ARZIQI RABO CHAPTER A

 ARZIQI RABO CHAPTER A

Kano 

Gidane madedeci d’aki biyu yake d’auke dashi tsakar gidan ma ba wani fad’i gareshi ba.Sede ba lefi gidan ya tsaru ga shafe da akai hakan ya nuna alamar ba a dad’e da tarewa ba.Cikin sitting room kuwa yanda aka ziba kujeru masu tsada ba za’ace a wannan gidan suke ba d’akin gado ma haka furnitures ne tsadaddu d’akin kansa da’kyar ya iya d’aukan gado ,wardrobe se a d’ayan d’akin aka sa.+

      Wata mace na gani a d’akin wadda ke zaune kan kujerar mirror tana tsara d’auri ,mashaAllah kallo d’aya zakai ka gano kyau da take dashi ,fara ce amma ba irin tass d’innan ba gata da hanci dogo haka girarta ma sirira lips nata yasha maroon janbaki ga earings da necklace nata masu stones green,tana sanye da atamfa green me d’auke da ratsin orange da black .Kayan jikin nata sosai sun d’auketa chif a jikinta,koda ta mi’ke bayan ta kammala d’auri na lura da tsahonta medium ce domin baza a kirata gajeriya ba haka baza a kirata doguwa ba  gashi batada ‘kiba .

     Wayarta ta d’akko dake kan gado ,call log naga ta shiga inda tayi dialing suna “My Dear”.Ba jimawa akai answering ta d’ayan ‘bangaren ” My Azizaty” aka fad’a.

      “Dear naji shiru baka taho bane?” Ta tambaya murya ‘kasa-‘kasa.

      “Azizaty sorry! Umma ce ta tsayar dani kinga amma yanzunnan zaki ganni”. Ya fad’a.

     ” Toh shikenan kagaida min ita”.Ta fad’a.

     “Yawwa my azizaty sena dawo”.Ya fad’a.

     Bayan ta katse wayar ne tayi hanging tare da sakin murmushi ,fuskarta ta sake kalla jikin mirror d’in sannan ta fita daga d’akin.

     Bayan like 10minute tana zaune a sitting room ta jera tray da sauran jug da cup ga warmers a kai ,tana danne-danne a wayarta tajiyo knock. Ba ‘bata lokaci ta tafi bud’e ‘kofar ,koda ta isa soron ta jiyo muryarsa yana waya lalla’bawa tayi ta bud’e ‘kofar da sauri ta la’be bayan ‘kofar.

    Yana shigowa kafin yayi wani motsi yaji an rufe masa ido da tafin hannu ,jin ‘kamshin turarenda ke sanyaya masa rai yasa yayi saurin sakin murmushi.

     ” Azizaty! “Ya kira sunanta.

     ” Na’am Dear sannu da dawowa”.Ta fad’a bayan ta sauke hannunta.

        “Wow! Azizaty irin wannan kyan haka ai seki sa na kasa shiga ciki”. Ya fad’a harda zaro ido.

      Wani murmushi ta saki wanda ya sake bayyana kyawunta.” Toh ka taimaka mu shiga”.Ta fad’a.

STORY CONTINUES BELOW

     Hannunsa cikin nata suka ‘karasa har d’aki.”Dear wanka zaka fara yi ko abinci zaka ci tukun?” Ta tambaya tana jiran amsarsa.

      “Duk wanda kika za’ba min Amarya ta” Ya amsa.

     “Toh na za’ba ,ka fara yin wanka”.Ta amsa.

     Da kanta ta tayasa rage kayan ya shiga wankan,cikin ‘yan mintina ‘kalilan ya fito.Shirinsa yayi cikin T-shirts fara se jeans blue ,sosai yayi kyau.

    Ahmad mutum ne me tsaho gashi fari ne wanda yama d’ara ta, baida ‘kiba sede ba siriri bane yana da murd’ewar jiki dede.Wajen kyau ma ba abarsa ba tsakanin shi da ita banga wanda zai nuna wa wani kyau ba sede fari daya d’areta.

      ” Harka gama shirin?” Ta tambaya lokacinda ta shigo d’akin.

   “Iyye Azizaty baki taya niba ina kika shiga?”

    “Daga shigarka toilet nayi ba’ki” Ta amsasa.

    “Ba’ki? Toh yanzu ya za’ai dani?” Ya tambaya kamar wani yaro ‘karami.

    Yadda yayi maganar ne yasata murmusa “Nasanki kina yin ba’ki zaki shareni”. Ya fad’a.

  

     ” A’a bazan shareka ba bari na kawo ma abincin d’akin”.Ta furta.

    Sitting room d’in ta shiga ta d’akko abincin ta mayar d’aki,su kuwa ba’kin ta d’ebo masu wani a kitchen. Koda yaga ta dawo d’akin ya tamabayeta”Ba’kin naki fa?”

    “Yara ne fah kuma na zuba masu abincinsu “. Ta amsa.

    ” Ok “.Ya fad’a.

  

     Zama yayi a kan sallayar data shimfid’a ,yana kallo ta gama zuba abinci tasa spoon.” Dear na zuba ma”.Ta fad’a.

     “Toh se yaya kenan?” Ya tambaya yana kallonta.

      “Se ci”. Ta amsa.

      ” Nikuma hannuna baze iya chiba”.Ya fad’a.

    Yana fad’ar haka ta gane me yakeke nufi,da kanta ta d’auki spoon d’in ta fara basa. “Ke fah baza kici bane?”

    “Ni ai naci nawa”. Ta amsa.

    ” Kefa kika ce zaki jirani mici tare”.

    “Toh ba kaine ba se 3 ka dawo”. Ta fad’a cikeda shagwa’ba.

    Tana birgesa idan tayi hakan ,kallonta kawai ya tsaya yi ” Ayya my Azizaty sorry nima nafiso mike ci tare “.Ya fad’a tare da tallafo ha’barta.

     “Yawwa dear shine baka bari minje wajen umma ba tare koh kayi min wayo”. Ta fad’a.

      ” Kinsan nikaina bansan zanje ba,ina makaranta umma tayi mini waya wasu ‘yan uwanta daga zaria sunzo shine fa naje muka gaisa”.Ya fad’a.

     “Ayya da ka kawosu nan mun gaisa”.

     ” Ai ba kwana zasi ba ba lokaci da na kawo su”.Ya fad’a.

      A haka tana bashi suna hirarsu har ya ‘koshi,bayan data gama had’a kwaninka takai kitchen ta koma wajen yaran da suka zo.

        Wannan ma’aurata Reyhana da Ahmad sun kasance masu ‘kaunar junansu,kafin suyi aure seda aka kai ruwa rana.Mahaifiyar Reyhana fafur ta’ki yarda Ahmad ya auri ‘yarta ,ba wani dalili bane illa saboda talaka ne ,da’kyar mahaifin Reyhana ya tsawatar mata haka bataso ta ha’kura akai auren.Ahmad  tun yana ‘karami mahaifinsa ya rasu,se dangin mahaifiyarsa ne da’kyar suka d’auki nauyin karatunsa na secondary dan dangin mahaifinsa basuda hali sosai kuma duk cikinsa kowa ya’ki d’aukan nauyin sa.A haka bayan ya gama secondary school yana ‘yan bige-bige ya shiga college yayi diploma.Kasancewar halin rayuwa da ake ciki da’kyar ya samu aiki a wata private yake teaching albashinsa ba yawa gareshi ba kunsan private school. Koda yazowa da umma mahaifiyarsa zancen auren Reyhana da farko bata goyi baya ba dan tasan Reyhana ta kere masa, yarinya ce data taso cikin gata ,iyayenta masu kud’i ne gasu ‘yan boko. Haka yasa Umma ta tsorata,ganin Ahmad ya’ki ha’kura kuma taga irin son da Reyhana ke masa yasa ta ha’kura ta bisu da addu’a.Momyn Reyhana kuwa da danginta sun tsani auren ,Abbanta ne kawai ya goyi baya, toh wannan kenan.

STORY CONTINUES BELOW

   Around 8:18pm bayan ya dawo daga masjid ,a d’aki ya isketa .”Azizaty am back “.Ya fad’a tare da zama kan gadon gefenta.

     ” Sannu da dawowa”. Ta fad’a tana murmushi.

     “Yawwa “. Ya fad’a tare da d’ora kai a cinyarta ya kwanta.

      “Ya labarin school d’in?” Ta tambaya.

     “Azizaty d’alibai rashin ji suna chaza min kai”.Ahmad ya fad’a tare da ri’ko hannunta ya d’ora kan cikinsa.

      ” Allah Sarki dear gashi kaikuma baka son hayaniya”.Reyhana ta fad’a d’ayan hannun nata tana shafa kan sumarsa dake d’auke da gashi yale-yale na Fulani d’innan gashi ba’ki.

     Hakan yasa ya rintse idanunsa kamar me barci.”Yes Azizaty dad’inta ma ina dake kinga kece me kwantar min da hankali a kodayaushe that’s why kullum position naki a ‘kalbi na ‘karuwa yake”.

    Murmushi ta saki wanda hatta ha’korinta seda ya bayyana ,tana jin dad’in kasancewa da mijinta ita kad’ai tasan halin abinta se Umma kankat ,Reyhana tasan Ahmad d’inta da rashin magana cikin jama’a amma ita a gunta daban ne tasan yadda zata bi dashi.

     “Yaushe toh za’a tsayar da ranar zuwa wajen Umma mu gaisheta?” Ta tambayesa.

     Shiru taji be amsa ba,data kalli fuskarsa kuwa taga yayi bacci ma.D’an murmushi ta saki, wayar ta dake gefe ta d’auka tayi ta ‘kyasta masa photo. Itama daga baya baccin ta soma ji ,a hankali ta shafa fuskarsa.”Dear 9:30 yayi ka gyara kwanciyar kar wuyanka ya ‘kage”.Ta fad’a a hankali.

      Kasancewar baida nauyin bacci yasa ya farka”Azizaty amma de ‘kafanki beyi tsami ba koh?”

      “Uhmm beba”. Ta amsa.

Tashi yayi daga kwanciyar ” Toh kema kiyi shirin kwanciya mu kwanta yanzu kema da wuri zaki kwanta”.Ya fad’a.

     Tashi tayi ta fad’a toilet dake d’akin tayi wanka tukun bayan ta fito ta sanya sleeping dress,shima already yayi shirin kwanciya.”Azizaty let sleep”.Ya fad’a tare da mi’ka mata hannu.

     Mi’ka masa nata tayi ,yana sani ya janyo ta ta fad’o jikinsa.”Kai Azizaty kinyi nauyi dayawa kinjiki kuwa”.Ya fad’a cikeda tsokana.

      “Nid’in ce nayi nauyi”. Ta furta tana gyara kwanciyarta.

      ” To shiru a kwanta”.Ya fad’a tare da kashe light d’in ya jawota jikinsa sannan ya jawo blanket ya rife.

       “Sleep tight”. Ya fad’a.

        ” Uhm”. Ta furta.

     Ba dad’ewa bacci ya kwashesu duka.

                  ****

    Washegari kamar ko yaushe 5:30am sun tashi ,ko Reyhana tayi sallah bata komawa bacci seta ga fitarsa,ita take tayasa shiryawa tayi  breakfast.

       “Azizaty! ” Ya kira sunanta .

     Tana kitchen ta taho”Dear kirana kake?”

       “Eh Azizaty kinga wani littafi ajje a kan drawer?” Ya tambayeta .

      Kad’a masa kai tayi tareda nufar inda drawer d’in yake. Jawo drawer d’in tayi  sanannan ta ciro littafin.

     “Gashinan”. Ta mi’ka masa.

      ” Thanks my wife”. Ya fad’a yana murmushi.

       Tana birgeshi yadda take kula dashi haka property nashi ma bata bari ba.

       “Ka gama shirin kenan?” Ta tambaya.

     “Yes Azizaty”. Ya amsa.

     ” Toh ga breakfast is ready”. Ta fad’a.

      “Wow! My wife hancina kina kasheshi da ‘kamshi”. Ya fad’a sanda ya bud’e sauce d’in ,plate kuma soyayyen dankali ne.

     Da kanta ta had’a masa tea d’in ,danma yayi late shiyasa sauri-sauri yaci.

     ” Allah ya kiyaye hanya”.Ta furta sanda ta rakoshi soro.

      Sunkuyowa yayi kad’an ya manna mata kiss a kumatu.

     “Sena dawo”. Ya fad’a.

     ” Bye”.Ta fad’a tana waving hannu.

    Bayan data kammala nata breakfast d’in ta tattare kwanukan ta wanke ,se sauran gyaran data ‘karasa,kan gado ta hau abinta ta koma barci.

Reyhana ba ita ta tashi ba se wajen 11:10am,wanka tayi tayi shirinta cikin material blue ya d’auketa sosai.Kitchen ta shiga ta d’ora tukunya tana canki-cankin me zatayi kuma tasan shi Ahmad ba ruwanshi ko ta kira ta tambayeshi ba za’ba zeba.Daga ‘karshe de ta yanke shawarar yin tuwon semovita da miyan alayyahu.
     Around 12:00pm ta kirasa a waya,lokacin yana class ya fita tukun yayi picking.
     “Azizaty!” Ya kira sunanta.
    “My dear ya school d’in yau?”
    “Kinganni ina class ma na fito”. Ahmad ya fad’a.
     ” Ok, toh go back to your student seka dawo”. Ta fad’a.
     “Toh my wifey sena dawo”. Ya fad’a.
    Daga haka sukai sallama,komawa tayi kan girkinta dama miya ya rage ta gama.
               ***
   2:23pm Ahmad ya dawo gida,Reyhana kuwa tuni ta kammala komai ta sake dusting powder a fuskarta se lipgloss data ‘kara a lips d’in.
       Tana jiyo knocking nasa tayi saurin fita,ba ‘bata lokaci ta bud’e ‘kofar.Bata ankara ba taga yayi hugging nata.
      ” My dear mutanen waje zasu hangomu fa”. Ta fad’a.
  
     “Ina mutanen suke azizaty banga kowa ba”. Ya fad’a dan unguwar ba hayaniya sosai.
     ‘Kofar ya tura ya rufa tukun yayi breaking hug d’in.” Kinyi missing d’ina ma kuwa azizaty? ” Ya tambaya.
     “Meyasa kace haka?” Ta tambaya.
     “Ehmana naga kamar baki missing d’ina ba”.
     ” I do mana”.Ta fad’a tana turo baki.
     “OK if you miss me then”. Ya fad’a tare da nuni da kumatunsa alamar tayi masa peck.
       Murmushi tayi tukun tayi d’age nan tayi masa peck.
      ” That’s my Azizaty “. Ya fad’a tare da tallafota jikinsa.
       Kamar koyaushe ta kai masa ruwan wanka toilet,bayan ya shirya kuma ta kawo masa abinci.Yau tare suke cin abincin dan itama bata ciba,suna ci suna hira.
       ” Yawwa my d yaushe zami je gaida Umma?” Reyhana ta tambaya.
      “Kede kawai kina so kiji yaushe zaki wajen mommy”. Ya fad’a yana mata dariya.
      ” Laaa! Ni ba haka nake nufi ba”. Ta fad’a.
      “Zaki wayence ba”. Cewar Ahmad.
      “Toh shikenan baka amsan tambayata ba”. Ta fad’a.
      ” Reyhana yau har kwanakin nawa a gidannan ma tukun?”
      “Kwana fa kace? Ana maganar wata fa kenan”. Ta amsa da sauri.
      ” A’a azizaty baki kaiba de”.
      “Toh na lissafa ma?” Ta tambaya.
      “Eh lissafa”. Ya amsa tare da tattaro attention d’insa kanta.
      Reyhana kuwa sosai ta fara lissafi tiryan-tiryan hadda yatsu a lissafin nata,yadda take lissafin ya bashi dariya sekace ‘yar yarinya.” Toh my azizaty na yarda”. Ya fad’a.
      “Kaga harna ‘kara kwana biyu akai ma”. Ta fad’a.
      ” Gaskiyarki uwargida”. Ya fad’a cikeda zolaya.
STORY CONTINUES BELOW
      Kallonsa kawai tayi tana jiran mey ze ce akai.”To shikenan ki shirya a week d’innan”.
     “Toh Allah ya kaimu”. Ta fad’a dukda ba haka taso ba tafi so yace ga ranar.
     ” Ko bakya so mu bari wani watan? ” Ya fad’a yana kallon reaction nata.
      “A’a inaso”. Ta fad’a da sauri.
      ” Sorry,da wasa nake”. Ya fad’a yana mata murmushi.
       Haka suka kammala cin abincin,koda zata d’auraye kwanukan tare suka wanke.Bayan daya je sallar asr ya dawo nan suka cigaba da hirarsu.
      “Nikam yau baza ka duba takardun d’aliban naka ba ?” Reyhana ta tambayeshi kanta akan cinyarsa.
       “Azizaty yau banyi musu test ba ai”. Ya amsa ta.
      ” Ok toh ya school da students naka?”
      “Ba sau’ki nake fad’a mini,thank god ina da gimbiya mey sani farinciki”.Cewar Ahmad yana shafa girarta.
       ” Ayya My dear “. Ta furta.
            ****
2days later
      Reyhana  wajen 4:12pm bayan ta idar da sallah tana zaune sitting room tana kallon Bollywood sega Ahmad ya dawo daga masjid.
      ” Sannu da dawowa”. Ta fad’a.
    
        “Yawwa”.
       “Azizaty ki shirya muje mu gaida mommy”. Ya fad’a tare da zama gefenta.
     Da sauri ta kallo inda yake” Da gaske?”
       “Bakyaso ne?” Ya tambaya fuskarsa a sake.
       “Wane? Yanzu zan shirya”. Ta fad’a tare da mi’kewa tsaye.
      D’aki ta shiga da sauri ta sauya kaya,lace tasa maroon da torches golden, se necklace nata golden me kyau,ta fesa turare me taushin ‘kamshi gyalenta ta yafa golden ta zira flat shoe se purse data sa phone d’inta.Duk wannan shirin befi a 10min ba dan gani take lokacin kamar ze ‘kare.
      ” My dear am ready”. Ta fad’a tana murmushi wanda har ha’koranta seda suka bayyana.
       “Iyye! Azizaty kamar wal’kiya har kin shirya?” Ya fad’a yana kallonta.
       “Eh na shirya”. Ta amsa.
       ” Zumud’i d’in kenan”. Ahmad ya fad’a tare da mi’kewa.
    Bayan ya kashe TV d’in ya fito ,seda ta tabbata ta rufo ko ina tukun suka fito.
    Abin gwanin sha’awa da suka jero.”Gaskiya next time zamu fita niqab zaki sa”. Ya fad’a yana d’an ‘bata rai.
     “Haba niqab “. Ta fad’a tana d’an turo baki.
     ” Bakiga ana kallemin keba?” Ahmad ya furta.
     Shiru tayi bata ce komai ba ,napep ya tsarar masu suka hau.
      “Gaskiya na dad’e banga gari ba ji nake kamar na shekara”. Reyhana ta fad’a tana kallon waje.+
       ” Just a month d’in ? Aiko ki saba “.Ahmad ya fad’a.
      A haka suna ta hirarsu har suka ‘karasa gidan,Ahmad bayan ya sallami me napep d’in suka shiga ciki.Da Baba me gadi suka fara cin karo a gate ,ganin su ya washe baki dama shi mutum ne me barkwanci.” Ahh yau Hajiya Amarya ce a gidan”.Ya fad’a.
       “Baba ina wuni”. Ta gaishesa.
     ” Lafiya qalau Reyhana”.Ya amsa.
     Ahmad hunnu ya mi’ka masa suka gaisa,daga nan suka shiga.Koda suka shiga makeken parlourn shiru kamar ba kowa,chan kuma bayan sunyi sallama sega Ikram ‘kanwar Reyhana ta sakko “Laa! Yaya Reyhana dama kece ? “
STORY CONTINUES BELOW
     ‘Karasowa tayi da sauri inda take tana murnar ganin yayartata “Sannu da zuwa yaya”. Ta fad’a tana murmushin jin dad’i.
     Itama Reyhana da farinciki fal a ranta take magana ” Yawwa Ikram”. Ta amsa.
      Tana ri’ke da hannunta suka zauna,Ahmad na d’ayan kujerar Reyhana kuma suna wata daban.”Ya Ahmad ina yini”. Ikram ta gaisheshi.
      “Lafiya lau Ikram, ya gidan?
      “Lafiya lau”. Ta fad’a.
     ” Bari na fad’a ma momy”. Ikram ta fad’a tare da mi’kewa.
      Momy tana d’aki ta hakimce tana kallon TV Ikram ta shiga.
      “Mommy yaya tazo”. Ikram ta fad’a.
       Mama da sauri ta d’ago kanta ta kalleta “Reyhana kuma da yammannan?” Mommy ta fad’a tana sake so ta tabbatar.
      “Da gaske Mommy tareda ya Ahmad ma take”. Ikram ta amsata.
     Jin an ambaci Ahmad yasa Mommy ta had’e rai.Kamar bazata tashi ba ta mi’ke zuwa parlourn.
  
     Ahmad yana ganin Mommy ta ‘karaso yayi saurin sakkowa daga kujerar.” Ina yini Mommy “. Ya gaisheta.
      ” Lafiya lau”. Ta amsa ba wani walwala tattare da ita.
      “Mommy ina yini”. Reyhana ma ta sunkuya ta gaidata.
     Bakinta a ta’be ta amsa wanda duk cikinsu ba wanda ya kula.Tana me mamakin yadda ‘yartata ta tsunduma kanta a wannan irin rayuwar dan gani take kamar a takure take.
     Reyhana ce ta katse shirun da d’akin ya d’auka da tambayar” Abba be dawo ba ?”
      “Eh be dawo ba”. Ta amsa.
      Mommy ko ‘kala bata cewa inba wai Reyhana ta tambayeta ba.Suna zaune a haka su Bassam da Walida(‘Kannen Reyhana) suka dawo daga islamiyya.Da gudu Walida ta ‘karaso tana mata oyoyo.
      ” Walida ‘yan mata an dawo”. Reyhana ta fad’a tana rungumo ta.
      “Eh yaya,dama zaki so?” Ta tambaya.
      “Eh gani na zo”. Ta amsa tana murmushi.
     Bassam shima ‘karasowa yayi ya gaida Ahmad sannan ya gaida ta,itama Walidan se lokacin ta lura da Ahmad ta gaisheshi.
       ” Toh Walida aje a sauya kaya “.Ikram ta fad’a lokacinda ta ‘karaso.
     Ma’ke kafad’a tayi wai bazata bar yaya ba.” Good girl jeki ki cire uniform d’in kinji seki dawo ina nan”.Reyhana ta fad’a tana lalla’bata.
      “Toh”.Ta amsa sannan ta kyalla da sauri zuwa d’aki.
       Shima Bassam nashi d’akin ya wuce.Inno(me aikinsu) ce ta kawo musu abinsha bayan sun gaisa.Mommy tashi tayi ta koma d’aki dan zaman ya isheta,se Ikram da Walida suna zaune kusa da Reyhana.
        Reyhana itace ‘yar fari a gidansu,su biyar ne duka.Maza biyu mata uku,daga Reyhana se sageer ,Ikram,Bassam then Walida auta.Reyhana nada shekara 1½ aka haifi sageer saboda haka basuda tazara sosai.Reyhana tana da shekara 22 a yanzu se shi 20½,Ikram tana da 18 yrs,Bassam 15 then Walida 9yrs suna da tazara.
      Reyhana tana kammala degree nata ta auri Ahmad dan karatunta yayi sauri ko secondary school da wuri ta gama,Bsc microbiology ta karanta.Sageer a yanzu haka yana level 2 MLT yake karanta,Ikram kuwa year d’innan tayi graduation na secondary se Bassam yana SS1 Walida kuma primary 3.
      Mommy kuwa business woman ce tayi-tayi Abba ya barta tayi aiki amma ya’ki ,shiyasa business ta du’kufa kuma dama a gidan su yawanci ‘yan kasuwa ne.Abba kuwa babban professor ne a university Buk.
     Sun kasance happy family kuma yaran sunfi sabo da Abbansu musammman Reyhana da Sageer kasancewar Mommy mace me zafi ,Abba yafi ta sau’kin kai.Toh wannan kenan.
      Wajajen 6:00pm Abba ya shigo ,cikin rissinawa ya gaishe da Abba itama Reyhana haka.”Kice yau kune a gidan”.Abba ya fad’a fuskarsa a sake.
      “Eh Abba d’azunnan muka zo”. Ta amsa.
   
     ” Toh mashaAllah yayi kyau Allah yayi albarka”. Ya fad’a.
       “Ameen” .Suka amsa.
      Daga baya Reyhana d’akinsu ta wuce,sukuma mazan suka tafi masjid tare da Ahmad.
      Mommy seda taji fitarsu ta fito daga d’akinta ta shiga d’akin Ikram ,da tare suke kwana sanda Reyhana tananan yanzu kuwa ita kad’ai ta’ki bari Walida ta komo d’akin.
      “Ana san a had’u ayi ta hira da ‘yan uwa amma baza a dinga waya dasu ba”. Mommy ta fad’a sanda ta ‘karaso.
    
         ” Laaa! Mommy ina fa kira”. Reyhana ta fad’a.
      “Ba wani,kuma da kika san zaki zo ba seki fad’a ba”. Cewar Mommy tana shirin zama kan wani kujera dake d’akin.
      ” Nima bansan da zuwan ba jinai kawai yace na tazo muzo gida”.Reyhana ta fad’a.
      “Toh seku tashi ai kuyi sallah”. Mommy ta fad’a.
     ” Mommy idan zasi tafi zan bisu”. Walida ta fad’a kanta a cinyar Reyhana.
     “Base ki bisun ba,tashi ki wuce ki sallah!”. Mommy tai mata tsawa.
      Ba Walida ba har Reyhana seda taji ba dad’i” Mommy meyai zafi haka ?” Reyhana ta furta.
      Mommy ko amsata batayi ba ta fice daga d’akin,Reyhana kallo kawai ta bita dashi a ranta tana fad’in Allah ya kawo ranar da zata dena jin haushin aurennan nata…
Bayan sun idar da sallah ne ikram ta d’akko mata wasu hotunan na bikin ta da bata gani ba.
     “Yaya kalleki a nan”. Ikram ta nuna wani pic da Reyhana ta rife idanunta.
     Dariya dukansu sukai suka cigaba da kalla.Misalin ‘karfe 7:08pm Inno ta gama abinci lokacin Abba suna parlour shida Ahmad suna ‘yar hira.
     Bayan an kawo wa Ahmad abincin Abba ya tashi domin ya bashi waje dan ya kula ya kasa sake wa.Reyhana kuwa a d’aki suka ci tare da Ikram.
       Sageer shima lokacin ya shigo ,hannu ya mi’kawa Ahmad suka gaisa.” Sageer ya school?” Ahmad ya tamabaya.
     “Alhamdulillah,kun shigo kenan?”
     “Eh d’azunnan”. Ya amsa.
     ” Ok,bari na watsa ruwa “. Sageer ya fad’a.
       D’akinsa ya wuce ,Reyhana kuwa ta shantake kamar bazata tafi ba hira ta’ki ‘karewa.
  
      Koda ya gama yana zaune shi kad’ai a parlour sega kuma Sageer harya fito.D’an hira suka soma yi har lokacin isha’i yayi.Suna dawowa daga masjid yayiwa Reyhana text.+
    ” Toh Azizaty se a fito dare yana yi”
       
      Tana gama karancewa ta kalli agogo taga 8:13pm,nan take ta sauya fuska dan ji take kamar karta tafi sosai tayi kewar gida.
     “Ya de?” Ikram ta tambaya dan ta lura da chanjin fuskarta.
       “Ya Ahmad ne wai na fito mu tafi”. Ta amsata.
       ” Ayya! Yaya amaryar Ahmad “.Ikram ta fad’a cikeda tsokana.
      ” Zan doke ki Ikram”. Reyhana ta fad’a.
      “Sorry sister nice fa”.
      ” Toh ni ba wannan ba,yaushe zaki zo ki yinammin?”
       “Au wuni kad’ai zaki gayyaceni watoh banda kwana koh?” Ikram ta fad’a tana kallon Reyhana.
        “Ke dallah idan kwananma nace ai ‘bata bakina zanyi”. Ta fad’a.
       ” InshaAllah zanzo bada dad’ewa ba yaya, yanzu de muje parlourn kar ya Ahmad yaji shiru”. Ta fad’a.
     Parlour suka sauka se kuma suka iske Mommy ma tana parlourn gefe Abba da alama shiya kirata ta sakko da bazata zo siyi sallama ba.”Reyhana kun fito kenan”. Abba ya fad’a.
     “Eh”. Ta amsa sanda ta ‘karaso.
      ” Sageer ashe ka dawo?” Cewar Reyhana.
       “Eh tun d’azu ,kina d’aki kunata hirarku”. Ya amsata.
       ” Toh ya school? “
       “Alhamdulillah”. Ya amsa.
         Abba ne ya bawa Sageer key d’in motarsa yace akaisu gida,Mommy kuwa ta’be baki tayi taso yace akaisu a tata da anga tsiya.A haka sukai sallama itade Mommy fuskarta ba sakewa.
    Har ‘kofar gida Sageer ya kaisu ,bayan sunyi sallama ya juya.Koda suka shiga gida ba light shiyasa da wuri suka kwanta tunda dama sunci abinci a gida.
                 ***
  Washegari 7:20am Ahmad ya gama shirinsa har breakfast ma ya kammala.”Yau me za’a dafa da rana?”Reyhana ta tambayesa.
          ” Ni duk abinda kika dafa yayi”. Ya amsata yana zira takalmi.
         “OK dear seka dawo toh”. Ta fad’a tare da mi’ka masa hularsa.
STORY CONTINUES BELOW
          ” Wata’kila sena yi sallar juma’a zan dawo”. Ya fad’a.
         “Ohh na tuna yau Friday koh”. Ta fad’a.
         ” Duk wannan kwalliyar danai baki tuna bama? Wait kinko ce nayi kyau ma?” Ahmad ya fad’a ya tsireta da ido.
        “Laa na fad’a abinda ma ko yaushe kyau kake, kawai de na sha’afa”. Cewar Reyhana tana murmushi.
         ” Au hakane ,toh sena dawo Azizaty karnayi late”.
       “A dawo lafiya”.Ta fad’a.
       ” Ameen”.Ya amsa daga nan ya fita.
     Kamar koyaushe nan da nan tayi aikin gida tayi wanka ta shirya tsaf cikin atamfa blue me ratsin fari da ba’ki.Ga turaren wuta daya turnu’ke ko ina Reyhana bade tsafta ba.
      Wayarta ta d’auka ta kira Saudat (‘kawarta ) tare sukai secondary school.
   
       “Amaryar Ahmad kin ya dani,daga kaiki gidanki se mijiki li’kwi bako flashing?”
        “Saudat da sharri yanzu gashi na kira ki ,kece ma kika manta dani baki zo ba”. Reyhana ta fad’a.
         ” Ina tafe ai ki shiryan kayan dad’i”.Saudat ta fad’a.
        “Karki damu zaki zo ki kwashi girki na”. Cewar Reyhana.
         Sun dad’e suna hira kafin daga baya siyi sallama.11:30am ta d’ora abinci ,a  hr d’aya da ‘yan mintina ta kammala ,zo’bo ta had’a shima nan danan tasa a fridge.
             ***
  Gidan Mommy..
         Tana d’akinta  ,wata yayarta(Anty asma’u),suna d’asawa kusan halinsu yazo d’aya.
        ” Ya amarya a gidanta?” Anty Asma’u ta tambaya.
        “Uhmm! Tana gidanta jiya ta shigo ma”. Cewar Mommy tana ta’be ba’ki.
         ” Ita kad’ai ko harda Ahmad d’in?”
         “Ita dashi ne”.Mommy ta amsa.
         “Toh ke yaushe zakije keda Abbansu?” Ta tambayi Mommy.
         “Sede shi yaje dan ba zuwa zan ba,wannan d’an ‘kurbibin gidan”. Cewar Mommy.
        “Toh ya za’ai ? Yaran yanzu ne bajin magana suke ba kana d’ora su a hanya suna kaucewa”. Anty asma’u ta fad’a.
       ” Ai du Abbanta ne wlhy badan shiba da ba abinda zesa na yarda da aurennan”.Mommy ta fad’a.
      “Eyyi ita dad’i miji zata gane me ake nufi rabu da ita”. Anty asma’u ta fad’a.
       ” Ni abinda yake sake cimin rai shine ko a karatu ta masa nisa shekarun kansu befi uku  ya bata ba yaro ne shakaf amma ita ta rife ido seshi”.
      “Allah de ya sawwa’ke”. Anty asma’u ta fad’a.
     ” Ameen “.Mommy ta amsa.
                  ***
1:45pm Ahmad ya dawo gida ,koda ya shiga d’aki bata ciki suitcase d’in ya ajje ya fita zuwa sitting room.” Laa! Dear yaushe ka dawo banji ba?” Reyhana ta fad’a tare da ‘karasowa inda yake.
         “Azizaty najiki shiru ne”. Ya fad’a.
    
         ” Sannu da dawowa toh “.Ta fad’a.
        ” Yawwa Azizaty”.Cewar Ahmad tare da rungumota jikinsa.
        “Bari na  kawo abinci dan naga se hamma kake”.Reyhana ta fad’a tare da yin dariya ta fita bata jira me zece ba.
       Girgirza kai kawai yayi yana murmushi dan kuwa bata yi ‘karya ba tun daya baro school ya fara jin yunwa.A tray ta jero komai ta kawo.
STORY CONTINUES BELOW
     ” Azizaty taya kiga gane ina jin yunwa?” Ahmad ya tambaya.
      “Naga kana ta hamma ne,gashi da’kyar kake magana”. Reyhana ta fad’a ta ‘kare da dariya dan ita kanta maganarta ta ‘karshe ta bata dariya.
      ” Azizaty da sharri kike,what ever de ziba min am grateful i have a special wife like you me gama abinci da wuri”.Ahmad ya fad’a.
        A plate ta sa musu suka ci yana ta santi yana yaba girkinta,ita de kawai murmushi take a ranta tana jin dad’in yadda yake yaba girkinta da dad’ad’an kalamansa masu sanyaya zuciya.
          Bayan sun gama ci kuma suka tsiri yin photo ,kala-kala tayi ta selfawa sosai sunyi kyau (Naga su wa’e an le’ko ‘yan ina ga selfie…lox bande fad’i suna ba😝).
                 ****    Rana Sunday da Asr Ahmad yace ta shirya suje gidan Umma.Ita kad’ai suka tarar gidan ko yaran ma’kobatan ma masu d’an le’ko mata basu shigo ba.”Yau Reyhana ce a gidan,sannu da zuwa “Umma ta fad’a tana ‘ko’karin shinfid’a tabarmar dake jingine a kusurwar d’akin.
      ” Ina yini Umma”Reyhana ta gaisheta cikin rissinawa.
     “Lafiya lau Reyhana”. Ta amsa.
      ” Ya zaman shiru?”Umma ta tambayeta.
      “Alhamdulillah “. Reyhana ta amsa.
  
       Shima Ahmad gaisawa sukai sannan Umma ta kawo mata ruwan sha da band’ashon gurasa.” Sannu da ‘ko’kari”.Cewar Reyhana kanta a sunkuye tana wasa da yatsunta.
       “Kinga ki sake jikinki se wani ra’bewa kike”.Ahmad ya fad’a mata ‘kasa-‘kasa ba tare da Umma taji me yace ba.
       Bayan ‘yan mintina kad’an ya tashi” Umma bara na le’ka waje”. Ahmad ya fad’a.
      “Toh seka dawo”.Umma ta fad’a.
       Kad’an -kad’an suke hirarsu ,Reyhana ba sabawa tayi da ita ba tunda yau ne karo na farko tazo,sede su gaisa a waya shiyasa ta kasa sakin jikinta.
    ” Kici band’ashon mana ai abin marmari ne”.Umma ta fad’a.
         Itade Reyhana murmushi tayi sannan ta fara gutsura.
       “Ki saki jikinki nan ai gidane”. Umma ta fad’a tana murmushi.
       Reyhana taji dad’in band’ashon kusan biyu da rabi taci(Nima naji dama..😋).
      Umma dama daga ita se d’anta Ahmad data haifa gashi yanzu ita kad’ai shiyasa ma wani d’an saurayin ma’kota yake kwana a shagon gidan na waje.Sunyi sabo da jam’ar unguwar sosai dan a nan aka haifi Ahmad abokanansa dayawa suna nan shiyasa a koda yaushe idan yana gida toh suna majalissarsu yanzun ma can ya tafi.Umma mace me ha’kuri ba sawa ba hanawa dattijuwa ce me son zaman lafiya ba ruwanta da ta’kurawa suruka..
      Har mahrib tayi bai shigo ba,tashi tayi tai sallah danma Allah yasa da wuta ‘yar ‘karamar TV dake d’akin  Umma ta kunna mata kallo.Haka yasa ta rage zaman shirun,Umma kuma ta koma kan girkinta.
       Ahmad bashi ya dawo ba se bayan isha’i ,a kitchen ya iske Umma.
      ” Sannu da aiki girkin ne?” Ya fad’a yana shafa ciki.
       “Baka ci a majalissar ba?”
       “Ai nasan zan kwashi girkin ki shiyasa”. Ya fad’a yana d’an dariya.
        ” Ni banyi girki dakai ba,daga ni se Raihana”. Umma ta fad’a tana kad’a miya.
      “Bafa Raihana ba Rey Reyhana ake cewa”. Ya gyara mata.
      Dama tana sani tace Raihana tasan seya gyara mata,ko kafin yayi aure ma haka sike da ita.Reyhana tana jiyosu a d’aki tana dariya yanayin rayuwarsa da mahaifiyarsa yana birgeta.
        ” Azizaty ina nawa bad’d’ashon?” Tajiyo maganar Ahmad.
        “Ga d’aya da rabi na rage ma”. Ta fad’a tana jiran meze ce.
        ” Lalle kinde cinye ,toh aiko tashi zaki mu tafi seki min abincin dare”.Ya fad’a.
       “Abincin dare a wannan lokacin?”
        “Ehmana ba kin cinyen na Umma ba”. Ya fad’a kamar d’an yaro.
    Dariya ya bata yanda yayi maganar,zata sake magana Umma ta shigo da abinci.
     ” Reyhana ga tuwo fah”.Umma ta fad’a tare da ajjewa.
      “Toh madallah Umma”.Ahmad ya fad’a tare da janyo warmer d’in kusa dashi.
     Reyhana murmushi kawai tayi ta d’auke kai kamar bata gani ba tasani yana sane yayi haka ita kuwa ba kula shi zatai ba balle ma Umma tana wajen.
         ” Bakya ci ne?” Ya tambayeta.
         “Niba kai na kawowa ba fah”.Umma ta fad’a.
         “Haba Ummana ya dahaka ita d’azu taci band’asho nikuma yanzu se a barni naci tuwo ai koh”.Ahmad ya fad’a yana bud’ewa.
      Tuwon dawa ne da miyar kuka ga wani ‘kamshin daddawa dayake tashi (Kai wayyo dad’i 😋).
   ” Hmmm! nayi missing d’in girkinnan fah”. Ya fad’a yana kallon Reyhana. 
        Gani yayi bashi take kallo bama,yana gama zibawa a plate d’in ta faki ido Umma taga bata kallon wajen tayi sauri ta janyo plate d’in wajenta.Kafin ya ankara Umma ta waigo ,basarwa yayi ya sake zuba wani a plate dan yasan ba ci zatai dashi ba.
      Kowa shiru yayi yana sambad’ar tuwonsa har suka kammala.
       “Alhamdulillah se tafiya kuma”. Ahmad ya fad’a bayan ya ajje cup d’in ruwa.
      ” Ai ka bari abincin ya fad’a kuma”.Umma ta fad’a.
        Seda suka ‘kara kusan minti 20 suka tafi.
        Koda suka koma gida Ahmad be kwanta da wuri ba dan akwai test na students nashi da be ‘karasa marking ba.Ita kuwa tuni tayi bacci bema lura ba dan a zaune yake kan gadon ya juya mata baya.
       Dayai magana yaji bata amsasa ba ya waiga yaga tayi bacci.Murmushi ya saki sannan ya gyara mata kwanciyar ya tofa mata addu’a….
     Barka da juma’a  to all  Muslims💞
  Da asuba bayan ya dawo daga masjid Reyhana ta kai masa ruwan wanka toilet.
       Da kanta ta za’ba masa kayan sawa yana fitowa ya gansu ta ajje a kan gado ,T-shirt ce dark blue da ba’kin jeans ,da sauri ya saka ya shirya tsaf tukun ya fito.A kitchen ya taddata tana soya dankali.
      “Ina kwana”. Ta gaisheshi.
       ” Lafiya,ya bacci Azizaty jiya da wuri haka kika kwanta”. Ahmad ya fad’a.
   
        “Eh toh naga kana ta marking”. Ta fad’a.
           ” Toh me ake dafa wa?” Ya tambaya.
           “Hmm dankali ne”. Ta amsa.
           ” Sannunki da ‘ko’kari”.
           “Yawwa dear”. Ta amsa.
       Bayan mintina ta kammala ta kawo masa.” Azizaty ke ba yanzu zaki ci ba?”+
      “Se anjima”.Ta amsa.
     Ba jimawa ya gama breakfast d’in,takalmi ta d’akko masa a d’aki yasa sannan ya tafi ,ita kuwa ta koma baccinta.
              ***
     Haka abubuwa suka cigaba da gudana ,Ikram da Walida sunzo sun wuni sageer ma yazo, Abba ne har yanzu daya cewa mommy suje seta ce ba yanzu ba ,sede yana waya da ita.
      Yau aurensu wata uku kenan,Reyhana na kitchen tana girki yau Saudat zata zo.
        ” Azizaty ‘kawar taki bata karaso ba kenan”.Ahmad ya fad’a sanda ya fito tsakar gidan.
        “Minyi waya tace ta taho”. Reyhana ta fad’a.
         ” OK,bara zan d’an le’ka waje ba dad’ewa zan ba”.Ya fad’a yana zira takalma.
         “Toh shikenan seka dawo”.
        ‘Yan mintina ‘kalilan ta ‘karasa dama couscous da miyan ne se lemon cucumber tun jiya dama tayi mata cake ga exotic guda biyu daya ragu ta had’a mata da d’aya.
        2:45pm Saudat ta ‘karaso gidan ,Reyhana tana d’aki tajiyo knocking d’inta da sauri taje ta bud’e.”Besty!” Reyhana ta fad’a tare da hugging Saudat.
     “K’awas kai nayi  missing d’inki sosai sosai”. Saudat ta fad’a.
      ” Toh mu ‘karasa ciki”. Reyhana ta fad’a tare da breaking hug d’in.
        Sitting room tayi mata jagora suka ‘karasa kowacce farinciki ya mamayeta.”Amarya ashe zan sake ganinki”.Cewar Saudat sanda suka zauna a kujera.
       “Ke d’ince koyaushe sa rana kin kasa zuwa,ya su Mama”. Reyhana ta tamaya.
       ” Duk lafiya suke,sunce a gaisheki”.Saudat ta amsata.
        “Bari ina zuwa”. Reyhana ta fad’a tare da fita.
         Abincin da sauran kayayyakin ta jero a tray ta kawo mata.” Sakko ki ci se ai hirar”.Cewar Reyhana.
          “Ohni Saudat du ni kad’ai”.
          ” Ehyi ke kad’ai.Ta amsa.
       Sakkowa tayi ta fara da,suna d’an hira tana ci.”Ya Mommy kuwa tazo”. Saudat ta tamabaya.
       “Ai Mommy har na fiddaran zuwanta har yanzu bata zo ba kuma Abba yana so zuzo amma shiru de,su Ikram de sunzo amma ko sisters d’in Mommy basu zo ba,na fad’a maki nifa bana ba’ki shiyasa kika ga ina azar’ba’bi kizo”. Reyhana ta fad’a fuskarta na nuna tsantsar damuwa da hakan.
STORY CONTINUES BELOW
      ” Ayya ‘kawata karki damu inshaAllah komai ze dedeta kiyi ta addu’a,amma kede kina waya da ita koh?” Saudat ta tambaya.
      “Eyyi ina wayo dasu”.Ta amsa.
      ” Toh hakan yayi kyau”.Saudat ta fad’a.
       Bayan ta gama cin abincin sega Ahmad ya dawo ,suna gaisawa da ita ya shige d’aki.
     Ranar ta musu dad’i sunsha hira abinsu da selfie,se wajen 5:30pm  Saudat ta tafi.
              ***
    Gidan Mommy..
          “Bafa inda zaki na fad’a maki”. Mommy ta fad’a tana zaune kan sofa na parlour.
      Walida dake tsaye ta yafa mayafi ita a lalle seta je gidan Reyhana.
     ” Mey ke faruwa ne?” Abba ya tamabaya sanda ya sakko ‘kasa dan yajiyo d’aga muryarta.
        “Abba dan Allah kace Mommy ta barni naje gidan Yaya”. Ta fad’a kamar zatai kuka.
      Abba Mommy ya kalla da ta ‘kura wa TV ido kamar bata san suna gun ba.” Mommyn Ikii ki barta taje mana”.
      “Na fad’a mata ba inda zata gara ma ta ha’kura”. Mommy ta fad’a ba tare da ta kallesa ba.
    Hakan da tayi ya ‘kona masa rai.” Walida jeki d’aki zan kira ki anjima”.Abba ya fad’a.
       Ba musu ta haye steps da sauri, Abba kuwa takawa yai ya ‘karasa wajen Mommy ba tare da ya zauna ba yace”Bana son abinda kike yi taya ina maki magana ki kauda kanki ,kuma wannan yarinyar gidan yayarta zata meye aibu a ciki tunda ke kin’ki zuwa seki barsu su dinga zuwa bafa kya kyautawa yarinyarnan duk abinda ze faru ya riga ya faru kowa da kika gani bada arzi’ki aka haifeshi ba a duniya ya samu ki duba mana”.
        “Allah ya taimaka ‘kofa ce a bud’e take sesi ta zuwa suke kwana ma”. Mommy ta fad’a ta bar parlourn.
     Abba yana tsaye ya kasa ta’bika komai wani hali sena Mommy sam idan taso tsiya sede ya rabu da ita.Girgiza kai kawai yayi” Allah ya sawwa’ke”.Ya furta tare da barin parlourn.
      Around 4:30pm Reyhana taji knock ya shigo,hijab ta zira ta tafi bud’ewa dan bata tunanin Ahmad ne.
      “Abba!” Reyhana ta kira tana me mamakin ganinsa.
      “Sannunku da zuwa ku ‘karaso “. Reyhana ta fad’a ta bud’e’kofar widely.
       Walida da sauri taje ta rungumeta,itama Reyhana haka suka shiga ciki.
          “Ina yini Abba”. Ta gaisheshi cikin rissinawa.
          ” Lafiya lau Reyhana “. Ya amsata.
        Sageer dake gefe shima suka gaisa,se Walida dake manne da ita.
         Allah ya taimaka tana da ragowar cake dayai saura jiya se exotic d’aya ta kawo musu da ruwa.” Ikram da Bassam fah?” Cewar Reyhana tana kallon Walida.
      “Suna gida su”. Ta amsa.
    Ba jimawa sega Ahmad ya dawo suka gaisa ya d’an zauna a sitting room d’in suna hira da Abba.
         Da suka zo tafiya Walida tayi ‘kememe baza ta bisu ba seta kwana.Ba yadda basi da ita ba ” Walida ba’a taho da kayanki ba fah”.Sageer ya fad’a.
         “Abba ku barta ta kwana mana na kawota d kaina”. Reyhana ta fad’a.
       Haka suka ha’kura suka tafi ,Reyhana taji dad’i sosai ta samu ‘yar hira.
             ***
Suna komawa gida Mommy tana parlour ita da su Bassam sun baje ice cream suna sha.
STORY CONTINUES BELOW
      ” Abba sannu da dawowa”.Yaran suka fad’a.
       “Ina Walidan kuma?” Bassam ya tambaya.
       “Mun barta can ta nace seta kwana”. Sageer ya amsa.
      
         Mommy ko tanka musu batai ba,illa shan ice cream d’inta data cigaba.
       Suma shirin sukayi Abba ya wuce d’aki Sageer ma sashensa ya wuce.
               ***
    Walida kwai surutu har Maghreb tana hira da Reyhana daga baya ta ‘karbi wayarta ta fara game. Reyhana se lokacin ta shiga kitchen girki dama kuma taliya zatayi jollof.
     Ahmad kuma ya tafi masjid har lokacin be dawo ba.Tana kammalawa ta ziba musu ,suna cikin ci ya dawo.
       ” Sannu da dawowa”.Reyhana ta fad’a.
       “Yawwa”.ya amsa yana ‘ko’karin zama kan kujera.
      Ita ma walidan sannu da dawowan tayi masa  ta cigaba da cin abincin.
      Reyhana tashi tayi ta zubo masa nashi shima tukun ta cigaba da ci tana mata labarin makaranta.
        Wajajen 9:30 Walida ta soma gyangyad’i ,d’akin gado ta kwantar da ita kamar yadda Ahmad ya bu’kata shi seya kwanta a sitting room.
      Chan cikin dare aka d’auke light gashi weather d’in da zafi kad’an Walida ba son zafi take ba tuni ta farka.
         Ga mosquito net shiyasa ta takura,Reyhana fifita ta hau yi mata sannan ta koma, ita kuwa Reyhana se wajen 4:14pm ta koma bacci.
        Ahmad koda ya tashi asubah kamar ko yaushe ya tashi Reyhana ya fita.Rashin bacci da bata samu ba yasa ta koma ba tare da ta ankare ba.
         Koda ya dawo 6:48am ya tarar bata tashi ba seda ya sake tayar da ita,da sauri ta mi’ke ganin hasken gari.
         ” Ya salam!” Ta furta.
   
         “Tabb! Kice baccin kika koma har 7 ya kusa fa”. Ahmad ya fad’a.
         Da sauri ta shige toilet tayi alwala sannan tayi sallah,nan ta yaye net d’in ta tashi Walida da ‘kyar dan akwaita da nauyin bacci.
       Kafin nan 7:15am yayi, data fito ta tarar ya d’ora ruwan tea hakan ya nuna ya sauke ma na wankan.
        Kitchen d’in ta shiga tana tunanin abin breakfast dan potatoes ya ‘kare gashi doya ma baze ishesu ba dan kad’an ya ragu ,tuna tana da flour kawai ta fere doyan nan da nan ta soya da ragowar egg dan shima yazo ‘karshe.
        Flour d’in kuwa ta kwa’ba fanke nan da nan tunda garin da d’an rana.
       Doyar ta d’iban masa ta had’a tea ta kaimasa ,sauri-sauri yayi breakfast d’in dan yayi late 7:39am ya fita.
       Ragowar doyar ta bawa Walida ta had’a mata tea tasha, ita kuwa seda ta jira ya tashi fanken ta soya taci. Kafin tayi breakfast tayi shara ya rage wanke-wanke da sauran ayyuka.
         ” Walida a ajje game d’in ga ruwan wanka na had’a maki”.Reyhana ta fad’a sanda ta shigo sitting room taga tana ri’ke da wayarta.
        “Yaya bari na fad’i sena ajje”. Walida ta fad’a hankalinta na kan wayar.
     Reyhana murmushi kawai tayi a ranta tana fad’in” Yarinya baki da damuwa”.
      Wajen 12:00pm ta gama shirinta gida yayi tsaf,saura girkin rana kuma.
     Shinkafa da miya ta dafa dan kayan abinci sunyi ‘kasa shinkafa ce ta ragu da taliya rabin carton ,se sauran kayan alatun d’and’ano dama kayan gara ne da aka had’ota dasu yanzu kuwa sun kusa ‘karewa,gashi har wata ya ‘kare ba’a biya albashi ba.
                   ***
    Yau Anty Asma’u tazo gidan Mommy nan take fad’a mata Walida tana gidan Reyhana.
      “Ai yau d’innan Sageer ze d’akko ta”. Mommy ta fad’a.
     ” Tana wani d’okin gidan Amarya ba uwadda zasu bata se shinkafa”.Mommy ta fad’a.
       “Hmm yaro kenan ita a jinta za’a had’ota da kayan ‘kwalama.Anty asma’u ta fad’a.
        Sageer yana jinsu shi haushi hirar take bashi ,besan lokacin da zasi dena aibata Ahmad ba sam basa ta’ba yabarsa.
        ” Sageer anjima kaje ka d’auko yarinyar nan kajini ko”.Mommy ta fad’a.
       “Mommy ku barta mana”. Ya fad’a.
       “An’ki d’in kana kallo yau da akwai school amma Abbanka ya ‘kyaleta saboda sangarta”. Mommy ta fad’a cikin fad’a.
        ” Toh ai gobe Saturday “.
         ” Seta je islamiyya ,na fad’a maka anjima zaka d’aukota”.Ta fad’a.
     Daga haka be sake cewa komai ba sema d’akinsa daya koma.
                ***
     Reyhana wajen Asr suna zaune da Walida akai knocking.Walida da sauri ta tashi ta bud’e ‘kofar.”Kai ya Sageer meye na zuwa d’in”. Ta fad’a tana turo baki.
     Ciki ya ‘karaso ita kuwa Walida kamar zatai kuka nan danan ta zauna gefe guda tana turo baki.
      “Kai Sageer da wuri haka, ni na zaci koh kayanta ta kawo”. Cewar Reyhana tana d’aga labilen d’akin.
         ” Mommy ce ta takura sena d’akkota”. Sageer ya fad’a.
        “Kaji Mommy, wai dan Allah meyasa ta’ki zuwa ko su Anty Asma’u ai sa zo sekace banida dangi har kunya nake ji”. Reyhana ta fad’a tana nuna alamar damuwa.
      ” Tana gida na barota ma Anty Asma’un”.Sageer ya fad’a.
       Tashi tayi ta kawo masa ruwa da zo’bon data had’a d’azu.
        Yana zaune Ahmad ya shigo, shiru tayi batace komai ba dan taji ba dad’i be dawo da wuri ba kuma be kirata ba.
         Koda suka gaisa da Sageer d’aki ya bita dan yaga mood nata ya sauya.
        “Azizaty mey nayi”. Ya tambaya.
         Shiru tayi masa harta d’auki abinda zata d’auka saboda haka ya shige toilet ya watsa ruwa.
          A sitting room kuwa alewoyi da chewing gum da Saudat ta kawo mata ta bawa Walida. Ba dad’ewa yasa kaya ya fito.
      ” Sageer bade tafiya ba”. Cewar Ahmad.
        “Gobe da islamiyya ne”. Ya amsa.
      ” OK”.Cewar Ahmad.
     Har mota Reyhana suka rakasu sannan suka dawo ciki.Koda suka komo ciki bata yi masa magana ba illa zama a kan kujera data yi ta shiga latsa waya.
Zama yayi kusa da ita yace “Azizaty mey nayi?” Ya tambaya.
Shiru tayi bata ce komai ba.
“Please say something ko naji sanyi my Azizaty”.
Yanda yayi maganar yasa ta kusa dariya amma seta maze ta cigaba da kallon waya.
” Ayya azizaty inde dan ban dawo da wuri bane ina me neman afuwa ,dubiya muka je da abokaina wayata kuma ba charge shiyasa ban kira ki ba”. Ahmad ya fad’a.
“Toh amma kasan zan damu dayawa aikoh da seka kirani da wata wayar”. Cewar Reyhana cikin shagwaba.
” Sorry my Azizaty next time haka bazata faru ba kinji”.+
Kai kawai ta kad’a bata ce komai ba.
“Kin ha’kura?” Ya tambaya tare da tallafo ha’barta.
“Smile my one and only always and forever”. Ya fad’a.
Hakan yasa ta saki murmushi ,shi kuwa hugging d’inta yayi tightly ” I love you Azizaty.Ya furta
“I love you too dear”. Ta fad’a itama ta sake ‘kan’kameshi.
***
Ta ‘bangaren Mommy kuwa Walida bayan sun koma take nuna wa Ikram alewar da Reyhana ta bata.Mommy ta’ba baki tayi dan tana zaune a palour.
” Wai sunan gidan Amarya aka je shine aka ‘kare da wannan mtchhwww!” Mommy ta fad’a tare da tsaki.
Ita Walida bata ji me Mommy tace ba amma Ikram taji tayi gum da bakinta.
Washegari…
Kasancewar weekend Ahmad yana gida throughout be fita ba ,suna sitting room abunsu suna kallo a TV Reyhana ta d’ora kanta a cinyarsa.
Wayar Reyhana ce tayi ringing hakan yasa ta tashi,koda ta duba taga Mommy bayan sun gaisa Mommy take fad’a mata bikin wata cousin tasu Reyhana da za’ai.
“Mommy kisa Ikram ta kawo min invitation dan Allah”. Reyhana ta fad’a.
” Idan ba’a kawo ba kenan bazaki jeba?” Mommy ta tambaya.
“A’a ba haka nake nufi ba wai da sena bawa ya Ahmad na d’aurin aure”.Reyhana ta fad’a a sanyaye
” Bikin danginki ake ko nashi? dole seya je?” Mommy ta tambaya cikin fad’a.
Allah yasa lokacin Ahmad ya fita daga d’akin da ze iya ji.
“Eyyi baki amsan ba”. Cewar Mommy.
“A’a ,toh Mommy Allah ya kaimu”Reyhana ta fad’a kwalla na cika a idanunta.
Daga haka sukai sallama gefe ta ajje wayar takaici ya isheta.Furucin Mommy ya bugi zuciyarta sosai taji ba dad’i koyaushe bata da buri irin Mommy ta dena tsanar mijinta ita da danginta.”ko su Mommy basu kawo IV ba ai gidansu Amaryar sa kawo”.Abinda ta fad’a a ranta kenan.
Tana cikin wannan batunne sega Ahmad ya shigo da sauri tayi ‘ko’karin saita kanta karya gano wani abun.
” Da Mommy kikai waya?” Ya tambaya.
“Eh tana gaisheka”.Reyhana ta fad’a.
Toh ina amsawa”. Ya fad’a.
” Dama maganar biki ce ranar alhamis za’a fara”. Reyhana ta fad’a.
“Ok toh Allah ya kaimu”. Ahmad ya fad’a ba tare da ya sake cewa komai ba.
” Ranar friday d’aurin aure kuma”. Ta fad’a.
Nan ma Allah ya kaimu yace.Reyhana a zuciyarta haushi ya mamaye dabadan ba da ba abinda zesa ta fad’a masa zancen d’aurin auren dande karya fuskanci ko da wani abun.
STORY CONTINUES BELOW
Haka abubuwa suka cigaba da gudana an biya Ahmad albashi ya d’anyi musu ‘yar siyayya ta kayan tea da sauran ‘yan abubuwa haka Umma ma.
Yau take alhamis ranar kamu,Reyhana ba ita ta shirya ba se 4:30pm ,su Mommy kuwa su ajinsu ko zata je da wuri gidansu Amarya idan yaso lokacin kamun yayi se a rankaya a tafi amma suka ji shiru.
Da Ikram tace zata kirata Mommy ta hana ta.Wajajen 5 kowa ya hallara hatta Amarya tazo waje ya cika ana shagali mutane dayawa suna tambayar Reyhana Mommy har ta gaji da cewa tana hanya.
Reyhana ba ita ta ‘karaso ba se 5:35pm saboda yanayin hanya.Walida ce ta hangota da sauri ta ‘karasa gunta.
Mommy tana zaune kan kujera suna gaisawa da wasu ta hangesu suna ‘karasowa.Tun daga nesa Mommy take hararar Reyhana har ta ‘karaso.
Seat ta samu ta zauna ta gaisheda mutanen wajen sannan Mommy da ta gama ‘kulewa.
“Ina wuni Mommy”. Ta gaisheta.
” Bansani ba,sannunki da ‘ko’kari kowa ya gama hallara banda ke se tambayarki ake harna gaji da yin magana,kin kyauta kenan?” Mommy ta fad’a rai a ‘bace.
“Mommy naga wai da yamma ne”. Cewar Reyhana.
” Ke a matsayinki yaci ace se yamma zaki zo sekace ba ‘yar uwakki ba”.
Ai Mommy tana cikin yi mata fad’a sega Anty Asma’u itama ta fara zazzaga mata nata,Reyhana jitai bikin dama bata zo ba gashi ba abinda ya sake ci mata rai irin yadda rashin zuwan nata ya shafi Ahmad. Shi suka koma blaming suna cewa “Watoh shi kulle yake seya ga dama zaki fito”. Mommy ta fad’a.
‘Kila ma seda ta gama yi masa girki”. Anty Asma’u ma ta fad’a.
Wani zazzafan hawaye ne ya sakko mata ,Allah sarki Ahmad abinda shi ke ta tuna mata tayi sauri ta shirya yamma nayi shine aka la’kaya masa abinda beba.
Ganin ta fara hawaye yasa suka rabu da ita karta tara musu dangi dan idan ta fara kuka ba kanta,kowa seya san tana yi.
Reyhana ko hoto da Amarya batai ba tana zaune gu d’aya Ikram ce daga baya tazo take bata ha’kuri dan su Mommy sun tashi daga gun.
Ganin Maghreb na shirin yi yasa ta tashi,zuwa tayi har inda su Mommy suke tayi musu sallama ta tafi duk cikinsu ba wanda yai maganar tafiyarta da wuri.
Mommy basu suka tafi ba se wajen 9:00pm.Aiko Walida bayan sun koma gida suna shiga ta nufi Abba da suka tarar zaune parlour.
” Abba kasan mey Mommy sukai wa yaya?” Cewar Walida.
“A’a Walida sekin fad’a”. Abba ya fad’a tare da tattaro attention kanta.
” Wlhy kuka tayi suna mata fad’a”. Ta fad’a harda zaro ido.
Mommy kuwa da tin shigowarsu suka haye sama ita da Ikram dan a gajiye suke.
“Da gaske Babyna?” Abba ya tambaya yana son sake tambatarwa.
“Da gaske nake Abba ka tambayi Ikram ma kaji hadda Anty Asma’u sukai ta mata..” Bata ‘karasa ba Abba ya katseta.
“Ya isa aje a kwanta dare yayi kinji”. Cewar Abba yana lalla’bata.
Kan kice me ta haye sama abinta Abba kuwa ya shiga tunanin abinda sukaima Reyhana.
Ita kuwa Reyhana sanda ta koma gida Ahmad ya kula da yanayinta amma seta ce ciwon kai take ji.Ko abincin dare bata iya girkawa ba dama akwai ragowar na rana suka ci suka kwanta.
Washegari da safe kasancewar d’aurin auren 11am ne Reyhana da kanta tace wa Ahmad ya ha’kura da zuwa tinda yana da makaranta,ko ba dan haka ba dama bata so yaje dan tana gudun kar a wula’kantashi.
STORY CONTINUES BELOW
Ita kuwa sunyi dashi zata tafi gidan bikin 12pm amma yana fita ta dawo tayi kwanciyarta koda ta farka aikace-aikacen gidanta tayi ta d’ora girkinta.
   
      Mommy kuwa suna can ana ta hotunan d’aurin aure ,gefe guda ta ware tayi dialing number Reyhana.
      ” Reyhana lafiya baki zo ba?”Mommy ta tambaya.
      “Na tashi banda lafiya ne”.Tayi ‘karya harda narke murya.
      ” Bakida lafiya? Har ankon dinner gashi kuma anyi miki”.Mommy ta fad’a.
      “Idan na samu sau’ki sena shigo anjima”. Reyhana ta fad’a.
       ” Toh Allah ya sawwa’ke”.Mommy ta fad’a sannan ta katse wayar.
      Reyhana kuwa koda rana tayi bacci ta koma abinta dama Ahmad ze biya gidan Umma daga makaranta.
    Haka aka gama biki bako d’uriyarta ,Ahmad daya dawo ya tamabayeta tace masa ciwonkan be dena ba.
    Mommy dama ta fidda ran zuwanta,akayi dinner ba ita.Washehari ma yini bata jeba haka aka ‘kare biki ba ita.
     Ranar sunday da safe Abba yana gida yayi kiran Mommy, ita bata kawo akan Reyhana bane bama.
       “Mommyn Walida me Reyhana tayi miki?” Ya tamabayeta bayan ta zauna.
      “Bangane ba”. Mommy ta fad’a tana neman ‘karin bayani.
       ” A biki mana an fad’amin kun saka tayi kuka a dalilin mey?”
       “Ita Reyhanan ce kenan ta fad’a maka ,amma meyasa bata fad’a maka dalili ba?” Cewar Mommy.
       “Sam ba ita bace and tambayarki nayi ba canayi ki tambayan ba”. Abba ya fad’a ba watsa cikin lamarin.
    D’an  gyara murya tayi Mommy kafin tace.” Fad’a ne bata so,dan me zata zo biki kusan to 6 kowa yana tambayarta amma shiru abinda tutuni an fad’a mata”.
     “Yanzu akan bikin shine kuka rifeta da fad’a? Yayi kyau Maryam kece da ita ko mijinta idan yayi niyyar hanata zuwa ya zakiyi? Dole fa ki ha’kura wannan yaran mijinta ne ko ki yarda ko karki yadda ,kuma bana so haka ya sake faruwa idan ba haka ba rai ze ‘baci walhy”. Abba ya fad’a cikin fushi.
    Mommy da ta gama ‘kuluwa yana gama maganar ta tashi ta fita bako bada ha’kuri.
     Ai d’akin Ikram ta wuce direct,bacci ma take taji ana d’ala mata duka a cinya.
      ” Tashi zaune nace!” Mommy ta fad’a.
     A zabure ta mi’ke dan dukan ya shigeta”Mommy !”Ta kira kamar zatai kuka.
       “Kece kika fad’a wa Abbanku nayi wa Reyhana fad’a a gidan biki?” Mommy ta tambaya.
     “A’a bani bace”. Ta amsa.
      ” Waye idan bake ba?”
       “Sede Walida”. Ikram ta fad’a.
      Mommy kai ta kad’a ta wuce d’akin Walida,itama tana bacci ta tasheta.
      ” Kece kika fad’a wa Abbanki nayi wa yayarki fad’a koh?”
      “A’a canai tayi kuka de”. Walida ta amsa tana murza ido.
     Rankwashi taji akanta wanda batayi tsammani ba,da sauri ta dafe gun tana shirin kuka taji dundu a bayanta ‘kwarara uku.
 
     ” Sarkin surutu manya suna magana kina zuba musu ido shashasha na sake ji kin fad’a masa wani abun”.Mommy ta fad’a ta dungure mata kai ta fita.
     Walida kuwa kai ta cusa cikin fulo ta fara rera kuka wanda baza a jiyota ba.
             ****
    Reyhana yau baccinsu suka sha se wajen 10 am suka tashi ,nan tayi musu abincin breakfast bayan sunci sukai wanka.
      Kayan wankinsu ya taru saboda haka koda Ahmad yace ze kai mata nata tunda shi dama baya kai wanki da kansa yake yi.Reyhana tace ya bari kawai sayi wankin tare yau tunda yana gida sesiyi ba yadda be da ita ba tace a’a dole ya ha’kura.Ganin baida isassun kud’i yasata yin haka dan kusan duka salary d’in a abinci ya ‘kare.
   
     Turyan turyan suka fara kusan shine ‘karfin wankin daga baya jagab sukai da ruwa dukansu wannan ya she’kawa wannan haka sukayi tayi har suka ‘kare wankin.
              ‘Bagaren Mommy kuwa koda suka fito breakfast dinning table, Abba ya lura da jan da kumbura da idanuwan Walida sukai.
     “Walida meya sami idanki? Ko kuka kikai?” Abba ya tamabayeta.
     Kowa kallonsa ya dawo kanta bare Mommy da take jira taji me zata ce.Wuri-wuri tayi da ido tana tsoron Mommy karta fad’a ta sake dukanta idan ta kalli Abba seta kalli Mommy ta rasa ya zatai.
      “Fad’a min kinji meya sami idon?” Abba ya sake tambaya.
Walida da ganin irin kallon da Mommy keyi mata yasa tace”Abune ya shigemin idon shine na sosa yayi ja”.+
“Ayya ya fita yanzu?” Abba ya tamabaya.
“Eh”. Ta amsa.
Mommy kallonta tayi alamar kin ceci kanki d’innan.
***
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa yau da dad’i gobe babu.
Reyhana tana d’aki tana nikke jera kayan data goge a wardrobe. Sallamar yaya Ahmad yasa ta fitowa dan wataran dama yana fita da key idan ya dawo ya bud’e base yayi knocking ba.
A sanyaye ya ‘karaso d’akin.” Sannu da dawowa”.Reyhana ta fad’a.
“Yawwa”. Ya amsa a sanyaye.
“Yaya wani abune?” Reyhana ta tambaya.
“Ahnn…kainane yake ciwo”. Ya amsa.
” Ayya sannu kayi wanka sena zubo maka abinci kasha magani”.Ta fad’a.
Tashi yayi ya rage kayan jikinsa ya shiga toilet,Reyhana kuma ta fita had’o abinci.
Sitting room d’in ya zauna yaci abincin kad’an -kad’an yake amsata.Paracetamol ta ‘ballo masa ta bashi ya watsa,kan kujera ya samu ya haye yayi rigingine hannunsa ya d’ora kan goshi kamar me bacci amma ba baccin yake ba.
Reyhana kuwa bayan data kwashe kwanikan d’aki ta koma ta cigaba da abinda take dan tana tunanin ko gajiya ce tasa shiyasa ta bashi space.
Shikuwa ba abinda yake tunani se ta yadda ze ‘bullo mata da wannan al’amari daya faru dashi.
Da asr ya tashi yaje masallaci bayan ya dawo kuma ya tarar tana kitchen had’a abincin dare saboda haka ya koma d’aki yana jiran anjima ya sanar mata.
Se bayan da suka kammala cin abincin dare sannan ya zauna da ita.
“Reyhana bansan ya zaki d’auki wannan abun da zan fad’a maki ba,ina me baki ha’kuri”. Ahmad ya fad’a.
” Yaya mene ka fad’amin du na tsorata”.Ta fad’a.
“Reyhana.. aa..an sallameni daga makarantar da nake teaching”. Ya fad’a da ‘kyar.
“Subhanallahi yaya meya faru? Meyasa?” Reyhana ta fad’a hankalinta a tashe.
“Director na school d’in ya fad’a mana cewa malaman school d’in sunyi masa yawa kuma biyan salary yana nema ya gagareshi and kuma yanzu sunfi son masu degree certificate”.
Shiru tayi Reyhana hannunsa biyu ta ru’ko.” Yaya addu’a kawai itace mafita ba damuwa ba jarabawace garemu,Allah ya musayya maka da wanda yafi wannan Yaya”.
“Ameen”. Ya amsa.
Sosai ta damu amma ta danne irin damuwar data shiga,ranar kusan dukansu basi cikakken bacci ba musamman Ahmad.
Ko washegari daya tashi yana d’aki ko breakfast d’in arzi’ki beba ya kwanta yana tunane-tunane.Reyhana ce ma take d’an kwantar masa da hankali da taga yana tunani seta zauna ta fara yi masa hirarraki kota kunna masu kallo da rana,haka da daddare dukansu tashi sike sallah.
Ko Umma be fad’a mata ba bayaso ta shiga damuwa,yanzu fafutukar neman abinyi ya tsindima.A rana seya fita yafi so uku,a haka har ya samu wajen aiki,sunayin sliding window.
A kullum ake biyansa kud’in ba masu yawa bana sede addu’a kawai.
Yau bayan fitarsa wajen 9am ko karyawa beba dan tashi sukai gas d’inma ya ‘kare gashi ba kud’in refilling danma Allah yasa da ‘yan wasu kud’i a hannunsa da Abba ya aiko mata sanda Sageer yazo.
Ragowar 3k ne dan haka da kanta ta fita bata da me aike.Ganin kayan abincin su sun ‘ka’kkare ta sissiyo wasu abubuwan se ragowar ta d’uro gas.
STORY CONTINUES BELOW
Ahmad ba shi ya dawo ba se 3pm,bayan watsa ruwa ya fito sitting room be ganta ba dan haka ya le’ka kitchen.
“Azizaty ina kika samu kud’in gas?” Ya tambaya.
“Hmm karka damu akwai wasu ‘yan kud’ine a guna shine nayi amfani dasu nayi siyayya”. Reyhana ta amsa.
” Meyasa kikai haka Reyhana? Kud’inki ne na amfanin kanki kuma shine…”
“Is ok wannan ba wani abu bane me zanyi dasu idan banyi hakan ba?karka damu mana”.
Shiru yayi yana kallonta a ransa yana jin sonta na sake ha’baka a zuciyarsa,ta wani side d’in kuma tausayinta dan bata taso cikin irin wannan rayuwarba.
***
Mommy kuwa batasan halin da Reyhana ke ciki ba dan bata fad’awa Mommy ba.
Gobe zasije wata dubiya dan haka tasa Ikram ta sanar wa Reyhana.
Ahmad yana zaune ta amsa kiran Ikram d’in saboda haka bayan ta gama wayar ta sanar masa.
Washegari around 2pm ta isa gida,Walida da gudu ta tarota dan ta hango shigowarta.
” Yaya oyoyo!” Ta fad’a .
“Walidandan ‘yan matan Mommy”.Reyhana ta fad’a tare da rugumota.
Hannunta a nata suka ‘karasa ciki ,Mommy tana d’aki ta fito.
” Mommy ina yini “.Reyhana ta gaisheta.
” Lafiya lau”.Ta amsa.
Yau ba kamar rannan ba fuskarta a sake take ko dan ganin ba Ahmad..
“Ina Ikram da Bassam?” Ta tambaya.
“Suna d’aki”. Mommy ta amsa.
” Walida maza jeki ce inno ta kawo mata masa(wainar shinkafa)”.Mommy ta fad’a.
Tashi tayi kamar yadda Mommy ta umarta,inno ta kawo mata wainar Walida ta taho da juice.
Kad’an taci wainar tace ta ‘koshi,bayan sunyi sallar asr suka fita,Mommy ce da kanta ta jasu a motarta.
Kasancewar dubiyane basu dad’e ba sosai,Mommy ta biya dasu gidan Anty Asma’u.Reyhana sam bata so zuwansu chan ba dan tasan halin Anty Asma’u gashi Ahmad’s besan da wani biyawa gidan Anty Asma’u ba ,tana kallo har suka isa bata iya cewa komai ba.
“Ahh! Yau harda Reyhana lalle irin wannan ba zatan”. Cewar Anty Asma’u.
D’akinta ta jasu kamar yadda suka saba da hakan,ita de Reyhana jikinta a sanyaye.
” Anty ina yini”. Ta gaisheta bayan sun zauna.
“Lafiya lau Reyhana yau an samu de an fito”. Ta fad’a.
” Atoh na tusota a gaba da baza ki ganta ba”. Mommy ta fad’a.
Yaran Anty Asma’u ne suka shigo suma suka gaggaisa dasu,a ciki akwai ‘yan mata biyu kusan sa’annin Reyhana ne shine suka soma d’an hira.
Me aiki tasa ta kawo musu abinsha,suna zaune har maghrib ita de Reyhana hankalinta ya fara yin gida.
Gashi tana tsoro tayi wa Mommy magana tace ta fiya zumud’in gidan miji dan haka tayi shiru.
“Reyhana de ta gaji naga tayi shiru”. Cewar Anty Asma’u.
” Toh ai nima yanzun nake so mu tafi”.Mommy ta fad’a.
Seda sukai sallah tukunnan lokacin har 7:25pm tukun suka fito ,har bakin gate ta rakosu sukai sallama.
A mota suna tafiya sega kiran Ahmad.
“Hello yaya”. Reyhana ta fad’a bayan data d’aga.
” Azizaty naji ki shiru”.Cewar Ahmad.
“Gani ina hanya ba dad’ewa zan ‘karaso”. Ta fad’a.
” Toh sekin dawo”
Yana katse wayar ta kalli Mommy a ranta tana fad’in Allah yasa ba gidan Mommy zasi wuce ba.
Tana wannan tunanin taji Mommy tace “chan zami koh?”
“Eh”. Ta amsa da saurinta.
Mommy har ‘kofar gida ta kaita,tana fita daga motar sega Ahmad yana fitowa daga gida zaije masjid.
Reyhana ce ta fad’a masa Mommy ce ta kawota.’Karasawa yayi har k’ofar mota Mommy ta sauke glass d’in motar ya gaisheta cikin rissinawa.
Mommy tana tafiya ya wuce majid karya makara Reyhana ta shiga gida.
Reyhana wani dad’i taji lokacin da ta le’ka kitchen taga ya siyo gurasa saboda haka miya kawai zatayi.
Tana dire bag d’inta da mayafi ta shiga kitchen had’a miyar a d’an ‘kan’kanin lokaci ta kusan kammalawa.
Ahmad daya shigo ya tarar da ita a kitchen.
” Uwargida daga dawowa se girki kuma”.
Murmushi tayi tare dayi masa sannu da zuwa.
“Ai naga ka siyo gurasa kaga miyace kawai zanyi nama kusa gamawa”. Ta fad’a.
” Toh sannu da aiki”.Ya fad’a.
“Yawwa”. Ta amsa.
Tana gama miyar ta turara gurasan ta sako musu.
” Azizaty ai baki ci dayawa ba”. Ya fad’a.
“Ya isheni naci waina a gida”. Ta fad’a.
” Mun biya gidan Anty Asma’u fah”.Reyhana ta fad’a dan bata so ta kasance me ‘boye-‘boye.
“Haba,daga gidan dubiyar kuka biya?”
“Eh”. Ta amsa.
” Toh ya suke?”Ya tamabya ba tare da ya nuna komai ba.
“Lafiya lau”. Ta amsa.
Haka suka cigaba da hirarrakinsu kafin lokacin kwanciya yayi suka kwanta.
***
Washgari Reyhana ta farka jikinta li’kis dan zazza’bi daya rufeta da’kyar tayi sallah.
” Azizaty ko asibiti zamu?”Ahmad ya tambayeta.
“A’a mu bari ze sauka”.Ta fad’a.
Goshinta ya ta’ba yaji da zafi amma ba kamar da asuba ba.
Da kanshi ya had’a mata breakfast ya kawo mata.
” Azizaty ki daure ki sha tea seki sha magani”.Ahmad ya fad’a.
Da taimakonsa ta mi’ke daga kwance,tea d’in ta d’an kur’ba.
“Kici doyan ko kad’anne”. Ahmad ya fad’a.
‘Kwaya d’aya tasa a baki da’kyar ta iya had’iyewa ta kora da tea.
Sede tunda ta had’iye ta kasa sukuni saboda tashin zuciya da ya tunkaro mata.
Ahmad yana mata sannu kai kawai take kad’awa ta kasa ko magana.
” Azizaty ki ‘kara ci ko kad’an ne”.
Kai ta girgiza masa alamar a’a.
“Azizaty ki….” Be ‘kare maganar ba yaga ta tashi da hanzari ta nufi toilet.
Seda ta amayar da abunda ke cikinta kaf,Ahmad ne ya wanke wurin ya taimaka ta koma d’aki.
Kan gadon ta zauna ta jingina Ahmad yana mata sannu.Daya ta’ba goshinta yaji ba zafin.
“Kin dena jin sanyin?” Ya tambayeta.
“Eh”. Ta amsasa.
Kwanto da kanta jikinsa yayi yana shafa bayanta,a haka bacci yayi gaba da ita.
Ranar Reyhana wuni tayi a kwance ,Ahmad se ha’kura yayi da fita. Jollof taliya ya dafa musu taci kad’an ,shima be iya yaci dayawa ba.
Washegari da safe ya taimaka mata tayi wanka ta shirya.
“Reyhana tashi fa zaki mu tafi asibiti”. Ahmad ya fad’a.
” Mu bari ze fa sauka zazza’bin”.Reyhana ta fad’a murya tana rawa.
“Ba shawararki fa nake nema ba tashi zaki nace mu tafi yanzu”. Ahmad ya fad’a in serious turn.
Tana turo baki ta tashi ta zira hijab da takalmi.A hanya yana mata hira ta’ki ko tanka sa.
Reyhana ba wani abu yasa bata son asibiti ba sedan tana tsoron allura(kamar ni😂).
Suna isa asibitin zuciyarta na sake tsorata a sanyaye ta shiga gun likita.
Koda ta gama zayyane masa abunda yake damunta test na mp da PT ya rubuta mata.
Data fito Ahmad yana tamabayarta takardar kawai ta mi’ka masa, nan suka tafi laboratory. Wajen blood collection da’kyar ta yarda aka d’auka jininta tund PT d’in serum ne.
Bayan kamar 20min aka bata result tana fitowa ko ta kansa bata bi ba.Yana mata magana amma ta’ki kula sa illa hannunta data ri’ke kamar wacce ta karye. Hakan yasa kamar yayi dariya amma dan kar ya had’a mata zafi biyu ya maze kawai.
Koda ta bawa doctor result d’in daya duba wasu ‘yan magungunan ya rubuta kad’an sannan yace.
” Congratulation”.
Kallonsa ta soma yi cikeda rashin fahimta.
“Kina d’auke da juna biyu,zaki je yanzu wajen scanning ga wasu maguguna da na rubuta maki Allah ya ‘kara lafiya”. Doctor d’in ya fad’a.
      ” Ameen nagode”.Reyhana ta fad’a bayan ta kar’bi katin.
   
    Lokaci guda tsoro da farinciki ya ziyarce ta,tana fitowa Ahmad ya ‘karaso inda take “Azizaty me doc yace?”
       Mi’ka masa katin tayi ba tare da tace komai ba.
       “Azizaty wannan kike ‘boyewa daman?” Ahmad ya fad’a fuskarsa d’auke da murmushi hatta ha’koransa seda suka fito.
     D’an waigar da fuska tayi tace”Nima ai d’azun ban duba ba “.
       ” Maman baby me tsoro”.Ahmad ya fad’a.
      Tafin hannunta ta d’ora a bakinta tana murmushi amma har lokacin bata waigo ba.
      Wajen scanning d’in suka ‘karasa ba dad’ewa akai mata ya nuna 5weeks.
       Dad’i gun Ahmad baze misaltu ba itade Reyhana kawai takardan ta zubawa ido dukda kuma cikin ranta itama farincikinne.
      A hanyar dawowa ya sayi fruit da balangu suka komo gida a napep yana ta mata hira itade uhm da a’a ne amsarta.
    
     Suna shiga gida Ahmad ya sata a gaba seta sha fruit da naman.Kad’an ta samu taci tace ta ‘koshi.
       “Kina so ki bar Babynmu da yunwa ne?Ahmad ya fad’a.
 
     ” Nafa ‘koshi anjima na sake ci”.Reyhana ta fad’a.
    “Toh yanzu me kike so?” Ya tamabyeta.
     “Bacci”Ta amsa.
     ” Laa! Azizaty yau bacci kike so ba niba”.Ahmad ya fad’a dan so dayawa ya saba tamabayarta haka seta ce masa shi.
      “Toh nima shikenan ,babynmu nake so”. Cewar Ahmad.
     Reyhana murmushi kawai tayi ,tashi tayi da niyyar tattare kayan gun da sauri Ahmad ya ri’ke hannun.
STORY CONTINUES BELOW
     ” Azizaty rufan asiri mey ta kaikai yin aiki a wannan lokacin kwantawa zaki ki bacci ba abinda zaki ta’ba”.Ahmad ya fad’a.
       Hannunta ya ri’ke suka nufi d’aki ,kan gado ya kwantar da ita ya saisaita mata fankar d’akin ,yana zaune gefen gadon har seda tayi bacci tukun ya koma sitting room.
      Kayan wajen ya tattare da kwanukan da suke ba a wanke ba ya d’aurayesu.
       Reyhana baccinta tayi ta ‘koshi se wajen 2 ta farka tayi sallah nan ta tarar da abinci shinkafa da miya koda ta tambayeshi shi waya dafa yace ai umma ce ta turo yaro ya kawo.
      “Kenan fad’a mata kai bani da lafiya”. Cewar Reyhana.
      ” Ehyi ta kira kina bacci ma”.Ahmad ya fad’a.
      “Ya babynmu ya tashi?” Ya tambayeta tare da d’ora hannunsa ya shafa cikinta dayake a shafe.
       Dariya tayi tana kallonsa “Taya zansani nikam?” Ta fad’a.
     “Kinjiki tun yaushe ma ni ai yanzu naji tunda ke baki sani ba”. Ahmad ya fad’a.
      ” Hmm!”Abinda kawai ta fad’a tare da girgiza kai tana murmushi.
       Da kansa yayi ta bata abincin kuma taci da yawa ba kamar jiya ba ,maganin ya ‘ballan mata tasha.Zazza’bin ma ya sauka yanzu se kasala de gashi baccinma ba dika ya tafi ba.
               ***
     Se washegari ya koma aikinsa ,itama Reyhana ta samu sau’ki zazza’bin yawanci se da dare takeyi kad’an se bacci ba wuyar tayi bacci.
        A ‘yan kwanakinnan haka take daga shingi’da se bacci ya kwasheta ,idan kuwa ya fita tana d’an yin abunda zatai se bacci wani sa’in ko shigowar Ahmad bata ji.
        Umma ma tazo ta duba ta har gida ,su Ikram ma sunzo  lokacin da bata jin dad’i.
         Yau tana zaune bayan tayi wanka ta shirya ,haka kawai taji tana son cin d’ata.
      Da farko tayi tunanin ko ta kira Ahmad idan ze dawo ya taho mata da ita,ganin bazata iya jiran har tsahon wannan lokacin ba ta yafa mayafi wasu ‘yan chanjin dake wajenta ta d’auka ta le’ka ‘kofar gida Allah yasa ta hangi wani yaron ma’kwafta nan tayi kiransa ta basa kud’in ya sayo mata.
      Bayan ‘yan mintina ya dawo Reyhana ana rawar jiki aka amsa ta shige gida nan danan ta d’aureye ta fara gutsurar kayanta.
     Taci kusan uku jin amai ze tunkaro ta ta ha’kura.Ta kunna TV tajiyo knocking, hijab ta zira ta tafi bud’ewa.
     Tasha mamaki ganin Mommy a tsaye gefenta Anty Asma’u.
       “Laa! Ashe kune, sannunku da zuwa”. Ta fad’a.
       ” Yawwa”.Suka amsata.
       Ciki ta ‘karaso dasu,har ‘kasa ta dur’kusa ta gaishesu.
       “Ina yini”.
       ” Lafiya lau”.Suka amsa.
         Tashi tayi ta  had’o musu zo’bo da yake a fridge se ruwa ta jero musu a tray.
       “Ya jikin naki su Ikram sunce kinyi zazza’bi”. Mommy ta fad’a.
        ” Na samu sau’ki”.Cewar Reyhana tana ajje tray d’in.
      “Toh Alhandulillah”. Suka amsa.
      ” Sageer ne ya kawo ku?” Ta tamabaya bayan ta zauna a kujera.
      “A’a shi ya tafi makaranta ma ,nina tu’komu”. Mommy ta amsa.
     ” Ya Ahmad d’in?” Anty Asma’u ta tambaya dan Mommy ba tamabaya zatai ba.
        
          “Reyhana inci?” Anty Asma’u ta  tambayeta lokacin da ta d’auki d’atar dake hannun kujera.
STORY CONTINUES BELOW
        Dariya tayi Reyhana sannan tace “Laa kici mana Anty”.
      Anty Asma’u dama tana son d’ata inde ta hangeta a hanya takan tsaya ta siya.
      Mommy kuwa ganin d’atar yasa hankalinta ya kasa kwanciya ,a sanyaye ta kalli Reyhana ta lura da sauyin da tai.
       Ta ‘kara fari ga ta d’an murje.
         Kitchen ta shiga ta had’a miya dan tattasan dama a soye yake.A ‘yan mintina ta ‘karasa ta zubo musu couscous d’in.
         Mommy idanta na kan abincin da Reyhana take zuba musu a plate so take taga koda nama ko babu.
     Aiko de babun ta gani a take ta ta’be baki.
      D’an kad’an taci tace ta ‘koshi gara Anty Asma’u ta d’an ci dayawa.
  
        Reyhana ganin d’atarta biyu ne ya ragu yasa ta tashi ta shige d’akinta ta kira Ahmad.
      ” Yaya ya aiki?” Reyhana ta tambaya.
        “Lafiya my Azizaty, ya babynmu?”
        “Lafiya lau”. Ta amsa.
        ” Yaya d’ata nake so”.Reyhana ta fad’a.
     
        “Iye! Babyn mu zeci d’ata,kunyar first born kike koh”.Ahmad ya fad’a.
          ” Kunya kuma?” Reyhana ta fad’a tana turo baki.
           “Ehyi idan ba kunya kike ba  repeat what i will say”.
           ” Babynmu zeci d’ata”.Ya fad’a.
           Shiru tayi a hankali tace “Babynmu zeci d’ata “.
         ” Banjiba”.Ahmad ya fad’a.
         “Kafa jini”.Ta fad’a kamar zatai kuka.
         ” Azizatyn Ahmad karki kuka shikenan zan taho maki dashi”.
         “Mommy fa sunzo suna parlor ma”. Ta fad’a.
         ” Ki gaida min dasu kafin na dawo”.Ya fad’a.
         “Toh seka dawo”.
         ” OK bye I love u two ki shafamin babynmu”.
         Dariya tayi sannan tayi hanging ,komawa tayi wajensu Mommy suka cigaba da hira.
         Wajen 4:30pm suka tafi Ahmad be samu ganinsu ba.
       Reyhana shikenan kuma yanzu bata zama ba d’ata koyaushe cin d’ata wani sa’in ma ta gwammace taci d’ata da abinci abun har ya ishi Ahmad.
       “Yau fa ba cin d’ata ni babynmu ya gaji”. Ahmad ya fad’a yana zira takalmansa.
       ” Dan Allah Yaya ka taho min da ita yau bansan inda zansa kaina ba idan ban ci ba”.Reyhana ta fad’a cikin shagwa’ba.
     “Shikenan amma yau sekin ci abinci sosai zaki ci kin yarda?”
      Kai ta d’aga alamar eh ,daga haka  sukai sallama ya fita.
        Haka rayuwa ta cigaba a kwana a tashi yau cikinta wata biyar ya fito.Ta fannin aikin sa de se addu’a inda Allah ya taimaka Reyhana mace me ha’kuri so da dama Mommy seta tayiwa Abba complain akan zaman Reyhana a gidanta dan yanzu ta gano baya teaching d’in.
      Abba idan ya kira ya tambayi Reyhana koda wata matsalar seta ce a’a,wani sa’in yakan tura Sageer ya kai mata kud’i ko kuma idan tazo ya bata. Sede kwana biyunnan ‘kwaras suke basuda kud’i gashi Umma bata jin dad’i ana ta zarwar kaita chemist amma ciwo seya dawo,a kaita asibiti abu ya gagara.
STORY CONTINUES BELOW
      Reyhana tana zaune tayi nisa cikin tunani wani idea d’inne ya fad’o mata aikam da sauri ta kira sageer a waya tace yazo gidanta.
      Daga school ya samu ya biyo.
     “Sageer kaga dama phone d’ina nake so ka sayar mini seka sama min ko ‘karama ce amma fa promise me bazaka fad’awa Mommy ba”. Reyhana ta fad’a.
      ” Kai yaya ya zaki sayar da phone naki ki fad’awa Abba mana idan kud’i kike so”.Sageer ya fad’a.
       “A’a bazan fad’a masa ba kana kallo ko sati ba’ayi ba ya bani 10k kuma sannan na sake tamabyarsa,nide kawai inda zaka sayar mini”. Reyhana ta fad’a.
      ” Toh shikenan kawo wayar”.Ya fad’a.
         “Promise baza ka fad’a mata ba”.
         ” Bazan fad’a mata ba “.
         ” Good”.Cewar Reyhana tana zare sim d’inta da mcard.
          Wayar ta mi’ka masa ya tafi,dama tuntuni bata jin dad’i taga Ahmad yana ri’ke ‘karamar waya ita kuma babba(Allah sarki Reyhana).
        Later wajen 4pm ya dawo ,an sayeta 16k ya saya mata ‘karama 5k saura 11kya bata.
      Ahmad sanda ya dawo gida bayan yaci abinci ta d’akko kud’in.
     “Yaya kaga nace wannan kid’in me ze hana akai umma asibiti dasu”.Ta fad’a tare da mi’ka masa.
       ” Ina kika sami wannan d’in?”Ahmad ya tambayeta.
       “Uh..wayata “. Ta amsa.
        ” Wayarki”.Ya kalleta cike da mamaki.
   
        “Dama fa ta fara samun matsala shine na sayar na sayi wata wannan kuma sauran kud’inne”. Tayi ‘karya dan ba wani matsala da wayar ta samu.
       ” A’a bazan kar’ba ba meyasa kikai haka ,taya zaki sayar da wayarki”.Ahmad ya fad’a dan beji dad’i ba.
        “Lefi ne idan nayi hakan?” Reyhana ta fad’a kamar zatai kuka.
        “Nide na fad’a maki bazan kar’ba ba”.
       Nan take Reyhana ta fara zubar da hawaye hadda shishshi’ka.
       ” Kukan kuma na miye daga nace bazan kar’ba ba”.Ahmad ya fad’a duk ya damu dan baya son kuka.
       “Toh kafi so mu cigaba da kallon umma a haka?”Ta fad’a cikin kuka.
        “No amma…” Be ‘karasa ba ta katse sa.
      “Dan Allah Yaya ka kar’ba ,naji wataran ka bani amma yanzu ka kar’ba”. Ta fad’a duk da kuwa ko wataran ya bayar ba kar’ban zatai ba tayi hakan ne dan ya kar’ba.
         Shiru yayi bece komai ba ya tafi tunanin halin da umma me ciki dan ko yanzu daya barota tana kwance.
        ” Ok naji zan kar’ba,shikenan?”
       Reyhana kai ta kad’a tana murmushi,shikuwa kallonta yai  a ransa yana jin ‘kaunarta ,jawota jikinsa yayi yana shi mata albarka.
         Washegari da safe yaje gidan umma ya tafi da ita asibiti, malaria ne yaci ‘karfinta har ruwa aka ‘kara mata se allurai da magunguna da aka rubuto mata,se yamma suka komo gida ,har ‘yan siya-siye yayi mata bashi ya komo gida ba se bayan maghrib ya komo gida dama akwai wata ‘yar uwassu da take a kano ita take kula da ita.
        “Ya jikin umman ?” Reyhana ta tambaya.
         “Ta samu sau’ki ammata ‘karin ruwa sai maguguna da allurai dasuka bata”.
 
         ” Allah ya ‘kara sau’ki,Yaya gobe zani fa na sake dubata”.Reyhana ta fad’a.
         “Toh Allah ya kaimu Azizaty ta,ya babynmu?” Ahmad ya fad’a yana shafa cikin.
    Reyhana murmushi tayi itama ta d’ora hannunta kan nasa.
                 ***
    Mommy de an samu Abba ya tisata a gaba sunje duba umma ,Abba yayi mata siyayya ta dubiya suka kai.
     Hakan ba ‘karamin yima Reyhana dad’i yayi ba.
       
      Cikin ikon Allah Umma taji sau’ki sosai.Akwai wani biki daya taso a Zaria Umma datace zata je Ahmad ya’ki yace ta ha’kura ai bata jin dad’i.
     Reyhana kuwa yana fad’a mata tace su suje mana,ba yadda beyi da ita ba ta’ki ha’kura har umma ta fad’awa ita kuwa ta goyi bayanta dole ya ha’kura.
      Reyhana se d’oki ake tun ana washegari ta gama had’a kayanta shi Ahmad dariya ma yake mata.
       “Maman baby kwana nawa za’ayi ne irin wannan shiri haka”.
        ” Kwana uku mana”.Ta amsa.
       “Uku ? Babynmu kuma yace d’aya”. Ahmad ya fad’a.
    
       ” D’aya haba de zami fa ziyara”.
       “Ziyara? Toh ai duk wa’anda za’a je gidan nasu zaki gansu gurin bikin”.Ahmad ya fad’a.
         ” Toh naga gari”.Ta fad’a.
         “Maman baby yawo de ,babynmu baya son yawo”.
      Haka sukai ta  fafatawa har sukai bacci ,ita a lalle kwana uku.
        Washegari wajen 10am suka nufi Zaria tunda 12pm za’ai d’aurin auren.
       Kafin su isa ‘kafarta tayi tsami,an tarbesu cikin mitintawa sun gaisa da ‘yan uwa da abokan arzi’ki,gidan wani yayan umma suka kwana washegari aka rarrakasu gidajen wasu ‘yan uwan kowa yana murnar ganin matar Ahmad ,around 3:30pm yace su tafi Reyhana haushi ya kamata dan ita sam bata gaji ba.
       Wata ‘yar’kanwar umma ana ce mata Zainab tare suka dawo kano da ita tunda ana hutun makaranta ,bata fi 13yrs ba wasu lokutan dama tana zuwa hutu gidan umma.
            ***
   Mommy suna zaune da Ikram tana so a turawa Reyhana wasu necklace sample ta za’ba Abba ze siya musu.Ikram koda ta duba  last seen nata taga an dad’e.
        ” Mommy anya kuwa zata gani naga bata hawa fa yanzu”.Ikram ta fad’a.
         “Ni ayya bata ma siyar da wayarta ba da rannan da muka je duba sirikarta ‘karama ce a hannunta”. Mommy ta fad’a.
        ” Anya kuwa bara de na kira”.Cewar Ikram.
    
        Bayan Reyhana tayi picking da Ikram ta tambayeta seta ce wayar ta samu matsala be.
        “Mommy wayarce wai ta samu matsala”.Ikram ta fad’a still wayar na kunnenta.
            ” Toh anjima Sageer zezo ya kai mata gyara “.Mommy ta fad’a.
     ” Yaya sageer zezo ya kai miki gyara”.Ikram ta fad’a.
        Reyhana jin haka yasa ta hau inda-inda “Uhmm..ai..ai yanzu na siyar da phone d’in dan ya ‘baci sosai” .
         “OK toh dama sar’kane zaki za’ba Abba ze saya mana”.
            ” Toh kawai ki za’ba min ba damuwa”.Reyhana ta fad’a.
        Daga haka sukai sallama,Mommy kuwa ko ba’a fad’a ba ta riga da ta gano.
           4:17pm Ahmad ya koma gida daga wajen aiki sede yau ba key a wajen gashi yana ta knocking bata bud’e ba.
         Reyhana kuwa bacci take lakadan,Ahmad har d’an ‘karamin dutse ya d’auka ya bubbuga amma shiru.
       Ransa har ya fara ‘baci dama a yunwace yake ga gajiya daya kwaso.
      Seda yai kusan 20min a tsaye kunnanta ya jiyo ,sede Reyhana tashi daga baccin da tai jikinta har rawa yake dan be isheta ba.
        “Mtchww!” Ta buga tsaki jin an sake yin knocking,hijab ta zira ranta a ‘bace ta bud’e…..
Cikeda takaici yake kallonta a ciki-ciki yai sallama itama a hankali ta amsa ta matsa ya wuce.
     Shi ba abinda ya sake bashi haushi kamar yadda itama ta wani shareshi bako sannu da dawowa sema turo baki dayaga tanayi wanda besan dalili ba.
         Kayan jikinsa ya rage seda ya watsa ruwa tukun ya fito  da ba’kar T-shirt da blue jeans.Kitchen ya nufa ya zubo abincinsa da kansa, tana kallo ya shiga sitting room.
      Ta kula da yadda yake ta cin magani haka yasa ta shige d’aki abinta .
      “Kajimin mutum ya tashe ni a bacci da bugun ‘kofa kuma yana cimin magani”. Reyhana ta fad’a a  a hankali.
     Ita sam bata san ya dad’e yana bugu ba.
        Har ya gama cin abincin be nemi inda take ba illa shingid’a kan kujera da yayi.
   
      ” Instead ta bani ha’kuri shine zata shige d’aki aiko naga meyiwa wani magana”.Ya fad’a a ransa.
        A haka har akai maghrib ya tafi masallaci be dawo ba har seda yayi isha’i tukun ya komo gida dama ya fita da key d’insa.
       Sanda ya shiga cikin d’aki yaga bata ciki ,waje ya samu ya zauna.+
      Reyhana lokacin tana sitting room cin abinci,taji shigowarsa sarai amma ta share dan haryanzu bata huce ba gashi dama ba wuyar yanzu tayi fushi abinka masu ciki.
      Around 9:30pm Reyhana ta fito daga sitting room, koda ta shiga d’akin.
      
        Yana kwance a kan gadon kuma bawai bacci yake ba.Ita kuwa toilet ta fad’a ta shiga ta watsa ruwa sannan ta zira sleeping dress nata ta hawo gadon.
      Duk abinda take yan kallonta,itama tana jin idonsa a kanta amma tayi burus kamar bata gani ba ,juya masa baya tayi tai kwanciyarta bayan tayi addu’ointa.
      Hakan ba ‘karamin sake sashi tunzura yayi ba ,shima kwanciyar yayi ya juya baya.Kowa a cikin zuciyarsa da abinda yake tunani.
               ***
Washegari da asubah bayan tayi sallah yunwa ta hanata komawa ,seda ta zubawa cikinta tukun ta komo d’akin.
     “Ina kwana”. Ta gaisheshi.
      ” Lafiya”.Ya amsa ciki-ciki.
       “Wai yaya laifi nayi koh meh?” Reyhana ta tambaya dan yadda ya amsa mata yasa taji hasushi tund ita ba haka ta gaidashi ba.
        “Bakisan mey kikai ba kenan?” Ahmad ya fad’a.
          “Kamarya ? Nifa kayiwa laifin ma,gafa yadda ka tasheni ina bacci jikina yana kyarma na bud’e amma kayi biris kamar bakasan ina gunba”. Cewar Reyhana.
       ” Lalle kuwa nida kika ajje a waje na shafe kusan rabin awa baki ko damu ba illa damuwa da bacci kawai”.
       “Amma de ai kasani kullum da key naka kake fita, kuma ai da idona biyu bazan’ki bud’ewa ba”. Reyhana ta fad’a.
     “Au haka ma zaki ce ?”
    
       “Toh Allah ya huci zuciyarka”. Reyhana ta fad’a.
       Shi hakan ma sake ‘kona masa rai yayi ,bece komai ba sakamakon kiransa da akai a waya.Koda yai picking yaji daga wurin aiki ne ogansu yana nemansa,dan haka ya mi’ke da sauri yayi wanka ya fito.
       Reyhana tana kallo ya sanya kayansa be ce mata ko ‘kala ba.
      ” Na tafi”. Abinda yace mata kenan sanda ya zira takalmi.
      Shiru tayi har ya fice tabi bayansa da kallo.Ba abinda ta tsana irin taga ya fita beyi breakfast ba.
       Reyhana agogon d’akin ta kalla taga 7:17am ,mi’kewa tayi kan gadon ta koma baccinta.
STORY CONTINUES BELOW
      Reyhana se wajen 10:34am ta farka, tashi tayi ta gyara gidan yayi tsaf se lokacin ta tuna da walima ta graduation d’in saudat ‘kawarta data kammala university.
     Gashi bata da isassun kud’i hannunta,tunani tayi ‘kila ma da biyu yayi hakan dan ya rama shiyasa yai ficewarsa.
      Koda rana data kira wayarsa beyi picking ba kusan 2missed call,daga baya ma jitayi wayar a kashe ba mamaki kashewa yayi.Abinda tayi tunani kenan a ranta.
       Tana zaune 3,4:30 har 5 lokacin ta gama fiddarai ranta yayi matu’kar ‘baci.
        Dama ta had’a wani leman tsamiyarta ,saboda haka ta tashi ta d’auko a fridge yayi sanyi gwanin sh’awa sitting room ta kai ta ajje.
     Bayan data ajje ta shige toilet, ba jimawa sega shigowar Ahmad ganin da akwai light yayi saurin shiga sitting room dan saka charge a wayarsa,a garin hakane ‘kafarsa ta shura center carpet d’in lemo ya kelaye ‘kasa😱
       Reyhana dede lokacin take shigowa d’akin.
      “Ya salam!” Ya furta.
   Jug d’in ya d’aga gashi tuni carpet d’in ya kusan tsotse  lemon dan haka ya mi’ke zai d’akko mopper.
     
       Nan fa ya lura da Reyhana dake tsaye a bakin ‘kofa ko ba’a fad’a ba yasan ta hau sama(up up🔥).
      Lemanta dako sha bata yi ba tana azar’ba’bin tasha ko taji sanyi shine ya zubar mata duka goma da ashirin(😀bani nace ba Reyhana ta fad’a).
     Kan kice me hawaye tarr ya fara kwaranyowa dama tuntuni ya tsaya a ma’koshinta kawai dama ce bata samu ba yanzu kuwa tana da dalili.
     Da sauri ya ‘karasa inda take ya fara lallashinta”Reyhana please am sorry bada sani na bane ban lura ba kinji”.
    Ai kamar zigata yake, hannunsa ta tankwa’be ta juya zuwa d’aki.Kan gadon ta fad’a tayita rera kukanta.
     “Dan Allah kiyi shiru Reyhana please am sorry”. Ahmad ya fad’a sanda ya zauna a gefenta.
       ” Kana sani kayi kuma dama haushina kake ji tuntuni”.Ta fad’a cikin kuka.
       “Meyasa zanji haushinki ,ki tashi komai ya wuce please bana son wannan kukan”.
          ” Ba haushina kake ba ka’ki d’aga kirana kasan zan fita yau”.Cewar Reyhana.
           Shi se yanzu ma ya tuna da wata fita unguwa.”Reyhana ai na manta sam, meyasa baki tunan ba? Kinsan bazanyi haka ina sane ba ko na ‘kuntata maki”.
    “Kuma wayata ba charge d’azu da kika kirani ,sanda naga missed call d’inki zanyi calling back wayar ta mutu please kiyi ha’kuri”.
      
       Shiru Reyhana tayi bata sake cewa komai ba amma ta tsagaita da kukan.
    ” Azizaty”.Ya kira sunanta.
     Reyhana bata amsa ba ,jin tayi shiru ya sake kira.
     “Azizaty”.
     ” Uhmm”.Ta amsa a ciki.
     “Kin ha’kura yanzu?” Ya tambayeta.
     Kai ta kad’a ba tare da tace komai ba.
      “Toh kinci abinci ?”
  Nan ma kai ta kad’a,hannu yasa ya d’ago ta a hankali.Fuskarta tayi sha’be-sha’be da hawaye.
     Idanta ta sauke ‘kasa ,hannunsa  yasa ya goge mata hawayen ya d’ago da ha’barta.
     “Please look at me”. Ya fad’a.
       A hankali ta kallesa sannan ta sake sauke idanuwanta.
       ” Am sorry kinji”.Ya sake fad’a.
        A hankali ta kad’a kai alamar ta ha’kura.
      “Ok smile”.Ya fad’a.
       D’an guntun murmushi ta saki ba tare da ta kallesa ba.
       ” Maman Baby saura na baby baki masa murmishi ba ko bakisan tana kallonki ba duk abinda kike”?”
     Jin ya ambaci haka ta d’ago da sauri “Tana kallona kuma? Yana de kallo na”.
       ” Auu! Naki choice d’in kenan ? Nide itace ba shi ba”.Ahmad ya fad’a.
      “Toh nikuma ba haka ba “. Cewar Reyhana.
     “Ok then we shall see ,nan bada dad’ewa ba”. Ahmad ya fad’a tare da jawota jikinsa yana shafa bayanta.
          Nan take suka mance da fad’an kamar basu ne ba.
               ***
    Mommy sautin muryarta ne yake tashi a part d’inta kana doso wajen zaka jiyo muryarta.
    Waya take da Anty Asma’u kuma hira duk bata wuce ta Reyhana ba.
      ” Yanzu wayar tata ta siyar ta bashi kud’in kenan?” Cewar Anty Asma’u bayan da Mommy ta labarta mata komai.
    “Eyyi taga zata iya se tai tayi”. Mommy ta fad’a.
     ” Ni yarinyarnan ma gani nake ciki gareta “.Mommy ta fad’a.
   
     ” Ahaf ai na ayyana ,yanzu a wannan ‘kuntacaccen gidan zata bari ta samu ciki”.Cewar Anty Asma’u.
  
      “Eyyi bata da tunani ai ,ni naga d’an ‘beran da za’a haifa gafa yadda take d’ura abincin lami a cikinta ko kifi babu a abinci ya kike tunani yaro ze kasance”. Mommy ta fad’a tana kumfar baki.
     ” Hmm Allah de ya sawwa’ke ,amma fa baza ki barta ta haihu a gidanta ba” Anty Asma’u ta fad’a.
      “Ahh dama yaushe ai dolensa ta dawo gida idan ba so yake jininta ya ‘kafe ba kuma”. Cewar Mommy.
       Sageer tun shigowarsa yake jin d’aga muryar Mommy ,kan wata kujerar d’akin ya zauna zaman jira ta gama wayar.
        ” Mommy ku baku da zance se maganar Reyhana koyaushe Reyhana kubarta mana”Sageer ya fad’a bayan data gama wayar.
      “Dalla rufen baki, kai haryau yarone baza ka gane mey muke nufi ba daga kai har Reyhana d’in”. Mommy ta fad’a.
       ” Kuka san gaba mey ze faru”.Sageer ya fad’a.
 
      “Koh? A hakan da certificate d’in diplomar zeyi arzi’ki?” Cewar Mommy.
       “ARZI’KI RABO de”. Ya fad’a.
       ” Kai kasani nide ina sa’kona dana aikeka idan bashi ya kawo ka ba ka iya bani space”.Mommy ta fad’a.
      “Gashi”. Ya mi’ka mata kud’in daya ciro mata a ATM.
             Yana bata ya fita ya koma sashensa…
 Yau Reyhana tun 10:30am ta gama komai dan yau gida zata da wuri Ahmad dama yau alhamis  yana azimi shiyasa ko girkin rana batayi ba wajen 11:37am ta gama shiryawa.
      Sanda ta shiga gida Abba ze fita nan ya tsaya suka gaisa tukun ya fita.
       Tana shiga ciki inno ta gani tana goge-gige a parlour.
   
       “Ina kwana inno”.Reyhana ta gaidata.
       ” Reyhana kece a gidan? Lafiya lau “.Ta amsa.
        ” Su Mommy suna d’aki ne?” Ta tambaya dan taga bakowa a parlourn.
        “Eh Walida ce bata da lafiya suna d’akinta dan basu jima da dawowa daga aibiti ba”. Inno ta fad’a.
       ” Tohh! Allah ya sawwa’ke bara na hau saman”.Reyhana ta fad’a.
      A kwance ta isketa a gado se fad’a ake da ita wajen shan magani.
       Tana ganin Reyhana ta fara ‘ko’karin tashi zaune.
      “Yi zamanki keda bakida lafiya”. Reyhana ta fad’a.
         ” Mommy ina kwana”.Reyhana ta gaisheta bayan ta zauna a wata kujera dake d’akin.
        “Lafiya “. Mommy ta amsa.
         ” Ya jikinnata ?”Reyhana ta tambaya.
        “Da sau’ki,tashi tayi da zazza’bi seda aka kaita asibiti”. Cewar Mommy.
       Su Ikram da Sageer ma suka gaisa da ita.
  Bassam kuwa yana makaranta.” Walida kisha magani kinji koh bakya so ki warke?” Reyhana ta fad’a.
     Kai ta girgiza alamar “A’a”.
      ” Toh maza tashi kisha”.Ta fad’a.
 
      Da ‘kyar aka samu tasha maganin sannan ta samu ta sake shan tea daga baya tayi bacci.Se lokacin ta barsu suka sarara dan Walida bade raki ba.
       Sageer ya wuce d’akinsa haka Ikram ma.Reyhana kuma d’akin Mommy.
       “Reyhana meyasa kike cutar rayuwarki?” Mommy ta fad’a .
        “Yanzu har takai ga kin fara sayar da abubuwanki ,wannan shine rayuwar da kika za’bawa kanki?” Cewar Mommy ranta a ‘bace.
         “Mommy fa daman ta fara bani matsala wayar”. Reyhana ta fad’a.
        ” Bawani nan ‘karya kike,nasan mijinki kika bawa kud’in”.Mommy ta fad’a.
        Reyhana shiru tayi ta sunkuyar da kai dan ta rasa abin fad’a.
          “Ke bazaki ta’ba gane mey nake nufi ba ,ki duba kiga tun ba aje ko ina ba kun fara shiga cikin wannan halin ina ga kun fara yara,Ahmad sam ba tsaran aurenki bane baki dace dashi ba baze iya ciyar dake ba a haka kuma kike tunanin kuyi ‘ya’ya dashi”.
         Reyhana kwallar da take ma’kale take ta zubo kalaman Mommy suna tsorata ta.
      ” Mommy umma ce fa bata da lafiya shine na siyar dan akaita asibiti”.Reyhana ta fad’a murya na rawa.
        “Ummansa ce ba lafiya? Yanzu kinzamo kece mijin kenan”. Cewar Mommy.
        ” Reyhana ina tausaya maki amma ke gani kike kamar na matsawa rayuwarki ki”.
       Sallamar Ikram ce tasa suka katse maganar da suke ,da sauri Reyhana ta goge hawayen idanuwanta.
        Mommy tashi tayi ta bassu suna ta hirarsu.Daga bisani suka shiga kitchen Ikram da Reyhana suka soya wainar flour dama gashi Walida tana so.
STORY CONTINUES BELOW
        Kasancewar Ahmad yana azumi yasa ta koma gida wajen 4pm saboda had’a masa abin shan ruwa.
         Mommy da hankalinta ya kasa kwanciya da al’amarin Reyhana yasa Abba yana dawowa ta zauna dashi ta zayyane masa komai.
       “Toh ke yanzu mey kike so nayi?” Abba ya tambaya.
       “Haba Abban Reyhana taya zaka fad’i haka kai da kanka ya kamata ka nemo abun yi”. Mommy ta fad’a.
      ” Nide na fad’a maki ba ruwana a cikin wannan zancen,ki bar yarinya kin’ki ke kullum complain tunda mike da ita bata ta’ba kawomin ‘karar yarannan ba suna zaman lafiya kuma sena sa baki”.Abba ya fad’a.
      “Aikuwa ni ina da abinyi tunda kai baza kace komai akai ba”. Mommy ta fad’a.
      ” Mey kike tunanin yi?” Abba ya tambaya yana jiran amsarta.
      “Ya sawwa’ke mata ,bazan bari ina kallo ‘yata ta zauna a ‘kuntatacciyar rayuwa ba”. Mommy ta fad’a.
        ” Ya sawwa’ke mata fa kika ce? Anya kuwa kina da tunani ?” Cewar Abba yana mamakin kalaman Mommy.
      “Toh wani abune? Ai gaskiya na fad’a baze iya ri’ke mana ‘ya ba dan haka seya rabu da ita bamu gaji da ita ba”.
      ” Kinga kunnena baze iya d’aukan wannan abun ke iya fita ko kiyi shiru”.Abba ya fad’a.
      Mommy bata sake cewa komai ba ta mi’ke tai ficewarta.Abba bayanta yabi da kallo kawai ya girgiza kai.
          
                ***
           Akwai lokacin da Mommy ana wani suna koda aka fad’a wa Reyhana ba ta samu zuwa ba saboda kud’in transport kuma bawai ta fad’a wa Ahmad ba yace baida kud’i,kawai ta san baida isassun kud’i shiyasa batai masa maganar sunan bama.Mommy kuwa tasha haushi nanma haka bata gaji ba seda ta fad’a wa Abba ita a lalle seya d’au action akai.
      Tun Abba baya biye zancen har shima abun ya fara damunsa kuma bawai ya fara ‘kin Ahmad bane kawai de ‘yar tasa ya fara tausayawa amma kuma sam be nuna wa Mommy hakan ba balle Reyhana.
      Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa da dad’i ba dad’i, Reyhana cikinta ya cika wata 8,zama da ‘kyar tashi da ‘kyar.Yanzu ta dena cin d’ata, mitimis da albishir ta tusa a gaba.
        Mommy kuwa tana kan bakatta na dawowar Reyhana gida,ita kuwa Reyhana ko Ahmad ma batayi wa maganar ba ta san baida ra’ayin mace ta koma gida wanka.
         Reyhana tana d’aki tajiyo ‘karar wayarta a sitting room, koda taje dubawa taga wanda ke kira taga Mommy ce.Se a karo na biyu ta d’aga kiran.
         “Ina yini Mommy”. Reyhana ta gaisheta.
         ” Lafiya lau,bakya kusa da wayar koh?”
         “Eh”. Reyhana ta amsa.
          ” Toh ya maganar komowarki ,ko har yanzu baki fad’a masa ba?” Mommy ta tambaya.
        “Eh amma yau zan fad’a masa”. Reyhana ta amsa.
         ” Toh kide fad’a masa dan ba ruwana kika haihu a gida dan kinsan ni bani da wacce zan kawo maki atoh”.Mommy ta fad’a.
     “InshAllah zan fad’a masa”. Ta amsa.
    Daga haka sukai sallama ,Reyhana tunanin yadda zata ‘bullo masa da wannan maganar take.
            ***
Ahmad kuwa a gurin aiki Umma ta kirasa take fad’a masa ya biyo ta gidanta.
    Dama lokacin tashinsa yayi dan haka ya biya gidanta.
     Bayan sun gaisa take ce masa Mommy ta kirata d’azu.
STORY CONTINUES BELOW
      ” Mommy ce ta kiraki?”
      “Ehyi ta fad’a min Reyhana gida zata koma”. Umma ta fad’a.
      ” Gida kuma?” Ya tambaya cikeda mamaki.
      “Ehyi a can zata haihu”. Ta amsa sa.
 
     ” Toh ai ni bata fad’a min ba”.Cewar Ahmad ransa a d’an ‘bace.
      “Toh gashi mahaifiyarta ta fad’a”.
      ” Nifa bana son komawa gidannan fa”.Ahmad ya fad’a.
      “Toh ai na lokaci ne kuma bayan haihuwar fari ce”. Umma ta fad’a.
       ” Sekace da yanzu fa an dena wannan”.
       “Toh sekayi ha’kuri da hakan”.
       ” Sede bayan ta haihu”.Ya fad’a.
      “Toh meye banbancin du d’aya ne fa kwana nawane”
     Ahmad badan yaso ba ya ha’kura, ko abincin Umman ma be ciba.
      Reyhana a gida tana ta tunanin yadda zata fad’a ma, koda ya shigo gida bayan yaci abinci yayi maghrib suna zaune kawai tunani take.
     Ana cikin haka taji yace “Meyasa baki fad’a min ba?”
     “Mey?” Ta tambaya.
     “Zaki koma gida”. Ya amsata.
     ” Dama yau nake son fad’a maka”.Ta fad’a.
     “Amma waya fad’a ma?” Ta tambaya a ranta tana Allah yasa ba Mommy bace.
     “Umma ce ta fad’a wa Mommy”. Ya amsa ta.
      ” Azizaty haka mukai dake?” Ya tambaya.
      “Yaya kaga idan na zauna a gida ba a da wacce zata kawon ta zauna shiyasa zan koma “. Ta fad’a.
       ” Ni kad’ai kike so ki barni?” Ya fad’a kamar d’an yaro.
      “No am always with you forever and where ever you are”. Ta fad’a tana murmushi.
     ” Dad’in baki koh? ” Ya fad’a.
     “No hakane ai”. Reyhana ta fad’a.
     ” Ok, but zanyi missing d’inku keda baby “.
      ” Muma”.Ta fad’a.
      “Yawwa an samo mana sunan?”
      “Eyi amma bazan fad’a ba that’s surprise”. Cewar Reyhana.
       ” Ko d’an hint?”Ya tambaya.
       “Wayo when the time zan fad’a ma”.
        ” Ok we are waiting “.Ahmad ya fad’a yana dariya.
        ” Yau ba tausa?”Ya tambaya.
        “Anjima”. Ta amsa.
         ” Ok Azizaty “.
     
              ****
       Seda Reyhana ta ‘kara kusan 2weeks sannan ta koma gida ,kayan baby da Ahmad ya sayawa baby ta tafi dasu ,su towel ne haka da saitin sauran kayan wanka na baby.Mommy a hakan ma seda ta kushe kayan Reyhana sede kawai ta kawar da kanta.
      Yau kwananta uku da komowa Ahmad yazo sau biyu.Tunda ta dawo gida ba wani aiki take ba tana d’aki idan yara sunje makaranta inko suka dawo sesi zauna suyi ta hirarsu da yamma kuma Ikram ko Walida ta raka ta fita waje dan tattakawa.
          Mommy kuwa yanzu dad’i take ji Reyhananta a kusa da ita yanzu ‘yarta zata ci me kyau(Mommy ta fad’a not me wooo!)
        8:12pm,suna zaune yaran harda Reyhana a parlour sun kunna TV suna kallon Bollywood”.
      ” Yaya ni a chanja channel d’innan akai MBC 3″ Walida ta fad’a.
  
     “Baza a chanja ba!”. Ikram ta fad’a a tsawace.
      ” Meyai zafi kiyi ha’kuri Ikram ki batta ta kalli cartoon ko d’aya ne”.Reyhana ta fad’a.
       “Nikuma fa na katse nawa kallon?” Ikram ta fad’a ranta a ‘bace.
     “Yaya ki rabu da walidannan idan baza ta kalla ba taje ta kwanta”. Bassam ya fad’a dama shi kullum kishiyanta ne.
       “Dukanku ha’kura za’kwi dan yanzu zan kai wrestling”. Sageer ya fad’a.
       ” Chabb! Lalle kuwa ashe bame kalla”.Ikram ta fad’a harda harara.
      “Ke! dawa kike?” Sageer ya fad’a yana ‘ko’karin mi’kewa.
     “A’a Sageer kaifa yaya ne ka cigaba da chat d’inka de”. Reyhana ta fad’a.
     ” Mey yake faruwa neh?” Abba ya tambaya yana ‘karasowa inda suke.
     “Abba sannu da zuwa”. suka fad’a.
     ” Abba rashin kunya ya Ikram takewa yaya Sageer “.Walida ta fad’a tana kallon idan Ikram taga ya zatai.
       ” Abba ‘karya take”.Ikram ta fad’a.
     “Toh ya isa”. Abba ya fad’a.
      Mommy dede lokacin itama se gata ta sakko.
      ” Abban Reyhana ka dawo kenan”.Cewar Mommy.
      “Shigowata kenan”. Ya amsa.
        Abba d’aki ya nufa bayan ‘yan mintina daya sakko suka nufi dinning dukansu domin cin abincin dare.Gwanin sha’awa full house ,sunayi suna hira har suka kammala ,daga nan kuma aka zo aka zauna a parlour shan ice cream ana hira.Sun zirfafa suna hira wayar Reyhana tayi ringing Allah yasa tana kusa da ita da bazata jiyo ba.Koda ta duba taga Dear❤ zame jiki tayi tabar musu parlourn ta haye sama amsa wayar habibinta.
      Mommy kuwa tana kallon sanda Reyhana ta tashi ,ta’be baki tayi ta cigaba  da hirarta.
Azizaty kin manta dani”. Ahmad ya fad’a.+
      ” Ashe zan iya mantawa da kaina ,kana raina dear “.Reyhana ta fad’a cikin sanyayyar murya.
        ” Toh ya kike ya babynmu?” Ahmad ya tambaya.
       “Lafiya but we miss you much”.
      ” Nima Azizaty tun d’azu ku nake tunani”.Ahmad ya fad’a.
      “Kaci abinci?” Ta tambayeshi.
       “Na kasa ci Azizaty,ba dad’i”.
       ” Ayya! Ka daure kaci kaji”.Reyhana ta fad’a.
        “Toh zanci amma ba yawa”.
       ” Yafi de ka’ki ci”.
       Sun d’au tsawon lokaci suna waya kafin daga bisani suyi sallama sannan tayi kwanciyarta dama da wuri take baccinta.
        Washegari da asubah kiran Ahmad ne ya tasheta ,bayan sun gaisa ta tashi tayi sallah tayi azkar d’inta.
      Da safe kafin ya fita seda ya  sake kiranta a waya.
       Kamar koyaushe Reyhana ta shiga kitchen ta had’a tea tasha da cake dan yunwa take tashi da ita.
     Koda ta koma d’aki jin baccin ya’ki zuwa ta had’a ruwan wanka a kettle,’yan  minute kad’an ta shiga tayi wankanta ta zira doguwar riga dan kusan duka rigunanta basa shigarta sede tayi ta fama da dogayen rigunan.
      Jin zaman d’akin ya isheta ta fito parlour ta kunnaTV ta soma kallo.Se chan bayan wasu ‘yan lokuta suka tashi Mommy ta sakko ‘kasa inno kuma tana kitchen ta fara had’a musu abun breakfast.
       “Mommy ina kwana”. Reyhana ta gaisheta.
      ” Lafiya lao,ke kuma baki koma baccin bane ?” Mommy ta tambayeta.
      “Eh”. Ta amsa.
      ” Toh ki sha tea d’in?” Ta tamabaya.
      “Eh nasha”. Ta amsa.
      ” Yawwa ya jikin Walidan ? “Ta tambaya.
     ” Walida taji sau’ki d’azu ta farka tasha tea sannan aka bata magani”.Mommy ta amsa.
     “Bari na shiga kitchen na duba inno”.Mommy ta fad’a.
     ” Toh”.Reyhana ta amsa ta cigaba da kallonta.
       Se around 9:30am suka hallara a dinning dukansu Ikram a haka ma bacci be isheta Reyhana ce ta tasota.
      “Yarinya kwanan zaki dena baccin safe”. Reyhana ta fad’a dan nan bada dad’ewa ba zata fara zuwa university tunda ta samu admission.
     ” Abinda nake fad’a mata kenan ai”.Cewar Abba.
    “Gara ma yarinya ki soma ‘koluwa kyaji yadda nake ji”. Sageer ya fad’a.
     Dariya sukai ,ita kuwa harara ta watsa masa.
    ” Toh kai ai dole kasha wuya tunda kake namiji ita ai mace koh”.Mommy ta fad’a dan ta kare ta.
      “Atoh kuma dole a kaini school”. Ikram ta fad’a tana masa gwalo.
     Shikuwa sageer baki ya ta’be ya cigaba da cin abinci,Walida kuwa ana d’aki ana bacci.
         ***
Da asr sega su Anty Asma’u da sauran sisters na Mommy ,Reyhana tana parlour tajiyo muryarsu kuma dama taji inno tana musu sannu da zuwa a waje.
 
     Da sauri Reyhana ta bar parlourn wai kunya take ji kar su ganta.
STORY CONTINUES BELOW
      Aikam basu dad’e da shigowar ba suka tambayeta.
     ” Ai tana jin muryarku ta ruga d’aki wai kunyar ku ganta take”.Mommy ta fad’a.
     Reyhana da take d’aki ta kasa kunne ta jiyo Mommy ta fad’i haka ji tayi dama tuntuni ta fita kafin ta fallasa ta.
     Gabad’ayansu dariya suka sa, Anty ummi (autar su Mommy) tace “Aiko ki dena kika sani ko mu zami kar’bi haihuwar”.
     Nan ma dariyar sukai mata ,Reyhana jitake kamar ta nuste.
     Seda ta gama ‘bata lokaci ta shiga d’akin Walida da tun d’azu ta tashi amma bata sakko ‘kasa ba.Lalla’bata tayi suka fito tare banda hijab d’inda ta zinbila tasa ta a gaba wai ta kare cikin.
       ” Ina yini ta gaidasu”.Tana daga gefe-gefe se wani raku’bewa take.
     “Lafiya lao”. Suka amsa.
     ” Maman boy ce ko maman girl?”Anty ummi ta fad’a.
     Shiru tayi bata ce komai ba,sede idan kai magana ta amsa da eh ko aa,daga baya ma sulalewa tayi ta koma d’aki.
       Wayarta ta d’auka ta kira Ahmad suka sha hirarsu ba jimawa sega kiran umma itama ta kira taji ya take.
       Seda za su tafi tukun ta koma sukai sallama,itama ba jimawa suka itada Ikram tattaki.
                ***
    Idan kuwa su Mommy duka zasi je unguwa ita kad’ai suke bari dukda de ma yanzu Mommy ta rage fita d’in saboda tsaro…
      Ahmad a week d’innan ma ya sake zuwa amma baya dad’ewa idan yazo dan yawanci bayan maghrib yake zuwa.
       A kwana a tashi Reyhana cikinta ya shiga 9month,Abba ya ‘kara mata wasu siya-siyen akan na Ahmad haihuwa yanzu ake jira yau ko gobe.
       Ahmad daga wajen aiki gidan Umma ya wuce koda suka gaisa ya fita majalissarsu ,Sadiq(kusan shine babban abokinsa ,beyi aure ba) se tsokanarsa yake wai ya zama gauro.
       “Aiko ‘karyarka ka kirani da gauro ko ba komai nasan ina da mata kaikuwa fa babu baka ma tunanin yin auren”. Ahmad ya fad’a.
      ” Zaka sha mamaki lokaci guda sede ka ganni nazo gidanka da matata”.Sadiq ya fad’a.
       “Haka de kace dan banga alama ba”.
      ” Ka zuba ido kawai”.Cewar Sadiq.
      Suna cikin hira sega kiran Reyhana, ganin haka Ahmad ya matsa daga gun.
       “Maman biyu”. Ya kirata.
       ” Niba maman biyu bace”.Reyhana ta fad’a.
       “Au bakyaso?”
       “Chabb! Kana so nasha wuya kenan”.Ta fad’a.
       ” A’a ai kullum ina yi miki addu’a”.
      “D’ayan de a yanzu is enough”. Ta fad’a.
   
       ” Azizaty kidena tsoro fah,inshaAllah komai zezo da sau’ki”.
        “Ameen”. Ta amsa.
     Hira kad’an suka ta’ba sannan sukai sallama.
       Walida ta samu sau’ki har ta koma makaranta,Ikram ma satinta biyu da fara zuwa school amma har an fara rigima da Sageer wai shi tana makarar dashi a tafiya kenan,a dawowa kuwa wataran har tahowarsa yake ya barta sede ta hau d’an sahu.
       Yau wajen7:43am ita Ikram tana da lecture na safe shikuma bashida ,da’kyar seda Mommy ta taso shi ya fito ko wanka beba kayan jikinsa ma wandan kawai ya sauya rigar kuwa T shirt d’in jiyace.
STORY CONTINUES BELOW
      A cukule ya fito fuskarsa ba annuri ,Ikram kuwa tun-tuni ta gama shiryawa shi take jira,ada taso yi masa tsiwa amma ganin yanayin annurinsa tayi shiru.
     Bayansa tabi tana masa gwalo har seda suka shiga mota ta nutsu.
      Koda suka hau titi Sageer ya fara wani tu’kin wula’kanci ,motar kamar bata tafiya se horn ake musu kowace mota sede tayi overtaken. Ikram kamar ta rusa ihu.
     ” Wai matsala ta samu ne motar?” Ta tambaya.
      “Bansaniba kuma yarinya zaki dakinsani”. Ya fad’a tare da makirin murmushi.
      Kafin tayi magana taji ya zugi motar kamar wani mey gudun race.
        ” Wayyo dan Allah ka bari rannan d’aya garemu”.Ikram ta fad’a a rikice.
       Kamar ma zigashi tayi  haka ya sake fyallarsu kafin a shiga school fuskarta ta cika da hawaye.
       “Gobe ki sake taso ni, kuma ki fad’a wa Abba kiga”. Ya fad’a lokacin da yayi parking a cikin school.
      Abinda ya guda shi ya faru,’yan click d’insu ya gani sun nufo inda yake,gashi Ikram bata fita ba dole suka taddashi.
      Yana zuge glass d’in suka fara.” Wanka(sunan da ake kiransa dashi) yane da matsalane muka ganka haka”.
     Se yanzu ya sake kallon rigarsa da yayi bacci da ita,haushi ya kamasa.Sageer akwai son gayu,haka yasa aka sa masa wanka.
       “Nayi dropping yarinyarnan ne se anjima zan shigo lecture”. Ya fad’a.
       Fitowa tayi ta wuce ko kallan inda suke batai ba.
      ” A haba kazo mu zagaya makarantar mana”.D’aya daga cikinsu ya fad’a.
      “No se anjima”. Ya fad’a .
     Ba yadda basi dashi ba ya tsaya amma ya’ki ,shikuwa baya so ‘yan mata su ganshi a haka su raina sa.
           ***
   Wajajen 5:27pm Reyhana suka dawo daga waje ita da Walida.
       Koda suka dawo d’aki ta shige tayi zamanta dan bata jin normal cikinta se hautsinawa yake kad’an-kad’an tana jin suka.
      Shiru tayi bata tafiya wa Mommy ba har aka bayan sallar maghrib ,koda aka zubo abinci ma kad’an taci.
     Suna parlour dukansu banda ita da tana d’aki tsoro ya kamata kuma ta’ki fad’a wa Mommy, kuma ita Mommy tayi zatan ko waya take shiyasa bata nemeta ba.
      Ahmad kuwa around 6 ya koma gida koda jona phone d’insa a charge se ta ‘ki hawa,da alama ko charging point ne.
        Hakannan ya fita masjid amma yana ta tunanin Reyhana dan yau tun safe basi sake waya ba wayarsa ta mutu.
      Reyhana kam har da Mommy ta shigo d’akinta data tambayeta lafiya bata sakko ‘kasa ba tace ba komai.
      Mommy ganin haka tai wucewarta d’aki,kowa ya koma d’akinsa.10:24pm kuma tana trying number na Ahmad a kashe,abi gaba yake ‘karayi ciwo se ‘karuwa yake.
      Tun tana daurewa ganin yin hakan ba mafita bane ta d’auki wayarta ta kira Mommy.
      Seda ta kira kusan 3× Mommy ta farka ganin Reyhana yasa da sauri ta mi’ke.
     D’akinta ta shiga ta ganta se mur’kususu take.
       “Reyhana jikinne? “
         “Cikina washh! Mommy”. Abinda take fad’a kenan.
       Agogon d’akin ta kalla taga 12:05am.” Tun d’azu Reyhana na tambayeki kika ce ba komai, bari na fad’a wa Abbanki”.Mommy ta fad’a tare da fita.
      Mommy ce ta taimaka mata suka sakko ,Abba ya fito da mota aka sata a ciki Mommy ta d’akko kayan da za’a bu’kata.
      Inno Mommy ta tasa tace ta lura da yaran ,su Ikram baccinsu ma suke.
        Suna isa nurses suka shiga da ita d’akin haihuwa koda suka dubata suka ce da saura,amma de zasu iya zama  a asibitin.
       Wayar Reyhana Mommy ta d’auka ta lalubo number na Ahmad. Koda ta kira aka she taji tsaki tayi,instead ta kira na umma ta’ki.
      “Ya kin kira Ahmad d’in?” Abba ya tambaya.
    “Gashi na kira switched off”. Mommy ta fad’a ranta a ‘bace.
        Reyhana tana ciki se mur’kususu.” Ku kirawon Mommy “. Ta fad’a ma nurses d’in.
       ” Hajiya kizo yarinyarki tana kiranki”. D’ayan nurse ta fad’a wa Mommy.
      Mommy a tsorace ta shiga ciki dan tausayin ‘yartata ya kamata.
      “Sannu kinji”. Ta fad’a.
      Kai kawai take kad’awa bakinta ya bushe.
      Idan ta fara salati seta koma addu’a kafin ta gama seta kamo wata, Mommy ma addu’ar take taya tayi Abba ma yana daga waje yana yi.
       ” Mommy kin sake kiransa?” Ta tambaya murya na rawa
  
     “Na kira a kashe wayar”. Ta amsata.
    Kai kawai ta kad’a tana tapping cinya dan azaba.
      ” Wayyo Allah Mommy !” Ta kurma ihu har Abba seda ya jiyo.
       “Sannu Reyhana”. Abinda Mommy take fad’a kenan.
         (Allah sarki mata😭)
      Daga baya nurses d’in suka fita guda d’aya ce ta tsaya akan Reyhana.
      An d’au  tsahon lokuta ana abu d’aya ,daga baya ya lafa tana maida numfashi hannunta ri’keda Mommy.
      Reyhana har gari ya waye tana na’kuda ta fita daga hayyacinta.
        Yanzu ihun ma ta bari se addu’oi iri-iri ,Mommy da’kyar ta iya barinta tayi sallah ta fito wajen Abba suka gaisa.
          Su Ikram da asubah Inno take fad’a musu,nan da nan jikinsu yayi sanyi ko baccin sun kasa komawa dama lecture d’aya take dashi aiko ta fasa zuwa.
      Koda suka kira Mommy take fad’a musu bata haihu ba.
     Mommy bata dad’e da ajje wayar ba Reyhana ta ‘kwala mata kira,da sauri ta koma d’akin.
          Na’kuda ce ta dawo fiya da baya ,gam ta ri’ke Mommy suna haka nurse d’in suka shigo,Mommy jikinta sake sanyi yayi ganin yadda Reyhana tayi firkai firkai ,Mommy bata doguwar na’kuda shiyasa ta tsorata.
       Mommy fita tayi daga d’akin tabar nurses d’in akan Reyhana.
         Mommy ta kasa zama Abba ma yana tsaye.”Addu’a kawai zami mata Mommyn Walida “. Abba ya fad’a.
         Lokaci guda suka jiyo ta kwalla ‘kara daga bisani tayi shiru sega kukan baby daya biyo baya.
       ” Kaji kamar kukan baby nake ji”. Mommy ta fad’a tana sake kasa kunne.
      “Eyyi nima de..” Be ‘kare ba nurse ta fito.
       “Hajiya congratulation ta haihu yarinyarki…”
    Dayawa suna cewa Ahmad abun yayi masa yawa. I want to remind you this is just the beginning,kude ku cigaba da gashi🔥
   Mommy da Abba a tare suka furta”Alhamdulillah”.+
       Bayan an gyaggyara maman baby da babyn kanta su Mommy suka shiga.Su kansu nurses admiring kyan babyn suke, Reyhana kuwa kallonsu kawai take a zuciyarta tana godewa Allah.
     “Mey aka samu?” Mommy ta tambaya.
     “An haifi mace”. Suka amsata.
     ” Toh mashaAllah ,Reyhana sannu ko”.Abba ya fad’a yana kallonta.
     D’an wahalallan murmushi ta saki ta maida kallonta wajen babyn.
     “Sannu koh”. Mommy ma ta fad’a”.
      Babyn tana hannun Abba Mommy tana daga gefe itama hannunta nakan towel d’in da aka nad’e ‘yar.
         ” MashaAllah”.Mommy ta fad’a.
        Mommy  wayarta ta d’auka ta kira su Ikram take fad’a musu,murna suka shiga yi.
       Bayan ta katse kiran ta kuma kiran Ahmad amma shiru kake ji.Mommy kuwa a ranta tace bazata sake kira ba.
      “Kin sake kiran Ahmad d’in ne?” Abba ya tambaya.
      Kai kawai Mommy ta kad’a fuskarta ta nuna alamar rashin jin dad’i.
      Reyhana tana kallonsu kanta kawai ta kawar ita kanta Ahmad ya bata haushi.
      “Taya za’ai ace ta haihu uban yarinyar ma baya gun? Kuma why not be nemesu ba tun jiya gashi har yanzu” Ta fad’a a ranta.
      Anty Asma’u ma an sanar mata da sauran sisters.
             ***
Shikuwa Ahmad koda gari ya waye da wuri ya shirya ya fita wajen aiki,sunyi da ogansa yau zasu je kasuwa dan haka suka tafi.Amma Reyhana tana ransa dan so yake idan sun dawo ya biya gidan Umma yai waya da ita kafin a gyara wayarsa.
       Wajen 11:00am aka sallamesu daga asibiti,kafin su koma gida dama inno ta d’orawa mey jego ruwa.
       Suna isa Walida ce the first d’in kallon baby har wani rawar jiki take a d’ora mata ita a cinya.
       “Walida baza ki iya ri’keta ba”. Abba ya fad’a.
       ” A’a zan iya “.
       D’an d’osana mata ita akai kafin Ikram da Sageer su kar’beta suma.
      ” Wow! Mommy kalli hancinta da lips d’inta”.Ikram ta fad’a.
       “Dani take kama”. Cewar Bassam.
      Daga Mommy har Abba seda suka dara,banda Reyhana da tunaninta baya gun ,rashin zuwan Ahmad shi ya tsaya mata a rai.
      ” Tabb! Ka cuceta amma ka kalli kanka  ka kalli yarinya  kace kuna kama hhh kade duba(😀 nima nace..).
      Haka suka cigaba da kalleta suna yaba kyanta da farinta (Nide dana kalleta naga copy d’in Ahmad😛).
        Gashinta ma irin nasa ne,kamanninsa sun fito a fuskarta sosai.
         Ruwan wanka Inno ta kai mata toilet,harda hawaye ita wai yayi zafi banda Mommy ta sata a gaba ba da seta surka.
          A cikin atamfofinta ta samu doguwar riga mara nauyi tasa,tea mey kauri Mommy ta had’a mata tasha,se farfesun kaza da inno ta dafo mata taci kad’an.
STORY CONTINUES BELOW
          Kwanciyarta tayi dan bacci ne a idonta ,babynma bacci take dan haka aka rufo musu d’akin suka fito parlour.
         Ahmad basu suka dawo daga kasuwa ba se 1:20pm dan sunsha yawo a kasuwar shi kanshi ya ‘kosa ya komo.Koda suka dawo wajen aikin nasu yana tunanin ko ogan nasu ze barshi ya tafi amma seya bar masa wajen shi ya tafi gida Ahmad kuma ya tsaya akan sauran yaran.Duk haushi ya isheshi ,gashi sam idea d’in ya ari waya be zo masa ba.
       Anty Asma’u wajen 4pm suka zo da sauran sisters, lokacin Reyhana ta tashi daga bacci babynma haka.
  
       “Me jego da babynta mashaAllah Allah ya raya”.Suka fad’a.
         Faten dankali Mommy tasa inno ta dafo mata da’kyar taci rabi hakan ma dan su Anty sunsa baki.
        Baby ta fara kukan yunwa gashi mama be zo ba.Reyhana dama ko gwada bata batayi ba ,se dabino ta tauna ta samata a baki ta lasa.
       Da’kyar tayi shiru ta koma bacci.
        Anty Asma’u dasu ka d’an ke’be take tanbayarta Ahmad.” Kinsan kuwa besan ta haihu bama?” Cewar Mommy.
     “Kamarya? Baku kirashi bane?” Anty ta tambaya.
     “An kira kusan sau nawa amma a kashe “. Ta amsa.
     ” Shine kuma be kira ba har yanzu”.
      “Ai yanzu ta fara gani kinga abinda nake fad’a tun ba aje ko ina ba ya fara wula’kantata,ace tun jiya bazaka nemi matarka ba kaji yaya take ciki”. Mommy ta fad’a.
     Kai kawai Anty ta kad’a” Aiko shima se an gwanya mashi rabi da d’an banza ai ze nemeta ko ba dad’e ko ba jima lokacin za’a nuna masa kuskuransa”.
      “Abbanta ma ai bece komai ba yasan yaran be kyauta ba itama Reyhana haka zata fara gane me nake nufi”. Mommy ta fad’a.
    Parlour suka koma suka cigaba da harkarsu,ita kuma Reyhana lokacin ta samu damar kiran friends nata.
      Ahmad se 6pm ya tashi daga gun aiki,gidan umma ya wuce direct kan ya ‘karasa maghrib tayi.Suna gaisawa ya tafi masjid se bayan ya dawo ya d’auki wayarta yasa credit tukun yayi dialing numbern Reyhana.
       Number busy yaji, har kusan sau uku number busy.Reyhana lokacin tana waya da sauran family and friends tana sanar musu.
     ” Meya sami wayar taka?” Umma ta tambaya.
     “Wajen charging tana ya samu matsala”.Ya amsa.
     ” Toh bakuyi waya dasu ba kenan?” Umma ta fad’a.
     “Tun jiya fa yau kuma aiki ya mini yawa shiyasa ban biyo nan d’in da wuri ba”. Ya fad’a.
      ” Yanzu bata d’aga wayar ba ne?”
      “A’a a busy”. Ya amsa.
       ” Sede ko anjima”. Ta fad’a.
       “Eh”. Ya amsa.
     Reyhana kuwa koda ta ajje wayar Inno ta kai mata ruwa toilet.Yanzu ma tana kwazazo wai ruwan zafi sukai ta drama a toilet.
       Mommy ta rigata fitowa daga toilet d’in tana kallo wayarta tana haske ana kira ,koda ta duba taga umma.
     Wani murmushin mugunta tayi ta d’auka wayar seda taga kiran ya katse tasa  a black list.
      Ya kirata ba adadi waya  busy har ya damu sosai.Hakannan ya ha’kura ya koma gida yana ta shawarar ko yaje gidan su se kuma ya fasa yace gobe.
         Reyhana tana expecting call nashi amma shiru taga gashi Mommy ta goge kiran umma saboda haka bata gani ba.
         Da daddare Abba ya sake shigowa ya dubasu ita da baby.
                  ***
     Cikin dare baby bata barsu sunyi barci ba tayi ta kuka Reyhana kuwa ta’ki bata mama wai ba komai a ciki.
       Washegari da safe ‘yar baby tayi ta bacci abinta jiya bata barsu ba, Reyhana tayi ba itama bacci tayi tayi.
     ” Reyhana tashi zaki ga ruwan wanka”.Mommy ta fad’a.
     Reyhana a cikin bacci taji muryar Mommy, da’kyar ta tashi.
      “Ance ki bata mama kin’ki ba dole ta hanaki barci ba ,bari kici abinci sekin bata dolenki so kike ki barta da yunwa ne”.
      Reyhana tana yamitsa fuska ta tashi,yau ruwan yayi mata dad’i dukda kuwa da zafi.Bayan ta fito aka had’o mata breakfast taci.
    
     Su Ikram lokacin suka shigo ,Walida dake d’aga murya Mommy ta sata yin shiru karta tashi baby.
      Ba’a jima ba ta farka Mommy ta had’a mata ruwan wanka.Walida tunda aka fara yiwa babyn wanka bata tashi ba har seda aka gama se data makara a school tayi tayi Mommy ta barta ta zauna wai yau ai friday amma Mommy ta’ki bari.
        Ikram ma suka tafi ita da Sageer, Abba ma ya fita aiki bayan ya shigo sun gaisa.
    Mommy da Reyhana suna ta drama akan seta bawa baby mama.
       “Mommy zafi fa”. Reyhana ta fad’a.
        ” Kowa da haka yayi raino ,zaki barta da yunwa ne”.Mommy ta fad’a.
        Seda tai da gaske tukun ta bata tana ta ‘yar ‘kara.
       “Ba gashi tana sha ba zaki wa yarinya azaba”.Mommy ta fad’a.
     Reyhana kuwa ta turo baki se hararar babyn take kamar tasan abinda ake(😂).
       Mommy se yanzu ta d’auka wayar Reyhana dake chaji da dabara tayi removing daga black list.
   Du wannan abun Reyhana bata lura ba hankalinta na kan baby.
     Ahmad koda ya tashi da sauri-sauri ya shirya ko breakfast beyi ba.Wajen daya kai wayarsa gyara ya tafi ya kar’bo,a take yayi dialing number na Reyhana.
        Mommy ta fita daga d’akin itako Reyhana ta kwantar da baby tana lalla’bata tayi bacci sega kiran Ahmad.
       Dama a vibration tasa ta ,koda ta duba taga Dear❤ wani sabon jin haushinsa ta sake yi.
       Seda ya kira sau uku tukun tayi picking.
       ” Hello Azizaty meya faru da wayanki tun jiya bana samunki?” Ya fad’a.
        A zuciyarta tace”Rainin hankali a ina ya kira ni jiya?”
       “Tawa wayar ko taka da tun shekaranjiya bana samunka”. Reyhana ta fad’a rai a ‘bace.
      ” Azizaty charging point ne ya samu matsala kuma aiki yayi min yawa shiyasa kika jini shiru”.Ya fad’a.
        “Aiki?” Ta fad’a cikeda rainin wayo.
        “Au baki yarda ba?” Ahmad ya fad’a.
         Yana so ya sake wata maganar ya jiyo kukan baby. Hakan yasa ya tsaya da maganar da zeyi.
      “Reyhana don’t tell me kin haihu bansani ba”. Ya fad’a cikeda mamaki.
      ” Uhmm”.Ta fad’a a ciki-ciki…
    

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *