ARZIQI RABO CHAPTER C KARSHE
Lokacin da ya dawo gida su Umma na falo yana jiyo su ita da Zainab,d’akinsa ya shiga ya zauna yana ta tunano Nasreen.+
Se yanzu ya sake gane rashin kyautawar da yayi na rashin bata kulawar da ta wajaba a kansa.
°°°
Se wajen maghrib daya fito zeje masjid Zainab ta ganshi.

“Laa dama ka dawo gida”.
” Eh ai ban jima da dawowar ba”. Ya amsa.
“Masallaci zaka?” Ta tambaya.
“Uhm”. Ya amsa.
” Toh seka dawo”. Ta fad’a.
Zainab bayan fitarsa ta shiga kitchen had’a abincin dare.
***
Reyhana tana d’aki hankalinta ya d’aga Sameer yazo Nigeria d’azu ya kirata ya fad’a mata.Yanzu bata da ‘karyar da zata fad’a masa,bama shi kad’ai ba har Abba.Nasreen tuni tayi bacci ita kad’ai se juyi take ta kasa bacci tunani ya isheta.
Saudat ce abokiyar shawara yanzu kuma dare yayi sede gobe,abunda ya fad’o mata a rai kenan.Dakyar ta samu ta iya yin bacci.
***
Washegari da safe bayan ya gama shirinsa ya fito falo ,Zainab ya tarar tayi shirin school da alama ma shi take jira.Shi ya mance ma da kaita school se yanzu ya tina.
“Ina kwana yaya”. Ta gaisheshi.
” Lafiya lau”. Ya amsa.
‘Kokari yayi ya kauda idonsa daga kallonta dan kwalliyarta tana masa ‘kwarjini,sosai tayi mugun kyau.Doguwar riga blue tasa se rolling datai golden d’in mayafi ta sa’kala jakarta golden fuskarta tasha kwalliya ga maroon lipstick daya haskata.
“Ka shiryo kenan”.Umma ta fad’a sanda ta shigo falon.
” Eh d’azu na shigo mu gaisa kuma kin koma bacci,ina kwana”. Ya gaisheta.
“Lafiya lau,bazaka karya ba?” Ta tambaya.
“Eh se anjima”. Ya amsa.
” Toh sekun dawo”Ta fad’a.
Yana ficewa tabi bayansa,a cikin ranta tana jin dad’i musamman da taga sunyi ango shi yasa blue d’in shadda.
Cikin ‘kan’kanin lokaci ya kaita kafin ta fita daga motar ya ‘kara mata kud’in makaranta dukda ana bata daga gidansu.
•••
Yauma daga aiki be koma gida ba seya je school d’insu Nasreen,4pm lokacin yana tsaya a gate d’in yana tunanin yadda ze ganta.
Da’kyar mey gadi ya barshi ya shiga wani daga cikin malamanne ya kira Nasreen tazo.
“Kinsan wannan?” Suka tambayeta.
Seda ta tsaya na d’an lokaci tukun tace “Eh”.
Wata daga cikin malaman tace ” Ai gashi ma kamar su d’aya”.
Dama sun fito sallah basu koma ba dan haka ya kamo hannunta suka zauna daga wani bench a compound d’in makarantar.Ita de Nasreen tana jin d’ar-d’ar musamman idan ta tuna abinda Ummienta tace.
“Nide ummiena ta hanani kula mutanen waje”.Ta fad’a.
” Kinmanta ni Uncle ne? Na kawo maki wannan “.Ya ciro mata Twix guda biyu daga aljihunsa.
Aiko da sauri ta mi’ka hannu ta kar’be” Amma karka fad’a wa Ummiena kaji”.Ta fad’a harda zaro ido.
“Toh”. Ya amsa tare da kad’a kai.
STORY CONTINUES BELOW

“Karatu zaka koyamini wai?” Ta tambaya tana ‘bare ledar.
“Eh amma yanzu zaku shiga aji se anjima idan kun tashi ina waje ina jira”.
” Kai zaka kaini gida?”Ta tambaya.
“A’a”.
” Dan Allah ka kaini gida ,kullum kullum semun dad’e ake zuwa d’aukan mu”.
“Ai zanyi hira daku kafin a zo d’aukanku”.
Kai ta kad’a tana cigaba da shan chocolate d’inta.Ba jimawa ta koma aji,kamar yadda ya fad’a seda ya jira aka tashesu.
Tana fitowa ta ganshi a bakin gate da gudu ta ‘karasa inda yake taji dad’i ganin ya jira an tashesun kamar yadda ya fad’a mata.
Kan mota tasa ya d’orata suma sauran yaran ma’kotan nasu haka kafin driver yazo.
Littafinta ta bud’o se nuna masa H/W d’inta take da C/W,kusan seda suka ‘kara 15min driver yazo da sauri yaran suka je,Nasreen ce ‘karshe sam drivern be kula bama ya jasu suka tafi ita kuwa se waving bye take wa Ahmad.
Ya kasa dena murmushi har ya isa gida,ya ji dad’in yadda Nasreen ta sake jiki dashi dama hakan yake so.
Yana shiga gida be jima ba ya fito waje ,Zainab ya gani tana tahowa se sauri-sauri take daga gefenta kuwa wani saurayine da alama magana yake mata amma ta’ki sauraronsa.
Har ‘kofar gida yana biye da ita ,se a lokacin Zainab ta kula da Ahmad dake tsaye .Shikuwa yiyai kamar be gansu ba dan kauda kansa yayi gefe kamar besan da mutum a gurin ba.
“Assalamu Alaykum”. Yaji anyi masa sallama.
Se lokacin ya lura Zainab har ta shige gida.
Hannu ya mi’ka masa suka gaisa,ita kuwa Zainab data shiga gida wuf ta shige d’aki ko Umma bata ji sallamarta ba.
Tana cikin sa’ke-sa’kenta a d’aki taji shigowar Ahmad, kunya taji ta lullu’beta tana jiyo muryarsa yana magana da Umma gudun karya fad’awa Umma yasa tayi sauri ta fito.
” Zainab dama kin dawo?”Umma ta tambaya.
“Eh yanzu ban jima ba “. Ta amsa.
Tana had’a ido da Ahmad taga yayi mata murmushi ko ba’a fad’a ba tasan ma’anar murmushin,a take ta sauke kanta katsa.
Umma ce ta koma d’aki tabarsu a tsaye gun,Zainab ma da sauri zata juya ya tsaida ita da fad’in.
” An bani sa’ko”.
“Yaya sa’ko kuma?” Ta tambaya.
“Eh ba’konki na waje shi yace na fad’a miki”.
” Mey?” Ta tambaya tana had’e gira.
“Wai yana sonki”. Ya amsa.
Bata sake cewa komai ba ta koma d’aki ,kafin ya sake wata maganar yaga ta bace masa dan haka ya koma d’akinsa.
A d’aki tunani ta shiga yi shin wace amsa Ahmad ya bashi? Ko zeji haushi? wata zuciyarce tace mata” Be damu ba”.
Jitai ba dad’i dan batai tsammanin haka ba,a tunaninta ze nuna kishi a fuskarsa sede taga ba hakan ba harda ma yimata murmushi.
•••
Koyaushe Ahmad inde ya dawo daga aiki seya biya school d’insu Nasreen, ta saba dashi sosai har home work yake koya mata idan taje gida ta fad’a musu se sike tunanin ko Uncle na school ne.
Ta ‘bangaren Sageer kuwa abu kullum gaba yake ko abinci yanzu be fiya ci ba a d’aki yake zama ya’ki fitowa ga wani mugun rama da yayi Mommy tun abun baya damunta yanzu ya soma ,kuma tambayar duniya baze fad’a mata ba Reyhana ma ta’ki fad’ar abinda ke damunsa.
Reyhana kuwa data yiwa Saudat magana akan Sameer shawara ta bata akan ta cigaba da addu’a.
Yau wasu ‘kannen Umma banda mahaifiyar Zainab suka zo daga Zaria,sanda suka zo Ahmad baya nan se Zainab yau bata da lectures.
Tunda take da Ahmad basi ta’ba maganar Reyhana ko Nasreen da ita ba,yau tana jinsu Sister’s d’in Umma suna hirar zasi je gidansu Reyhana suga Nasreen.
Tana daga d’aki amma kunnanta yana kwashewa,ita jitai tsoro ya shigeta kada ace fa Ahmad ya dawo da Reyhana.
Umma tana kallo suka fita wajen 4pm,hadda yi mata siyayyar kayan biscuit.
Sanda suka shiga Walida suka tarar a falo, ita taje ta fad’awa Mommy da tana d’akinta Anty Asma’u tazo.
Da farko Mommy bata gane su ba seda sukai bayani.Anty Asma’u tasa Walida ta kira da tana d’akin Mommy.
°°°
Ahmad daga aiki ya wuce wajen Nasreen ,yana zuwa aka tashesu.Kamar koyaushe tana ganinsa ta ruga da gudu ta d’ale shi.
“Uncle ina chocolate d’ina?”
“Gata”.Ya d’akko a aljihunsa.
Tana tsalle ta kar’be suma sauran abokan tafiyarta ya basu nasu.
°°°
Reyhana datai waya da driver yake fad’a mata yana kwance baida lafiya dan haka daga gidan Saudat tayi makarantarsu Nasreen.
Daga gefen gate tai parking ta fito ,’yan tsirarin student dake wajen ta kalla ko zata ga Nasreen.
Daga can nesa ta hango Nasreen d’are-d’are a kan mota.Mutum taga tsaye a kusada Nasreen amma kuma ya juya baya.
‘Karasawa tayi har inda suke,seda ta ‘karasa kusa tukun Nasreen ta ganta.
” Ummie!!!”Ta kira sunanta da ‘karfi.
Ahmad daya ji ta ‘kwala kira ta ambaci Ummie hakan ya tabbatar masa Reyhana ce.Cak ya tsaya ya kasa motsi balle juyowa.
Da gudu ta ‘karaso inda Reyhana take ta rungumeta.
“Yau da kanki kika zo d’aukanmu?” Ta tambaya.
“Eh”. Reyhana ta amsa.
” Ummie kinga Uncle”.Nasreen ta fad’a tana nuna inda yake.
Se lokacin Reyhana ta dawo da kallonta kansa.
“Uncle kaga Ummiena”. Nasreen ta fad’a.
Ya rasa mey zeyi ,wata zuciyar tana cewa kar ya waigo ? “Toh idan ma be waigo ba ya zeyi baida choice dole ta ganshi”.Ya fad’a.
A sanyaye ya juyo idanunsa suka sauka kan Reyhana, wani irin blinking ido tayi tana so ta tantance gaske ko mafarki.
Suman tsaye tayi ta kasa ko motsi ganin ba mafarki take ba,duk cikinsu kowa ya kasa magana kuma basu dena kallon juna ba…1