ARZIQI RABO CHAPTER B
Ahmad jin amsar ta yasa ya kasa sake cewa komai ,shiru dukansu sukai credit na tafiya.
Mommy data ke tsaye a jikin ‘kofar d’akin ‘karasowa tayi kusa da Reyhanan.Wayar ta kar’ba daga hannun Reyhana ma’kale a kunnenta.
“Ahmad yanzu abinda kayi ka kyauta kenan? Reyhana ta cancanci kayi mata haka?” Mommy ta fad’a.

Ahmad jin muryar Mommy kamar daga sama yasa ya gyara tsaiwarsa da yana jingine a garu amma jin muryarta yasa ya mi’ke tsam.
“Eyyi? Activities naka sunfi lafiyarta,ace tun shekaran jiya rabon da kayi waya da ita rashin damuwa da ita ne komey?” Mommy ta d’ora akai.
“Mommy wlh wayata ce ta samu matsala se d’azu na kar’bo daga gyara jiya na kira a wayar umma bana samun ta”. Ahmad ya fad’a.
” Mommy dan Allah kiyi ha’kuri”.Ahmad ya fad’a.
“Kiyi ha’kuri”. Ya sake bata ha’kuri.
Mommy bata sake cewa komai ba wayar ta katse sakamakon credit daya ‘kare.
” Matalauci”. Mommy ta fad’a.
Reyhana taji abinda Mommy tace amma tayi kamar ba sauraro take ba.
Ahmad kuwa ba tare da ya ‘bata lokaci ba ya taho izuwa gidansu Reyhana.
Seda yayi kusan 5min ya iya shiga gidan dan nauyin had’a ido da Mommy yaji balle Abba.
Yana shiga tun a harabar gidan ya had’u da Sageer.Bayan sun gaisa ya ‘karasa dashi ciki.
A parlour suka tarar ba kowo dan haka Sageer ya hau sama ya sanarwa da Mommy.
Babyn na hannu Mommy lokacin Sageer ya isketa.
“Mommy gafa ya Ahmad yazo”. Sageer ya fad’a.
“Shine yazo?” Cewar Mommy.
“Eh yana parlour”. Ya amsa.
” Toh ungo ta kai masa “. Mommy ta fad’a tare da mi’ka masa babyn.
Hannu yasa ya amsa sannan ya fice.
Itade Reyhana ko ” a” batace ba kuma bata tashi ba .
A parlour Ahmad yana tsammanin ganin Mommy amma yaga Sageer tafe da baby,bawai be damu da yaga babyn ba amma a yanzu Reyhanansa yake son gani.
A sanyaye ya kar’beta daga hannun Sageer daya mi’ko masa.
Yana mi’ka masa ya fita daga parlourn dan school ze koma, Ahmad daga shi se baby a hannunsa.Ji yake kamar ba ‘yarsa ba saboda mamaki.Daya kalli fuskarta da idanuwanta suke a rufe a ziciyarsa yana me godewa Allah.
Sunan da za’a saka wa babyn ne ya fad’o masa dan,tuna Reyhana data ce zata fad’a masa sunan da take so a saka wa babynsu ya shiga yi.
A zuciyarsa kuwa yana fad’in ina ma yana nan ta haihu.
Addu’oi yayi ma babyn ya ‘kura mata ido yana sake ganin kammaninsa a fuskarta.
Sakkowar Mommy ce tasa yayi saurin d’ago da kansa.So yake ya sakko ‘kasa daga kan kujerar amma kuma ga baby a hannunsa,hakannan ya ‘kwantar da ita a kan kujerar daga gefe ya sakko ‘kasa.
“Ina kwana “. Ya gaisheta.
” Lafiya”. Ta amsa.
“Mun samu ‘karuwa kuma ,Allah ya raya “. Mommy ta fad’a.
” Ameen”.Ya amsa a hankali.
Yana so ya tamabayeta jikin Reyhana amma ya kasa, Mommy ta gano hakan kuma dama haka take so shiyasa bata cewa Reyhana ta sakko ba.
STORY CONTINUES BELOW

“Kaci gidanku bazaka ganta ba”Mommy ta fad’a a zuciyarta.
Inno tasa ta kawo masa abin sha har lokacin Reyhana bata fito ba Mommy kuma ta bar parlourn.
Wayarsa ya d’auka yayi dialing numbern Reyhana yaji ba kud’i dan haka yayi rance ya kirata.
Tana jin wayarta tana ringing tasan shine,ya kira kusan 3× amma bata d’aga ba.
Please pick my call am sorry.
Ya tura mata,tana karantawa taji tausayinsa ya kamata ta sani haka kawai baze kashe wayarsa ba dole sede da dalili.
Tana cikin wannan tunaninne tajiyo kukan baby da alama ta tashi.Sosai take tsala ihu Mommy kuma tana d’akinta ta shiga toilet inno ma tana sashen d’akinta bata jiyo ba.
Reyhana jin shiru Mommy bata shigo da baby ba yasa ta sauka dan ta kasa jure kukan da babynta take😜
Wani sanyi Ahmad yaji a ransa ganin Reyhana kukan babyn ma be damesa ba.
‘Karfin hali tayi bata ce komai ba se tsayawa datai tana jira ya mi’ka mata.
Mi’ka mata yayi idanuwansa yana kanta,ita kuwa bata bari sun had’a ido ba ta kar’ba.
Ya kula da yanayin kumburin fuskarta da idanuwanta take yaji tausayinta.
“Reyhana please kiyi ha’kuri kiyi min magana dan Allah”. Ya fad’a a raunane.
“Reyhana baki yarda da abinda na fad’a maki bane ? kinsan bazan barki ba ina sani koh please ki amsa min i am sorry”.
” Please ka barni yanzu de kaga kuka take”.Ta fad’a.
“Toh ki zauna mana anan ki…”
Be ‘kare ba sega wasu ba’kin suna shigowa parlourn,dan haka dole ya basu guri ya fita haraba ya zauna a kujera dake wajen.
Umma ya kira yake fad’a mata tayi masa fad’a ,tace laifinsa ne.
Reyhana zama tayi ta bata mama tasha tukun ta mi’ka musu.Mommy ta fito suka gaisa da ba’kin.
Ahmad kuwa yana waje har lokaci ya sake ja ,kiran wayarta ya sake yi again shiru kuma tana d’aki ta lura da kiran ta’ki picking.
“Am very sorry please forgive me” Ya sake tura mata text.
Tana karance text d’in ya sake kira seda ta kusa tsinkewa tayi picking.
“Azizaty kina son kasheni ne?”
“Mey kuma nayi?” Cewar Reyhana.
“Baki sani bama? Please ki saurareni dan Allah kiyi ha’kuri”. Ya fad’a.
” Kin ha’kura?”Ya tamabaya.
Shiru tayi bata ce komai ba.
“Please badan ni ba”. Ahmad ya fad’a.
” Toh naji”.Reyhana ta fad’a.
“Thank you so much Azizaty ,toh ya jikinki?”. Ya tamabaya.
” Da sau’ki”.Ta amsa.
“Are you sure?”
“Sure”. Ta amsa.
” Sannu my Azizaty nasan babynmu ta baki wahala”.
“Maman baby wane sunan aka sama mana?” Ya tambaya.
“Uh…sunan Umma”. Ta amsa.
” Are you serious? “Ya tambaya yana me mamaki dan sam be kawo hakan ba.
” Yes”.Ta amsa.
“Nagode sosai,zan kira Umma yanzu na fad’a mata”.Ahmad ya fad’a.
” Kaga ma tana kirana”.Reyhana ta fad’a.
“Ok toh bara na katse ki amsa i will call u back”. Ya fad’a.
Bayan tayi picking call na umma tayi mata barka sannan ta sake bata ha’kuri.
Suna gama waya da umma Ahmad ya sake kira.
” Azizaty ban gaji da ganinki ba fa keda baby ya za’ayi ne?”
“Ga baki basu tafi ba”.Ta fad’a.
” Azizaty kinsan ya za’ai?”
“A’a”. Ta fad’a.
” Anjima da maghrib zan dawo tare da umma ma zamu zo kinga lokacin Abba ma ya dawo koh?”
“Eh”. Ta amsa.
” Toh yanzu de kiyi wa Mommy magana zan tafi se miyi sallama”.Ahmad ya fad’a.
“Toh”. Ta amsa.
Tana gama wayar ne ma sega Mommy ta shigo.
” Mommy ga Ahmad ze tafi yace zakuyi sallama”Reyhana ta fad’a.
“Uhm waya kukayi kenan”. Mommy ta fad’a tare da ta’be baki.
” Yaran yanzu baku da zuciya”.Mommy ta fad’a.
“Mommy kuka fa take shine naje kar’barta”.Cewar Reyhana.
“Rabu dani “. Mommy ta fad’a.
Daga haka ta fita sukai sallama dashi.Wajen aiki ya wuce se wajen 4pm ya tashi kafin yaje gidan umma ya tsaya a store yayi wa Reyhana ‘yan siyayyan mey jego dede halin sa.
***
Around 6:40pm suka je gidan su Reyhana,har da’ki Mommy tayi mata iso shima Ahmad d’in tare da ita ya shigo.
Bayan sun gaggaisa Mommy ta fita ,Reyhana ce ta rage a d’akin sesu Umma.
“Umma Reyhana ta miki ta’kwara fah”. Ahmad ya fad’a.
” Toh! mashaAllah an gode Allah, Allah ya raya mana AISHA”.
“Ameen “. Suka amsa.
Suna zaune Abba ya dawo shima ya shigo suka gaisa dasu,lokacin da zasu tafi ya ajje kayan da ya siyo.
A waje Ahmad ya ke’be da Abba ya bashi ha’kuri akan abinda ya faru Abba yace komai ya wuce.
Mommy bayan sun tafi da ta shigo taga kayan kawai ta’be baki tayi bata ce komai ba.
Se lokacin Reyhana ta samu tayi wanka akaiwa baby ma ,nan su Ikram sukai ta rangad’a mata pic iri-iri.
Kusan kullum Ahmad seya zo ya dubasu idan ya tashi daga aiki,a haka kwanaki suka ja har ranar suna tazo.
Anyi shirye-shirye sosai komai Mommy sun tanada Ahmad ya aiko da ragon suna aka yanka yarinya taci suna AISHA Mommy taji ba dad’i sede bata nuna ba.
Nasreen za’a ke kiranta dashi,tasha ado daga ita har mey jego Reyhana swiss lace purple me white torches tasa se necklace silver Ikram ta rangad’a mata d’auri sekace amarya.
Ansha hotuna ‘yan uwa da abokan arz’iki sun hallara,Ahmad da yamma shida abokansa uku suka zo se Umma da wasu sisters daga zaria.
Reyhana dama ta tanadar musu abinci da sauran lemuna ta ajje dan haka da suka zo ta basu,sukai hotuna suma.
Bayan an watse daga Nasreen har Reyhana sun gaji sosai ana wa Nasreen wanka tayi bacci Reyhana ma wannan tayi tasha tea ta kwanta.
Nima pen d’ina na ajje na kwanta😀
AR²💖
Washegari gajiyar da dama-dama sede Nasreen tasha bacci dan har lokacin bata farka ba.
Har tayi wanka tayi breakfast Nasreen bata tashi ba,koda ta duba wayarta taga missed call na Ahmad ya kira tana bacci dan haka tayi calling ba.
Kira d’aya tayi masa yayi picking.

“Ummu Nasreen”. Ahmad ya kira.
“Abu Nasreen”. Reyhana ta fad’a itama.
” Ina kwana “.Ta gaisheshi.
” Lafiya lao Azizaty,ya gajiyarku?”Ahmad ya amsa.
“Gajiya ansha ta,har yanzu bacci take”. Ta fad’a.
“Allah sarki babyna du mutane sun wahalar min da ita”.Ahmad ya fad’a.
” Sannu mey baby”.Reyhana ta fad’a cikin zolaya.
“Ha! Toh ai gaskiya na fad’a”. Cewar Ahmad yana dariya.
” Toh nikuma fa banfita gajiya ba?” Reyhana ta fad’a.
“Iyye! Kishi” Ahmad ya fad’a.
“Haba kinsan da ina kusa da nayi maki tausa”.Ahmad ya fad’a.
” Nayi missing Azizaty ta ,your cooking pretty face everything yours Ummu Nasreen “.+
” Me too”.Reyhana ta fad’a.
“Toh yanzu kayi breakfast?” Ta tambaya.
“Tea kawai nasha,yanzu zan fita ma”. Ahmad ya fad’a.
” Please ka samu kaci wani abun ko a wajen aikin ne”.Cewar Reyhana tana mey nuna damuwa.
“Ok Azizaty i will”. Ya fad’a.
” Toh bari na barka ka shirya”.Ta fad’a.
“Ok ki shafamin kan babyna i love you all”. Ya fad’a.
” Love you too,Allah ya kare mana kai”.
“Ameen”. Ya amsa.
Daga haka sukai sallama kowannensu fuskarsa d’auke da murmushi cikin ransu suna ‘kara jin son junansu”.
Ba jimawa Nasreen ta tashi ,da kuka ta farka dan yunwa da take ji.Ta ded’e tana shan nono tukun aka yi mata wanka.
Komai ya cigaba da gudana, Nasreen har bayan suna ana zuwa barka ga kayan gudumawa da ake bawa Reyhana yarinyar tayi goshi sosai banda kayan da Abba ya ‘karo mata akan wanda su Umma suka kawo na barka.
Ikram idan suna gida itace me d’aukan Nasreen Reyhana hutawarta take ,yarinyar ana ji da ita a gidannan Ahmad ma yana yawan zuwa baya kwana uku beje ba.
Umma ma tana yawan kiransu su gaisa taji ya ta’kwararta.
3weeks later,Ahmad yana ta irga musu kwanakinsu bashida buri su cika kwana 40 su dawo baya jin dad’in gidan kusan koyaushe yana unguwarsu wajen abokansa.
***
Mommy yau tai shirinta na zuwa gidan Anty Asma’u dan tunda Reyhana ta haihu bata samu ta fita ba.
” Mommy dan Allah ku dawo da wuri saboda wankan Nasreen”.Reyhana ta fad’a.
“Yau ke zaki mata da kanki ai gara ki koya”. Mommy ta fad’a.
” Cabb! Kina so nasa mata sabulu a hanci”. Reyhana ta fad’a.
“Gaki gata kika samata kyasan yadda kikai”. Mommy ta fad’a.
Walida da tun tuni ta gama shiryawa Mommy take jira kawai su tafi.
STORY CONTINUES BELOW

” lala Yaya baby Nasreen tayi pupu”.Walida ta fad’a tana toshe hanci.
“Ga babarta ta wanke mata danni na gama nawa”. Mommy ta fad’a.
” Kai Mommy nifa ban iya ba”.Reyhana ta fad’a.
“Zaki iya ne, ga inno can kice ta cire mata danni nayi nan,Walida taho mi tafi”. Mommy ta fad’a tana sa’kala Jakarta.
” Se kun dawo”.Ta fad’a.
“Muhmm! Me d’oyin kashi”. Reyhana ta fad’a lokacinda Nasreen ta kalleta.
Haka nan ta tashi ta cire mata tana yi tana toshe hanci.
***
Mommy a d’an ‘kan’kanin lokaci ta isa gidan Anty Asma’un.
Suna parlour ita da yaranta.” Oyoyo Walida”.Anty ta fad’a tare da nufo inda suke.
Walida tana gaisheta ta nufi inda Ameera take,kusan itace sa’arta sukuwa Mommy suka tafi d’aki.
“Ya masu jego ?”Anty ta tambaya.
” Mey jego tana nan qalau ita da baby”.Mommy ta amsa.
“Saura ‘yan satittika su koma koh?” Cewar Anty.
“Hmm!” Mommy ta furta .
“Ya hmm! da wani abune?” Anty ta tambaya tana neman ‘karin bayani.
“Kusan de”. Cewar Mommy.
” Mey fah?” Anty ta tambaya.
“Nifa ba maganar komawa da yarinyar nan zatai”. Mommy ta fad’a.
” Toh! dalili?” Ta tambaya.
“Nifa bazan yarda da irin wannan rayuwar ba ta gidan Ahmad Reyhana ba class d’insa bace ki duba kiga nauyi ya ‘karu a kansa idan da yana kula da mace d’aya toh yanzu ga nauyin babynnan abin is not easy”. Mommy ta fad’a.
” Amma fa kin matsa dayawa kina tunanin Abbanta ze bar faruwar hakan?”Cewar Anty Asma’u.
“Barni dashi nasan ta inda zan ‘bullo masa”. Mommy ta fad’a.
“Su kuma ya zaki dasu?” Anty ta tambaya.
“Wannan bame wuya bane Reyhana ba kamar Ikram take ba,taimakon rayuwarta zanyi ita bata san kanta ba ita so ya rufe mata ido bazan zuba ido ta sake samun cikin na biyu ba gara tun wuri na dakatar dama rabon ‘yace ya had’asu”.Mommy ta fad’a.
“Maryam kenan ,toh Allah ya saww’ake deh”. Anty ta fad’a.
” Yanzu Toh yaushe zaki fad’a ma Reyhana d’in?” Ta tambaya.
“Nan bada jimawa ba”. Mommy ta fad’a.
Daga nan suka tsindima wata hirar ta daban.
Reyhana kuwa a gida tana ta fama da Nasreen dan ta’ki komawa bacci gashi ta barta a d’aki ita d’ai tasa ihu Ikram bata dawo ba balle ta taya ta ,inno kuma ta fita.
Ahmad daga wajen aiki ya tashi da wuri,wajen 4pm yazo gidansu Reyhana. Har lokacin Mommy bata dawo ba ,kiranta yayi a waya ya fad’a mata yana haraba tace ya shigo.
A parlour ya zauna chan ba dad’ewa ta fito Nasreen a hannunta.
Murmushi ya sakar mata me ‘kayatarwa itama ta mayar masa,be jira ta zauna ba ya mi’ke domin kar’bar Nasreen.
” Ummu Nasreen irin wannan kyau haka”.Ahmad ya fad’a.
Kuma powder ne da lipstick kawai ko kwalli bata sa ba,tayi kyau sosai cikin green d’in atamfar.
“Babyna ta gane ni kinga tana mini murmushi”. Ahmad ya fad’a yana ‘ko’karin zama.
Itama Reyhana zama tayi a kujerar dayake three seater ce.
” Watoh har ta fara gane ka?”Cewar Reyhana.
“Ehmana baki gani ba taga mey kama da ita”. Ya fad’a.
” Sonkai koh”.Ta fad’a.
“Mommy bata nan?” Ya tamabaya.
“Ta fita d’azu”. Ta amsa.
” Yau ke aka bari da babyn tamu,karfa kice zaki mata wanka karki sa mata ruwa a hanci”.Ahmad ya fad’a.
“Aiko na iya”. Reyhana ta fad’a.
” No sekun dawo zaki dinga yi mata”.Ya fad’a.
“Kin fara had’a muku kayan ku de koh?”
“Wane kaya ana zaune lau,sekace gobe zamu komo”. Reyhana ta fad’a.
” Lalle just kwanaki ne fah,gara ma ki fara shiri dan kun kusa komo wa keda baby Nasreen “.
Tashi tayi ta tafi kitchen ta had’o masa abunsha da snacks ta kawo masa.Hira sosai sukai tayi har Ikram ta dawo Nasreen tayi bacci ta kaita d’aki,se kusan maghrib ya tafi har lokacin Mommy bata dawo ba.
Se to 8pm tukun ,ba dad’ewa Abba ya dawo.Mommy se lokacin akai wa Nasreen wanka,Reyhana kuwa bayan tafiyar Ahmad.
Mommy maganar tana cinta amma ta kasa fad’a wa Abba,a kwana a tashi Reyhana sunyi kwana 37 Mommy bata yi wa Reyhana maganar komawa ba.
Shikuwa Ahmad kullum cikin lissafi dan yanzu a tunaninsa baza suyi 5days basu dawo ba,dan har siyayyar ‘yan kayan stuffs yayi musu jiran dawowarsu kawai yake.
Mommy yau de ta d’au alwashin fad’a wa Abba duk abinda ke ranta,around 8:32pm bayan sun gama dinner ta shiga d’akinsa lokacin yana ‘yan danne-danne a phone d’insa.
” Abban Reyhana ina so zami magana ne”.Mommy ta fad’a tana tsaye.
“Toh shigo ina jinki”. Ya fad’a tare da ajje wayar gefe.
Mommy waje ta samu ta zauna a kan gadon tana tunanin ta inda zata fara.
” Dama akan Reyhana ne,ina nufin komawarta”.Mommy ta fad’a.
“Toh ina sauraro”. Ya fad’a yana ‘kara tattaro hankalinsa gareta.
” A gaskiya nifa bazan yadda yarinyar nan ta koma gidanta ba”.Mommy ta fad’a.
Kuma yadda take maganar zaka gane da gaske take.Abba zama ya gyara yana kallon ikon Allah.
“Toh bazata koma ba a gidanki zata cigaba da zaman auren kokuwa mey kike nufi?” Abba ya tambaya.
“Ina nufin Ahmad ya sawwa’ke mata”. Ta amsa ba tare da ta nuna alamar damuwa ba.
” What!” Abba yayi exclaiming cikeda nuna damuwa.