunda ka samu abinda kake so ai ni yanzu I’m useless “Ta fad’a a zuciyarta ‘kwalla ta cika idanunta.
Kan couch ta nufa ta zauna tana kallon handout d’in dan ba karantawa take ba,yana kallonta be sake cewa komai ba ya gyara yayi kwanciyarsa yana jira yaga iya gudun ruwanta.Tafi 1hr a haka daga bisani ta soma gyangyad’i cikin lokaci ‘kalilan bacci ya saceta ta saki handout d’in a ‘kasa.Koda ya d’ago kansa yaga tayi bacci,ganin haka ya mi’ke tsaye ya ‘karaso inda take ya d’auketa ya kwantar kan gadon tare da rufa mata blanket daga gefenta ya kwanta bayan ya kashe light d’in d’akin yana ri’ke da hannunta yana murzawa softly ” I love you “Yayi kissing d’inta a forehead ,shima cikin lokaci ‘kalilan bacci ya d’aukesa.
★★★
Washegari da asubah ta farka,d’akin hasken wata ne kasancewar light a kashe yake ,cikin sauri ta mi’ke ganinta kan hannunsa.Zata sauka daga gadon kuma seta dawo tana ‘kare ma fuskarsa kallo ,cikin kwanciyar hankali yake baccinsa.Gashin kansa ta shiga kalla tana ganin irin cikar sumarshi da ‘kyalli da take kamar yanzu aka shafa mai,a hankali ta mi’ka hannunta kai tana so taji yanayin laushinta.” Very silk”Zuciyarta ta fad’a.Ta shagala sosai daga baya ta sakko kan girarsa tana so tayi comparing da tata,idan ta shafa tata seta shafa tashi ,gashin kanta ta shiga shafawa shima tana so taga na waye yafi laushi,data sake shafa nashi taji nashi ya d’ara nata.”Ai de kad’anne,nima nawan da laushin”Ta fad’a tana guntun murmushi.
Ganin zatai late ta mi’ke ta shiga bathroom, tana shiga ya bud’e idanunsa fuskarsa ya saki ‘kayataccen murmushi dan tun d’azu duk abinda take yana jinta.
“Laila” Ya fad’i sunanta cikin sanyayyar murya.
Koda ta fito ta ganshi zaune bata wani yi mamaki ba dan tayi tunanin ko ‘kofar data buga ne sanda ta fito ya firgita dan tana sani tayi hakan.Jira take taga ze shiga bathroom d’in aiko bata gama sa’ke-sa’ken ba ya shiga.”Da gaske yake wannan”Tayi maganar a ranta.
Ganin yana shirin siyi sallah bayan ya fito tace”Wai kai baka zuwa masallaci?”
“If that is what you want then I will go”
“Eh,ka tafi” Ta fad’a tana waigar da fuska.
Hakan kuwa akai tana tsaya ya fita.”Mutum kullum sallah a gida sekace munafiki,hala a can Canadan baya zuwa”
Sanda ya dawo ta koma bacci,gefen gadon ya zauna yana ‘kare mata kallo blanket d’in yaja mata tare da kissing cheeks nata ya fita daga d’aki,a d’akinsa kuwa laptop d’insa ya d’auka ya shiga dube-dube.
Last chapter
Laila sai 9:04am ta farka daga bacci,bathroom ta fad’a tayi wanka bayan ta fito tayi shirinta cikin riga da wando Pakistan red se d’an ‘karamin gyale tayi yafe dashi ba abinda ta shafa a fuskarta illa spray data fesa ta sauka ‘kasa.A kitchen d’in ta tarar dashi ko meyake sha ma oho tade ga bowl a gabansa yana zaune kan stool ,yitai kamar ba mutum a kitchen d’in,bama tasan mey zata girka ba dube-dube ta shiga yi du abinda take yana kallonta.Mi‘kewa yayi daga zaunen ya ‘karasa inda take “Laila relax,I know you’re here to see me stop pretending and wait for my hello”
Fuska a tamke ta juyo ta kalleshi,kamar zatai magana kuma setai shiru ta bud’e fridge ta d’akko ‘kwai indomie da kwai kawai ta shiga preparing yana daga gefe ya wani sunkuye se magana yake mata baya ko gajiya ita kuwa ta’ki fad’in ‘kala.”Heartbeat please talk to me”
Tana gama had’in da zatai ta nufi gas cooker ta barshi anan yayi yun’kurin sake matsawa gunta kuma ya fasa yayi hanyar fita a dede bakin ‘kofa ya tsaya hannunsa na dama ya d’ora a dede saitin zuciyarsa ya dur’kusa ya soma mur’kususu yana hakin ‘karya.Laila da hankalinta dama yana gun da sauri ta ajje frying pan dake ri’ke hannunta ta ‘karasa inda yake cikin rikicewa ta tallafoshi hannunta ta d’ora kan ‘kirjinsa tasa kuka.”Amjad! Please “
“My heart …it’s ..paining” Yayi maganar da ‘kyar.+
“Please don’t leave me I love you wlhy i’m here for you”Tayi maganar cikin kuka da rud’ani ganin yadda face d’inshi yayi ga jijiyoyinsa sun tashi kamar gaske.
Ta rasa wane taimakon zatai masa daga bisani ta mi’ke ta tafi d’akko waya.Bayan 2min ta dawo kitchen d’in tana searching numbern da zata kira idanta na sauka bakin ‘kofar taga empty place daga gefe taga mutum a tsaye ya jingina da bango hannu d’aya yayi folding a ‘kirji d’ayan kuwa yasa alawa a hannun yana ‘barewa da baki.” You..”Ta ‘karasa inda yake ta d’uma masa dundu a ‘kirji.”Ahhg!”Yayi ‘kara.
“You wanna kill me?” Ya ri’ke hannunta.
“Let me go” Ta fad’a tana kici-kici.
“I love you wlhy please don’t leave me” Ya ‘kwai’kwayi abinda ta fad’a d’azu.
A hankali ta kai masa wani dukan fuskarta d’auke da murmurshi,yana dariya yayi hugging d’inta itama hugging back d’in tayi tana murmushi.
★★★
Yanzu soyayya suke nuna wa junansu sosai a kodayaushe inde suna gida to fah suna tare,Laila yanzu ma ta koma d’akinsa no more ‘buya again.
3 years later
7:09am,Amjad yana kwance bacci yake cikin kwanciyar hankali,beyi aune ba yaji saukan remote control a kansa.Da sauri ya mi’ke yasa hannu ya ri’ke”Stop!”Ya tsawata.
Wata iriyar ‘kara yaran dake zaune kan gadon ya tsala nan take ya fara shararar hawaye kamar fanfo.Cikin kid’imewa Amjad ya mi’ke shhh! ya d’aukesa ya d’ora a cinya se faman lallashinsa yake amma kamar zugashi yake,hannu yasa ya toshe bakin duk dan ya dena amma mey makon hakan se cizo daya gasa masa a hannu.
“Laila!” Ya ‘kwala mata kira.
Tana d’aki tana shirya ‘yar baby dake hannunta wacca bata fi 5month ba,jin yadda ya kira ta tasan ba ‘kalau ba,ko riga bata sa mata ba daga wando se band tsabar rikicewa ta tashi zuwa d’akinsu.
“Mene kuma?” Tayi maganar tana daga bakin ‘kofa.
“Look” Ya mi’ke daga zaunen ya ‘karasa inda take ya mi’ka mata hannun da aka ciza.
“Toh nina yi?” Ta fad’a kamar zatai dariya.
“Allah ya sake sena rama”
STORY CONTINUES BELOW

Yanzu kwa dariya take sosai “Adil d’in zaka ciza,gaka gashi wlhy da anyi cije-cije har ha’koransa nawa just 8 ko twelve fa kai mey thirty two tabb!
Adil dayai cizon ya tsiresu da ido kukan ma ya dena ya kalleta ya kalli Amjad d’in haka yayi tayi.”Zo “Ta mi’ka masa hannu.
Ba musu ya sakko daga kan gadon ya ‘karaso inda take” Mummi ,daddy”Yayi maganar yana nuna Amjad.
“Ya matse ma baki ko,next time ma ya sake cizon zefi haka” Taja hannunsa suka fita.
‘Kofar yayi banging ya koma kan gadon jiya be samu yayi isashshen bacci ba dan tsabar kukan “Ashalina” baby girl d’insu ,ba yadda beyi da laila ba kan take sata nata d’akin amma fafur ta’ki ita seda ita zasi bacci ko Adil seda yayi 10month ta ware masa d’akinsa.
Adil(Mustafa;sunan baba) 1½year kawai ya bawa Ashalina shiyasa komai ya cakud’ewa Laila dan ma Allah yasa ta kammala school wannan year d’in yanzu ta samu relief.
Se 9:30am Amjad ya sakko ‘kasa a dinning ya tarar dasu Adil yana kujerar gefe,kusan shine yayo kamar Amjad sak Ashalina da Mumminta take kama.
“Morning heartbeat” Ya fad’a tare da manna mata kiss a kumatu.”Morning Hayati”Ta amsa fuskarta d’auke da murmushi.
Plate dake gaban Adil ya d’auke cancaras ,a take ya kurma ihu kamar wanda ake cirewa ido,ba shiri ya mayar masa tare da dungure masa kai.”Shut up!”
“Nide ya zama fat ba ruwana na dena d’aukansa na fad’a miki ki dena bashi abinci mey irin wannan.” Cheese, chocolates duk shi kad’ai”.Ya ‘kare maganar tare da zama kan kujera opposite dasu.
“What of my sweetheart(Ashalina)?”Ya tambaya.
“Sleeping” Ta amsa.
“And you let her?”
“Uhm”
“I’m gonna wake her as soon as I’m done with my meal”
“Ka barta mana she’s too young”
“An’ki d’in sanda mike bacci ta dame ni da safe tayi nata no way itama yanzu bazatai ba”
Haka suna yi suna hira bayan sun gama ta mi’ke tattare kwanukan se lokacin ya lura da dress datai,leggings black ne a jikinta se yellow shirt paralyzed hand tayi parking gashinta jelar ta zubo a bayanta. “Looking. se…..” Had’a ido da Adil da yayi yasa ya’ki ‘karasawa.
Mi’kewa yayi daga dinning d’in slide cucumber dake plate d’insa ya caka ya danna wa Adil a baki,ba shiri ya tofar dashi ya d’auke tissue yayi wiping bakinsa kamar yadda yaga anayi.Cije lips Amjad yayi tare da barin dinning d’in ya nufi kitchen .
Tana tsaye jikin drawer taji hug ta baya.”Heartbeat you don’t even care about me now”Yayi maganar a han ankali.
Juyowa tayi tare da zagaye hannayenta a wuyansa”After all why am I here,isn’t it all because of you ? Because of you I decided to came in here wait for my man..”
Shigowar Adeel yasa tayi shiru,gira ya d’aga mata alamar “what?”
Hannunta tayi pointing inda Adil yake,yana tsaye ya tsiresu da ido ko ‘kiftawa ya’kiyi.”Ya Allah “Amjad ya furta tare da furzar da iska daga bakinsa.” Wannan wannan inde muka je Canada baze dawo ba ,kajini you are staying with Mom “Yayi pointing d’insa.
Laila ‘karasawa tayi inda yake ta tsuguna dede tsahonsa.” My boy mey kake so uhm? Chocolate? “
Kai ya girgiza alamar “a’a”.Nan ta sake tambaysrsa ” Cake?”
STORY CONTINUES BELOW

“No,Apple”Ya amsa.
Apple d’in ta d’akko masa a fridge ta mi’ka masa, haka yasa hannu ya kar’ba ya tafi se waige-waige yake.” Ohni”Ta fad’a.
“I’m serious a Canada za’a barshi kina gani ya takura mini” Yayi maganar fuskarsa ba dariya.
“Oh hayati ,calm down”
“A hakan? Bama shi ba Ashalina now maganarta ,you refused to ..”
“Zan maida ita d’akinta nan da few months”
“Months? Geez!”
Ring! Ring! Wayarshi tayi ‘kara haka yasa be sake wata maganar ba ya fita,kallo ta bishi dashi tana murmushi.
★★★
Haka ranar Ashalina ta wuni tana bacci da daddare kuwa ido ‘kiri ta’ki ko gyangyad’i,Laila data gaji ta sata tsakiyarsu itama tayi kwanciyarta ,ko minti 5 ba’ai ba ta fara ihu kamar daga sama yaji ‘kararta aiko a kid’ime ya farka,gefe ya kalla yaga Laila ta rufe ido tana kwance aiko a hankali ya mi’ke ya d’auke pillow d’insa ya nufi bakin ‘kofa ze fita yajiyo muryarta.”Where are you going? “
Yana shafa ‘keya ya waigo”Don’t worry I’m soon coming back I want to see Adil and come back”
“Dawo,dawo he is sleeping comfortable I just came back from his room come back”
“Laila” Yayi maganar kalar tausayi.
Mi’kewa zaunen tayi tare da d’aukan Ashalina dake kuka ta ‘karasa inda yake tsaye ta mi’ka masa ita.” Wait for me here”Ta bud’e ‘kofar ta fita.
Ya rasa inda zeyi da ita ya jijjigata ya d’agata ganin zata shid’e ba shiri ya fito daga d’akin,baki ya saki ganin Laila kwance a parlour se sharar baccinta take,’kararta yasa ta mi’ke tsaye.Girgiza kai kawai tayi cikeda takaici ta kar’beta tana kar’barta tayi shiru dan dama ba yunwa take ji ba,da niyyarsa ya koma ya kwanta sekuma yaji ba dad’i dole ya ha’kura ya zauna dasu ,da ‘kyar suka samu tayi bacci seda ya kwanta rigingine a sofa ya d’orata kan ‘kirjinsa yayita jijjigata a haka tayi bacci shima baccin ya d’auke sa Laila tana d’ayan kujerar itama tayi bacci.
6:30am ,hasken daya kwallare mata ido yasa ta farka da sauri,6am taga agogon ya nuna.A kasalance ta mi’ke kanta yayi mata nauyi ta aza idonta kan Amjad dake ta bacci Ashalina a kan ‘kirjinsa itama baccin take,’karasawa tayi inda suke tasa hannu ta d’auketa dede lokacin ya bud’e ido.Ganin ya makara yayi saurin mi’kewa shima a gajiyan yake haka suka koma sama,nan yayi shirin office d’insa Laila kuma ta sakko shirin breakfast,Amjad a tsattsaye yayi breakfast ya wuce office dan ya makara sosai ita kuma ta kama aikin gida tayi wannan tayi wancan kan ace mey lokaci yaja mutuniyar kuwa se 9am ta farka 12 bayan anyi mata wanka ta koma bacci (Mata muna aiki😓).
Ko 2 weeks ba’ai ba suka tafi Canada dan tunda aka haifi Adil basi je ba rabon da suje tun da cikinsa,Mom se nan -nan ake dasu ‘yan jikokinta Adil da Ashalina kamar ta lashe su.Adil ta’bara se abinda ya ‘karu abinda yake so shi Mom suke masa.Duka familyn suka ware rana suka je park ranar sun wataya pictures ba adadi kamar karsu koma,Laila seda sukai 3 weeks cir suka komo gida.
2 days da dawowarsu, furnitures na d’akinsu yau suke sakewa Laila tana kwashe kayan drawer taga picture na Amjad tare da wata baturiya ya dafe kafad’arta su biyun duk sunyi dariya a photo d’in data kalli date taga kusan 6 years da d’aukan picture d’in.Wani irin kishi taji ya tokareta hoton ta yasar ta tashi aikin ma ta fasa,Amjad ta gani tsaye bayanta picture d’in ya kalla sannan ya kalleta.”My heartbeat “Ya ‘karasa inda take.
Gefe ta kauda kanta ta tamke fuska tare da nad’e hannu a ‘kirji.
” This “Ya sunkuya ya d’akko picture d’in,hannu biyu yasa ya yaga into pieces yasa a shara tana kallo.” Shikenan?”Ya tambayeta.
Kallo d’aya tayi masa ta fita dukda taji relief.Wajejn 8pm ya dawo daga masjid dede lokacin ta gama waya da Mami, tana ganin shigowarsa d’akin ta soma d’aga yatsun hannunuta se wasa take dasu sunsha ‘kunshi red.”Wow! heartbeat I love this “Ya ‘karaso ze ri’ke hannun ta d’auke.
” What?”Ta tamke fuska.
“Laila henna”Yayi maganar yana zama kusa da ita.
” Ok listen to me”Ta gyara zama ta d’ora ‘kafa d’aya kan d’aya.
“I’m all ears”
“Amjad,I ..I ” Ta’ki ‘karasawa tana kallon reaction d’insa a yanzu. Sosai ya bada attention a abinda zata fad’a.”I’m pregnant “Tayi maganar a ta’kaice.
A razane ya zaro ido kamar zeyi kuka” Laila you’re p…”
Dariyar data shiga yi ne ya tsayar dashi,harda ri’ke ciki tana nuna shi.”Ka fiya tsoro”
“Kansa ya waigar yasha kunu ” You scared me”
“Ooh come on my man I’m just joking” Ta dafe kafad’arsa.
Juyowa yayi har lokacin fuskarsa a tamke seda tasa hannu biyu ta kama kunnenta ya saki fuskarsa.”Let me see this”Ya ri’ko hannunta.
Waje guda ya had’a hannayen nata ya manna musu kiss.”Looking pretty always “
Murmushi ta shiga yi tana kallonsa bata ce komai ba,d’agowa yayi yana kallonta daga baya ya jata jikinsa yana shafa bayanta.”I love you heartbeat “
“I love you too Hayati”.
Alhamdulillah
Anan na kawo ‘karshen littafina mai sunaAmjad,abinda na rubuta ba dede ba Allah ya yafemin.