AUREN FANSA CHAPTER 10 BY ✍🏾 NIMCYLUV

AUREN FANSA CHAPTER 10 BY ✍🏾 NIMCYLUV

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Baffa ne yabi bayan Grandson ɗin nasa da kallo yana mmki hali irin na Ibrahimul Khalel.

Not too long Ya Heemu ya dawo cikin ɗakin ɗauke da gorar ruwa yana kafawa a bakinsa tare kwankwaɗar ruwan da sauri da sauri kamar zai janye gorar ruwan zuwa cikinsa.

Yana gama sha yaja ya zauna dab da Baffa kansa a ƙasa amma jikinsa har yanzu was vibrate amma ko a fuska baza ka taɓa gane ai nayin abinda yake cikinsa a zcy ba.

Huci kawai yake yana fesar da iska hatta gashin kansa wanda suke a murmurɗe kamar anyi masa (Dada)

Sai da suka miƙe tsaye.

Baffa ya gyara zama yana ɗan daidaita nutsuwarsa cike da kamala da kuma haiba irinta kamilallun maza Baffa ya kalli Al’mustapha yace.

“Al’mustapha ina neman amincewar ka akan ka bawa jikana auran ƴar kuma jikata idan babu damuwa”

Wanda aka kira da Al’mustapha yaja gajeran numfashi tunanin halayyar Moha yake.

Yarinyar tana da wahalar sha’ani mai gane mata sai ya shirya.

Bata da tsoro sam ga tsaurin ido haɗi da zallar ƙuruciya, bata sanin dai-dai da abinda yake ba dai-dai ba, sai dai ita ɗin abin tausayi ce sosai.

Musamman idan ciwonta ya tashi ko da yake duk zafin ciwonta bai kama ƙafar na (Hawwa’u Jidderh, kulu kuma Julde ƴar makauniyar Abu Maleek ba).

Tana da rauni sosai amma shi kansa bai san mene rauninta ba, har gobe kuma abu guda yake sawa ta saduda shi kansa baya gane wannan lamari nata domin abun yana masa kama da JUYAYI.

rawar kai yay mata yawa over nutsuwarta ɗaya Ya Heemu gashi wani dalili na sawa ya cire dukkan wani hope nasa akan ɗan ƴar uwar tasa.

Idan Khalel baya kusa mgnar wa Mamansa za taji? Wazai mata tsawa ɗaya ta samu nutsuwa?

Baffa ne yay gyaran murya yace

“Alhj Al’mustapha kai muke saurare”

Numfasawa Alhj Al’mustapha yay kafin ya ɗaga kai ya kalli Aysuhtul humaira yaga taiwa Ya Heemu ƙuri da idanu kana ya mayar da kallonsa ga Ya Heemu yaga hankalinsa kwance kamar ba shi ya shiga tension ɗin daya shiga yanzu ba.

Kansa a ƙasa yana latsa Wayarsa mai ƙirar Iphone 12 max pro.

Cikin sanyin nutsuwa haɗi da kamala da kuma kamewa irinta mazan jiya masu sanin darajar na gaba dasu yace.

“Baffa Nima kamar ɗa nake gareka to bana da haufi akan dukkan wani shawara daka yanke akan wannan sabon al’amarin, yadda Jikar ka Aysuhtul humaira zata amince da sharaɗin ka haka nima zan amince da sharaɗin ka Baffa, ka amince ɗari bisa ɗari Allah yasa Albarka ya kaɗe fitina”

Ya ƙare maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa yana mai tausayin yarinyar tasa, wacce har yanzu bata san abinda yake mata ciwo ba, girman jiki ne kawai da Ubangiji ya bata.

Jinjina kai Baffa yay cike da gamsuwa da kuma girmama girman karamcin da Al’mustapha yay masa.

Kullum yana buƙatar kasancewar da yarinyar sa, amma baya samun damar haka.

Domin dashi da Baffa ba’a san wanda yafi son Moha ba, ƙarfin soyayyar da Baffa ya kewa Moha yasa gaba ɗaya ya dawo da zamanta wajansa, ganin haka yasa sauran jikokinsa dawowa wajansa baki ɗaya, Shoona, Hannah Sai kuma Sunaina ita wannan tana karatu waje sbd tana ɗan gaba dasu, Murgayiya Safa kam ƙulafucin uwa gareta kamar dai SARAUTA haka take, sometimes shike ɗaukan ƙafa yaje wajanta yana cewa yaje biko.

Tuna wannan karamcin na Al’mustapha yasa Baffa faɗin.

“duk da cewa ina da iko akan abinda zan aiwatar amma dole dai na nemi amincewar ka domin kai ka haifi Aysuhtul humaira, Ina gdy ƙwarai da wannan karamcin ka nuna min nima mahaifi nake gareka kamar yadda nake mahaifi a wajan Matarka (Aunty Meera)”.

Casbahar hannunsa ya ajjiye tsohun yasan me yake duk da cewa ya tsufa ainun amma sosai yake da himma da kuma saurin fahimtar abubuwa masu muhimmanci.

Yaransa ya kalla sannan ya kalli  jikokin nasa a nutse yace.

“Haruna fito min da dukkan abinda yake aljihun ka”

Baba Haroon ya sanya hannunsa ya ɗauko harfar kuɗi ta 500 wanda ya kasance 50k ne, kuɗin ya ajjiye gaban Baffa da sauri kuma yasa hannu ya ɗauki zoben daya faɗa daga cikin kuɗin.

Zoben Ya Heemu yabi da kallo sai kuma ya janye idanunsa yana maida kallonsa ga Wayarsa.

Baffan yace

“A bisa abinda yake faruwa ga yaran nan ni kuma na yanke nawa hukuncin da nake ganin shine dai-dai da abinda nai nazari, dan haka na bawa Omaru auran Aysuhtul humaira, bisa sadaki dubu hamsin Allah ya sawa Auran albarka”

Gaba ɗaya suka amsa da Ameen.

Nan Baba Haroon ya zama waliyin Ango Ya Omer sai Kawo Shuriem ya zama waliyin amarya.

Ya Omer wani hawayen farin ciki ne ya sakko daga cikin idanunsa ya rungome Baffa yana masa gdy.

Moha kam shiru tai sai zare fararan Idanunta masu sheƙi wanda kamarsu ya ƙara fita sak dana Ya Heemu.

Ji tayi abu mai girma da kuma nauyin gske ya danne mata kai.

Yayinda bugun zcyarta ya tsananta, ƙarfi da harbawar ko wacce ƙofa da take jikin zcyrta ya ƙaro fiye da ko wanne lokaci.

Cikin rashin makamar abinyi da kuma rashin gane ainahin abinda yake faruwa idanunta ya fara fidda wasu zafaffun hawaye mai fidda zafi da kuma kala, yadda hawayen suke gudu a saman farar ƙyakkyawar fuskarta zai sanya ka tabbatar hawayen bana jin daɗi bane sam-sam ko kaɗan.

Duk wannan abinda ake idanunta yana kan Ya Heemu ita kanta ba tace ga kallon da take masa ba.

Wasu abubuwa na shekarun baya suka fara dawowa gareta da tunanin, Shadow’n photon abin ya fara yawo cikin ƙwayar idanunta masu fidda ƙyallin zaiba.

Ya Heemu ya ajjiye wayarsa ba tare daya kalli kowa na wajan ba ya mayar da ganinsa kan Baffa yace

“Baffa ina da buƙata”

Shafa kansa Baffa yay yana mai jin so da kuma ƙaunar Ya Heemu na ƙara huda ƙofar jijiyoyin zcyarsa.

Cike da kulawa yace

“Haba zakina, faɗi ko mene indai maifi ƙarfina ba Tabbas zan maka”

Lumshe idanunsa Ya Heemu yay yana tsotsar laɓɓansa wanda suka gama yin jaaa sbd azabar da yake gana masu wajan cijesu.

Numfashinsa na fita ɗai ɗai yana samun daidaito a tsakiyar ƙahon zcyarsa wacce take wassafa masa dukkan abinda yake yana fesar da kuntun numfashi mai zafin gaske tare matsawa sosai wajan Baffa nasa cikin ƙasaitacciyar muryarsa wacce ya gama dai-dai ta yace.

“Aure na keso ka nema min, Nima yau na keson Auran ya kasance”

Jinjina kai Baffa Yay domin daman abinda yake jira kenan bashi da Burin daya huce ya ɗauki baƙaƙen yaran Ya Heemu wanda yake fatan su ɗauki baƙar fatarsa sbd jar fatar ta ishi idanunsa da gani.

Yana Murmushi yace

“Kada ka damu gaya min Wacece wacce kake so, kuma ƴar ina ce waye mahaifinta”

Idanunsa ya lumshe yana kokawa da Numfashinsa wanda ya ke son fallasa a sirin zcyarsa yace.

“Baffa Mumyn Arman na keso”

Ba Baffa ba hatta Moha da take ƙarama sai data ɗaga kai ta kalli Ya Heemu haka Ya Omer da sauran mutanan cikin ɗakin.

Sam Baffa bai mmki ba sbd Uncle ɗin Mannal ya jima da faɗa masa, kuma ya amince da haka sbd babu haramci ciki, fiyayyan halitta ma ya auri wacce ta girmesa so dukkan abinda za’ai koyi dashi bai huce nasa ba, kuma daman shekaru ai lamba ce kawai.

Kawo Shuriem yace “Khalel mariƙiyyar taka? Mahaifiyar Arman best friend ɗin Hjy Ruma fa?”

Ko kallan inda yake Ya Heemu bai kalla ba Baba Haroon yace

“ikon Allah kenan”

Uncle Aliyu kam Shiru kawai yay dan ba komai kake jin yay mgna ba, sai abu mai muhimmanci yanzu ma har yay Shiru sai kuma yace.

“Son a shekarunka? Baka son mure ƙuruciyar ka ne? Mannal fa, this is difficult dear age mate ɗin Mahaifiyar ka”

Alhj Al’mustapha yace

“Ai age is just a number ba dai shi yaji ya amince ba to Allahamdulillah ai, kawai ku saka albarka is better than talk”

Baffa yace “Aliyu kiramin Mahaifin Mannal”

Ba musu ya kira ya bawa Baffa suka gaisa Suna jin sanda mahaifin Mannal yace “ikon Allah”

Ya Heemu kam jikinsa yaja zuwa na Baffa yana yanayinsa na sauyawa ya shiga tasbihi a ransa yana ƙara kwantar da kansa jikin Baffa.+

STORY CONTINUES BELOW

  Kano state/Nassarawa G.r.a

Mannal na cikin ɗakin ta ta sauya kaya zuwa sleeping dress Black Silk short robe

Companyn La Perla.

Sai Aquaholic Slippers bedroom slippers kenan, ta rufe kanta da wata tattausar red hula mai gashi.

Tana zaune saman kujera tana operating system ɗinta sbd duba oder da tayi daga Dubai zuwa 9ja.

Cikin nutsuwa take danna keyboard ɗin system ɗin tana ƙara zaɓar wasu sabbin kaya wanda zata zuba Mall ɗinta.

Yadda take ɗan sauke ajjiyar Zcy da sauri da sauri kaɗai zai tabbatar maka cewa bata cikin hankalinta.

Amma a zahiri ka kalleta cewa zakai babu abinda yake damunta jan da idanunta yay ta ɗiga masa wani abu ya washe ta wanke fuskarta tass.

Amma har yanzu tsoro da kuma fargabar abinda zaizo ya dawo take domin tunda Dad ɗinta ya fita mgnar aurenta bai dawo gida ba shiyasa tsoro da fargaba shigeta sai dai bata bari yay tasiri a zcyarta ba bare abin ya taɓa rauninta.

Hamdala kawai take ga Allah domin da ace Ya Heemu ya samu nasara a kanta gwamma ko ɗan garuwa ne Dad ɗinta ya bata bare kuma ɗan uwanta Sufyan.

Turo ƙofar bedroom ɗin nata akai aka shigo tare dayin sallama.

Ba tare data ɗago kanta ba ta gyara zaman farin siririn glass ɗin idanunta wanda suke ɗan ƙara mata ƙarfin gani.

Kafin a hankali ta miƙa hannu ta ɗauki mug ɗin gabanta wanda yake ɗauke da haɗin fruits wanda yasha fresh milk.

Zame mug ɗin tayi cikin nutsuwa da ɗan dakewa tace “Wasalamu alaiki”

Kallonta Anuty Lubna tayi kafin tace.

“Dad ɗinki na son magana dake”

Jinjina kai kawai tayi tare da rufe system ɗin ta ɗauki hijab ta sanya saman kayan baccin tabi bayan Anuty Lubna.

Downstairs ta sakko ta samu Dad ɗinta zaune yana sanye da Jallabiya yana kallon tafsir ɗin Sheikh Imam Deedat Balarabe.

Sai coffee dake gabansa da kuma gashasshen naman zabo.

Zamewa tayi gefen ƙafafuwansa ta zauna tana ƙasa da kanta zcyrta na ɗan bugawa.

Gyara zama yay sosai ya bata dukkan nutsuwarsa yace “Khadijertou matsayin wa nake gareki?”

Kanta a ƙasa tace “You’re my father Dad!”

Jinjina kai yay yace

“Good”

Kallonta ya ƙarayi yace

“A matsayina na Mahaifinki kamar yadda kikace a karo na biyu na aurar dake, daman na farko bawai dan ina so bane, na rabu dake ne sbd ke zaki zauna dashi, a yanzu kuma nina zaɓa maki miji wanda zaiyi dai-dai da rayuwarki, na san har abada bazan taɓa dana sanin wannan auran ba koda ke zai zamana anyi maki ba dai-dai ba, wannan bai daman ba in dai ba wanda aka aura makin bane yace baya so”

Ita dai kanta a ƙasa amma sam bata gane komai abu ɗaya ta fahimta shi ne Dad ɗinta ya ɗaura mata Aure da Sufyan.

Kasa motsi tayi sai Ajjiyar zuciya da take saukewa, kafin ya ta ɗaga kai tace

“Dad kana da ikon yimin komai, nasan cewa baka son Abban Arman amma soyayyyar da nake masa ne yasa ka amince dashi, Dad indai zaka samun albarka ka daina fushi dani na amince da Sufyan matsayin miji”

Tattausan Murmushi Dad Yay mata yana shan coffee ɗinsa ya kalli Anuty Lubna yace “My dear explain to her”

Yana faɗin haka ya miƙe tsaye tare da nufar part ɗinsa.

Shiru Anuty Lubna tayi sai kallon juna kawai da suke, jin shirun yay yawa yasa Mannal cewa

“ki faɗa min menene, me kuke hiding keda Dad?”

Ɗauke kai Anuty Lubna tayi tace

“bada Sufyan aka ɗaura maki Aure ba da Captain Ibrahimul Khalel ne”

Miƙewa tsaye Mannal tayi tana nanata sunan can kuma tace

“Kamar dai na san sunan amma waye haka nakasa fahimta waye ne Captain”

Cikin tausayi da kuma rashin adalcin da akai mata tace

“Chief of Army Ibrahimul Khalel Ibrahim, wanda a yanzu ya sauya matsayi zuwa *Flight Officer* ma’ana dai (Ya Heemu)”.

Girgiza kai Mannal ta fara idanunta ya sauya kala fuskarta ta sauya kala tai jajir.

Jikinta ya ɗauki rawa tana jin zcyrta a cunkoshe idanunta ya fara duhu yana janyewa, bakinta na rawa tace

“Khalel? Ya Heemu my son?”

Sai kuma tai baya ta faɗi saman kujera babu numfashi, salati Anuty Lubna ta sanya da sauri ta fara kiran Dad ɗin Mannal kafin ta ɗauki ruwa mai sanyi ta shiga sheƙa mata, Dad kam yasan za’a rina yasan dole za taji wani iri amma bashi da wani zaɓi wanda ya huce haka.

Yana da tabbacin wata rana zatai masa gdy wannan auran zata zo masa da yaran data haifawa ɗan riƙon nata kuma mijinta a yanzu.

Mumy zama tayi kamar mahaukaciya ta shiga ihu tana fasa dukkan abinda tayi karo dashi.

Fitowa yay cikin nutsuwa da kamewa haɗi da kwanciyar hankali amma fuskarsa a ɗaure take tamau ba walwala kamar baƙin hadari.

A karo na farko yana sanye da wani tattausan farin voyal fari ƙal mai manyan zane sumar kansa sai sheƙi take sai kwance har ƙasan wuyansa.

Ya zura Dukkan hannayensa cikin aljihun wandon kasancewar rigar half body ce mai ƙaramin hannu.

Kana ganin kuma farar singlet ɗin dake jikinsa.

Sai baza ƙamshin turaren Arabian Ohud yake.

Duk abinda yake idanun Ummi a kansa da Anuty Meera wacce zuwanta kenan.

Sam bai kula dasu ba ya nufi downstairs zai sauka yaji Muryar Ummi tace.

“Ohh hello!”

Tsayawa yay tare da zaro hannunsa na dama yana ɗan sosa kansa da key ɗin motarsa.

Zama yay a armchair yana taune leɓansa tare da fesar da iska a tattaushe cikin sabuwar miskilar Muryarsa yace “Ummi”

Kallon tsaf tayi masa fuska ba walwala tace.

“Ashe baka da hankali Ibrahim? Ashe nice bani da hankali da nake tunanin kasan me kake?”

Lumshe idanunsa yay kana ya buɗe kamar bazai mgn ba yace “Ya rabb! Me Ibrahim yay da wannan sanyin safiyar Ummi?”

Haɗe fuska tayi tace “Kayi aure ba tare dana sani ba, amma ba wannan ne matsalar ba ace ka rasa wacce zata aura sai sa’ar uwarka? Kace kayi aure kenan? Kaga bana baƙin ciki da auran infact ma Am happy billahi amma wanne abu kayi me kaiwa Arman a matsayinsa na babban abokin ka? Wannan adalci ne ko mene ace ka auri mahaifiyar Amininka Goodness”

Ta ƙare maganar tana sauke numfashi sbd sam bata iya faɗa ba bata kuma jure masa.

Zamewa yay ya ɗura kansa saman cinyarta tare da kama hannunta ya ɗura saman sumar kansa Muryarsa bata fita sbd abinda ya keji a zcyarsa wanda yake fama dashi Shekara da shekaru baya jin kuma zai iya rabuwa da abun domin mganin abun ya suɓuce masa.

Cikin dakewa da juriya yace

“Ayyah! Ummi kada ki fara da haka ki shafa kaina ki sawa Ibrahimul Khalel ɗinki albarka, kada ki manta hakan ba kaifi bane domin shekaru number ce, kuma hakan bazai taɓa zama haramun ba, sau tari ni mutane suke haramta abinda ya zama halak ga mutane, miye laifin Ya Heemu dan ya auri age mate ɗin Umminsa, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama shima ya auri wacce ta girmesa kinga hakan ba laifi dan Allah Ummi kada kice komai ki sawa Abokin ki Albarka, kuma na wannan Auran…,”

Sai kuma yay Shiru Anuty Meera tana jan numfashi tace “Khalel kalle ni nan?” Kallonta yay yana jiran yaji ita kuma mene za tace

“Ina biye maka ne sbd sanin halinka, na sanka sanin da kai kanka baka san dashi ma, mai yasa a gabanka kuma akan idanunka kana ji kana gani zaka bari Aysuhtul humaira ta auri waninka ka sanya ido ka zama masu sheida aure ko?”

Miƙewa yay ba tare da yace komai da sauri ta Miƙe tace “mgn nake kana jina”

Ba tare daya kalleta ba yace “Ke ba’a gidan Mijinki kenan ba ne? To ita jiƙata zaki kisha da ba zaki aurar da ita ba?”

Gabansa taja ta tsaya idanunta cike da ɓacin rai tace

“Kai kasan a girme na girme ka, na kwana da sanin kana hana idanunka bacci akan zazzafar soyayyar da kakewa Moha, ko kuma so kake ka cutar da kanka akan abinda kake da iko akai? Nasan ciwon zcyr daya kamaka duk a dalilin Aysuhtul humaira”

Da sauri Ummi ta miƙe tsaye tana dafe ƙirjinta jikin ciwon zcy yasa hankalin ta ya tashi kuma ma wai Ya Heemunta keda wannan wahalallan ciwon.

Ya Heemu kam ƙuri Yay wa Anuty Meera da ido kafin ya ɗan taune bakinsa ya saka hannayensa ya ɗaga Anuty Meera cak ya matsar da ita gefe da sassarfa kuma ya fara taka strains ɗin yana haɗa bibbiyu.

Yana shiga motarsa Wayarsa tayi ƙara connecting yay da bluetooth cikin fesar da iska ya shiga danna wani mahaukacin horn kana yay waje da gudu yana faɗin “Uhm Wasallamu Alaika Dad”

Dad yana zaune yana jin yadda Mannal ke fashe fashe yace “Ibrahimul Khalel ka hanzarta zuwa ɗauka kan matarka, domin dukkan abinda data ƙara fasa min a gida kai ta ɗurawa nauyi domin saika biyani, idan ka ɓata lokaci kuma zaka zo ka sameta a waje”

Yana faɗin hakan ya kashe kira, wani ƙyakƙyawan tsaki Ya Heemu yaja domin shi ya gama da wannan shirin barin ƙasar yake ma, domin idan ya zauna Tabbas zcyarsa zata iya yin bindiga.

Amma dole ya zame masa ya ɗauko ta tunda abu yake nema gareta.

Gidan Baffa ya nufa domin yi masa sallama, yana shiga yaga ba kowa tsakar gidan juya idanunsa yay kamar zai koma sai kuma ya nufi cikin ɗakin Baffa a ciki ya samu Inna Shoona da Hannah sai Amatu budurwar Areef.

Idanunsa ne ya sauka akan Moha tana kwance jikin Baffa yana mata tofi yana shafa mata, jikinta gaba ɗaya ya saki numfashinta na wani irin fita da sauri kallo ɗaya yay mata yasan cewa ciwon ta ne ya motsa wanda ta gajesa wajan mahaifiyarta.

Inna tace “Yawwa Mijin yanzu ake ta ƙoƙarin kiran mijinta number baya tafiya wai yaje Zaria”

Bai ce komai ba ya juya zai fita sbd he can’t wait any longer idan yace zai tsaya za’a iya samun matsala, salatin da Inna ta rafka shiyasa Ya Heemu jiyowa a 180 bai tsaya jiran komai ya sunkuce ta zuwa jikinsa ya riƙeta sosai jinta jikinsa yasa ta numfashinta ƙara sarƙewa ba kin Ya Heemu na rawa yace “No please Humairahhhhhh!” Sai kuma yay waje kai tsaye asibiti ya nufa da ita aka sanya mata drip akai mata injection yana zaune yana ganin Ummi dasu Kawo Shuriem na kiransa yaƙi ɗagawa daga ƙarshe kuma Alhj Al’mustapha ya kira shima yaƙi ɗagawa, ana gama yi mata komai har lokacin bacci take ya ɗauke ya nufi Kano da ita tana kwance a saman kujera ya ɗura kanta a cinyarsa.

Bai isa Kano ba sai bayan Asr lokacin harya kashe Wayarsa sbd kiran da Ya Omer yake masa.

Yana fitowa daga motar tana farkawa ba tare da yace komai ba yay gaba ganin hakan yasa ta shiga taka ƙafafuwanta a hankali tana jin jira na ɗibanta, a bakin ƙofar shiga parlo suka haɗu da Dad, Dad ko sauraran Ya Heemu bai ba ya fice abinsa.

Mumy har lokacin fashe fashe take duk ta yayyanke ta fita hayyacinta sai faɗin ɗan cikina shi zai zama mijina hauka ake? Harɗe hannayensa yay ya tsaya cak tsakiyar Parlo yana kallon ta yasan cewa tana sane take dukan haukan ta ɗauka hakan zai sanya Dad wargatsa auran, Wata jibgegegiyar mage ce ta fara ihu sbd Glass ɗin daya cake ta kai tsaye kuma magen ta nufi inda Mannal take, cak Mumy ta tsaya da abinda take idanunta ya firfito da sauri ta juya zatai waje suka haɗa ido da Ya Heemu wanda yake raɓe sai Moha da take gefensa kana Kallonta kasan cewa tana cikin halin jinya.

Tsayawa Mumy tayi shi kam Kallonta kawai yake da kayan jikinta domin ko bra babu tun kayan baccin data sanya jiya ne ƙilan ko sallah ma ba tayi ba.

Wani kuka magen tayi tana jijjiga hakan yasa Mumy ƙara yin gaba idanunta a rufe tsoro ya kamata don a duniya babu abinda take tsoro irin mage, kusan hakan take ga Moha domin tunda taji kukan magen hawayen tsoro ya fara zubu mata ta ƙara matsawa bayan Ya Heemu kamar zata riƙesa amma tana jin tsoron ruwan masifar sa.

A hankali ya fara takawa zuwa inda Mumy take yana gab da ƙara sawa magen tai wani ihu tare dayin tsalle.

Mumy da Moha a tare suka saki ihu kowa yayo kan Ya Heemu a dai-dai lokacin kuma magen ta sauka bayan Mumy hakan yasa Mumy tayi kan Ya Heemu tana sakin wani firgitaccen ihu, Moha ma tsoran ne ya kamata tayo wajan Ya Heemu a tare suka rungomesa Mumy ta rungomesa ta kama Moha ta rungomesa ta baya da sauri ya runtse idanunsa yana fisgo Numfashinsa tare da ƙoƙarin zare Mumy daga jikinsa ita kuma tana ƙara shigewa jikinsa tana tura fuskarta a ƙirjinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *